SONE AJALINA Part 2
.
Sunyi nisa kafin yatsaida motar gefen hanya, yajuya dubansa gareta yakasa cewa komai. "yaya sultan meyake faruwa, badai tasamu matsala ba"? "Hutawa zamuyi nagaji da tuk'i". "Haba yaya d'an nanda nan d'in"? yayi murmushi kawai kafin yace "tambayarki zanyi, banaso kib'uyemun komai Hafsat". Tadaidaita nutsuwarta ta zuba masa na mujiya, lolx "Naga duk wanda yazo wajenki korarsa kikeyi, kinada wanda kike sone ko kuma baki ra'ayin aure yanzune"? wani malalacin murmushi tasake aranta kuwa tace meyakawo wannan tambayar, azahiri kuma cewa tayi "yaya inada ra'ayin aure yanzu, even if i have any bansamu wanda yamun ba to". A hak'ik'anin gaskiya tun baki girmaba ranarda aka kawoki wajen Inna nafad'a a kogin k'aunarki, nayaba da d'abiunki da kuma surar kyau da Allah yabaki".
.
Ta d'ago da sauri ta kalle shi, yad'an kashe ido d'aya yace "Yes Hafsat, ke kanki kinsan me kyauce, dole a soki inafatan nayi nasaran d'aukar abata tazama nawa ni kad'ai". . sosai kunya yakamata batayi tunanin hakaba amma idan tace bata sonshi batakyauta ba, da kunyama tace masa a'a, to mema zai hana ta soshi tunda bawanda take so.. "Kiyi magana mana Hafsa, nayi miki nima kina sona? "Yaya kadaina wannan wasar kana so Inna tamun fad'a nadad'e ko? "Hafsa ba'a wasa da irin wannan maganar, ki fad'amun kina SOna"? "yaya taya za'ayi nace bana sonka, ina sonka Allah yatabbatar mana da alkairi". wani ajiyan zuciya yayi, fuskarshi kad'ai ta nuna yanayin dayake ciki na farinciki. "Nagode Nagode Hafsa". . ko rufe motar baiyiba yanufi cikin gidan da gudu, bai lura da suwaye a falon ba yafad'a ajikin Momy yana murmushi kamar k'aramin yaro. "Sultan wani kyautar kasamu yau kake irin wannan farinciki?" Baa dake cin abincinshi yace "Yarone ai tunda basuda banbanci, yara sun girma basu tunanin aure musamman Muhammadu (JUNAID)... Junaid da shigowarsa kenan yace "Baa me nayi nikuma"? "Aure nakeso kayi Junaid, bakaganin yanda ka girma ko? yaci ace kanada yara yanzu..." . An fama masa yanda yake masa k'aik'ayi, yana son yara sosai wacce yayita dakon soyayyarta yake mafarkin ta haifa masa yara yanzu tamasa nisa, yashare hawayen daya gangaro mishi yace "Baa bansamu wacce nake soba haryanzu, idan ba laifi ku auramun wacce kuke so". . Haulat tayi caraf tace "Baa yanada 'yanmata wallahi k'in kulasu yakeyi... hararar daya watsa mata yasata yin shiru. cikin tausayawa Momy tace "indai hakane akwai SADEEYA 'yar k'awata kasanta ai, kaje kushirya yarinyar tanada Hankali". "TO" . kawai yace yanemi waje yazauna. Sultan yace "nima inada albishir, nasamu mata yau". Kowa yafad'ad'a fara'arsa banda Junaid daya zuba masa ido yana neman k'arin bayani. Nasan zakuyi farinciki da zab'ina, HAFSAT ce ta amince zata aureni". . Kamar sauk'ar aradu maganar ta doki Junaid, yamik'e da baya da baya yake tafiya har yafice ad'akin yanufi part d'insa. . . Bawanda yalura da halin da yashiga sai Sultan, Shima sai yanemi farincikin yarasa jikinsa yayi sanyi sosai, su Baa kuwa sai murna sukeyi suna yimasa fatan alkairi, Haulat harda rawarta ta dad'e tana fatan Hafsat tashigo cikin zuri'arsu dukda tafi sha'awar Junaid ya aureta amma tunda baisamuba itadai tana murna. . . Asanyaye shima yamik'e yabar wajen yanufi wajen Junaid. Kuka yakeyi sosai kamar bashiba, tsoro da fargaba da mamakine suka mamaye zuciyar Sultan, Da sauri yakoma tunkafin yaganshi. . . "Me yake damun Broz, me aka mishi lokaci guda yake irin wannan kukan"? shima sai yafashe da kuka da iya k'arfinsa. . .
.
Ko waye ya rarrashesu oho nidai naga duk sunyi shiru. Bayan Sati D'aya. Soyayyah tsakanin Sultan da Hafsta ba'a magana, kullum suna tare har Innah saida tafahimci komai. Ta b'angaren iyayen Sultan farinciki suke sosai abu har ya karad'a dangi. Baa baiyi k'asa a gwiwaba yak'ira amininsa yashaida masa sunyi kusan had'a yaransu Aure, SULTAN da HAFSAT. Sosai mahaifin Hafsat yayi murna suka tsaida magana akan tana gama sec. za'ayi Auren. Momynsu Haneefa taji dad'i ko ta sanadin auren zasu samu su zo Bauchi.
...................................................................
"Momy nifa banason yarinyar nan tacika fitina dayawa, kullum sai ta k'irani yafi sau goma idan band'auka ba tayitamun kuka, plz mom kibar maganar aurennan yanzu ahankali zan samo irin wacce narasa abaya". "Ah ah Junaid kanada lafiya kuwa? menene don tak'ira ka sau goma, kana so kasani naji kunyane tunda angama magana yanzu kace baka so? to naji fad'amun wacce irin macece karasa abayan, iya zamana dakai ban tab'ajin labarin ka nemi wata yarinya ba, nafara zargin aljana ce ta aureka, yau zanfara karb'a maka ruwan rubutu kanasha ko za'a dace". Murmushi yasake "Mom lafiya ta lau kidai tayani addu'a kawai amma ina cikin wani hali, jikina yana bani abu 2, kodai na mutu banyi aure ba ko kuma SO yazama AJALINA"! Mamaki yakama Momy tazuba masa ido na tsawon lokaci "Ta yaya SO zai zama AJALINKA a ina take yarinyar". "Tayi aure ne". yabata amsa kai tsaye. Tausayin shi ya kamata tace "Zaka samu wacce tafita, Sauda yawa mutum yakansa kanshi a k'unci saboda wani, alhalin wanin bai san yanayi ba, ko tayi aure ko batayi ba dole kacire ta aranka Junaid, nasan wacce kake so bana so kayi gigin da d'an uwanka zai gane halin da kake ciki, shiyasa nahad'a ka da sadeeya.... kallon mamaki yake binta dashi. "k'warai kuwa nasan wacce kake so, kada kabari shaid'an ya raba muku zumuncin ku, idan har kafi k'arfin zuciyar ka to cireta aranka bazai baka wahala ba". Ya langwab'ar da kansa yad'aura akafad'ar ta. "Nayi tunanin ni kad'ai nasan inason Hafsa' ashe kema kin sani, bansan yaya akayi nafara sonta ba tsintar kaina nayi da haka, a lokacin da bazai mun amfani ba, na haramta wa kaina ita a halin yanzu saboda ina son d'an uwana, amma wlh da wanine sai inda k'arfina yak'are saboda nasan duk duniya nafi kowa son ta Momy, bawanda zai kaini sonta, sanadiyyar haka nakamu da hawan jini babu wanda yasani har nagama jinya ta, nayan ke hukunci muna gama jarraba wa zan bar k'asar bazan zauna naga auren ba, Mom tunda kinsan komai kiyita mun Addu'a kar SO yazamo AJALINA.......
.
Sultan da tun shigowar sa yake tsaye ya kasa shiga saboda abun da yaji d'an uwansa yana fad'a, tun yana ganin duru2 har yadaina ganin haske yaji kanshi ya fara juyawa, sa k'afa yayi ya shiga baya ko ganin gabanshi, shigar yayi dai dai da fad'uwar sa a wajen... Subhanallah!!! Azabure suka taso cikin tsananin kid'ima suka rufu akanshi, ganin baya ko motsi Momy ta fashe da kuka. Duk nauyin shi haka Junaid ya kin kimeshi ya kaishi mota. Gaba d'aya basirar su ta b'ace da k'yar ta tuna cewa ana yafa mayafi idan za'a futa. Taimakon gaggawa aka mishi dak'yar aka samu ya farfad'o amma har lokacin zuciyar shi tana harbawa a hankali2. Likita yana fitowa sukayi kanshi da gudu suna tambayar halin da yake ciki, saida yace ku kwantar da hankalin ku sannan yayi wa Junaid umurni daya bishi office. "Razana yayi zuciyarshi tayi mummunan bugawa, yanzu alhmdlh ya farfad'o banda hayaniya kuma kada asake kusantar sa da duk wani abun da zai razana shi, idan yaci gaba da razana zaku iya rasa rayuwar shi gaba d'aya". "Doctor me ya razana shi"? cikin kid'ima da damuwa yayi tambayar. "shine ban saniba, amma yana cikin mawuyacin hali, a bishi a hankali do Allah". . "Yanzu bazaki tashi ki wanke kwanukan ba". "Inna yaya sultan fa nake jira ai yace kada nayi najira shi yanzu zai dawo". Tafaɗa tana zunb'ura baki. "To ai shikenan, naga alamar nan gaba ma tafiya zai gagare ki saiya tayaki". "Inna me kike ci na baka na zuba, ke dai zaki sha kallo". Tafad'a tana jawo hijab d'inta, "Inna zanje na dubashi naga shirun yayi yawa".
.
A can nesa ta hango Haulat tana ta safada marwa ta k'arasa gare ta. "Sista me ya ke faruwa naga kamar akwai damuwa a tattare da ke". Haulat taja numfashi "Sista ban san me yake faruwa ba na dawo banga kowa ba kuma wayoyin nasu duk suna falo... "Kina nufin har yaya Sultan bashi nan"? "wlh bashinan zo muje ki gani". Gidan suka duddu ba babu alamar kowa. Hafsat tayi tagumi tace "Musu fa mukeyi da yaya sultan yace muna gama Exams da sati za'ayi biki, ni kuma na ce sai bayan wata guda, shine ya fita da gudu wai zai je ya tambayo momy tun da Baa baya nan". Haulat tayi dariya ta ce "Allah ya nuna mana ranar auren nan naku naga alamar kun kusa ku kai kan ku". Dirin Mota sukaji suka mik'e da sauri, Junaid ne kana ganin shi zaka gane yasha kuka, fuskar nan nashi kamar anyi Gobara a ciki, jikin Hafsa yayi sanyi tun da ta ganshi haka tasan ba lafiya ba. koda suka k'arasa wajen shi harara ya sakar musu, ya wuce su. "Haulat inaga ba lafiya ba, wannan d'an shan k'amshin ba kulamu zaiyi ba, ki d'auko key d'in motar Momy yana fito wa mubi bayan shi". "Yess sista haka za'ayi". Da hanzari ta wuce d'auko key d'in. A inda ya barsu a nan yazo ya sameta ta buga tagumi tana tunanin ina sultan yashiga. "Zaman me kike yi a gidannan ne wai"? Taji muryar sa a gabanta. "uncle don Allah ina yaya sultan ya shiga... Tsak'i yayi ya wuce ta ya shige mota abun shi, yayi dai2 da isowar Haulat tace "sista muje". Jiki a sanyaye ta shiga, tsanar da JUNAID yake nuna mata ya fara isan ta, ji tayi ta tsane shi sosai, a hankali hawaye ya fara gan garowa kan kuncin ta, ta share da sauri kada Haulat ta gani ta tsare ta da tambayo yin da bata san amsar su ba. Gudu yake ta sharara wa suna biye dashi har suka iso asibitin. Gaban Su ne yafad'i suka fara tunanin waye bashi da lafiya. Idanuwan nan nashi a lumshe kamar me bacci, a yanzu zuciyar shi ta daina bugawa sai tunanin da ya cika zuciyar shi fal. Junaid ne yayi sallama yashiga ya k'arasa gaban shi yace "Mom ya bud'e ido kuwa"? .
.
Ta cire tagumin da tayi tace "Har yayi magana yanzu ya koma bacci". Dai2 lokacin su Haulat suka shiga suna ta zazzare ido kamar munafukai. Da mamaki yake binsu da kallo, Hafsat Kam batama san yana wajen ba sakamakon hango Sultan da tayi, kanshi tayi da gudu a kid'ime tana tambayar me yasame shi.. Momy ta taso ta rik'e ta tace "kiyi hak'uri kada ki tashe shi ana buk'atan ya huta sosai". Girza giza kai tayi tace "yanzu fa muna tare lafiyan ka k'alau... sai kuma ta fashe da kuka, Haulat ma tashiga tayata, ba yanda ba'ayi ba suyi shiru sun k'i ganin haka yasa Junaid yabar d'akin, kukan nata yana tab'a masa zuciya. A hankali ya bud'e idanuwan sa yak'ira sunanta, dukkan su sukayi kanshi suna tambayar yaya jikin. murmushin nan nashi yayi me tab'a zuciya ya rik'o hanun Hafsat "Ina sonki Hafsat, Soyayyar da bata da iyaka, muradi na yana gare ki, you know me alone but baki san komai akaina nagame da sonki ba, ina kishin ki kishin da zai iya zamowa ajalina duk ranar dana gane wani na sonki wlh zan iya mutuwa nafiso kizamto tawa ni kad'ai, zuciya ta tanada rauni a kanki HAFSAT, Mahaifiya ta da K'anwa ta sune shaida, duk ranarda na rasa rayuwa ta *SONE AJALINA*". . . Kuka take sosai ta ce "Yaya Sultan wlh kai kad'ai nake so don Allah kadai na irin wannan maganar, ko kamanta auren mu ya kusa, yanzu damuwa ta nasan abunda ya kawo ka asibiti alhalin lafiyanka law". Hanunta dayake rik'e dashi yad'an matsa yace "kinga sistan ki har yanzu kuka takeyi ku koma gida yanzu muma zamu dawo, ciwon kai ne kad'ai ke damuna". Momy ma murmushin k'arfa fa gwiwa tayi tace "kuje gida yanxu zamu taho". . . . . . . . kwanci tashi babu wuya su Hafsat angama jarrabawa, tun daga nesa ta gane yau gidan nasu a cike yake saboda 'yan kano sun iso. A k'ofar gidan suka ci karo da Abban ta shida Baa suna tattauna yanda zasu gudanar da hidimar. Cikin farinciki tafad'a jikin Abban ta tana kuka. fuskarshi d'auke da farinciki yad'ago fuskanta "Kukan me kikeyi tunda gamu mun iso Hafsat". Ya fad'a yana share mata hawayen. "Abba wlh kukan murna nakeyi, inasu Haneefa"? Hango Yaya Haidar tayi shida yaya Khaleefa ta koma gunsu da murna suma suka tare ta. kar kuso kuga murna wajensu Haneefa da momynta, (nidai nace wannan familyn badai son juna ba kam). Gidajen 2 ya runcib'e da jama'a ga hidimar gama karatu ga hidimar biki amma har a lokacin Sultan bai dawo normal ba, yazama so silent. Kowa ka ganshi zakaga yana cikin farinciki amma banda Junaid, Momy da Sultan.. Su Ukun duk akwai abunda yake k'unshe a zuka tansu. Momy kam dai nasan rashin ganin walwalan 'ya'yan nata ne da kowanne a cikinsu yake nema SO ya zama AJALINSA.
0 comments:
Post a Comment