SONE AJALINA Part 3
.
Komai aka sanyawa lokaci to fa zai zo har ma ya wuce, domin yau da gobe babu abunda ya bari. To haka abun yake su Hafsat anyi candy inda ta karb'i kyautuka da dama haka Haulat ma, suka dawo gida cike da farinciki, haka a ranar aka kawo lefen Hafsat, Sultan ya taka rawar gani sosai domin komai me tsada yasaka. Sultan ne zaune a gaban Baa yana masa bayanin yanda bikin zata kasance domin ya gayyaci manyan mutane. "Ina Junaid ne Momyn ku tace tare za'ayi bikin naku amma naga bai yi taken action akan abun ba, je ka k'ira mun shi naji me yake jira". Mik'ewa yayi ya nufi d'akin Junaid. Jin motsin ruwa yasa yagane wanka yakeyi don haka ya zauna domin jiran shi yafito. Idon shi ne yakai kan screen d'in wayarsa, photon Hafsat ne akai ta zunb'ura baki kamar zatayi kuka da uniform ajikin ta.
.
A take yaji wani mummunan fad'uwar gaba bai san lokacin da ya shiga gallery ba, duk pix d'in Hafsat ce yawanci ranta a b'ace ne guda d'aya ne yaga tana dariya. wani kishi da bak'in cikine ya turnuk'e shi ya ajiye wayar sai huci yake yi, a haka Junaid ya fito ya same shi kallo d'aya ya mishi yagane a kawai matsala, wayar sa ya kalla yaga ba'a nan ya a jiye ta ba, yasa hanu ya d'auka ya dubi Sultan da ya had'a rai yana binshi da kallo. "Me kake nema mun a d'aki, kasan baka da lafiya me yasaka mun bincike? ina ta k'ok'arin kauce wa duk wani abun da nasan zai b'ata maka rai amma sai da ka kalli abun da kasan zai b'ata maka rai, Hafsat taka ce har abada nasan matsalar ka kenan kake ta huci haka, na haramta wa kaina ita tun ranar da kazo da albishir d'in zata aure ka, kada kadamu da maganar daka ji inayi wa momy abunda ya wuce muke tattauna wa akai, bana son rasaka zan iya sadauk'ar da komai nawa na sama maka farinciki Sultan". Sultan yayi murmushin nan nashi ya mik'e yace "kada kadamu, Baa yana nemanka". yana fad'in haka yasa kai yabar d'akin. Junaid ya zauna dishan a wajen ya kama kanshi da yake ta sarawa ya fara sumbatu "Ban san ina zan tsoma rayuwa ta ba, kullum soyayyar ki k'aruwa takeyi a cikin raina, ban san yaya zanyi in cireki a raina ba, why Hafsat zaki shigo mun rayuwa ta yanda bai dace ba, why".. sai kuma ya rushe da kuka "Mutuwa ta tafi mun sauk'i a kan narasa ki, ta yaya zan yi rayuwa babu ke, dawa zan rayu to...? Babu amsa dole ya daina sumbatu yayi kuka me isan kafin ya rarrashi kanshi, ya fad'a toilet ya wanke face d'in ya nufi k'iran Baa. "Dama maganar auren naka ne naji kayi shiru abu saura kwanaki". "Baa ai an janye wannan maganar, mom ta hanani nema da tun tuni nabar k'asar nan ta ce sai anyi bikin Sultan zan tafi". "To Allah yasa jinkirin ya zama alkairi". "Ameen Baa".
.
Sultan kam gidan su Hafsat ya nufa ko hankalin sa zai kwanta. Haneefa badai surutu ba kamar ana saka mata batir. "Aunty wlh naso a kano akayi bikinnan na gayya to k'awaye na da yanzu gidannan ya cika da mutane". "To sarkin surutu ko za'a tattara a koma chan ne saboda k'awayen ki". Momyn su Haneefa ce tayi maganar. "Mom kema kinsan bani da suru.... Inna datake ta yab'a lalle a hanu ta ce " Fad'i abun ki yarinya bata da k'awaye kamar me aljanu". Zunb'ura baki tayi ta kwanta jikin Mom tana mata shagwab'an da basu jima me take cewa ba. Haneefa ta tuntsire da dariya "Aunty wlh baki sanin kin girma shagwab'a ta miki yawa, koda yake tsohuwa ce ta sakalta ki, idan ba haka ba menene abun wani kuka anan, idan kinyi auren zamuga mawanda zaki rik'a narkewa ai... Mom ce ta tabita zata buge bakin ta tashi ta fita da gudu tana dariya, karo sukayi da Sultan da yake k'ok'arin shigowa ai kuwa ta shige bayansa ta na cewa "Mom kiyi hak'uri". Dariya yayi daya gane laifi tayi yaja hanunta suka shiga cike ya ce kidaina tsokana nasan tsokana kikayi". Ya russuna ya gaida Mom yajuya ya gaida Inna. ya juya kallon sa ga Hafsat da tayi kicin2 zata yi kuka, shi dariya ma take bashi abu ba abuba tayita kuka wa mutane. Mom mik'ewa tayi dama wanka zata shiga. Da sauri ya koma kusa da ita yana tambayar ta waye ya tab'ata. Haneefa me zatayi inba dariya ba ta ce "wlh ashe ku kuke sakalta ta, babu fa abunda aka mata". yace "Hafsy na wai haka"? "Inna muje na wanke miki lallen yayi yanzu".
.
Ba musu ta mik'e suka fita. "Hafsat tambayar ki zanyi, yaya kuke da yaya Junaid Don Allah"? Banbarak'wai taji tambayar "Ban gane me kake nufi ba yaya Sultan". Ya dafe kai "i mean a makaranta kukanyi magana ne"? Ta zuba masa ido na tsawon lokaci shima d'in ita yake kallo ta ce "yakan koya mun karatu idan bangane lesson ba, bayan wannan babu wani abunda yake had'amu... yauwa sai kuma yakan yimun bulala idan yabani assgnment banyi ba, mutumin da bashi magana yaushe har zanyi magana dashi". Zaro Ido yayi "Bulala yake miki"? "kuma fa ni kad'ai yake duka bai tab'a zane kowa ba sai ni, duk gidanku suna sona shi kad'ai ne bashi.... Dakatar da ita yayi a d'an tsawace ya ce "Auren mu saura kwana 2 amma.. sai kuma yayi shiru. "Amma me"? "Amma duka yak'are". yafad'a yana dariya, itama dariya tayi ta ce "Gabana fad'uwa yakeyi tun jiya amma Innah tace nafara jin tsoron auren ne". yaja hancinta ya ce "kuma kin yarda tsoron ne"? Ta rufe fuskanta tana dariya. "Na zone ki fad'amun ko akwai abunda kike buk'ata na hidimar dazakiyi, nasan waccan kud'in sun kasa miki". "yaya sun isa, walimah kawai zamuyi Abbah bazai bari ayi wani bidi'a ba, anjuma za'a zo amana lalle da wanke kai gobe muyi walimah shikenan kawai". yayi murmushi ya ce "Jibi kuma ayi me"? "kai yaya". yayi dariya ya ce "zan wuce ki kularmun da kanki". "to yaya kaima haka". Tunda ya koma yake tunane2 a hankali kanshi yafara ciwo, lokaci kad'an jikinsa yayi zafi sosai kuma still tunanin da yake bai daina ba, ciwon da yake ji ma baya gaban shi ko kad'an.
.
wajen dinner ne aka ga bai fito ba Momy ta ce "Haulat k'ira shi kwana biyunnan da yunwa yake zama na rasa me yake damun sultan". Junaid ya ce "Nima na matsu ayi aurenan ko zai koma normal". Baa ya girgiza kai kawai bai ce komai ba. A hautsine ta dawo tana kuka "yaya sultan bashi da lafiya sai rawar sanyi yakeyi". su duka suka mik'e suka nufi wajensa, ba b'ata lokaci aka kaishi asibiti. . . . . Wacce Mom ta mata wayane tazo tun daga me duguri, gyara ta mata normal wanda ake k'ira da gyara d'aya tamkar ga dubu, lallen ma simple a ka mata manyan zane irin na 'yan me duguri, kitsone dai aka yaryad'a shi k'ananu tayi kyaw sosai sai shek'e takeyi kamar zinare. Nan fa daru ya tashi Haneefa ta fara bori dole itama a gyarata haka. Akayi rarrashin akayi dukan amma fafur tak'i tayi shiru ita fa sai taga tafara shek'i irin na Aunty Hafsat, Innah kuwa ta ce a mata dole itama haka aka mata dilke aka yarfa mata kitso da lalle, tayi kyaw sosai kamar ta had'iye kanta idan ta kalli madubi. Su Ya Haidar sukayi ta tsok'anan ta wai itama a d'aura mata aure da limamin anguwan tunda tafito kamar amarya. Basu suka gama abunda zasuyi ba har kusa asuba don haka ba wanda halin da sultan yake cike a gidan. suna brkfst Abban su ya shigo jiki a sanyaye ya ce "Ashe yaronnan bashi da lafiya baku fad'amun ba"? Abincin da takai baki ta tofar ta ce "Yaya sultan ko, naji ajikina Abbah na kasa gane me nakeji ne, don Abbah kace mishi gobe ne fa auren idan na rasashi mutuwa zanyi wlh Abbah". Sosai take kuka, bata san me suke cewa ba tayi waje da gudu yayi dai2 da fitowar Yaya Junaid zai koma asibitin ya hangota, jan glass d'in yayi ya ce "ina zakije"? "plx uncle ina yaya sultan"? Tausayi ta bashi ya bud'e mata front ya ce ta shiga, bata musa ba tashiga.
.
Jikinshi ta kwanta tana kuka tana ta k'iran sunan shi baima san tanayi ba saboda jikin nashi yayi tsanani zuciyar tashi da ba'a so ta buga sai da ta buga, allura suka mishi ya samu yayi bacci. Ahaka su Innah suka iso suka sameta ba wanda bai tausaya mata ba awajen musamman Haneefa da itama taketa rusa kuka, da k'yar aka jasu aka fitar dasu. *WASHE GARI* Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya. Dubban Mutane sun hallara kamar yadda aka gayyace su. Abokan Baa da Abbansu Sultan Duk Sun Hallara Hardaga K'asashe Daban2. Sun yanke shawarar ayi auren tunda mutane sun taru. Junaid aka bari a jikinsa sai yaya khalifa. . . saura baifi 2mnt a d'aura ba sak'o ya shigo wayar Baa, a kid'ime ya nufi asibitin baiyi wa kowa magana ba. kukan dayaga Junaid yanayine ya tabbatar masa da gaske SULTAN ya MUTU. . shima kuka yashiga yi wiwiwi kamar k'aramin yaro, d'aya b'angaren kuma anata k'iransa a waya ko b'a fad'a ba yasan masu d'aura aure ne shi ake jira, cikin kuka ya shafa fuskan Sultan ya ce Allah yajik'an ka d'an albarka. fita yayi ya koma gefe ya k'ira amininsa Muhammad Jut mahaifin Hafsat. "saifa hak'uri Allah yayi wa sultan rasuwa". "what! Kasan me kake fad'a kuwa"? "Nasani Abokina, ashe taron mutanennan mutanen sa ne... kuka ne ya kubce masa yakasa magana. *INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN* Abunda muhammad jut yaketa nanata wa kenan. "calm down aboki na, tunda hakane angama shirya komai me zai hana a d'aura da JUNAIDU". "Nima nayi wannan tunanin, a d'aura kafin a sanar dasu zancen mutuwar". . . . Haka kuwa akayi, aka d'aura auren JUNAID da HAFSAT akan sadaki naira dubu d'ari. . . . Baa yana gama wayar ya koma d'akin da sultan yake, Gaban gadon yanufa ganin JUNAID ya k'ura masa ido baya ko k'iftawa "Baa zo kagani naga kamar yana motsi". . . .
.
Da sauri Baa ya matsa yana zare ido kamar wanda yayi laifi. ya matsa da kunnuwan sa wajen k'irjin Sultan, a hankali sautin numfashin sa ke fitowa alamar yana raye. yajuya dubansa ga Junaid ya ce "yanzu ya za'ayi"? cikin rashin fahimta Junaid ya ce "zanje nak'ira Doctor... "No! ina nufin maganar aurennan... sai kuma yayi shiru ya ciro wayar sa, shi dai Junaid binsa kawai yayi da kallo. "Ina fata ba'a d'aura aurennan ba domin ya farfad'o". Banji me aka fad'a ta d'aya b'angaren ba naga Baa ya zabura ya mik'e "ok ina zuwa yanzu". Nan ya kashe wayar har yanzu Junaid shi yake kallo. "JUNAIDU! an d'aura auren dakai"... A Rud'e yabi Baa da kallo ya kasa magana, Baa bai bi ta kanshi ba yadubi Sultan ya ce "Nasan bakaji na sultan balle ka gane magana ta ina fatan Allah ubangiji ya d'agamun kafad'un ka, na gode wa Allah da ya barmun kai a raye". Junaid k'iran likita yafita yi yafara tunanin Baa d'in ma yana buk'atar a dubashi, tun lokacin da ya ce an dakai aka d'aura auren yagane ciwon sultan ya juya shi. Atare suka shigo da likita yayi dube duben shi ya tabbar sultan na raye dogon suma yayi, sai dai zuciyar shi tana buk'atan hutu kafin yadawo hayyacin sa, za'a masa allura yanzu yasamu bacci na tsawon awa 24, dazaran ya farka insha Allahu zai dawo normal. Abu kamar wasa mutuwar sultan yafara bazuwa yakai har kunnen Hafsat, . "Doctor kad'an yi chkn wannan d'inma.. ya nuna Baa yafad'a yana susa k'eya. wani wawan kallo Baa ya mishi ya ce "kaci ubanka nace, haukace wa nayi ko? Tunda ya farfad'o yanzu zaka saketa a d'aura dashi". Maganar tashi ta sake baiwa Junaid dariya ya farayi k'asa2, shi kan shi Doctern dariya yakeyi. Baa ya bud'e baki zaiyi magana wayarshi tafara ringn, ganinan zuwa kawai yace ya watsa wa Junaid wani kallo kafin ya ce "ka kula dashi ina zuwa". Tunda ga nesa mutane suka fara tururuwan gaishe shi, wasu suna cewa yaya me jiki wasu suna cewa yaya hak'uri, duk amsa d'aya yake basu *ALHAMDULILLAH* Kutsawa yayita yi har ya iso wajen Amininsa." "Kaji wani abun al'ajabi yanzu yaya za'ayi"? Baa ya ce "zamu sa ya saketa yanzu in yaso sai a d'aura da sultan d'in". Muhammad Jut ya girgiza kai "Ba haka za'ayi ba, shi lamarin aure rikitar wane dashi kuma matar mutum ai kabarin sa, tunda abun yazo da haka nabaiwa Sultan d'in auren 'yata HANEEFA sai a d'aura yanzu". cikin tsananin farinciki Suka rungume juna, atake aka d'aura Auren Sultan da Haneefa. . . .
BAYAN AWANNI .
.
"Ohhh ni wannan lamarin da d'aure kai, wannan ai kuskure kuka tafka, memakon kumayar masa da matarsa sai ku aura masa wacce bai santaba, yaya zakuyi da soyayyar da suke fama dashi ga yarinya sai suma takeyi wa mutane". Abbah Ya kad'a kai kawai ya ce "haka Allah ya k'addara hak'uri zatayi a hankali zata so wannan d'inma, ita Haneefan tasan da zancen aurene? amma tayi tawakkali, akwai wanda take so acan kano haka ta hak'ura saboda ta yadda da k'addara, kinga Inna don Allah kibar surutu duk mun rufawa juna asiri ne kuma insha Allah zai zame mana alkairi tunda bada niyyar yimusu dole mukayi ba Allah ne ya juya al'amarin sa". Hafsa dai kukan ta taketa sha arasa wanda za'a had'a ta dashi sai wanda yatsane ta, adduar ta Allah yad'au ransu itada sultan suhuta yafi. Haneefa ma kukan takeyi gani take kamar itace zataci amanar 'yar uwanta, tasa aranta sai tasan yanda za'ayi wannan auren ya juye. ...................................... Bayan awa 24 Sultan ya farka, a hankali yafara buɗe idonshi yana gani dishi2, salati yayi yafara k'iran sunan Hafsat, Junaid ya mik'e da sauri ya isa gabanshi ya rik'o hannun shi ya ce "Sannu broz". Ya gyaɗa masa kai kawai. Likita yak'ira yazo ya duba shi yace "Alhamdlh yanzu inane yake maka ciwo". Kanshi ya nuna dayake ɗan sarawa. Ya ce "anjuma zaka daina ji insha Allah. daganan yagama rubuce2 ya fita. Junaid ya matsa kusa dashi yana masa sannu. "Ina Hafsa, an ɗaura mana auren ko"? Ya tambaya yana k'ok'arin tashi. Sai a lokacin maganar Baa yadawo wa Sultan na cewa an ɗaura auren dakai. Yaɗanyi murmushi ya ce..,,..,
0 comments:
Post a Comment