SONE AJALINA Part 4
.
Dak'yar aka samu Hafsat tayi shiru, sai da momyn Haneefa tayita rarrashi tare da cemata idan har ta yadda aka kaita ta kwantar da hankalin ta to dakanta zata sashi ya saketa sai tadawo sultan ya aure ta, haneefa kuma bama za'a kaita ba za'a datse auren, da wannan magana yasa tayi shiru har ana d'an hira da ita. Zagewa Momyn tayi ta gyara yaranta, duk wani tanadin gyaran da tayiwa Hafsat su biyu yanzu take musu, tasha alwashin babu wanda zai d'and'ana mata yara ya wulak'an tasu, darajar mace a gidan miji shine ta samu 'yanci, soyayya da ban 'yanci daban, duk sonda namiji zai miki matuk'ar baki nemi 'yancinki ba to fa bazaki ji dad'in soyayyar ba, domin a zuciyarsa ne kad'ai zai rik'a mutuntaki. Bayan Sun dawo daga asibiti dak'yar aka hanashi zuwa gidansu Hafsat aka fake mishi da cewa a kwai mutane da yawa a gidan ba lallai ne ya gantaba. Bawani Biki akayi sosai ba, Hafsat ta saki ranta sosai momy tana dad'a rarrashin ta tana kwantar mata da hankali akan dazaran tayi biyayya ta kwantar da hankalinta to sultan zai dawo gare ta. Innah Kuka tayi sosai dak'yar aka b'anb'are Hafsat ajikin ta duk sun cika gidan da kuka lokacin da aka zo d'aukar amarya. Sultan dai ce masa akayi sai ya warware ayi bikinsu da Hafsat, Tunanin sa duk yatafi akan Junaid ya amince an d'aura masa aure da sadiya ne ganin ba'a daina shagali ba. Wajen Abbahn ta aka kaita yayi mata nasiha me ratsa zuciya daya sata zubarda hawaye sannan aka kaita gidansu Junaid, Sashin Baa. Nanfa kukan ta yazamo sabo gani take kamar ta yaye rufin kanta ko zataga sultan. zaune suke a parlour daga momy sai Baa aka shigar da Hafsat, da sauri mom ta mik'e ta rik'ota ta rungume ta tace "kidaina kukan nan hafsat, da Junaid da sultan duk abu gudane, yanda sultan zai kula dake nayi imanin Junaid zai baki kulawa shima, k'addara ta riga da ta zama fata, tun ran gini tun ran zane Allah ya k'addara Junaid ne mijinki, kiyi k'ok'ari ki cinye wannan jarrabawar... Baa ma nasiha yamata daganan aka wuce da ita gidanta. Bawani k'awaye take dasu ba daga tsofin da suka kaita sai k'annen momy su biyu da Haulat, Sai Kuwa 'yan gayyan sod'i su Hajara Da Sadiya 'yan Leken Asiri Kenan.
.
Basu Wani juma ba suka tafi bayan sun gama santin gida aka bar amarya daga ita sai halinta. kifuwa tayi taci gaba da kukan ta kamar ranta zai futa. Junaid kam yana d'aki jin yanda aketa gud'a a gidan, yarasa farinciki yakeyi ko bak'inciki, shidai yasan yana cikin jin dad'i yana jinshi kamar bashi ba idan ya tuna cewa Hafsat itace matar sa. Mom ce ta tura k'ofar tashiga tayi mamaki ganin kamar ma bacci yakeyi, duka ta d'aka masa daya sashi mik'ewa cikin sauri, "baccin me kakeyi? wazaije yayi maka gadin matar taka, kasan k'arfe nawa kuwa yanzu"? k'arfe 11 yagani yad'an ja numfashi "haka akeyi ranar da aka kai amarya sai miji yaje, da kinbarni gobe sai naji da wuri..." "Idan kagama surutun kashi ga ka shirya yanzu ka wuce kabar gidannan". . Shiri yayi yasaka farar shadda datasha aiki da bak'in zare yafito ango sak k'amshine kawai ke tashi. Mom tana ganinshi tayi dariya tace ko kaifa, kayi sauri kaga dare yayi Allah ya tabbatar da alkairi. . . Gajiya tayi da kukan tayi shiru tana ajiyan zuciya, ta k'udun dune awajen har bacci yayi awon gaba da ita. A hankali ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga, ya k'arewa d'akin kallo sannan yajuyo ga dubansa gareta yaga bacci takeyi da gaske, ya yaye mayafin kanta ganin yarufe mata fuska ya gyara mata kwanciyar yabar d'akin kamar kyaftawar ido. kusan 2rh ya kwashe a zaune bai sani ba. kuka ya fara ji k'asa2 mara sauti yana shiga kunnen sa adaidai lokacin da bacci ya fara fizgan shi, da sauri ya mik'e ya nufi d'akin daya tabbatar cikin sa take, ganin yanda ta runtse ido take ta kuka ne abun yaso bashi dariya kamar ba yanzu ta gama shan baccin ta ba. Tsawa ya daka mata ya ce "menene kike kuka wa mutane a darennan, kin gama baccin ki zo kina wani b'are baki". Dad'a b'arke wa tayi da kuka harda birgima, ya kama kanshi ya ce nidai nashiga uku, me kukan nata yake nufi, bata sona kenan lallai zan canza taku, zuba mata idanuwan nan nasa yayi, k'aramin bakin ta kawai yake kallo da yasha jambaki, ya sauk'e ajiyan zuciya kafin ya futa bai sake bi takan ta ba, kukan nata yana matuk'ar shiga ransa idan ya ci gaba da kallon ta shima zai iya yin kukan. Kwanciya yaje yayi amma yakasa baccin kuma gani yake idan ya rarrashe ta zata iya raina shi, ji yake zuciyar shi duk a jagule. Zuwa yayi ya rage kayan jikinsa, har ya zauna ya tuna da abincin da momy ta bashi ya kawota. Lokacin ta daina kukan sai ajiyan zuciya take yi, sultan kawai take tunawa tana tunanin yanzu wani hali yake ciki, jin an buɗe k'ofa ne yasata mik'ewa da sauri don ita mungun tsoron shi takeji idan ta tuna dukan da yake mata a makaranta.
.
D'aure face yayi kamar wani zaki ganin yanda take ta zaro ido, cikin takun nan nasa ya k'arasa cikin d'akin ya ajiye foodflask d'in dake hanunsa tare da flet da cokali, ya koma ya d'auko mata Bottle water da fresh milk, da kanshi ya zuba mata soyayyen indomie ne da k'wai, saboda yunwar da take ji sai had'iyar yawo takeyi duk da indomie bai dameta ba amma takasa motsi har yagama zubawa ya mik'e ya koma kan stool d'in dake jikin mirrow ya zauna ya zuba mata ido, mungun tsoron shi take ji takasa koda motsawa ne ganin baice ta ci ba. "ko sai an baki abaki ne? kin cika wa mutane gida da kuka kin hanasu bacci har asuba ta kusa, kinsan kinajin yunwa ai saiki fad'i gaskiya". zunb'ura baki tayi kafin tajawo abincin ta fara ci, rabonta da abinci tun ranar da aka ce mata sultan yana asibiti, don haka ta cinye tas tasha fresh milk d'in kad'an ta ajiye ta koma gefe ta zauna, ba k'aramin mamaki yayi ba ganin ta cinye, bai ce mata komai ba ya kwashe kayan ya fita dasu ya barta tana lek'ensa tana mamakin yanda yasauk'o har ya zuba mata kuma ya kwashe. Ranar dai babu wanda yayi bacci a cikin su, gari yana wayewa kuwa yabar gidan, wanka tayi ta saka atamfa d'inkin riga da siket ta nad'a d'an kwalin kamar goggoro, ta saka yari gold tayi simple makeup amma fa tayi kyaw sosai, gidan ta shiga zagaya wa d'akin dake kallon natane ta gane shine na Junaid an tsara d'akin sosai, gadon dake d'akin har yafi nata girma, kitchen ta duba taganshi k'aton gaske komai akwai ciki ta bubbud'e fridge d'in tayi murmushi ganin komai yaji aranta tace inama yaya sultan na aura da yanzu muna tare, nan hawaye yafara wanke mata fuska, knokn k'ofa akayi ta share hawayen da sauri taje ta bud'e, Haulat tagani suka rungume juna suka k'arasa ciki. tad'an had'a rai ta ce "shine jiya kuka tafi kuka barni baku tayani kwana ba".
.
Haulat ta zaro ido ta ce "mukwana a ina? wlh yanzu ma banyi niyyar zuwaba momy ce tace na kawo miki abinci, kinsan fa boss d'innan kika aura bazaki rik'a ganina sosai ba don nasan zai iya korata". Narai2 tayi kamar zatayi kuka ta ce "Ina yaya sultan d'ina ya warke ko"? Haulat ta kama baki "kinada hankali kuwa Hafsat? kinada auren kike tambayar lafiyar wani? to nidai babu ruwana kuma kiyi istigfari". mamaki ne yakama Hafsat ta ce "yanzu kina nufin bazan auri yaya sultan ba"? Dariya Haulat ta tintsire dashi ta ce "wannan k'azamin tunanin naki ya bani dariya, wani irin aure kuma bayan ya auri k'anwar ki, to wlh kicire shi a ranki ki rungumi mijin ki don natabbata yaya Junaid yafi sonki akan kowa, kina ganin bai damu da kowa yayi karatu ba saike, kuma in fad'a miki yaya sultan d'inma ya manta dake yanzu soyayyar su suke sha da Haneefa, saboda ke sakarai ce bazaki yi tunanin tayaya zanyi biyayya wa mijina ba kina tunanin wani wanda ya manta dake". sosai maganganun suka sosa ran Hafsat Sai yawo yake mata a zuciya duk da ita dai Haulat tayi hakane saboda ta manta da yaya sultan, ganin ta kasa maganane Haulat taci gaba da cewa "kinga yaya Junaid sauk'in kai gareshi, kiyi k'ok'ari ki koya mishi sonki zakiyi alfahari dashi ko ba yanzu ba zaki gasgata magana ta". wani k'aramin littafi ta ciro a handbag d'inta ta ce "ki karanta wannan ni zan wuce, idan kikayi wasa da damanki mijin ki ya tafko miki kishiya ba yanda kika iya". ta fad'a tana dariya. "Don Allah kada ki tafi yanzu kibari muci abincin sai ki tayani gyara gidan". Dak'yar ta zauna kafin wani lokaci gidan yayi fes ko ina ya d'au k'amshi.
.
kayan turaren wuta dasu humra kuwa mom ta mata kamar bazasu k'areba Kafin ta tafi sai da tayi ta bata shawara duk akan ta manta da Yaya Sultan ne. Tunda ya futa da sassafe gida yayi yaje yayi kwanciyar sa a d'akin momy har wajen k'arfe 12, shima shigowar Haulat ne ta dameshi da b'uruntu ta tab'a can ta tab'a can, ai kuwa yana tashi yafara balbale ta da masifa, dama so take ya tashi yasa tayi haka. "uncle kayi hak'uri, pics d'in Aunty Hafsat ce data manta zan tattara na kaiwa yaya sultan tunda bai samu ya aure... tafad'a tana k'unshe dariya da gayya tayi maganar, wani wawan damk'a ya mata ya d'aga hanu zai mareta sai kuma ya fasa, yana huci yabar d'akin da sauri ya nufi sashinsa yayi wanka yayi sallah yasaka k'ananun kaya sun masa kyaw, ko sallama baiyi wa mom ba saboda tana wajen sultan tana bashi magungunan shi. Tun daga harabar gidan yafara jin sanyi aranshi har ya k'arasa shiga, lumshe ido yana shak'an k'amshin daya sanyashi jin bacci. Ba kowa a perlourn don haka ya nufi d'akinta, littafin da Haulat ta bata take karanta wa, lokacin ta sake wanka tasaka englishwrs ta d'aure kanta da hairbon pink me kalan kayan. Tsayawa yayi yana kallon ta ba k'aramin kyaw tayi masa ba, k'aramin pink d'in bakinta ya zubawa ido, takawa yayi ya isa gabanta ya tsuguna, har lokacin karatun ta takeyi tayi nisa a ciki wani waje taji kunya ta lumshe ido wani waje tayi dariya, tsintar kanshi yayi da kamo hannun ta da yasha lalle, ta mik'e da sauri zata kurma ihu ya toshe mata baki ya ce "sai ayita sallama baki amsawa ko, bani naga me kike karanta wa". da sauri ta b'oye littafin tana dariyar daya sashi sandarewa, wutar sonta ne ya dad'a ruruwa a cikin zuciyar shi, shima murmushin yayi yana binta da wani irin kallo idanuwan sa a lumshe ya mik'e ya ce "kinci abinci"? kad'a ido tayi wai ita ala dole zatayi fari da ido yanda ta karanta acikin littafin, hakan datayi kuwa ba k'aramin tsumashi yayi ba. "Baki bani amsaba". Ta d'an shagwab'e fuska ta ce "na ci". murmushi yayi ya bar d'akin, da gudu ta tashi tana lek'ensa don bataso ya futa ba yamata kyaw fiye da yanda take kallon shi a baya, ko don bai d'aure fuskan bane oho. Kwanciya yayi yana tuno siffar ta, fara ce tanada manyan idanuwa, k'irar ta kuwa ta kalangu ce, zara zaran yatsunta ya tuno yayi ajiyan zuciya ya mik'e zaije ya nemawa cikinsa abinci, duk kasala ta sauk'a masa. .
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::: :::::::::::::::
Kiyi hak'uri Haneefa kinga ba lafiya yake dashi ba ki tausaya mishi ki kula dashi ki mantar dashi komai, idan kikayi kin gama mana komai, zamu zauna dake anan dazaran ya gama warkewa zaku koma gidan ku don Allah kiyi hak'uri ki kula dashi a hankali zai soki". Haneefa Sarkin Tausayi ta share hawaye ta ce "Insha Allah zanyi iya k'ok'ari na kuma basai kun had'ani da Allah ba tunda mijina ne zan kula dashi". Baa yayi ta saka mata albarka. Sashin Sultan aka kaita, mom ta nuna mata wajen ta ce "Bazan ce masa komai akanki ba tukunna, kibishi aduk yanda ya d'auke ki kinji d'iya ta". sunkuyar dakai kawai tayi tana murmushi. Haneefa Wayayya ce nak'in k'arawa, irin matannan ne masu iyayi ga saurin sabo don haka take da tarin k'awaye da ita kanta batasan yawansu ba, Allah ya zuba mata surutu ba'a tab'ata ta k'yale sai dai tanada tausayi sosai.
.
D'akin nashi ta murd'a ta shiga, yana kwance da alamun bacci yakeyi, tasha mamaki dataga d'akin tsaf2 duk da ba lafiya yake dashi ba, hakan ya tabbatar mata cewa yana tsafta, k'arewa d'akin kallo tayi na tsawon lokaci kafin ta mik'e ta futa ta koma perlour, batasan me zatayi ba don haka ta kwanta awajen har aka k'ira sallar azahar, tana yunk'urin tashi taji motsin shi yana fitowa, turus yayi awajen da mamaki don shi ko Hafsat bata tab'a lek'owa sashin sa ba, d'an murmushin nan nashi yayi ya ce "Haneefa me yafaru, Hafsa ce ta aiko ki ko? yanzu nake cewa zanje tunda nasan mutane sun ragu ko"? wani murmushi ta sakar mishi ta ce "Eh Aunty ce tace nazo na duba ka, kuma... umm kumaaa wai..... nataya ka zama kafin agama bikin.. nanda sati d'aya dai infact.... zaro ido yayi yace "ki tayani zama a ina wai, kinsan me kike fad'a kuwa"? k'ugu ta kama ta ce "na sani mana, kasan kana buk'atan a kula dakai saboda ciwon ka, ganin ba yanzu za'a gama bikin ba sai nanda sati yasa aka yanke hukuncin nazo na zauna dakai". kallon mahaukaciya ya mata ya saki dariya ya ce "ok naji, wani irin kulawa zaki bani"? "zan rik'a yi maka abinci nazauna nayita maka tad'i, na gyara maka waje, nayi maka wanka, nasaka kayi bacci..... Dariyar dayake tayi ne yasa ta tsuke bakin ta tayi shiru tana watsa mai harara wanda ya gama tafiya da imaninsa, karo na farko da yaji wata mace ta burge shi bayan hafsat. yarfa hanu yayi ya ce "ki fara aikin ki yanzu, zanje wajen mom naji wannan banzan al'amarin waye ya k'irk'iro shi"... .
.
still dariya yakeyi har yabar d'akin. Tana ganin yafita tasaka key, tasha d'amara ta hau aiki, komai ta canza masa wajen zama ta canza tsarin wajen gaba d'aya, ta jawo kayan da mom ta biyota dashi, akwatina ne guda 8 cike da kaya sai manyan gana massgo guda 2 tayi murmushi ta ce "Ashe dai mutanennan sun gane". kayan make up ta cika akan mirrow, takai duk wani abunda zata buk'ata na toilet takai, ta d'ibi kayan shi dataga na daud'a ne ta zubasu a ingine wanki ta jefa sabulu ta rife, kafin wani lokaci ta gama wanke su tass ta shanya, batayi tunanin akwai kitchn a wajen ba sai taga akwai tayi murna kuwa sosai, ganin har dasu nama a fridge d'in ya bata mamaki batasan mom ce ta zuba musu komai ba. farfesun kifi tayi daya cika gidan da k'amshi, tayi alalan doya sannan ta markad'a kwakwa da dabinon ta ta tace tasa mai k'ank'ara da flavour taje ta jera masa su. Sau Uku kenan tanaji ana buga k'ofan tayi banza aranta tace zama ka gaji da bugawa sai nagama wani ya shigo. Wanka tashiga ta dad'e tana gasa jikin ta saboda duk ta gaji, ta d'auro alwala tayi sallah sannan ta duk'ufa kwalliya, humra ta shasshafa ajikin ta sannan ta fesa turarruka, dogon riga ta saka bak'i me adon duwatsu agaban wajen k'ugun yad'an kamata, ta yane kanta da k'aramin hijabi. (nidai nace wallah tasha kyaw). Jin muryan momy a bak'in k'ofar tana k'wala mata k'ira ne yasa tayi hanzarin zuwa ta bud'e k'ofar. *masha Allah* Abun da mom tafad'a kenan data ganta kafin ta k'arasa shiga, murmushi tayi ganin wajen gashi k'amshi duk ya cika wajen aranta ta ce "lallai mace rahama ce wannan itace matar da tadace da d'anta me larurar ciwon zuciya, tasan zaman nasu zaifi dad'i saboda be fara sonta ba tun farko balle *SONTA YAYI AJALINSA* "Duk ke kika sha aikinnan haka". ta sunkuyar dakai tana murmushi. "Naji dad'i sosai Haneefa Allah yayi miki albarka, gashi can yanata masifa ki rufe k'ofa kink'i bud'ewa ashe aiki kikasha, Allah ya miki albarka" Ahankali Ta Ce "Ameen". Mom tana mik'ewa itama ta tashi ta d'auko flask d'in data zuba musu abincin tabi bayan ta dashi. Yana kwance a d'aya daga cikin kujerun falon yana latsa wayar sa suka shiga, bai san tare suke ba, ya ce "Kin korata ta tafi ko mom, narasa gane inda maganar ku ta dosa ace wai zata kula dani haba Mom baku tsoron wani abu yafaru ne"? "mun dai gama magana dakai kada nasake jin wata magana a bakin ka". "nadaina mom". Dai2 lokacin ya d'ago ita ya fara gani ta kafe shi da ido kuwa, saida hanjin cikinsa suka murd'a, ya had'iye yawu yayi murmushi ya ce "m sorry". Murmushi Kawai tayi ta d'an saci kallon Mom taga hankalin ta yana kan Tv, ta kashe masa ido d'aya tare da karkad'a masa eyelashes d'in ta. k'irjin sa ne yayi fat, da sauri ya mik'e yana fad'in innalillahi aran shi, wani irin feelings yakeji har tsak'ar kanshi.
0 comments:
Post a Comment