SURBAJO Part 04
.
Surbajo idanuwantane suka fito kurukuru ganin bindigar datayi jikinta sebari yake
Alameen yace umarni zanbaki inkika kuskura kika ki bi sena harbeki yafada in a serious talk
Girgizamasa kai yakeyi alamar tayarda
Cigaba yayi da magana yace surbajo yau kinbatamin raina sosai so dole ne nahukuntaki Dede da iri laifin dakikamin
Don Allah kado kayi hakuri aradu bazansakeba
Tsawa yadakamata wacce ta tilastata yin shuru jikinta nabari
Kara matso da bindigar alameen yayi dede goshinta aytuni fitsarin datake rikewa ya kubce alameen seji yayi yajike da fitsari bedamuba yacigaba da cewa
umarnina shine zan aureki ko kinaso kobakyaso kuma idan kika sake kika nuna cewa nina tilasta miki aurena harbeki zanyi
surbajo wacce tunda yafara magana numfashinta ke barazanar daukewa dakyar tace Don Allah kado kayi hkr inada Wanda nakeso kumashi zan aura .
.
Bigemata baki yayi yace ay ba raayinki nakeson jiba umarni nabaki kuma dole kibi inkinki ko dagake har Jaen sena harbeku
Jikintane yakama Bari kamar mejin sanyi tace kayi hkr Don Allah karka kashemini jae aradu naamince zan aureka
Wani malalacin murmushi alameen yasaki alamun samun nasara cikin ruwan sanyi
alameen bekyale surbajo tatafiba seda yagama tsoratata sannan yace tawuce
da gudu tafito tayi cikin gida kamin takai cikin gidan tafadi yafi so uku sabida agigice take koda tashigo Kowa yashige dakinsa sabida sanyin daakeyi itama nata dakin tashige wutar jin dumi ta tarar sumaye takaimata dakin ga kuma abincinta a akushi
Gaban wutar taje tazauna bayan ta karo kofar dakin
kuka tashigayi Mara sauti duk da tabon daya bata mata kaya bata damu taciresuba
ita kawai tunaninta alameen Dan fashine Dan inba Dan fashiba baabinda zekawo bindiga gurinsa itayau yazatayi da rayuwarta Ashe Dama basuda rabon aure da jae gaskiya kado mugune Allah seya sakamana tafadi Tana cigaba dakukanta
Wanda babu mesharemata
ranar azaune surbajo takwana kowanne motsi akunnanta Dan tsoro takeji takwanta kado yazo ya harbeta
Shima alameen Tana fita ruwa yadiba yasa ajikinsa inda fitsarinta yashafa sannan yaci abinci data kawomasa gaskiya yaji dadin abincin ruwa yasha sannan yakwanta badan yayi bacciba seda yaji dadin tuno dramarsa da surbajo juyi kawai yake yana murmushin jindadin gano surbajo nada tsoro dayayi
ayko yasamu abinyi shima ranar beyi bacciba
da sassafe ardo yaje cikin gari nemo mesa iska yaci wuya kamin yasamu Wanda yaamice zebiyoshi zuwa rugarsu
suna zuwa yasa iskar alameen Wanda tuni yashirya yabiya mutumin kudinsa sannan yakarasa gurin ardo domin suyi sallama sosai ardo yadunga kara bashi hkr abisa tsautsayin dayafaru sallama yamasa yanufi gurin motarshi kamar anjefota yahango surbajo tafito daga gidan dauke da tulu Zata dibar ruwa tsayawa yayi harta karaso
ko kallonshi batayiba Tana kokarin wuceshi Dan ita yanzu tsoronshi takeji
kiran sunanta yayi arude tajuyo Dan tunda take babu Wanda yataba kiranta da sunanta taji dadin sunan kamarshi
tsayawa tayi ainda take
ba gaisuwa yatambaya
kayi hkr ina kwana murmushi yayi sannan yaamsa da Lfy
yakara da ina Zaki ruwa zan debo tabashi amsa
muje inrage miki hanya yafadi sannan yajuya yashige motarshi bude mata gaban motar yayi tsayawa tayi kamar da karta shiga sekuma ta tuno bindinga dagudu taje tashige yarufe kofar yatada motor suka tafi
.
Tafe suke yana janta da hira har suka iso bakin rafin yana parking Ta bude motar tafice
Tanufi rafin ko sallama bata masa ba
Murmushi yayi sannan yace halin surbajo se ita shima bedamu ba yaja motarshi yawuce yana fita agarin wayarshi tafara ringing abokinshine Usman bayan sungaisa yace yanemi wayar alameen din besamuba ko Lfy
Dariya yayi sannan yabashi labarin abinda yafaru tsakaninshi da surbajo dariya shima Usman din yayi yace shege mutumina wlh dukanku kunburgeni kunyi dede Allah de yanuna mana ranar bikinnan
Hakade suka Dan jima suna hira daga baya sukayi sallama
.
Alameen gidansu yasauka yaci abinci anan abba yake shaidamishi sati mezuwa zasuje nemarmasa auran surbajo
.sosai alameen yanuna jin dadinsa dajin zancan godiya yamusu sosai sannan yanufi gidanshi fuskarsa dauke da faraa
Koda isarsa Kai tsaye cikin gidan yanufa bayan yagama gaisawa da masu tsaron Lafiyarsa
Yana shiga falon Aisha ta taso afusace ta kama kwalar rigarsa tarike sannan tace daga ina Kake kuma agurin wacce shegiyar ka kwana batare daka sanar daniba tafadi cike da rashin kunya
ran alameen tuni yafara zafi jin takira surbajo da shegiya
Dagowa yayi yace sakeni inwuce Aisha banason rigima yanzu
shewa tayi sannan tace ay Wlh inkaga nasakeka kafadamin gurin wacce ka kwana ko anfadamaka bansan taketakenka ba ay Tunda kafara zama bunsuru nagane to Wlh baka isaba bade agidannanba
Tass yadauketa da Mari kamin tawatsake yasake Kai mata wani daga bisani yarufeta da duka ihu take Tana neman agaji seda yamata dukan dashi kanshi besan iya adadinsaba sannan yakyaleta tuni tajima da sumewa
Ko ajikinshi ya dauko ruwa yasheka mata tafarko
sannan yabata amsa dacewa
Aisha Tunda nake bantaba ganin jaka kamarkiba dakikiya kawai mahaukaciya
Wai kindauka tsaron ki nakeji to Wlh ko daya tausayinki nakeji amma Tunda kin nunamin kedin dabba ce Wlh sena baki mamaki kuma dakikace daga ina nake daga gidan matar dazan Aura nake kisama ranki Wlh aure zanyi nanda sati guda kuma it doesn't matter to me kome nene ze faru yafaru banza tinkiya kawai ko kigyara halinki ko kada ki gyara damuwarkine ko tablet nahana haihuwa dakike sha keze cutar baniba Danni wuyarta nayi auran
ya ingijeta tafadi akan tiles sannan yawuce yabarta da faasshen jiki se kuka takeyi
********
Surbajo Tunda alameen yatafi kullum da tunaninsa take kwana take tashi sosai take kewarsa sakamakon so da kaunarsa dasuka addabi zuciyarta tabbas yanzu tana sonshi dari bisa dari zuwa yanzu sunfara samun sabani da jae ganin yanzu batashi takeyiba shiyasa yaja baya shima da ita duk da yanasonta amma baze jure tadunga shareshiba
su daddy sunje nemama alameen auranta inda ardo yay matukar murna da afkuwar hakan badan komaiba sedamutuncin iyayensa
kamar yadda alammeen yafadawa mahaifinsa daga baya cewa shima bayason bikin yawuce sati guda tokoda suka sanar da ardo bemusamusuba aka tsaida ranar auran sati mezuwa bayan an tambayi surbajo shin kotana sonshi ta amsa da eh tanasonshi
.
Acikin satin aka soma shirye shiryen biki dan ranar asabar zaa daura auren
Aisha Data fuskanci dagaske aure alameen zeyi hankalinta vakaramin tashi yayiba Dan haka tanufi kawayenta subata shawara
Koda isarta gidansu zuly kuka tasa mata tace kawata nashiga uku alameen aure zeyi Dan Allah kitaimakeni narasa abinyi
Wani dadine yarufe zuly Dan Dama sun jima suna jiran wannan ranar Amman afili kukan tasa itama suka rungume juna dakyar sukayi shuru zuly tace wannan tashin hankali dame yay Kama wallahi bazamu zuba ido muna kalloba semun dauki mataki ki kwantar da hankalinki
Gobe in Allah ya kaimu zamuje gidan wani malaminmu yaiya ayki sosai zeshare miki hawayenki sosai Aisha tayi murna da shawarar aminiyartata Dan bata bar gidanba se dare
Alameen murna yake sosai Badan komaiba sedan auren cartoon dinshi dazeyi
Usman dariya kawai yakeyi dazaran yaji alameen yakira surbajo da cartoon Dan yana da tabbacin alameen dinne zekoma cartoon din
Shiri suke sosai musamman gidansu alameen Dan sunfi kowa murna da auren da alameen zeyi
Dubai mommy taje tahadowa surbajo kayan lefe da kayan daki sabida sunce ardo base yayiwa surbajo kayan dakiba su zasuyi
Dakuna biyu dake falon kasa nagidan alameen aka shiryawa surbajo kayanta aka kulle dakin yayinda kayan lefenta aka ajiye gidan su alameen sabida ardo yace a ajiyemata acan
**********
.
jae dayasamu labarin surbajo aure zatayi har gida yaje yasameta koda tazo
jae rufe idonsa yayi ya zazzagamata masifa har yana cewa auran kwadayi zatayi kuma insha allahu se an sakota kuka surbajo tasa Tana rokonsa ya yafemata Dan tasan bata kyauta mishiba amma bata da iko da zuciyarta takamu da son alameen me tsanani Wanda tanajin bazata iya rabuwa dashiba kuma ita badan kudinsa takesonsaba sedan Allah
Jae shima kukan yakeyi Dan kukan surbajo yadagamasa hankali cikin kuka yace ya yafemata Allah kuma yabasu zaman Lafiya da mijinta daganan yawuce yatafi yabarta Tana Ta kuka
alameen shida Usman suka dauko hanyar makarfi Dan sunason ganawa da Amarya suji shirye shiryenta
.
da isarsu ardo yasaukesu a dakin saukar baki yasa aka kawo musu fura da nono me kyau sosai Usman yasha furar sabanin alameen dashi ba cimarshi bace
seda suka Dan jima dazuwa sannan aka turo surbajo wacce ta yafo mayafi tarufe fuskarta sabida jin kunya sallama tayi tashigo dakin tasami guri tazauna daga nesa dasu dakyar ta iya gaishesu suka amsa cike da barkwanci
Usman yace amaryarmu kunyarmu kuma kike Yi haka
Ko fuskar bazaki budeba
Ay surbajo jitayi wata kunyar tasake kamata Dan haka Kara Rufe idonta tayi Tana murmushi daga cikin mayafinnata
hakade Usman yay tajanta da hira amma takasa bashi amsa sabida kunya
mikewa Usman yayi yafice daga dakin Dan yabasu guri su tattauna
shuru ne yabiyo bayan fitar Usman
jin shurun yayi yawa ne yasa surbajo zaton sun fitane daga dakin ne dukansu yaye rufar datayi tayi carab idonta yasauka akan na alameen da tun tuni ita yake kallo dasauri tamaida rufar
matsowa alameen yayi gab da ita har jikinsu na gogar juna lullubin ya bude surbajo kankame hannunta tayi a kirjinta sabida batason yakalleta murmushi yayi Dan yafahimci me take boyewa hannuwanta yakamo yaruke anasa sannan yabita da ido yana karewa halittarta kallo ba laifi duk da kankantar shekarun surbajo hakan be hanata mallakar duk wani Abu da yamace ke daukar hankalin da namiji dashiba
.
surbajo duk Ta takura da irin kallon da alameen yake mata kokarin kwace hannunta takeyi amma takasa cikin siririyar muryarta tace kado Don Allah kasakarmin hannuna Wlh kunyarka nakeji tafadi Tana runtse idonta
akasalance alameen yafara magana sabida kallon kirjin surbajo dayayi yahaifar masa da damuwa sabida surbajo batasa bresiar ba hasalima bata da ita garigar jikinta me budadden wuyane irin na Fulani shiya Kara bayyanar da halittar dukiyar fulaninta ganin hakanne yasa hankalinsa yasoma tashi
dakyar yace surbajo kunyata kuma yanzu kikeji ko kinmanta saura kwana biyu yarage kizamo mallakina Toni banason kunyar nan taki kinji ko kai tadaga masa
yaci gaba ko bakyasona ne
dasauri tace kado aradu ina sonka kawai inajin kunyarkane kunnenta yaja da Dan karfi Wanda hakanne yasa ta samishi kukan shagwaba Dan dama surbajo gwanace gurin kukan banza bare yanzu dame dalili yasamu
.
alameen yace daga yau nasauke sunan kado inkika kuma kirana dashi kuma zanyi Maganin bakin daya kirani da sunan kadon
cikin kuka surbajo tace aradu kado bazan Kuma........bata karasa fadin abinda zata fadaba yahada bakinshi da nata yashiga kissing kamar yasamu sweet
hankalin surbajo kusan barin jikinta yayi asakamako fadawa duniyar dabata taba sanin akwaitaba arayuwarta
seda yajita jikinta yagama mutuwa sannan yakyaleta surbajo dasauri ta janyo mayafinta tarufe jikinta har fuskarta jikinta se rawa yakeyi ita bata san sunan abinda yamataba jikinta duk yamutu
ga wata matsananciar kunyarshi data kamata shima daurewa kawai yayi amma Allah kadai yasan yanayin dayakejin kansa
hira yay tajanta da ita amma bata bashi amsa hakanne yasa yamike yace tosu zasu tafi dubu dari yabata akan kozatayi amfani dasu dakyar taamsa sannan tayomasa rakiya inda Usman yake jiranshi ajikin motarshi dakyar surbajo tayima UsmUsman sallama sannan tacewa alameen kado kugaida Gid.......bata karasaba tasa hannunta tarufe bakinta sannan takwasa da gudu tayi cikin gida
dariya alameen yayi Dan yasan me yasa surbajo guduwa
mota suka shige bayan sunyiwa ardo sallama suka dauki hanyar kaduna
Usman se tsokanarshi yakeyi
.
Abangaren uwargida Aisha kuwa jitake kamar takashe kanta dan bakinciki sabida koda sukaje gurin bokan su Zuly cemusu yayi kawai suyi hkr Dan aure ba fashi se anyishi shiyasa gabadaya tarasa natsuwarta ga alameen yanzu yayi wuyar gani sabida shirye shiryen bikin
Ganin tadamune yasa su Ruky kwantar mata da hankali dacewa tabari akawo Amaryar bayan kwana biyu sumata dukan tsiya hakanne yasa Zuciyart yin Sanyi danko kayan fadan kishiya daaka bata batabi takansuba kawayentane suka dau na dauka itama suka zabarmata Wanda zata sa in amfara bikin
**********
Surbajo Tunda alameen yatafi yabarta kullum cikin tuno abinda yamata takeyi itade batasan sunan abunba amma in tatuno abun namata dadi har addua take Allah yasa yakara yimata
Ardo sosai yake shiri shima Dan tun ana sauran sati guda bikin kullum se an kwantar da sa anyanka dangin maman surbajo suma baa barsu abayaba sunzo bikin kwansu da kwarkwatarsu suma sunyma surbajo shatara ta arziki
*RANAR BIKI*
.
ranar asabar 31-12-2011 dubban jamaa suka shaida daurin auran Zahra Muhammad mahmud (wato surbajo)tare da angonta alameen jibrin sulaiman daurin auran dayasami halattar manyan shuwagabanni da yankasuwa uwauba sojoji manyansu da kanana
Ko ina kakai dubanka alummane tako ina ranar garin makarfi bamasaka tsinke sabida yawan alumma ga jiniya takoina natashi kowa mamaki yakeyi me alameen zeyi da surbajo yar kauye kamar haka hakade akagama taron daurin auren jamaa suka fara watsewa
.
Dayake tare zaa wuce da Amarya tuni motocin daukar Amarya sunfara dibar jamaa
Inda yawancinsu mutanen kaduna ne sabida ardo yace yana gudun kauyancin yan rigarsa shiyasa masu natsuwar kawai aka dauka
Amarya survajo wacce ke nade cikin wata lafaya Medan karan Kyau da tsada se kuka takeyi sabida rabuwa da gida dazatayi ammafa tayi kyau sabida wata yarinyar yayan mamanta me suna Bilkisu dasuka zo daga kaduna itace tayima surbajo Kwalliyar duk da ita surbajon bataso Amman seda akayimata kuma tayi kyau farinta yafito sosai
Sumaye tajima Tana yiwa surbajo fada akan zama da miji haka yan uwan mamantama sunmata fadan sabanin ardo da kukan da surbajo takeyi yakeson sashi kuka dakyar yaiya cemata surbajo aure ibadane kiji tsoron Allah.... Hawayen dayake tarewane suka kubce dsauri yabar dakin dabaze iya jure ganin kukan surbajoba
dakyar aka ja surbajo zuwa gurin motor dazata dauketa wacce ango alameen yake ciki yana jiranta yayinda Usman ke zaune agaban motar shida driver abaya alameen ke zaune se motoci guda hudu biyu gaba biyu baya sunsa motor atsakiya excode dinshine
bayan motor aka budema surbajo tashiga dakyar Tana shiga takifa kanta akan cinyarta tacigaba da kukanta bata lura da alameen dake gefentaba
.
tuni motocin suka fara tafiya ana jiniya Usman dake gaban motar ne yajuyo yana fadin
haba amaryarmu aymana afuwa haka munyi laifi Amman aymana afuwa
alameen ne yaamshi zancan dacewa sede inkaine kayi laifin Amman baniba wayace taamsa tanason auran kagako tunda taamsa dole tadau naannabawa tunda taga Dan fari me dimples tamakalemishi ita wai me wayo tacuceni ta taba raminko ay ga makomar cutarnan yakarasa zancan yana dariya
dasaurin surbajo tadago kanta Tana kallonshi Dan bata dauka yana motarba ido suka hada danshima ita yake kallo dasauri tayi kasa da idonta Dan bazata iya jure irin kallon dayake mataba
hannunta yakamo yana kallon zanen lallen dake Zane akan hannun lallen yayi kyau sosai wasa da hannun yashiga Yi tasigar daduk macen daakayiwa setaji dadin hakan
.
jawota yayi jikinshi yarungume yafara yimata magana akunne
yace
baby waya miki wannan lallen
dakyar tabashi amsa da Bilkisu ce tayimata
wannan Kwalliyar fa yatambaya duk itace tayimin tabashi amsa
kinyi kyau sosai yafadi yana hada bakinshi danata seda yafara kissing seda yaga yana shirin fita daga hayyacinsa sannan yasaketa
surbajo wacce bataso yadenaba kwanciya tayi ajikinshi Tunda yasaketa rungumeta yayi yana shakar kamshin jikinta tuni bacci yadauki surbajo gyara Mata kwanciya yayi ajikinsa tayadda bazata wahalaba kamin sukai gida
dago idonsa yayi carab suka hada ido da Usman ta mirror yanamasa dariya dan duk abinda yafaru tsakaninsu akan idonsa akayi
kunyace takama alameen Amman se ya maze yace to munafiki saidonnaka wato har akan mata da mijiko to thanks God matatace ay yafadi yana hada rai dariyace takwacewa Usman yace ikon Allah inbanda tsarguwa nimekaji nace
aynasan zakacene shiyasa natari numfashinka inji alameen
dariya Usman yasake yi yace rufamin asiri da kallon mata da miji ni kawai cartoon din Tom and Jerry nake kallo
duk yadda alameen yaso daurewa kar yayi dariya Amman yakasa duka yakaiwa Usman yana dariya yace saido de bakyau
harsuka iso gida Usman na tsokanar alameen Wanda kunya tahanashi ramawa
itako surbajo har suka iso gidan iyayen alameen bacci takeyi hankalinta kwance
0 comments:
Post a Comment