AUREN JARI Part 16-20
.
Tun kafin su bar anguwan kamal ya kira shema'u ya shaida mata komai ta jinjina wa al'amarin ta ce toh Allahsa wannan aure alkhairice garemu gaba daya ynxu sauran a sanarwa da umma yace eh na ma alhaji bayani gamu nan zuwa cikin lokaci kadan suka karaso kamal yace umma wannan shine ya taimaka aka miki aiki kuma ynxu nake aiki karkashinsa umma ta shigo kwararo godia alhaji mahir yace ai ba komai an zama daya yace sai dai hajia amana afuwa na yanke hukunci batareda an bi ta kanki ba wlhy wata marainiyace da ke cikin halin ukuba ta nemi mu taimaka mata ta fita daga kangin rayuwa na azaba da take sha ta roki Kamal da ya aureta ya cireta a gidansu ko ta samu saukin rayuwa shine toh muka gama komai ynxu haka ma har an daura aure umman kamal tace ai hakan yayi kyau ai taimakone kuma an ceto rayuwar yar nan Allah dai ya mana jagora suka amsa da amin yace sai dai hajia sudan zaku koma da zama dan kamal zaije yana kula da kampanina da ke can kunga bai dace ace ku zauna ku kadai a nan ba ummansu ta danyi jim sannan tace ai wannan hidima yayi yawa alhaji yace ba komai ai yi ma kaine ni a matsayin da na dauki kamal kuma ku dauki abunda nake a matsayin sadakace ummansu tace toh Allah shi amfana ya dada budi suka amsa da amin yayinda kamal ya kalli yarsa ta mai alaman ya kwantar da hankalinsa fita sukayi alhaji yace na kammala komai na tafiyarku gobe da dare sai ku tashi akwai wanda zai jiraku a airport so
Kawu ne ya shigo jikinsa sai rawa yake ya dubesu duk sunyi jugum kaman masu zaman makoki ya ce ku shirya mijin Rahima zai shigo ya gaisheku ynxu darduma suby ta shimfida mai Mahmoud ya fita suka shigo tare cikin girmamawa ya gaida su umma kuma suma sun karbesa cikin sakin fuska suby ta kawo mai abun motsa baki yayinda nani suka tashi suka shige ciki aka barsa daga shi sai Mahmoud sun danyi hira kadan kafun ya tashi ya shige dakin Rahima a dunkule ya sameta ta bashi tausayi sosai ya zauna tare da riko hannunta yace sis tashi kije yana jiranki Rahima ya mun bayani ba yau zaku tafi ba sai zuwa gobe shi ya dauko mata mayafinta ya lullubeta da shi tare suka fito ya ma kamal sai da safe ya fice ya bar gidan tunda ta mai sallama bata sake magana ba shi ya gaisheta kunya ta hanata amsawa dan ita ya kamata ta gaida shi yace Rahima ban san da wasu kalamai zanyi amfani dan baki hakuri ba wlhy ba so na bane in miki dole a zancen aurenmu nima an fi karfina ne amma ki yadda dani ni matsoyinki ne na haqiqa maganganunsa sun daure mata kai tace bn gane anfi karfinka ba yace Rahima for now so nake mu fahimci juna i wil explain everything to u but now is not d tym just trust me pls tace trust u is sumtn i cnt do bn sanka ba bn san waye kai ba lokaci daya kazo ka shiga rayuwata ka rabani da farin cikina ka yi amfani da matsayinka ka nuna mana fin karfi ka sani aurena da kai na daukesa ne a matsayin kaddara kuma biyayya da zanyi face haka kar ka yaudari kanka a cewa zan taba sonka bn ma san ya zan fara rayuwa da kai ba cos na tsaneka tsanan da bn taba ma wani irinshi ba tana kawowa nan ta tashi ta shiga daki ta hau kuka jikinsa a sanyaye ya bar gidan yana isa ya ci karo da yarsa fadawa jikinta yayi yana kuka wiwi kaman yaro yace ta tsaneni sis Rahima hates me da bakinta ta furtamun ta tsaneni sis rahima ce rayuwana ya zanyi in zauna da ita while she hates me tana shafa kanshi tace bro just gv her tym evrytn wl come to pass ka ji habibi xafin abunda aka yi mata takeji she didn't mean it with tym Rahima zata so ka trust me on dat sai sannan ya saki ransa ranan daga shi har Rahima ba wanda yayi baccin kirki
~~~
Mahmoud ne suka shigo da kawu ya musu bayanin cewa sudan zasu wuce dan a can yake aiki kuma yana son umma da Mahmoud su biyosu can umma tace ita ba inda zata dan ita bata ga dalilin da zai sa taje tayi kanene kane a gidan yarta ba da kyar Mahmoud ya shawo kanta akan cewa a hankali in sunje ya samu aiki zai nema musu gida su koma umma tace naji na yadda amma wannan tafiyan ba da ni za a yi ba in kunje kayi settling sai ka dawo mu koma wajajen 12 jirginsu Rahima ya tashi sun sha kuka itada suby nani ma sai da tayi kwalla dan sun basu tausayi Rahima kuwa da kyar aka banbareta daga jikn ummanta suna hawaye sai ranan su shema'u suka ga Rahima rungumeta tayi kaman dama sun jima da sanin juna haka ma ummarsa waje daya suka zauna itada shema'u yayinda kamal ya zauna da ummansu Mahmoud kuwa na can gefe suna sauka suka karasa wajen da ake daukan mutane yaga wani ya rike sunansa ya karasa suka gaisa sannan suka shige ya jasu wata katafaren gida ya shigar dasu wanda za a yi kiransa da aljannar duniya kusan sashi ukune a gidan ya musu bayanin komai sannan ya musu sallama yace gobe in Allah ya kaimu driver da masu aiki zasu zo sashi daya umma da shema'u suka shiga dayan kuwa Mahmoud ya shige dayan kuwa kamal ya dauki kayansu yayi ciki da shi yayinda Rahima ke biye da shi
Suna shiga sukayi arba da katuwar falo wanda gefenshi an rufe da wani abu kaman labule but u cn tru it dan na hango yar dining daga parlor sai wata yar corridor can kamal ya nufa yayinda Rahima ke biye da shi dakuna biyu suka gani suna fuskantar juna ya bude daya ya saka mata kayanta a ciki murya can kasa ta gode mai murmushi yayi ya fice daga dakin ya bude kofan da ke fuskantar tata wanda ya sada shi da wani parlor gskia ba kamal kadai gidan ya burge ba dan nima bily tsarin gidan wani daki ya bude yaga computer ce a ciki sai kujeru murmushi yayi alaman ya burgeshi ya yi gaba ya sake cin karo da wani daki budewa yayi yaga bedroom ce ya shigo tareda aje kayansa drawer da ke dakin ya bude ya shirya kayansa sannan ya dauki towel ya shige toilet ya sake wa kansa shower shirin kana nan kaya yayi yayi kyau sosai cikin black shirt da blue jeans ya fito ya sake ganin wata kofa gaba da nashi ya bude sai yaga wata kofa opp his on his left kuwa hanyace da zai sada shi da cikin gida ya bude kofan itama yar bedroom ce sai toilet ya fito yayi cikin gida side na ummansa yayi ya dubasu bai jima a wajensu ba ya fito inda ya hadu da Mahmoud shima na zaga gida tare sukayi surveyn gidan inda suka tadda garden da wajen motsa jiki ta bayan sai yar bq da ke kunshe da dakuna uku tare suka koma ciki Mahmoud yayi sashinsa shi kuwa ya shige nasu Rahima ta kai hannu zata bude kofan kenan taji an ja kofar ganinta kawai ta yi a jikansa da kyar ya iya karesu daga fadiwa tayi sauri ta raba jikinta da nasa wanda kamal bai so dan shi kadai yasan meh yaji dan contact da sukayi ta dago taga ita yake kallo tayi saurin kawarda kanta tareda shigewa ciki ya bita da ido tayi mai kyau sosai cikin kayanda ta canza red gown ne ta dauko karamar kashka baki ta yafa xama yayi a falo yana jira ko zata sake fitowa dan bai gaji da ganinta ba ita kuwa sashin dinning tayi taga kitchen ta shiga ta hau dube dube kitchen in ba abunda ya rasa ta bude kofan da take gani kamr store wanda tayi sa'a dan store inne cike yake da kayan abinci su potaoes shinkafa da sauransu fridge ta bude taga shima a cike yake ta debo carrots da su green beans ta yayyanka ta dauko hanta shima ta yankashi kanana ta sa a tukunya ta mai hadi shinkafa ta debo ta zuba ruwa a tukunya na per boiling sai da duk ta gama tayi juyin duniya bata ga risho ba sai gas cooker gashi ita tunda take bata taba amfani da shi ba tafi minti biyar a tsaye a wajen bata ji shigowansa ba kawai taji yace bari in fita in nemo mana abunda zamu ci ta dan razana ya fahimci hakan yace sorry i startled u tareda karasowa wajenta sai sannan yaga uban aikin da ta yi ya dubeta yace ai da baki wahalar da kanki ba zanje in nemo mana abinda zamu ci kije ki huta kawai tace da ka barshi kawai tunda na fara ba ynda bai yi ba tace sam ita sai tayi girkin nan yace toh since u insist is dia anything i can help with shiru tayi yayinda her gaze went to the cooker ya bi inda take kallo da ido ya fahimci meh take nufi ashana ya dauka yace dan matso kiga cikin jin kunya ta matso ya nuna mata yanda ake kunnawa shima dai zuwansa service ya san yanda ake kunnawa ya tayata daura ruwan yace barin dan fita ok kawai tace shagon da ya gani yayin shigansu ya nufa ya sayo drinks ya dawo ita kuwa ta yaye gyalen ta daure kanta da shi mutuwan tsaye yayi da ya ganta a hakan ashe yarinyar nada sura mai kyau haka juyowan da zatayi kawai ta gansa ya tsura mata ido ta ga kallonsa ya koma kirjinta dan gaban rigan ya dan sauko nan take ta hada rai ya zai na mata irin wannan kallon ni Billy nace mutum da abunshi gyalenta ta yaye ta rufe jikinta da shi ta wuceshi ta yi dakinta shima a sanyaye ya karasa gun fridge in ya bude ya ganta a cike falo yayi gefen dinning ya hango wata fridge in ya karasa ya bude ya ga drinks ne da ruwa a ciki ya sa wanda ya siyo ya koma falo ya zauna jin motsinta ya sashi juyowa yaga ta cire gyalen ta sa hijabi murmushi yayi a xuciyansa yace wt tym kitchen ta nufa ta zuba abinci a coolers in ta fara jera nasu a dining bata bi ta kansa ba ta dauki nasu Mahmoud ta fice da shi
.
A harabar gidan ta hadu da ya Mahmoud ta mika mai nasa ta shige side nasu umma a falo ta samesu suna yar hiransu ta gaishesu da gajian hnya adda shema'u ne tace ba dai girki kikayi ba amaryanmu murmushi kawai ta yi umma tace lallai a gaisheki yannan ina kamalun mesa xai barki kiyi girki da gajiyan nan bazai sayo abinci ba tace umma naga akwai komai a gidan ba amfani a saya a waje karma ya zamo bamu iya cin abincinsu ba tace kinyi gskia Adda ta tashi ta dauko musu plate ta fara xuba musu cikin jin kunya Rahima tace adda ki sa dani dan ban saba cin abinci ni daya ba murmushi tayi tace mesa toh baku ci da kamal ba ta sunkuyarda kanta tace ya fitane kafun ta kara fadin wani karyan sai gashi ya shigo da sallama adda tace yauwa bro habibi kazo a daidai dama matarka na korafin cewa bazata ci abinci ita daya tunda kazo sai kuci tare abunku kunya ya sa ta kasa cewa komai umma tace tashi yannan ki sa muku abincin dan mu ba irin kunyan nan a al'adarmu ynxu ki saki jikinki ku ci abinci da mijinki kar kiji kunyanmu cin abinci da miji akwai kara soyayya kinji Rahima tashi tayi ta shiga neman plate dan ita kunya ma maganganun umma ke bata irin wannan suruka haka ba kunya adda ne ta taso ta tayata dauko plate ta mika mata da spoons ta xo ta xuba musu ta kawo gabansa ta aje ta takure ta zauna a gefensa ya dubeta yace bismillah sannan ya fara ci ita kuwa shiru tayi ta kasa motsa spoon in umma ta juyo ta kalleta ta ce kamalu bata a baki tunda ta ki ci ba shiri ta ja cokalin ta fara ci murmushi yayi ya debo ya kai mata baki,baki bude take kallonsa ita kam bazata iya wannan rashin kunyan ba ta dubi gefen su adda ta ga hnkalinsu bai wajensu ta juyo ta hararesa ya maida cokali ya cigaba da cin abincinsa a haka hr suka gama umma tace wannan amarya da kunya take ana cin abinci da miji ko dan hira babu murmushi Rahima tayi itakam dariya ma take bata tareda adda suka dauraye kwanukan sunayi suna yar hiransu anan Rahima ta yini har dare dan umma nata kashesu da dariya a yar kankanin lokaci Rahima taji sonsu na shiga ranta tana sallar isha Kamal ya shigo ya dubeta ya ce muje ko ya miko mata hannu gudun maganan umma ya sa ta miko mai ya dagota a sallayan suka musu sai da safe suna fita ta fara kokarin kwace hannunta jawota yayi ta fada jikinsa turarensa mai dadi ya shagalar da ita ya tallabo fuskarta yace y do u hate me Rahima while kin san ni ba cutanki ba kinsan ni mai sonki ne look into my eyes n tel me if u c d opp ina sonki Rahima so mai tsanani pls ki soni Rahima bata ankara ba taji bakinsa a nata ya fara kissing nata Rahima taji bakon al'amari ta fara kiciniyar kwace kanta yana saketa tayi side nasu da gudu ta fada dakinta ta kulle gado ta hau ta fara kuka tunanin Malik ne fal ranta yayinda take jin sonsa a ranta da sauri ta kauda tunaninsa tareda yin istigfari ta tashi tayi nafila ta roki Allah ya cire mata sonsa a ranta dan ynxu matar wani take
Karfe shabiyu daidai jirginsu Malik ya sauko taxi ya dauka yayi kwatancen gidansu Rahima tunda suka yo kwanan gidan yaji gabansa na fadiwa kai tsaye ya shige gidan tareda sallama sai dai ya rinka cin karo da bakin fuska budurwan da ke shara a tsakar gida ta dago taga sai leke leke yake shi duk wai ya gano Rahima ta karaso tace malam lafia batareda ya kalleta ba yace Rahima nake nema ta ce gidannan ba Rahima ya juyo yana mata kallon kar ki raina mun hankali sannan yace masu gidan nake nufi tabe baki tayi sannan tace mu kenan n if bazaka damu ba zan koma aikina kaikuma la gaggauta barin gidan nan kafun ummana ta fito ya kansa bai gama daurewa ba sai da yaje gidan kawu yaga suma basu gidan abunda nima sai yanxu nake sani ashe bayan tafiyansu Rahima suka koma sabon gidan da kamal ya siya musu ko ince abban Fadeela ya bashi da kyar kafafunsa suka kaisa gidan ganinsa kawai iyayen nasa sukayi suna gaisawa ya wuce dakinsa wayansa ya cire for d tenth time ya sake gwada line na Rahima da Mahmoud amma a kashe toh wai meke faruwane tsaki yayi tareda wurgar da wayan ya rike kansa da hannayensa biyu bai ji shigowanta ba kawai ganinta yayi gabansa ta sa hannu ta cire mai tagumi da yayi tace welcome home sweet i rily missed u ynxu mama ke sanar dani shigowanka shine nace barin shigo inyi welcoming naka evendo ban san a ina miji ke kin sanar da matansa cewa yana hanya ba ai da na sa a ma abinci but first tin first ynxu tashi muje kayi wanka baki bude yake kallonta ya san dai bata shaye shaye da sai yace effect nashi ne ko dai tayi ta samu tabin hankaline da baya nan hr take tunanin an musu aure bai gama razana da al'amarinta ba sai da yaga ta ja towel biyu ta jefo mai daya ta hau cire kayanta da sauri ya tashi ya riko hannunta yace Fadeela kinada hankali kuwa murmushi tayi ta kai hannu zata shafi fuskarsa ya ja baya cikin tsawa yace bace mun da gani fita ki bar mun daki gogaggiyar ko a jikinta sai ma kara matsowa da take tana cigaba da cire kayanta ba shiri ya fita daga dakin a guje har yana fadiwa ummansa dake falo ta taso tace lafia Malik da yatsa ya nuna dakinsa yace umma Fadeela ta haukace kuje ku cirota a dakina dai dai nan Fadeela ta fito umma ta ce Fadeela me ke faruwane ko kunya babu tace ma waifa dan nace muje in tayasa wanka shine ya kama cewa na haukace dariya umma ta hauyi Fadeela ta tayata umma ta dubesa tace sai dai in kai ke haukan kana ina aka daura muku aure ko ka manta alkawarinku da abbantane kafun yace wani abu ummansa ta shige side nata Fadeela ta dubesa tareda mai fari da ido tace ina jiranka a ciki jin abun yake kaman mafarki duk da ya san da zancen aurensu but y zasu mai haka key yaja ya fita ya bar gidan bai zame ko ina ba sai gidan amininsa Dr Nura
Dr Nura aminine ga Dr Malik kusan tare suka taso hr zuwa inda iyayensu suka turasu india karatu ynxu kuwa sun dawo suna bautawa kasarsu
Horn yayi mai gadin ya bude mai ya gaishesa ya ce baba yana cikine yace eh shima ynxu shigowansa yayi parking motan ya shige a falo ya zube kan kujera ya jingina kansa tareda rufe idonsa dan kansa da ke sarawa a haka Dr Nura ya fito ya sameshi yayi mamakin ganinsa hr bacci ya fara daukansa ya ji an dan bugesa yace kaifa dan iskane Dr Nura ya fada cikin wasa yaushe a gari tsaki Malik ya yi tareda mikewa a kan kujeran na bar gida dan in huta in ka isheni kaima barin gidan naka zanyi yace hutawarka lafia ango wane ni in takuraka ya juyo da sauri yace wato dan iska ka sani kenan shine da mukayi waya ko ka gayamun yace ai kai zan tambaya tunda kaki sanar dani kuma beside dat Abba yace kar in gayama ni ma sai da ya kirani ya ban kati na sani ya dubesa yace katin mene yace na dinner da aka shirya muku mana ni dai na gama rabawa hr munyi shopping ni da madam for d big day sai ynxu ya ce ina ma takene yace ta je gida bt inaga ynxu ma tana hanya malik ya tashi ya zauna yace zakuyi kayanku banda ni dan ba da ni za a yi wannan bidi'ar ba ni ynxu damuwana Rahima Nura tun shigowana nake neman Rahima ba ita ba labarin yan gidansu Wlhy Nura am rily dsturbd i nid to c her in gaya mata tun kan taji a bakin wani tace na yaudareta I nid to tell her once more dt she is ma lyf n aurena da ita na nan daram ITACE ZABINA aurena da Fadeela kuma *Biyayyace* nake ma iyayena Dr Nura ya tashi ya dauko wata yar leda da ya aje a drawernsa da ke falo ya miko mai malik ya dubesa sannan ya dubi ledan yace karba nakane ya karba ya bude wayace da ya siyawa Rahima sai ATM da zoben da ya bata cikin i'i'na ya ce wa ya baka su Nura Zama yayi yace ina office wata tazo nemanka shine ta barmun su yace kuma ba Rahima ba yace haba buddy Rahimance bn sani ba yace amma dai suna dan kama da yarinyar ya ce it must b suby nan ya hau safa da marwa a falon Dr Nura sai binsa yake da ido Malik ya dawo ya zauna ya ce Rahima Y yace Nura bata ce ma komai ba kai ya gyada alamar a'a yace dia must b sumtn dia sudden disappearnc n now dis haka kawai Rahima bazata maido mun su ba Dr Nura yace am suspectn two tins Malik ya dubesa alamar yana son jin me zai ce yace its eida taji labarin aurenka ko kuma ita tayi aure wani abu ya ji ya tokare mai a makoshi jin Dr Nura ya ambatawa Rahima aure yayinda bugun zuciyarsa ta tsananta ya ce nop bn yadda Rahima zatayi aure ta barni ba no my Rahima bazata mun haka ba daidai nan matar Nura ta shigo tareda sallama tana ganin Malik ta hau zolayansa ango an sha kamshi tashiwa yayi yace sai anjimanku tace ba dai ni na koreka ba yace ai in na zauna ke da mijinki wil worsen ma situation Dr Nura yace da ka tsaya muci abinci ficewa kawai yayi nura ya biyosa da ledan riko hannunsa yayi yace easy man kwantar da hnkalinka insha Allah zamu sami Rahima ka kwantar da hnkalinka man ka sha angwanci yanxu warce ledan yayi tareda kai masa bugu ya yi hanyan shiga gida yana dariya
~~~
Yau ake dinnern Malik da Fadeela ba a son ranshi ya je wajen ba Fadeela kuwa kaman an mata alkawarin aljanna ko ina yayi tana like da shi sai daukansu hoto ake
Rahima ta fito daga dakinta cikin riga da skirt tayi bala'in kyau remote ta dauka ta hau kan tree sitter ta mike tareda kunna TV ta hau searching channel Kamal ne ya shigo tareda sallama ya karaso ya zauna a gefenta ta tashi tareda mai sannu da zuwa ya amsa tareda mata sannu da gida tace in kawo ma abincinka nan ne ya dubeta yace kefa tace naci da su adda murmushi yayi yace barshi kawai zan tashi na diba yace meh kike kallo ne tace channel na ke nema remote na dish ya dauko ya sa musu arewa channel daidai inda presentern ke cewa munyi tattaki har zuwa garin Borno dan hallarar bikin yayan shahararran dan kasuwan nan Alhaji mahir sai ku biyoni Kirjin Rahima ne ya hau bugawa ganin Malik da Fadeela inda suke takawa a floor ana musu kari sunyi bala'in kyau sai haskasu ake Fadeela ta kai bakinta daidai kunnensa tana mai magana yayinda ta zagayesa da hannayenta shikuwa ya bartane dan kar yayi embarrassing nata if not sam bai so rungumesa da ta yi ba hawayene taji ya taru a idanunta ta danne ta hanasu zubowa Kamal kuwa sai yanxu ya dago yace Wow Dr Malik masha Allah gskia sun dace zanso ace i was dia ya juyo ya dubi Rahima dan ya gaya mata irin taimakon da ya musu yaga tana hawaye tayi sauri ta share hawayen tareda mikewa tayi dakinta key tasa ta haye gado pillow ta dauko tayi burying fuskanta a ciki ta hau kuka hankalin kamal ya tashi sosai ya taso ya bita yaji ta sa key kunne ya sa a jikin kofan ko zai jiyo motsinta amma shiru falo ya dawo ya zauna tunani kala kala a ransa babban damuwarsa abunda ya sa Rahima kuka karar wayarsace ya katse mai tunani alhaji mahir naga rubuce kan screen ya dago ya dubi dakin Rahima sannan ya fita bayan sun gama wayan yake tambayarsa ko akwai damuwa yace am alhaji dama inason in tambayeka wani abune gameda Rahima yace ina ji alhaji mehsa kace na aureta kuma ka sani yin nisa da ita yace look my friend ba na son kananan maganganu ko ka manta deal namune in d contract akwai inda ake cewa on no occasion should u question my doing so tk note yace yi hakuri Alhaji juyowan da zaiyi yaga Rahima cikin i'i'na ya ce tun yaushe kike nan wani kallo ta mai sannan tace ynxu fitowa na dama znce ma zn shiga side nasu umma ne ya ce ok hr ta juya ya kira sunanta ta tsaya batareda ta juyo ba ya tako zuwa inda take yace r u ok kai ta gyada mai yace toh mesa kike kuka dazu ta dago tace its ma nature tins lyk dt mk me cry sorry u hd to c dat ta fada tareda mai murmushi da ya sanyaya mai rai shima murmushin yayi kafun duk suka wuce ita tayi side nasu umma shi kuwa yayi side nasu
Tafe suke a mota tunda suka bar wajen dinner sai wani tattaba shi take tana cewa i cnt wait to gt home to show u how much i luv u Dr Nura da ke tukasu sai gintse dariyarsa yake Malik ya dubeta murya can kasa yace haba Fadeela wannan wacs irin rashin kunya ne haka ba kya kunyan idon nurane bata rai tayi tareda janye hannunta a jikinsa hr suka iso ba wanda ya tanka wa wani horn nura yayi mai gadi ya bude musu gidane na agani a fada wanda abban Fadeela ya basu a matsayin wedding present nura na parking ta bude motar ta yi shigewarta ko godia Dr Nura bai samu ba ya kalli Malik ya hau daria hrda rike ciki Malik ya hararesa yace dan iska me ke baka daria yace yau kana hannu ma guy hr ka fara ban tausayi ya bude bayan motan ya miko mai leda biyu daya yogurt ne mai sanyi a ciki daya kuma ledan kajine na _The_ _Ultimate_ ya miko mai yace a angwance lafia yana daria ya shige motarsa ya tada ta Malik yace ynxu kai tafia zakayi dan Allah ka dan zauna ya ce wa yanda matanka take hannu ai korani zatayi kaga tafiata na bat matana ita kadai a gida ya figi motar cikin sanda ya shigo falon a hankali ya bude fridge in ya sa yogurt da kajin juyowan da yayi ya ganta tsaye ya razana da ganinta ta canza kaya zuwa yar slvlss nyt gown shara shara da ya tsaya a gwiwa ta fara takowa tana mai wani irin shu'umin kallo ya fara ja da baya hr ya jisa a jikin fridge ta karaso tana daria meh haka sai kace ba na miji ba pls kr ka ban kunya ya malik hnnun shi ta kama yayi saurin janyewa ta langwabar da kai tace ko dai sai na kira hajia ne ya san kadan daga halinta zata iya dan ba kunya take jiba sum sum ya bita zuwa dakinta ya sata tayi alwala ba dan ta so ba sai wani hada rai take suka yi raka'a biyu tareda addu'a yace dauko mana yogurt in nan gani kawai nayi ta ja sa zuwa gado ganin abun Fadeela ya fi karfina ya sa nima na ja musu kofa
Karfe hudun dare ta fara tashinsa cikin magagin bacci ya bude ido yana kallonta tace i nid more zumbur ya tashi yace wai Fadeela ke wace irine ne ni gskia bazan iya da jarabanki ba a kwana ana abu daya sannan ynxu na sami bacci ki hanani ko ance miki abinci ne gskia bazan iya ba ya dauki rigarsa ya fice ya barta wayanta ta ja da niyyan kiran hajia taga its four in d mrn tsaki tayi tareda wurgar da wayan kiran asuban fari ya tashi ya shige bandaki ya sake wanka tareda dauro alwala ya nufi dakin Fadeela tayi shabe shabe tanata tirkan bacci ya tadata dan tayi sallah tsaki tayi ta gyara kwanciyanta ganin zai takura mata ya sa tace naji zan tashi amma meh da ya dawo daga masallaci inda ya brta nan ya sameta kada kai yayi cikin takaici ya ye bargon da ke jikinta ya ce wlhy ko ki tashi ko nayi miki wanka da ruwan sanyi tashi tayi tana tsaki tareda mai harara ta shige toilet shima ya wuce dakinsa
~~~
Tun Ranar da Rahima taga Malik a TV ta yi alkawarin cireta daga ransa ta kuma hakura zata zauna da kamal ko bata sonshi tana zaune ya shigo tareda yar file a hannunsa ta mai sannu da zuwa ya zauna gefenta ta taso ta kawo mai ruwa mai sanyi ya sha tareda gode mata ya ciro wayansa yayi dialing wata numba ynda yake wayan ya sa ta gane da ummanta yake waya ta matso kaman zata shige jikinsa ji tayi yace gata nan umma ya miko mata wayan tareda bata waje sun jima suna waya kana ta baiwa suby da nani suka gaisa bayan suka sake mikawa umma tace Rahima ina ce kuna zaman lafia da mijinki tace eh umma tace toh ki cigaba da hakuri Rahima kuyi zaman lafia mijinki na sonki sosai bakiga hidiman da yake mana ba tafiyarku ya canja mana gida ki gode mai Rahima tace toh umma kawu fa tace yana nan tace ince bai takuraki tace krki damu kanki Rahima da haka suka aje wayan ya fito cikin jin kunya ta mika mai wayan tace nagode da hidiman da kake wa su umma yace no Rahima ba godia tsakaninmu ai nima uwata ce ta dauko abinci ta fara zuba mai yace kefa tace naci da adda ya dan bata rai yace dole in ja ma adda kunne ta dibesa baki bude ta ce addan yace iyi tana hanani cin abinci da matata tace nikam kr ka mata magana zan na jiranka Sallamar ya Mahmoud ya katse
[10/1, 9:48 AM] Billy: Ta tashi ta bude mai kofan ya shigo ya mikowa kamal hannu suka gaisa itama ta gaishesa ta ce Ya Mahmoud in sama abinci ya shafi kanta yace a koshe nake sis wanda kika kai mun ma ban cinye ba nazo gaya miki dama na samu aikine kuma hr sun ban gida sun mun alfarma na karbi leave jibi zani in taho da umma farin cikin da Rahima ta shiga bazai misaltu ba ta kankame hannunsa tace am happy for u bro Kamal ma ya tayasa murna har kofan dakinsa Rahima ta rakasa tace yaya wlhy naji dadi umma zata dawo nan da zama yace ai ni tunda mukazo hnkalina na wajenta nasan zama gidan kawu bazai taba mata dadi ba ki koma ciki sai na shigo anjima
Tafiyan ya Mahmoud da kwana biyu Rahima na site na su adda tana gyara mata kai Kamal ya shigo ya mace da kallon gashi irin na Rahima dan ko ni ban san tanada suma haka ba suka juyo suna kallonsa ya karaso ya gaidasu Rahima kuwa ta mai sannu da zuwa envelope ya mikowa Adda shema'u ta bude taga admission letters ne guda biyu daya na public administration daya na medicine yace dauki naki ki bata nata ta mikawa Rahima na medicine Rahima ta kasa boye farin cikinta godia sosai take mai Ya karaso wajen Adda da ke hawaye ya riko hannunta ya ce dnt cry pls u'v always tk kia of me u deserve more dis isnt even enuf n i cnt tnk U enuf duk matsayin da na taka a rayuwa da taimakonki na kai kin hana kanki komai dan ganin na samu cikakkiyar ilimi ynxu its ur tym pls dnt say no pls murmushi tayi tareda shafa kansa tace tnx bro habibi am rily proud of u ta sumbaci gefen kumatunsa muryan umma suka jiyo nacewa toh kunga kunsa mun ya kuka suka juyo suka ga Rahima na share kwalla tana dariyan furucin umma ya dubeta cikin kulawa yace umma wannan yar taki ai cry baby ce umma ta tabe baki ta ce kai kasan wannan kiry babin duk suka yi daria
Bayan kowa ya watse kamal ya dubi adda yace adda na samu aiki fa tace aiki kuma a ina yace wani karamar organization ne haka dey lyk ma result evendo d salary is nt dt much it wl do tace toh kudin da alhaji ke turowa fa yace dts it sis bazan iya rike Rahima da shi ba it dsnt sim ryt to me ni kadai na san ynde nake ji gameda da Rahima dnt knw hw she wil feel in ta gane aurena da ita *Auren* *Jari*ne i cnt stand seeing her hate me n sanin cewa da kudin nake ciyar da ita hr in mata makaranta wl worsen d situation she wil hate me more lt me bear wt d former first a hankali zn gaya mata gskian ta daura hannunta a kafadarsa tana patting nasa tace an rily proud of u n ol wl b well insha Allah
.
Tunda ta tashi da asuba bata koma ba potatoes tayi frying sannan tayi egg soup bayan ta jera komai kan dinning ta shige toilet tayi wanka ta shirya cikin abaya baka ta yi rolling light mk up tayi ta fito ta zauna tana shan tea kamshinsa da take bala'in so ya fara sanar da ita fitowansa tana dagowa kuwa suka hada ido yayi bala'in kyau cikin black suit da red tie bata san lokacin da ya karaso ba ji tayi ya hura mata ido ta dan razana cikin jin kunya ta gaishesa ta ja plate ta zuba mai tareda ajewa a gabanshi yace kefa tace tea wil b ok for me tashi yayi ya koma kujeran da ke gefenta bugun kirjinta ya karu cup da ke hannunta ya karba ya aje ya debi dankalin tareda kaiwa bakinta ba musu ta karba yace u nid to eat bakisan yaushe zaku gama da skul ba n ba lallene ki iya samun abunda za ki iya ci ba so eat sai da ya tabbatar ta koshi sannan shima ya ci nasa tare suka fito sukayi side nasu umma suka gaisheta kafun su fito already driver na jiransu karfe tara daidai suka isa international university of Africa sai da yi putting nasu tru sannan ya musu sallama da zai tafi ya miko musu waya yace duk na sa muku no a ciki if u nid anything just kol ba su suka gama ba sai around 12 Adda ta ce Sis kira mana Kamal ya zo ya daukemu cos am damn exhausted numban da ta gani tayi dialing bugu daya ya dauka ya ce mata gashi a bakin skul in su fito yana ganinsu ya fito ya bude musu motan Rahima ta shiga gaba yayinda adda ke baya adda tacw drivern fa yace sumtn cm up shine ya tafi ynxu mai zaku ci dan na san kun gaji my wifey cnt cook da gajiyan nan ya dubeta tareda mata murmushinsa da ke kashe mata jiki murmushi itama tayi tayi sunkui da kai tana wasa da yar yatsunta tace nayi stew kafun mu fita so in mun koma rice kawai znyi boiling n it wont tk long ji tayi adda ta rungumeta ta baya tace i luv u sis kaman kinsan ina son cin rice n stew kamal ya ce ina wifey daidai mu kikayi ko ita ta je ta dafa musu itada umma a daina wahalar mun da mata ta mirrow ya hango zata kai mai duka ya kauce yace sis am drivn fa tace den u shldnt hv start it n besides ma new sis wunt deny me anything koh Rahina murmushi tayi Kamal yace oh sis dan shinkafa hrda sa mata wani Rahina daria sukayi tace da alama bro Habibi yau da tsokana ka tashi bt baka isa ka shig tsakanina da Rahima dan ni da ita now r lyk 5&6 hr suka isa bata san sun iso ba ya zagayo ya bude mata ta gode mai adda kuwa ta bude kayanta ta ce tunda ni baza bude mun ba nayi ciki ya dubeta tareda sosa keya yace sorry sis kafun ta cire kayanta hr ya daura rice in yana per boiling ta shigo ya riko hannunta ya ja kujera ya zaunar da ita so he knws how to cook ta fada a ranta tana bin duk wani motsinsa duk dagowan da zai yi sai sun hada ido kunya duk yabi ya rufeta ta rasa gane mesa ta kasa dauke ido a kansa d guy is so handsome ya gama ya sa musu nasu a plate sannan ya dauki nasu umma ya kai musu a palor ta shimfida musu food mat ta aje musu abincin a kai tarda drinks bayanda baiyi ba yayi feeding nata amma taki tare suka dauraye plates in yace i almost forgot ya Mahmoud ya ce in tura mishi numbnki tace lt me dry ma hnds sai in kirashi sun jima suna waya yake shaida mata widn d week zai zo tace bro pls kace nani ta daka mun su yaji n inason sobo da kayan kamshi da su kuka da tagama ta juyo taga ita yake kallo yace duk wannan ke kadai yar daria tayi tace nayi missing abincin gidane
Washe gari ita kadai ta tafi skul tare da kamal suka nemi lcture hall nata hr bakin hall in ya rakota yace kol me wen u r tru tace k yarinyan da ke gefenta ta juyo ta miko mata hannu tace hi ta mika mata hannu itama tareda cewa hello yarinyan tace if dats ur bro den girl u r ma new bestfriend ur bro is damn hot wani kallo Rahima ta watsa mata tareda janye hannunta ta shige hall in empty seat ta nema ta zauna wata black ta zo ta zauna tareda mata sallama tace am Hauwa bt u can kol me Hauwie am from nigeria n u Rahima tace wow nima am from dia sai gasu sun sake suna hira da aka gama lectures sukayi exchangn no tace gobe i wil introduce u to d rest of ma frnds tace Allah kaimu tana fita taga Kamal tsaye da yarinyan daxun ko me take gaya mai oho ga wani irin kallon da take mishi Rahima taji wani abu ya taso ya toshe mata makoshi a take mood nata ya canza ta karaso gani nayi kawai ta riko hannunsa tareda kai masa peck a kumatu tace hey luv baki bude yake kallonta ta juyo gun yarinyan ta watsa mata harara kamal ya dubeta yace tnx Elena my wife is here so we hv to go ya bude mata mota tareda rufe mata tace wato hr ya san sunanta Allahsa dai bai karbi numbnta ba ya shigo ya tada mota suka dau hanya ya lura da yanayinta shi mamakinta ma yake wt did she jst do ba dai Rahima ta fara sonshi ba wani dadi yaji ya ziyarce shi in dai hakan ne toh da zaifi kowa murna hr suka isa ranta a bace yake yana parking bata jira ya bude mata ba tayi cikin gida
0 comments:
Post a Comment