AUREN JARI Part 21-25
.
Tunda ta shiga ba ta fito ba sai da ta ji cikinta na kuka a falo ta gansa yana danne danne a laptop insa ya dago ya dubeta suka hada ido tayi saurin kawar da kanta kitchen ta shiga taga hr yayi warming abincin da tayi kafun ta fita ta diba ta koma dining tana ci ta gama ta dauraye plate in ta shige daki sallah tayi sannan ta fito taga baya falon side na su umma ta wuce hr dare tana wajen ta jira ko zai shigo amma shiru ta ma su umma sai da safe ta wuce side nata dn ita bata da tsoro irin na maman ili😜
Tana dai kwance ne amma hnkalinta na wajen jin shigowarsa hr bacci ya dauketa wata azababbiyar ciwon cikine ya tadata sai murkusu take a kan gado zufa sai keto mata yake hawaye na bin kuncinta da kyar ta iya tashi ta ji kafanta duk ya riketa da rarrafe ta karasa kofan dakin kamal tana bugawa yayi mamakin ganinta a zaune ya sunkuya tareda tallabo fuskanta kafun ta yi magana ta fadi jikinsa sumammiya a rikice ya dau key ya sungumeta yayi waje da ita gudu yake tsakaninsa da Allah hr suka iso asibiti inda yaga an rubuta emergency ya nufa da sauri aka bata gado an dubata sannan akayi transfern zuwa wani daki nurse da ta dubata tace she wil b nidn ds ta miko wani takadda tace n brng her some new clothes ya shiga yaga tana baccinta ta cikin kwanciyan hnkali nurse in ne ta sake shigowa tace u r stil here cnt u c shs staining d bed n her clothes sai sannan ya lura da yanda gadon ya fara baci da jini ya dubi list da aka bashi ya ga pad akace ya siyo da pnts ya ce pls tk kia of her for me nurse in ta juyo tareda mai murmushi tace i wil wannan karon ma gudu yayi bai tada su umma dan yasan hnkalinsu tashi zaiyi dn ba wani matsala bane toh me ma zai ce musu karo na farko da ya shiga dakinta knan ya nufi wardrobe nata ya dauko mata yar gown ya dan sha wahala kan ya samu kit na undis nata a ciki hrda always ya dauko cikn sauri ya fita ya dawo ya tarar hr an sa mata ruwa nurse in ta dubesa tace who r u to her yace am her husband tace i c,newlyweds? kai ya gyada mata tace ok gt her cleaned up o shuld i hlp ya ce i cn do it tace ok u wl gt ol u nid in d bathroom tayi dsconnctn line tace lt me knw wn u r tru so dt i put it bk ta fita tareda ja musu kofan hr zai fara ya juya ya fita ya kira nurse in yana sosa keya yace i dnt tink i cn do it wt her slipn n i dnt knw hw to use ds ya fada tareda dago always da ke hannunsa murmushi tayi ta kira yar uwarta cikn kankanin lokaci hr sun gama sun gyarata tsab a hnkali ya tura ya shiga hrynxu bacci take ya dubi nurse yace dnt u tink shs tkn tym slipin ta mai murmushi dan taga damuwan dake rubuce a fuskarsa tace shs bn up wyl we r attndn to her dts how we came to knw shs in her period its good she slips d pain wl b gone wn she wakes a hankali ya furta mata tnk u sister............ya ja dan yana son jin sunanta tace Razan tareda murmushi ta ce gudnyt ta fita tareda ja musu kofan kujera ya ja ya zauna yana facing nata hnnu ya sa ya shafi fuskanta hannunta ya riko ya makale da nata ya daura kansa a kan gadon duhune ya gauraye dakin bisa dauke wutar da akayi wayarsa ya ciro ya kunna torch ya hau neman abunda zai fifita da shi da ya rasa ya cire shirt nasa ya fara fifita da shi sis Razan ta bude kofan tareda hasko tocin da ke hannunta karasowa cikin dakin tayi tace d lyts is off for jst few seconds n u r fanning ur wyf,i like dt shs rily lucky to hv u murmushi yayi d lyts wl soon b bk ta fada yayinda take fita ba a jimaba kuwa wutan ya dawo ya maida rigarsa ya koma ya kwanta
Duk shigowan Razan ynda take samunsu ba karamin burgeta yake ba
A hnkali Rahima ta bude idonta ta saukar da su kan kyakkyawar fuskan kamal a zuciyanta tce hs rily hndsum hannu ta kai kaman zata taba curly hair nasa ta pasa a hnkali ta cire hannunta daga nasa amma dukda haka sai da ya tashi mikewa yayi yana sosa keya alaman kunya shi da ke kn mara lafia amma yaketa tirkan bacci a hnkali ta furta ina kwana ya amsa tareda tambayanta ya jiki ta amsa da sauki sai sannan ta lura da kayan da ke jikinta ta dago suka hada ido tayi saurin kawar da knta yace nurses inne suka cnza miki daidai nan Sis Razan ta shigo ya gaisheta ya fice dn amsa kiran da ya shigo wayansa Razan ta mata ya jiki tana dubata tana mata hira tace u r rily lucky to hv such a handsum n caring husband n he rily luvs u its ol ova hs face murmushi kawai Rahima tayi ya shigo tareda sallama suka hada ido taga duk shma ya cnza kaman shine ba lafian taji tausayinsa yayinda lokaci daya taji sonsa na ratsa duk ilahirin jikinta ta san ta so Malik kuma hr ynxu akwai burbudin sonsa can kasar zuciyanta bt she wnt to forgt ol dt n love her husband kaman ynda yake sonta she promise her self from nw on zata mnta da komai ta bude sabon babi na rayuwa itada mijinta wajajen 8 aka sallamosu suka wuce gida inda su adda ke jiransu duk hnkali tashe dan adda ta kirasu da taga side nasu a kulle kuma motan bai gda sai da suka gnta hnkalinsu ya kwanta dakinta ta wuce ta fada toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin dinkin gown na wani hadaddiyar material wayantane ya hau kara ta daga ta ga kawrta na skul ne ta ce ya yau baki zoba ta shaida mata bata ji dadi bane amma insha Allah zata fito zuwa gobe ta mata fatan samun sauki kan suka aje wayan [10/9, 6:09 PM] Billy: 💰💵 *Auren* *Jari*💵💰2⃣1⃣
.
Dr Malik ne ya shigo cikin harabar gidansa yayi parking yana rufe motarsa yaga wata mota ta danno kai ya kuwa gane ko motan wayene Dr Nurane ya fito tareda matarsa ya karasa wajensu tareda musu sannu da zuwa ya ce lalle mutumina kaji dadin hutunka gakuma madam na kula da kai sukayi daria yace mu shiga daga ciki ynda ya sami falon ba karamin kunya yaji ba yace su zauna ya hau tattara kayan da ke falon kwanon da taci abinci ma anan ta barsu ya kwashe yayi kitchn dasu ya ce ina zuwa da ya fito side nata yayi ya sameta ta baje tana kallon film a system ta dago ta kallesa ta cigaba da kallonta yace Fadeela na fa gaji da abunda kikeyi jibi fa ynda kika br falon nan kaca kaca wani irin kiwuya ne haka ko kuma ince kazanta da zak ci abinci ki bari awajen ta turo baki tace ni da wanne znji da laulayin cikinka ko aikin gida daria ya so subuce masa an dai shiga uku da wannan cikin da ko girma bai fara ba yace dama Fadeela wani aiki kike gidannan in bnda kallo murmushn takaici yayi yace ki fito ga Nura da matarsa ya koma wajensu yace sorry na brku fa sukace a'a bakomai sai da ta sha zamanta ta fito tana wni shan kamshi ta gaishesu fuskan nan ba yabo babu fallasa Malik yace kawo musu abun sha mana ta tashi tana wani yatsine fuska ta nufi kitchen can ta fito da faro da cups da ya baci da jirwayen ruwa Malik yaji kaman kasa ya tsage ya shige dan kunya cikin takaici ya dubeta yace drinks in sun karene tace eh kafun ya kuma wani maganan wayanta ya hau kara ta daga ta ce ku shigo ina ciki kawayenta Zeenat da jamsy ne suka shigo ta yo kansu tareda rungumesu a tsattsaye suka gaisheda su Malik ta jasu sukayi daki bata jima ba ta fito tayi kitchen sai gata dauke da tray da faro da drinks na five alive da hollandia akai baki bude malik ke kallonta yace ina kince ya kare zai tashi Dr Nura ya rikosa yace easy man ka brta ta je kawai yace mu ynxu ma zamu tafi duk ynda ya so ya boye bacin ransa ya kasa ace amininsa yazo hr gidansa amma a mishi wannan tarban yace a'a wlhy ku zauna ina zuwa cups in ya dauka yayi kitchen ya daurayesu ya bude fridge yaga hollandia daya ya fito da shi ya kawo ya tsiyaye musu a kopi Dr Nura da matarsa ke ce mishi ya bita a hnkali jinsu kawai yake amma shi yasan abunda ya shirya mata hr wajen motansu ya rakasu ya koma jiran fitan kawayenta ba su suka bar gidan ba sai bayan isha ta fito ta wuceshi ta shige kitchen cikin mamaki tace ina hollandian da k fridge ba dai ka bayarda shi ba yace kwarai kuwa ko kinada abunyi ne tace wlhy sai ka biyani ka san tun yaushe nake tattalin kayana kuwa ka tashi ka ba kwadayayyun can saukar mari tace ni ka mara malik yace an mara maras kunya kawai kawayenki ne dai kwadayayyun nida gidana da kudina kice bazanyi iko da abu ba ynxu ke ko kunya baki ji ba ace baki suzo wajenki for d first tym amma su fahimci halinki nakin ma ba rowa bane rainin hnkali ne cikin nasu nawane da zaki kwashe musu kuma daga yau na daina sa drinks a fridge innan tsaki tayi tace to sai me kaine matsiyaci bakon juice kn ta karasa maganar ya gama wanketa da mari yama mnta da cikin da ke jikinta sai da ya mata lilis sannan ya fice ya bar gidan da ya shigo baiyi mamakin ganin motan gidansu ba yana shiga yaga umman Fadeela da ummansa ya nemi waje ya zauna ba wanda ya amsa gaisuwan da ya musu umman Fadeela tace wai ni jaka aka kawo ma ne Malik da ka zubar da cikin fa wai ma tukun meh tayi da aka manta wannan dukan nan ya kwashi komai ya fada musu umman Fadeela tace ai duk da haka bai ci a ce ka mata dukan nan ba kuma batun aiki ynxu zn turo direba ya taho da jummai in yaso ni na nemi wata hr wajen motansu suka rakosu ummansa tace ka sake tabata ni da kai Malik kuma kr ka sake inyi abbanku yaji kuma kr ku rufe kofanku sai jumman ta zo
Ai kuwa safiyar Allah jummai ta hau aiki dukda dai babbace hakan bai hana Fadeela ordering nata ba bayan ta mata brkfst ta gyara ko ina ta turata ta gyara mata daki Malik ya fito cikin shiri ya dubeta yace ba abunda za bukata ko dn fita znyi tace babu jummai ta fito tace hajia nagama tareda russuna ta gaida Malik ya amsa cikin sakin fuska tace shiga dakinsa ki gyara ya dubeta cikin mamaki sannan ya dubi jummai yace kr ki damu ki barshi kiyi sauran aikinki tace toh je ki wanke mun bayi ya dubeta yace ke wace irice wai ke dakin mijinkima sai dai kisa a gyara toh bn ydda ba tunda dama can ba ke kike gyara mun ba sabida haka ko da wasa kr ki sake ta shige mun daki ya fice yana mamakin hali irin na Fadeela tabe baki tayi ta cigaba da kallon da take yi Tir! da wannan hali da yawancin mata ke yi wai ace mai aiki ake bawa lasisin gyara dakin miji minti nawane zai dauki mace ta gyara dakinta da hr zata bari wata yar aiki ta mata irin wannan sakaci ke jawo matsala da dama wnda ba sai na lissafosu ba ranandai jummai ta aikatu dan duk inda ta sa kai sai taji kaman an shekara ba tsabtace wajen nan ba ita dai tana mamakin kazanta irin na Fadeela
.
Zaune yake a yar karamar office nashi colleague nashi ma'aruf ya leko yace ya kamal zani break r u coming yace eh zani dn two days madam bata jin dadi bana break a gida,restaurant da ke ma'aikatar suka nufa suka nemi waje gefen wasu samari biyu suka zauna tareda yin order daya daga cikin samarin yace wato aboki yarinyan nan ta raina ni wlhy ko kadan bata jin tsorona gashi ko ajikinta take furta rashin sona da take abokin nasa yace ai kai ke raga mata yace bazaka gane ba wlhy sonta bazai brni in mata wani abu ko in wulakantata ba Yace ai ni na gaya ma me zaka yi kada kanshi yayi yace nifa bana so in mata dolene sai ma ta dada tsanata abokin yace ai mace duk kinka da take duk rashin kunyanta kuna hada shinfida ya kare abokin yace toh zn jarraba in gani duk wannan hiran da suke kamal ya nutsu yana ji dan matsalarsu tazo daya sai dai nashi da sauki dan ya daina ganin tsanarsa a idon Rahima ya yanke shawaran jarraba abunda yaji yau karfe biyu na rana yayi parking a harabar gidan ya fito yayi side na ummansu ya gaishesu tareda aje musu ledan fruits da ya shigo da shi ya ce umma yau ina yar taki tace ynxu ta gama matse mun kafa ta shiga ciki yace toh bari nima inje in huta da ya shiga side nasu bata falo ya leka kitchen nan ma bata nan dakinsa ya shige ya watsa ruwa ya sanya yar jallabiya ya fito ya tura kofar dakinta tareda sallama a kan sallaya ya ganta alamar sallah take ya zauna a bakin gadonta ya jira hr ta idar da sallan ta juyo tareda mai sannu da zuwa ya amsa shima ya mata sannu da gida yace kin ci abinci ne ta ce a'a yace mesa cikin jin kunya tace kai nake jira murmushi yayi wnda ya nuna yaji dadin maganarta yace yau ba a cu da su adda bane tace ba cewa kayi inna sake ci da su zaka mata magana ba shine nace gwara ina jiranka ynda tayi maganar ta bashi dariya yace taso muje ki zuba mana toh da daddare fruits da ya zo da shi kawai suka sha ta mai sai da safe ta shige dakinta shi kuwa tunda ya kwanta yaketa juyi a kan gado can ya ja wayarsa ya shiga dailing numbnta bugu daya ta dauka alamar itama batayi baccin ba ya ce bakiyi bacci ba tace eh na danyi karatu ne yace tea nakeso ki kawo mun pls tace ok kitchen ta wuce ta hado mai ta koma daki ta sanya doguwar hijabinta dan kayan dake jikinta da shi da babu duk daya a hankali ta tura kofar tareda sallama ta ji motsinsa a bayi a gefen gadon ta aje ma ta zauna tana jiran fitowarsa ya fito daga shi sai gajeren wando sai yar towel da yake goge kansa alamar wanka yayi gefenta yazo ya zauna ta ji duk ta takure ya dubeta ya nuna mata bayin yace shiga kiyi alwala tace ynxu na idar da shafa'i da witr ya tashi ya sa jallabiyarsa ya dubeta yace taso muyi sallah ya lura duk dardar take da shi a ranshi yace yaukam sai dai tayi hakuri ya jasu sukayi raka'a biyu ya dubeta yace cire hijabin naki ki miko mun tea ba dan ta so ba ta cire ta tashi ta miko mai sai binta yake da ido kadan kawai ya sha ya dubeta yace hau ki kwanta ba musu ta haye gadon ta je can karshen gadon ta tattare shima ya tashi ya kashe wutan dakin sannan ya haye gadon a hnkali ya kai hannunsa ya fara juyo da ita jikinta ne ya hau rawa ta knkame jikinta yayinda hawaye ke bin kuncinta ynda take rawar jiki abun hr tsoro ya bashi ya saketa ya koma can gefe ya kwanta itama ta takure can krshn gadon tana share hawayenta ta rasa dalilin hanashi kanta da tayi ji tayi ya tashi ya bude fridge da ke dakinsa ya ciro wani abu a gora ya kwankwada ya ja pillow yayi palor a hankali ta tashi ta zauna wasu sabbin hawaye ne ke sintiri a fuskarta ta san yanxu tana son kamal amma ita bata shirya bashi kanta ba ita tunanin abun ma tsoro yake bata ta san fushi yayi wata zuciyar tace ta tashi ta bishi ta bashi hakuri yayinda dayar ke cewa ta brshi kawai sai ya huce da haka bacci ya dauketa ba ita ta farka ba sai bakwai na safe ta ganta dakin kamal abunda ya faru jiya ya dawo mata tace wato fushin nashi hr ya kai yaki tadata tayi sallah hijabinta ta sa tayi dakinta tayi alwala tayi sallah ta fito ta wuce kitchen tea ta hada ta hau dinning inda idonta ya kai kan wata paper ta daga taga kamal ne ya br mata sako yake cewa tafia ta kamasa kuma zai kai a week ya bada sako xa kawo mata anjima hawayene taji ya taru a idonta ba dai dan abunda ya faru jiya yayi tafia ba kasa shan tean ma tayi ta dauki jakanta ta wuce makaranta
Kwanan kamal biyu da tafia amma tunda ya tafi ba kira ba message hnkalin Rahima yayi matukar tashi amma taki fadawa kowa,suna zaune itada hauwie da sauran kawayenta intisar da manal sai duba wayarta take hauwie da ke lura da ita tace Rahima ds d tenth time u r chckn ur phone wani abune cikin murya na me shirin kuka tace kamal ne sai kuma ta fara musu kuka da kyar suka samu tayi shiru tace yayi tafia yau kwana biyu knan n he hvnt kol me Intisar tace to y not u kol him ta fada tareda jan wayar tana duba numbers da ke wayan ta juyo ta dubeta tace beb i can only see our numbers n one unsaved no tace dts his no n i dnt tink u wl reach him cos hs out of town manal tace mijin naki ne kiyi saving numbnsa wtout a name haba beb duk swt swt names da suke nan birjik ki rasa sunan da zaki sa mai nan suka hau jero mata sunaye masu dadi ta dubi razan tace hw do u say swthoney in sudan tace Hilwa Asal tace dt wil do bayan sun tashi hauwie ce tayi dropping nata a gida tayi mamakin ganin side nata a bude tace kodai kamal ya dawo ne tana shiga taji an rufe mata ido ta juya taga suby rungumeta tayi cikin mamaki tace suby anya kece kuwa ta dan bugeta tace gashi ki tabbatar ta jata zuwa falo tace yaushe a gari amma kawu ya yadda kika zo tace ke dai sis sai mun zauna kawai tace wlhy fara shafa mun dan bazan jiraba tace guess tace kinga suby bn son jan rai in zaki gayamun ki gayamun tayi fari da ido tace aure mukayi da ya Mahmoud baki bude take kallonta suby tace bakiyi murna bane tabe baki tayi tace a gaisheku ta tashi suby ta riko hannunta tace sakeni suby ba abunda zaku gayamun ke da ya Mahmoud ta kamata ta zaunar da ita tace haba sis wlhy abun ba shiri akayi ko taro ma ba a yi ba kekam da kyar ma kawu ya yadda ta dan saki ranta tace am happy for u sis Allah bada zaman lafia dama nace in tayi sami ai zamuji kuma shima ya Mahmoud in zaizo ya sameni ta harareta tace mijin nawa dariya tayi tace oh masu miji manya tace toh umma fa tace duk tare muka zo ta jira ta gaji shine tace Mahmoud ya maidata gida tace kai umma duk kwanakin da mukayi bamu ga juna ba ta kasa hakura tace ynxu kam ai sai kin gaji da ganinta tace kamal fa tace yauwa sis dama akwai abunda ke damuna kuma bnda wnda zn fadawa sai gashi Allah ya kawoki nan ta kwashi komai ta gaya mata suby tayi ajiyar zuci tace Rahima gskia baki kyauta ba da kin san hidiman da Kamal ke yi da mu da baki mishi duk abunda kika lissafomun ba wlhy kamal na sonki kuma ni bnga abun ki a jikinsa ba ga nutsuwa da hnkali kullum su nani yabonsa suke muna can ma ai yaje in suna hira da umma kya ce uwa da danta tace wlhy suby ynxu son mijina nake so mai tsanani tace ai sai ki gyara nan ta bata wasu shawarwari da kuma tips na zama da miji sai wajajen magrib ya Mahmoud ya zo daukanta ya sha korafi gun Rahima da kyar ya kwaci kansa hr wajen motansu ta rakosa tace ka gaida umma kace gobe zanzo yac jiki fa keda mijinki baya nan tace toh dan Allah ya Mahmoud gobe ka kawo mun ita yace toh in ta yadda zaki ganmu
.
A gaje ta shigo gidan dan yau sun sha lectures a falo ta aje komai nata dakin kamal ta shige dan tunda ya tafi a nan take kwana dan ya kan rage mata kewarsa kan gadonsa ta zauna daidai side da ya kwanta ranan ta aje kanta tana shakan kamshinsa tashi tayi ta fada toilet ta yi wanka ta fito hr zata wuce dakinta ta juyo tana kallon wardrobe nasa a hnkali ta tako ta sa hannu ta yi sa'a bai kulle ba sleeve nashi fari ta dauko ta sa dukda ya mata yawa ta koma kan gadon ta kwanta tareda tattaro kayan zuwa hancinta tana shakar kamshinsa da ta ke mutukar so taji hawaye na bin kuncinta a hnkali ta furta i love u kamal,i miss u pls come bk bacci barawone yayi awon gaba da ita kaman a mafarki taji ana shafa gashinta ta bude idonta a hnkali ta daurasu a kan kyakkyawar fuskar kamal ta sake rufesu ita a zatonta mafarki take gani nayi ta sake waresu ta tashi ta kankameshi tace u r rily here shima kankameta yayi cikin kuka tace am sorry am sorry i luv u my kamal zameta yayi daga jikinsa ya dago fuskarta yana share mata hawayen yace its k amma sake fada mun abunda kika fada last hannu tasa ta rufe fuskanta yace su Rahima sarkin kunya tashi toh ki tayani inyi wanka tace ni nayi nawa yace kinsan tun yaushe nake zaune nake kallonki a nan kuwa zo kawai muje ki wanke zufan dake jikinki tana ji ya cire mata kayansa da ke jikinta ya dauketa kaman yar bebi ta wani cusa fuskanta a kirjinshi daria yayi yace gskia yakamata ayi maganin wannan kunyan taki sai da yayi nashi sannan ya wanketa ya nadota a towel shi ya shiryata sannan ya jata suka kwanta ta ce abinci fa yace it can wait wannan karon bata hanashi ba amma ta gurzu sai da komai ya lafa ya juyo ya ganta ta daina kukan hr bacci ya fara daukanta ya tashi ya shige toilet yayi wanka sannan ya hada mata ruwan zafi azabar da taji ne ya tasar da ita ta kankamesa tana kokarin tashi ya fara shafa gashinta yace sorry my Rahima ki daure ki zauna a ciki kinji in ya dan huce sai kiyi wanka ki fito ya fita ya ja mata kofa ya yaye bedsht in da ke kan gadon ya canza da wani yana zaune bakin gadon ta fito tana takawa da kyar ya taso ya dauketa cak ya dire a kan gado kuka ta fara mai yace shhh! Rahima ba komai zn miki ba ya goge mata jikinta ya dauko slv da ya cire mata ya sa mata ya rungumeta suka kwanta Tare sukayi salgidan
suba suka sake kwanciya da safe ya rigata tashi yayi wanka ya wuce kitchen ya hada musu break ya daura a kan tray yayi dakinsa ya tarar hrta tashi tayi wanka cikin jin kunya ta gaishesa ya aje trayn yazo ya zauna a gefenta yace ya gajia hop ba inda yake miki ciwo tayi kamar bata ji shi ba ya kamo hannunta ya zaunar da ita a kan carpet ya fara feeding nata sai data yi nak tukunna shima yaci sannan ya fara shirin fita office har wajen mota ta rakosa ya jawota ya fara kissing nata wannan karon itama ta mayar mai ya kai bakinsa daidai kunnenta yace tnx 4 ysterday am looking forwd to me za aje mun yau ya dago tareda kinne mata ido harara ta mai irin na masoya yayi kaman zai kamota tayi baya tana daria tareda daga mai hannu zuciyansa fari kal ya bar gidan
~~~~
Yau a gidan ya Mahmoud ta yini sai da kamal ya taso daga aiki ya biya ya dauketa suna shiga suka yada zango a falo abincin da umma ta basu suka zauna suka ci sannan ya miko mata hannu yace zo muje ki tayani watsa ruwa bayan sun fito tayi dakinta dan shiryawa ta tarar baya nan ta shiga zaga side nashi computer room nashi ta shiga ta zauna ta hau dube dube karar shigowan email taji ta duba ta ga ansa message from Alhaji subject contract taga message in ance in d file is d renewal form of our contract go tru it n sign n scan n send me a copy hop ka koma lafia file dake saman computern ta ja taga its sealed hr zata bude taji an janye a hannunta ta juyo ta ga kamal yace dts private ta tsare shi da ido ya tsunkuya tareda tallobo fuskarta yace u luv me dnt u kai ta gyada mai n u trust me nanma kai ta gyada mai yace dn trust me wen i tel u u dnt nid to c dis ya karasa shigowa cikin dakin gaban wani akwati ya tsaya ya sa code na akwatin ya wurga file in ya rufe tace wt abt ds ta fada tareda nuna email in ya karaso ya karanta dukda gabansa ya fadi ya dake ya riko hannunta ya jata zuwa falonsa ya zaunar da ita yace actually i hv bn workin as a secret agent dalilin zuwana sudan knan n i hv sworn neva to dsclose their secret to any1 so pls dnt lt me brk dt prms murmushi tayi tareda shafa fuskanshi tace its k dia i blv u
Yana shiri ta shigo ta rungumesa ta baya tareda manna mai kiss a wuyansa ya juyo yace hr kin shirya ya jawota tareda manna mata kiss yace u look beautiful habibty tace kaima kayi kyau habibi ta dauko turarensa data bala'in so ta fesa mai kamshin na isa hancinta tayi toilet nasa da gudu ta hau kwararo amai yabi bayanta yana mata sannu ya wanke mata bakinta ya ce taso muje in an dubaki sai in dawo da ke gida tace ka kaini skul dai yace it depends yan gwaje gwaje akayi aka shaida masu tanada cikin wata biyu murna a wajen kamal ba a cewa komai da kyar ya yadda ya kaita skul ta isa ma already lcturer na class Hauwie ta ce beb ina kika tsaya haka tace wlhy sai da muka biya asibiti tukunna tace waye kuma ba lafia tace nine wlhy Razan da ke baya itada intisar ta miko kai tace ina hauwie na gaya miki shegen baccinta a ajin nan da biyu nasan ciki gareta Rahima ta juyo cikin mamaki tana kallonta tace sannu Razan ta dubi hauwie wato hr gulmana kuke bari a gama lecture zakuyi bayani
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah har cikin Rahima yana wata 7 yayinda Fadeela ke watan haihuwarta ta tasa malik a gaba tanata shagwaba kawayenta ne jamsy da zeenat suka shigo falon tareda sallama yana amsa gaisuwarsu ya tashi ya shige dakinsa ya kwanta drawern da ke gefensa ya bude ya ciro ledan da Dr Nura ya bashi kwanaki dn tunda ya krba bai waiwayeta ba wayan da ya ba Rahima ya ciro ya kunna inda yayi tozali da kyakkyawar fuskarta ya shige watsapp nata ya fara karanta chat nasu wasu yayi daria wasu yaji kaman yayi hawaye ya gama ya shiga gallery yaga pics da suka dauka ran birthday inta ya jima yana kallo system nashi ya ja yayi transfern dn dama yayi luzin nasu ya zabi wnda sukayi tare ya sa as wallpaper da wayan a kirjinshi bacci ya daukesa ihun da yaji ne ya farkar da shi Fadeela ya gani rikeda wayan Rahima ya san hoton ne tagani ya sata ihun nan hada wayan tayi da bango duk ya tarwatse malik ya dubeta cikin bacin rai yace Fadeela me hakan ta hararesa ta ce tambayana kake wani irin rashin mutuncine da wulakanci zaka zo hr dakina a cikin gidana ka tasa hoton wata banza a gaba kana kallo ya nunata da yatsa kika sake zaginta sai na babballaki wlhy mara kunya kawai itan da kike zagi dai ta fiki tace Allah sauwake wlhy ace wannan kucakar ta fini ya yo kanta sai kuma ya tsaya yace wlhy kin ci sa'ar abunda ke cikinki da yau kin gane kurenki tace ko dai kai ba dan ba tsayawa zanyi ka ringa jibgata ba ya dubeta cikin takaici yace lalle Fadeela kinyi nisa sai dai ace Allah ya shiryeki amma ki sani znyi maganinki soon sai nayi maganin wannan tsiwar taki wayan yaje ya tattara ya shiga hadawa ya kunna yaga screen in yaki kawowa tsaki yayi ya dauki key yayi hanyar fita ta sha gabansa tace wlhy ka ji tsoron Allah in baka sani ba toh ka san cewa abinda kake matsayinsa daya xina dan matar mutum kake kallo ynda yake kallonta ya sa ta gane tayi subul da baka dn ta san da auren Rahima shi da iyayensa ne basu sani ba ya ce meh kike nufi da matar wani ta wayance tace toh zama zatayi tayi ta jiranka bazatayi aure ba ai by now kam tayi aurenta kallon tuhuma ya cigaba da yi mata yace i knw u r hidin sumtn ko ma menene i wl soon fnd out i hv my ways kuma ki rubuta ki aje ko ma tayi auren ko nanda shekara darine ta fito sai na aureta ke ko hakwaranta sun zube ta fito ko wani nakasa ya sameta ba wai ina fata ba toh ni mai aurenta ne ya fice ya brta kuka ta sa ta shige daki ta dau wayanta ta kira Abbanta inda ya kwantar mata da hnkali ya dada tabbatar mata in har yana raye malik nata ne ita kadai,ku ji mun uba
~~~~
Dr Malik na office kiran ummansa ya shigo take shaida mai sun kawo Fadeela a rikice shima ya fita tareda shi akayi komai aka gama gyara yaron aka miko mai dansa mai kama da shi ya rike yaron tareda tofa mai addu'a ya karasa wajen Fadeela yana mata sannu su umma ma suka shigo kowa sai krbn yaron yake iyayen nasu maza ma sunzo duk wanda yaga malik ya san yau yana cikin farin ciki dan akwaishi da son yara abbansa yace ka mai huduba ne yace eh sunan Abba ya ci wato abban Fadeela duk sukayi murna da jin haka tunba alhaji mahir ba ranan suna anyi barin kudi souvenirs har an rasa inda za a zuba su anyi su agogo,jaka,calender,
jotter,tea mugs in na tsaya lissafosu ma bata lokacine kayan takwara kuwa dubai alhaji mahir ya tura matarsa ta hado masa a ciki kuwa hrda kyautan kampaninsa da ya masa abun ba a cewa komi bayan yan suna sun tafi ya rage sai Fadeela da aminanta suna tayata hada kayan suna da ta samu Jamsy tace gaskia junior yayi goshi Zeenat tace abun sai son barka Allahsa na kannensa ya fi haka harara Fadeela ta mata tace ke rabani wannan ma Allahsa albarka daga shi na rufe kofa Jamsy tace ke dai fada kike ynda mijinki ke rawan jiki akan junior kinaga bazai so ya sake samun wani ba tace kufa baxaku gane ba nikadai nasan ynda naji ynzu jibi cikina jibi yanda na canza gaba gabama lalacewa znyi yace zai kara aure Zeenat tace kinyi gaskia kuwa Jamsy tace toh baki ganin in kin hanashi yara zai auro wanda zata bashi su murmushi tayi tace in iyayenmu sun yadda kenan jamsy ta cigaba dacewa ai Fadeela haihuwa bai bata mace akwai abubuwa da dama da mace keyi idan ta haihu dan gyara jikinta ta daga mata hannu tace krma ki bata bakinki dan ba ji znyi ba balle inyi amfani da shi dan ni already an mun booking Dr da zai dubani ya bn tsarin iyali da ya dace da ni sanin halin Fadeela ya sa jamsy ta tsuke bakinta tayi shiru
Zaune take gaban kamal yana matsa mata kafafunta suka kumbura yana mata sannu yace habibty insha Allah kin kusan hutawa ina sunce any moment from now ta gyada mai kai shi ya shiga kitchen dan hada musu lunch ya gama ya fito ya ganta durkushe a kasa tanata murkusu ya karasa wajenta da sauri tareda riketa yace habibty muje asibiti koh da sauri ta gyada mai kai dan ita kadai ta san azabar da take ji ya ciro wayarsa ya kira adda shema'u suka sata a mota sukayi asibiti suna isa akayi labor room da ita kamal ya ciro wayansa ya kira Mahmoud ya gaya musu asibitin da suke bai fi minti goma da kiransu ba sai gasu sunzo can aka bude dakin kamal da ke ta safa da marwa tunda aka shige da ita yayi saurin karasawa wajen nurse in sukayi saurin gane juna yace sister razan ya matata ya fada cikin harshen turanci murmushi tayi tace matarka ta haifo maka bouncing baby girl n both of dem r in gud hlt murmushi yayi tareda daga hannu yana ma Allah godia sai da aka gama gyarata suka shiga dubata har rige rigen daukan jaririyar suke ya ce toh ni bari naje in duba matana tunda ku ta yarinyar kuke ya zauna a bakin gadon da take ya riko hannunta tareda kissin nashi yace sannu habibty nasan kin wahala hw r u filin now tace much better ya tashi ya zauna gefenta ta lankwasar da kanta tareda daurawa akan kafadarsa suna ganin ynda ake ta rawar jiki a kan yarsu ya juyo ya kalleta ya ga itama shi ta ke kallo ya kai bakinsa kan nata ya mata brief kiss sannan ya furta tnk u ta dago tana mai wani irin kallo sannan tace for wat ya maida kallonsa wajen babyn yace for ds ta sake kwantarda knta a kafadarsa tareda kissing nasa a wajen tace me 2 kamal yayi gyaran murya yace adda in an gama a miko mun ita ta nan ya karbota ya mata addu'a tareda mata huduba ya juyo ya mikata ga Rahima ya ciro wayansa ya fara daukansu hoto sannan ya zauna aka daukesu basu jima ba aka sallamosu
Ranar suna yarinya taci sunan umman Rahima amma za ake kiranta da Fatiha su hauwie,intisar da manal ne kirjin biki sai kaiwa da kawowa ake duk da ba sanin mutane tayi garin ba ni billy nayi mamakin yawan mutann da na gani dagowan da zanyi naga su meenah adam,juwairiyan khalil,pherty,maman ili da sauran members in CIWON YA MACE group da kuma yan group in BACK 2 Kitchen sunyi tattaki tun daga maiduguri dan suzo su taya Rahima murnan wannan rana ni dai duk wanda ya pasa plate ba ruwana eehn
~~~~~~~
BAYAN SHEKARA GOMA
Karfe goma ta fito daga Khartoum Teaching Hospital a parking lot ta ji an kira sunanta Dr Rahima ta juyo tana duban meh kiranta naga murmushi ya bayyana a fuskanta ta karaso ta rungumeta tareda bata peck irin gaisuwansu na larabawa tace sister Razan u luk good seems u enjoyed ur nyt off murmushi tayi tace sure bt u my dear u look exhausted ajiyar zuci tayi sannan tace ai jiya bn samu bacci ba n today maimakon su barni suka rikeni sai yanxu zn tafi ta fada cikin harshen turanci Razan tace do rest ma dear n tel Kamal to do d house chores today n ma kissess to ma kids ta ce sunata damuna ma wai zasu bini nace su bari weekend muje tace i wl b xpctn u dn ta tayata bude motan ta rufe tana daga mata hannu hr ta fice
Tunda ta gama ta fito da grade mai kyau akayi retaining nata inda suka sake haduwa da sister Razan shakuwansu ya dadu
Horn daya tayi megadi ya taso ya bude mata tayi parking ta fito megadin ya karaso yana yunkurin krban kayan dake hannunsa tace a'a mal hamza barshi kawai an tashi lafia yace lafia lau sannan ta shige ciki tana shiga falo ta fara cin karo da kayan wasa ta karasa taga falon duk kaca kaca ranta ne ya baci sosai dan in akwai abunda Rahima ta tsana shine gidanta in a mess labcoat nata ta wurga kan kujera ta cire hijabinta ta hau gyara ta maida komai wajensa sannan ta wuce kitchen shima ta gyara ta fito ta hau mopping kamal ne da Fatiha suka shigo falon suka tsorata da ganinta dn sunsan halinta sarai da sun san da wuri zata dawo da sun gyara kafun su kwanta kamal ne ya karasa tareda rungumeta ta baya yana kokarin krban moppern ta jnye knta daga jikinsa tace not now pls yace pls let me habibty u nid to rest tace ai kunsan i nid to rest in kuka bata mun gida so ku barni inji da aikina am gone for just a day n u turn ma house into a mess hutun da nake da niyan yi ma duk kun rushe Fatiha ta karaso tace umma kawo in karasa kallon da ta mata ya sata karasawa tace ke kuma ki cigaba macece ce girma kike wataran zaki gidan miji haka zaki je kina zama mai da datti ni dai Allah ya sani bnda kazanta kuma ban koya miki ba in ka kai wanna hali gidan miji aka zageni toh Allah zai saka mun hawayene ya taru a idonta ko kadan bata son ganin bacin ranta ta wuce daki Kamal ya dubi Rahima sannan ya bi bayan yarsa,dan autanta Fahad da ake kira daddy dan takwaran abban kamal ne ya shigo falon kyakkyawan yarone dan shekara biyu tana ganinsa ta ware mai hannu yana gudu yana yar dariyarsa ya xo ya shige jikinta tareda mnna mata kiss a kumatu ita ma ta mai tace dungui na yace kaifa asbahti ya ummi dan Rahima ta fi musu magana da larabci bikhairin ya dungui,wa anta ta amsa mai shima ya amsa mata ta dagosa tace dungui na ya ci abinci kuwa yace yap tace toh muje muyi wanka bayan sunyi wanka ta shirya shi ta ja shi suka fito a falo taga Kamal da Fatiha na zaune bata bi ta kansu ba dan hrynxu fushi take da su side na umma taje dan ynxu ita dayane dan adda shema'u itama tayi aure ta auri wani lecturernsu inda itama ynxu takeda yaranta uku biyu mata daya namiji ta dan tayata hira sannan tace umma bari inje in huta ta tafi ta brta da Fahad dake ta cikata da surutu ba ita ta tashi ba sai karfe biyu mika tayi tareda yin addu'an tashi daga bacci sannan ta shige toilet ta dauro alwala tazo tayi sallah sannan ta shige kitchen Fatiha ta gani da Kamal suna hada lunch bata bi ta kansu ba ta bude fridge ta Ciro fruits ta yayyanka ta koma falo ta zauna tana cin kayanta Fahad ya shigo yace umma nima tace zo muci dunguin mama Fatiha ta fito ta jera komai a dinning ta karasa wajen ummanta tace umma food is ready tayi kaman bazata amsa ba ta sake furtawa tace umma tace naji cikin sanyin jiki ta koma dinning in sai da suka gama suka dawo palor ta ce dungui na tashi muje muci abinci koh kafun malaminku yazo sai muyi bitar karatu
Har dare bata bi ta kansu ba da haka suka kwanta Da safe tana bacci kaurin konewar abu ne ya tasheta ta tashi ta fito kitchen ta nufa dan taji ta side in kaurin ke zuwa ta shiga taga Fatiha da kamal nata musu akan me za a fara sawa ita tanace kwai comes b4 d milk shi kuma yace milk comes first da alama dai ice cream zasu hada basu ma san da shigowanta ba sai da suka ji ta aje musu cake in a gabansu hannu Fatiha tasa a baki tareda kallon Abbanta Rahima ta kallesu sunyi wani zuru zuru da ido kaman yaran da ke jiran fada wajen uwarsu suka so bata dariya amma ta dake tace wow u two hv bn rily hlpful ds days first mess ma palor n now ma kitchen me zan yi da kune ni Rahima a tare suka furta mata happy Birthday mum Fatiha ta zo ta rungumeta cikin fuskan tausayi tace sorry mum it wunt hppn again i promise kukan Fahad suka ji ta ce oya Fatiha je ki duba mun shi n am not done wt u cos u r cmn bk to tidy ds kitchen ta juya ta sara mata tareda cewa yes ma dariya sukayi duka Kamal ya karaso tareda rungumeta yace Happy birthday habibty tareda kissing nata jin motsin yaransu ya sa ya saketa ta dauko cake in ta ynke inda ya fara konewa sannan ta gama hada ice cream in ranan sun yi yawo sosai hr gidan Razan sunje sai wajajen taran dare suka dawo duk a gajiye basu tsaya wani hira ba suka shige kwanciya
~~~~~
Dr Nura zaune gaban Dr Malik ya ce yau albishir da nazo ma dole in samu babban goro yace ina jinka fadi duk abunda kakeso yace toh Dr na samo maka a sudan gameda matsalar Fadeela in kaje ka dawo ina jiran gorona dnt tnk me now kai kam sai ka dawo bai tsaya ya sauraresa ba ya fice
Alhaji Mahir na zaune a office nashi akayi knockn ya bada umarni a shigo,Malik ne ya shigo hannunsa rikeda junior Alhaji Mahir na ganinsu ya taso ya zo ya rungumi takwaran nasa ya jasu kan 3 seater da ke office nashi suka zauna bayan sun gaisa malik yace na dauko sa daga makaranta shine yace sam sai mun biya ta nan dariya alhaji mahir yayi tareda shafa kan junior Malik yayi gyaran murya yace daba Abba kan matsalar Fadeela an hadani da Dr any moment zamu iya tafia yace toh Alhamdulillah amma ina Dr yake haka kafun Malik ya bashi amsa aka shigo office in Alhaji Mahir ya taso da fara'arsa ya tari bakon da ya shigo Malik ya tashi tareda gaishe da bakon haka ma junior bakon nan yace alhaji ba dai takwaran naka ba yace shi fa ya zama saurayi ko yace gskia masha Allah malik yace toh Abba mu zamu wuce yace toh shikenan ku dai sameni a gida mu karasa maganar bakonsa ya ciro bandir in kudi yar dubu dubu ya mikowa junior yace a sha sweet koh sai da ya dago ya kalli malik ya gyada mai kai sannan ya krba tareda godia washe gari kasancewar yana gida suka shirya duk suka tafi wajen abban Fadeela inda umma ke sanar dasu cewa tafia ya kamashi ba shiri kuma zaiyi kwana biyu kafun ya dawo nan ya bar su Fadeela ya wuce gida dan yin sallama da iyayen nasa sai da yayi la'asar ya bar gidansu ya biya ya dauki Fadeela dan junior acan zai zauna sabida makaranta jirgin dare suka bi zuwa abuja suna isa suka wuce hotel da ya kama musu wanka yayi ya fito yaga Fadeela na sana'a wato kallo ya dubeta yace kema tashi ki watsa ruwan mana sai kiji dadin kwanciya tace sai kace wata kifi ina kafun mu bar gida nayi hayewa kan gadon yayi tareda dauke system in ya kashe ta dan bata rai tace ya malik ya haka yace kwanciya zamuyi kar mu makara ya matso tareda rungumeta yar wasanni ya fara mata bai je ko ina ba ta riko hannunsa tareda kwanciya ta juya mai baya tace ina cewa kayi kwanciya zamu yi komawa yayi shima ya kwanta tunani kala kala a ransa shi ya rasa gane irin son da Fadeela ke mishi ita kullum tana ikrarin sonsa amma ba hakkinsa da ta daukewa musamman na kwanciya ya san tanada matsala amma ba wanda zai hana wasanni ba gashi Allah yayi sa mabukaci da ba yana kai zuciya nesa ba da ya fada wata rayuwar da wannan tunani bacci barawo ya sacesa Da kyar ya tasheta tayi sallan asuba suka hau shiri,suna isa suka tari cab ya kaisu masaukinsu numban abokin Dr Nura ya kira yake shaida mishi isowarsu yace toh a huta gajia gobe in kun xo sai in hadaku da Dr da haka suka aje wayan
Rahima na zaune da Kamal suna kallon wani program kwatsam aka watso tambayan data girgixa Kamal tambayar kuwa itace shin zaka iya cigaba da zama da mijinka bayan ka fahimce cewa ya aureka bisa wata manufa ma'ana auren jari gabansa ba karamar mugun fadiwa yayi ba Rahima ta juyo ta dubesa tace habibi kaji kuwa ya daure yanata fahimtar tashin hnkali da ya shiga ya ce mene ta sake maimaita mai tambayan sannan ta tabe baki tace nikam wlhy ranar da na fahimci hakan za a raba aurena da kai dan baka cancanci a zauna da kai ba jin kalamanta ya dada rikitar da shi yace Rahima toh in hakan da yayi akwai dalili mai karfi fa tace wace daliline zai sa mutum yayi abunda Allah yayi hani dashi zufa ne ya fara keto mai duk da AC da ke falon ya sake dubanta yace toh Rahima in suna da yara fa tace habibi mubar maganan nan kawai dan raina baci yake ta juya taga damuwa kwance a fuskansa ta dago fuskarsa tace habibi wts wrong ya ce bakomai kai na ne ke dan ciwo in na sha magani ma zai yi sauki Rahima tace taso toh muje kasha,ranan bacci yayi kaura a idonsa har wajen biyu idonsa biya ya dubi gefen Rahima inda take baccinta cikin kwanciyan hankali Ya tashi ya dauro alwala ya zo ya tada sallah yana ta kwararo addu'a ji yayi an kunna wutan dakin haske ya gauraye dakin Rahima ta taso tace habibi shine kaketa kwasan ladan kai kadai ko ka taso ni murmushi yayi yace ynxu nake shirin tashinki tunda kin tashi shikenan ai ki taso kiyi alwala ta tashi itama ta tada nata sallan har ta idar yana zaune yanata kwararo addu'a ta shafa addu'anta sannan ta juyo tace habibi wani irin addu'a ka mana haka ta fada tareda kwanciya a cinyansa ya shafi fuskanta yace addu'a nayi kar Allah ya nuna mun ranar da zaki gujeni ta dago ta sa hannayenta guda biyu ta tallabo fuskarsa tace y wl u tink of dt habibi mutuwa ce kawai zata rabani da kai yace i jst wnt u to knw dt u r my lyf n i luv u so much in har bake to ki sani ba kamal duk ranar da kika gujeni kika fita daga rayuwata toh zan iya rasa raina bana fatan hakan ya faru ina rokon Allah ya dau raina kafun wannan rana sai ga hawaye a fuskansa ta kankamesa itama tana hawaye tace pls habibi ka daina fadin haka u knw u r also a part of me dt i cnt liv wtout ka daina tunanin cewa Rahima zata iya fita daga rayuwarka ni takace har abada kuma mutuwa kade zai rabamu ta share mai hawaye ta jasa suka kwanta
Da safe sai da ta biya ta aje yara a skul shima ta kaisa wajen aiki dan motarsa ya samu matsala sannan ta wuce aiki 8 daidai ta isa office nata dan Rahima is very punctual ba kaman sauran likitoci ba da za aje anata jiransu sai kace............
..
tun fitar ta a motan take amsa gaisuwan mutane hr ta karaso office nata ta gaida pts da suke layin jiranta ta Ciro key dan bude kofarta Gud morning Rahima taji an fada ta juyo dan ganin ko wanene colleague nata isma'il ta gani ta ce Mrn Dr Isma'il mai ya faru yau ka fito da wuri yace bn son tsokana dama can ina fita da wuri tace gayawa wanda bai sanka ba yace am dama wani friend ina ne ya turo patient nashi so dey r on dia way in sunzo zanyi guidn nasu zuwa wajenki tace ok ba matsala ta karasa cikin office nata ta dan gyara shi sannan ta fito sanye da labcoat nata ta wuce ward dan gaisar da pts nata bata jima ta fito ta zo ta fara jin matsalolin mutanen da suka zo wajenta tana kan pt na uku Dr Isma'il ya bugo mata waya yace Dr Rahima ga bakin nawa suna zuwa tace ok ta tashi ta fito ta dubi mutanen da ke waje ta ce pls ku danyi hakuri in duba wata pt insha Allah bazan jima sai mu cigaba ba komai dr suka amsa mata cikin turanci shi yasa Jama'a ke sonta sabida saukin kai da sanin hakkin mutane ta koma ciki tana yar rubuce rubucenta turo kofar office in akayi tareda sallama ta amsa ba tareda ta dago ta kalli wanda ya shigo ba har suka zo suka zauna a gabanta bata daina rubutun da take ba tace pls jst gv me sum seconds ta gama rubutun da take sannan ta dago tareda cewa u r wlcm hw cn i hlp.
..
...
maganan ne ya makale bisa mutanen da ta gani zaune gabanta duk sunyi mamakin ganin junansu Fadeela kuwa gaba daya ta rikice mamaki ne da fargaba ya bayyana a fuskanta Sunfi minti biyar ba wanda yayi magana a cikinsu Rahima ce tayi karfin halin yin magana dan dama ita ta dake bata bari mamakinta ya fito sosai ba ta dauke idanunta daga kan Malik ta dubi Fadeela tace me damuwarki wani uban harara tayi mata tareda jan tsaki ta tabe baki sannan tace Allah kasheni ai gwara in mutu da damuwata akan in zauna in bude miki cikina ta dubi Malik da har yanxu bai gama fita daga shock in ganin Rahima ba tace Ya Malik wannan wani irin rashin mutunci da cin fuskane haka ka rasa wanda zaka kawoni wajenta sai tsohuwar kucakar budurwanka kace kawai dama zuwan nan da biyu kayi toh wlhy ba ka isa ba kuma zamana nan garin ya kare maza muje ka maidani gida dama tun farko bn yadda da zuwan nan ba matsalar da a can ma za a iya maganceta ka nace sai anxo nan ta tashi tana dubansa tace sai ka tashi muje ai wani harara ya watso mata yace Fadeela mesa ke a ko ina sai kin nuna rashin hankalinki ne kuma da kike zargina da cin fuskanki ai ke shaidace ban san da wa aka hadamu ba hasali ma ni na dauka namiji zamu gani kuma ke baki isa ki juyani ba in kuma kene mijin zamu gani sabida haka ki dawo ki zauna dan wlhy bazan yi asarar zuwan da mukayi ba kuma in har kika yadda raina ya baci toh wlhy haka zakiyi ta zama da matsalarki tace toh sai meh ai na gwammaci in zauna a hakan akan wannan kucakar ta dubani ta fada tana nuna Rahima wanda ita ta nuna ko a jikinta bata ma san tana yi ba Malik ya ce Fadeela ki iya bakinki wai ke yaushe zakiyi hankaline wai ya juyo gun Rahima yana bata hakuri murmushi kawai ta yi ta duba agogon da ke hannunta ta tashi tareda cire labcoat da ke jikinta ta dauki key ta dubesa ta ce in bazaku damu ba inaso in rufe office ina dan tym na daukan yarana a skul yayi Malik ji yayi kaman an buga mai kusa a ka ynxu Rahimarsa ta yi aure harda yara nace toh dama jiranka zata zauna tayi Fadeela ta tabe baki tace ai sai muje tunda tace fita zatayi ya tashi hrynxu bai bar kallon Rahima ba mamakinta yake ynda ta nuna kaman batayi mamakin ganinsa ba hasalima nunawa tayi kaman bata taba saninsa ba yace toh Dr Rahima zamu iya jirankine ba tareda ta kallesa ba tace na baku tym naku kuma kunyi exhaustn wtout usn it in na dawo kuma wayanda ke waje zan duba so kuyi hakuri ku ga wani Dr ta na gama fadan haka ta wuce ta bude kofar amma bata fita ba alamar su take jira su fita ta rufo kofarta Fadeela ne ta ja uban tsaki sannan ta fita Malik shima ya bi bayanta Rahima ta rufo kofarta ta juya gun masu jiranta tace zani daukan yarona a makaranta in da mai sauri sai in hadaku da wani ya dubaku duk suka amsa da zamu jira ta wuce zuwa inda tayi parking motanta tana budewa taji muryan Malik na kiranta bata tsaya ba ta cigaba da budewa rawan da hannunta yake ya sa keyn ya fadi daga hannunta kafun ta dago ta bude hr ya karaso zuwa wajenta zata bude motan ya sa hannu ya tura yace idanunta ta rufe dan hana hawayen da ke shirin fita saukowa yace Rahima nine fa Malik naki ki juyo ki kalleni Rahimana da na sani bazata taba yi kamar bata sanni ba Rahima nayi matukar farin cikin ganinki yayinda nayi bakin cikin jin cewa kinyi aure Rahima ya za ki manta da alkawarinmu Rahima baki mun adalci ba kin san halin da kika jefani kuwa baki bude ta juyo tana kallonsa yayinda mamakinsa ya cikata wato itace ma mai laifin yar gajeriyar murmushi tayi wanda yake dauke da takaici tace lalle Malik ka bani mamaki bazan tsaya ina tuna baya ba sabida tsayawa da kai ma haramun ne tunda da auren wani a kaina amma ka sani Rahima bata taba karya alkawari ba kuma bata san yaudara ba ka sani ka jima da mutuwa a zuciyan Rahima ka dauka baka taba sanin wata Rahima ba dan itama ta mance da kai yace Rahima karya kike kice kin manta da Malik naki dukda baki rike alkawarinmu ba na san ina nan daram a zuciyarki kuma da kike cewa bakisan yaudara ba Malik ma bai santa ba ganin zai tara mata mutane ya sa ta bude motarta zata shiga ta dan juyo tace Malik bai san yaudara ba ya yaudari zuciyata bata jira mai zai fada ba ta ja motarta cikin zafin nama ta fice Fadeela ce ta karaso inda yake tace wai ina ka shigane ina ta jiranka harara ya watso mata ya bude motan zata bude ta shiga yace kar ki kuskura ki shiga mun mota ki san yanda zakiyi ki koma amma ba dani ba cikin mamaki take kallonsa har ya ja motarsa ya brta tsaye a wajen
0 comments:
Post a Comment