AUREN JARI Part 6-10
.
Da wuri ya kammala aikinsa ya yo gidansu Rahima ta gabatar mai da abinci ya hanata tafia yana ci yana dan janta da hira a haka Mahmoud ya shigo ya samesu dariya ya soma yi yace mama in kina barin wannan yana zuwa nan gaba gaba local govt ne zata rikemu dariya sukayi duka yace amma kai dan iskane umma ta fito tace bar Mahmoud da shirme u r always wlcm ya dubi Mahmoud ya mai yace na gode umma tace yauwa Mahmoud in ka huta sai kuje ku gaida baffanku tun tuni nake muku waka hr nagaji yace zamuje insha Allah ya zauna sukaci abincin tareda Malik Rahima kuwa ta sulale ta gudu daki suna gama ci Mahmoud ya yo kiran Rahima ta fito yace kwashe kayan nan Malik ya hararesa yace amma kai dan rainin hnkaline kwanon ma sai tazo ta kwashe maka gaskia dole in dauke matata if not za a karasarmun da ita murmushi tayi ta tattare kwanukan tayi waje da su tazo shiga dakinta Mahmoud yace shirya muje gidan kawu Malik yace ina gidan yake yace can custom suke yace ai sai muje in ajeku
A bakin kofa suka hadu da kawun nasu yana shirin fita suka russuna suka gaidasa tareda mai ya me jiki ba yabo babu fallasa ya amsa tareda cewa ai mu mun mantama da tayi ciwo shine sai ynxu kuka ga daman zuwa sai ku shiga ai tana ciki Mahmoud ya ce Abba zaka dawo ynxune yace aikana zakayi yace a'a dama wnda ke neman Rahima muka zo tare yake son gaisheka sai sannan Malik ya fito a motan suka shige ciki Suwaiba ya daya ga kawunsu tana ganinsu tayo kan Rahima ta rungumeta tana yar uwa rabin jiki sai yau tace rashin kirkin ne yayi yawa ai shiyasa na daina zuwa ummanta da suke kira da nani ta fito daga kitchen tace sannunku da zuwa nan suka mata ya jiki Suwaiba ta ja Rahima suka shige daki dayake Malik na sauri basu wani jimaba da suka tashi tafia ya ciro bandir na kudi ya aje gaban kawun nasu yace gashi a sai mata lemo nan naga fuskan kawun ya canza yace harda wahala haka toh angode sosai suka musu sallama Rahima ta fito tace yaya kuje ni sai anjima zan tafi suna fita Kawu ya ja kudin ya kai aljihu nani ta dubesa ta tabe baki tace Allah kyauta yace amin dan kawu idonsa idon kudi kuma ynxu haka sai ya cinye bai basu ko naira ba nani tace sai ka kawo na cefane ai sai yau miyanmu tayi zaki yace matsalanku mata kenan ina kin gama girkin a ci haka wannan akwai kuran da zan kashe dasu tace toh ko lemo a siyo mun in dan ji dadi a bakina yace nani gwara ma ki ciri rai a kudin nan dan na gama budget nashi tace mai hali dai bai pasa hali ka dai ji da shi wlhy ya tafi yana banbami ku mata ba a iya muku duj kokarin mutum bakwa kallo su Rahima suka fito Suwaiba tace nani ke dawa tace waye in banda abbanku ta tabe baki tace me kuma yau ya hadaku nan ta kwashe ta gaya musu ta kalli Rahima tace ban mu sha kikayi babbar kamu haka ko ta jata sukayi daki tace tell me everything sis murmushi tayi tace dia is ntn to tell tace look nifa kar kimin kunyan nan naki ta ja pillow tana rufe fuskanta suwaiba tace bude fuskanki jorr Rahima tace abokin ya Mahmoud ne ta ce amma kun dace n u r very lucky sis dan gayen ya hadu ina kina sonsa murmushi Rahima tayi sannan tace wa zaiga first class guy haka kuma Dr yace ba ya so tace wlhy rikeshi da kyau in kin yaba da hnkalinsa cos ynxu samun irinsu da wuya wayan Rahimane yayi kara sai data kalleta tayi dariya ta daga ta mai sallama yace hlo swty dama na kira ince in kin tashi tafia kol me tace nagode amma da ka bari zn iya tafia da kaina yace no i insist ma queen just flash me in kin tashi tafia tace ok tana aje wayan Rahima ta ja tace muga da meh akayi saving no angon namu taga blnk tace sis ya ba suna fa tace na rasa me zan sa mai but bani i just tot of sumtn ta karba tayi saving as habibi da ta tashi tafia kuwa tayi flashn nashi bai jima ba yazo tareda suwayba suka fita suka gaisa tace a kula mun da yar uwata pls yace insha Allah suka mata sallama suka dau hanya yanata janta da hira duk dan ta sake da shi amma ta ki sake jiki hr suka iso gida ya dubeta yace sai nazo da daddare tayi saurin dubansa tace nikam a'a kar kazo yace sabida tace ni tsoron umma nake dazu muna tare anjima kuma ka sake zuwa yace toh gayamun abu mai dadi in bakiso inzo anjima da kyar ta iya cewa ka kulamun da kanka tayi sauri ta shige gida murmushi yayi yace ko ba komai an fara dauko hanya soon zata sake da shi su sha soyayya yana shiga gida ya tadda mutumiyar nasa a falo ta sha wata matsatten top da leggings kallo daya ya mata ya watsar ta taso ta taresa tace wlcm swty ga abinci can na ma hararanta yayi yace gv me way as u can c a gajiye nake tace ok zan shigo ma da shi in ka huta saika ci cikin tsawa yace wai ana dolene abincin ne bani ci dnt u gt it bazan ci muryan umma ta jiyo tana salati Fadeela taje ta fada kanta tana kukan shagwaba tace Malik abunda kake kana kyautawa knan ace baka jin maganan kowa sai abunda zuciyanka ya lissafo ma yace umma nifa a koshe nake tace na lura ds days ba a gidan nan kake cin abinci ba ina lura da kai koma menene ina dab da ganowa kuma zncen Fadeela bari abbanka ya dawo in hadaku dan ni bazan iya ba daki ya shiga yayi wankansa ya ja wayarsa ya kira Rahima hira sukayi sosai kafun suka aje wayar
.
Soyayya sosai Rahima da Malik ke zubawa Mahmoud kuwa tuni ya soma aiki a companyn baban malik Fadeela kuwa ya shawo kanta yana lallabata kafun yasan ynda zaiyi da ita cikin ikon Allah Rahima ta zana jamb rananda result ya fito suna zaune da umma Malik ya kirata a waya yace ta fito tana fita ya bude mata mota tace ina zamu kuma yace ke dai shigo tace toh bari in gayawa umma yace ai munyi waya da ita shigo mu wuce kawai daidai fidelity sukayi parking ya zagayo ya bude mata suka shige ciki cikin sauki ya bude mata account dukda uban layin da ake sai da suka koma gida ya ciro jamb slip nata ya bawa umma tana dan kishingide amma ta tashi tace masha Allah Alhamdulillah Rahima ta zagayo ta leka dan bai ma ce mata ya duba ba tana gani ta kankame ummanta tana murna tace cikani karki karasani yan nan ynxu saura a jira admission koh Malik ya gyara murya yace insha Allahu shima bazai zama matsala ba na riga da na bawa wani abokin abbanmu kuma ya tabbatarmun zata samu barinma score nata is super good umma tace toh Allah tabbatar suka amsa da amin
Ranar da admission ya fito tare suka je dubawa batasan lokacin data yi tsalle ta haye jikinsa ba da ta ga sunanta tayi saurin sakesa lokacinda ta gane abunda tayi cikin jin kunya tace sorry shima sai da ya tattaro kansa yace its k dn ba karamin shock yajiba da ta kankamesa a hnyarsu ta komawa ya ciro ATM ya bata yace gashi ur password is 2018 ta dubesa tace 2018 ya kinne mata ido yace year da zamuyi aure insha Allah na sa miki registration fee da duk abunda zaki bukata a ciki so ba sai kin dami su umma ba gani yayi ta aje mai yace ya dai tace am sorry i cnt tk it ya dubeta wt a serious face yace zamu fara ko Rahima in ba kinaso mu bata ba toh gwara ki karba hr suka iso gida bata dauka ba hasalima ganin ransa a bace ya sa ko sallama bata mai ba ta shige gida kashe motan yayi komai ya gayawa umma oho sai gashi ta shigo da ATM in ta aje mata dama ita tsoronta knan kar umma tace rokonsa tayi wayanta ta ja ta kirasa yaki picking tun tana kira ta gaji ta daina shiru hr kwana biyu ba suyi waya ba na ukun ta taso a islamia ta hadu da makwabcinsu suna takowa tare suna yar hiransu tun kan ta karaso kofar gida ta hango Malik ya hada giran sama da kasa kamar zai fashe ta wucesa zata shiga gida a hankali ya kira sunanta ta tsaya cak amma bata juyoba ya tako hr inda take yace Rahima ni ya dace inyi fushi amma dukda haka na tako kafa nazo kuma kike neman kara shareni ko kallo ma bn ishki ba hasalima ke dadi kikeji dan naga hnkalinki a kwance alaman ma kin mun kishiya ta kulle idanunta tana jin zafin kalamansa ita kadai ta san ynda ta rayu d past two days rashin jin muryansa da ganinsa ba karamin tashin hnkali ta shiga ba gida ta shige tayi sa'a ba kowa a harabar gidan dakinta ta shige ta sami kanta da yin hawaye indai haka soyayyan yake itakam bata so da daddare kuwa sai gashi yazo bata ma san yana nan ba sai da taji umma na kiranta ta fito ta gansa tana zama ya tashi ya fita umma tace kije yana miki magana bataso umma ta san mh ke tafia ba ta sa hijabinta a zauren gidansu taji tayi karo da mutum ji tayi an rungumota ta fara kici kicin kwace kanta taji ya mata rada a kunne yace its me Rahima yace i mssd u swty pls kar ki sake mun irin wannan horon tace mssd u too but ka sakeni pls kr wani ya shigo ya jata har wajen motansa ya bude musu sai gashi sun shirya suna hiransu
Yau Rahima zata fara zuwa school ta tashi ta gama aikinta da wuri tana shiri text na malik ya shigo yace mrn swty naso nine zan kaiki skul on ur first day bt ynxun nan aka kawo theatre case bt i promise wl b dia to pick u up murmushi tayi ta dau jakanta ta ma umma sallama da taimakon mutane ta samu tayi registration nata ta gama komai saura biyan fees cikinta ne taji na kuka ta nemi restaurant ta shiga wasu yan mata ta samu su uku sai maza biyu ta ja kujeran da ke opp dem zata zauna aka bangajeta hr ta fadi a kasa ta gurje hannunta ta juyo mata uku ta gani daya daga ciki tace Fadeela gskia abunda kike ya fara yawa da kin ji mata ciwo fa Fadeela na juya na duba ko wace Fadeela ce wannan ganin Fadeelan Malik ya sani cewa yau ana yinta wannan ma bata san wacece Rahima ba ta mata wannan dabbancin ina kuma ga inta san matsayin Rahima a gun Malik, ta dubeta tace jamsy matsalana da ke knan tausayi ta dubi dayan ta ce pls zauna zeenat Rahima ta tashi ta kade jikinta ta taso ta zo wajensu in akwai abunda Rahima ta tsana shine a wulakantata a cikin mutane ta karaso tareda musu sallama cikinsu jamsy ce ta amsa ta dubi Fadeela tace amma kin san abunda kikayi ba daidai bane ni bnga ma abun fada a wajen zamaba n gashi ku uku ne n stil akwai space da zanyi fitting wnda aka kira da zeenat ta dubeta tace amma ke jjc ce ko bakisan waye F3 bako d fantastic 3 Fadeela zeenat n jamcy JFC toh in baki sansu ba yau kin sansu n kiyi nesa da su if u wnt ur stay in skul to b trouble free in kuma ba haka ba we wl mk ur lyf msrabl itakam Rahima abun mamaki ya bata wannan shine ga duka ga zagi murmushi tayi tace bnga laifinku ba dan kunyi hakan n wat eva u kol urselvs dt wont scare me n ku sani in kun ma wani ya barku wataran zaku sami daidaiku n to u d oldest bully ta nuna Fadeela i say u wise up dan tun a sec skul aka bar yarantan nan tana fadan haka ta juya ta fita juice da ke hannun fadeela ne ya fado baki bude ta bi Rahima da kallo tace amma lallai yarinyan nan zata raina kanta ku tashi ku bimun ita ku ga inda zata i nid evry in4 on her kafun in bar nan zeenat da jamsy suka tashi suka fita jamsy ta dubi zeenat tace nifa bnga laifin yarinyar nan ba tace ai sai ki koma ki gaya mata karkashin wata bishiya suka hango Rahima tana waya ganinsu tayi a kanta bata ma ganesu ba ta ce pls nan ina ne suka gaya mata suka tsaya dan gefe da ita bai jima ba sai ga wata mota tayi parking Malik ne ya fito sai da ya karaso wajenta suka aje wayan zeenat ce ta dubi jamcy tace wannan ba Malik na Fadeela ba jamcy taja wayanta ta duba pic nasa dn basu taba haduwa ba pic nasa suka gani holy crap shine abunda suka fada a tare Zeenat ce ta fara dialing no Fadeela jamsy ta dubeta tace n wat r u doing tace telling her ofcos nan suka fara arguing suna kai Fadeela ta fito har ta karaso wajensu tace n wat r u guys doing gaba daya sukayi tsit jamsy na kokarin hanawa Zeenat ta nuna mata inda su Malik suke daidai lokacin da yake budewa Rahima mota da kyar su jamsy suka iya riketa tsawa ta musu tace we should b following them ba wai rikeni zakuyi ba da kyar suka sata a mota suka bi bayansu
.
Kuka sosai Fadeela ke yi tunda taga Malik ya budewa Rahima mota sun shige jamsy sai aikin bata hakuri suke ta dubi jamsy dake drivers seat tace ciremu daga nan arean cos i feel lyk trowin up suna barin anguwan ta ce tayi parking ta ce su sauko ta zagaya ta karbi tukin ta dubesu tace sai ku san inda dare ya muku sukace toh wa zai kaimu gida Fadeela tace dama ai bai zama dole in kaiku ku besides am not ur driver ta ja ta barsu a wajen zeenat tace amma Fadeela akwai rainin hnkali da irin halin nan nata she dsrv abunda ya mata jamsy zatayi magana ta daga mata hannu tace zip it bn son ji ta tari abun hawa ta tafi ta barta a wajen
.
Fadeela bata wuce ko ina ba sai gidansu dan ta gaji da fadawa umma bata komai da kuka ta shiga gidansu cikin tashi hnkali iyayenta suka tareta da kyar suka shawo kanta ta gaya musu dalilin kukanta cikin bacin rai abbanta ya kira kaninsa wato abban malik shima ransa ya baci sosai cikin bacin rai ya shiga kiran umman malik yace dama abunda yaron nan keyi knan banda masaniya tace meh kuma alhaji yace wacece ya samu hr yake shirin tozartani a wajen dan uwana hr yaki jininsa ynxu ai ga Fadeela can a gida tanata musu kuka sai sannan ta dago kan zaren tace ai Alhaji dama ina ce zn gayama dn nima yafi krfina amma bn san cewa yana neman wata ba yace toh kirawo mun shi ynxun nan yana ganin kol na abbansa jikinsa ya basa ynda ya zo ya samesu ya tabbatar mai akwai matsala waje ya nema daidai kafan abbansa ya zauna tareda gaishesu Abbansa ya dubesa yace Malik ya amsa na'am abba yace ba sai na sake gayama matsayin Fadeela da abbanta a wajena ba ko ya kada kai yace mesa kake son bata tsakaninmu toh akan meh kake son ganin ka tozartani cikin nuna rashin fahimta yace Abba kasan dts d last tin i wil do duk dunia bnda kamarku kuma ina iya kokarin ganin na kaucewa abunda zai bata muku abbansa yace toh wacece Fadeela ta ganku tare a skul shi ya ma mnta Fadeela ma a nan unimaid take karatu inda take final year a accounting yace oh Umma kanwar Mahmoud ne abokina kuma i jst hppn to mt her shine na rage mata hnya Abbansa yace ka tabbata yace gaskian knan Abba yace toh ka gaggauta zuwa can gidan ka musu bayani kuma ka dawomun da Fadeela cikin sanyin murya yace toh Abba da dare yayi ya shirya cikin manyan kaya sai da ya biya wajen Rahima suka taba hira sannan ya garzaya gidansu Fadeela fada sosai abbanta ya mai da kyar ya yadda ya barsa ya dauki Fadeela zasu fita ya kira sunansa ya juyo yace na'am Abba yace ina jin wani abu ya sake faruwa zan suke zncen jiranku da nake in daura muku aure a ranan so tk note suka mai sai da safe suka wuce
.
Kamar kullum Rahima ta tashi ta gama ayyukanta ta ja wayanta ta bude data birthday wishes ne na Facebook yaketa shigowa wayanta ita tama manta today its her birthday message na malik ne ya shigo yace ta shirya yana zuwa ynxu xasu fita toilet ta fada tayi wanka ta shirya cikin wani gown sky blue light mkup tayi ta yafa pink kashka a kai ta fito palo tayi mamakin ganinsa tareda ummanta ya ce umma bari muje tace toh adawo lafia Rahima ta sunkuya tace umma sai mun dawo tace ki kula da kanki kai ta gyada mata tafia sosai sukayi kaman zasu bar gari dan ni billy da ke binsu a baya bn san ko ina zasu ba karkashin wata katuwar bishiya yayi parking gaskia wajen ya ban sha'awa daga inda nake na hango darduma a karkashin bishiyan an zagaye da flowers sai wata katuwar cake an rubuta HBD MY Luv sai drinks da wasu kayan ciye ciye ya zagayo ya bude mata motan tareda rufe mata idanu a haka suka karasa kan darduman ya bude mata idonta tareda furta mata hapi birthday hawayene ya taru a idanunta da kyar ta iya furta mai tnk u ya riko hnnayenta yace my cry baby kar ki ce zakiyi mun kuka ita haka Allah yayita so emotional abu kadan ke sata kuka ya dago fuskanta idonta cikin nashi yace Notin mks me happy than U Rahima I so much luv u n i promise to do so for d rest of ma lyf n ina fata n year to come we wl b celebratn ur birthday togeda til we grow old ya ciro wani box a aljihunsa ya bude ya ciro wani zobe wnda daga gani kudi yaji jiki kan a siyesa ya sa mata a ring finger hawayen da ke makale a idanunta suka gangaro yace dis ring is a symbol of ma undying love for u n kaman alkawarine tsakaninmu rananda naga babu shi a hannunki it mins u r saying no to us n i hope dt wnt hppn yace now share hawayenki we r here to celebrate ur day murmushi tayi ta share hawayenta sunyi creating memories sosai a wannan ranan sunyi hotuna da dama sai da ya mata tkaway ya maidata gida da zata sauka ta juya ta kallesa tace tnx for everything ds was d bst birthday eva yace ni bn gmsu ba a gayamun abunda zai farantamun rai cikin jin kunya ta furta mai i love you ta shige gida wani dadi yaji dn tunda suka fara dating sai yau ta furta mai cikin nishadi ya bar kofan gidansu
.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah yau Rahima ke zana last papernta na partone tana fitowa ta kira Malik dan sunyi shi zai zo daukanta ya fito dan zuwa daukanta ummansa ta tsayar da shi tace Malik dama wajenka zani Fadeela ce taketa trying numbnka wai kaje hostel ka daukota ta gama exams nata yace umma kap drivers na gidan nan sai ni zanje na dauketa gskia inada wajen zuwa ynxu ma jirana ake in baxata iya tuka knta ba a aika driver ya daukota me amfanin motan nata ni meeting zani sai na dawo umma kr nayi letti bai jira mai zata ce ba ya fice ta kira Fadeela ta lallabata akan ta yi driving ta dawo Malik kuwa na shiga ya kira Layin Rahima tace mai ta biyo kawarta hostel ta karbi sako ta gaya mai inda take bai jima ba yazo ta ma kawarta sallama ta fito a jikin motansa ta hangosa suka sakewa juna murmushi kan ta karaso ya bude mata mota ji tayi a fincikota an watsar gaba daya kallonsu ya koma kan wanda yayi hakan Fadeela na gani tana huci ta nunata da yar yatsa tace wlhy kinyi kadan kice zaki shiga gonata wato hrynxu u hvnt learned a lesson abunda na miki rannan is ntn compared to wat am gonna do to you next hrynxu baki san wacece Fadeela ba Malik ne ya dagota yace gyara jikinki ki jirani a mota Fadeela ta hararesa tace in tashiga motan nan nikuwa yace wts wrong with you Fadeela cnt u c u r creatn a scene kije gida zamuyi magna in na dawo tsaki tayi ta shiga jan Rahima dake aikin kuka ganin haukan nata sai gaba yake tana tara musu mutane ya sa shi marinta cikin mamaki ta juyo tace Malik ni ka mara akan wannan shegiyar wani marin ya sake mata yace kr ki sake sheganta mun matar da zan aura da iyayenta bari kiji n in kikayi wasa kin san sauran dariya tayi tace ok let's C ta juya ta ja motanta ta bar wajen da kyar ya rarrashi Rahima suka bar wajen har suka isa gida ba wnda yayi magana zata sauka ya riko hannunta yace Rahima pls kiyi hakuri n pls kar kiyi umma ta ga damuwan nan a fuskarki murmushi tayi tace who is she yace Rahima jst do as i said zanzo anjima n wl xplain evrytn to u bt i hv to go now ynda suka rabu ya tabbata ranta a bace yake bt bai shirya gaya mata komai ynxu ba hr sai ya kashe wutan da Fadeela zataje ta hura dan yasan by now d damage must hv bn done
.
Gabansa ne yayi mugun fadiwa da ya shiga gida da kyar kafansa ya kaisa palor inda duk an hallaru ana jiransa bai san marinda ya ma Fadeela ya shigeta haka ba har yatsunsa sun fito a fuskanta fuskan iyayensa a turnuke ya nemi waje tareda gaishesu ba wanda ya amsa a cikinsu saima marinda abansa ya kai mai abban Fadeela ya riko hannunsa yace matsalana da kai saurin hukunci ai sai ka bari aji ta bakinsa yace yaya yaci bulus knan ai gwara da na rama mata Abban Fadeela yace Malik me ya hadaku da kanwar taka bai boye musu komai ba shiru duka sukayi sai kukan Fadeela ke tashi tace dama ai nasan sonta yake Abbanta yace kr in sake jin bakinki a nan ya dubi Malik yace ina baka manta alkawarinmu ba rannan yace eh Abba amma ina neman alfarma ynda nayi biyayya gareku na amshi zabinku nima ku dubeni ku amshi zabina ina tausayin baiwar Allahnan ina tausayin halinda zata iya shiga ku yarje mun in aureta kar ku bari nazama mayaudari a idanunta umman Fadeela tace kasan da auren yar uwarka sannan kaje kake neman wata yace umma ni namiji ne kuma Allah ya yarjemun in aje hudu ummansa ta kai mai bugu tace tunda muka taso wannan family mace daya ake aure baka isa ka canza mana tsari ba Abban Fadeela yace ba komai malik ba damuwa zaka iya aurensu duka biyun ammafa ka sani a yau za daura muku aure kai da Fadeela in yaso daga baya ka auro wancan dukda bai so haka ba yace nagode Abba yace ku tashi kuje suna fita suka zubo mai ido yace i knw wat am doing n i hv a plan ku dai ku zuba mun ido ku gani.
0 comments:
Post a Comment