BAKAR MACE Part 11-15 (THE END)
.
Farouq koh kalli Salimat bata ishe shiba! Domin sam ya tsani ya kalle ta, hakan yasa duk lokacin da ya shigo side din Umma ya ganta. Saiya bar wajen! Umma dai bata damu da yadda Farouq yake wa Salimat ba domin bata son bacin ran autan nata. Ita kanta Umma yadda taga Salimat na wannan iyayin hakan yasa Umma bata takura ma Farouq. Farouq bashi da babban aboki irin Ishaq. Domin kuwa childhood friend dinsa ne, hakan yasa suke kamar yan uwa. Duk wani hali da Farouq yake ciki, Ishaq ya sani haka kuma Ishaq duk halim da yake ciki Farouq ya sani. Ishaq yayi aure harda yarinya daya. Ishaq yaso ace sunyi aure tare amma tun alokacin da Farouq ya hadu da Farida when she was in 200lvl. Tun daga wannan lokacin Farouq ya leqe mata. Ita kuma alokacin bata da raayin sa koh kadan. Shi kuma Ishaq abnda yasa yake qin Farida shine yadda yaga tana wulaqnta Farouq. Ishaq adunia ya tsani yaga wani yana debasing friend dinsa. Hakan yasa ya dauki kin Farida ya daura shi cikin ransa.
.
Tun tashin Farouq ya kasan ce abn so da qauna awajen al'uma! Arayuwar sa baya wulaqanta kowa, gashi abn hannun sa baya rufe masa ido. Farouq yana girmama yayan Usman! Domim yana yi masa kallo kmar Abban shine, kasan cewar Usman yanxu yakai shekaru 44. Kamar yadda yake girmama yayan nasa haka yake girmama matar sa. Sai dai abu guda daya tsana game da matar yayan nasa shine yadda take turo masa Salimat. Wannan abu yana cima Farouq tuwo aqwarya. Gashi baya son shiga harkar Salimat hakan yasa koh gaishe sa tayi baya amsawa. Domin ya lura kanta yana yi mata rawa. Salimat ta kasan ce kamar kaska ga Farouq! Don akwanakin baya har office ta riqa binsa. Saida yayi mata dukan gaske cikin office sannan yayi mata korar kare. Wannan dalili yasa Salimat jin tsoron Farouq sosai da kuma ja baya gare shi. Ta rasa gane dalilin da yasa Farouq baya sonta. Abu ma farko dai ita tasan tana da kyau domin koh cikin mata masu kyau toh ta kai. Gata kuma yar gayu, amma Farouq koh kadan baya ganin wannam baiwar da Allah yayi mata.
BAQAR MACE! CIGABAN LABARI!
Kamar yadda Farida tayi alqawarin cewar xata fadi masa cewar tana sonsa. Haka kuwa akayi, domin bayan ya kira a waya ne take qara bashi hakuri akan abnda tayi masa baya. Sannan tayi declaring cewar tana son sa. Murna wajen Farouq baa magana. Wasa wasa soyayyah tsakanin Farida da Farouq ta ginu. Soyayyah suke tsakani da Allah, babu wani aibu acikin kalar son da Farouq yake mata. Farida wani lokaci har mamaki take akan yadda Farouq yake nuna kulawar sa akan ta. Wani lokaci gani take kamar mafarki taki. Wani lokaci kuma gani take anya bata cuci Farouq ba? Domim shi mai kyau ita Mummuna. Farouq da Ishaq sun shrya domin yanxu Ishaq in banda yabon Farida babu abnda yake yi. Hakan yasa suke shiri sosai da Farouq yanxu. Kuma shi kanshi Ishaq ya gano halin Farida da yadda take da mutunci. Hakan yasa ya gane ashe abaya yadda ya dauke ta ba haka take ba. Ahalin yanxu Ishaq yana girmama Farida badan komai ba kuwa sai yadda ya lura da halayyar ta da dabi'un ta suke. Maganar aure ta taso gadan gadan domin an saka ranar biki wata biyu kacal. Murna wajen Fati da Hindu baa magana. Haka wajen Farouq da family dinsa Excluding Hafsat and Salimat.
.
Ahalin yanxu an saka ranar bikin su. Wata uku kawai aka saka... Farouq ne xaune yana tunanin inda xau samo ma Farida Maganin aljanu. Domin yanxu aljanun ta sun cika tashi. Shirin biki akeyi, sosai domin yanxu baifi saura 3 weeks ba. Anyi siyama Farida kaya na gani na fada. Amma still har yanxu aljanun ta suna tashi. Farouq aduk lokacin da aljanun Farida suka tashi yana shiga damuwa sosai. Hakan yasa yake qara sonta sosai domin wannan lalurar tata. Akwana a tashi yau baifi saura kwana 8 bikin ba hakan yasa hidima koh ta ina ta kacame. Dangi ta koh ina sun iso, Farida sai shiri suke ita da su Fatima. Haka Farouq shima duk wanda ya gansa yasan yana cikin farin ciki. Salimat tafi kowa baqin cikin wannan bikin. Hakan yasa ta tattara ta koma Kano. Domin ita a ganin abn kunya ne ace wanda take so xai auri wannan BAQAR MACEN. what a big slap on her face? That's what she thnk.
BAQAR MACE!
Yau Friday aka daura aure Farouq Sulaiman da Farida Ahmad. Bayan sallan juma'a, an daura auren ne abisa sadaki naira dubu ashirin. Babu wani party da akayi, da dare aka dauki amarya aka kaita gidan ta dake, Malali. Gida ne na gani na fada, matar Usman ji take kamar ta kashe Farida dan baqin ciki. The next day akayi walima, kowa ya gama gaban sa tare da neman musu xaman lafia.
.
BAYAN WATA UKU.
Soyayyah suke tsakani da Allah, Farida tana bin duk wata doka da umarnin Farouq. Farouq yana qaunar matar sa koh kadan baya son abnda xai bata mata rai. Aljanun Farida suna tashi akai akai, Farouq yana bala'in tausaya mata. Ishaq yaxo masa da labarin Arriyad Islamic Chemist! Ba tare da bata lokaci ba suka je harda Farida. Cikin ikon Allah aka basu magani, duk rana kafin Farouq ya tafi Office sai ya bata tasha sannan ya tafi. Haka kuma da yamma. Cikin ikon Allah yanxu Farida sai tayi... wata 6 ba tare da aljanun sun tashi ba.
.
Farida ce xaune bisa qafar Farouq. Farouq sai jan ta yake yana fadin mai ciki... Farida sai turo baki take tana fadin wallahi bani son sunan nan. Farouq ya fashe da daria, yace Allah dai ya rabaku lafia. Farida tace ameen! Farouq yace inace yanxu cikin 6 months yake koh? Farida tayi saurin cewa wallahi, 9 months ne ka daina maida ni baya. Farouq ya fashe da daria, yace wai miya baki son na maida ke baya ne? Suna cikin maganar suka ji sallama. Ahankali Farida ke shirin tashi dan bata son atarar da su ahaka. Farouq ne ya temaka mata! Tun kafin su shigo Farida ke fadin Oyoyo ga sisters. Bayan sun shigo sun gaisa da Farouq, sun taba yar fira, kafin daga baya Farouq ya bar gidan.
.
BAQAR MACE!
Hindu ce ke fadin wallahi sis cikin nan ya miki kyau. Nidai Allah yasa idan nayi aure nawa yayi mani kyau! Buge mata baki Farida tayi tare da fadin marar kunyar banxa kawai. Hindu turo baki tayi, tare da fadin ay gaskia ce. Fati babu abnda take yi sai daria. Basu bar gidan Farida ba saida sukayi Magrib prayer sannan. Farida ji tayi kamar kada su tafi. Yau Farida ta tashi da nakuda. Sun isa asibiti, an shiga da ita labour room. Farouq sai safa da marwa yake yi. Kafin kace haka dangi sun cika asibiti. Farida ta sauka lafia inda ta haifi 'Yar ta mace mai kama da Farouq. Murna wajen Farouq baa magana. Haka both families din! Bayan an sallame su, gida aka wuce da Farida! Farouq yaso ace gidan sa xatayi wanka amma Umma ta hana.of Hausa Novels BAQAR MACE! 29 Ranar suna yarinya taci suna Aisha! Farida ta samu abn dunia dai dai misali. Taron suna ya tashi lafia kiwa yana fadin Allah ya raya. Ya kuma maido su wata shekarar suna. Bayan wata 3 suka koma gida. Murna wajen Farouq kamar me, more especially da yaga babyn sa sai qara kyau take gata bulbul. Farouq yana taking good care of them. Hakan yasa Farida ta qara kwantar da kanta wajen mijin ta. Aljanun Farida suna tashi amma ba sosai ba. Bikin Fati da Hindu ya matso domin yanxu baifi saura 14 days ba. Hakan yasa suke ta shiri basu cika xama sosai ba.
BAQAR MACE!
Anyi biki an gama lafia amare gaba dayan su Kano aka kaisu. Farida sunsha kukan rabuwa da yan uwan nata ranat walima. Sun dawo gida ita da Farouq kamar wasu marar da lafia. Farouq ne da yaga abn nata yayi yawa yace Allah idan bata saki ranta ba xai ce bata qara xuwa Kano. Hakan yasa Farida ta saki jiki ta koma kamar da. Amma tunanin sisters dinta cike da ranta. Xaune take tana tunanin wannan kasalar da take fama da ita yan kwanakin nan. Basu bata lokaci ba suka isa asibiti. Gwajin farko likita ya sheda musu Farida tana dauke da ciki wata 4. Farida abn ya bala'in bata mamaki domin alokacin Mama shekarar ta daya da wata uku. Farida bata tada hankali ba domin taga yadda Farouq yake ta murna. Hakan yasa ita ta taya shi murnan tasa.
.
BAYAN 6 MONTHS.
.
Farida ta sauka lafia, ta haifi danta namiji shima mai kama da Farouq but some how yana kama da ita. Yaro yaci sunan Abban Farouq wato Sulaiman, suna kiran sa da Junior. Haka rayuwar tacigaba cikin jin dadi da qaunar juna. Farouq dai qara samun daukaka yake ta koh ina.
.
ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo qarshen wannan littafi mai suna BAQAR MACE. Nayi wannan littafin badan komai sai dan na jayo hankalin marubutan littafin Hausa. Akan musan cewa bawai macr mai kyau fara kadai bace in the world. And ba ita daya bace maxa suke so. And also ba Farar Mace mai kyau kadai take da aji ba.
.
Suma BAQAQE MA MATA NE. Kuma masu Aji. Masu aji, domin gaba dayan mu babu wanda yafi awajen Allah sai wanda yafi tsoron Allah. Na fiddo Star din wannan novel BAQA kuma MUMMUNA. Kuma mai ALJANU. Kuma ahaka classic guy ya aure ta. Kuma ya gwada mata SO DA QAUNA. No body is better than any one to Allah except the one who fear him the most. So ina son musan cewa kyau ba wani abu bane, domin da wani kyan gara muni.
.
Naku akoda yaushe Abdullahi yahaya Sa'a zaria
CALL or SMS
07066508080
.
Whatsapp
07066656752
0 comments:
Post a Comment