BAKAR MACE PART 6-10
.
Farida ce xaune sai baqin rai take, tunda Umma taga haka tasan cewar Aljanun ta ne suke da niyyar tashi! Gashi gida babu kowa hakan yasa Umma ta dauki wayar ta, ta kira Malam Ahmad qanin Abban Farida. Domin dama shine yake mata Ruqiyya! Kamar jira suke Umma ta gama wayar kuwa Aljanun Farida suka taso. Umma ce taje ta debo ruwa cikin cup tayi mata addu'a sannan ta watsa mata ruwan. Aljanun Farida sai ihu suke, suna kiran ki daina watsa mana wannan ruwan. Umma suna cikin wannan hali sai ga Baba Sani ya shigo da sallamar sa. Nan ya shiga yi mata Ruqiyya, koh da aljanin ya fita nan take Bacci ya dauke Farida. Dama haka suke mata duk lokacin da aljani ya fita toh saita yi bacci. Idan kuwa batayi bacci ba, toh xata tashi jikin ta sam babu kwari. Wani lokaci sai ta riqa tambayar yaushe Baba Sani ya xo or some thing like that. Baba Sani ne yace Allah dae ya kawo ma yarinyar nan sauki. Umma tace ameen, amma yanxu naga abn da sauki tunda yanxu tana kai kamar wata uku basu tashi. Unlike da tunda a da cikin sati sai su tashi sau 3! Baba Sani yace gaskia kam abun sai godia. Ahankali cikin ikon Allah sai kiga sun rabu da ita har abada. BAQAR MACE! Umma tace Allah ya nuna mana ranar da xasu rabu da ita gaba daya. Domin wallahi yarinyar nan tana bani tausayi! Tun bare idan ta tashi tana tambayar abnda ya faru bayan sun sauka! Ni roqona daya Allah yasa har ta ida karatu ba xasu tashi ba! Baba Sani yace ameen! Alhajin baya nan ne? Umma tace eh bai dawo ba, amma nasan kamar yanxu yana bisa hanya. Bata gama rufe baki ba kuwa saiga Abba ya shigo da sallama. Baba Sani yace kin kuwa gani gashi nan! Nan Abba ya xauna suka gaisa, yayin da Umma taje dauko masa ruwa. Bayan ta dawo yake tambaya halan Aljanun Farida ne! Umma tace ay kuwa dai sune! Abba yace toh Allah ya sauke ma dan uwa musulmi. Gaba daya suka amsa da ameen! Bayan Baba Sani sunci abnci ne ya tafi gida. Nan Umma da Abba suka cigaba da tattauna matsalar. Suna cikin maganar saiga Fatima da Hindatu sun dawo. Bayan sun gaida mahaifan nasu ne suke tambayar Yayar tasu. Umma tace tana daki, su shiga daga ciki. Basu qara magana ba kuwa sukayi hanyar daki, kowa da abnda yake saqawa cikim xuciar sa.
.
WACECE FARIDA???
Cikakken sunan ta shine Farida Ahmad Mahaifin ta Ba Kano ne amma suna xaune a Kaduna! Mahaifinta yana da kudi but not that much dai dai misali. Sunan mahaifiyar ta Hajia Asma'u! Mahaifiyar ta itama yar Kano ce aure ya kawo ta Kaduna! Mahaifan ta mutanen kirki ne! Gasu da taimakon na baya gare su! Suna xaune a Rigasa cikin garin Kaduna! Su Uku ne wajen Mahaifan su! Farida itace First born, Fatima sai Hindatu itace Yar auta. Farida BAQA CE and frankly speaking bata da wani kyau. idanun ta ba wasu manya bane, haka xalika lips dinta dai dai, bata da gashi kai. Domin wani namijin ma yafi ta gashi! Amma kuma yar gayu ce taqin qarawa! Farida ta kamu da cutar Jinni tun tana yarinya! Amma yanxu abn nata da sauki tunda ba ko yaushe suke tashi ba. Ahalin yanxu Farida tana 400lvl! Shekartun ta 23 tana karantar Biochemistry! Yayin da Fatima take 300lvl sai Hindatu 200lvl! Gaba dayan su suna karatu a Kaduna States University! Suna maida hankali sosai! Abunda ke daure kan wasu yan mata game da Farida shine yadda maxa sune sonta. Domin duk inda ta shiga saita samu sarauyi.
BAQAR MACE!
Gani suke kamar Farida bata da wani matsayin da Xaisa wani yace yana sonta. Kuma abnda ke qara basu haushi duk wanda xaice yana sonta daga mai Kudi sai handsome guys! Farida duk min yadda Allah yayi mata muni that doesn't mean ta saki kanta any how. Allah yayi mata wani irn kamun kai! Hakan yasa wasu suke gulmar ta wai duk munin ta amma ta cika girman kai as if ta hadu. Ita dai Farida duk maganar da mutane ke yi akan ta. Bata damuwa, ita daria ma wata maganar take bata idan sunyi. Farida Allah yayi ta mai haxaka, yes tasan cewa ita ba wata mai kyai baice. Amma hakan baisa ta watsar da mutuncin ta na 'Ya mace ba! Bata shiga harkar daba nata ba! Duk wanda ya nuna yana yi da ita. Toh itama tana yi dashi. BAQAR MACE! Babban abnda yafi damun mutane shine yadda suka ga Farouq yana nan nan da Farida. Ita kuma tana wani jan qasa! Domin da fari Farida bata son Farouq koh kadan! Shi kuma har skul yake binta, akwai ranar da Farouq yayi ta bin Farida duk inda ta saka qafa. Ay kuwa saida suka je har cafeteria taxo xama shi irin yadda indiawa ke yi ya jawo mata kujera ta xauna. Ay kuwa mistakenly ya shafar mata hannu ay kuwa ta wanka masa wani wawan mari. Mutane duk suka jiyo suna kallon su maxa da mata! Gashi wurin cike! Harga Allah Farouq baiji haushin abnda tayi masa ba. Domin son da yake mata yayi over! Shi ji yayi ma ta qara kwanta masa cikin rai! Duqawa yayi har qasa yana bata hakuri. Farida ji tayi kunya duk ta kamata ace babba kamar Farouq ya duqa yana bata hakuri. Cike da kunya Farida tabar wajen! Nan fa mutane kowa ya shiga fadar albarkacin bakin sa! Wasu matan na fadin wannan Mummunar Faridar ta cika iyayi. Wata Aisha tace nifa i don't know why maxa suke son ta after all gamu masu kyau farare amma wai.... Zainab ce ta amshe ta da cewar nima kaina abn nan yana bani mamaki! Ki duba kiga yadda Allah yayi mana halitta babu inda Allah ya rage mu amma waccen banxar BAQAR i just hate her! Ahaka suka cigaba da maganar Farida kowa yana fadin albarkacin bakin sa!a
.
Farida bata da wata intimate friend ita kowa nata ne! Amma sai idan ka nuna kana yi da ita! Bata da wasu abokan shawara sai sisters dinta. Duk gidan su Farida ita kadai ce Mummana amma sisters dinta duk masu kyau ne. Domin su sun biyo iyayen su kasan cewar mahaifan ta fulani ne! Farida bata damu da munin ta ba domin tasan haka Allah yake son ganin ta. Duk gidan su Farida babu wanda bai san Farouq ba! Domin har mahaifin su yasan da Farouq kasan cewar yana xuwa ya gaishe shi. Kuma Abban nasu yana son Farouq domin ya yaba da hankalin sa! Farida tana da farin jini koh cikin family dinsu domin kuwa tana kirki sosai da sosai. Abun hannun ta koh kadan baya rufe mata ido. Kowa yabon ta yake! Awajen karatun addini Farida ba daga baya domin tayi sauka sau 2 yanxu ma hadda take. Babban abnda yake jan hankalin jama'a koh ince samari wanda suka san ciwon kansu. Shine Farida koh kadan bata yin shigar banxa. Koh da yaushe tana cikim hijabi duk inda xasu je!
BAQAR MACE!
Duk inda mace matashiya mai hankali takai toh Farida takai wajen. Sam babu wanda xai budi baki tace yau ga abnda Farinda tayi mishi. Knowingly sai dai me Dan Adam ajixi ne tara yake bai cika goma ba! Sisters dinta Fatima da Hindatu suna bata girman ta sosai! Domin ta kame kanta, and when it comes to advice she seeks it from her sister or mother but not from a friend! Abu daya ne sisters dinta suke ganin bata kyautawa akan sa kuma suna fadi mata. Shine yadda take debasing din Farouq kuma hakan yana bata musu rai kuma suna fadi mata gaskia. Akan ta daina masa abnda take yi it's not good. Wani lokaci Farida taji haushi wani lokaci kuma ta share su. Ita kanta wani lokacin tana tunanin abnda take ma Farouq bata kyautawa. Amma wata xuciar sai tace mata maxan yanxu sai ana musu haka. Abu daya yake saka Farida tsayawa da Farouq shine yadda taga Umma tana son sa. Not only Umma but her family!
BAQAR MACE!
CIGABAN LABARI! Koh da suka shiga daki suka ga Farida tana bacci! Fatima ce Allah dai ya bama Babbar Yaya lafia. Hindatu tace ameen! Amma wallahi Aljanun nan suna wahalar da ita. Allah yaso yanxu ma da sauki akan da! Fatima tace addu'a xamu cigaba da yi mata! Hindati ce ta shafa mata goshi domin yadda AC ke aiki hakan bai hana mata xufa ba. Sun juya xasu fita daga dakin, Farida ta tsaida su. Tashi taxo yi amma jikin ta babu qarfi. Hindatu ce tayi saurin qarasawa ta tayar da ita. Farida tace yaisge kuka dawo? Fatima tace yanxu muka shigo gidan. Farida tace toh yanxu ina xaku je??? Hindatu tace abnci xamu ci. Kinci abnci kuwa? Farida daga musu kai tayi domin wahalar maganar take ji. Da taimakon su taje tayi wanka, kafin ta fito Fatima ta fiddo mata kayan da xata saka. Sannan suka tafi dining domin yunwa suke ji. Bayan sun gama ne suka ji maganar Farouq a parlour! Clapping hands sukayi tare da fadin sis muje muyi labari da Yaya Farouq. Suna tashi Dayyaba mai aiki taxo ta kwashe komai wanda suka gama dashi ta wuce domin yin wanke wanke.
.
Da Sallama suka qarasa parlour suka gaishe da Farouq. Cike da far'a ya amsa, nan suka shiga labari shida su Fatima. Umma na xaune tana sauraron su sai daria take musu. Suna cikim haka Farida ta fito sanye da hijabin ta har qasa. Har qasa ta duqa ta gaishe da Farouq! Sannan ta samu waje ta xauna. Da dai daya da dai daya su Fati suka bar parlour. Parlour ya koma daga Farouq sai Farida. Nan suka shiga labari Farouq yana yi yana sako kalaman soyayyah. Farida kuwa yana yi tana rufe fuskan ta. Domim kunyar Farouq take ji sosai! Ahaka suka sha labari kafin daga bisani suyi sallama. Farouq yace baxai ta fiba har saita fada masa cewar tana son shi. Farida rufe fuska tayi sannan tace nifa baxan iya ba gaskia. Maimaita maganar da tayi yayi. Farida cike da Shagwaba tace Allah ka daina. Farouq yace i won't until you tell me that you love me. Farida yace i'll but not now. Farouq yace ni kuma yanxu nake so. Farida tace i said i'll but not now, i'll tell you but through the phone. Farouq yace ok promise? Farida tace yh promise. Ahaka sukayi bankwana Farouq ya tafi gida cike da farin ciki marar misaltuwa.
BAQAR MACE!
WANENE FAROUQ?? Farouq shine na biyu awajen mahaifan su kuma shine last born. Cikakken sunan sa shine Farouq Sulaiman, sunan mahaifitar sa Hajia Amina. Mahaifin sa da mahaifiyar sa sunyi auren soyayyah. Mahaifin sa Attijiri ne suna xaune. Suna xaune a anguwar Rimi gidan su gida je qato kuma mai kyaun gaske. Mahaifin sa Senator ne mahaifiyar sa kuma Lecturer ce. Amma ahalin yanxu ta ajiye aiki. Babban yayan sa shine Usman yana da aure harda yaya 2 duka mata. Farouq yana da shekaru 38 yana aiki a NNPC kuma yana business. Farouq ya kasan ce mutum kirki ga mutane baki daya. Farouq dogo je fari yana broad chest, yana da dogon hanci, cutely lips which are pink.... yana da manyan idanu. Sumar kansa kwance take, haka sajen fuskar sa! Farouq ya hadu iya haduwa, hakan yasa yan mata ke son sa sosai. Duk cikin matan Farouq babu wacce ta liqe masa kamar Salimat qanwa ce ga matar Usman. Sunan matar Usman Hafsah, Hafsah tana son Salimat ta auri Farouq domin tasan qanwar tata xata huta. Shiyasa Salimat kusan kullun tana nan wajen Umman Farouq.
0 comments:
Post a Comment