Dayake Anwar yana d'akin Fateema ne baima sani ba, a daddafe ta samu tayi Sallah saboda wani jirin da yake kwasar ta, akan Sallayar bacci ya kwashe ta, sau biyu Fateema tana lek'owa taga tana bacci sai ta koma, don haka tayi aikin ta ita kada'i.
sai kusan k'arfe 10 Anwar yafito, cikin shirin shi da alama futa yakeson yi, d'akin Maryam ya nufa yana tunanin wani irin bacci takeyi har yanzu.
har lokacin bata tashiba, kwanciyar kad'ai ya gani yagani ya fahimci ba kwanciyar jin dad'i bane, kusa da ita ya matsa yad'an rank'wafa kansa zai sumbace ta, da sauri yad'ago jin wani irin hucin zafin daya bugi fuskar shi, hijabin yayi sauri ya warware shi, yana k'ok'arin cirewa ta bud'e idanuwan ta da sukayi ja, ta lumshe su hawaye ya biyo baya saboda wani irin azaban da take ji akan ta, yana wani irin sarawa kamar zai fad'o, a rud'e yafara tambayar ta me yasame ta, ba abunda takeyi sai hawaye, da sauri ya mik'e ya Deb'o ruwa a cup, ya zauna ya mik'e k'afafuwan sa ya jawota yad'aura ta akai, kayan jikinnata ya cire yafara
matsa mata jiki da ruwan, sai da yaji jikin yad'an yi sanyi ya rungumo ta sosai, "me yake damun ki maryam, don Allah kiyi mun magana".
kai kawai ta kad'a mishi, ya dad'a mannata ajikin sa, kafin yayi magana Fateema ta turo d'akin ta shigo, ganinsu a haka sai da k'irjin ta ya buga, da sauri tayi baya zata juya, taji muryan shi yana cewa
"ina zakije"?bata juyo ba ta k'wak'ulo murmushi ta ce "nazo duba Aunty ne".
ya ce "shine zaki koma"?
bata tsaya bashi amsa ba tasa kai ta futa.
ita kanta maryam kunya taji, daga ita sai pant ajikin ta, gashi ya wani matseta a jikin sa.
Ahankali ya d'agata ya d'auko mata kaya ya sanya mata harda hijabi, sannan yanufi d'akin Fateema, tana jinshi tayi toilet da gudu ta wanke fuskar ta tafito, binta yayi da kallo kafin ya ce "me ya sami idonki"?
murmushi tayi tace k'waro ne yashiga har yanzu ina jinshi, ka huremun, ta isa gaban shi tana ware idanuwan, kama kan yayi, yafara hure wa, yayi sau uku ta ce yafita, sannu yayi mata sannan yace, "zan kai Maryam Asibiti ashe batada lafiya".
tausayi k'arara a fuskanta ta ce "me yake damun ta, shiyasa bata tashiba, sai muje tare".
ya ce "a'a ki zauna yanzu zamu dawo, inaga zazzab'i ne kawai".
Har bakin mota ta rakasu, tanayi wa maryam sannu.
Gwajin farko aka shaida musu cikine ajikin ta, kuka Anwar ya farayi na tsananin murna, a take yayi sujjada yana godiya ga Allah, d'aga Maryam sama yayi yafara juyi da ita, shi kanshi likitan tayashi murna yakeyi, dak'yar ya iya tsayawa aka rubuta musu maganin da zai sa jikin yad'an rage zafi, tsam ya d'auke ta kamar wata jaririya, haka yayi ta ratsawa cikin mutane anata kallon su, bai damu ba don gani yake kamar idan tayi tafiya cikin zai zube.
koda suka isa gida ma d'aukar ta yayi, ta ce "ka sauke ni zan iya tafiya fa".
bai ko saurare ta ba ya tafi abunshi.
Fateema ta k'urawa tv ido taji shigowar su, da hanzari ta mik'e ganin Maryam nad'e a hannun shi, tayi tsammanin ciwon yayi tsanani ne, kawai sai gani tayi Anwar yana danse rawa harda 'yar wak'a
*Soyayya tayi k'arko masoyiy a kula da ita, kada ayi mata ɓatanci sahiba akiyaye ta, Wayyo ni Allah daɗi ya cikani....*
sororo Fateema tayi tana tunanin me zaisa Anwar farinciki haka, haihuwa, tabaiwa kanta amsa, kenan Maryam tasamu ciki, ai batasan lokacin da murna ta kamata ba, itama rik'o maryam tayi tana taya Anwar rawa tana amshi, Maryam daɗi kamar ya kashe ta ganin soyayyar da Fateema take nuna mata, ranar wuni sukayi suna abu ɗaya, duk ciwon da Maryam takeji haka ta daure kada ta ɗaga musu hankali.
Dare ya tsala amma Anwar ya kasa bacci, zuciyar shi sai kitsa mishi takeyi yaje ya dubo maryam, baiyi dogon tunani ba ya mik'e ya nufi k'ofa, Fateema ta ce "ina zakaje".
ya ce "zan dubo baby na".
Dariya tayi ta mik'e tace "muje tare nima inaso mu gana".
ya nok'e kafaɗa ya ce "nak'i wayon".
ta ce "wlh tare zamuje nima nak'i wayon".
da dariyar su suka nufi ɗakin Maryam.
Maryam ta daɗe da bacci saboda maganin da tasha, har rige rigen taɓata sukeyi, a hankali ta buɗe ido, ganin mutane akanta yasa tayi saurin tashi ta zauna tana mutssuka ido, waro ido tayi tace "lafiya"?
Fateema ta ce "yi hak'uri Aunty mun tasheki, rigimane dashi wai zai duba babyn shi".
Maryam ta ce "kodai rigima ne daku, tunda kum tashe ni sai kuzauna muyi ta kallon juna".
Dukkan su suka fashe da dariya, Anwar kamar jira yakeyi yaja hanun Fateema suka zauna a kusa da Maryam, Fateema ta ce "ga shawara, kada mubari Hajiya taga cikinnan, mubata mamaki".
Duk sukay na'am da maganar.
Rayuwa me daɗi sukeyi, Fateema bata gajiyawa ko kaɗan da halin da Anwar yake mata, ranar girkin ta aɗakin Maryam yake kusa kwana wai kada wani abu ya sameta, Maryam tayi2 ya daina yak'i, Fateema tace tabarshi kawai wataran itama zata rama.
Adaidai lokacin Fateema ta cika shekara guda agidan, Maryam kuma tanada shekaru uku, cikin ta wata biyar harya fara fitowa, har lokacin Hajiya batasan Maryam tanada ciki ba, ita bata zuwa gidan ko kaɗan, acewar ta zasu rainata ita kuma akwai son girma, shiyasa batasan abunda yake faruwa ba.
yau tun safe Fateema ta shirya zataje gaishe da Hajiya kamar yadda ta saba takanje mata wuni wani lokaci, a hanya Anwar ya mata siyayya wanda zata kai mata.
Tun shigarsu Fateema taga canji, fuskar Hajiya a murtuk'e, dak'yar ta amsa gaisuwar da suke mata, Fateema ta ce "na shiga uku, kaddai shekara ɗaya har zata dawo kaina....
Maganar Hajiya ne ya katse mata tunani
"Anwar nifa nagaji da irin matar da kake kwasowa, ace har yanzu ba wani labari, to wallahi aure zan maka wacce zata cikamun gida da jikoki, kullum zuwa babu hayaniya babu komai".
Anwar daya zuba mata ido ya ce "Hajiya shifa haihuwa na Allah ne".
Ta taɓe baki ta ce "kullum maganar kenan, Allah yace rashi in taimake ka ai".
Zufa duk yagama wanke Fateema, "nafaɗa mata Maryam nada ciki kawai a huta, kai a'a banyi shawara da Aunty ba".
Ita kaɗai take saka da warwara a zuciyar ta.
Anwar yace "kinga irin wannan rashin hak'urin ne yasa kika so tafka kuskure".
Hajiya ta masa wani kallo kafin tace "yanzu don inaso naga ɗanka shine kake faɗa mun magana, ita waccan saboda taurin kunne kak'i sakin ta, bayan har k'wayoyi takesha, menene kuskure na anan".
Ta k'arashe kamar zatayi kuka, Anwar ya ruɗe ya ce "Ina nufin kuskuren da kikayi na bada magani asawa Maryam, gashi yanzu ta samu rabon ta, Allah ya bata cikinnan".Zunɓur Hajiya ta mik'e, wani gefen zuciyarta tana nanata Maryam nada ciki, mummunan kallo ta watsa wa Fateema ta ce "Ashe ke algunguma ce? Zuwa kikayi kika faɗa masa? To wallahi bazan zauna dake ki rainani ba".
iya ruɗewa Fateema ta ruɗe, ta kalli Anwar ta fara girgiza mishi kai, shima girgiza mata kai yayi,
"Hajiya me kike tunani ne, ranarda kika bata maganinnan ina tsaye ina gani...
da sauri ta katse shi, "k'arya kakeyi Anwar, yanzu zaka saki yarinyar nan kafin mahaifin ka yadawo k'asar "Hajiya menene laifin Fateema a ciki, don Allah kimun rai kada ki rabani da farinciki na, idan har kika yi haka bakiyi adalci wa kanki...
tsawar data masa shi yasa shi yin shiru, lokaci guda tayi d'aki, da gudu Fateema ta fad'a jikin sa ta saki wani kuka, "kada kabari ta rabamu, ina sonku kaida Aunty Maryam, idan natafi wazai kula...
cikin tsananin tausayi ya had'e bakin shi da nata, biye mishi tayi har suka zauna basu sani ba.
"eyeeeh
*LALATA*
zaku nuna mun? wlh kaji na rantse saika sake ta".
muryar Hajiya suka jiyo, ta futo d'auke da bairo da takadda a hannun ta, a duburbure suka saki juna, Fateema tana kuka ta ce "HAJIYA nayi miki al'kawari bazan rainaki ba...".
ko kallo bata ishe ta ba, cike da masifa ta mik'a masa takaddar, runtse ido yayi ya ce "sai dai kiyi hak'uri, bazan iya saketa babu abunda tamun ba, idan laifine kece me laifi hajiya...".
Kafin ya gama ta tsinke shi da mari har sau biyu, "wlh matuk'ar baka sake ta ba zan tsine maka".
"zan sake ta".
a rud'e Fateema take kallon shi, bai ko kalle ta
ba ya mik'a hanu ya amshi takaddar wajen Hajiya, rubutu yayi ajiki ya nad'e ya baiwa Fateema, Kukan da ta b'oyene ya fito tayi waje da gudu, tana ji yana k'iran ta bata tsaya ba.
wani murmushi yayi ya ce "sai me kike buk'a ta? uwata me ran k'arfe".
Ita kanta jikin ta yayi sanyi, ta shige d'aki ta barshi.
Taxi Fateema ta nema ta nufi gida, sai da ta isa ta d'auko mishi kud'in, taji dad'i ganin Maryam bata falon, idon ta harya kumbura don kuka, bata b'ata lokaci ba ta had'a kayan sawar ta, ta jefa takaddan da Anwar ya bata ajaka, ta sid'ad'a taja kayanta tabar gidan.
Anwar kam gidan Bilal ya nufa suka sha hirar su, kusan wunin sa agidanne baya so ya koma ya tarar da masifar da take tun k'aro shi, a tak'ai ce sai dare ya koma, yasan duk rintsi Fateema bazata sashi kaita Jos a darennan ba.
Maryam yasamu zaune duk kad'aici ya dame ta, tana jiran dawowar su, tana ganin shi ta mik'e ta rungume shi "yau kun cutar dani da yawa, tun safe ni kad'ai".
cikin shagwab'a ta k'arasa, cike da mamaki ya ce "ina Fateemar"?
"Ba tare kuka futa ba? ko kamanta ta agidan Hajiya ne"?
zare hanun shi yayi anata, jiki a sanyaye ya ce "Fateema bata dawo gidannan ba"?
.
A ɗaya daga cikin kujerun Falon ya zauna, yakama kanshi yana jin zafi a ciki, cikin nutsuwa ta isa wajen itama, duk da kujeran ya kasa musu sai da tayi ɗare2 akan cinyar shi, ta tallafo kanshi da hannuwan ta, ta ce "me yake faruwa Husby? A ina kabar Fateema"?
Hanun ta yakama yafara murzawa, a hankali ya shaida mata komai, cikin tashin hankali ta fara masifa, "Nima ba zama zanyi ba, yarinyar da babu ta biyun ta a hak'uri zaka saka? Hajiya ai idan aka mata dabara baza ta gane ba, me yasa zaka....
rufe mata baki yayi ya ce "ki kwantar da hankalin ki Maryam,
Kinsan Hajiya uwata ce, kina so ta tsinemun ne"?
Ta girgiza kai ta ce "a'a".
Yayi murmushi ya ce "yanzu abu ɗaya yaragemun, shine na k'ira naji ko Fateema ta isa garinsu
Nanma gyaɗa masa kai tayi.
Yak'ira yafi a k'irga wayar swchoff, har wani zufa ya farayi, duk k'ok'arin shi kada Maryam taga tashin hankali a tare dashi amma abun ya faskara, itadai sai binshi da kallo takeyi, tunawa yayi yanada numban Sakina, nan yafara k'ira, da yaji numbn ta shiga saida yayi ajiyar zuciya, tare da Sallama ta ɗaga, ta ce "yanzu nake shirin k'iran ka kuwa, sai naga k'awata a gida, kuma sai kuka takeyi tak'i magana, wani abu ya farune?"
Ji yayi hankalin shi ya tashi, amma ya daure harda murmushin sa, ya ce "idan kuna tare taimaka ki bata wayar".
Ta ce "To".
Ko kallon ta Fateema batayi ba, duk nacin Sakeena dole ta hak'ura ta shiga baiwa Anwar hak'uri.
Ya ce "kin gane Sakeena, akwai matsala ne, ki tayani bata hak'uri, ki rarrashe ta don Allah, bana so nasake jin tana kuka, idan ta huce zan k'ira ta".
D'uf ya ka'tse k'iran, mik'ewa Maryam tayi batace komai ba, tausayin Fateema duk ya cikata, abinci ta ɗauko masa ta shirya masa a wajen, bayajin ci ko kaɗan, tabbas yarinyar ta tafi da wani ɓangare nasa, amma duk k'ok'arin da zaiyi ganin Maryam bata gane ba zaiyi, baya so ta fara wani tunani mara tushe da har zai taɓa mata zuciya da abunda yake cikin ta, amma sosai yakejin kewar Fateema a tare dashi.
Bai ankara ba sai ji yayi ta kai abinci bakin shi, bashi da wani zaɓi daya wuce yaci, kamar magani yayi ta ɗurawa har tagama bashi ya cinye tas, kunun ayar ta tsiyaya mishi, nanma ya shanye tas,
Mamaki takeyi irin abincin daya ɗura yau baiyi k'orafi ba, batasan shi baima san yak'oshi ko bai k'oshi ba, murmushi tayi ta ce "kana lafiya kuwa baby"?
Ya zuba mata ido ya ce "me kika gani"?
"naga cinka yayi yawa ne".
Ya lakuce mata hanci ya ce "ke kika ɗuramun".
Ta ce "yau kuma harda sharri? Idan ka k'oshi ai baka bari a ɗura ka".
Yayi dariya ya ce "muje muyi wanka bacci nake ji sosai".
Harda 'yar hamman sa.
Suna fitowa daga wanka ta zura doguwar riga ta fara sallah, ganin haka yasa ya nufi ɗakin shi, kasa taɓuka komai yayi, yarinyar nan akwai shiga rai, yafaɗa gami da tsaki, mik'ewa yayi ya nufi ɗakin ta, anan yagane ta kwashe kayan ta, yayi mamaki da har ta shigo ta kwashi kaya Maryam bata sani ba, k'amshin ɗakinne ya sauk'ar masa da kasala tareda tsantsar kewar ta, ya kwanta a gadon yana tuno rayuwar su, ji yake kamar dun kai shekara da rabuwa, a haka har bacci yayi awon gaba dashi.
Tana idar da sallah ta tashi tayi ɗakin sa, dubawa tayi har toilet baya ciki, gidan ta shiga dubawa amma wayam babu alamar Anwar, shiru tayi tana nazari, can ta nufi ɗakin Fateema, a mik'e ta ganshi yana sharar baccin sa, ajiyan zuciya tayi ta ce "lallai akwai aiki a gabana, ina cikin gidan amma ya kasa nutsuwa har saida ya shigo ɗakinnan, bata bari ranta ya ɓaci ba ta fara tunanin menene mafita, dole ta mantar dashi tunda babu amfani, gaban gadon taje tsaya tana k'are masa kallo, haɗaɗɗen matashi dashi, kyau iya kyau Anwar ya wuce misali, "ni nayi sakaci har wata tasamu daman shiga zuciyar haɗaɗɗan mijina".
Murmushi tayi ta koma ɗakin ta, zama tayi tayi kwalliya sosai, gaba ɗaya gidan ya ɗume da wani irin k'amshi, duk turaren da tasan bata amfani dasu sai datayi a ƙlokacin, shigar bacci tayi, Faɗar irin rigar baccin da tasaka ɓata lokacine, ku k'iyas ta da kanku, cikin ta daya ɗan fito kaɗan ya k'arawa shigar kyau, shi kanshi gashin kanta sai da ta bashi hakkin shi domin wani irin k'amshi ne yake tashi a ciki, kwanciyar ta tayi duk da idon ta ya k'ekashe babu alamar bacci, ganin zata fara mummunar tunani ne yasa ta ɗauko wani littafi na adduoi ta fara karantawa.
.
.
Baccin shi yake sha sosai, duk mafarkin Fateema ne ya cika mishi baccin, sai wajen 12 ya farka, da sauri ya mik'e ganin inda yake baccin, fargaba da tsoron kaddai Maryam ta fito neman shi ne yasashi zare ido, yasan dole bazata ji daɗi ba, cikin sanyi ya koma ɗakin ta, a bak'in k'ofa ya tsaya yana k'are mata kallo, tayi masifar rikita shi, ta zama kamar wata 'yar tsana, bata ko nuna tasan ya shigoba, tanajin shi ma baccin k'arya tayi, rufuwa yaje yayi akan ta ya mata runfa yana shinshina ta, cike da shagwaɓa ta buɗe ido tana hararar shi, marairaicewa yayi ya ce "Bacci kikayi kika manta da ɗan saurayin ki ko".
kuka take shirin farawa ya ce "kiyi hak'uri, idan kikayi nima yi zanyi".
yasa hanu a k'asar cibin ta yana shafawa a hankali, ya ce "Babyn mu yak'i ya girma, anya kina bashi kulawa kuwa"?
Cikin zunɓura baki ta ce "wani irin kulawa ake bashi daya wuce kaci abunda kaji kana son ci".
Murmushi ya yi yace "baki canka ba, akwai wata kulawar".
Zare tawul ɗin jikin sa yayi, ya mirgino da ita kanshi, shi ya koma k'asa, binshi tayi da kallo da idanuwan ta da suka k'ank'an ce saboda sha'awar mijin ta dataji yana fizgan ta, a hankali ya raɗa mata "na nuna miki"?
Kasa ce mishi komai tayi jin irin abunda yake mata, ya lumshe ido ya ce "kin canza da yawa Maryam, jikin ki har tsantsi yakeyi, ko akwai wani sirrine......
Kasa k'arasawa yayi jin tana lasan k'irjin sa, wani iri yakeji kamar ya suma, har wani tsotsan kan takeyi tana shafa k'asan marar shi da hannun ta, wani irin ninshi yake yi da bai taɓa yi ba, sai da taga ta gama ruɗa shi ta haɗa bakin shi da nata, shafata ya shiga yi yana matseta kamar yana so ta koma ciki, donma yana tunanin cikin ta da matsan yafi haka, zazzafan kissn ya fara mata, gaba ɗaya yagama rikice mata, mayen turaren ta yafi komai fizgan shi,
Ohhhhh!
Nidai ganin Haleema s Bichiki ta zuba ido yasa najata muka tafi garin Jos.
.
.
Mahaifiyar Fateema ta rafka tagumi, kukan Fateema yafi komai k'ona mata rai, tayi tambayar duniyar nan amma amsar babu komai, sakeena haka ta tafi gida da tunanin menene matsalar k'awarta, tafi alak'anta haka da sun samu saɓani da kishiyar tace, washe gari kuwa da sassafe Maman ta ta aika aka k'ira mata Aunty Hadiza akan tazo ta mayar da ita ko yaji tayi, nanfa hankalin Fateema ya tashi, dole ta buɗe baki tayi magana, ta ce musu yasake ta.
Da mamaki uwar ta ce "wani irin saki kuma Fateema, yanzu kashe Auren kikayi muna murna kin samu kishiya ta gari, ni banyadda ba sam, menene shaidar ki na cewa an sakeki"?
Tace "Mama wallahi da gaske nakeyi".
D'auko takaddar tayi ta nik'awa Maman tata, ta ce "yo ni kuma karatu na iya da zaki mik'omun, kibaiwa Hadiza tagani".
Aunty Hadiza ta taɓe baki ta ce "kayan bak'in cikin zan gani? Kije ki ɓoye abunki zaifi miki".
Ta ce "Aunty nima Wallahi ko karantawa na kasa yi, inajin zafin rabuwa da mijina, ina son Anwar Aunty".
Sak kuma ta fashe da kuka.
Kama baki sukayi suna kallon ta, maman ta tace "kina sonshi kika kasa hak'uri har ya sako ki, zaman talauci ne bai ishe ki ba Fateema".
"mama ke kin iya mata magana ma, ni ji nake kamar namata duka, kuma nasan yanzu haka kishiyar nan tata me kama da aljanu ne ta haɗa su, idan kinga makirci irin yanda take jan Fateema a jiki zaki sha mamaki, kema ba irin makircin da bamu koya miki ba amma kika tsallake, ai baka taɓa iya zama da kishiya sai ka koyi makircin hak'uri da kai zuciya nesa....
"Aunty sai zuba kikeyi kina ɗaukar alhakin baiwar Allah, Maryam bata taɓa nunamun bata sona ba, mahaifiyar shi ce tasa ya sakeni wai....
sai kuma tayi shiru.
Mama ta tafa hannu ta ce "wai me? Yau anshiga uku, uwar tasa kika taɓo kuma Fateema"?
Fateema dai labarin komai ta basu, koda Mahaifin ta yadawo cewa yayi Allah yasa hakan shi yafi alkairi.
.
.
Anwar duk wata sai ya tura da kayan abinci nik'i2 gidan su Fateema, hatta tufafi, bai daina aika mata dashi ba, kuma yana haɗawa da kuɗi me tarin yawa, tun bata jure rashin shi har tafara jurewa, ta gama idda da wata ɗaya Maryam ta fara nak'uda, Hajiya Jamila tsaban tsaurin ido tafi kowa ɗoki akan cikin, har gida taje ta nemi yafiyar Maryam akan haɗa mata sharri da ta so yi..
Anwar kam sosai ya manta da kaɗaicin Fateema, yasan dai tana manne a k'asan zuciyar sa amma bawai na kaɗaici ba.
Lokacin da ta fara nak'uda cikin darene, Anwar duk ya ruɗe, tana kuka yana kuka, ganin abun nata yana gaba gabane yasa ya kinkime ta, du k'aton cikinnan baisa yaji wani nauyi ba, mota yasata suka tafi asibiti, duk ta jigata shima ya jikata, da sauri aka sgigar da ita saboda takai matakin k'arshe, minti 10 tsakani aka fito aka shaida masa ta haihu.
Santaleliyar 'yarta mace ta haifa, kyakkyawa me kama da Anwar, murna wajen Anwar da dangin sa ba'a magana, Hajiya Jamila abun nema ya samu, Manya manyan mutane ta gayyata, kuma a lokacin Dadyn Anwar ya dawo, Ansha shagali kamar ba gobe, ansaka wa yarinya suna AISHA!
takwara akayi wa Eshat Aysm, Bichiki Fans ina gani suna taka rawa saboda anyi wa k'anwar su takwara, iyalan gulma saida sukaje wajen taron sunannan su Afeefah, cure Farida, Janan beauty, Ayusha Durln...
Sunada yawa iyalan gulman🙄
Maryam tasha kyautuka sosai, bayan suna k'anwar Momyn ta tace dole fa akai ta wankan gida, fushi sosai Anwar ya shiga yi amma ta ce fir sai Maryam ta tafi wankan gida, abu har yaje gaban mahaifin Anwar, hak'uri ya bashi ya lallaɓa shi ya ce kwana Arba'in ɗin nawane kamar yaune, Hajiya Jamila ta ce "nima shi nagani".
Dady ya ce "kuma ba kanada wata matar ba"?
Da sauri Hajiya ta kalle shi tana k'yafta mishi ido, yayi kamar bai ganta ba, ya ce "Dady ai bata nan, tayi wata 5 a gida yanzu".
Jaridar hanunsa ya ajiye, yamaida nutsuwar sa ga ɗan nasa, "me yafaru"?
Hajiya Jamila tayi caraf ta ce "yarinyar batada kunyane, shiyasa ya saketa".
Dady ya ɗaga mata hanu "Bafa ke na tambaya ba".
Ta tsuk'e bakin ta tayi shiru, Anwar ya ce "Ban saki matata ba, Dady, matsala aka samu....
Sai kuma yayi shiru yana kallon Hajiya, yana so ya rufa mata asiri amma idan ya biyeta Fateemar sa bazata dawo ba kenan, Dady yace "matsalar me zai janyo har ka kasa hak'uri kayi saki, kana yaro dakai kafara saki, idan ba sakiba me zaisa taɗau tsawon lokaci tana gida, bana son shashanci fa Anwar".
Anwar ya sunkuyar dakai yace "Hajiya ce tasan komai".
Harara ta watsa masa "Ni ina uwar taka zakamun sharri"?
Alhaji ya ce "banaso kisake magana Jamila, nasan halinki sarai ba tausayi kike dashi ba, Anwar faɗamun duk abunda yafaru kaji".
Anwar kuwa baiyi k'asa a gwiwa ba yasanar masa duk abunda ya faru, Hajiya har wani ɓari takeyi saboda kaɗuwa, Alhaji ranshi ya gama ɓaci ya ce "kana nufin ba takaddar saki ka bata ba"?
"wallahi ban saki Fateema ba Dady".
Wani kallo Alhaji ya watsa mata ya ce "ke har ɗannaki ma mugunta kike masa, to nima zanyi abu guda ɗaya, matuk'ar auren yaronnan bai gyaruba to wallahi zan sakeki".
Anwar ya ruɗe ya ce "Haba Dad yaya zaka faɗi haka kuma harka rantse, uwata ce fa, ni nayafe mata duk abunda tayi".
Hajiya Jamila kam tuni hawaye ya fara wanke mata fuska, Alhaji ya ce "kidawo masa da matar sa sai auren ki ya gyaru, kinma samu yanada hankali da yanzu yayi saki da kincuce shi kinkuma cuci kanki, maganar wankan gida kuma kayi hak'uri kabarta taje, kwanakin basuda yawa".
Russunawa Anwar yayi ya masa godiya sannan ya mik'e ya tafi.
.
.
Fateema tuni ta saki ranta, bata tunawa da komai saiɗmda jefi2, tunda taga ta gama iddah taci gaba da rayuwar ta kamar bata taɓa aure ba.
.
.
Mahaifin Fateema ne zaune a kasuwa wajenda yake sayar da yalo da mangoro, garin yau kwata2 babu ciniki, ya haɗa tagumi yaji tsayuwar mota a gefen rumfar shi, mata ne su biyu, kana ganin su kasan basuda wata matsala, sallama suka masa ya amsa da fara'arsa, 'yar matashiyar ta ce "ka zuba mana yalo".
ta mik'a mishi 1000, da ɓari ya karɓa yana washe baki, ya cika leda ɗaya ta viva matar ta ce "wannan ai yayi yawa, idan banda kwaɗayin masu ciki mezai kaiki cin yalo".
Zunɓura baki ɗayar tayi kamar zatayi kuka ta ce "Ummi zan iya cinyewa fa".
"to amsa mutafi kinsan akwai tafiya agabanmu".
Har sunfara tafiya matar ta ce "kinga wannan tsohon da zai amince da mun tafi dashi zai mana amfani".
"kaji Ummi da wani magana, wazai biki haka kawai baisan wacece ke ba, duniyar nan kowa bai yadda da kowa bane, amma kinga da ya huta da wannan shan ranar, sai dai kuma baza'a rasa yanada iyali ba".
matar da aka k'ira Ummi ta ce "dazai amince harda iyalin nasa sai mutafi mubasu gida ɗaya, shikuma yana mana gadi muna biyan shi, tsoron mutanen Meduguri nakeyi shiyasa nakasa nema acan".
"to nidai mutafi tunda tsayuwar bashi da amfani".
H
Duk abunda suke faɗa Mahaifin Fateema yana jinsu, Sosai yaji yanaso yabisu, ganin sun shige motane yasa ya kwasa da gudu ya tsinkaye su, Ummi ta lek'o ta ce "Baba wani abune"?
Yasusa kai ya ce "Naji kuna maganar aiki, shine nace na amince".
Suka kalli juna kafin matashiyar ta ce "ka amince damene? Mufa gadi zaka mana, idan kanada mata da yara zamu tafi da ku duka, tunda garin banan kusa bane".
"To Hajiya wazaik'i ci gaba a rayuwar sa, inada mata ɗaya sai yarinya ta ɗaya sauran sunyi aure".
Buɗe mishi sit ɗin baya tayi ta ce "shigo mutafi muje gidan naka".
Ba musu ya shiga suka tafi yana nuna musu hanya.
.
Fateema suna zaune da Sakeena Maman tana hura wuta sukaji tyayuwar mota, Sakeena ta ce "yau kuma Anwar ya tuna dake kenan yazo".
Fateema ta taɓe baki ta ce "idan yak'irani yana wani maganar kamar baisan ya sakeni ba, harda bani umurnin kada naje kasuwa, kada na tsaya da wani, kinji fa wani kulle kamar zanyi ta zama masa babu aure ne".
Sakina mamaki ya kamata ta ce "kinsan yana sonki, shima babu yanda ya iyane, ɗaukomun takaddarma naga saki nawa ne".
Fateema taja tsuka "Don Allah manta da takaddarnan ko saki nawane ai anriga da anyi, ni so nakema na canza layi yadaina k'irana, kullum famamun ciwon sonshi yakeyi".
Maman ta tanajin su, ajiyar zuciya tayi ta ce "kullum bakuda taɗi sai Anwar, zanga ranar da zaki cire shi aranki....
Bata k'arasa ba Baba me yalo ya shigo, sai washe baki yakeyi.
"yau akwai alamar nasara a kasuwa, sai farinciki kakeyi".
Ya ce "sosai ma, nan ya kwashe yanda sukayi da Matannan ya faɗa mata, itama washe baki tayi tana adduar Allah yasa k'arshen talauci ne yazo, Fateema kam kuka tasa tana cewa babu inda zataje, itama Sakeena kuka takeyi kada atafi mata da k'awa, masifa ya shiga surfa musu, yana ganin zai huta yara zasu masa buk'ulu, dole ma ta bishi su tafi ko kuma ya ɗaura mata aure yau yayi tafiyar sa.
Cikin k'ank'anin lokaci yayun ta suka zo, suma sunyi murna, su hakanma yafi musu tunda basuda 'yan uwa agarin sungaji da ganin mahaifin su yana saida yalo, su Ummi kam tunda suka ajiye Baba me yalo suka koma masauk'insu akan da asuba zasu zo ɗaukarsu kafinnan sun gama shiri, dak'yar aka shawo kan Fateema ta amince sai da taga da gaske duka zata sha.
.
.
Hajiya Jamila zaune ta rabka tagumi, nadama ne ya cika ta sosai, tunanin ta ɗaya bai wuce ta ina zata fara ba, gashi tunda Alhaji yaji maganar ya daina kula ta, dabara ne ya faɗo mata, ta ɗauko wayar ta tafara k'iran Anwar, yana kwance sai juyi yakeyi, kewar matan sa duk ya addabe shi, musamman Fateema dayake jin wani bugun zuciya idan ya tuna ta, ga tsananin sha'awar datake takura mishi, duk yayi wani zuro a kwana biyu.
Jin wayar shi ta fara ruri ya tashi a kasalan ce, ganin Hajiya yasa shi watssakewa yana tunanin ko lafiya.
"Hello Anwar kana ji na"?
"inajin ki Hajiya".
"kayi hanzari ka dawo da matar ka".
Anwar me zaiyi idan ba dariya ba "yaufa kwanan ta biyu da tafiya kuma sai tayi kwana arba'in zata....
Katse shi tayi da sauri "Ubanka na ce, ni zaka raina ko Anwar, kasan wacce nake nufi".
K'unshe dariyar yayi yace "Gobe insha Allah zanje, kina tsoron Dady....
D'uf ta kashe wayar tana zage2, yaronnan ya raina ni wallahi.
shikam dariya yayi ya ce uwata sai Dady, yayimun dabara.
.
.
Washe gari da safe bayan yaje yaga Baby Aisha ya nufi garin Jos, hankalin shi a kwance.
yana isa ya tarar da gidan gark'ame da kwaɗo, can ya hango yaro ya k'ira shi, tun kafin ya tambaye shi ya ce "mutanen gidan sunyi tafiya jiya, amma inaga bazasu juma ba naga basu ɗauki kayansu ba".
Anwar yayi jum sannan ya masa godiya yabashi 1k.
Zuciyar shi fal tunani ya koma gida, gidan Hajiya ya wuce kai tsaye, tana ganin shi ta hau tambayar shi ya ɗauko ta, girgiza mata kai kawai yayi yaje ya kwanta abunshi.
.
.
Tafiya me tsayi sukayi kafin suka isa garin Meduguri, isar dare sukayi duk sun gaji musamman su Baba me yalo da ba'a saba tafiya me nisa ba, duk da darene haka masu aiki suka shiga aikin kawo musu abinci, wani part aka kaisu me ɗauke da ɗakuna biyu, sai kitchen da toilet a gefe, wankan gajiya Fateema tayi, ta cika cikin ta da abinci sannan ta hau Sallah, tana idar wa, ta ɗauko jakarta zata ɗauki wayar ta, waya yace ɗaukeni inda kika ajiyeni, ba irin neman da batayi ba amma babu, haka ta hak'ura ta kwanta tabari akan yana wajen su Baba me Yalo.
Ƴ
.
.
Washe gari da safe Ummi ta aika aka k'ira mishi Baba me Yalo, yauma matashiyar nanne ajikin ta, sai zuba mata surutu takeyi, Ummi bata mishi magana ba har saida ta lura ta gama surutun, rabin surutun ma k'anzon kuregene.
"kamar yadda muka rabaku da garin ku, ina fata zaka mana aiki cikin aminci, nidai banida wasu yara a gidannan, yaro na guda ɗaya ne kuma bashi da futuna, zaka rik'a yimana gadi muna biyanka 50k a wata, tunda ka taho da iyalan ka, zasu iya shigowa suna mana wankau sai ana biyan su, ko yaya ka gani".
russunawa yayi yamata godiya.
.
.
Maman Fateema sosai tayi murna, ita dai Fateema taɓe baki tayi ta ce "nidai wallahi babu aikin da zanyi".
"sai kiyi ta zama ai".
Inji maman ta, Baba me yalo kuwa cewa yayi "kiyi zamanki, dama ba nufina kiyi wani abuba, su suka buk'ata, tunda bakiso babu dole, amma da zaifi miki zaman kaɗaicinnan".
"Baba ni yanzu waya ta zaku bani"
Ya kama baki, "ni kuma me zanyi da waya Fatee, kidai duba cikin kayan naki".
Shiru Fateema tayi, don tasan babu irin duban da batayi ba, shikenan wayata ta ɓata kenan, ta faɗa a ranta.
.
.
Zaman gidan babu yabo babu fallasa, mahaifiyar ta tana shiga ta musu share2 harda wanki, da yake Mama akwai tsafta ga raha yasa har suka fara sabawa da Ummi, abu ɗayane yake damun ta, ta rasa wannan me cikin 'yarta ce ko kuma, kome tace tana so a gidan shi akeyi, ga wani girma da Ahmad yake bata duk k'ank'an tarta, shagwaɓa da iya shege babu wacce batayi, kuma taji Ummi ta ce ɗanta guda ɗayane, itadai bata tambaya ba
Satin su biyu a gidan Maman Fateema ta tashi bata jin daɗi, don haka da asuba tacewa Fateema taje tayi aikin kamar yadda ta saba, zunɓura baki tayi kafin tace "Nifa bansan kan gidan ba Mama, kuma ai bansan aikin da kikeyi ba".
Mama ta taɓe baki ta ce "gidan zaki share musu, sai ɗakunan su, sannan ki haɗa kayan da suka cire ki wanke su".
Fateema tayi tsaye tana kallon Mama.
"yanzu wai duk wannan aikin ke kaɗai kike yi, bansani ba da ina zuwa ina tayaki".
Dungure mata kai tayi ta ce "Ina nan akace kije kika k'i".
Tafiya tayi tana k'unkuni.
Dak'yar ta gane kan gidan sannan tahau gyarawa, saida yayi k'al sannan ta nufi ɗakin da taga Ummi ta nufa ranarda suka iso Garin, akan Sallaya ta samesu itada me cikinnan, Ummi ta ɗaga hanu tana addu'a "Allah ka gafarta wa mijina, Allah ka shiryi mijina, Allah kasa mijina ya shiga Aljannah, Allah kabaiwa mijina arziki na duniya da lahira me anfani.....
Duk abunda tace me cikinnan tana cewa Ameen, har suka shafa sannan Fateema ta russuna ta gaishe su, da fara'a suka amsa, Ummi tace "badai ciwon kan ya hanata zuwa ba"?
"Da sauk'i dai yanzu".
Fateema ta faɗa tana murmushi, Ummi ta dubi me cikinnan tace "Farida je ki haɗo mata wankin ɗakin ki".
Saida ta shagwaɓe fuska ta ce "wallahi ban iya tashi yanzu".
Ummi tayi murmushi ta ce "bari naje na dubo dakaina".
Itadai Fateema sake baki tayi ta kallon su, mik'ewa tayi ta gyara ɗakin sannan suka nuna mata ɗakin Ahmad akan idan 8:30 tayi kafin taje ta gyara saboda ba'a shiga sai ya futa.
"to".
Kawai tace taci gaba da aikin ta, k'arfe 8:30 tanayi ta nufi ɗakin Ahmad, ba damuwar komai tunda lokacin akace taje, ɗakin ta gyara duk da taga agyare yake kawai ɗan gyara wani wajen tayi, tana gamawa ta kwashe kayan da tabbatar su ya cire ta nufi toilet kai tsaye, wani mahaukacin k'ara ta saka ta fito a guje, bata gama maida numfashi ba taji an fizgo ta, ko ɗauraye jikin shi baiyi ba ya fito, sake wani k'aran tayi ganin mutum tsirara a gaban ta, ya wanke ta da mari, "ke mahaukaciyar inane, k'aramar 'yar iskace ke, tunda kin iya lek'a mutum yana wanka baki iya kallon shi ba, waye ya faɗa miki ana shigomun ɗaki".
Kuka ta rushe dashi da iya k'arfin ta, ya ware ido yana kallon ta yana mamakin to me yasa tashiga tasan yana wanka, cikata yayi ya koma wankan sa, aikuwa da gudu tabar ɗakin tana haki, ko wajen su Ummi bata nufa ba, ɗaki ta wuce ta kwanta, duk haushin Ahmad ya cikata, harda cemata k'aramar 'yar iska alhalin ahine ɗan iska da iya biyota haka, aikuwa ba inda zan sake zuwa.
.
.
Ruɗewar da tayi yayi masifar bashi dariya, tun yana wanka yake ta dariya har yafito ya gama shiri ya nufi wajen Ummi, har k'asa ya tsuguna ya gaishe ta, sannan ya juya wajen Farida, "Aunty ina kwana".
Ta ɗan shafo kanshi ta ce "bazan amsa ba sai nasan dalilin da yasa naga fara'a kwance a fuskar ka".
Murmushi yayi yace "Naga wata jerry taje gyaramun ɗaki, yau ina Maman tata"?
Farida tayi dariya ta ce "jerry fa kace, Fateema sunan ta, yau naga ka makara meyasa"?
Kafin ya bada amsa Ummi ta ce "kefa idan ba Ahmad kika gani ba sam baki warewa, yanzu ai sai kin makarar dashi zakiji daɗi"
.
.
.
.
.
.
.
.
.
Hajiya Jamila fa hankalin ta ya fara tashi, duk bayan kwana uku sai tasa Anwar ya tafi Jos amma har yau Fateema basu dawo ba, kullum Alhaji daɗa mata rashin mutunci yakeyi.
Anwar duk abun duniya ya isheshi ko yak'ira ta awaya har tagama ringn ba'a pickn, yanzu hankalin shi ya fara tashi, dama baka sanin kana son mutun sai ya maka nisa.
.
Tana zaune a bakin gado a ɗakin da aka bata, tana baiwa Baby Aisha nono, ta zuba mata ido tanajin wani sanyi a ranta, Anwar yayi sallama ya shigo, idon shi yana kanta yana murmushi, itama murmushin tayi ta ce "Abban Aisha sai yanzu, nidai kwana biyunnan nakasa gane meke damun ka".
D'an murmusawa yayi lokacin da yake zama kusa da ita, yasa hanu ya shafa kan Baby Aisha, yace "Yaushe zaki dawo".
Binshi tayi da kallo ta ce "ko sati uku fa bamuyi ba".
Bakinshi yakai saman nonon, sauk'an numfashin bakinshi taji akai tayi saurin ɗago dakan shi, "me kakeyi haka Anwar"?
Susa kai yayi yana dariya ya wayince da cewa "inaso nafaɗa miki wata magana Maryam, naje garin su Fateema yafi a k'irga bana samun ta, kullum gidansu a rufe, wallahi hankalina ya fara tashi".
Da mamaki take kallon shi, ta ce "me kake zuwa yi mata, bacin ka saketa kuma kake wani hankalin ka ya fara tashi, to Allah yasa Aure tayi ma".
Ta karashe tana zunɓura baki.
Karɓan Baby Aisha yayi ganin tayi bacci, yakai ta wajen kwanciyar ta yana cewa "menene kike ɓata rai to, kuma adduan ki ba ameen ba".
Shima yafaɗa yana ɓata rai.
Shiru tayi batace komai ba, ya zauna ta bayan ta ya ɗaura kanshi a gefen wuyan ta, ya ce "fushi kike yi don naje wajen Fateema"?
Sai da ta harari iska ta ce "Ni munafunci ne bana so".
Ya zagaye hannayen shi akan k'irjin ta ya ce "Nine munafukin"?
ture shi ta fara yi, ya ɗan matsa nonon ya ce "menene kike tureni kuma, ko idan antafi wankan gidan ba'a komai ne".
a ranta tace yau rigima ta tashi kenan, tamaga k'ok'arin sa.
hannu tasa ta janye hannayen shi ta ce "meyasa kake zuwa wajen Fateema har yanzu"?
Dariya yayi ya ce "tau kishi ta motsa".
kai mishi duka tayi ya rik'e hannun ya ce "zan faɗa miki, lokacim da Hajiya ta matsa na saketa ai ban saketa ba, nayi hakane saboda hankalin ta ya kwanta, kafin Dady ya dawo nasan zaisa indawo da matata, to yanzu lokaci yayi ne, inaso ta dawo".
Shiru tayi batayi magana ba, ya ci gaba da cewa "yanzu hankalin Hajiya yafi na kowa tashi, har 'yar rama tayi".
Kallon shi tayi tana neman k'arin bayani, "Dad ya ce idan Fateema bata dawo ba zai sake ta".
Dariya Maryam tasa harda sunkuyawa, ganin ya ɗaure fuska ne yasa tayi shiru, ya ce "Hajiya ta kikewa dariya"?
Ta waro ido ta ce "ni na isa, kawai dariyar ne tazo, yanzu sai kusan nayi tunda abun hakane".
da dariyar ta k'arasa maganar, ya ce "musan nayi ma zakice, ko wayarta fa na k'ira bata ɗauka".
Wani sabon dariya Maryam ta saki ta ce "Da yanzu ni ce nake gida, Fateema tamun abunda bazan iya kishi da ita ba, Hajiya kuma ta so taga bana raye, saboda rabuwarmu yana nufin mutuwa ta, da zanbi ta zuciya ta, danayi adduar Allah yasa kada kaga Fateema har abada, idan kuma nayi haka ban kyauta wa Fateema ba, don haka zan taya ku binciken inda sukaje, ta shafo sajen shi ta ce "zan nemo maka Fateema insha Allah".
murmushi yayi ya ce "kiman ta da abunda Hajiya tayi, tayi nadama sosai, bana burin auren ta ya samu matsala Maryam kinsan uwata ce".
Saida ya jagwalgwala ta ya rage sha'awa kafin ya tafi.
Tagumi tayi tana tunanin ta ina zata fara, wannan wani damane da zan daɗa gyara shimfiɗa ta, tabbas idan nayi k'ok'ari Anwar zai sake ganin girmata da daraja ta.
wayar ta ta ɗauko ta k'ira numban Sakina, bugu biyu ta ɗauka.
"Hello Aunty Maryam ashe zaki tuna damu"?
"Ai kullum ina tunawa daku, ina mutumiyar ko na k'irata bata ɗagawa".
Sakeena tace "wallahi nima haka, tun tafiyar su Meduguri aka daina samun ta".
Cikin jinjinawa Maryam ta ce "Meduguri kuma? Me yakaita"?
"sun koma can da zama fiyeda sati biyu data wuce".
Maryam ta ce "ikon Allah, yanzu bawani numban da za'a sameta"?
"Gaskiya babu sai dai ki k'ira su Aunty Hadiza ko suna da wani numban da suka k'irasu".
sallama sukayi tare da mata godiya.
koda ta k'ira suma magana ɗayane babu wata hanyar da zasuyi magana, sai dai kafin su tafi Ummi ta bata address ɗin inda suke, nan Maryam ta buk'ata.
Anwar daya dawo da dare daɗa kwantar mai da hankali tayi ta ce dazaran tayi arba'in zata nemo masa Fateema, da yafara gardama kada tasa kanta a wahala ta nuna masa ita tayi niyya kuma ai kamar yiwa kaine.
.
.
.
.
Ahmad fa tun daga ranar tunanin Fateema ya hanashi sakat, sosai yaji yanason yarinyar, har Allah2 yakeyi gari ya waye
ta sake zuwa mishi gyara ɗaki.
Ita kam da tace bazata sake zuwaba, ganin Mama bata warkeba yasa ta koma, kamar jiya tare tasami su Ummi suna addua, saida suka shafa ta gaishe su, bayan ta gyara ko inane Ummi ta k'ira ta, "Yau me gidan zak dawo, ki zauna ki tayamu aiki".
Amsawa tayi da "to".
Farida ta ce "idan kin gyara wajen Ahmad sai kidawo".
Nanma "to".
ta ce.
Itakam wajensu ta koma tayi kwanciyar ta, ba abunda takeyi sai kewar Anwar, yanzu nasan Aunty ta haihu, ko me ta haifa oho.
Sai juyi takeyi ita kaɗai, sai k'arfe tara ta mik'e ta koma wajen su Ummi.
Ahmad yana gefen Ummi yana karyawa, Farida tana jikin Ummi, can nesa dasu ta zauna ta ce "Me za'ayi yanzu"?
Ahmad da tun shigowar ta yabita da kallo ya ce "me yahanaki gyaramun ɗaki"?
Bata kalleshi ba tace "nagyara".
Shima shiru yayi don yasan bata gyaraba, Farida ce tace "muje mufara".
Itadai binta tayi kawai, inda ta zage tana aiki Fateema bata ɗauka tana aiki haka ba, taga kullum tana mak'ale a jikin Ummi, ita kuwa Ummi ko wajen da suke aikin bata nufa ba, sun dafa abinci yayi kala goma, abunsha yafi kala biyar, abunda ba'a magana, basu gama ba sai wajen 5 na yamma, Sallah kawai suke tsayawa yi, saida suka jera komai Fareeda ta wuce ɗakinta, itama Fateema ta juya zata tafi Ummi ta ce "idan kinyi wanka kizo ki karɓa muku naku".
.
.
wanka tayi tashirya sannan ta jira akayi magriba tayi, Mama ta ce "yau wani irin aiki kuka sha haka"?
"Kedai mama bari kawai, kuma mu biyu mukayi, bansan me cikinnan tana aiki hakaba, gashi ta iya girki k'amshin duk yacikamun hanci, yanzuma zanje na karɓo".
Gyaɗa kai Mama tayi "to ko k'anwar matar gidanne"?
Fateema ta ce "Inaga k'anwar tace, bakiga yanda take dangarta ta ba".
mama tace "ni zanbaki labari wannan, yanzu dai tashi kije kada suga kink'i komawa".
Mayafin ta tajanyo ta tafi.
a bakin falon sukayi kusan cin karo da Ahmad, wani malalacin murmushi yayi ya ce "ni zaki raina wa hankali ko"?
Tsaki tayi ta ce "daga isowata har nayi laifi"?
ya ce "wani rainin hankalin zaki kuma yimun, cewa kikayi kin gyaramun ɗaki ɗazu".
Saida ta watsa mai harara ta ce "mezan sakeyi a ɗakin ka bacin ko inama wajen wankan kane, dama bani bace me aikin kajira ta warke ta koma bakin aikin ta".
kafin yayi magana sukaji hayaniya ya karaɗa gidan, murmushi Ahmad yayi ya ce "Boss ya iso".
"to matsamun na wuce".
b
"bazaki wuceba sai yafara cin karo da surkar sa".
Kallon rashin fahimta ta masa ta ce "zan koma kawai".
da sauri ya bata hanya ta wuce shi kuma ya nufi inda hayaniya ke tashi, yana isa Dad ɗinshi yana fitowa a mota, ma'aikatan gidanne cike awajen kowa yana murna, da gudu Ahmad ya faɗa jikin shi yana murna, shima Dad cikin farinciki ya daɗa rungumeshi.
.
.
wani irin kwalliya Ummi da Farida sukayi, Fareeda tayi masifar kyau ga wani k'amshin da yake tashi ajikin ta, itadai Fateema sake baki tayi aranta tana cewa "wannan kam akwai shiga uku, har ta fi matar gidan haɗuwa".
Tunanin ta ne ya tsaya cak lokacin da taga Dad ya shigo, cikin wani irin taku Fareeda ta k'arasa ta rungume shi ta saki kukan shagwaɓa, sai bubbuga bayan ta yakeyi yana rarrashin ta, wai tana kukan tayi missing ɗinshi, yana rungume da Fareeda ya mik'a wa Ummi hanu, k'arasawa tayi itama taɗan kwanto ta gefenshi fuskar ta cikeda murmushi.
ganin irin kallon da Fateema take musu ne yasa Ahmad Yayi sauri yaja hanun ta suka bar wajen.
Fateema kasa daure wa tayi ta ce "tsaya na tambaye ka, wannan Aunty Fareedan itama 'yar Ummi ce".
ya ce "a'a, Farida matar Dady
ce".
Da mamaki take kallon shi, "matar Dady fa kace Ahmad".
"eh haka nafaɗa, Farida tanada kirki sosai, lokacin da Dady ya aurota bakiga irin wahalan datasha a wajen Ummi ba, amma ta jure tayi hak'uri har suka zamto tamkar uwa da 'ya".
Ajiyan zuciya ta sauk'e, ta juya zata tafi yayi sauri yaja mayafin ta "Don Allah ki tsaya muyi magana, Dady bazai wuce sati ɗaya ba zai koma, tun ranar da naganki naji nasamu matar aure".
Gaban ta ne taji ya faɗi.
"zan faɗawa Dad nasamu mata, don Allah kada kice baki sona".
Shiru tayi tana nazari, can ta ɗago tace "Allah ya tabbatar da alkairi".
.
.
Abu kamar wasa Dady ya amince ya aure ta, wasa2 suka fara soyayya duk da ita hankalin ta yana kan Anwar, idan ta tuna wani abune kawai take k'ok'arin mantashi, ba wanda bai goyi bayan auren ba saboda Fateema tanada shiga tai ga hankali, sati biyu akasa biki, Ahmad murna kamar me, lokacin ta fara shirin zuwa Jos amma mahaifin ta yace shi zaije basai taje ba.
Ranar Talata Maryam anyi Arba'in, har wani shagalin biki akayi, Anwar ya zama tamkar ango yana murna zata koma gidan ta, tunda sassafe yaje ɗaukan ta, yasa mata rigima Mamy ta lallaɓa shi sai zuwa dare.
Ranar an gurji juna, Maryam sabuwa ta zame masa saboda irin gyaran da tasha, har tausaya mishi takeyi saboda baya gajiya ko kaɗan, mantawa da komai yayi yarungumi Matarsa da 'yarsa saboda yanzu ta gyara *SHIMFID'AR TA* sosai.
kwanan ta biyu da komawa ta shirya zataje Meduguri, da k'yar ya barta ta tafi, badon Mahaifiyar sa tana tsak'a me wuya a da ya hak'ura da Fatima tunda ta masa nisa.
Ranar alhamis ta nufi garin Meduguri, isar dare tayi Allah ya taimaketa batasha wahalar gane gidan ba saboda ba ɓoyayyen mutum bane, gida kam a cike ta sameshi da alama wani hidima akeyi, wajen Ummi aka kaita, bayan sungaisa take ce mata "tambaya nakeyi, Fateema wanda suka zo daga Jos".
Da fara'a Ummi ta ce "nanne gidan, kinji labarin bikin ko, wlh abunne yazo a k'urarren lokaci shiyasa bamu barta taje ta sanar muku da kanta".
Maryam tayi murmushi tace "Kingane Fateemar kuwa, itafa wannan matar aure ce".
Ummi tace "aiyo to gaskiya inaga banan gidan bane, wancan sunce mana bazawarace shekara ɗaya mijin ya saketa....
Maryam ta ce "Ba ita bace amma ko zan iya ganin wannan ɗin".
"mezai hana, muje nakaiki wajen ta".
a gajiye Maryam tabi bayan Ummi, wani ɗaki duka nufa, ta wajen babu kowa kamar ba'a cikin gidan yakeba, wani hayak'i ake turara mata me k'amshin gaske, da sauri Maryam taje ta lek'a fuskan ta, sake baki tayi tana ganin ikon Allah, wannan kam Fateema ce, to wani aure zatayi kuma bacin Anwar yace mata ba sakinta yayi ba, kodai itama bata sanibane.
jin Muryar Ummi ne yasa Fateema ɗagowa, duk hayak'in yacika ɗakin, ido huɗu sukayi da Maryam, da gudu ta rungume ta tana cewa "kece Aunty, waye ya kawo ki, ashe baki manta dani ba, ina Babyn mu, me kika haifa...
"wannan tambayo yi haka Fateema, yanzu dai a gajiye nake".
Ummi tayi saurin cewa "muje ciki tunda kinga itace, idan sungama zata zo ta nemeki".
D'akin da Fateema take kwana aka kaita, abincin da aka kawo mata ta dira akai, saida ta k'oshi tabaiwa Aysha nono sannan tayi wanka tayi sallah ta mik'e, mamaki ne fal aranta, A haka Fateema ta shigo ta sameta, ko gaisawa basuyi ba tace "Fateema bangane ba, wai auren waye za'ayine?".
Bata ɓoye ba ta faɗa mata.
"to nidai kaina ya kulle, yanzu haka zuwa nayi na tafi dake, Anwaar ya ce bai sakeki ba".
"k'arya yakeƴyi aunty, har tagadda ta ya bani".
"ɗauko takaddar mugani, kun kulle mun kai".
m
jakarta ta ɗauko ta zazzage, takaddar tananan inda ta ajiye shi, ko warewa batayi ba ta mik'awa Maryam, warware wa tayi ta fara dubawa,
_Bazan sakeki ba Fateema, kije gida idan komai ya lafa zan ɗauko ki, ki kulamun da kanki sosai_
*SHAWARATA GAREKI*
_DUK WANI ABUNDA ZAKIYI KI TABBATAR KI. RIK'E ADDUA, BABU WANI ABUNDA ZAKIYI KISAMU KWANCIYAR HANKALI MATUK'AR KINA WASA DA IBADAR KI, AKWAI MAZA MASU TAURIN KAI KOME ZAKIYI BAZAKIGA FUSKABA, MAGANINSU KENAN ADDUA, KADA KIYI WASA KEDAI NEMI ALJANNAR KI TA GUDAN AURENKI_
.
.
Mik'awa Fateema takaddar tayi ta kasa magana, koda Fateema ta karanta zufane ya fara wanke ta, cikin ruɗu ta ce "Aunty wallahi ban karanta ba sai
yanzu".
Maryam ta ɓata rai ta ce "yanzu da kinyi aure akan aure fa? Yanzu tashi muje mu sanar musu basai gobe ba, nagode da Allah yakawoni kafin a ɗaura aure gobe".
Mik'ewa Maryam tayi tana mita, Fateema kam hawaye ne ya fara sauk'owa, don ita harga Allah yanzu tafison Ahmad, zama da kishiya ai sai dole, kuma tasan tunda abun ya kasance haka babu yanda za'ayi Anwar ya saketa, inama da anɗaura auren ace ta zaɓi wanda take so....
Maryam ne ta katse mata tunani, "to wai kukan me kikeyi"?
Fateema ta share hawaye tace "zauna Aunty, don Allah ki fahimce ni, ni yanzu bazan ɓoye miki ba banason Anwar Ahmad nake so, ki taimakamun ki k'ira Anwar ya sakeni yau ɗinnan basai kowa yaji ba, kinga zamuji daɗin zumunci dake".
Wani murmushi Maryam tayi ta ce "kina nufin bazaki koma ɗakin ki ba"?
Gyaɗa mata kai kawai tayi, Maryam batace mata komai ba ta ɗau wayarta ta k'ira Anwar.
"Maman Baby kin kasa bacci bana kusa ko, naga yanzu muka gama waya, ki tabbatar kun fito da asuba kada ku sake kwana fa".
Murmushi tayi ta ce "sarkin 'yan son kai, kace dai ka kasa bacci".
Dariya yayi ya ce "amma kin gane, sai juyi nakeyi wajen yayi mun faɗi, ina Fateemar bata naji muryar ta kafin ki kawomum ita".
"Gaskiya akwai matsala, gobe auren Fateema".
Wani wawan tsalle ya buga sai gashi a a zaune, "what? Da auren nawa akanta, sun haukace ne, wallahi duk wanda ya kuskura ya ɗaura aure da matana sai nasa an kulle shi".
Da sauri ta mik'awa Fateema wayar, ita duk jikin ta yayi sanyi, surutu yayi tayi baima san wayar a hannun Fateema yake ba, lokaci guda tausayi ya kamata, ji tayi tana son komawa gidan mijin ta, tsinke k'iran yayi duk ran maza ya ɓaci.
I
Kukan ma kasayi tayi, itadai Maryam ta zuba mata idanuwa ko k'iftawa batayi,
Anwar yana kashewa ya k'ira numban Bilal, saida yayi kusan tsink'ewa ya ɗaga, cikin magagin bacci ya ɗaga, "Anwar yayane"?
"Don Allah kazo yanzu akwai matsala".
Mutssuka ido Bilal yayi "matsala da darennan? Kabari gari ya waye mana".
Anwar ya marairai ce yace "bazaiyiyu ba, meduguri zamuje".
Bilal ya tuntsire da dariya "to kodai ka fara shan wani abune"?
Anwar yayi tsaki ya ce "kaifa ɗan air ne, ba abunda nasha".
Ganin Bilal zai ɓata masa lokaci yasa ya zayyane masa abunda yake faruwa, Bilal ya jinjina kai yace "ba zuwa zamuyi ba, abun me sauk'ine, kayi waya kafaɗa musu baka saki matarka ba, bawanda ya isa yayi aure akan aure, kaga sai su taho da Maryam ɗin kawai".
Anwar yayi na'am da hakan.
Bayan sun gama waya da Anwar, ta faki idon Maryam ta jero numbobin Ahmad ta fara k'ira, yana ɗauka ta fashe mishi da kuka, ruɗewa yayi yafara tambayar ta lafiya, kina inane?
"ina ɗaki".
Amsar da tabayar kenan ta katse kiran, Maryam ta ce "wa kika k'ira kuma, iyayenki ya kamata ki k'ira ki faɗa musu, kinga da safe sai mu wuce ko"?
Murmushi me ciwo tayi tace "bari yazo idan nafaɗa mishi sai yasanar da iyayenshi".
Kafin Maryam tayi magana Ahmad ya diro ɗakin, hankalin shi a tashe ya nufi Fateema, kusa da ita ya zauna ya ce "me yasaki kuka, kin ɗagamun hankali, ina fata lafiyar ki k'alau"?
Wani kukan ne yazo mata, ya sake ruɗewa ya ce "kiyi hak'uri ki faɗamun, kukan yana taɓamun zuciya da yawa".
Ganin tashin hankali a k'wayar idon shi yasa Maryam ta ce "kuka bazai fissheki ba Fateema, kifaɗa masa gaskiya kawai".
mik'a mishi takaddar Fateema tayi, batajira yagama karantawa ba ta ce "Ashe Anwar bai sakeni ba, wallahi ban buɗeba, kayi hak'ur.......
faɗuwar da Ahmad yayi ne yasa tayi shiru, gaba ɗaya hankalinsu ya tashi, da gudu Fateema tayi cikin gidan, batasan inda ta nufaba ma, kawai ganin ta tayi tashiga wani fankacecen falo, ashe sashin mahaifin Ahmad taje, da kuka tafara nuna mishi hanya tana cewa "Ahmad".
remot ɗin hanunshi ya ajiye ya ce "ina Ahmad ɗin, yanzu yabar nan".
dakyar ta iya cewa "ya faɗi, yana ɗakina".
Da sauri ya nufi ɗakin, Maryam sai safada marwa takeyi, tayi k'ololuwar ruɗewa, bata ɗauka zai ɗau abun da zafi hakaba, indai hakane Lallai shi yadace da Fateema ba Anwar ba, ɗagoshi yayi yafara hura masa iska a kunne, a hankali ya buɗe ido, ganin mahaifinshine yasa ya fashe da kuka, "Dad inason Fateema, ban taɓa so ba sai ita don Allah kafaɗa mata tadaina mun wannan wasan".
kanshi ya kulle ya dubi Fateema sai kuka takeyi, Maryam ne ta shaida masa abunda yake faruwa, murmushin manya yayi ya ce "haba Ahmad kamar ba namiji ba, ka godewa Allah da yasa angane kafin aure, yanzu dai maganar aure babu shi, kuma kada na sake jin ancemun kayi koda ciwon kai ne".
Kafin gari ya waye har itayen Fateema sunji wannan kwamacalan, 'yan biki kuwa da safe duk suka fara watsewa, kafin kace me zazzaɓi ya kama Fateema da Ahmad, ba k'aramin so Ahmad yakeyi wa Fateema, tanada shiga rai lokaci k'ank'ani, ta iya takunta sosai, abun duniya duk ya ishe gidan, Maryam dai ta kafe akan sai ta tafi da Fateema, Fateema ta kafe ita bazata komawa, ganin haka yasa ta shaidawa Anwar halin da ake ciki, shikam bai iya ɓacin rai ba, haushi ya kamashi, watau batason zama dashi, a tsawace yace abaiwa Fateema wayar, k'in karɓa tayi, ganin haka yasa Baba me yalo ya karɓi wayar akan zai bashi hak'uri, kafin yayi magana Anwar yafara zazzaga ɓacin ranshi, karshen furucin yace basai kin nunawa duniya sakinki nayiba saboda son zuciya, kiyi ta auren ki na SAKEKI saki UKU"....
Baba me yalo ya buga salati, yana faɗin assha, duk fa saida suka kaɗu harda Fateemar, Maryam ranta baisoba don tanason zama da Fateema sosai, tunanin ta ɗaya batasan wata irin kishiya za'a sake kawo mata ba, gashi taji ance maza idan suka ɗanɗani zama da mata biyu basu iya sake zama da ɗaya.
Aranar ta koma gida tabarsu da jimami.
Basai nabaku labarin irin murna da farincikin daya ziyarci Ahmad ba, duk da ance lokacin babu idda akan ta saida tasake sabon iddah.
watanni biyar tsak'ani aka ɗaura auren Fateema da Ahmad, tsantsan soyayya da k'warewa take nuna mishi a matsayin ta na bazawara, shikam ji yake kamar budurwa ya aura tunda dama baisan yaya budurwar takeba.
itakam Maryam tun daga lokacin ta rik'evmijin ta sosai, gyara kuwa tanayi ba kama k'afa, sai tazamto mace ɗaya tamkar dubu, tayi alk'awari bazata sake yin sake ayi mata kishiya ba, dak'yar suka shawo kan Alhaji ya yafewa Hajiya Jamila, yanzu nunawa Maryam so take sosai, kuma zumunci me k'arfi ya k'ullu tsakanin Maryam da Fateema.
Bayan shekara ɗaya Fateema ta haifo ɗanta na miji, Maryam kuma lokacin tanada ciki amma bansan wata nawa bane.
Wannan shine k'arshen *SHIMFID'AR MIJINA*
Wlh *SHIMFID'AR SA*
Yafi komai muhimmanci ki gyara kisha mamaki.
Taku akoda yaushe Priciss Aishat Aysm
Sai kuma ni dana kawo muku Abdullahi yahaya Saad (AYS) Nake cewa mu hadu a wani littafin
CALL or SMS
07066508080
.
Whatsapp
07066656752
bissalam
0 comments:
Post a Comment