MOTAR KWADAYI PART 11-15
.
Bayan k’wana biyu, Khaleel ya dawo, yaro ya aika, ya kira masa Ayshat. Dai- dai lokacin Malam ya fito, yaji ana cewa a kira Ayshat, Khaleel yana ganinsa, yarusuna ya gaida shi, Malam Yace”kaine ka aika Ayshat tazo?. Khaleel ya rusuna tare da sunkuyar da kai,” eh nine Baba. Malam ya kalesa sosai, yaron yana da nutsuwa, a tare da shi. Malam ya kaleshi Yace”ina fatan lafiya dai ko?. Khaleel ya k’ara rusunar da kai, “lafiyalau Baba, daman sai ya d’anyi shiru, Malam yace”ina jinka yaro, Khaleel ya sanar da Malam abunda ke tafe dashi. Malam ya ji dad’i kuma Allah ya tabbatar mana da alkairi. Bari na turo maka ita, Malam yana shiga cikin gida, d’akin Amina ya shiga, yana zama Ayshat ta gaida shi, Umma sanu da zuwa ta masa, ya amsa fiska sake, gyara zama yayi, ya kali Amina, a “hankali ya kira sunanta, ta amsa masa, nan ya fara bata hak’uri, akan abunda ke mata, murmushi tayi bakimai Malam. Nan ya fad’a mata mai son Aysha ne yazo, kuma ga dukkan alamu, yana da nutsuwa da hankali, na bashi daman yazo, su sasanta kansu, ina son kema ki cigaba da addu’a. Ta nisa “ba komai Malam Allah ya mana zabin alkairi, Umma tace”Mamana tashi kije ku gaisa, cikin jin kunya, ta d’au hijab d’inta ta fita. A zaure ta taras da shi, da sallama ta ‘karasa gurin, cikin fara’a ya amsa, sun gaisa tayi shiru, ta sunkuyar da kanta, a hankali ta d’ago, karaf suka had’a ido.
.
Wani lallausar murmushi ya sakar mata, ita ma murmushin tayi, cikin murya mai kama da rad’a, yace”my beauty kinyi kyau sosai. Ayshat bata san lokacin, da ta murmusa har saida, dimple d’inta suka lotsa. Suna haka saiga Safiya cikin Matsatsun kaya, tana taku dai-dai, tana shigowa zaure burki ta taka, ganin Ayshat na hira, hirar ma irin ta kauyawa, wanda basu wayeba, bata san lokacin da ta fashe da dariya, har tana rike cikinta. Inna tana jin dariyan Safiya, ta fito da sauri, ganin abunda Safiya ke ma dariya, yasa itama tafara, Malam dake d’aki jin dariya, yaki karewa suka fito shida Umma, yana zuwa zauren ganin, abunda sukayi masu Ayshat, tsawa ya dakamusu, Inna ta masa kalon uku saura kwata, suka tafi suna dariya. Malam hak’uri ya bama Khaleel, suka koma cikin gida. Sannu a hankali soyayya gamida sha’kuwa, suka shiga tsakanin Khaleel da Ayshat, harta kai magabata, sun shiga al’amarin, a tsayar da biki su, Aysha na kamala Secondary school, shi kuma yagama bautar kasansa sai ayi Aure. WAYE IBRHIM KHALEEL?. Ibrahim Khaleel, asalin iyayensa yan Yola ne, zamane ya kawo su garin Kaduna. Su uku ne a gun iyayensu, shine Babba sai kanwarsa, Hafsat dake aure a badarawa, sai autarsu wacce bata wuce 14yrs ba, Umma Halima itace mamansu, kuma ita kad’ai Malam ya aura, bai k’ara aure ba. Malam Kabir mutum ne mai kirki, yana sana’ar sai da kayan koli, duk da rashin k’arfin da ke dashi, hakan bai hanasa tsayawa, tsayin daka gurin ganin Khaleel yayi karatu, cikin ikon Allah ko da kunbiya-kunbiya, had’a har Khaleel ya kamala karatunsa, a fanni kasuwanci, yanzu haka yana bautar kasa. A cikin garin Kaduna, Khaleel yaro ne mai farin jini da kamala, shiyasa duk inda yaje, yana da mutane, kuma yana da hak’uri sosai. ……..
.
Safiya duniya ta, dawo musu sabuwa fill, tanzu naira ta zauna mata a hannu, ta mallaki filaye uku, ga gwala-gwalai, har d’aki Seema, ta bata a gidanta, tana kawo Maza suna bad’alansu, a gidansu kuwa ta gyara d’akinsu, harda kebe shashinsu, d’akinsu gwanin kyau, kulum Inna tana cikin gabaici ma Umma, amma ko kad’an bai dameta ba, Malam kuma ya zuba musu ido, kuma suma sun had’a da boka, sun rufe masa baki, baya iya cewa komai. Kamar kulum Safiya tayi wanka, wasu tsinanu riga da siket ta saka, don sunyi zasu had’u da wani Alhaji da suka had’u a Facebook, kuma babban d’an siyasa ne, yana da naira, sai da tagama shiryawa, tace”Inna zan d’anyi tafiya, zan kai kwana biyu. Kafin na dawo, don a kwai wani aikin da nake nima, nan take Inna ta washe baki, ah! To Allah ya bada sa’a.
.
Jakarta ta d’auka tasaka turarukanta da wasu magun-gunan mata da tsumi, harda na turawa, ta had’a ta fito cikin takama, tashiga Napep, tace”Mai Napep, zaka kaini, Asaa pyramid hotel, ok bada 500 muje ba matsala, sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso hotel d’in, kudinsa tabashi ta nufi cikin hotel d’in, d’akin mai lamba 10 ta shiga nan Alhaji zubairu yace ta sameshi. Da yamma Khaleel ya shirya, cikin shigan mutunci, yanufi gun gimbiyarsa, yaro ya aika bata dade ba, tafito, cikin shigan kamala, nan sukayi hira, yazo zai tafi ya mika mata yar laidan da yamata sayayya, k’in karb’a tayi, sai da yanuna b’acin ransa tasa hannu ta amsa, sukayi sallama, tana shiga gida, taba ma Umma kayan, ko da suka bud’e, Sabulu ne sinkin d’aya na wanka, sai man shafawa skin code cream da lotion, sai yar powder, da turare mind night forever. Duka sayyan bazai wuce, dubu d’aya zuwa dubu biyu ba. Umma godiya tayi sosai, ta nuna farincikinta, ni kam nace” uwar kwarai kenan masu son gaskiya, ba’abun duniya ba. Safiya a hankali ta kwan-kwasa qofar, yana daga ciki, Yace”yes come in, tun kafin tashiga, ta cire doguwar rigan, yazamana daga ita sai wani riganda bai kai iya cibiba, daga sama kuma bai rufe mata k’irji ba. Duk dukiyan fulaninta a waje, Siket d’inko shi, da babu duk d’ayane, don har ina iya hango, pant d’in jikinta kalar fari. Tana tura qofar d’akun wani d’an dattijo na gani, wanda sai dana tsorata, don yana d’aya daga cikin masu niman zabe, salon tafiyarta ta canza tana kwar-kwasa, ta iso kusa dashi, kan cinyansa ta zauna, cikin murmushi, Yace” my baby, gaskiya kinyi ban kuma tsamani haka zan ganki ba. Cikin mataudarin Murmushi, ta sak’ala hannuta, a wuyansa, tana masa yasa, da yatsanta a wuyan sa. Duk ya soma rikicewa, tsikan jikinsa yasoma tashi, a hankali ya soma kai hannusa kan west d’inta, yasoma wasa da su, nan ta soma rikita shi, da salonta kala-kala, kasa hak’uri yayi, hannusa ya kai kan… . ……
.
Duk wani iskanci su, da la’anan su, a falon sukayi, Alhaji yaji dad’i Safiya, abun ya mata yawa, ga kyau ga gamsarwa, Alhaji atake ya bata kyautar 150k, nan tana makale dashi, a hiransu take bashi labarin zuwanta, cikin yanayin damuwa, Yace”Baby kamarki ace kina shiga Napep, gaskiya baiyiba, cikin salon gogagu matan, da suke juya bariki a hannu, tace”yazanyi hakanake shiga. Ina dole na sai miki mota, matsawan zakina min yanda nake so, to baki da wata matsala. Nan take ta sauya salon zance, suka sha-shance, Safiya sai da tayi sati, kafin Alhaji ya mata shopping nagani na fad’a, ya kawota har qofar gida, ya ajiye ta, yayi mamakin ganin gidansu haka, sai da sukayi sallama, Yace”beb zan turo yaro na, ya fara koya miki mota, kafin in kin kware, a kawo miki motar ki. Cikin murna tayi hug d’insa, ta baa wani hut kiss, ta shige gida. Inna kam baki har kuni, yarta tasamu aiki, a cikin Abuja. Kwanan Safiya biyar da dawowa, driver ya fara koya mata mota, har ta soma ganewa, tafiya ne takama Alhaji na gaggawa, gashi waje zai fita baya son fita shi kad’ai. Waya ya kira yasanar da Safiya, ta shirya zasu fita waje, cike da murna da rawan kai, ta sanar da Innata, ana kiransu a gun aiki, tana tsammanin hala ma za’a fita da ita waje, haka ta shurya driver ya kaita Abuja. Kwanata biyi yamata ciku-cikun komai suka d’aga, sai Dubai. Ayshat kuwa har sun fara SSE, don haka Malam, ya fara shirye-shiryen biki. A bargaren Khaleel ko, sai kundun bala yakeyi, na had’a kayan akwati, ga garin ba kud’i. Kulum soyayyansu sai kara karuwa yakeyi, cikin ikon Allah, da kyar ya samu, ya had’a dan, abunda zai had’a. Safiya duniya tayi dad’i, idan alhaji baya nan, haka take fita cikin hotel d’in, harta saba da wasu yan 9ja. Sai da suka saba, ta soma janyosu zuwa room dinsu, har suka fara tambadewa. Suma suka kawo abokansu, Safiya ta kara wayewa, ga kud’in da ta tarasu. Satinsu uku, suka dawo 9ja, Alhaji da motarta, yasa aka rakota har gida, Toyota Camry 2015. Karkuso, kuga murna agun Inna, Malam kala bai iya cewa ba. Kwanan Safiya uku da dawowa, sai wadaka suke da naira, don ta samo musu kud’i. Yau Umma ta tashi da murna, za’a kawo kayan yarta, nan ta aika ma yan uwanta. Safiya har zata fita, ta fasa don kawai taga mai za’a kawo, Ayshat sun yi cake da mai kyau, tare da sayan, juice sua ajiye. Da yamma kusan k’arfe biyar, yan kawo kaya sukayi. Inna sai zuba ido suke, masu kawo kaya, suka shigo da akwati guda 2, Inna tana jiran, taga ko za’a karo wasu, amma shiru. Bayan sun gaisa, akayi addu’a tukun aka fara bud’e kaya. Ana d’agawa sun kirgawa, turmi goma da riga da sket ya mata, mai su Inna zasu in banda dariya, har suna hawaye, Umma ko ko ajikinta, don su albarkan aure suke so. Inna cikin wulakanci, ta kali Umma tasake kwashewa da dariya, tana nuna su da yatsa. …..
.
Sai da suka yi dariyan su, mai isarsu, Inna ta kali Umma tace”sai dai ta tafi a hakan kam, don irin wannan bak’in jinin a gado ne, ace akwati biyu turmi goma, ae tun zamanin baya aka bari, kuma duk talauci miji yanayin turmi ishirin a babu. A yi dai ma gani tunda a jini a gado, ta juya ta kali dangin ango tace”to su gayyan na ae gayyan siya, mu masu maik’o muke so, amma tunda yar ba farin jini da ita ba, ae an had’u da an dace, ta sa kai ta fita.
.
Umma kam kuka ta fara, danginta sai ba ma dangin ango hak’uri sukeyi, don basu so su tanka a gaban, dangin ango abun, bazaiyi kyau ba. Suma yan’uwan Khaleel hak’uri suka ba ma Umma, tukun suka tafi. Tun daga wannan ranan Inna da Safiya suka saka Umma gaba da habaici, kusan kulum sai tayi kuka. Safiya ta kware a tuka mota, yanzu ita take kai kanta ko ina. Ga rayuwan bariki data saka a gaba, kamar ba mutuwa, kud’i shigo mata suke ta ko ina, ana haka ran nan ta tashi da matsanacin ciwon kai, komai taci amai takeyi, ga zazzabi dake damunta. Seema ta kira tace tazo gida yanzu-yanzu, ba’a dad’e ba kuwa, sai ga Seema ta iso, ko da tazo d’aki suka shiga, Seema tace”Sofy ya naganki haka?. Sofy ta d’an ciza baki alamar jin-jiki, tace”Seema amai ke damuna ga tashin zuciya, sai yawan ciwon kai. Seema ta zaro ido! Tace”Sofy yaushe rabonki da kiga period d’inki?. Sai da tayi jim alamar tunani kafin ta nisa tace”inaga tun danayi kafin muyi tarayya da Alhajin abuja, kinga yanzu kusan 2 months da kwanaki. Seema tace”na wawo kenan ciki ya shige ki, kuma ayanzu bazaki iya cewa ga ubansa ba, don nasan bazaki iya k’irga mutanen da kikayi tarayya da suba. Nan take yan hanjin cikin Sofsy suka kad’a. “Seema yazanyi yanzu?. Bazan bar cikin nan ba, zai iya zama gori a garemu, da inna na, kuma ban shirya ajiye d’an shege ba. Seema tace”hakane but yanzu zamuje kiyi test in mun tabbatar sai mu wuce Abuja, dan dole mu tatiki Alhaji kud’i kafin a zubar. “Haka za’ayi kawa shiyasa nake son ki, kina da kaifin tunani mai kyau”. Seema tace”yanzu ki d’ibi yan kayan da zakisa kaman kala uku da fallen zani ki biyu, sai ki sanar da mama, yau sai mu wuce. Haka akayi tace”ma Inna ana nemansu a Abuja batun k’arin girma za’a basu, ya zama dole taje, Inna tace”Safiya da jikin kin haka?. “Eh Inna inaga acan Asibitin gun aikin zanga likita. “Ni Safiya naga duk yanayinki ya canza kin kara haske, sai d’an rama da kikayi. Sai da gaban Safiya ya bada dam! Cijin dauriya tace”Inna ina aiki kud’i na shigowa ae dole, Inna tace”aikam ko ni nan ae na canza har yar murjewa nayi. Murmushi Safiya tayi tace”mun wuce sai na dawo ko in na kiraki a waya”. Inna tace”Allah ya kare yasa ki samu babban matsayi”. Suna fita da Seema gidansu suka je, ta ibi yan kayanta itama, suka wuce gidan mai, saida sukayi full tank tukuna suka d’au hanyan abuja. Tafiyan awa biyu da rabi sukayi, suka shiga cikin garin Abuja. Sai da sukaje Hotel suka kama d’aki, bayan sunyi wanka sun huta, Sofy takira wayan Alhaji”ta tashaida masa, tashigo cikin Abuja”.
.
Da murna yace”zuwa ko sanarwa but ban yan mituna ina nan zuwa gunki”.salkama sukayi ta ajiye wayan, a ban garen Alhaji kuwa murnan sa yau zai kwashi gara, don yasan Safiya da bance cikin mata. Ko da ya iso Hotel d’in da suke har d’akin yaje, da murna tazo ta taresa, bayan sungama iya shegensu ta zauna a cinyansa. Sai a likacin ya lura da Seema, cikin girmamawa suka gaisa. Seema tace”barin baku guri tana zolayansu ta fiti haraban hotel d’in. Alhaji na ganin ta fita ya fara kissing d’in Sofy sai da yayi mai isarsa. tukun bayan sun lafa ta kaleshi cikin kirsa da shagwab’a, tace”Ya Alhaj ya aiki?. “Ya amsa da Alhamdulilah! Bacin kin hanani aiki kulum ina cikin tunanin ki. Murmushi tayi tace”ni da babyn ka muma muna tunaninka. Cikin kid’ima da rud’ewa, Yace”what? Mai kika ce?. Sai da tayi murmushi ta sake cewa”ni da Babyn ka munyi missing d’inka. “Wani baby kuma bayan ke?. “Babyn da ka ajiye min aciki na mana. “Alhaji kasani tun bayan da akayi min fyad’e, bansake tarayya da wani ba sai kai. “Haka zalika bacin kai bana tarayya da kowa, kwanaki da suka wuce duk muna tare, yanzu kimanin 2 months, banga period d’ina ba. “Kuma ni ban shirya haihuwa yanzu ba. “Ban shirya barin d’an titi ba a yanzu. “Don haka ina son inzubar da cikin nan. Wani sassayan ajiyar zuciya Alhaji ya sauke, tare da yar murmushi”nima ban yarda da barin shiba, don haka yanzu zan baki kud’i kuje acire, zan kula da jinyanki har ki warke, kuma ina son in kin warke za’amiki planning. Fari tayi da ido”haka za’ayi Alhaji. Sai da suka shek’e ayarsu tukun ya tafi, ya ajiye mata kud’i masu yawa, ya kuma biya musu kud’in 1month a hotel d’in. Sofy suka shiga niman Asibiti da za’a mata abortion, da kyar suka samu wani karanin Asibiti, hakan ma sai da Dr ya nimi had’in kanta, kafin ta yarda bayan ya biya bukatarsa. Ya yace su dawo washe gari, suka tafi suna murna. Washe gari suka d’auki duk abunda zasu d’auka suka nufi asibiti. ……
.
Da safe kuwa yanda naga, idon Ayshat ya yi ja, nasan ta niku ba kad’an ba. Khaleel ko sai tarairayata yakeyi, tamkar kwai. tundaga wannan rana suka shimfid’a soyayyansu, mai cike da burgewa, komai tare sukeyi, inka gansu gwanin ban sha’awa, Khaleel ta tattala matarsa, itama tana gudun abunda zai bata masa rai. Ayshat tayi kyau ta k’ara haske. Niko Rash “nace anya wannan ,haske haka na kalau ba”. Sannu a hankali rayuwa ke tafiya dad’i da ba dad’i, kayan garansu ya kare, randa inya samo musu mai maik’o suci. Randa in bai samu ba har garin kwaki suke ci, ko kad’an Ayshat bata taba nuna fushinta ba, kulum tana cikin masa, Addu’a da fatan alkairi. Safiyar yau ta tashi da zazzabi mai tsanani, ga jiri da ke d’ebanta. Hankalinsa ya tashi matuk’a, gashi ko si- si bai kwana dashi ba. Ko dayaje gidansu, yatarar da iyayensa, gari kwaki suke sha, ya gaida su Mamansa tace”Khaleel lafiya na ganka haka?. Cikin damuwa yace”Aysha ba lafiya kusan sati d’aya, gashi banda ki naira a hannuna. “Yasalama towo gashi muma haka muka wayi gari, amma ga wancan tv kaje ka sayar sai a samu a mata jinya. Tv ya d’auka yaje ya sayar dubu biyar da d’ari bakwai, sukaje asibiti a ka mata gwaji, likita ya tabbatar da tana d’auke da juna biyu, har na wata hud’u. Magunguna ya rubuta musu, sauran ya sai musu kayan abinci, rabi ya kaimusu, saura ya kai ma su Ummansa. Ko da Ayshat ta samu sauki, yace ta shirya, kaita gidansu ta gaida iyayenta, daga nan suka wuce gidansu Khaleel da murnan Umma ta tarbeta, tarinka ina zansaka dake.
.
Da daddare da zasu tafi, “Umma ta mata nasiha sosai, da takara hak’uri da yanda mijinta ke. Ayshat”tayi godiya ma Umma suka tafi. Khaleel result ya fito yayi kyau sosai, yanzu aiki ya dunkufa nema, kulum sai ya fita amma shiru, Ayshat ko kulum tana cikin masa addu’a da fatan alkairi. Safiya kam harka take ba sanya, ta maida bariki kamar rigan sakawanta, ko shakka babu, yanzu motanta biyu, kud’i kuma ta tarasu ba’a magana. Samarukanta na da duk ta canza, Abuja kuma ya dawo mata kamar gida. Kwanki sun ja, Aysha ta shiga watar haihuwanta, Khaleel ko kula ta musamman yake bata, yana tattala yar matansa. Safiyar yau ta tashi da nakuda, hankalin Khaleel ya tashi, mai napep ya nimo suka nufi asibiti, aka shiga da ita labour room, “addu’a yaketayi Allah ya sauketa lafiya. Wayarsa kiran nokia, irin mai tocin nan, ya kira Baban Aysha ya sanar ma, ya kira gidandu ma ya fad’a musu. Ayshat ta kasa haihuwa da kanta, likitoci sukazo suka sanar masa dole sai an mata tiyata. Ba k’arami min tashin hankali ya shiga ba, don kud’in da ya tara 8k ne, ana haka sai ga iyayensa, nan ya sanar musu, Malam yace”abasa ruwa a kofi da ruwa, murfin flaks aka miko masa, Addu’a ya yi, dake wanda suke kanta mudulmai ne, ba’a samu matsala ba, sukabata cikin ikon Allah ba’ayi minti biyar ba, ta zankad’o yaranta guda biyu, mace da na miji. Wayyo karkuga murna gun khaleel, bayan nurses sun gyarata, ta huta suka dawo gida. Yan’uwa da abokan arziki sai murna sukeyi, Khaleel daman ya sai ragonsa yana kiwo bai samu matsalaba, ana gobe sunane aka kirasa ne, fidelity bank suka kirasa, daman ya rubuta musu Application, ya samu aiki a gurin. Cikin murna ya zo gida ya sanar musu kowa sai murna yake masa. Ko ni Rash nayi murna sosai, gaskiya yan biyu sunzo da goshi.
0 comments:
Post a Comment