*UMMU AYMANA PART I*
.
.
Zahra Muhammad Mahmud
*Pure Moment of Life Writers (p.m.l)*
Ruga ce ta Fulani me d'auke da yawan jama'a Dan Rugar tana da girma sosai.
Wannan Rugar ba a ko ina take ba se a cikin Garin Gwongola,mutanan cikin wannan Ruga suna da al-adu kala-kala,kuma koda wasa basa sake da al-adun su Sun d'auki al-adun kamar ibada.
Malam Audu yana d'aya daga cikin mazauna rugar shida zuri"arsa gaba d'aya.
Malam Audu tsohone d'an kimanin shekaru 77 yana da mata d'aya Gwaggo Uwani da yara guda uku duka maza,Hamisu shine babba seme bimasa Shu'aibu,se k'aramin su Mahmoud wanda ake kira da Mudi.
Gaba D'ayan yaran na Malam Audu sunyi aure Sun hayayyafa ma kuma suna zaune tare dashi a Gida d'aya, shiyasa akewa Gidan kirari da Gidan gandu,gaba d'ayan su babu wanda yayi karatun Boko acikinsu dagasu har matansu sede na muhammadiyya sukayi.
Baba Hamisu kamar yadda yaransu ke kiransa,matarshi d'aya mesuna Saude, da yara guda hud'u,duka maza na farin sunanshi Jamilu,se Uwaisu,Nura,Usman.inna Saude macece mara mutunci ko kad'an bata ragawa duk wani mahaluki A cikin Gidan, shiyasa gaba d'aya Gidan kowa yake jin tsoronta harda shi kanshi Mijin nata yana under her control,be isa yayi abinda ba itace tasashi ba shiyasa kosu sirikan nata tsoronta sukeji, sabida gwanace gurin iya Bin bokaye da y'an bori.
Shu'aibu shima matarsa d'aya Furera da y'ay'a biyar biyu mata uku maza,Shafi'u shine babba se Muntari, se Hauwa,Ramatu,Suwaiba,Hauwa da Rahmatu sunyi aure tun tuni,sabida a al-adar Garin yarinya dole sede ta fara jinin al-ada a gidan mijinta, inko aka bari tafara a gidansu to ba makawa y'ar iskace,shiyasa daga shekara goma ake aurar dasu.Inna Furera irin matan nanne da ake cewa bakin ganga,munafukace ta ajin farko, tasan duk Wata hanya da zata bi ta hada mutum fad'a da Inna Saude sabida wannan halin natane ma yasa suke d'an d'asawa da ita Sauden.
Baba mudi ma matarsa d'aya me suna Zainabu da y'arsu guda d'aya me suna *UMMU AYMANA*.Zainabu Mace ce me sanyin Hali gata da hak'uri da kawaici,ko kad'an bata da d'aukar lamuranta da zafi,anashi b'angaran Baba mudi shima baya d'aukar rayuwa da zafi shima yanada hak'uri sosai da kawaici.
A al-adar Garin yara mata basa zuwa makarantar Boko, sabida acewarsu b'ata tarbiyya takeyi shiyasa kosu mazan basu d'auketa da muhimmanciba, sunfi maida hankali wajan neman kud'insu da kiwo da noma.
Baba Mudi yafi kowa rufin asiri a Gidan,dan a Rugarsu kaf babu me arzik'insa sabida d'an kasuwane, har fita yake zuwa wasu Garuruwan ya siyo kaya yazo ya siyar a rugar tasu,ganin hakane yasa mahaifinsa malam Audu k'ark'ashin jagorancin Inna Saude.ya d'oramasa nauyin ciyar da Gidan gaba d'aya da d'aukar d'awainiyar komai na Gidan, wannan hukunci beyiwa Mudi dad'iba,dan inde yaci gaba a haka wataran shima nashi k'arewa zasuyi Amman dayake shi mutum ne me kunya da kawaici Uwa Uba kuma biyayya,shiyasa ko a fuska be nuna yaji haushiba.
Tun daga wannan lokacin ko Maggi za'a siya sede a turo gurinshi,suko sauran y'an uwanshi sun mik'e k'afa basa komai sede ya je ya nemo ya kawo adafa suci, kuma ko godiya bazasuyi masa ba, sede ma su zageshi gaba d'aya haushin shi suke ji, hassada suke masa ba kad'anba.
Ummu Aymana tun tana jaririya yarinyace kyakkyawa,tana kama da mahaifiyarta sosai gata da hak'uri tun tana k'arama,wannan kyau da Allah yayiwa Ummu Aymana shine yajamata bak'in jini acikin Gidan nasu ko kad'an babu mesonta se Iyayanta,dan har kakan ninta tsoron kulata ma sukeyi sabida kar Saude taji haushi,shiyasa duk inda ta shiga kyarar ta akeyi acikin Gidan, sab'anin wajan Gidan kowa sonta yakeyi.
Ummu Aymana idonta irin blue eyes d'in nanne, hakanne yasa y'an gidansu suke kiranta da mayya, sabida acewarsu mayu ne kad'ai keda irin idonnata.har turaran mayu Inna Saude tasa adunga Yi a Gidan wai karta lashe musu kurwa.
Wannan al-amari yana k'ona ran iyayanta, sede basu da yadda zasuyi da Sauden sede su had'ata da Allah,kullum Inna Zainabu setayi kuka a d'aki gameda wulak'ancin da akema y'arta a Gidan.
.
Itama Ummu Aymana abun na damunta Amman kasancewarta yarinya shiyasa batasa abun a ranta ba kamar mahaifiyarta.
.
Itama Ummu Aymana abun na damunta Amman kasancewarta yarinya shiyasa batasa abun a ranta ba kamar mahaifiyarta.
Ko shi Baba Mudi sede ya dunga rarrashin Zainabu dan dole bawai dan shima abun be damunsa ba.
Haka suke rayuwa a cikin Gidan batare da cikakken y'enciba,komai se in Saude ce tace ayi sannan a keyi,ta kasa ta tsare.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah yanzu Umma Aymana shekarar ta Tara saura shekara d'aya a aurar da ita,ga maneman auranta ta ko'ina a cikin Garin kowa sonta yake,ita ko bata masan bidirin dasukeyi a kanta ba bare abin ya dameta.
Shi ko mahaifinta zuba ido yayi akan masu neman auran y'ar tashi, domin ya zab'o mata wanda zefi kulawa da ita, wanda har zuwa yanzu be samu ba,dan kowa ya duba se yaga yana da matsala.
Hakanne yasa y'an uwanshi suka fara gulmar sa, wai ya tsaya ruwan idone shi yasa yak'i zab'a mata mijin a cikin jerin masu zuwa neman auran nata,shide nashi ido tsakaninshi da su be cemusu k'ala.
Inna Saude ce zaune ita da Jameelu suna hira,kai da ganin yadda suka zauna suka natsu kasan zancan me muhimmanci ne, matsawa nayi dan inji me suke cewa.
"kai d'annan barifa kaji ingaya maka nifa ba yarinya bace nasan duk abinda nakeyi,dan haka nide umarni na baka, nace kafito neman auran Ummu Aymana ko kuma ranka ya b'aci".
Rai a b'ace Jameelu ya fara magana.
"Haba Inna so nawa zan fad'amiki ni hanne y'ar Gidan me unguwa nake so?kuma ita wannan d'in da kike so in aura meye hujjarki taso na aureta,?bayan ke ce kika cemana mayya ce.wato ni na aureta ta lasheni kenan ba damuwarki bace?".
Wata arniyar dariya Inna tayi sannan tace
"K'uruciya dangin hauka,wato bazaka fahimce ni ba sena maka bayani,to ba komaine yasa nace ka aureta ba sedan dukiyar mahaifinta, kaga da zaran ya mutu itace zata gajeshi mu kuma semu k'wace a hannunta cikin sauk'i ,Amman ana maka magana kana wani k'in amincewa, zancan maita kuma wannan hirace nice kawai na fad'i hakan dan a tsaneta badan wai mayyar bace ba".
Tunda Inna tasoma yimasa bayani bakinshi yak'i kulluwa gaba d'aya murna da farin cikine ya lullub'eshi cike da nishad'i ya mik'awa Inna hannu suka tafa sannan yace yana dariya.
"wato Inna shiyasa nake sonki, nayi imani da ace ba kece mahaifiyata ba da tuni rayuwata ta k'are a masallaci, Amman da yake nononki nasha ganinan ina abinda nakeso,gaskiya na gamsu da wannan shawarar taki kinga nima kwanannan za'a fara Kirana ina amsawa sabida kud'i sun zauna".
Dariya Inna tayi shima dariyar yake daga bisani yace yana mik'ewa tsaye alamar ze tafi.
"barima kiga naje na fad'awa Baba Mudin tun yanzu dan kar wani yamin shigar sauri"
"To maza d'an albarka ay dama da zafi-zafi ake dukan k'ota dan haka kaje kafad'a masa kuma nima anjima zan tara kowa na fad'a masu inga shegen da zece ba hakaba"
Ficewa Jameelu yayi fuskarshi d'auke da fara'a kai tsaye shashen su Baba Mudi ya nufa da yake Gidan shashi shashi ne.koda ya isa samun su yayi suna cin abinci ko sallama be yi musu ba ya samu guri ya zauna yana murmushi.
Baba Mudi ne ya lura maganace takawoshi dan haka tambayar shi yayi da cewa.
"Jameelu na Lura akwai magana a bakin ka dan haka ka sanar dani damuwar ka in ina da hali zan taimaka maka"
Wani murmushinne yasake kubcewa Jameelu najin dad'i, dan haka hankalinshi kwance yace.
"Baba dama bakomai bane illa iyaka inason auran Ummu Aymana"
Cikin tashin hankali Zainabu ta amshi zancan da cewa.
"Allah yayiwa y'ata tsari da samun mijin aure irinka,wlh bazaka tab'a samun ta ba matuk'ar ta jikina ta fito, wlh kasha k'arya daga kai har wacce ta turoka,in Ummu Aymana ta aureka tace ta auri wa?mazinaci,d'an giya,koko barawo,kokuma me wasa da sallah azumi senaga dama? Wlh tun wuri kasa wa ranka hak'uri dan wlh bazaka auri Ummu Aymanaba"
Tak'arasa zancan tana huci wanda ba Baba Mudi ba shi kanshi Jameelu mamakin hakan yakeyi dan basu tab'a tunanin zatayi magana ba.
cikin fushi shima Baba Mudi yafara magana.
"Wlh Jameelu duk da munanan halayanka yau da ace kaine dan ra'ayin kanka ka fito kace kana sonta wlh zan aura maka ita Allah ze shiryeka a hankali. to Amman yanzu nasan turoka Saude tayi tunda inda sak'on naka ne da kajima da shaidamin damuwarka, dan haka wlh bazan Aura maka Ummu ba sede duk abinda ze faru ya faru dan haka katashi ka b'acemin da gani"
Cikin azababben fushi Jameelu ya fara magana cikin muryarsu ta k'auraye.
"Ayyade Alhaji da Hajiya ay shi rikicin duniya Dame rai ake yinshi dan haka ku kwantar da hankalinku shi kunu labarin wuta yake ji shiko tsire zahiri ya gani mu zuba ni da ku".
Yana gama magana ya sa kanshi yabar shashin nasu zuciyarsa na k'una.
Suko basuyi mamakin d'ibar albarka da Jameelu ya musu ba sabida inda sabo Sun saba abinda yafi hakama tsaf ze iya.
Suko basuyi mamakin d'ibar albarka da Jameelu ya musu ba sabida inda sabo Sun saba abinda yafi hakama tsaf ze iya.
Sabida Jameelu ba ya jin magana,sata a gurinshi ko b'era albarka,gashi fasik'ine neman mata a gurinshi kamar masifa,sallah ko se yayi sati guda bekai goshinshi k'asa ba,haka shima lokacin azumi ba kullum yake yiba se.yaga dama.
wannan kenan
.
Bayan fitar Jameelu Zainabu kuka tasa ta fara magana.
.
Bayan fitar Jameelu Zainabu kuka tasa ta fara magana.
"Wlh Malam hak'urina ya k'are, bazan tab'a zuba ido ina kallon zalincin da ake son yiwa Ummu ba wlh,sede duk abinda ze faru ya faru Amman wlh bazan yarda ba".
Ta k'arasa zancan cikin kuka.
Cikin sigar rarrashi Baba Mudi yace.
"Haba Zainabu yaya da hankalinki zaki maida kanki yarinya?cemiki aka yi nima zan amince da wannan had'in gambizar? ay kinsan nima ba yarda zanyi ba, Ummu y'ar muce dole mu tashi mu kare mutuncinta dan haka kisa ranki a inuwa nima ban amince ba kuma se iya inda k'arfina ya k'are matuk'ar ina raye wlh".
Murmushin jin dad'i ne ya bayyana akan fuskar Zainabu.
Dariya Baba Mudi yayi sannan yace.
"Oh Allah ya kawomu zamani wai Zainabu ce take kuka akan kar a cutar mata da y'a,wacce da kina kallo zata fad'i ba zaki tare ta ba dan kunyar y'ar fari".
Ya k'arasa zancan cikin sigar tsokana.
Rufe fuska tayi tana dariya daga bisani ta mik'e da gudu ta shige d'aki,dariyar shima yayi sannan ya bita d'akin.
Shi ko Jameelu daga fitarsa d'akin mahaifiyarsa ya nufa cikin fushi,yana shiga ya fara zage-zage,da kyar Inna Saude ta samu yay shiru ya fad'a mata abinda ya faru,ay bata kai gajin k'arshen bayanin ba tayi kukan kura ta fito tsakar Gidan ta fara bala'i.
"Yau za'a yi bala'i a Gidan nan, dan wlh yau sena ga uban da ya tsaya muku da har zaku iskanta min Yaro da raina ban mutu ba".
Ay ilahirin mutanan Gidan kan kace me kowa ya taru a gabanta Amman banda Iyayen Ummu Aymana.
Da kyar Malam Audu ya samu tayi musu bayanin abinda ya faru.
"In banda su tsinannu ne taya dan Jameelu yace yana son y'arsu zasu hana shi sannan kuma harda rakiyar zagi da tsinuwa,to wlh bazan yarda ba dole Jameelu ya Aureta ko suna so ko basa so".
Muryar Baba Mudi ne ya katse ta.
"kinsha k'arya wlh kin kwana da yunwa, babu wanda ya isa ya had'a Aure tsakanin Ummu da Jameelu matuk'ar nine mahaifinta kuma ina Raye to wlh ke baki isa ba".
inji Baba Mudi da yake k'ok'arin k'arasowa gurin shida Zainabu.
Mamaki ne ya kama kowa dake gurin ganin ba halin shi bane.
Inna Saude cike da bala'i taci gaba da magana.
"lalle mudi wuyanka ya isa yanka har ina fad'a kana fad'a,to wlh kataka a sannu niba kanwar lasa bace,dan haka umarni ne na bada dole Jameelu ya Auri Ummu Aymana wlh".
Inna Zainabu ce ta amshi zancan.
"Tunda ke kika haifa mana ita ba,to wlh baki isa ba,kibar ganin ina miki shuru to wlh shuru ba tsoro bane gudun magana ce,Amman yanzu tunda kika shigo hurumin da ba naki ba dole kiji magana wlh"
Inna Furera ce tasoma magana.
"Amman Zainabu baki da kunya yanzu har Yaya Saude tana magana kina bata amsa? wlh baki kyauta ba".
"kyale ta Furera so take ta nunamin ta haifi y'a d'aya kamar mayya, waya sanima ko itace ta cinye sauran kwayayan haihuwar?".
Inji Saude ta fad'i tana hararar Zainabu.
"Mun godewa Allah daya bamu y'a D'ayan da kike tada jijiyar wiya akan an hana D'anki Auran ta,da baki hangi mamora a tattare da ita ba da bazaki so Jameelun ya Aura ba".
Zainabu ta bata amsa.
Zainabu ta bata amsa.
Nande sukai ta fad'i in fad'a bame saurarawa wani,abun na Saude har mamaki ya dunga basu sabida k'arfin halinta nason yin iko akan abinda bata da iko dashi.
Da kyar malam Audu ya samu sararin yin magana.
"Wannan ba abin rigima bane Jameelu da Ummu Aymana duk abu d'aya ne, dan haka Gida be k'oshi ba ba za'a kaiwa na waje ba,tunda ya ganta kuma yace yana so to ko ba makawa se anyi wannan Auran".
Kuka Zainabu tasa tabar gurin,shi ko Mudi tsayawa yayi ya fuskanci Mahaifinshi yace.
"Baba y'ay'a amana ce Allah ya bamu kuma ze tambayemu game da amanar ranar gobe k'iyama,shi ya mana umarnin mu aurar dasu ga mazaje na gari, dan haka bazan yimaka biyayya akan wannan son zuciyar taka ba. Auran Ummu Aymana da Jameelu wlh baze yiwu ba Baba,sabida ba dan Allah suke son hada auran,ba ka gafarceni Baba yau zan bar maka Gidan ka da Garin ma baki d'aya nida Iyalina, na gaji da wannan zaman bautawa wannan tsinanniyar matar da batasan darajar kowa ba a Gidan nan".
Ya k'arasa zancan yana nuna Saude.
Malam Audu shuru yayi yana nazari akan zancan Mudi wanda yasan tabbas gaskiya ya fad'i.
Ita ko Saude ashar ta shiga surfawa Mudi gami da shan alwashin aurawa Jameelu Ummu Aymana ta k'arfin tsiya.
tsoro ne ya kama sauran y'an uwan nashi jin yace zebar Gidan, wanda Sun sani insuka barshi yatafi Sun kad'e dan haka dole ayiwa tufka hanci.
.
Sannu a hankali kowa na gurin ya watse,itama Inna Saude dole ta koma d'akinta sabida wanda zatayi bala'in dasu suma sun bar gurin.
Sannu a hankali kowa na gurin ya watse,itama Inna Saude dole ta koma d'akinta sabida wanda zatayi bala'in dasu suma sun bar gurin.
Baba Hamisu da Baba Shu'aibu ne suka keb'e a k'ofar gida suna tattauna yadda zasu shawo kan Mudi yafasa tafiyar.
"Shu'aibu nasani base ka sake maimaitamin ba,tabbas Saude ce taja komai,Amman ya kamata ka fahimta, Saude ba niba ma da nake Mijinta su Malam kansu tsoronta suke ji bata da dad'in sha'ani wlh".
Baba Hamisu ya fad'a cikin sigar dake nuna abun na damunshi.
"Yaya inaga wannan ba abun tada hankali bane, kamata yayi kaje ka sameta ku fahimci juna ka gano dalilinta nason Jameelu ya Auri Ummu Aymana inaga shine kawai,to kaga idan ka gano se kasan yadda zaka yi kaja ra'ayinta akan tabar maganar zuwa wani lokacin inaga zefi"
Shu'aibu ya fad'i yana kallon Yayan nasa.
Shurune ya biyo baya na y'an mintuna kana daga bisani Baba Hamisu yace.
"Wannan shawarar taka tayi dan haka Bari inje in sameta dan mu shawo kan matsalar da wuri".
yana kaiwa k'arshen maganar ya mik'e ya shige cikin Gidan.
Shima Shu'aibu barin gurin yayi.
Koda Baba Hamisu ya iske Saude a d'akinta har lokacin bata dena zage zage ba,jiki a sanyaye yayi sallama ya shiga d'akin.
Bata amsa sallamar ba,shima kuma be damu ba ya sami guri ya zauna yana kallonta, yana tunanin ta ina ze faro mata zancan daya kawoshi, muryar tace ta katse shi da cewa.
"Kai nifa bana son munafurci,daga ganinka akwai abinda kake son sanar dani Amman tsohon munafurcinka ya hana ka fad'amin dan haka kayi gaggawar sanar dani abinda ya kawoka kokuma katashi ka bani guri namijin hotiho kawai".
Jikinshi har rawa yake ya fara magana cike da tsoro.
"Ranki ya dad'e dama akan maganar d'azune, koni na goyi bayan Jameelu ya Auri Ummu Aymana,to matsalar anan shine kinji Ubanta yace zasu bar Gidan wanda in aka bari hakan ta faru kinga bazamu sami damar had'a Auran ba shine nazo na shawarce ki".
Ya k'arasa zancan cikin matsanancin tsoro sabida besan yadda zata d'auki maganar ba.
Ita ko shuru tayi tana nazari akan batun nashi, tabbas in suka bar Gidan burinta baze cikaba dan haka cike da gamsuwa da bayanin nasa tace.
"Haka ne Hamisu to Amman taya ya kake ganin zamu shawo kan matsalar?Dan ni da cewa nayima zan kaisu gurin Boka na kan tudu yayimin maganinsu".
Sosai yaji dad'in yadda ta bashi damar shiga zancan dan haka cike da kwarin guiwa yace mata.
"ki ajiye batun Boka a gefe kibari mu basu dama in sunk'i amincewa to seki je gurin Bokan asan abinyi,Amman yanzu so nake nasan aynihin dalilin ki nason had'a Auran dan musan hanyar dazamu bi".
Ba tare da tsoron komai ba tace "Sabida dukiyar Mudi Ta dawo hannun Jameelu".
Baba Hamisu beyi mamakin zancan ba dan dama baya raba d'ayan biyu akan hakanne ta tada hankalin Gidan..
"Wannan tunani ne me kyau kikayi,to ki kwantar da hankalinki yanzu kibar maganar Auran sesun saki jiki akan maganar ta kwanta lokacin mu kuma mun gama shirya duk abinda ya dace mu shirya semu sake d'ago da maganar".
Wata uwar shewa Saude ta saki dake nuna alamar taji dad'in batun na Mijin nata.
"Gaskiya nagode da wannan shawara kuma zanyi amfani da ita Allah kuma yabamu Sa'a".
Amsawa yayi da "Ameen"
Anasu B'angaran Zainabu da Mudi kuwa tun komawarsu shashinsu Zainabu take kuka kamar Ranta ze fita akan hukuncin da sirikin ta ya zartar akan gudar y'ar ta, Mudi ne yayi k'ok'arin kwantar mata da Hankali da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki, wlh Ummu bazata auri Jameelu ba matuk'ar ina raye, kuma ko bayan Raina in kika bari Ta Aureshi ban yafe miki ba,dan haka na yanke shawarar gobe da asubar fari zani tasha in samo mota ta kwashe mana kayanmu mubar musu Garin gaba d'aya dan akan Ummu zan iya salwantar da farin cikina domin nata, dan haka kisa ranki a inuwa Mijin Umma kamili natsatstse nanan zuwa da yardar Allah".
Dan dad'i Zainabu bata san sanda ta rungume Mudi ba tana masa godiya.
Daga nan had'a kayansu suka shiga yi Dan asubanci zasu yi shiyasa suka fara shirin tun yanzu.
.
Da magarib bayan Sun fito masallaci da sauri su Baba Hamisu suka tsaida Mudi a k'ofar Gida.
Da magarib bayan Sun fito masallaci da sauri su Baba Hamisu suka tsaida Mudi a k'ofar Gida.
Ba walwala A fuskarsa ya fara dubansu yace.
"Lafiya de ko kuka tsaida ni?".
Da sauri Baba Hamisu ya fara magana.
"Mudi tabbas mun san abinda aka yi maka ba'a kyauta ba kuma itama Sauden naje na sameta na nuna mata bata kyauta ba kuma ta fahimce ni dan yanzu haka Ta janye maganar Auran,dan haka Don Allah kayi hak'uri ka janye zancan barin Gidan nan"
Shu'aibu ne ya k'ara da cewa.
"Kuma Mudi in kabar Gidan nan zumuncin mu lalacewa zeyi, Yaran mu ba zasu san junansu ba, dan haka Don Allah tunda itama Yaya Saude ta janye zancan Auran Don Allah kaima ka janye zancan tafiyar".
Kallo kawai Mudi ya bisu dashi,dan yasan halin Saude farin sani bata fad'in abu ta dawo ta janye,dan haka kad'a kanshi kawai yayi sannan yace.
"To naji kuma nagode Amman yanzu bazan yanke hukunci ba se nayi shawara da med'akina tukuna in yaso daga baya shawarar damuka yanke zaku ganta,in mun yarda mu zauna zaku ga mun zauna in bamu yarda ba zaku ga mun tafi,dan haka kuyafemu duka sabida halin rayuwa".
Gaba d'aya jikinsu ne yayi sanyi da batun na Mudi amma basu da zab'in daya wuce suyi fatan alkha'iri,dan haka suka had'a baki gurin fad'in.
"To Allah ya tabbatar mana da alkha'iri Amman de ka duba maganar da idon basira".
Murmushi ya musu ya shige cikin Gidan.
Suma Gidan suka shiga jiki a sanyaye .
Koda Mudi ya yiwa Zainabu bayani akan abinda su Shu'aibu suka tare sa suna fad'amasa fafur tak'i amincewa dasu ci gaba da zama a Gidan, dan harda kukanta ita de subar Gidan, dan haka dole Mudi ya amince dasu bar Gidan shine masalaha.
Da daddare da misalin k'arfe takwas na dare Mudi yaje yiwa Mahaifansa sallama sabida asubanci zasu yi.
Koda ya musu bayanin abinda ke tafe dashi kuka Inna tasa akan bata amince ba in kuma ya tafi to bata yafe mishi shayar dashi da tayi ba.
Hankalin Mudi in yayi dubu ya tashi, rasa inda zesa kansa yayi koda yayi yunk'urin bata hak'uri mik'ewa tayi sannan tace.
"Wlh matuk'ar kabar Gidan nan bada yawuna ba Allah ya isa ban yafe maka nono na daka shaba har abada".
Tana kaiwa nan a zancan tayi shigewarta d'akinta,ta barshi shida Malam Audu.
Shima Mahaifinsa cewa yayi in yabar Gidan to ya tabbata su ya Bari ba Gidan ba.
Dan bak'in ciki Mudi har kuka yayi,haka ya baro b'angaran Iyayan nasa ya nufi nasu.
Koda shigarshi zainabu tsorata tayi da yanayin sa dan haka jiki a sanyaye ta tambayeshi abinda ya faru, be b'oye mata komai ba ya sanar da ita,itama kukan tasa daga bisani ta share hawayenta ta mik'e ta fara maida kayayyakin su mazaunin su.
Cikin k'ank'ani lokaci komai yayi tsaf,sannan taje ta kawo musu abinci suka ci,shi de K'ara rarrashinta yake tayi.
murmushi kawai tayi tace,"haba Malam ay dole na taya ka yiwa mahaifanka biyayya, in ban taya ka ba waye ze taya ka?Dan haka ka dena ma bani hak'uri, Allah yasa hakan shine alkha'iri".
*Bayan Wata Shida*
Tsawon wa'innan watannin ba'a sake d'ago da zancan Aure tsakanin Ummu Aymana da Jameelu ba se yau.
Saude ce ke zubar da ruwan bala'i a tsakar Gidan tana fad'in, "wlh nagaji dayin shuru yau ko sede ayi wacce za'a yi, in ko aka hana Jameelu Auran Ummu, to wlh zan bashi damar fita yak'in neman Auran ta koda kuwa da kaifin takobin shine tunda abun ba mutunci".
Sosai maganganun nata suka firgita Zainabu dan tasan kashe Mutum a gurin Jameelu tamkar kashe kiyashine,shi yasa duk tabi ta firgita gashi acikin daji suke ko hukumar Y'an sanda babu a gurin bare su d'auki mataki.
Shiko Mudi ko a jikinshi maganar bata dameshi ba harkokinsa kawai yake yi, abinda ya sanide shine Y'a tashice Ba kuma wanda ya isa ya sashi Aurar da ita ga Wanda be dace ba.
KANA TARE DA NI?
0 comments:
Post a Comment