*UMMU AYMANA PART 2*
Koda dare yayi su Baba Shu'aibu ne suka sake zuwa gurin Mudi akan zancan Auran.
Kai tsaye yace musu.
"Ni bazan Aurawa Ummu Jameelu ba sabida be dace da ita ba, kuma wlh babu Wanda ya isa yasani yin abinda be dace ba".
Ko sauraron su be sake yi ba ya tashi ya barsu a gurin.
Gaba d'ayan su Ransu ya b'aci, dan haka daga gurinshi kai tsaye gurin Inna Saude suka nufa,suna zuwa suka kwashe k'arya da gaskiya suka fad'a mata.
Ga mamakinsu se kawai tayi murmushi tace musu, "ku kwantar da hankalinku,aure kamar anyi shi angama, ayni bana magana ta tashi a banza,inde na furta sena tabbatar, dan haka ku tashi kubani guri zanyi nazari".
Cike da mamakinta suka bar gurin.
Dare ya tsala sasoi baka jin motsin komai sena Shanun da Awakin da suke Gidan,kasancewar duk wani Bil Adama dake Garin ma yayi bacci,dan Dare ne sosai misalin k'arfe biyu na dare.
Jameelu na hango d'auke da wata sharb'eb'iyar wuk'a fuskarshi b'oye cikin rawani,ya nufi b'angaran Baba Mudi, koda ya haura ta katanga kai tsaye D'akin da suke kwana ya nufa.yana shiga be b'ata lokaci ba ya samu Dede zuciyar Mudin ya Burma masa wannan wuk'a wacce sabida kaifinta seda ta tsago jikinshi ta caki katifar da yake kwance.
Nishi me k'arfin da Mudi ya saki shine ya farkar da Zainabu daga bacci, da sauri ta kunna cocila dan ganin meke faruwa, hakan yayi dede da lokacin da rawanin da Jameelu ya rufe fuskarsa dashi ya kwance.
A razane Zainabu ta furta.
"Jameelu me ya kawo ka D'akin mu a dede wannan lokacin? me kake nema? Ko kayi makuwa....."maganarce ta mak'ale a mak'oshin ta sanda tayi arba da sharb'eb'iyar wuk'a soke a k'irjin mijnta jini se ambaliya yake.
Wata razananniyar k'ara ta Saki ta fad'i k'asa sumammiya, shi ko Jameelu jikinshi na rawa ya fice daga b'angaran, kai tsaye D'akin Mahaifiyar shi ya nufa.
Da yake tasan da zuwanshi k'ofar a bud'e take kuma bata bar Baba Hamisu ya kwana a D'akin ba, dan haka da shigar Jameelu da sauri ta tare shi tana tambayarsa
Cikin matsanancin tsoro ya bata labarin ya kashe Mudi Amman Zainabu ta ganshi wanda sanadin hakan gata can ma a sume.
Wani murmushi na mugunta Saude tayi sannan tace .
"Ka kwantar da hankalin ka,kasa a ranka cewa ka kashe banza, ay ka godewa Allah daya baka jarumar Uwa me zurfin tunani,ay sanin da nayi za'a iya samun matsala gurin aywatar da aykin shiyasa na amso kan ta kwana a gurin Boka na kan tudu, dan haka yanzu zanyi Maganin komai".
Tana gama fad'in haka ta bankad'a katifar ta ta d'auko wani abu da wata k'aramar wuk'a ta fice daga D'akin ta nufi Garken Shanun Gidan wanda suke mallakin Baba Mudi ne,shi de Jameelu bin ta kawai yake da ido dan gaba d'aya ya gama tsorata.
Tana zuwa rami ta hak'a da Wata Wuk'a dake hannunta tana gama hak'awa ta d'auko wasu tarkace a wani Jan kyalle ta saka a cikin ramin Tana Kiran sunan Zainabu, seda Ta Kira so bakwai Amman a hankali sannan ta rufe ramin da kyallan a ciki,da sauri suka koma d'akinta gudun kar wani ya Gansu.
Tunda suka koma D'akin in banda dariya ba abinda suke yi sabida ta shaidawa Jameelu manufar abinda Ta burne, ashe asirine ta yiwa Zainabu wanda ita da hankali sede wani Ikon Allah ma'ana ta haukata ta hauka me tsanani.
Acan kuwa b'angaran su Zainabu,tana nan kwance a sume kamar a mintsineta se kawai ta farka, tana farkawa ta fara soshe soshe tana cire duk wata sutura ta jikinta,seda tayiwa kanta tsirara sannan ta shiga tik'a rawa akan gawar Mijin nata.
.
Haka Ta kwana akan gawar Mudi tana chashewa ba tare da damuwar komai ba.
Da gari ya waye Dariyar Zainabu ce ta farkar da Ummu Aymana Wacce take ta faman shirgar baccinta,koda ta farka mamaki take na ganin mahaifiyar tata tsirara, Amman abunka da yarinta seta rufe idonta wai gudun kar Umman tata tace ta kalleta idon nata a rufe tace.
"Umma zaninki ya kwance ki d'auka kisa zan wucene".
Dariya Zainabu ta sake fashewa da ita cikin haukanta ta cewa Umma Aymana.
"kajimin tsinanniyar mata! uban waye yace miki tsirara nake?dan Kan ubanki duk tulin kayan dake jikina baki gansu ba da har kike cewa nasa zani ayko yau se naci uwarki".
Tana gama maganar ta diro daga kan gawar Mudi,tasa hannu ta finciko wuk'ar da aka sokawa Mudin ta nufi Ummu Aymana da mahaukacin gudu, ganin hakane yasa Ummu ta kwasa da gudu zuwa tsakar Gidan su inda kowa ya fito yana harkokin gabansa harda Inna Saude wacce bame cewa ta aykata wani abu mummuna duba da yadda hankalinta yake kwance.
Da gudu Ummu tayi cikinsu tun kamin suyi wani yunk'uri Zainabu itama ta fito rik'e da wuk'ar da aka kashe Mudi wacce take d'igar da jini.
Hankali atashe suka mik'e kowa ya nemi gurin b'uya da kyar su Uwaisu suka murd'eta suka amshi wuk'ar,itako se dariya take tana fad'in.
"Kisan gilla zanyi tunda na koya na iya".
Abun d'aurewa kowa kai yayi Inna Saude ce fuska d'auke da damuwa da yanayi na tausayawa kamar gaske tace.
"Ikon Allah Zainabu ciwon haukane Kuma ya kamata,watak'ila ma yanzu ne abun ya sameta bayan Mudi ya tafi masallaci".
Baba Shu'aibu ne ya katseta da cewa.
"Ay yau Mudi ya makara dan ko masallacin be jeba sede ko in asubancin tafiya kasuwa yayi".
Ummu Aymana wacce ke b'oye a bayan Inna uwani ce tace.
"Ba kasuwa yaje ba dazan fito naga suna wasa da Umma na ta haye kanshi tana rawa, shi kuma yana kwance a kan Gado".
Da sauri suka nufi d'akin abunda suka gani ba k'aramin firgita su yayi ba,su duk a tunaninsu Zainabu ce Ta kashe Mudi bayan ta sami tab'in hankali sannan Kuma ta biyo Ummu Aymana itama zata kashe.
Cikin jimami suka Fara y'an koke koken su na munafurci wanda zahirin gaskiya murna suke giwa ta fad'i zasuci nama.
Cin k'ank'anin lokaci gari ya gama d'auka Zainabu ta kashe mijinta kuma tana neman kashe y'arta a sakamakon haukacewa da tayi.
Ayko jama'a se zuwa kallo sukeyi,haka mutanan Gidan suka bar Zainabu ba Kaya kowa yazo haka ze ganta tsirara,tana ta surutai.
Ummu Aymana ko kuka kawai takeyi gwanin tausayi,abunka da farar fata tuni har tayi ja sabida kuka,kowa yazo seya tausaya mata,haka aka yiwa Mudi wanka aka sallaceshi aka kaishi makwancinshi, ita kuma Zainabu aka kwashe kayan D'akin tas sannan aka sata a ciki aka mata tirke kamar Wata Akuya aka d'aureta kuma har zuwa lokacin basu suturtata ba.
Haka akai Ta zaman makoki har zuwa lokacin da akayi rabon Gado inda sabida da zalinci Ummu Aymana da mahaifiyarta, suka tashi da Saniya daya da Raguna guda biyu acikin Shanu sama da d'ari biyu da Raguna sama da guda hamsin iya gadon da suka samu kenan,sauran ko harda su Saude a cikin jerin magada inda kasonta yafi na kowa yawa dan ko Furera Shanu biyu aka bata.Koda aka ba Ummu Aymana nasu bata damu ba dan bata san me hakan ke nufi ba.
Duniya sabuwa ta dawo a Gidan kowa ya samu dukiya se walawa yake yi, sab'anin Ummu da Umman ta kullum tana mak'ale da ita tana kuka gashi ko abinci ba'a ba Umman tata wai a cewar su mahaukata basa cin abinci a k'oshe suke,shiyasa a cikin nata wanda ake bata seta k'i ci ta kawowa Umman nata ga mamakinta seta ga ta cinye tas tana neman k'ari.
Kullum Ummu cikin tausayawa mahaifiyarta take kasancewar Zainabu ba Y'ar Garin bace Y'ar Asalin jihar Adamawa ce shiyasa babu wani nata daya san abinda ke faruwa, shiyasa Ummu ke tausayawa mahaifiyar tata.
Kwanci tashi rayuwa tayi tsanani garesu dan yanzu ko lomar abinci babu me basu sede tafita bara tasamo ta kawowa mahaifiyar tata,gashi babu Wanda yatab'a yunk'urin nemawa Umman tata magani, d'an Gadon nasu ma wayar gari tayi taga babu su a tirken da suke kwana, koda ta tambaya cewa akayi barayine suka sace haka dole ta hak'ura.
Yanzu D'akin da suke kwana tsutsotsine ke yawo ko ina sabida Umman ta tunda aka d'aureta tsawon wata shida koda wasa basu tab'a kwanceta ba a gurin take kashi take fitsari,Ummu Aymana kuma bazata iya gyara mata ba kuma tayi iya yinta ta kwanceta Amman ta Kasa, gashi daga alamu Umman tata bata da lafiya dan ta lura cikin Umman nata se motsi yake gashi lokaci zuwa lokaci cikin na k'ara girma.
Ta rasa wanda zata fad'awa sede tai tayiwa Umman nata Addu'a akan Allah ya bata Lafiya.
Abinda Ummu bata saniba tun kamin rasuwar Mudi, Zainabu ke d'auke da ciki na Wata biyu wanda ko ita kanta batasan tana dashi ba bare wani na Gidan.
*Bayan watanni biyu*
Ummu Aymana ta dawo daga barar abinda zasuci kwatsam Ta sami mahaifiyarta a cikin wani mummunan hali na ciwo gaba d'aya ta fita hayyacinta,a gigice Ummu taje cikin Gidan neman suzo su taimaki Umman ta Amman ba Wanda ya kulata dan Saude asiri tayiwa kowa na Gidan akan ya tsani su ummun.
Ganin bame Taimako ne yasa takoma gurin Umman tata kamar wasa ta Fara kwance igiyar da aka d'aureta kawai se gani tayi ta kwantu.
Kamar jira tana kwanceta umman tata ta kama hannunta ta rik'e da k'arfi tana kuka me tsuma zuciya gami da wani nishi me k'arfin gaske,kwatsam Ummu Aymana se ganin Jariri tayi ya fad'o yana tsala kuka.
A gigice ta kwace hannunta daga ruk'on da Umman nata tayi mata ta matsa gefe jikinta na rawa kamar mazari, ita ko Umman D'an na fad'owa ta koma ta kwanta tana maida numfashi sabida ta wahala..
Shi ko Jaririn in banda kuka ba abinda yake yi ga shi kwance cikin kashi tsutsa ta Fara bin jikinshi,tausayin Yaron ne yasa Ummu Aymana d'auko wankakken zani tazo ta d'aukeshi ta lullub'eshi bayan ta cire tsutsar da ke binshi ayko take yanke yaron yayi shuru.
Ajiye yaron tayi akan shimfid'a tafita tsakar Gidan tace Umman ta ta Haihu.
Ay ila hirin Gidan ba wanda be razana dajin zancan ba,da sauri suka nufi D'akin kowa yana toshe hanci, abinda suka gani shine ya firgitasu wato Yaron babu ta inda ya baro kamannin Mahaifinshi, hakan ke nuna Dan Mudin ne, kuma hakan na nufin Gadon da suka ci na Mahaifinsa sesun dawo dashi ma'ana de ya koresu daga cikin Magadan Baban shi.
Ko cibiya basu ji tausayi Sun yanke masa ba haka suka baro D'akin cike da zullumi akan in suka Bari duniya taji labarin haihuwar D'a Namijin da Zainabu tayi,sun bani.
Ummu ko tasa Yaron tayi tana kallo k'aunarshi na ratsa zuciyarta, ita ko Zainabu bacci kawai takeyi na huce gajiya.
Ummu naso Ta goya yaron Amman wannan mahaifar da zaranta sun hanata yin hakan, kuma taga intaja da niyar ta cire Yaron kuka yake duk da a hankali take jan, kawai seta yanke shawarar ta rage masa tsawonta zefi kawai dan haka Reza ta d'auko sabuwa tazo ta yanke cibiyar,tana yankewa se taga jini na zubowa da sauri ta sami bakin d'an kwalinta ta yanka ta d'aure masa sosai seda taga jinin ya dena zuba sannan hankalinta ya kwanta.
Goya shi tayi tafita yin Icce dan tana tsoron ajiye shi Ummanta ta dukar mata shi,da yake tasa hijab kowa yaganta da goyo d'auka yake y'ar tsanace haka har ta isa daji tayo itacen ta dawo gida,had'a wuta tayi ta d'orawa Ummanta ruwan wanka dan ita gani take yanzu Ummanta ta warke zata iya yin wanka,seda ruwan ya tafasa ta kwashe a bokiti sannan ta nufi D'akin domin tashin mahaifiyarta ta a bacci tazo tayi wanka.
Abunda ta gani shi ya firgitata wato ba Umman nata a Dakin ba alamarta, Da gudu ta fita waje tana dubawa nanma ba ita, seda tayi tafiya me nisa goye da yaron a bayanta tana neman Ummanta Amman bata ganta ba kowa ta tambaya sede yace yaga tawuce da gudu ba kaya a jikinta.
haka Ummu Aymana tagaji ta dawo Gida tana kuka tana addu'ar Allah yadawo mata da Ummanta lfy.
Ruwan Data dafa domin Ummanta shi ta juye a baho ta tsunduma yaron a. ciki ta fara yi masa wanka abun ba k'aramin mamaki ya bani ba ganin yadda take masa wankan kamar wata uwar mata,amman dana tuno wayo da dabara irin na bafulatanin mutum kuma mazaunin k'auye se abin yadena bani mamaki ya koma burgeni.
tsaf tamasa wanka shiko se kuka yakeyi na alamar yaji dad'in wankan.
Duk abinda takeyi gani take yanzu Ummanta zata dawo dan haka guri tasamu a gefe ta kwantar da yaron bayan tashafa mishi man kadai ta lullubeshi da zannuwa guda biyu,seta shiga gyara D'akin dan kar Ummanta Ta dawo taga bata gyara ba.
Ummu akwai juriyar ayki kamin lokaci me tsayi ta gama gyara D'akin fess bame cewa shine me tsutsa sede warine har lokacin be dena ba, d'aukar yaron tayi suka shiga D'akin suna jiran dawowar Umman su.
.
Ummu Aymana tana nan zaune har dare yayi amnan Umman ta bata dawo ba kuma a lokacinne Yaron ya fara kuka wanda ko ba'a faɗa ba yunwa yake ji.
Hankalin ummu ne ya tashi tarasa yadda zatayi dashi gashi bame taimaka mata ay kawai itama seta fashe da kukan.
Rarrashin shi ta shigayi tana bashi ruwa a hankali bacci ya ɗauke shi be sake farkawa ba se wajan ƙarfe ɗaya na dare,Ummu rasa abin yi tayi ay kawai wata shawarace ra faɗo mata,miƙewa tayi ta ɗauƙi ƙoƙo ta nufi garken Shanun Gidan,tana zuwa ta samu me shayarwa a cikinsu ta tatsi Nononta da yake a ɗaure take bata mata komai ba.
Da sauri ta koma ɗaki tasa cokali ta dunga ɗiba tana bashi ay kamar jira yake,take Ya kama sha bada wasa ba,ci gaba tayi da bashi har seda ya fara turoshi waje inta bashi hakan ne yasa ta gane ya ƙoshine,rufewa tayi ta cire mishi zannuwan data rufa mishi ɗazu sabida yayi kashi a ciki.
Wasu ta ɗauko ta rufa masa bayan ta goge mishi kashin,Allah sarki bawan Allah ay jin cikinshi ya ɗauka se bacci,itama baccin tayi cike da kewar Ummanta.
Washe gari da safe tayi masa wanka ta goyashi tasa hijab ta fita barar abinda zata ci bata dawo ba se Azahar,tana zuwa ragowar Nonon jiya data rufe shi ta ɗauko taba Ƙanin nata yasha ya ƙoshi ya koma bacci.
Haka ta dunga ɗawainiya da ƙanin nata har tsawon kwanaki biyar,kuma dama tun bayan rasuwar mahaifinta Inna Saude bata sake zancan Auranta da Jameelu ba sabida dama dukiya sukewa kuma sun samu.
Gaba ɗaya sun gama tsaida shawarar kashe yaron ko kuma salwantar dashi,amman basuyi shawarar dasu Malan Audu ba su eh su sukayi shiyasa su Malan Audu basu da masaniya.
Jameelu aka wakilta akan kashe yaron kuma ya amince ze aywatar.
Da daddare misalin ƙarfe goma na dare yaron cikinshi ya fara ciwo gashi cikin ya kumbura, hakane yasa tsoro ya kama Ummu ta kwantar dashi ta nufi gurin Inna Saude domin ta faɗamata ko zata taimaka mata.
Tana zuwa ƙofar Ɗakin abinda taji ne yasa takasa ƙarasawa cikin Ɗakin,muryar Saude ta jiyo tana ba Jameelu umarni akan yaje yanzu ya kasheta ita da Ƙaninta kuma ya tabbatar ya musu irin kisan da yawa Mahaifinsu.
A gigice Ummu ta baro gurin jikinta se ɓari yake yi har faɗuwa take gurin gudu, a haka ta ƙaraso Ɗakin nasu tana zuwa ta sungumi Ƙanin ta dake ta faman kuka sabida ciwon da cikin shi ke masa ko hijabinta bata saba tafice da mahaukacin gudu daga Gidan.
Tana fita ba jimawa Jameelu ya shiga Ɗakin domin aywatar da mugun nufin shi sede yayi rashin sa'a domin sunbar Gidan.
Da sauri ya fito yabi bayan su dan ya fahimci basu jima da fita ba.
Ita ko Ummu gudu take irin na ceton Rai rungume da Ƙanin nata shiko se kuka yakeyi,Garin lokacin damina ne dan haka hadarine baƙiƙirin a sama Ruwa gab yake da sauka.
Ganin hadarin sosai hankalin Ummu ya tashi amman hakan be hanata cigaba da gudunba musammam data fahimci kamar anbiyo sawun su,a haka har ta shiga ƙurgummin Dajin Garin bata dena gudunba.
Shigarsu Dajin keda wuya Ruwa ya kece kamar da bakin ƙwarya harda ƙanƙara,amman hakan be hana baiwar Allah Ummu Aymana ci gaba da gudu ba duk da cewa ko gabanta bata gani sabida tsananin duhun dajin.
Ci gaba tayi da gudun har takai dede inda tagaza ci gaba da gudun dan tana zuwa dede gurin taji kamar an riƙe mata ƙafa tayi tayi ta ɗaga ƙafarta amman abun yaci tura hakanne yasa ta durƙushe a gurin tana kuka tana roƙon Allah akan ya kawo musu agaji,gashi daga ita har ƙanin nata ruwa ya musu shegen duka wanda hakanne yaja ƙanin nata ya suma sabida wahala.
Tana nan durƙushe ruwa na dukansu taji wani abu me santsi yana bin jikinta hannu takai tana shafawa dan ta gasgata tunaninta ilai kuwa abinda take zargine wato *Maciji*
.
Runtse idonta tayi taci gaba da shafa micijin har zuwa sanda tazo dede kanshi da sauri ta shaƙi wuyan macijin sede ga mamakinta seji tayi babu komai a hannunta.
Da sauri ta buɗe idonta abun da tagani shine yayi matuƙar bata mamaki gami da farin ciki,umman ta tagani zaune akan wata kujera ta alfarma cikin shiga ta alfarma tana mata dariya.
Da gudu ummu ta miƙe ta ƙarasa gurinta tana kukan murnar ganinta,tana zuwa rungumeta rayi ita kuma tasa hannu ta amshi yaron dake hannun ummun.
Ga mamakin ummun ruwan da akeyi yadena sauka akansu sannan gurin ya wadata da haske tamkar rana,koda ummu takai dubanta gaba ƙaton kogin garinsu ta hanga wanda da ace taci gaba da gudun da takeyi ba makawa ciki zata faɗa dasu.
Gidiya tayiwa Allah sannan takai dubanta gurin ummanta wacce tun ɗazu inbanda murmushi ba abinda tace mata,cike da murna ummu tace.
"Ummana da badan Allah ya taimakemu kinzoba da tuni mun mutu dan Allah tunda kinji sauƙi kar ki kuma cire kayanki kuma yaronki se kuka yakeyi".
Murmushi umman kawai tayi sannan ta kamo hannun ummun ta zaunar da ita akan cinyarta,zamanta keda wuya se ganinsu tayi ita da ƙanin nata a wata bukkar kara ga wani abinci me rai da lafiya se kuma madara me kyau itama,kuma abinda ya bata mamaki shine ita de da tasan darene yanzu kuma safiyace kuma tana jin ƙarar motoci daga inda take.
Ta duba ko ina bata ga umman tasu ba ƙanin ta kuma gashi cikin ƙoshin lfy harda kayan sanyi a jikinshi,se ɗaga ƙafa sama yake yi yasa hannunshi a baki yana tsotsa.
Lokacinne ummu ta gama yarda Allah ne ya turo wannan aljana ta taimakesu dan ko shakka batayi da aljana ta haɗu,godiya ta sake yiwa Allah sannan taja kwanon abincin batare da tunanin komaiba ta kama ci har ta cinye tasha ruwa,shima ƙaninta madarar ta bashi amman yaƙi amsa alamar a ƙoshe yake ,daukarshi tayi sede ga mamakinta tana ɗagashi se taga ashe akan kuɗi yake kwance ƴan dubu dubu guda goma da sauri tasa hannu ta ɗauki kuɗin ta ƙulle,a zaninta sannan ta goya ƙanin nata ta fito daga cikin bukkar.
Koda ta fito se taga ashe a bakin titi suke motoci se wucewa sukeyi.abun sosai ya bata mamaki kuma daɗin daɗawa titin ba irin na garinsu bane,ƙara ɗaure ƙaninta tayi a baya da kyau ta saka hijab ɗin da tagani a rumfar ba me cewa ɗane a bayan nata kasancewar tana da girman jiki duk da cewa shekaranta goma sha ɗaya lokacin.
Ƙarasawa tayi bakin titin se ta hango wata tasha daga can gaba kaɗan dan haka can ta nufa,tana zuwa taga motoci da mutane a ciki ita kuma gashi batajin yaran hausa bare ta fahimci inda kawai wata mota da taga ta kusa cika ita taje ta shiga itama, dama mutum ɗaya suke jira tana shiga akazo karɓar kuɗin mota,Ayko ansha fama kamin ta fahimci yawan kuɗin da zata bada sabida kaf gurin bame fahimtar yaranta itama kuma bata fahimtar nasu ,a cikin kuɗin da aljana ta bar musu ta bada kuɗin motar,sannan direba yajasu suka tafi inda ummu batasan inda zasu ba.
Tafiya suke amman taƙi ƙarewa Ummu har gajiya tayi da zama ga ƙaninta se ƴan koke koke yakeyi, sakkoshi tayi ta rungume ta bashi madarar da yaƙi sha a bukkar nan dan taho mishi ds ita tayi dan tasan ze buƙata anjima, Jama'ar cikin motar se mamaki suke daga ƙarshe se suka dena sabida kama ta jini da suka gani se duka suka ɗauka ɗantane sabida sunsan fulani da auran wuri.
Basu isa inda zasu ba se cikin dare gaba ɗaya Ummu ta gama gajiya,haka suka iso tashar garin da suka zo kowa ya sauka itama saukar tayi tasake goya ƙaninta a baya ta lulluɓeshi da hijab,cikin tashar ta shiga tana ta waige waige wanda kowa yaganta yasan ƴar ƙauye ce.
Ganin bata gane kan tashar bane yasa ta fito ta bi wani titi me yawan hasken fitulun kan titi abin yayi matuƙar burgeta, nan ta shagala da kallon fitulun har dare ya tsala bata sani ba,ci gaba tayi da tafiya a ƙafa har ta iso wani guri me yawan mata sanye cikin shiga ta zubar da mutunci duk,wani me tsoron Allah in ya musu kallo ɗaya baze ƙaraba sabida tufar dake jikinsu ita da babu duk ɗaya.
Kasancewar Ummu batasan meye karuwanci ba shiyasa ta ɗauki shigar tasu a matsayin al-adar Garin, haka taita binsu da kallo,yayin da gefe ɗaya kuma motoci ne na alfarma ke fakawa suna ɗaukarsu.
Can ɗan nesa dasu taje ta zauna tana ci gaba da kallon ikon Allah, tanason fahimto abinda hakan ke nufi,dan ita de taga kamar masu motar wacce tafi fitar da surarta suke ɗauka, hakanne yasa Ummu fahimtar ashe al-adar Garin me kyauce tunda masu kuɗin garin ma masu irin shigar suke taimakawa,FCT ABUJA KENAN
take taji itama tanason kasancewa ɗaya daga cikin matan da ake ɗauka a motocin,domin a taimaka musu,waige waige ta farayi na inda zata hango inda ake siyar da irin kayan dan ta siya itama
Carab idonta ya hango mata wani boutique daga can nesa dasu kaɗan, ayko da sauri ta miƙe ta nufi gurin domin siyan irin tufar da ta gani a jikin waincan matan.
.
Gudu gudu sauri sauri Ummu take yi har ta ƙarasa boutique ɗin.
Da sallamarta ta shiga,da yake ba musulmai bane ba wanda ya amsa mata,sema binta da ido da sukayi azatonsu ma mahaukaciyace.
Ido Ummu tashiga warewa tana kallon kayan dake ciki,can ta hangi wata riga ayko seta musu magana da fulatanci akan tanason rigar,ayko gaba ɗayansu suka kwashe mata da dariya,dan basu san me tace ba.
Wata sassanyar murya taji daga bayanta cikin harshen fulatanci tana mata magana,da sauri Ummu ta waiga inda ta jiyo muryar,wata kyakykyawar budurwa ajin farko ta gani zaune akan kujera tana mata murmushi.
Sosai Ummu taji daɗin ganinta sabida itama sanye take cikin irin shigar,dan inba idon Ummu bane yay mata ƙarya ba, to da tace shigar wannan budurwa tafi ta kowacce acikinsu muni, dan kayan dake jikinta daga kan na shanunta se gabanta kawai suka rufe amman sauran jikin duk ana gani.
Cikin harshen filatanci budurwar tacewa Ummu.
"Ƙanwata me ya fito dake da daddare haka?sannan waccan Rigar da kikeson siya me zakiyi da ita? ko ke matar aurece?".
Idon Ummu ne ya kawo ruwa sharewa tayi sannan tace.
"Ni ba anan nake ba mota na hau kawai ta kawoni nan,kuma ni ba matar aure bace,inaso in siya ne in saka inyi kamar yadda kikayi sabida nima masu motocin can da suke taimaka muku nima su taimakamin".
Ta ƙarasa zancan cikin kuka.
Dariyace ta ƙwacewa wannan budurwa cikin dariyar tayiwa sauran na shagon bayanin da Ummu tai mata ayko suma gaba ɗaya dariyar suka sa, sun jima suna dariya sannan sukayi shuru.
Budurwarce taci gaba da magana.
"Ƙanwata ay ko kin siyi Rigar bazata miki kyau ba sabida ke yarinyace baki da cikar halittar da Rigar zata miki kyau,sannan wa'incan da kike kallo ba taimakonsu ake yiba kasuwace in masu motar suka zo wacce ta musu ita suke siya seta shiga su tafi,dan haka ko kinsa kinje bazasu zaɓe kiba".
Abunka da bafulatanin mutum ay gaba ɗaya tsorone ya kama Ummu najin cewa siyan matan dake gurin akeyi.
Budurwarce tace.
"ya sunanki ?"
"Ummu Aymana"
"Da kyau,ni kuma sunana Husna,amman anan kowa da Ƴarfillo yake kirana,ni ƴar Garin Yola ce karatu ne ya kawoni nan Garin".
Ido Ummu ta bita dashi kawai dan bata jin zata faɗa mata daga inda ta fito.
Ƴarfillo ce taci gaba da cewa.
"Ban taɓa yin taimako ba a rayuwata amma yau na tsinci kaina da son taimaka miki,sede kuma ni ba yanzu zan tafi Gida ba, dan nazo gwada sa'a tane nan,akwai wani ɗan sarki da yake wucewa tanan duk bayan wata uku,to sometimes yana tsayawa anan ya ɗauki wacce zata tayashi kwana dan baya iya bacci seda mace a kusa dashi, to na jima ina zuwa amman ban taɓa sa'ar ganinshi ba, sabida ina zuwa a makare shiyasa yau na fito da wuri,dan haka kimana addu'a Allah yasa ya zaɓeni in ya zaɓeni kema zakiji daɗi dan zan ba wata ƙawata ke ta kaiki Gidana seki dunga yimin shara da gyaran Gida ina biyanki".
Farin cikine ya bayyana akan fuskar Ummu da sauri tace mata.
"Allah yasa ya zaɓe ki in kuma ya zaɓeki Allah yasa daga kanki ya gama zaɓar wata kuma har abada".
Jin daɗin addu'ar da Ummu tamatane yasa ta rungume Ummun sede tudun goyon da taji a bayan tane yasa tayi saurin sakinta gami da ɗaga hijab ɗin Ummun,Jaririne yake ta faman shan baccin shi hankali kwance.
"Ummu Aymana Jaririn waye a bayanki?".
Cikin kuka Ummu tace.
"Ƙanina ne".
"Ƙaninki kamar ya?ina Mamanki take da zata barki ki fito mata da Yaro?".
Kwashe labarinta tayi kaf ta sanar da Ƴarfillo amman bata faɗa mata sunan Garinsu ba.
Sosai Ƴarfillo ta tausayawa Ummu da Ƙaninta dan har kuka seda tayi,gyarawa Ummu goyon tayi da kyau suna cikin hakane suka jiyo ƙarar motoci alamar Ɗansarkin yazo, da sauri Ƴarfillo taja hannun Ummu suka nufi gurin dandazon karuwan.
Duk inda ƴarfillo ta wuce sede kiji ana tsaki badan komaiba sedan tafisu kyau da haɗuwa,zuwansu gurin ba jimawa tawagar Ɗansarkin ta ƙaraso, nanfa mata aka shiga gyarawa ko za'a dace.
Motocine guda biyar huɗu iri ɗaya se ɗaya daban,guda huɗun baƙaƙene Range Rover new model se ɗayar kuma fara Bugatti.duka baƙin glass ne ajikin motocin,suna ƙarasowa gurin parking sukayi ba kuma wanda ya fito,zuwa can se wani mutum ya fito a ɗaya daga cikin baƙaƙen motocin kai tsaye inda su Ummu suke tsaye ya nufa,yana zuwa gurin ƴarfillo yaje yace mata.
"you are lucky, yallaɓai yace ki biyoni".
Yana gama magana ya juya ya tafi,Ƴarfillo wata shewa tayi yayin da sauran karuwan suke jin haushinta hannu Ummu taja zuwa gurin Shema'u Duniya ƙawarta, tana zuwa cikin sauri tace.
"Don Allah ki kaita Gidana gobe zan miki manni inna dawo".
Bata jira amsar ta ba tajuya tanufi motocin Ɗansarkin, tun kamin ta ƙaraso wani ya fito ya buɗe mata bayan motar da Ɗansarkin yake ciki ta shiga ya kulle suka ja motocin suka bar gurin.
Shema'u Duniya Ranta a ɓace taja hannun Ummu suka nufi Gidan Ƴarfilon, ta kai Ummu Gidanne badan komai ba sedan tasan Ƴarfillo bata ƙaramar kyauta.
Suna zuwa Gidan tayiwa Maigadi bayani shi ya buɗewa Ummu ƙofar falon ta shiga ita kuma Shema'u Duniya ta juya ta wuce.
0 comments:
Post a Comment