*UMMU AYMANA PART 3*
Shiga cikin falon tayi ta nemi guri ta zauna tana kalle kalle alamun ƙauyanci,kwanto ƙaninta tayi a baya wanda shima ya tashi daga bacci yanason abinci amman hasken daya gani ya hanashi yin kuka sede turo harshe waje da yake yi.
Kwantar dashi tayi tafara neman inda zata ga abinci ko ruwa,a tsorace take zaga gidan har Allah ya kaita dinning area,tsyawa tayi tana kallon kulolin dake jere kan dinning ɗin batasan ko menene amfaninsu ba amman haka kawai taji tana shaawar ganin meye a cikinsu.
Ƙarasa tayi gurin hannu tasa da niyar ɗagawa se kawai taga ta buɗe dayake baa kulle ba ande kawai ɗora murfinne,ganin abincine aciki Ummu batasan sanda dariya ta ƙwace mataba ɗauko kular tayi gaba ɗayanta ta dawo falon ta zauna.
Har zata soma cin abincin se ta tuno da ƙaninta fasa ci tayi ta miƙe ta koma inda ta ɗauko kular dubawa tayi tsgani ko zata sami abun bashi,flaks ɗin data gani akan table ɗin ta ɗauka jin shi da tayi da nauyine yasa ta fara kici-kicin buɗeshi har de Allah ya bata saa ta buɗe,murfin flaks ɗin ta tara sannan ta,juyo abinda ke cikin flaks ɗin,damammiyar costard ne tasha madara amman dayake Ummu batasan ko meye ba ɗan dangwalowa tayi a hannunta ta ɗanɗana jin ɗanɗanonta ne yasa ta amince ƙaninta ze iya sha batare data cutar dashiba.
komawa tayi gurinshi ta ɗaukeshi tafara bashi ayko bawan Allah jin,sabon ɗanɗano ay tuni ya buɗe baki yana amsa,bata ƙyale shiba seda ta fahimci ya ƙoshi sannan ta kwantar dashi itama taci abincin ta ɗanɗanon da taji har addu'a tayi akan Allah ya bata irinshi a Aljanna,tana gama cin abincin tafara neman gurin alwala amman bata ganiba haka ta haƙura ta dawo falon ta rungumi ƙaninta tana tunanin inda Allah kuma ya jehosu.anan bacci yay awon gaba da ita da Ƙanin nata.
Ƴarfillo.
shigar ta motar keda wuya taji wani sassanyan ƙamshi wanda bata taɓa jin irinshi ba,dubanta takai gun Ɗansarkin wanda ke kwance a lungun kujerar motar yana latsa wayarshi,bata iya ganin fuskarshi sabida rufe take cikin rawani idonshi ma sanye yake cikin baƙin glass,maana hannunshi kawai take iya gani.
matsawa tayi kusa dashi ga mamakinta se taga ya ɗaga mata hannu alamar dakatarwa batare daya kalli inda takeba,jiki a sanyaye ta koma gefenta ta zauna cike da mamakin wannan bawan Allah,dan ita de tasan duk cikakken ɗan barikin daya ɗauketa tun,a mota yake fara wasanni da ita amman taga wannan ko kallo bata isheshi ba.
Basu ɗauki wani lokaci me tsayiba suka iso guest house ɗinshi,faɗin haɗuwa da tsarin gidan ze ɗaukemu tsawon lokaci bamu gama ba.
Koda suka isa ƙofar Ɗansarkin aka fara buɗewa yafita,seda ya jima da fita sannan aka buɗewa Ƴarfillo ƙofa ta fice itama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar ɗansarkinne yamata jagora zuwa ɗakin dayake,amman kamin su barta ta shiga seda suka amshi wayarta da jakarta sannan sukayi serching ɗinta sosai suka tabbatar daga ita se kayan jikinta take sannan suka bata izinin shiga,shigar ta ɗakin seda kanta ya kusa juyewa sabida tsabar haɗuwar ɗakin,ga wani ƙamshi na musamman dake tashi a ɗaki dubanta takai kan doguwar kujerar dake ɗakin,jikake tim ƴarfillo ta faɗi ƙasa badan komaiba sedan kyau da cikar zati da tagani atattare da wanda yake zaune akan kujerar,wanda ko baa faɗa mata ba tasan shine Ɗansarkin.
Shiko ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana ƙare mata kallo,sanye yake cikin singlet da wando three quater duka farare,gashin kanshi baƙi kwance akanshi,farine sosai gashi da dogon hanci daya dace da tsarin fuskarshi,koya ya motsa bakinshi beauty point ɗinshi seya fito,gamida haɗaɗɗiyar wushiryarshi wacce ta ƙarawa bakinshi kyau,yana da tsawo da faɗi jikinshi a murɗe yake alamar dake nuna maabocin training ne shi,fuskarshi kuma zagaye take da saje wanda ys kwanta lub a fuskar tashi.
Ƴarfillo jiki na ɓari tamiƙe tsaye gaba ɗaya se taga ta raina kanta duk kyan da take taƙama dashi sabida taga wanda ya fita.
Wani arnen murmushi Ɗansarkin ya saki sannan ya motsa bakinshi da niyyar magana kamar wanda aka yiwa dole.
"A tsarina in anyi checking ɗinki a waje in kin shigo gurina nima inayin nawa dan haka ki cire kayan jikin ki yanzu dan inga irin hajar dana ɗauko danni ko gado bana hawa senayi checking ɗin dan haka ina jiranki".
Tunda ƴarfillo take yawon karuwancinta bata taɓa haɗuwa da irinshiba,bata da zaɓin daya wuce tayi abinda ya buƙata,cire kayanta tayi haihuwar uwarta ta tsaya a gabanshi,shi kuma yana ta kallonta daga ƙarshe de seda yasata ta ɗaga har ƙafofinta yasa hannunsa a ........yaji yanayin matsewarta. seda ya duba komai wato general check off sannan ya miƙe ya isa kan gado yamata nuni data biyoshi.
.
Ƙarasawa ƴarfillo tayi kan gadon cikin takunta me ɗaukar hankali,tana hawa yareema ya ruƙota ya shiga ɓatar mata da tunani wanda tunda take bata taɓa haɗuwa da wani namiji dayasan kan hanya irin shiba.
Cigaba yayi da wasa da ita irin wasan da zamuce ko a gidan aure ba kowane yake sakin jiki yayi shiba,ƴarfillo takai matakin da bazata iya cigaba da amsar wasannin nashi ba burinta kawai yayi abinda yasa ya ɗaukota,ga mamakinta kuma shi yaƙi cire kayan jikinshi duk,abunda yake mata da kayanshi a jikinshi.
Koda taga ya ɗago yana kallonta ta ɗauka zece ta gyara ne zeyi ay seji tayi ya mata abinda bata taɓa tsammanin ze iya ba wato s bakin shi da yayi yana sucking ɗinta,tun tana daurewa ƙarshe de sabida daɗi ihu tashiga yi kamar numfashinta ze ɗauke,seda ya ɗauki kusan minti goma tana mata haka ganin tana shirin sumewa ne yasa ya ƙyaleta ya miƙe ya shige toilet.
Ƴarfillo se jiyo sautin ruwa tayi alamun wanka yakeyi,wasu zafafan hawayene suka shiga sunturi akan fuskarta sabida takaici,shi wanne irin azzalumine seda ya bari takai matakin da bazata iya jurewa ba sannan ze barta,cigaba tayi da kukanta yayinda marar ta tafara murɗewa sabida shaawar data taso mata.
Ya jima a toiet ɗin sannan yafito,ga mamakin ƴar fillo sanye cikin kaya yafito ba kamar yarda tai tsammanin ze fito ɗaure da tawulba,se ƙamshi yake bazawa abinshi kan kujera yaje ya zauna ya hakimce yana kallonta.
Kukan tane tafara damunshi dan haka cikin ɗaurewar fuska yace.
"ke kilaki meye na kuka kuma?kodan ban tara dake bane kike kukan?inko hakane kinada ayki,danni da kika ganni nan mutumne me kishi bana haɗa rami da kowa,in kin ganni a rami to nawane maana ni nafara samar dashi,inko kikaga nayi iya haka to ramin banawa bane kenan shiyasa nake checking kamin na rufta,dan haka wlh inde kece ko zaa tashi duniya iya abinda ze dunga haɗani dake kenan,kina da ƙira me kyau shiyasa nake tunanin zaɓarki a matsayin me zuwa tayani kwana aduk lokacin dana shigo garin nan".
Wani kukan tasake fashewa dashi tana roƙonshi akan yazo ya biya mata buƙatarta,miƙewa yayi ya buɗe wata loka ya ɗauko wani abu ya wurga mata sannan yace.
"ni adaline shiyasa bana zalinci a wannan harkar,dan haka ga wannan kiyi amfani dashi ki biyawa kanki buƙata in kingama kiyi musu magana zasu kawoki inda nake".
Ko sauraronta beyiba ya juya ya fice daga ɗakin cikin tafiyar ƙasaita.
Ƴarfillo bin abinda ya wurgo mata tayi da kallo, irin.......mazane amman na roba,da kamar ta yardar se kuma tafasa tayi amfanin dashi,ba laifi ya rage mata zafi,miƙewa tayi ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito ta maida kayanta,tafice tana fita masu tsaronshi suka taso suka mata rakiya zuwa ɗakin da yake.
A kwance tasameshi cikin kayan bacci ya lumshe ido akan tsttausan gado,tana shiga hannu ya miƙo mata ba musu ta ƙarasa inda yake itama ta kama hannun nashi janta yayi ta faɗa jikinshi yaja bargo ya rufesu yayinda ya rungumeta akan faffaɗan ƙirjinshi,zatayi magana ya haɗe bakinta da nashi ya shiga kissing ɗinta seda yaga jikinta ya mutu sannan yace.
"Sorry Baby is time for sleep".
Tanason magana haka dole tayi shuru har bacci yayi awon gaba dasu duka.
Asuba tagari ƴarfillo.
Ummu bata farkaba seda gari yayi haske sosai shima kukan ƙanintane ya tasheta da sauri ta miƙe ta ɗaukeshi,ashe kashi yayi shine yake kukan.
cire mishi kayan jikinshi tayi abinda ya bata mamaki shine zaran cibiyarshi yafaɗi gurin yayi baƙi kamar wanda ake gasawa,(abunda ummu bata saniba shine wannan aljana data taimakesu ita tagasa mishi har seda ta faɗi).
Gogo mishi tayi da kayanshi sannan ta goyashi a baya,gabs ɗaya zamsn gidan ya isheta taƙosa me gidan ta dawo.
Anasu ɓangaran ƴarfillo kuwa farkawa tayi taganta ita kaɗai akan gadon da sauri ta diro tana waige waigen inda zata ganshi,motsi taji a bayanta da sauri ta waiga,danƙari abinda tagani sosai yabata mamaki,Ɗansarki tagani sanye cikin kakin soja,a gaban rigar daga hsnnun hagu ansa NIGERIAN ARMY,daga ɓangaran hannun dama kuma ansa COL AYMAN ABU AYMAN.
Abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba haka taita binshi da ido,shiko wani killer smile ya sakar mata sannan yace.
"Suprise,Suprise,Suprise,ko baki faɗaba nasani,sabida ni haka nake kullum cikin ba mutane mamaki".
Murmushi tayi sannan tace.
"Wannan gaskiyane,tun jiya kake bani mamaki,sede abunda yafi bani mamaki shine duk wacce kataɓa ɗaukowa a inda ka ɗaukoni babu wacce ta ta taɓa faɗin kamanninka sannan babu wacce tasan sunanka,kawai de sede suce kai ɗansarki ne,but ni kuma naga gashi ina ganin kamanninka kuma kayan jikinka ya nunamin sunanka,ko meyasa hakan?".
"Yarda da kene yasa hakan,kuma tabbas ni ɗansarkine,kuma ni sojane ina riƙe da miƙami me girma a gidan soja,so idan kika bari wannan labarin ya fita waje se na tabbatar dana ɓatar dake a doron duniya dan babu wacce tasan hakan seke,inason mutum me sirri inde kika riƙe sirrina zan cigaba da baki mamaki,so nagode da tayan bacci da kikamin,dan haka ga tukuici".
wani ƙaramin akwati ya miƙa mata sannan ya juya ze fita da sauri ƴarfillo tace.
"Prince ko sunana baka tambaya ba bare ayi zancan phone number".
Murmushi yayi sannan yace.
"Inada mantuwa may be ko kin faɗamin kan na fita daganan na manta dan haka kije gida nagode kuma ba'a kawomin ziyara inde bani ne nayi gayyatar ba,ki kiyaye,na barki lfy".
yana kaiwa nan a jawabinsa yasa kai ya fice daga ɗakin,se ƙarar jiniya tajiyo.
Cikin sauri ta miƙe ta kimtsa ba batun sallah ta ɗauki akwatin daya bata ta fice daga ɗakin,se alokacin kunyar kayan jikinta takamata tana tunanin tayadda zata keta gari a haka,rasa abunyi tayi dan haka ƙarasa fita tayi zuwa falon gidan wanda ya gaji da haɗuwa jiki a sanyaye,tana fitowa ta tarar da wani yana jiranta,kayanta ya bata sannan yace.
"Prince yace a maidake gida".
murna ce ta kamata da sauri tabishi abaya zuwa gurin wata haɗaɗɗiyar mota ya buɗe mata baya ta shiga yajata zuwa Gidanta.
Cike da farinciki ƴarfillo ta,shiga falon gidanta gaba ɗaya ta manta dasu Ummu da suke Gidan se yanzu data gansu ta tuno,da sauri ta ajiye kayan hannunta ta nufesu.
"Ayya ƙanwata kuyi haƙuri na barku ku kaɗai wlh na mantane"tafaɗi tana daukar Ƙanin Ummu wanda se tsala kuka yakeyi.
Sannu da zuwa Ummu ta mata,amsawa tayi cikin sakin fuska sannan tajasu zuwa ɗakinta,toilet ta shiga ta ɗebo ruwa tazo tayiwa Ƙanin Ummu wanka wanda tunda yazo duniya be taɓa samun irinshi ba sosai ta wankeshi,sannan ta naɗeshi a tawul tun kan tagama naɗeshi ya fara bacci kwantar dashi tayi sannan taja Ummu zuwa toilet ɗin itama tamata wanka na haƙiƙa ta tsefe mata gashinta ta wanke sannan suka fito.
Dukansu ita tamusu shafa,acikin ƙananun kayanta ta samoma Ummu riga da wando wanda zasuyi mata ta bata tasa shikuma Ƙanin Ummu Megadi taba kuɗi yaje ya siyo masa riguna harda pampers da safa da takalmi,harda madarar jarirai,kamin wani lokaci Ƙanin Ummu yafito fess a matsayin cikakken Jariri me cikar gata.
Itama wankan tayi ta shirya cikin kayan mutunci sannan ta dafa musu indomie sukaci, shikuma ta dama madarar ta bashi yasha ya ƙoshi sannan ra goyashi be jima ba yayi bacci,itama Ummu baccinne ya ɗauketa a gurin,ɗaukarta ƴarfillo tayi ta kaira ɗaki ta kwantar da ita akan gado shima Ƙaninta kwantar dashi tayi a kusa da Ummun sannan tabisu da kallon idonta na zubar da hawaye na tausayinsu so da ƙaunarsu na ratsa zuciyarta.
Falo ta dawo ta ɗauki Akwatin da Ayman yabata ta buɗe, wani ihu tasaki na ganin abinda ke ciki kuɗine dollers.juyesu tayi tana ƙirgawa,miliyan biyu da rabi ta gani numfashinta har kusan ɗaukewa yayi dan daɗi,kwashe kuɗin tayi zata maidar cikin Akwatin kawai se taga wata ƴar takarda ta faɗo Ƙasa da sauri ta ɗauka tana dubawa,complimentary card ɗinshi ya bata.
Ƴarfillo rasa inda zata sa kanta tayi dan murna,tabbas wannan Ayman ɗin bazata taɓa rabuwa dashiba,duk wuya duk runtsi seta mallakeshi,musamman inta tuno abinda ya wakana tsakaninsu jiya jitake kamar tayi tsuntsuwa ta koma su maimaita,sosai ta kamu da mahaukaciyar soyayyarshi a ranta,wacce take fatan takaisu ga Aure.
Da la'asar ta ɗauki su Ummu suka shiga gari mota ta siya ta milyan biyu sannan ta siyowa su Ummu sutura da duk wani abu da za suyi amfani dashi,daganan Asibiti tawuce dasu inda takai Ƙanin Ummu aka duba lafiyarshi aka basu magunguna sannan aka rubuta nau'in abincin daya kamata abashi.
kasuwa ta shiga ta siyo masa sannan suka wuce Gida cikin sabuwar motar ta da yake dama ta iya driving motarce de bata da ita.
Me karatu nasan zeso yasan aynihin labarin ƴarfillo,to muje zuwa dan sanin wacece ita.
*Wacece ƴarfillo*
Husna Adam shine cikakken sunanta,ƴar Asalin Garin Yola ce,mahaifanta sun rasu da daɗewa,su uku ne a Gidansu ita da ƴan'uwanta maza guda biyu.
Tun tasowar husna bata jin magana sam macece meson mu'amala da maza,ko kaɗan bata da kunya,ƴan uwanta sunyi faɗan,sunyi dukan amman taƙi jin magana sam,daga ƙarshema da taga zasu takurata shine ta gudu Abuja da sunan karatu amman sheƙe Ayarta kawai takeyi,dede da rana ɗaya bata taɓa zuwa makarantar ba to dama ay seda Admission ake zuwa Ita kuma Bata dashi,ƙarya tayiwa ƴan uwan nata dan tasamu ta gudu,ayko tunda ta shigo Garin Abuja da wasa bata ƙara bin hanyar Garinsu ba sim card ɗinta ma yarda shi tayi tasa sabo gudun karsu nemeta.
Husna kenan wacce a yanzu sunanta ya koma ƴarfillo.
*Cigaban labari*
Suna isa Gida Ummu sabida ɗoki tasa aka fara gwada mata kayanta,shiko Ƙanin Ummu se wasanshi yake yi,ƴarfillo ko ta biyewa Ummun se gwada mata take yi.
Suna cikin hakane Shema'u Duniya tazo Gidan,da faraa ƴarfillo ta tarbeta,itako Shema'u hannu ta miƙawa ƴarfillo tace.
"Inji dumus,kyan alƙawari cikawa".
Dariya ƴarfillo tayi sannan taciro dubu ɗari ta ɗorawa Shema'u a hannun,wata uwar ƙara ta saki sannan ta rungume ƴafillon tana godiya.
"Meye na godiya sekace kyauta na baki aykifa kikamin na biyaki so kidena godemin"ƴarfillo ta faɗi cikin dariya.
Daganan hira suka shigayi akan Ɗansarki duk yadda Shema'u taso jin wayeshi ƴarfillo taƙi faɗa mata sede ta bata amsar da sauran matan suke badawa wato Ɗansarkine.
Shema'u bata so haka ba amman yata iya tunda dama kowa in taje ta dawo haka take cewar.
Se dare ta musu sallama ta tafi cike da mamakin su Ummu da ƴarfillo ta ajiye a Gidanta da sunan zata taimaka musu.
.
Har dare ƴarfillo takasa bacci sabida tunanin Ayman gashi tanason kiran wayarshi amman tana tsoron kartayi laifi a gurinshi,hakade ta yiwa su Ummu wanka bayan sunci abinci ta kwantar da Ummu ta goya Ƙaninta a baya dayake rigima yakeyi yaƙi yayi bacci.
Haka taita jijjigashi har tasamu shima yayi baccin ta kwantar dashi,tsakiyarsu ta shiga ta kwanta itama cike da tunani gami da kewar Ayman.
Cikin dare wayarta ta farkar da ita sabida kiran daya shigo,da kamar karta ɗaga sekuma ta ɗaga muryar da tajine yasa tamiƙe zaune ba shiri ta furta.
"Prince Ayman".
Dagacan ɓangaran yafara magana cikin isa yace.
"Wanne irin abune haka? nufinki yau bazanyi wasa dake ba kenan ko me?,".
Cike da tsoro ƴarfillo tace.
"Ranka ya daɗe tuba nake kaine kace baa kawo maka ziyara se kayi gayyata shiyasa banzoba wlh".
Tsaki yayi sannan yace.
"To number na kuma me ya hanaki kira?".
"Shima gudun kar inyi laifine yasa bankiraba".
"Good to laifin dakike gudun yi to kinyi,ns baki 30 minutes inganki a gabana".
Bakin ƴarfillo har rawa yake tace.
"Wlh inason zuwa gurinka sede akwai wata amana a hannuna yanzu wanda bazan iya fitowa na barsu su kaɗai adede wannan lokacinba sabida suna buƙatar kulawata wlh don Allah karkayi fushi dani".
Ƙit,taji ya kashe wayar hankalinta inyayi dubu yatashi,miƙewa tayi tafara sintiri a tsakar ɗakin,tabbas bazata iya barinsu taje gurinshiba adede wannan lokacin,ko jiya dan bata shaƙu dasu bane amman yau kam bazata iya fitaba.
Ƙanin ummu ne ya tashi daga bacci yana kuka da sauri ta nufeshi ta ɗaukeshi ta haɗa mishi abincinshi tabashi yasha taci gaba da jijjigashi,kamar daga sama taji ana buga ƙofar falon gidan,tsorone yacika zuciyarta sabids tasan basuyi da wani zezo tayata kwanaba.
A firgice tafito ɗauke da Ƙanin ummu a hannunta tanufi ƙofar leƙawa tayi dan ganin ko waye amman bataga kowaba har tajuya,zata koma se taji anci gaba da bugawa,bakinta ɗauke ds addua ta buɗe ƙofar.
Sanye yake cikin ƙananan kaya wanda suka amshi zubi da tsarin halittar shi,Prince Ayman kenan Ɗansarki me abun mamaki.
Da sauri ƴarfillo ta matsa masa hanya ya shige cikin falon ita kuma ta maida ƙofar ta rufe,ta bishi zuwa cikin falon,jikinta se rawa yakeyi,fuskarta ɗauke da mamakin ganinshi a Gidanta.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana bin jaririn dake hannunta da ido kamin daga bisani yace.
"No wonder naji kin buɗe da yawa she mejego ce,amman gaskiya Kin iya shiga bariki tunda har ɗa kika ajiye,amman ina fatan de kin tanaji amsoshin da zaki bashi sanda ya girma yamiki tambayoyi gameda waye ubansa?".
Hawayene suka biyo fuskarta sannan tace.
"Wallahi Prince ba ɗa na bane hasalima su biyune da yayarsa ƴar kimanin shekaru goma sha ɗaya sanin kanka ko ni ƴar shekara Ashirin da biyar ban isa ajiye ƴa me shekaruntaba,kuma nima wlh taimakonsu nayi bansan daga inda sukeba dan wlh ko suna wannan yaron bashi dashi".
Daganan,ta kwashe labarin haɗuwarta da su ummun ta faɗa mishi.
"Muje inga yayar tashin"shine abinda Prince ya furta.
Miƙewa tayi tana gaba yana binta a baya har zuwa ɗakin,da shigarsu ɗakin ummu ta ɓararraje tana shan baccinta gashin kanta duk ya bazu akan gadon wani akan fuskarta,sanda idonshi ya sauka akanta gabanshine yayi mummunar faɗuwar dabe taɓa yiba.
Hannu ya miƙa ya kwashe gashin fuskar tata ya maidashi baya sannan yabi fuskar da kallo,steel gabanshine yaci gaba da faɗuwa badan komaiba sedan kamannin da ummu take masa da masoyiyarsa ta mafarki wacce yayiwa alƙawarin baze kusanci kowacce mace ba a duniya se ita,kuma wacce yake jiran bayyanarta agareshi domin suyi aure,itace wacce ƴan uwanshi da mahaifanshi ke fushi dashi akan yaƙi amincewa da zaɓin da suka yimasa sabida ita.
Gaba ɗaya tunanin shi yatafi besan inda yakeba seda Ƴarfillo ta taɓoshi ita a tunaninta duk tausayinsune yasa yatafi dogon tunanin.miƙewa yayi yana me cigaba da kallon ummu Aymana sannan daga bisani ya miƙa hannu ya amshi ƙanin nata a hannun ƴarfillo yana kallo,hannun ƴarfillo yaja suka dawo falon,sannan yace.
"Se yanzu na amince ds zancanki gaskiya kinada imani wanda banyi tsammanin me zaman kanta,zata mallakeshiba,kin ƙara samun wani matsayi azuciyata kuma wannan yaron zan sa masa suna yanzu insha Allahu kuma,zan zama uba agaresu yayinda kike mazaunin uwa a gurinsu muddin kika sake kika koyar dasu tarbiya irin taki wallahi zakisha mamakin,hukuncin dazsn miki,daga yanzu duk wata ɗawainiyarsu tana hannuna na ɗauka".
"insha Allahu zan yi iya bakin ƙoarina wajan ganin na inganta tarbiyarsu,sede hakan baze hanani innaji buƙata ta tasomin nsƙi neman me kawatmin da itaba tunda de kassn jiki da jini".
"Ban,amince ki shigo da wani ƙato domin biyan buƙatarkiba,duk lokacin da buƙatar hakan tataso miki just call me zan taimaka miki amman bazanyi sex dakeba sede i promised you zanmiki abinda ze kawar miki da duk wata shaawa data taso miki,ina fatan kingane?".
Murmushi tayi gamida ɗaga mishi kai cike da jin daɗi sabida a ganinta haƙarta zata cimma ruwa.
Huɗuba yayiwa yaron inda ya raɗamasa sunansa wato Ayman jinior,sosai ƴarfillo taji daɗin,sunan,ɗaukarshi tsyi taje ta kwantar dashi sannan ta dawo gurin Prince suka shiga ɗaya ɗakinnata inda suka aykata mashaarsu son ransu ammande be kusancetaba sede wasannin kuma be cire kayanshiba sam.
Haka sukaita abu ɗaya se karfe huɗu na asuba yabar Gidan tare da alƙawarin ze dawo da daddare.
Koda da gari ya waye dare yayi prince yazo Ummu na bacci sede Ayman jinior ne beyi bacciba,haka yatafi batare da yaganta ba.
Washe gari yasa ƴarfillo takai ummu makaranta irin wacce ke haɗe da islamiyya in ta tafi tun bakwai na safe se shida na yamma zata dawo yayi hakanne dan ya rage zamanta tare da ƴarfillon,kuma school fees gaba ɗaya ya biya tundaga primary har ta gama secondry ya biya mata.
Sosai ummu taji daɗin sata a makarantar da akayi se godiya takewa ƴarfillo a zatonta itace ta sata,tundaga wannan lokaci zaman ummu a gidan yayi ƙaranci koda yaushe tana makaranta,in dare yayi kuma tayi bacci.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ga ummu cikin kwanciyar hankali ita jinior duk abinda sukeso ko babushi a nigeria inde sun nuna sunaso se Prince yasa ansamo musu shi ko menene kuwa.babu abinda prince yakeso irin yazo ya tadda ummu batayi bacci ba ƙwayar idonta kawai yakeson gani dan tabbatar da hasashenshi,uwa uba kuma yanaso magana ta shiga tsakaninsu dan yaji da wacce kalma zata fara yimasa magana,dan masoyiyarsa ta mafarki akwai wani suna da take kiranshi dashi wanda duk duniya babu me kiranshi dashi se ita.sede duk zuwan da yakeyi tana bacci inkuma yaso zuwa da yamma yanayin aykinshi baze barshi ba.
Muamala tsakaninshi da ƴarfillo kuwa ba abinda suka fasa,kullum ba ranar banza,kuɗi kuwa sanadin su ummu ƴarfillo bazata iya faɗin nawa ta mallakaba,gashi prince ya semata wani danƙareren gida acikin garin Abuja ta koma dama wanda take ciki haya takeyi.
Faɗin kyau da haɗuwar Gidan ƙauyancine dan gama babuce kawai babu a gidan.ɗakin ummu daban haka na ƙaninta,ankashewa ɗakunan dukiya bata wasa ba.
*Bayan shekaru Biyu*
Yau jummaa ummu tana gida ba makaranta dayake duk ranar jummaa basa zuwa,tsifa ƴarfillo tayimata ta gyara mats gashin sabida anjima zasuje saloon ayi mata kitso.
Sanye take cikin Riga da wando ja da fari ƴsn kanti wandon three quater ne yayin da rigar armless ce,gashinta an ɗaureshi da rimbom fari da ja,ƙafarta sanye cikin takalmi shima fari da ja.
*UMMU AYMANA*kenan baiwar Allah.
kyau iya kyau ummu tana dashi duk wani abu da ake kira kyau ga ƴa mace ummu ta mallakeshi tun yanzu da take da shekaru goma sha uku a duniya,fitowa tayi falon gidansu cikin tafiyarta me ɗaukar hankali gurin ƴarfillo ta nufa wacce ke ƙoƙarin ɗaurawa jinior igiyar takalminsa amman yaƙi tsayawa se wahal da ita yakeyi.ummu na ƙarasowa hayewa bayanta tayi wanda hakanne ta tilastawa ƴarfillo sakin abinda takeyi ta riƙeta,cike da shagwaɓa cikin gurɓatacciyar hausarta wacce kowa yaji yasan bafulatana ce tace.
"Mummy har yanzu baki gama shirya jinior ba bare mutafi da wuri,nifa kinsan banason rana wlh,shimane shegen jiniorn ya tsaya yaƙi tsayawa"ta faɗi gamida dungurewa jinior kai wanda bemasan tanayiba wasan shi yake da teddy bear ɗinshi.
"Lalalala kika zagi me sunan daddy tonide bs ruwana kuma sena faɗa masa kin zageshi".
A gigice ummu take kallon ƴarfillo kai da gani base sn faɗa makaba ta tsorata bakinta har rawa yakeyi gurin furta.
"Don Allah karki faɗa masa wallahi bazan ƙaraba,kuma dama kinga ni ban taɓa ganinsaba zakisa yace baze bari inganshi ba,nide kiyi haƙuri".
Dariya ƴarfillo tayi sannan tace, "to karki kuma zaginsa kinji ko".
Daganan gama shiryashi tayi sannan ta kwashesu a mota zuwa gurin saloon,akan hanyarsu ta zuwane Prince ya kira ƴarfillo a waya ɗagawa tayi cike da farinciki.
"Ina kuma kika kwashi yaran kukaje nazo gidan duk ba ƙwanan?kinsanfa banason yawo".
Prince ya faɗi cikin muryar dake nuna bashida walwala.
"Ayya prince wlh naje kai Aymana saloon ne ba wani guri najeba".
*Aymana*itace kalmar da prince yashiga juyawa akan bakinsa kamin daga bisani yace.
"Wacece kuma haka?,ina kika baro ummu da kika tafi yawon raka wata saloon?".
dariyace ta ƙwacewa ƴarfillo sannan tace.
"Prince kenan to ay ummun ce Aymanar,duka sunanta ne koda yake kai da ummu kawai kasanta to sunanta Ummu Aymana".
"Hasbunallahu waniimal wakil"itace kalmar data fito daga bakin prince badan komaiba sedan tsananin mamakin yadda akayi take ɗauke da sunan masoyiyarsa wato Aymana.
Ƴarfillo ce ta katse mishi tunani da cewa.
"Prince lafiya kuwa?".
Da kyar ya furta.
"lafiya lau,ko a ina kike please kiyi gaggawar zuwa gidana yanzu na baki 30 minutes"yana gama faɗa mata haka ya kashe wayar.
Hankali atashe ƴarfillo ta juya aƙalar motar zuwa Gidan Prince dan a rayuwarta babu abinda ke ɗaga mata hankali irin ganin Prince cikin damuwa.
Tana zuwa dayake ansanta buɗe mats get akayi ta shiga,tana yin parking ta ɗauki jinior a hannu ta kama hannun Ummu suka,shiga cikin gidan.
.
Suna shida falon gidan ƴarfillo ta ajiye su ummu sannan ta shiga ɓangaran da prince yake.
Yana ganinta ya miƙe yana murmushi rungume juna sukayi sannan ƴarfillo tace.
"Prince ka ɗagamin hankali wallahi ban ɗauka,zan sameka cikin nishaɗi ba".
murmushi yayi sannan yace,
"se gashi kuma kin samenin,ina kika bar su Aymanan?".
"suna falo"
"ok to muje mu gaisa dan so nake zan fita".
dariya ƴarfillo tayi sannan tace.
"wlh prince kanada rigima yanzu dama dan ka gaisa dasu ummu ne yasa kace inzo?"
dariya shima yayi sannan ya ɗaga mata gira ya kashe ido ɗaya yace.
"Laifine dan uba yaso gaisawa da ƴaƴanshi?"
"rufamin asiri ni bance ba muje ka gaisa da kayanka" tana kaiwa nan taja hannunshi zuwa falon.
gab da,zasu shi falon Prince ya ƙwace hannunshi daga nata,juyowa tayi tana kallonshi murmushi ya mata itama ta mayar masa suka ƙarasa shiga falon,lokacin da suka shigo yayi dede da lokacin da ummu take wasan hajijiya a falon jinior yans dariya juyowar da zatayi ta faɗa ƙirjin Ayman,kwantar da kanta tayi a ƙirjinshi sabida jirin da take gani sedr ƙamshin turaren da tajine ya haddasamata ɗagowa da sauri dan ganin shi ɗinne na mafarkinta ko ba shi bane.
Ɗago idonta keda wuya suka haɗa ido ita dashi,bakinsu ne yafara rawa wajan son furta kalma,atare kalmar ta fito daga bakunansu,Prince yace.
*HAYATI*
ita kuma tace.
*QURRATU AYNI*
Gaba ɗaya prince rasa inda zesa kansa yayi dan tsananin farincikin dayake ciki na haɗuwa da hayatinsa da yayi bayan ya kwashe tsawon shekara biyar yana mafarkinta da ita yake kwana da ita yake tashi,kullum so da ƙaunarta ke ɗawainiya dashi.
A nata ɓangaran itama Ummu tayi matuƙar farincikin ganinshi sabida shekara uku kenan tana mafarki dashi yana taimaka mata kuma yana bata labarai masu daɗi itama kullum se tayi mafarkinshi amman bata taɓa faɗawa kowaba.
Ƴarfillo ce ta katsesu daga kallon ƙurillan da sukewa junansu,da sauri suka ɗauke idanuwansu akan juna kowannensu yan murmushi.
Cike da mamaki ƴarfillo tace,
"Qurratu ayni,hayati,dama kunsan junane da jimawa?"
Murmushi prince yayi wanda tunda ƴarfilo take tare dashi be taɓa yimata irinshi ba,sannan yace.
"Kema de kinjiki da wani zance,ina na taɓa ganinta ma inba yauba,suna kuma da kikaji na kirata dashi tana kama da wata ƴsr film ɗin larabci ne to kuma jarumar sunanta kenan Hayati shiyasa kikaji na kirata dashi" .
murmushi tayi wanda ke nuna ta gamsu da bayanin nashi,sannan tace.
"Haba nifa ince,amman kaga ummu harda wani cewa Qurratu ayni,ni nasan larabcin da ake koya matane a islamiyya shine ta karramaka da sunan a farkon haɗuwarku".
Murmushi Prince yayi sannan yace,"wannan gaskiya ne"
Ranar wuni sukayi a Gidan Prince sam ya hanasu tafiya saloon ɗin da ƴarfillo ta takura cewa yayi ta kawo kayan kitson shi zema Aymanan kitson.
Dariya sosai abin yaba ƴarfillo dan ta ƙureshi seta miƙa masa jakar kayan kitson ummun,ayko kiran ummun yayi taje kan kujerar da yake kai kwantar da kanta yayi akan cinyarshi yashiga kitsa gashin,.
Ba ƙaramin mamaki abin yaba ƴarfillo ba bakinta har harɗewa yakeyi wajan yimada tambaya.
"Prince taya ka iya kitso haka? abun yafa bani mamaki sosai wlh"
Murmushi yayi sannan yace.
"ba abin mamaki bane ƴarfillo, sabida shekara biyar na kwashe ina yin wannan kitson a mafarki wanda koda wasa ban ɗauka zan iya yinshi a zahiri ba, segashi kuma nayi,wannan kitson da nayi wallahi ya ƙara gasgatamin mafarkina"
Dariya sosai ƴarfillo tayi sannan tace.
"lalle ka amsa sunanka Ɗansarki me abun mamaki,kace mu yanzu ba ruwanmu da saloon kawai da mun tsefe kai muyo nan" ta ƙarasa zancan tana dariya shima dariyar yakeyi.
Ita ko ummu aymana duk inda Prince ya juya idonta na kanshi so take yamata irin hirar da yake mata a mafarki wani sain har bacci zantukan suke sata,shima idonshi nakanta so kawai yake tamasa shagwaɓar da take masa untanjin bacci a mafarki tace se ya goyata,amman dayake shi yafita wayo yanayine da system gudun kar ƴarfillo ta ɗagosu.
ƴarfillo ko koda taga ummu na kallon Yman ɗauka tayi dan yau ne tafara ganinsa shiyasa take kallon nasa shiyasa bata ɗauki abun serious ba.
Ba su suka baro gidan Prince ba se bayan ishsha'i tare da rakiyar prince da muƙarrabansa.
Hmmm me karatu nasan ya ƙosa da son sanin waye Wannan prince ɗin,to muje zuwa.
*WAYE PRINCE AYMAN*
Ayman Abu Ayman shine sunanshi,saurayine ɗan kimanin shekaru talatin da uku a duniya.
Ɗa ne ga Sarki Abubakar,Amman tundaga ranar da aka haifi Ayman mahaifinshi yamaida sunan shi Abu Ayman shiyasa yanzu kowa da wannan sunan yasanshi,sarkin dake mulkar masaurata mafi Girma a faɗin ƙasar nigeria,wato masarautar kano.
Abu Ayman adalin sarkine me tsoron Allah,yanada mata biyu da ƴaƴa huɗu dayake Allah be bashi haihuwa da yawa ba shiyasa yake tsananin son ƴaƴan nashi.
Hajiya Zaituna itace uwar gida wacce ake kira da Hajiya babba,ƴaƴanta uku duka mata,Zainab,khadeeja,Hafsa.
Se Hajiya Jameela wacce ake kira da gwaggo amarya itace mahaifiyar Ayman,shi kaɗai Allah ya bata,kuma shine ƙaramin gidan dan sauran duk sun girmeshi.
Gidan babu kishi acikin shi shiyasa gaba ɗaya kulawar Ayman ta koma hannun Hajiya babba tana sonshi kamar ita ta haifeshi dan seda yayi wayo ne ya gane ba itace mahaifiyar shiba,haka suma sauran yaran gwaggo amarya na nuna musu soyayya ta aynihi.
Gaba ɗayan yayyan nashi sunyi aure dan haka shikaɗaine yarage yanzu a cikin gidan,se kuma ƴaƴan yayyan nashi da suke gidan.
Tun tasowar Ayman mutumne da beson hayaniya ko kaɗan dan koya hayaniya take yanzu kanshi ze fara ciwo shiyasa Mahaifinshi ya turashi Oxford University dake turai yayi karatun shi acan bayan ya gama primary da secondry ɗinshi a Nigeria.
Zuwan Ayman Turai karatu be lalata tarbiyar da iyayenshi suka bashi ba har yagama ya dawo gida,babu wani abu daya sauya daga ɗabiunshi.
Bayan ya dawone ya nuna yanasom shiga aykin soja,fafur Abu Ayman yaƙi amincewa sabida acewarshi in Ayman ya shiga aykin soja aka turashi yaƙi aje tsautsayi yasa akashe shi acan shikenan ya rasa magaji dan haka shi be,amince ba.
Duk yadda Ayman yaso shawo kan mahaifinnashi amman fafur yaƙi amincewa,hakanne yasa Ayman dena cin abinci har na tsawon kwana biyu,ganin,Ayman na ƙoƙarin kashe kanshi da yunwane yasa Sarki Abu Ayman amincewa da buƙatar Ɗan nashi,kuma ya tsaya masa har yasamu matsayi babba a gidan sojan.
Tunda Ayman yafara aykin soja mutumne shi me juriyar wahala dan har mamaki yake ba abokan aykinnashi dan inyana ayki babu me cewa daga gidan sarauta yafito,hakane yasa ya dunga samun promotion har zuwa yanzu dayake riƙe da miƙamin Conel.
Anyi mishi transfer daga wannan jaha zuwa wannan kuma yaje yaƙe yaƙe da dama inda daga ƙarshe de aka ajiyeshi a garin Abuja wanda har yanzu acan yake aykin.
Ayman ba iya aykin soja da mulkin mahaifinshi ya dogara dashiba,Ɗan kasuwa ne inda A halin yanzu har kamfani gare shi guda biyu,da na yin takalma da jaka,dakuma nayin atamfofi,sosai Allah yasa albarka acikin harkokinsa shiyasa yake da tarin dukiyar da koshi kanshi besan yawanta ba.
Ayman a ɓangaran addininshi mutum ne me tsantsar ruƙo da sallah baya wasa da ita sam kome yakeyi aka kira sallah ze ajiye yaje yayi sallah sannan ya dawo.mutum ne shi me tsananin tausayawa na ƙasa dashi yanada tausayi sosai dan ko a hanya yaga wani na buƙatar taimako yana tsayawa ya taimaka masa
Yau Jumma'a yaune Ranar da Ayman ya shirya dan zuwa Ganin gida kano,dayake shi be fiye son tafiya a jirgi ba shiyasa yake da masu tsaron shi har mutum ashirin da biyu motocin dake take masa baya guda huɗune kowacce mota akwai mutane biyar a cikinta se tashi wacce ke ɗauke da mutane uku direba me buɗe masa ƙofa se shi kanshi.
Haka motocin suka jeru akan titi daga Abuja zuwa kano inda suke ta sharara gudu,gab,da zasu shiga garin Kano dede wani titi daze sadaka da garin kofa in ka wuce ƙauyen gwarmai kaɗan kamar ance Ayman ya waiga.
Wata mace ya hango kwance agefen hanyar tana murƙususu wanda ke nuna alamar bata da lafiya,da sauri yabada umarnin a tsaya, ba musu duka motocin sukayi parking a gefen titin,shida kanshi ya fita yaje inda matar ke kwance tana ta kuka,sallama ya mata,amman da ƙyar ta amsa sabida halin da take ciki,umarni yayi da a ɗauketa asata a mota.
Nan da nan akasata a motar da yake ciki,suka ja zuwa cikin garin kano kai tsaye Asibiti aka kaita likitoci suka rufu akanta kamin wani lokaci har ta dawo cikin natsuwarta inda ta buƙaci likitan daya kira mata wanda ya taimaketa dan tayimishi godiya.
Dayake koda suka kaita Asibitin Ayman be tafiba dan haka likitanne yafito yace masa.
"Ranka ya daɗe mara lafiyar da ka kawo tanason magana dakai".
Batare da damuwar komaiba Ayman ya miƙe yabi bayan likitan zuwa ɗakin da matar take.
0 comments:
Post a Comment