*UMMU AYMANA PART 4*
Koda shigarsu ɗakin matar tana zaune tana kallonsu.
Likitan juyawa yayi yafice yayinda Ayman ya matsa kusa da ita yamata ya ƙarfin jiki,cikin faraa ta amsa da cewa.
"Jiki Alhamdulillahi yayi sauƙi,nagode da taimakon dakamin bazan taɓa mantawa dakaiba,kai mutumin kirkine wanda yadace da abun kirki,banida da abin biyanka,sede ka faɗamin abinda kake nema a duniya na tayaka da adduar samun shi"
Murmushi Ayman yayi sannan yace.
"Nagode sosai da wannan yabon da kikamin,kuma ni azahirin gaskiya jin daɗin rayuwar duniya Allah be rageni da komaiba,na farko ya yoni musulmi,yabani kyau,ya bani ilimi,yabani mulki,yabani ƙarfi da lafiya,ya bani dukiya,sannan yasanyamin sonsa da ƙaunarsa a zuciyata,kinga Allah yamini komai,abu ɗaya nake fata tamin kuma yanzu shine ya bani matar aure tagari domin samun zuria tagari,na ƙarshe shine yasa in ajalina yazo yasa na mutu cikin imani,shine kawai burina".
ya ƙarasa zancan yana kalon matar.murmushi tayi Sannan tace.
"Duk mutum nagari dole nagartacciyar mace ze aura,dan haka zantaya ka da addu'a nagode da karamci irin naku na bil adama".
Tana gama faɗa masa haka ta ɓace a gurin.
Tana gama faɗa masa haka ta ɓace a gurin.
A razane Ayman ya miƙe yafara waige waige amman ba bu ita ba dalilinta.
Da gudu yafice daga ɗakin sede bekai ga inda yakeson zuwaba ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme.
Da gudu yafice daga ɗakin sede bekai ga inda yakeson zuwaba ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme.
Da gudu securities ɗinshi suka nufoshi yayinda wasu kuma suka nufi ɗakin,da matar take amman basu gantaba,da sauri suka ɗaukeshi zuwa Asibitin da yake ganin likita.
Emmergency aka kaishi tuni likitoci suka rufu akanshi dan bashi taimakon gaggawa,wanda seda suka kwashe awa uku akanshi kamin su samu numfashinshi ya dedeta.
Sanda labarin ya samu ƴan gidan su hankali a tashe suka iso Asibitin,halin da suka,ganshi seda suka zubar masa da ƙwalla.
Tsananta bincike akayi akan a gano matar daya taimaka,ko ina jamian tsarone akan tituna suna bincikar ababen hawadomin kamo matar.
Wasa wasa seda Ayman Yayi wata biyu a kwance ba magana,abun ba ƙaramin ɗaga hankalin duk wani me sonshi yayiba,daga ƙarshe de na gargajiya aka koma yimasa inda Allah yasa aka dace yafara samun sauƙi,kamin sati uku ya,warke sarai ba me cewa yayi jinya,koda aka tambayeshi abinda ya firgitashi be ɓoye musu ba ya sanar dasu komai,ayko kowa seda ya girgiza dajin batun.
Daga ƙarshe de addua suka shiga tayashi akan,Allah ya tsare shi,aduk inda yake.
Tundaga wannan Lokaci Ayman yafara mafarki da wata yarinya ƙarama tana kuka gata a tsakiyar zakuna tana miƙo masa hannu akan ya taimaketa.
Kusan kullum seyayi mafarki da ita,sannu sannu har takai ga ya taimaki yarinyar har soyayya tashiga tsakaninshi da ita,kullum inya kwanta da kalar mafarkinta da zeyi,tun abin be damunshi har yafara ɗaga mishi hankali,Hajiya babba ya sanarwa,addua tace ya dunga yi Allah ya tabbatar da alkhairi.
Sannu a hankali son yarinyar ta mafarki yafara shiga zuciyarshi,har yayi girman da yakejin inde ba ita ya aura ba baze iya rayuwa ba.
Kullum cikin nemanta yake ko ze ganta sonta na wahal da zucuyarsa,kuma duk sanda zeyi bacci se tazo masa a mafarkinsa sunsha hirarsu ta masoya ta tafi,ganin hakane yasa Ayman siyo maganin bacci ya ajiye duk sanda kewarta ta dameshi se yasha ya kwanta bacci dan ya ganta.
Gaba ɗaya yafice daga natsuwarshi burinshi kawai ya ganta,ba abinda ke burgeshi da ita irin blue ice ɗinta,uwa uba shaawarta kullum ƙaruwa take a zuciyarshi,Addua kullum yinta yake dan ganin burinshi ya cika.
Ganin halin dayake cikine Magaifinshi ya yanke shawarar yimasa Aure ko ze samu kwanciyar Hankali,koda ya tuntuɓi Ayman da zancan son yimasa Aure,fafur ya tubure akan shi ba yanzu zeyi Aure ba.
Tun Mahaifinshi na ɗaukar abun wasa harde yaga da gaske yakeyi dan haka ya yanke shawarar ɗaura masa Aure da yarinyar takwaransa sarkin sokkoto,wacce ta gama karatu amman har lokacin Allah be kawo mijin aure ba,
*FIDDAH*kenan ƴa ga sarkin sakkoto.
Lokacin da Ayman yaji hukuncin da mahaifinsa ya yanke na haɗashi aure da fiddah har suma yayi,duk da besanta ba amman ya tsaneta.
Kuka ya dunga yi da idanunshi kamar ba soja ba akan mahaifinshi ya fasa auran dolen da yake shirin yi masa,kunnen uwar shegu Sarki Abu Ayman yayi da roƙon da Ayman ɗin yake masa.
Memakon Ayman yaga an fasa se gani yayima anata shirye shirye har kuɗin gaisuwa ankai,ba abinda ke ɗaga masa Hankali irin,alƙawarin da yayiwa Aymana wato hayatin sa na cewa shi mijintane ita kaɗai,daga ita ba ƙari har ƙarshen rayuwarshi.
Yau mahaifinshi ya matsa masa akan yaje su gana da fiddah,bashi da yadda zeyi haka ya ɗauki hanyar sokoto,koda ya isa sun karramashi sosai kowa se murnar ganinshi yake,daga ƙarshe de aka turo masa Gimbiya Fiddah domin su gaisa.
Tafe take kuyanginta na binta a baya suna riƙe da kasan rigarta dake jan ƙasa,yayin da dogarai su kuma keta faman yimata kirari,a haka har ta ƙaraso falon da aka saukeshi.
Lokacin data shigo kanshi a ƙasa yake ƙamshin turarantane yasa shi ɗagowa dan ganin waye.
Ganinta yayi zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon tana ta faman sakar masa murmushi gami da kashe masa ido ita ala dole zata ja hankalin shi.
Ba tare da damuwar komai ba Ayman ya kalleta yace.
"Don Allah kije kicema yayar taki ta fito haka mu gaisa, nifa ba kwana zanyi ba bare ta ɓatamin lokaci a banza"ya ƙarasa zancan yana me duban agogon hannunshi.
Zancan nashi ba ƙaramin ƙular da Gimbiya Fiddah yayi ba,wato ma dan rainin wayo ita bata kai matsayin wacce zata zama matarsa ba sede yayarta.
Fuska a haɗe tace.
"Bangane nakira maka yayata ba, gurina kazo ko gurin yayata?".
Cike da mamaki ya maida kallonshi kanta,sannan yace.
"Wai kina nufin kece wacce aka turoni gurinta?".
Murmushine ya kubce a kan fuskar Gimbiya ta ɗauka abun arziƙi ze faɗa da saurinta tace.
"Haba koda naji nasan dan baka ɗauka ni aka baka bane yasa kake ta fushin nan, to ay nice Gimbiya Fiddah".ta ƙarasa zancan tana fari da idonta.
"Kan bala'i!!! Wallahi da sake,yanzu ke in banda balagar zuci uwar me zakimun a gidan auran idan na aureki? ,tambayarki nake Uban me zaki iya mun inna Aureki?"ya faɗi cikin ɗaga murya.
Ido Fiddah ta ƙwalo waje tana kallonshi cike da tsananin mamaki, daurewa kawai tayi ta bashi amsa da cewa.
"Duk abunda kowaccen macan Aure takewa mijinta shi zan maka inka Aureni".
"Da wannan tsukakken kwankwason nakine zaki min abinda cikakkun mata ƙosassu suke yi a gidansu na Aure?"ya tambaye ta kamar ze doketa.
Gimbiya tafara fusata dan haka amsa ta bashi da cewa.
"Kabar Raina allura wlh itama ƙarfe ce,kuma da ƙosassun matan a gari mahaifinka ya tsallakesu yace Ni Gimbiya Fiddah ni nafi dacewa da Yarima Ayman".
Ayman sabida tsananin takaici da baƙin ciki ko amsa be bata ba ya fice daga falon. ko takan yiwa mahaifinta sallama be biba yabar masarautar zuwa tasu Masarautar.
Cikin dare ya iso kano dan haka dole ya haƙura da son ganin mahaifinsa zuwa gari ya waye,amman fafur ya gaza yin bacci dan baƙin cikin zaɓin da mahaifinsa ya masa.
Tun daga sallahr Asuba Ayman ɓangaran mahaifinshi ya nufa yana zuwa ko gaisuwa beyi ba ya fara ƙorafi.
"Haba Abba meyasa zakamin haka? taya zaka rasa wacce zaka zaɓamin se waccan tsinken sakacan?,ni wallahi bana sonta ko kaɗan banga abinda ya burgeni a tattare da ita ba , ita ba irin macan dana keso bace,dam haka nide wlh aka aura min ita se anyi danasani,tunda nace banaso".
Marin da mahaifinshi ya ɗauke shi dashi ne ya dawo dashi daidai,Ayman cike da mamaki yake kallon mahaifin nashi,dan tunda yazo duniya dunguri mahaifinshi be taɓa yi masa ba, yau gashi akan waccan talatsuruwar ya mareshi.
Ji yake kamar yaje ya kamata da duka,mahaifinshine ya katse shi da cewa cikin kakkausar murya.
"Ni sa'an ka ne da zaka zo gabana kana faɗamin magana son ranka?to ita naga ta dace da kai kuma ya zamar maka dole ka zauna da ita matuƙar nine mahaifinka,tunda ita kace tsinken sakace ce ina taka naman,?wawa kawai shasha wanda besan abinda ya dace dashi ba"ya ƙarasa zancan cikin fushi.
Zuwa lokacin Ayman kuka yake sosai na takaici,zuciyar ƴan mazance ta motsa ya miƙe a fusace ya dubi mahaifinsa.
"Wlh Abba ko kasheni zaka yi bana son Fiddah ,zan ƙara maimaita maka wlh bana ƙaunarta muddin aka aura min ita akwai matsala, kuma wlh tunda aka ƙi ji ba za'a ƙi gani ba",be jira amsar Abban nashi ba yasa kai yafice daga ɗakin yabar Abban nashi cikin matsanancin mamaki.
Ran Sarki sosai ya ɓaci game da abinda Ayman yamasa amman se ya shanye duk ɓacin ran nasa.
Shi ko Ayman yana bari gurin Abban nashi kayanshi ya haɗa yabar garin be musu sallama ba ya koma bakin aykinshi.
Tafiyar da Ayman yayi ita ta ƙara tunzura mahaifinshi nason ganin ya aura masa Fiddah,dan haka tuni ya matsa aka tsaida ranar auran.
Fiddah amarya de gyara take sha abinku da ƴan sokoto sosai suka haɗata ta haɗu,tun saura sati biyu bikin masarautar sokoto tafara shagalin bikin.
Saɓanin masarautar kano,dan ko angon basu ganshi ba bare suyi shagalin bikin.
Duk wayoyinshi kashe su yayi gudun karma akirashi,yayinda kullum Hayatin sa na zuwa ta ɗebe masa kewa,shiyasa duk yamance damuwar da ke damunsa.
Rana bata ƙarya.
Yau dubban jamaa suka shaida ɗaurin auran Ayman tare da Amaryar sa Gimbiya Fiddah,ɗaurin auran da akayishi batare da sanin Angonba danshi gaba ɗayama yamanta da wata Fiddah.
Ana gama ɗaurin Aure aka sako Amarya da muƙarrabanta a jirgi zuwa kano,sosai dangin Angon suka tarbeta duk wani abu na alada sun mata shi,daganan aka kaita gurin Sarki Abu Ayman,sede ga mamakinsu a mota suka sameshi a zaune,ana kawota yace ta shiga mota ba musu aka sata aciki,tana shiga direba yaja basu zame ko inaba se airport suna zuwa komai is ready dan haka shiga kawai sukayi jirgin ya ɗaga zuwa Birnin tarayya wato Abuja.
Basu daɗeba suka isa motoci suka tarar suna jiransu,shiga sukayi aka kaisu Gidan Ayman wanda besan bidirin da ake yiba danshi ba gwanin shiga social media bane bare yaji an masa aure,tv ko yadena kalonta sabida hayatinsa tana da kishi.
Dayake week end ne tana gidan yana bacci,har ɗakinshi sarki Abu Ayman yashiga tare da Fiddah wacce se kuka takeyi,suna shiga yamata umarni da ta zauna,zaman tayi sannan shi ya ƙarasa gurin gadon da Ayman ke kai yana bacci se murmushi yake base nfaɗa muku ba shida Hayatinsa ce.
Girgizashi yayi,da sauri Ayman ya miƙe a fusace dsn ganin wannen ɗan rainin,wayonne.
Carab ya haɗa ido da mahaifinsa,wata kunya ce gami da mamaki suka kama Ayman duƙar da kanshi yayi ƙasa ya kasa magana kuma ya kasa kallon idon Abban.
"Ba wani abu bane ya kawoni ba amaryarkace na kawoma wacce aka ɗaura muku aure yau,gatanan na kawota inde ka haifu kuma kacika tantiri,inna fita kabiyo da gawarta,".
yana kaiwa nan ya juya gurin Fiddah yace.
"Ki ta haƙuri kinji aljanna baa samunta a kwance,na barki lfy"
Godiya Fiddah takeyi tana kuka a haka Abu Ayman yafice daga gidan cike da tausayinta,jirgi l
Ya lula dashi da muƙarrabansa zuwa kano.
Ya lula dashi da muƙarrabansa zuwa kano.
Jikin Ayman gaba ɗaya yayi sanyi game da kalmar tantiri da mahaifinshi ya kirashi da ita.
Ko kallon inda take beyiba yafice daga ɗakin ya koma wani ranshi a bace,tabbas Abbanshi yagama cutar dashi tunda ya aura masa waccan skeleton ɗin,tabbas ko tantama bayayi yasha alwashin yimata hukunci dede da abinda aka masa.
Haka suka wuni a ɗaki ba wanda yaje gurin ɗan uwansa,Fiddah ta sha kuka har ta godewa Allah.
Se yanzu take danasanin ƙin bin shawarar ƙawarta JIDDAH ABBAS,domin seda ta gargaɗeta akan karta yarda ta auri Ayman tunda ya nuna ƙarara baya ƙaunarta,amman se tayi kunnen uwar shegu da shawarar Jiddan ta biyewa ta ɗayar ƙawar tata wato SALMAB JB,inda ta nuna mata ay ansha yin hakan ayi aure namiji baya sonka kuma daga ƙarshe yadawo yana sonka.
Ci gaba tayi da kuka amma bata karaya ba har yanzu bata sauka akan tsarin Salmab ɗin ba,tanaji a ranta cewa watarana Ayman ze sota.
Shiko anashi ɓangaran ganin ya gaji da zama a ɗakinne yasashi fitowa falo ya zauna,ya kunna kallo ji yake gaba ɗaya ya takura acikin gidan,wallahi da badan yana gudun kar Abban shi ya mishi bakiba da ba abinda ze hana be saketa a darannan ba.
Da misalin ƙarfe takwas na dare Fiddah ta fito zuwa falon gidan dan neman abinda zataci sabida yunwa take ji sosai,dinning ta nufa shima dakyar ta gano inda yake.
Kulolin abincine a jere a gurin wanda da gani yanzu kuku yagama jerasu dan ko alamar taɓawa babu,da sauri taja kujera ta zauna ta zuba abincin tafara ci ,ta kusa cinyewa Ayman ya nufo gurin,yana ganinta yaji duk duniyar tamasa zafi,rai a ɓace ya nufeta,tana ganin ta nufota ta miƙe a tsorace tana raba idanu.
yana zuwa ɗauketa yayi da wani gigitaccen mari,ze fara balai idonshi yadauka kan ayka aykar da gimbiya tayi,ba komai bane se fitsarin daya gani yana biyo ƙafafunta,sabida tsabar zafin marin da taji,takasa kuka ta ido setacan,jikinta ɓari yake kamar mazari,sabida tunda take a duniya batasan zafin duka ko mariba,dan babu wani mahaluki daya taɓs yimata ɗaya daga cikin su se yau.
Dariya ce ta kwacewa Ayman wacce besan sanda tafito ba kujera yajs ya zauna yana kallonta yana dariya,gaba ɗaya tagama fitsare jikinta da fitsarin.
"Kan balai fitsari kikayi daga ɗan wannan mari? toko lallai ba,shakka in na miki wani kalar se kinyi kashi,kuma wallahi bazaki jamin abin kunyaba ke da kanki zaki gyara gurin bazansa masu ayki ba,ni nayi mamakin ma yadda akayi wannan fitsarin me uban yawa ya taru a wannan marar taki,maza ki ɗauko abin gyarawa ki gyaramin gida tun kan afara jiyo kukanki a gidanku".
Fiddah baki ya mutu se hawaye wanda tasamu suka fito da kyar,har zata wuce yasata ta dawo sabida ganin dayayi fitsarin na ɗigowa daga jikin siket ɗinta.
"bazaki gama lalatamin gida da ƙazanta ba,dan da gani ko dama can ke ƙazamiyarce,dan haka sede ki cire wannan kayan adede inda kikayi fitsarinki,in kuma ba hakaba na lahira se yafiki jin daɗi ".
Ido ta waro da kyau dan tabbatar da abinda kunnanta yajiyo,ganin ba alamar wasa ko wargi a tattare dashine yasa tagane da gaske yake nufin rabata da kayanta.
tsugunawa tayi tafara bashi haƙuri.
"Prince don Allah kayi haƙuri kabarni da kayana a jikina wlh zan,goge duk inda na ɓata".ta ƙarasa zancan cikin kuka.
"in tunaninki zan ga wani abune a jikinki ya burgeni to kidena kawai raayina kenan wallahi sekin tuɓe kayan nan anan inko ba hakaba wlh inna fara dukanki se gari ya waye".
Jiki na ɓari Fiddah ta fara tuɓe kayanta tana kuka abin gwanin,tausayi amman prince be tausaya mata ba,tuɓewa tayi gaba ɗaya daga ita se pant da bra da sauri tajuya masa baya tana ci gaba da kukan yayin da ta kare ƙirjinta da hannayanta.
"Kan uba toshi pant ɗin da kika barifa,ko nufinki shi bazaki cireba? shi dayafi ma kowanne shan fitsatin".
Haƙuri zata bashi da amman ganin ya miƙe yana shirin kwance belt batasan sanda ta cire pant ɗinba sabida tsabar gigita har da bra ɗin ta cire ta tsaya a gaban tana kyarma.
Wata uwar dariyace ta kwace masa wacce yayi iya yinshi dan ganin ya shanyeta tunda Fiddah tafara cire kayan amman abun yacu tura,dan dariya ko magana ya kasa se dariya yake yana nuna ta.
Se lokacin Fiddah ta gane Ayman yayi niyyar tozartatane shiyasa yace ta tuɓe a gabanshi,da gudu ta ruga ɗakin da Abba yakaita ɗazu, kulle ƙofar tayi ta faɗa kan gado tashiga rusa kuka.
Shiko Ayman gudun Fiddah ma dariya ya ƙara bashi,wanda dalilin dariyar ne har yafaɗa kan fitsarin be saniba.
Jinshi cikin fitsarinne ya ƙatse dariyar da yake da sauri ya miƙe tsaye,a fusace ya nufi ɗskin da ta shiga.
yayinda ita kuma tana tsaka da kukanne wayarta ta shiga ƙara,dubawa tayi dan ganin me kiran.
*Salmab jb lagos*,shine sunan da tagani da sauri tashare hawayanta ta ɗaga wayar.
to ko me zasu tattauna ita da aminiyar tata?
"Hello ƙawata wlh kamar dama kinsan nemanki nakeyi".Fiddah ta faɗi cinkin damuwa.
Daga can ɓangaran Salmab tace.
"Amarya da damuwa kuma,kode Prince ya kashe boss ne?"ta ƙarasa maganar cikin dariya.
"hmmm wannan ay tafi ƙarfin kashe boss kawai harda actor ɗinma duk yakashe"ta kai ƙarshen zancan cikin kuka.
Hankalin salmab ne yayi matuƙar tashi a gigice take tambayarta abinda ya faru.
Da ƙyar tasamu Fiddah tai mata bayanin komai daya faru.
Wata uwar shewa Salmab tayi gamida kwashewa da dariya daga bisani tace.
"Tur wallahi,kinban kunya yanzu har akwai wani wulaƙanci da ɗa namiji ya isa ya miki baki rama ba?wlh babu shi,to bari kiji in gaya miki,koda wasa karki sake nuna kina tsoronsa,dazaran yafara dukanki wallahi ki riƙe masa gabansa tsaf zaki ga yadena ya koma baki haƙuri,haba ƙawata me akayi akayi prince da har ze saki kuka,?kuma tunda shi yasa kikayi tsirara,to karki sake kisa kaya daganan zuwa shekara se in da kansa ya samiki,kuma ko uban waye a gidan ki fito haka wlh zaki ban labari".
Tunda Salmab ta fara huɗubarta Fiddah take dariya,duk da batayi mamaki ba,dan Salmab bata tsoron kowa duk wanda ya mata se ta rama.
Godiya Fiddah tayiwa Salmab sannan ta kashe wayar,hakan yayi daidai da ƙarasowar Prince ƙofar ɗakin,buga ƙofar ys shiga yi cikin zafin rai yana kiran sunanta.
"Ke!!!dan ubanki bazaki fito ki gyara gurin can ba,gashi kinsa nima fitsarin ya ɓata kayana,kinsan Allah in Baki fitoba nidake ne".
"wlh bazan gyara ba sede ya shekara a haka,angaya maka ni baiwar gidankuce?,uban wa yace kamin marin dayasa nayi fitsarin?wlh sede ka gyara amman ni bazan gyara ba,mugu kawai".
cewar Gimbiya Fiddah daga cikin ɗakin.
cewar Gimbiya Fiddah daga cikin ɗakin.
Ayman zuciyarshi har tafasa take sabida baƙin ciki,dukan ƙofar yashigayi iya ƙarfinsa amman taƙi buɗuwa,cikin zafin rai yace.
"in har kinsan kin haifu cikin ubanki to kizo ki buɗe ƙofar nan na faɗamiki uban dayace na marekin".
Ba musu Fiddah tazo ta buɗe ƙofar,sede yana shiga ta cafke gabanshi da hannunta iya ƙarfinta,ƙara Ayman ya saki,sannan jikinshi ya kama rawa,ko motsi ya gaza yi idonshi ya rufe yayin da hannunshi ke nuna alamar tayi haƙuri.
Dariya Fiddah tayi na ganin taci nasara,shawarar Salmab ta mata rana.
"wlh daga yau se yau koda wasa kakuma yunƙurin dukana se na maka kaciya sabida ni ba baiwa bace bare kasa a gaba kana azabtarwa".
Gyaɗa kai Ayman yake alamar yaji ya amince,sakar masa tayi amman kamin tasaki seda ta murɗa.
Ayman kasa motsawa yayi ita ko toilet tashige tayi wanka ta fito ko tawul bata sako ba,ta haye kan gado tayi shigewarta bargo.
D ƙyar Ayman yasamu ya iya ficewa daga ɗakin,ya nufi nashi,har ya kwanta yatuno da fitsarin dasauri ya miƙe yaje ya gyara gurin,yadawo yayi wanka ya kwanta,(Anya Fiddah taci bulus kuwa?)
Wai wacce irin surace da Fiddah dayasa Ayman ke mata dariya樂?
Fiddah ko ince muku model,fara ce sosai bata da tsayi amman ba gajera bace,tana da yalwar dogon gashi a kanta baƙi me ƙyalli,tana da idanuwa masu haske gami da girma daya dace da kyakkyawar doguwar fuskarta me ɗauke da dogon hanci me kyan tsari,bakinta ƙaramine me kyau,yayinda ƙirjinta ke cike fam da na shanu,cikinta zuwa marar ta a shafe suke sosai yayinda ƙugunta ya buɗe daga ƙasa wato cocacola shape,in tana tafiya jikinta babu inda baya rawa kamar tarwaɗa,Gimbiya Fiddah kenan.
Shiko Ayman ba komai yakewa dariyaba se shafewar cikin nata dan shi anashi ganin ba haka mace ya kamata ta zama ba,sabida kullum consider yake da Hayatinsa wacce take yarinyace ita amman yana mata kallon babbar mace.
Ayman kwana yayi beyi bacciba sabida baƙin cikin fiddah,kuma bakomai yasa ya kwashe fitsarinba sedan gudun abun,kunya amman da bazai kwasheba.
Ba abinda yaba ayman mamaki irin kama gabanshi da fiddah tayi aranar da aka kawota gidanshi,kuma take yawo tsirara a gabanshi batare da taji kunya ba,wanda shi a ganinshi tabbas fiddah ƴar duniya ce dan inde basu ba ba wata amarya da,zata iya yin hakan a daranta na farko.
haka ya kwana wannan tunanin,gamida neman mafita,ita ko anata ɓangaran bacci take harda munshari batare ds damuwar komaiba.
washe gari da asuba fiddah,Waldrope ɗinshi ta buɗe ta ɗauki doguwar rigarshi tasa tayi sallah,tana idarwa ta tuɓe ta maidar mishi inda ta ɗauka,takoma baccinta.
Bata farkaba seda gari ya waye,tayi wanka,ta ja handbag ɗinta ta ɗauko kayan kwalliya ta tsantsara,tana gamawa ta mayar tafice daga ɗakin timbir timbir abunta tana juya mazaunai.
A daidai wannan lokacin Ayman ne zaune a falo shida Abokinsa Faisal daya kawo mishi ziyara suna hira,jin motsin tahowane yasa Ayman maida hankalinshi hanyar dayaji motsin,shiko faisal hankalinshi nakan tv ko motsinma be jiba.
Fiddah ya hanga tafe tana rangwaɗa kai ka rantse da Allah cikin kaya take,tsallan da Ayman yayi daga inda yake yadira gabanta me karatu inda kana gurin se kaji tsoro.
yana isa girinta beyi watawata ba yasureta da gudu zuwa ɗakinta,harga Allah Fiddah bataga Faisalba amman da Ayman yafara faɗa mirtsikewa tayi tabashi amsa da cewa.
"kaga malam ka isheni ina abun yake,da har zakayi kishin wani yaganni tsirara,to bari kaji ni nan dakake ganina wlh jina nake kamar da kaya ajikina dan haka kabarni naje mugaisa kawai,"ta fara yunƙurin kwacewa daga ruƙon daya mata.
"Haba silinder baki da hankaline zaki fita tsirara wannan ay tozartani zakiyi,in wani yaganki a haka pls kisa kaya se kizo ku gaisan".
"Ayni duƙ abinda ze tazartaka sonshi nake,kuma kaya wlh bazan saka ba,silinder da kake faɗi kuma wannan ƙarya kake wlh,dubeni da kyau,full option ce ni"tana kaiwa nan a maganar tagirgiza mazaunanta da ƙirjinta cikin wani yanayi daya jefa ayman cikin wani hali wanda ko farkon ganinta tsirara be taɓa jiba.
Bin ta ya dunga yi da ido tana jujjuyawar,da kyar ya fauke idonshi ya kamota ya zaunar da ita akan gadon sannan shima ya tsugunna,ya ɗora hannayanshi akan cinyarta ya kamo hannunta,ya fara magana.
"in kika fita a haka mutuncinkine ze zibe dana masarautar ku da tamu,don Allah kisa kayanki kinji princess".
Wata uwar harara ta doka mishi,sannan tace.
"wlh bazan sakaba"ta ƙarasa zancan dayin fari da idanuwanta.
Ayman ganin da gaske takeyine yasa yamiƙe ya ɗauko wasu riga da wando acikin kayansa yazo ya fara saka mata,kuma bata ƙi yarda ba tsayawa tayi tsaf ya shiryata.
komawa gefe yayi yana kallonta,tabbas se yanzu ya fahimci fiddah macece ta nunawa aboki,ammam da ko ganimta yake akasin hakan.
itako se wani juyi take tana wani gantsarewa ita ga haɗaɗɗiya.
hularshi ta cire tasa akanta sannan ya jata zuwa falon inda Faisal ke zaman jiranshi.
Mamakine yakama faisal na ganin Ayman ya ruga da gudu wanda shi besan dalilin gudunba,shiyasa yazauna yadawo yatambayeshi abinda ya faru.
0 comments:
Post a Comment