HIBBAH Part 1-5
.
Cikin bacin rai yake magana "Habba mutum sai kace maye ance kufita kubarmun gida kunki fita saikace gidanku" "Umma na gefe hawayene ke fita idonta, zuciyarta tamkar zai fito don bakin ciki da takaicin tijarar da ake musu Sadeeq ya durkusa har kasa yana kuka "baffa don Allah kayi hakuri idan mukabarnan bamuda inda zamu Kallo ya kare musu tare da takaici" nabaku nan da kwana biyu wallahi inbakubarmin gidaba watsamuku kayanku waje zanyi, Aiba tare muka sai gdn dakuba. Yana gama hayaniyarshi yayi waje Matan gdn suna Kallo Uwar gdn tace "mutum sai nacintsiya ance kufita kubamu waje kunkiya da hidimarshi zaiji koda hidimar naki yaran? Dayar tace" gaya musudai ni na matsu subar dakin in dawo ciki dama nawa yamin kadan Umma ta kwashi yaranta sukayi daki tace "kar ku yadda ku fita kujirani yanzu zanje indawo.
.
_HIBBAH_" ummah don Allah karki jima idan kinje masifasu Mmn ahmad zasuta mana Insha Allah barin jimaba zan dawo Toh ummanah Allah tsare hanya ya dawo dake lfy Ameen Idan kannenku sundawo makaranta kubasu abinci suci kuyi wanka ku tafi islamiya ida bandawo da wuri ba. Bayan fitar umma kai tsaye gidan kawunta ta wuce dake tsohuwar makabarta cikin garin bauchi. Tsabar ko nisan wajen bata gani burinta kawai Allah ya kaita lfy, Bayan isarta sun gaisada inna asabe matar kawu usman take" tambayarta ko yana gd? "yana wajen aiki zuwa karfe hudu zai dawo insha Allah Allah dawo dashi lfy Nan sukayi ta hirarsu har lkcn sallar la'asar tayi suka bada farali Sai wajen karfe biyar kawu usman ya dawo, saida ta bari y ci abinci ya huta sannan taje ta gaidashi Ya tambayeta y lfyr yrn Fatan ba wani matsala "ba komai kawu dama so nake idan da hali mu dawo nan da zamakafin musami wani gdn koda haya ko na sayarwane mu saya, Tunda gdn damuke ciki ya fita agadon yrn inaga kuma zamu karama kallah dawainiya Tunda shima yanada nashi iyalan. Kawu usman yadai jitane amma kodaga yanayinta yasan halin kanin mijin nata kuma mijin y'arshi Badamuwa, nanma ai gdn ki tattarosu ku dawonandin da zama Da yaddar Allah abunda zamuci bazai gagaremuba fatanmu Allah karamana rufin asiri da wadatar zuci Ameen *. Bayan umma tabar gdn kai tsaye gdn dillaliya ta wuce akan tazo ta sayi kujerunta da wasu tarkacen. Sai wajen karfe shida ta koma gida lokacin su hibbah sun dawo daga islamiya, bayan sunyi sallar magrib da isha'i suka fara harda kayakinsu, saida suka gama hada komai cikin daren kafin suka kwanta.
.
Washe gari tun asuba suka tashi sukai sallah sukai wanka. Kasancewar ranar asabarne ko islamiya basujeba don umma ta daura damarar barin gdn ayau basai gobe ba da yaddar Allah. Wajen karfe tara mai sayan kujeru tazo harda carpet din dakinta ta hada ta sayar, dake kayan basu wani jima da sayansuba tayi sa'a an saya da mutunci ta cake mata kudinta cas ta bata aka kwashe kayan. Mutan gdn sai tsegumi suke, itako ko kallo basu ishetaba. Moto ta nemo akazo aka kwashe kayan tsab ta hada kan yrn su hudu suka fara gaba a moton kayan. Sallama tayi k'ofar dakin mmns ahmad uwar gdn kallah, bayan sun gaisa da ita da maigidan tace"nazone inmuku sallama da neman afwanku da gdy agareku, Mungode sosai Allah yasaka muku da alkhairi Allah ya biyaku. Tana kaiwanan ta tashi tayi gaba tana tafiya tana hawaye, Dagaske yau zatabar gidannan? Dagaske zamanta yazo karshe agidan? Gidan da suka kafa rayuwarsu cikin soyayya, kaunar juna, kyakkyawar alaka da mutanen unguwar amma yau rana guda zatabarshi badon tasoba saidon anfi karfin ta. Allah sarki mutuwa mairaba d'a da uwarshi, Mairaba uba da d'anshi, Mairaba mata da mijinta, Mairaba miji da matanshi, Mairaba mutum da kowa nashi Mutuwa mai tonon silili. *ALLAH KAMANA KYAKKYAWAR KARSHE* Saida tashiga duk gdn mokotansu ta musu sallama tare da neman yafiyarsu. Mutane da yawa sunyi kukan rabuwa da ita. Don umma da mijinta mutunene masu son mutane akwaisu da barkwanci da wasa da dariya, shiyasa gidansu bai rabuwa da mutane babba da yara, gashi yau rana tsaka anrabu rabuwar da rai baisoba wannan shine *RABUWACE SANADI* ( _QUEEN MIEEMI_) Haka tabar cikin unguwar ranta kamar wuta. Bayan isarta gdn kawu usman ta samu an share musu d'akin da zasu zauna ciki da taimakon 'yan matan gidan suka gyara d' akin tsaf, mazan zasu rinka kwana dakin y'anmazan gidan,"Habba"kuma suna tare da umma. Haka suke rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi. Duk kud'ad'en hannun umma ta hada da dan gadon yaranta da aka tsakura musu ta damka wa aminin mijinta ya sama musu dan gidan da zasu mak'ale don batason zama karkashin wani ta dauramai nauyinsu harsu biyar. *
.
*ASALIN LABARIN*
GARIN BAUCHI KARAMAR KARAMAR TAFAWA BALEWA Garine mai tarin kauyuka, *Malam Adam*yana daya daga cikin mazauna wannan kauyen babba malamin addinine kuma manomine sosai. Mafi yawan mutanen kauyen nasu basu damu da neman ilmi ba, yanada mata daya maisuna *Hauwa'u* da yara biyu dukkansu maza babban, sunanshi *Sa'ad* sai kaninshi maisuna *Musa*ana kiranshi da *Kallah*kasancewar sunan kakanshi na wajen uba yaci. Tsakaninsu akwai tazarar shekara bakwai, *Sa'ad*yadau son duniya ya dora kan kaninshi duk abundaya samu na *Kallah*ne. Suna zuwa makarantar boko awani kauye dake gaba dasu, *ALLAH*yabasu baiwar ilmi sosai.
.
Haka suke rayuwarsu cikinso da kaunar juna. Bayan *Sa'ad* yagama makarantar gaba da primary aka mishi aure da masoyirshi maisuna *khadija*makarantarsu daya tayi jarabawar aji uku shikuma lokacin ya gama aka musu aure. Bayan fitowar jarabawar tashi ya nemi izini gun mahaifinshi yanason shiga cikin garin *Bauchi* ko Allah zaisa yasamu aikinyi, mahaifinshi ya amince ya mishi Fatan alkhairi da samun nasara. Da taimakon wani d'an uwanshi ya sami koyarwa awata makarar turawa, har wajen zama suka bashi dayake lokacin ba kowa ke yadda d'anshi yayi makarantar bakoba. Kuma zasu rinka bashi albashi mai tsoka, da gudu yaje ya dauko matanshi suka dawo. Bayan dawowarsu da da y'an watanni *ALLAH* ya azurtasu da samun d'a na miji, mai sunan *ABUBAKAR SADEEQ* yataso cikin kulawa da soyayyar iyayen shi, shekaranshi hudu ummanshi ta sami wani cikin. Lokacin har yafara zuwa makaranta, umma na hango tanata shirye2 tafiya bikin *Kallah*wanda za'ayi a kyauye ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Sunje sunsha biki *Yaya Sa'ad*ya taka rawargani domin shine jigon komai na bikin, angama biki lahadi suna shirin dawowa ran alhamis haihuwa tazoma *Ummah* ta sauka lafiya tasami katuwar d'iyarta, dole aka daga tafiyar sai bayan suna zasu koma. Ranar suna ansha shagali yarinya taci sunan *HIBBATULLAH* *Abbah yace su zauna sai bayan wata daya zasu koma yanaso yamusu y'an gyare2 agidansu. *Bayan wata daya* *Abban Hibbah*yazo daukarsu asabuwar motar daya saya don yanzun Allah ya buda mishi sosai har cigaba da karatunshi, antayashi murna sosai tare da addu'a.
.
Nan yake shaidamusu yagama ganin sabon gidanshi anzuba komai yanzu ma insha Allah can zasu wuce, idan an kwana biyu kaninshi da matarshi suma zasu dawo gidan da zama, *Umma*aranta "tace gida!" Dama yana ginine? Tayi mamaki Amma kuma saita share, iyayensu har kukan murna saida sukayi na yadda yake dawainiya dasu da yadda yakeson kaninshi hatta y'an garinsu suna yabonshi dayi mishi Fatan alkhairi. Bayan tahowarsu *Abban*kebata hakurin rashin sanarda ita ganin da yakeyi dama so yake yamata *Bazata*_Rash kardam_ Tace "lahhhh! Bakomai ai Allah yasanya alkhairi ya kara budi. Bayan dawowarsu sabon gidan suka nufa, balaifi gidan yayi daidai na mai karamin karfi. Ciki da falone guda uku sai kitchen da bayan gida guda biyu, sai wani daki ciki daya sai wadataccen filin tsakar gd. Takardun gida dana motor da duk wani kaddarar da Abban yasaya duk sunan kaninshine ajiki Tab! Wannan shine babban kuskuren daya tafka. Da isarsu basu z'ame ko ina ba sai sabon gidansu" gidane d'an madaidaici, w'anda ya kunsha d'akuna ciki da falo guda uku, ciki d'ayan guda biyu ne, sai kitchen d'aya, bayan gida g'uda biyu, sai filin t'sakar gida. K'afin su shiga s'aida su kayi addu'an shiga gida. D'akin *Umma* kuwa k'omai sabo aka samata, ta zama tamkar wata amarya.
.
Rayuwar su suke cikin jin dadi da mutunta juna girmama juna, zaman lfy da k'wanci yar hankali, zamansu g'wanin ban sha'awa. *Abbah* yayi nacin duniya akan *Ummah* takoma makaranta, Amma sam t'aki tace gara ta z'auna tayi bautar aurenta, da kula da yaranta, da yaga taki yasata makarantar Islamiyar cikin unguwarsu. "Haka rayuwarsu t'aci gaba da tafiya, k'ullum gidansu bai rabuwa da mutane sabida akwai suda son mutane" g'ashi sun iya zama da mutane cikin aminci, daga y'an uwansu har mutanen unguwa k'owa rubibin z'uwa yake. *Umma* dama gwanace w'ajen ihsani shiyasa mutane keson ta. (hummmm! d'an adam kenan idan kanada abu kaine nasu inko bakada komai babu mai kusantarku) *HIBBAH* k'uwa har ribibin daukarta ake sabida k'ullum cikin gayu da kamshi t'ake, balle y'anzun data fara tafiya gata y'ar duma_ duma. Yau *Ummah* sai gyaran gida t'ake ga bakinnan yaki rufuwa ga girke2 da akayi duk na tarbar baki ko ince masu gida *Musa Kallamu* *da matarsa *Saude* da d'ansu *Ahmad* Tun s'afe *Umma* aikatuwa sai wajen k'arfe 2:00MP tagama k:omai taje tai w'anka ta gyara jikinta sai d"aukar kamshi take. *Abbah* ankasa samun nutsuwa sai shiga da fita ake yau sahibinshi zaizo" sai w'ajen k'arfe hudu suka iso tare da sauran kayansu.
.
Bayan sun huta sunci abinci sunyi w'anka suka hau gyaran d'akin da zasu z'auna da taimakon *Umman* k'omai yayi dai-dai. Yau tsawon wata biyu kenan da dawowarsu *Saude* ko tsintsiya bata t'aba d'auka da sunan sharan gidan ba b'alle girki da wanke wanke bata komai *Umma* ita keyi hatta wankab *Ahmad* itakeyi, *Saude* Saidai t'aci ta k'wanta kwanon dataci abincima sai anzo an d'auka, *Ummah* ko ajikinta. Gata da d'an k'aran kishi, sa ido, son kai, ko silifas *Umma* ta chanza hankalinta atashi y'ake saita saya itama hankalinta yake kwanciya. Komai na gidan y'anzun ya dawo hannun *Kallah* don yanzu *Abban* ya koma makaranta. *BAYAN WASU SHEKARU* Abubuwa da dama sun faru ciki harda rasuwar *Malam Adam* da haihuwar *Ummah* yara biyu d'uka maza, *Salman* da *Adam* anacemai *Abbah* *saude* tasake haihuwar d'a namiji *Aliyu* *Kallah* ya kara aure sunan matar tashi *fauziyyah* diyar kawun *Umman su Hibbah* kayu *Usman* gida ya cika da yara harda yaran rik'o, duk *Abban* ke daukar d'awainiya dasu makaranta su, su turarsu, komai na rayuwa shike musu don yanzu kam _Alhamdulillah_ akwai rufin asiri sosai *Kallah* shima yajima da samun koyarwa Saidai baya tabuka komai cikin gidan" ga matanshi kullum cikin fada ga kishin dasuke da *Ummah* ko suda suke kishiyoyi basama junansu hakan, duk jumma'a ko ranar *Abbah* yakan debi duka yaran suje masallaci bayan sallah anyi duk gidajen y'an uwansu saisunkai ziyara, Haka rayuwa taci gaba da tafiya da dadi ba dadi *Abbah* har mukamin kwamishina yasamu, tundaga wannan lokacin k'uma ya kamu da rashin lafiyar da aka kasa gane kanshi" har ya k'wanta asibiti, kullum asibitin baya rabuwa da mutane, kullum shalelen *Abbah* tana makale dashi idan sundawo d'aga makaranta, bacci k'awai ke rabashi da *HIBBAH* Satinshi uku a asibiti k'ullum *Ummah* tana wajen tareda d'an data kuma haifa maisuna *Muhammad* Cikin wannan satin jikin yayi nauyi sosai t'sabar azabar ciwo da kyar yake iya bud'e ido, maganama saika matso k'usa da bakinshi k'afin kaji me yake cewa. k'owa yafara karaya da wannan ciwon nashi, har k'auye akaje aka d'auko mahaifiyarshi, randa tagan shi tayi kuka sosai tare da addu'ar Allah tashi kafa dunshi indan da sauran rayuwa a nan gaba.....
0 comments:
Post a Comment