HIBBAH Part 6-10
.
Tunda Karsu *HIBBAH* tazo taga *KALLAH* kozaman asibitin baiyi wataran saiya kwana biyu baizoba, idan anyi maganar magungunar da za'a saya saiyace baida kudi, karshe saida akasaida moton *Abban* ba'aje ko inaba kudi sun kare, ga gidansu cike da mutane Wai sunzo dubiya Amma sun kasa tafiya Saidai suci su kwanta, da mahaifiyar *Kallah* taga bai zama gun yayannashi tamai magana cemata yayi "ai yaga kodayaushe abokanshin suna zuwane" tace "ina ruwanshi da zuwansu shiyafi kusanci dashi, shiya kamata kodayaushe yana kusa dashi musamman yadda yanzun jikinshi yayi nauyin nan, bai kamata yana nisaba" Bayan kwana biyu da zance, ranar laraba Tunda ya tashi jikin da sauki sosai kowa ka gashi murna yake, dama gashi sarkin zolaya, wasa, da dariya kowa ya dubashi saiya tsikaneshi Ahaka kowa zaifita cikin farincikin da walwala, duk abunda ake *Umma* ko kadan jikinta ba kwari ko kad'an idan ta matso kusadashi idan yayi magana wani irin wari takeji kamar na gawa, karshe barin d'akin tayi tafito waje gurin mutane ta zauna, hirarsu suketayi Amma sam hankalinta baya wajen. Juyawar da zatayi taga k'ofar gate taga wata mata rik'e da hannun *HIBBAH* idonta ya kada yayija abunka da farin mutum fuskar ma tayi ja alamar tasha kuka. Ashe Auntynsune "yau tunda taje makaranta take kuka akawota gurin *Abbanta* wasu mutane zasu tafi mata dashi". Tunda *Ummah* taji "haka jikinta ya k'ara sanyi". Kamata tayi sukayi d'akinda yake, suna shiga da gudu ta d'ane gadon tana murnar ganin mahaifinta. Haka suka yini yau jikin da sauki sosai, mutane kuwa yau kamar ana turosu.
.
Yau har wajen 11:00pm *Umma* bata tafi gidaba saida *Kakarsu HIBBAH* tayi da gaske kafin ta tafi badon ranta yasoba, tana tafiya tana tuna wasu maganganun mijinta na yau wasu tamkar wasiyace agareta, _"ina rokonki daki bama y'arana tarbiya ta gari"_ _"kobayan raina ki gwadamusu basuda wani uba face kanina"_ _"ban yarda arabamun kan y'a y'anaba"_ _"Kibasu ingattaciyar ilmi"_ _"ki gwada musu zumunci"_ Maganganu dai da dama, magana d'ayace ta tsaya mata arai ta wata y'ar uwansu, lokacin bakowa d'akin duk sun fita sallah *Umma* ta kama hannun k'ofar d'akin zata shiga ta d'auko hijabinta ta cire na jikinta taji matar tana cewa _"Malam sa'adu na bika ta laluma da rarrashi akan ka auri d'iyata_ *Kande* _Amma kakiya shiyasa nasa ahad'aka da ciwon da zaisa ka gangara garin da ba'a dawowa, tunda kamana kyashin cin arziki don haka dole yau kabar duniya, iyalanka kuma sunyi hannun riga dajin dadin rayuwa"_ Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo, yace _"goggo Indo kenan"_ _"batun yauba nasha gaya miki banda ra'ayin mata biyu, matata ta isheni rayuwa tanamin komai, ciwo kuma dakike ikirarin kece sila wannan keda ubangijiki sannan duk abunda ya sami bawa mukaddarine daga Ubangijishi, Rayuwa da mutuwa duk tana hannunshi"._ _"bakida ikon yimin komai nida iyalaina face abunda ALLAH ya tsara mana"._ _"mikewa tayi tace nizan wuce saimunzo zaman makoki"_ Dasauri *Ummah* tabar wajen ta shige bayan gida taci kukanta tasake alola ta fito, tana fitowa taga matarnan cikin jama'a sai rafsa kuka take kamar ba'ita ta gama Maganganunnanba. Haka ta isa gida tanata tunani iri_iri Tana shiga ta sake *Muhammad* d'an wata uku aduniya taje ta dauro alwala sallah ta kwanayi ko gajiya bataji har asuba tayi tagabatar da sallar asuba bata tsaya komaiba ta chanzama *Muhammad* kayan jikanshi ta tashi yaran suyi sallah sannan ta fice sai asibiti kasan cewar ba wani nisa sosai dasu da kafa suke zuwa, tun kafin ta isa taki kirjita sai bugawa yake, gashiyau asibitin yamata nisa. Lokacin data iso taji kirjita ya tsananta bugewa, sai _Innalillahiwa'inna'ilaihirraju'un_ taketa fadi a zuciyarta, tana isa kofar d'akin taji sautin kukan Surukar ta, da sauri ta murd'a k'ofar tashiga abunda tayani yasata daskarewa a wajen, hawayene ya ziraro daga idonta. _Waime *Umman Hibbah* taganine yasata hawaye haka?_ _nayi kokarin lekawa Amma ta tare kofar_
.
Dak'ar na samu na shige ta gefen *Umma* na wuce, abunda nagani yasa na juyo nima ba ashiri, *Ummah* kam tagama mutuwar tsaye. *Abban Hibbah* nagani kwance anrufe jikanshi tundaga k'afarshi har kanshi, ashe tun cikin dare wajen k'arfe uku *ALLAH* ya amshi abunshi. Saida surukarta ta tab'ata ta dawo daidai *KALLAH* ne yata basu hakuri kafin suka samu nutsuwa, angama komai asibiti tabasu gawar, suntattara kayan da sukazodashi Saidai *Ummah* tayi mamakin rashin ganin wasu kayan mijin nata, batadai yi maganaba kuma bata zargi kowama. Lokacin da ta d'aga pillown da yake kwance taji nauyi ta bud'e zip d'in rigar pillown kudi tagani ciki da wani guntun takarda da sauri ta maida ta rufe kasancewar ba kowa a d'akin, sun koma gida ankai *Abbah* makwancinsa na gaskiya _saimuce Allah jikanshi da rahma ya gafarta mishi yasa Aljannah makimarshi_ *HIBBAH* kam lokacin zazzabi ya rufeta dukda tana da k'arancin shekaru, tanada shekara 8 a duniya, *Umma* tashiga takaba saimuce Allah fiddata lafiya yabada ladan ibada. _Bayan kwana biyu_ da rasuwar *Abban* da dare *Umma* ta d'auko wannan pillown ta bud'e ta d'auko ta kardan rubutu tagani kamar haka:
.
_ki hakuri khadija, nasan kinji maganar goggo inda ta fad'a, inarokonki da karkisa abun aranki, ciwona kuma ku dauka *ubangijina* ya saukarminda bawa bazaitaba yin abunda Allah bai kaddaroshiba Saidai yazama shine silar abun, kizama mai yarda da k'addara maikyau ko marakyau don hakan yana d'aya daga cikin halayen musulmai na kwarai yadda da k'addara._ _Sannan bazan gaji da rokonki daki kulamin da yaranaba kibasu tarbiya da ilmi domin shine kawai gatan dazaki musu, iya tsawon zamanmu dake baki ta'ba sabaminba Allah ya miki albarka idan na miki ba daidai ba ina rok'inki daki yafemin, ga kudinan 20k nabakishi halak malak_ _Bana tunanin wannin ciwon zan tashi duk sanda mutuwata ta riskeku ina rok'onku daku zama masu addu'a domin addu'arku nafi bukata ba kukaba_ *Wassalam* *ALLAH HADA FUSKOKINMU GIDAN ALJANNAH* Tana kaiwanan taji wani sabon ciwo akirjinta kayi hakuri fitar hawayena shine samun saukin zuciyarta, nayafeka bakamin komaiba Allah ya gafartamaka ya had'a fuskokinmu gidan Aljannah, insha Allah zan zama mai cikama burinka a rayuwa, haka tayita sambatu batasan iya tsawon lokacin data d'auka awajenba daga karshe ta tashi ta d'auro alwala tayita jera sallolindaba iyaka, washegari akayi addu'ar uku kowa ya watse harda y'an garinsu don bazasu iya zama da *KALLAH* bah sam baida hali. Haka rayuwar tacigaba da tafiya *Ummah* da yaranta sunga chanjin rayuwa sosai da sosai domin *Baffan* nasu ya kankame komai Bayan wata da rayuwarsshi mahaifiyarshima Allah yamata rasuwa, gida yazama abunda yazama kayanda akabari *Kallah* yayi kane kane akai hatta da suturarshi sawa yake, sanda akai rabon gado kuwa shafama idonshi toka yayi yace basuda wani gado don komai nashine Tunda duk wani kadara sunashine ajiki basu wani sami abun arziki ba, haka sukaci gaba da zama wataran abincima sai anga dama ake basu da ummah taga haka bashiri ta kafa murhu d'an kud'in dake hannunta take saya musu kayan abinci, ad'ad'are sukakai shekara agidan tundaga lokacin yatada fi'ilin afita abarmai gida tunda bamuda gado, wulakancin yau daban na gobe daban har abun yakai makura inda ummah ta tattara shirginta sukayi gaba yazauna ya tabbata agidan tunda wanda yayi silar samuwar gidanma yabar duniyan _muje zuwa donjin yadda rayuwarsu HIBBAH zai kasance_
.
*Cigaban Labari*
Tsawon shekara d'aya kenan da rasuwar mahaifinsu *Hibbah* abun mamaki duk abokan arzikin *Abban* kowa ya kama gabanshi hatta wasu daga cikin y'an'uwanshi ba wanda yayi tunanin d'aukarma *Ummah* yaro ko d'aya duk yara biyard'in d'awainiyarsu na kanta lokacin *Sadeeq* na aji shida a primary, *HIBBAH* tana aji uku, *Salman* na aji d'aya, sai *Adam* da yake nursery 1,sai Auta *Muhammad* dake zaman gida, Allah ya taimaka makarantar ta d'auki nauyin karatunsu har sugama dakuma littafan rubutunsu. Kawu Umman shike basu kud'in abun hawa na zuwa idan antashi su tako da k'afarsu kasancewar shima nashi iyalan suna makarantar. Ummah ta yanke shawarar fara sana'a don taragema Kawun nata wani nauyin, kasancewar yanada tarin iyalai yara da manyan matasa wasu sunyi aure wasu shike ciyar dasu ga girma ya kamashi masinjane a babban asibitin bauchi. D'anyen kayan miya ta saro da wake kasancewar ranar asabarne bayan mun dawo daga islamiya ta k'ulla kayan miya d'a ur amin, ya Sadeeq kuma aka izamar kwanon wake Umma tace "maza ku d'an zazzaga dashi cikin unguwa ku dawo, don Allah karkuje ku zauna" "Toh Umma" Muka d'au kayan tallanmu mukayi gaba sanda muka fito kowa yafara raba idanuwa nace "Ya Sadeeq ina zamuje yanzun?" Yace "gidajen zamushiga, Amma ke zaki rinka magana" "tam nayarda muje." Haka muka ta shiga gidaje tallah wasu su saya subamu kud'i wasu suce muje mudawo muna fita shikenan ba dawowa, haka muka rabarda kayan ba wani kud'in kirki tare damu, da yunwar ta ishemu muka garzaya gida.
.
Sanda muka isa k'ofar gida sai akabarmu da ra'be ra'be don kud'in hannunmu ba yawa munma manta gidajenda mukabada bashi, Hibbah tace "yayah kazo mushiga," "idan munshiga mezamucema Ummah?" kafin sukara magana saiga Ummah kamar anjefota da hijab a hannu tana shirin sakawa, tana ganinsu ta fasa sa hijabin tace "kuzanje nema tund'azu, kunfita ba labarinku kundawokuma kun tsaya raka'be raka'be lafiya daiko? " lafiya Umma" "toh kuwuce muje ciki." Wucewa sukayi ciki, bayan sunshiga sunba Umma kud'in da kayan miyar da wake tace "ya haka? Ina sauran kud'in?" Kallon kallo suka farayima junansu Ummata harzuka "Tambayarkufa nake Amma kunmin banza! Nace ina sauran kudin?" "uhm, uhm, asan siya akace muje mu dawo mu kuma mun manta gidan," "shine maimakon kudawo gida tun d'azun sai kuje ku zauna?" "ba zama mukayiba muna zazzagawane." "kun kyauta kuci abinci kuje kuyi wanka kuyi sallah ku tafi islamiya. Haka washe gari Ummah ta d'aura musu tallah baifi gida biyu suka zagaba suka sami waje suka zauna wasunsu, sanda suka gaji suka koma gida ba tare da wani abun karkiba, Tunda taga haka tace ta hakurada sana'ar don ko cikin gidanma ba wani saya akeshigowa yiba. *Bayan shakara d'aya* Lokacin ya Sadeeq ya tafi J. S. S one a makarantar gwamnati dake cikin barikin sojoji yakanje a abun haya ya tako da k'afarshi ga makarantar da d'an karan nisa ba ba yadda zaiyi haka yake fama.

0 comments:
Post a Comment