TUDUN DAFAWA Part 1
.
Na
Ummiee Ja'afar
.
"Dan Allah kiyi hakuri Umma,wallahi ba da sani na ya fashe bah",Bilkisu take cewa cikin shesshekan kuka..
Wacce ta kira da Umma kuwa sai zabga mata bulala take yi ba kakkautawa,"Wallahi sai na ci uban ki yau da uwar ki da ta ke kwance a dakin can,shegiya 'yar iska,ki fasa min tulu sannan kice ba da sanin ki ba!,ja'ira kawai",sannan ta daina dukan ta sai huci take faman yi kaman zaki kana ta shige dakin ta ta bar Bilkisu a wurin.
.
Bilkisu Yarinya ce 'yar kimanin shekara goma sha biyu a duniya.Baka ce amma irin _'black beauty'_ din nan neh..Tana da suma mai dan tsayi da kuma idanuwa fici fici kanana...
Sunan mahaifinta Mal. Idrisu Maikwano,mahaifiyarta kuma Malama Lami Madaki,sannan da uwargidan baban su, Jummai(Umma)wacce dalilin rashin haihuwan ta,Mal ya auro maman Bilkisu...
Suna da zama ne a kauyen Gurmana dake Minna,Niger state...Mahaifin ta yana sana'ar kera kwanuka neh shiyasa aka fi sanin sa da Mal. Idrisu Mai kwano..Mahaifiyarta kuwa tana yin cin cin neh na siyarwa a da kafin ta fara rashin lafiya bayan ta haifa Bilkisu,tana haifan ta ta fita hayyacin ta,ba ta cewa uhm bare uh'uhm,kullum tana kwance a daki,Mal. ne mai tallafa mata har Bilkisu ta danyi wayo a hannun kishiyan ta,Umma sannan Bilkisu ta fara renon mahaifiyarta da kanta..
.
Tunda aka haifo ta baban ta ya tsane ta amma shi bai san Umma tana Muzguna mata ba..abinci sau daya take bata a rana, ga duka da aiki kullum kamar jaki...
Bilkisu ta rasa *TUDUN DAFAWA*,da wanne zata ji,da mahaifiyar ta da bata da lafiya,ko kuma mahaifin ta da ya tsane ta ko Umma da take muzguna mata...Kullum cikin tashin hankali ta ke..
Da kyar Bilkisu ta iya mikewa daga wurin tana hawaye,dakin da mahaifiyar ta ke ciki ta wuce kai tsaye.Tana shiga,jikin Maman ta ta fadi kai tana shesshekan kuka,"Mama ki tashi ki taimake ni, Mama kiyi min magana ko naji sanyi a raina"..
Maman ta sai kallon ta take yi amma komi baza ta iya tabukawa ba,wani kuka mai ratsa jiki Bilkisu ta soma yi kuma,"wayyo Allah kai ne gata na,Na san kai kadai ke so na,Allah ka ba wa mahaifiya ta lafiya saboda na san itace zata so ni bayan kai ya Allah, way...",kafin ta karasa maganar taji muryan mahaifin ta akan ta,"toh munafukar yarinya tashi daga jikin mata ta,muguwa wacce ta illata mahaifiyar ta" ya fadi cikin tsawa..Da gudu ta fita daga dakin tana kuka mai kona rai..
"Shegiya mayya kawai,ki karata can ke da uwar ki,Umma ta fadi yayin da Bilkisu ta gitta ta gaban ta..Da gudu Bilkisu ta fita wajen gidan tana jin dama ba a haifo ta duniya bah.......
Ni kam nace Allah sarki Bilkisu 'yar karama dake amma har duniyan ta ishe ki .......
Tana fita waje ta samu wuri ta zauna ta cigaba da shesshekan kuka har kawarta kuma yarinyar makwabtan su tazo gittawa..Da sauri Bilkisu ta goge hawayen ta don karda ta gane cewan kuka take yi...
"Haba Bilkisu,mai yasa kike son boye mini damuwar ki,iyye??sai kace ba kawar ki ba"..cewan Fatima..
.
Share guntun hawayen da ya karasa sauko mata tayi..."kiyi hakuri,na san halin da kike ciki,kullum ni da umma ta sai munyi zancen ki,karda ki damu komai zai wuce in shaa Allah,baban ki zai so ki,mamanki kuma zata samu lafiya kinji".
Gyada kai tayi alaman eh taji.."toh ni na wuce kawata,sai anjima sannan ta mike ta wuce gida..'Yar albarka!,'ya ta ina kike!,da sauri Bilkisu ta mike taje amsa kiran Umma saboda haka take kiran ta idan Mal na nan don ta tunzura shi..Kwata kwata Mal baya son yaji an kira Bilkisu da 'yar akbarka,ya kan ji tamkar ya fashe...
Karasawa gaban Umma tayi ta gan ta rike da ciki tace je ki gayawa Mal cewa yazo ciki na yana ciwo.. Da sauri Bilkisu ta juya zata dakin shi sai taji ta bangaje mutum..Wani mahaukacin Mari ya dauke ta dashi,tuni ta tsuguna ta fara kuka wiwi.."Muguwar yarinya,wato kina son ki karasa ni yadda kika karasa Maman ki koh?toh wallahi baki isa ba,kur wata kur mayya kawai"inji Mal...ni kam nace o'oh duk ita kadai
..
Goggo kuwa tana gefe tana jin dadi Ana bari ta na jin haushi,daman ta ga Mal a bayan Bilkisu di gan gan tace wa Bilkisu taje ta kirawo Mal..Tana ganin ya jiyo kanta,ta Fara wani murkususu kana tace "haba Mal ka daina yawan yi wa yarinyar ga fada man...",kin ga ba ruwan ki,karda ki kuma abinda zai bata min rai"cewan Mal..
"Toh yi hakuri Mal, kaga ciki na yake matukar ciwo, dan Allah na shirya muje kilinic ( _clinic_)?,"toh shirya mana ina jiran ki"sannan ya juya zai tafi,da sauri Umma tace 'yar albarka zo ki taimaka min na tashi..Da sauri Mal ya juyo ya hankade Bilkisu dake shirin mikewa,"karda ki kuskura ki taba min mata,bace min da gani a nan.. Da gudu ta tashi ta wuce dan karamin dakin ta kamar akurkin kaza..
Umma kuwa wani dadi taji yayin da Mal yayi fam kamar zai fashe..suna fita Bilkisu ta fita da gudu ta je dakin maman ta,ta rungume ta tana kuka,a haka ta sami nutsuwa har bacci Mai dadi ya sace ta..UWA UWACE,KO A WANI HALI TAKE,RAHAMA CE A GARE MU...
.
Mal kuwa suna isa clinic tayi musu bayanin yadda take ji..suka karba fitsarin ta da sauran abubuwan da za a bukata na gwaji..Bayan Awa daya, _lab attendant_ yazo ya sanar dasu cewan cikin wata daya ne gare ta kana ya taya su godewa Allah..Murna wurin Mal da Umma kam ba ya misaltuwa, ace mutum shekara goma sha biyar da aure,amma sai yau Allah ya azirta su da abinda suke ta nema ido rufe,ikon Allah kenan,Mal kuwa saboda tsabagen jin dadi har alkawura yayi mata na cewan duk abinda take so shi za ayi....Haka suke ta tafiya suna hira cikin nishadi har suka isa gida..
Haka su Umma ake ta laulayin gaskiya da karya, Bilkisu kuwa na jin jiki in mal baya nan..in yana nan ta kan dan ji sa'ida ta fannin aikace aikace da yunwa saboda Umma na nuna wa Mal cewa tana son ta...Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa a gidan Mal kullum cikin takura wa Bilkisu'yar albarka har wata tara suka cika....
*Toh Ku biyo ni don jin wani jinsi Umma za ta sambado
Umma ta sambado 'yar ta fara mai kama da ita sak.Murna a wajen Mal da Umma ba a iya cewa komai..
Bilkisu ma tayi murna da zuwan kanwar ta,a tunananin ta zata samu kawa,abokiyar hiran cikin gida in tayi wayo.Amma bata san cewa wannan yarinyar zata zamo annoba ba ne a gare ta...
Duk da murnan da take yi,Mal ya hana ta zuwa kusa da Umma ko jaririyar a cewan shi karda ya shafa musu bakin jini..Makwabta kuwa sai shigowa ake yi ana masu barka..
Ana haka wani dan kasuwa da ya dauki Abba aminin sa yazo masu barka.. Bayan ya dauki jaririyar ya sa mata albarka, ya Kira Bilkisu tazo ta karba jaririyan.
Mallam na ganin haka ya tsuke fuska yayi sauri ya mika hannu ya karbi yarinyar tare da watsa mata harara.Jiki a sanyaye Bilkisu ta juya ta wuce..
"Haba Mal ina zaton kace min kana kula da yarinyar ka yanzu,meh yasa kayi mata haka,kaji tsoron Allah fah,All...","kaga Alhaji ya isa haka,ai ita zaka cewa taji tsoron Allah,don ita ta nakasar da mahaifiyar ta garin haihuwa,ehhe"...
.
"Haba Mal ya kake magana kamar jahili,to gaskiya ni in baka daina ba zanzo na dauke ta na kaita gida na","wallahi je ka,ka rabani da annoba ne ma",inji Mal..Alhaji yace "Allah ya shirya,zan dawo na dauke ta in mun shirya da Mai daki na,sai anjima"..ko Kala Mal bai ce ba,ji yake tamkar ya fashe idan ana zancen Bilkisu....
*Bayan sati daya*
.
Alhaji Uthman yazo daukar Bilkisu..Bilkisu yarinya mai hankali tace fafur ita baza taje ko ina ba,Umma ma ta dage saboda wasu dalilai nata,na daya baza ta samu 'yar aike bah,sannan kuma bata son Bilkisu taje birni idon ta ya bude tazo ta rama abinda take yi mata..
Mal ne ya jajirce yace wallahi ko ta halin qaqa neh sai ta bi Alhaji,ya gaji da ganin ta a nan gidan..Shi dai Alhaji neh ya lallaba ta har ta yarda kana yace wa Umma tayi hakuri kuma Bilkisu zata dinga zuwa masu hutu a man..
"Wa? Allah wadai,meye maraban dambe da fada,nace ka wuce da ita kace zata zo wani hutu, meye amfanin wucewan ta toh,ka ga ko fuskan ta bana son na kara gani,ehhe",Mal yace tare da hada rai kamar tsummar tsohuwa .
"Hmm,Mal kana bani mamaki,lafiyan ka kuwa?",inji Alhaji.."Garau nike Alhaji,ku dai je Ku,Allah ya kiyaye hanya",Alhaji yace ameen,'ya ta zo mu wuce..
Da gudu Bilkisu ta ruga dakin Maman ta,"kaga munafuka,ke! Karda ki kuskura kije kusa da mata ta",Bilkisu koh jinsa bata yi,haka take ta ruzgar kuka har Alhaji yazo ya bambare ta a jikin Maman ta yana mai takaicin hali irin na Mal.
Umma kuwa data cika fam da takaici ta dau jaririyar ta ta shige daki.Haka Bilkisu tabi Alhaji tana mai kukan rabuwa da mahaifiyar ta......
Allah sarki Bilkisu,ban ga laifin ki bah,ba abinda ya kai rabuwa da mahaifa tausayi musamman rabuwa da mahaifiya
*Billionaires quarters*
"Assalamu alaikum",Alhaji yayi sallama ya shigo rike da hannun Bilkisu.."Wa alaikumussalam, Alhaji bakuwar tamu ke ga?"Hajiya ta tambaye sa..
"Eh itace","Allah sarki 'ya ta karaso mana",cewar Hajiya..Sum sum take tafiya har ta kai gaban Hajiya, ta durkusa"ina wuni Anty"..."kul da bakin ki, karda ki kara Kira na da Anty, ki dauke ni a matsayin mahaifiyar ki,oya yanxu meh zaki kira ni??
"Mami",Bilkisu tace a hankali don taji wai ana kiran Mama, Mami a birni.."yawwa that's my girl",inji Mami,"Mami bani da gyale fah"Bilkisu tace.ni kam kyalkyalewa nayi da dariya,ina ruwan Bilkisu anji girl wai gyale .Da sauri Mami ta kalli Alhaji da yake musu dariya,
"Alhaji daman yarinya ga basu sa ta a sch ba da wayon ta haka,"ta tambaya fuskarta cike da mamaki.."ah ya kike magana tamkar kin manta dalilin da yasa na dauko ta nan,wacce ake treating kamar bare a gidan su,ina taga ta schooling"Alhaji ya fadi tare da mikewa,"Toh anyi baby an manta da Mai gida"...
"Haba ya zan manta da oga,bari na gana da 'ya ta,ina nan shigowa",Mami ta amsa tana dariya...Bilkisu dake tsugunne a wurin taji ana zancen sch,lallai tana ganin yaran makota a garin su suna zuwa,ba ma dai kamar gidansu Fatima kawar ta ba,amma kirikiri ita Umma ta hana ta zuwa...
"Toh,'ya ta zo na kai ki dakin ki,anjima yayan ku zai zo ya kai ki ku siya kayan sawan ki sannan gobe za a miki register a makarantar boko da ta islamiya" Mami tace tare da riko hannun Bilkisu,"Nagode Mami"...."shhhh"....
*Alhaji Uthman Barwa*
Wani hamshakin dan kasuwa ne,yana da shagon _accessories da jewelries_,sannan da shagon kwanuka wanda ta dalilin haka ne suka zamo aminai da Mal. Idrisu..
Matar sa daya ce,wato Hajiya Sa'adart amma an fi kiran ta da Hajiya *Adart*,tana aiki ne a hukumar Lura da hakkokin iyali dake nan garin Minna..Ita bagwariya ce yayin da Alhaji Uthman bahaushe ne tsantsa...
Yaran su guda uku ne kuma dukka mazaje..Ja'afar shine dan su na farko,sai Ramlan,sannan Sultan wanda ya kasance autansu..
Ja'afar ya gama makarantar sakandire kenan yana jiran _admission_ a Ibrahim Badamasi Babangida _University_ Lapai inda yayi _applying_ ma _business administration_, yana da kimanin shekaru 18 a duniya kuma yayi walimar saukan Qur'ani a lokacin shekarar sa 14 kasancewar yana da hazaka sosai,shi mutum ne mai son kowa da kuma dauka kowa nashi..
Ramlan yana ss1 neh a makarantar Bilal bn Rabah dake London street,Minna..yana da kimanin shekaru 14 a duniya,shi yake ba su Alhaji ciwon kai a duk family din saboda girman kai da rashin ji da ya sa wa kan shi,gashi babu cigaba a karatun shi na boko da islamiya,kullum sai ci baya...
Sultan kuma yana jss2,yana da kimanin shekara 10 a duniya,kuma ya kusa yin walimar saukan al-Qur'ani saboda shima yana da kwazo..shi da Ja'afar ne suka biyo Maman su sak,Farare kuma kyawawa kamar fillo,kasancewar Mahaifiyar su ba a barta a baya ba wajen kyau........
*Cigaban labari......*
.
Mami ta Kai Bilkisu dakin ta,Bilkisu na sa kai a dakin kawai ta sulale a kasa ta fadi sumammiya...........
*Ni kam nace toh? Wata sabuwa......,mu hadu a shafi na gaba,don jin me ya sanya Bilkisu ta suma
Abin ya matukar firgita Mami,da sauri ta dibo ruwa a bathroom na dakin...tana yayyafa mata ta tashi za tayi waje da gudu Mami ta rikota.."wai lafiyar ki Bilkisu?, nice fa Mamin ki...."wayyo Mami ina ne nan?ta fadi tana rike Mami....
Nan Mami ta dago cewa tsoro dakin ya bata ,ta kyalkyale da dariya..."Kai Bilkisu a kwai wauta daman saboda dakin kika suma",kada kai tayi alamar eh..Mami ta dafa kafadarta kana tace,"in ban da abinki,ai bazan kai ki inda zaki cutu bah,nan dakin ki ne,matso nan"..
"Kinga wannan,wurin kunna fitilar dakin kenan, wannan kuma na fanka, wannan kuma na A.C mai sa daki sanyi"..Haka Mami take tayi mata bayani game da abubuwan dake dakin..Bayan ta gama,sai ta fita..
Bilkisu dai bin dakin take yi da kallo..Komai na dakin pink ne harda fentin kuma da gani bai dade da akayi fentin ba..Zama tayi kan lallausan gadon tasa hannu tana shafa bargon da aka shimfida kai.Hawaye na ga ya zubo mata kan fuska.Ni kam nace ko meh ya sa take hawaye?
Sai naji tace "ya Allah ka ba wa mahaifiya ta lafiya,ya Allah ka ganar da mahaifina gaskiya,kasa ya so ni,kasa ya gane ina bukatar soyayyarsa a matsayin mahaifina,ya Allah kasa zama na a gidan nan ya kasance alkhairi a gare ni,Allah ka saka musu da alkhairi, ma tausaya musu yadda suka ji tausayi na,ameen...
Bilkisu yar baiwa,karamar yarinya amma ga kaifin tunani da basira...Mikewa tayi ta shiga bayi,ta bude shower yadda Mami ta nuna mata,ta watsa ruwa kana ta bude famfo tayi alwala ta fito...
Gaban mirror taje ta dauki _hair conditioner_ ta narka wa jikinta,sai walkiya take yi...kana ta dauki riga da hijabin da ta gani kan gadon ta sanya sannan ta shimfida darduma..Tana son tayi sallar azahar amma ta kasa gane alqibla,haka dai tayi sallan..
Bayan ta idar,mikewa tayi ta bi lafiyar gado,barci mai dadi ya dauke ta a sanadiyyar AC dake ratsa ta ta ko ina..anjima kadan Mami ta leko ta, ta ganta ta na narkar bacci,tayi wani baje2 ta bararrake kan gadon..Murmushi Mami tayi ta rufo kofan ta na Mai cewa "Allah sarki 'ya ta...
Mami na isa falo naji ta ce"toh kanwar taku ma barci take yi abin ta,anjima kwa gaisa.."Toh Mami Allah ya kaimu anjiman"a cewar Ja'afar.."mtssssw,haka kurin an kawo wata bare tazo ta dinga takura wa mutum a gidan nan"inji Ramlan..
"Kul da bakin ka ko nasa yayan ka yayi ma dukan tsiya yanzu,wai kai wani irin yaro ne iyye,toh ka jira Abban ka ya dawo sai ka gaya mai ya kore ta,kai ka ma je ka Kore ta yanzu in kai ke da gidan,yaro da tsiwan tsiya,Allah ya shirye ka",Haka Mami ta cigaba da bambamin ta,karshe ma mikewa Ramlan yayi ya wuce abin shi a zuciyar shi yana cewa" _I will make your life miserable_ shegiyan yarinya kawai"...
Ja'afar ne ya bawa Mami hakuri da yaga har muryan ta ya fara sarkewa alamar kuka zata yi,yace "Mami dan Allah karda ki zub da hawayen ki kan Ramlan,kin san zub da hawayen iyaye wa yaran su in sunyi abu marasa dadi bashi da kyau..Mu cigaba da yi Mai addu'an Allah ya shiryar dashi"..
.
"Toh Ja'afar nagode,Allah shi yi maka albarka","ameen Mami, bari naje na huta,yau na sha _huzzling_"ya karasa maganar yana dariya,"je kaci abinci tukun my son",cewan Mami.."Toh Mami na", ya fadi tare da mikewa ya wuce _dinning area_..Mami kuma ta mike ta wuce daki tana mai gode wa Allah da ya bata da mai share mata hawayen ta......
Zuwa la'asar Bilkisu ta tashi daga barci,tayi addu'a sannan ta mike ta shiga bayi,tayi tsarki sannan ta dauro alwala ta bada farali..Tana idarwa ta nannade sallaya sannan ta fito daga dakin domin taje wurin Mami...Ji kake tummmmm!!..........
*Toh,ko wa ya fadi haka,kuma meye sanadiyyar faduwan wannan,,ku biyo ni don samun amsoshin ku*
Ji kake tummmmm!!,Bilkisu ce ta fadi sanadiyyar kafa da Ramlan yayi mata..Kokarin mikewa tayi amma sai ta kuma jin saukan mari, a razane ta mike ta shiga dakin da gudu ba tare da taga fuskan wadda ya mare ta ba...
Ramlan kuwa wani dogon tsoki yayi sannan ya shiga dakin ta,"hey you local champ!!kadan kenan kika gani,wallahi sai na sa rayuwar ta kasance a very miserable one!! Ya karasa zancen shi tare da bugo kofar da karfi yayin da ya fita..
_*"Allahummak fineehim bima shi'eta"*_,shine kawai abinda Bilkisu take fadi tare da kuka mai cike da tausayi,"Umma na kin gani koh,shiyasa nace miki ba zan zo birni ba,amma suka tursasani,Umma babu mai so na,ya zanyi da rayuwa ta???"...
Sai da tayi kuka mai isan ta,sannan tayi a mahaifiyar ta addu'an samun lafiya..Bandaki ta shiga ta wanke fuskar ta saboda bata son Alhaji da Mami su gane tayi kuka saboda ta san su tsakani da Allah suke son ta..
Amma waye ne wannan da ya zabga mata wannan rashin mutuncin daga fitowan ta,meh tayi masa da har yayi mata irin wannan muguntan??tambayoyin da take ta jefa wa kan ta kenan wacce tasan bata da amsoshin su...
Fitowa tayi daga dakin ta sauko kasa domin yamma yayi,tana son taje ta taya Mami aiki a kicin..Gashi bata san ina ne kicin din ba..Dudduba wurare ta fara yi tana addu'a a zuciyar ta karda ta hadu da mugun da ya mare ta...Ni kam nace Bilkisu karamin yaro ne fa kamar ki,karda kiji tsoron shi amma kamar na kara ingiza ta ne ma....
"Ke ce kanwar tamu?",da sauri ta juyo saboda jin muryar shi da tayi a bayan ta...Ja'afar ne ta gani a tsaye yana mata murmushi..Daga kai tayi alamar "eh".Murmushi ya kuma yi kana ya ce "sannu da zuwa kanwar mu, shin mene ne sunar ki?","Bilkisu",ta amsa a takaice..
"A'a,toh?,kice min su Bilkisu Mai gadon zinari ce ashe?? Maganar tashi ya bata dariya har ta dan murmusa.."ni kuma sunana Ja'afar"...Murmushi kawai tayi..Nan Ja'afar ya gane ita ba mai yawan surutu ba ce,unlike others.."Toh ina zaki je?","Mami nike nema,ban gan ta ba"....
"Toh in banda abin ki,ai dakin ta zaki je ki duba","ban san dakin ba",cewan Bilkisu.."toh muje na kai ki"...Sadaf sadaf take bin shi a baya har suka kai dakin Mami..........
Daidai bakin kofar dakin Mami ya tsaya yayi knocking tare da yin sallama.Daga ciki Mami ta amsa sannan ya shiga Bilkisu na biye dashi."Surprissse!!!",yace wa Mami yana murmushi sannan ya matsa domin taga abin da ya boye a bayanshi wato 'Bilkisu'...
Dariya Mami tayi kana tace "kai Ja'afar, Allah ya shirya min kai"..Da sauri yace"ameen,gashi na kawo miki 'yar ki,a falo na gan ta wai tana neman ki"...Dariya Mami ta kuma yi sannan tace " 'ya ta zo ki zauna oh,'yar albarka har kin farka daga bacci ashe"....."eh Mami"...
"Toh wannan shine yayan ki Yaya Ja'afar, shine zai kai ki makaranta gobe domin ayi miki rijista".."Su yarinyan Mami za a makaranta",inji Ja'afar.."kai,karda ka takura min 'ya fa","haba Mami,ni a wa?wai dan wake a super market",dariya sosai Mami tayi har Bilkisu ma sai da ta murmusa.Ja'afar kuwa tamkar bashi yayi maganar ba...
"Kai Ja'afar ba zaka kashe ni da abin dariya ba,you're so funny my child,"dan Allah ka kula min da 'ya ta,she is like a daughter to me,ka san yadda nike bala'in son Allah ya bani diya mace,gashi kuma Allah ya kawo min har gida,dan Allah karda ka bari Ramlan ya muzguna mata,haka zalika karda ka bari Sultan ya raina ta,ka taimaka mata da abubuwan da take bukata musamman ta fannin makarantar boko da islamiya"cewar Mami....
"Karda kiji komai Mami, in shaa Allah zan bata kulawa tamkar kanwa ta, ta jini,anything for you Mami".."yawwa, that's my boy...ina alfahari da kai,Allah ya kare min kai,ya Kara maka wadatar zuci..ke kuma Bilkisu, ki ba wa yayanki girman shi,banda rashin kunya kuma kisa ido a karatu sosai domin nan gaba zai amfane ki,sannan ki rage sa damuwa a zuciyar ki,duk lokacin da kika tuna iyayenki,ki dinga yi musu addu'a ne,kin ji koh 'ya ta"...
"Eh naji Mami, nagode,Allah ya saka da alkhairi".."shhhh,oya tashi muje ki ci abinci kafin na girka na yamma","a'a Mami ba zan ci komai ba,da muke hanya Abba ya siya min abinci naci".."toh shikenan,Ja'afar in baka da wani _schedule_ da yamman ga,ka dauke ta a mota kuje yi yawo domin ta ga yadda garin yake",inji Mami.
...
"Ok Mami, muje koh 'yar lele?",cewan Ja'afar... Mikewa Bilkisu tayi suka sallami Mami,dawowa Ja'afar yayi kuma"Mami nace ko na kai ta shopping gabadaya?","eh lallai kam kayi tunani mai kyau tunda bata da kayan kirki na sawa,bari na dubo ma credit card dina"ta fadi tare da mikewa...
"A'a Mami ki bar credit card din nan,ina da isasshen kudi a hannu na wanda Abba ya bani last week,zai ishe mu in shaa Allah".."oh Allah Sarki,Allah shi yi maka albarka dana,maza jeka yamma na kara yi,please karda kuyi dare fa"...
"Ok Mami",sannan ya je falo ya jira Bilkisu da taje dauka silifas dinta..tana fitowa ya bude mata kofan falo suka fita zuwa parking lot,wata farar mota mai kyau ya ciro ya bude mata kofa ta shiga sannan ya sa mata seatbelt bayan ta rufe kofan kana yaja motar suka fita daga gidan.......
_Bomaz supermarket_ ya kai ta bayan sun gama zagaya anguwar su...Wurin kayan mata suka shiga,ya fara zabo mata kaya masu bala'in kyau,su English wears,jallabiya,Arabian gowns,Indian wears,atamfa,lace da shadda kala uku uku....kaya dai bila adadin ya siya..
Sannan suka shiga bangaren takalma,ya daukan mata guda takwas da na makaranta guda hudu,ya Kama goma sha biyu,sannan suka shiga bangaren kayan ado,dankunne da sarka kala biyar ya daukan mata da wrist watch uku sannan da make up kit da mayukan jiki da su turare....
Kai komai da ya kamata mace mai irin shekarun ta tasa,sai da ya siya mata hatta underwears..Sannan suka jibgi kayan zuwa mota bayan ya biya kudin kayan.Bilkisu kuwa tsoro ya Kama ta,irin wannan kashe kudin...hmmm nan da nan ta tuna Maman ta,ta fara kuka a hankali,da yake Mami ta bashi labarin komai game da ita, sai ya fara lallashin ta har tayi shiru sannan suka je _Safara foods_ ya siya mata ice cream da cupcakes sannan suka wuce gida....
Mami da Abba sunji dadi matuka ganin yadda Ja'afar ya kashe wa diyar su kudi,suna ta suburbuda mai albarka..Mami ta jera mata kayan da kanta a daki tare da yi mata bayanin yadda zata dinga amfani da su shampoo,man shafawa,kayan kwalliya da sauran su sannan ta kwashe su atamfa,lace da shaddan domin ta bawa telan ta...
Zuwa karfe shida Sultan ya dawo daga islamiya,"Assalamu alaikum, _Mami I'm bacmkk!!_..ya fadi tare da shiga kicin.Turus yayi ganin wata a gefen Mamin shi.." _Mami who is she??_","yayan ka ce sultee na"inji Mami.."okkaayy!itace wacce kike bamu labarin ta wai zata so?".."Eh Sultan"..
"Oh..sannu da zuwa yaya"..murmushi ta sakan mai kana ta rungume shi,haka kawai taji dadin ganin tsaran ta a gidan..Sultan shima yaji dadin samun sister saboda duka abokanan shi suna da sisters,saboda haka shima ya shiga layi...Jakkan shi ya dauka zai tafi daki ita kuma don yaranta ta bishi,suna kai wa daidai bakin kofar dakin Sultee...Aka daka mata tsawa..."kee!!!"...a razane suka jiyo.......
...
Ramlan ya daka mata tsawa,"ke dawo nan,ina zaki je"!!..."Bro raka ni zata yi"cewan Sultee.."raka ka?,yau ne ka fara zuwa daki kai kadai,c'mon get in!!",da sauri Sultee ya shiga daki yana kuka..Bilkisu itama ta juyo da sauri zata koma kasa ya finciko ta _"where do you think you are going to??!"_..Bilkisu dai kuka take yi har da kakkarwa....
Dakin shi ya shiga da ita sannan ya zauna a bakin gado,"oya ki fara frog jump",inji Ramlan.Tsayawa tayi tana kallon sa saboda ko kashe ta za ayi, bata san meh yake nufi da wannan yaren ba..Tsawan da ya daka mata ne yasa kukan ta ya tsanan ta..
"Kalli nan,durkusa,mike,durkusa,mike...."haka zaki dinga yi ko na zabga miki belt din nan",ya nuna mata wani skin belt,haba wa da sauri Bilkisu ta fara yi,tana yi tana kuka,tayi shame shame da majina abin tausayi..Ni kam nace karamin yaro amma sai masifan tsiya,just 14yrs amma sai girman jiki....
Ta kai kusan minti talatin tana abu daya, sannan yace tayi tukin babur (shima punishment ne).."Dan Allah kayi hakuri,ba zan kuma ba"...tassss! Kake ji,karan belt da ya watsa mata,take ta saki wani irin Kara...
Da karfi aka budo kofan dakin dayake bai rufe ba..."innalillahi wa inna ilayhirraji'un",abin da Mami ta fadi kenan tana ganin ta'addancin da Ramlan keyi wa Bilkisu.."Ja'afar!! Ja'afar!!!,zo kaga abinda yaron ga ke yiwa 'ya ta",ta karasa maganar cikin shesshekan kuka..
Ja'afar na isowa ya shiga dakin,"subhanallah!! _Are you stupid_, _are you insane!_, _are you...."_wani lafiyayyen mari ya sauke meh a fuska.."kai wani irin yaro neh,meh tayi maka?, _what did she do to you,answer me!!_"..
Shiru Ramlan yayi kamar ba dashi ake yo ba saboda ya san halin yayan nashi.."dazu fa take tare dani muna aiki a kicin,shine Sultee ya dawo ta bishi,ina ta ihun sunan ta amma naji shiru ashe tana nan tana shan ukuba..Allah ya shirya min kai,'ya ta taso mu tafi"...amma shiru bata amsa ba,lokacin suka lura da fitar numfashin ta..Da sauri Ja'afar ya sunkuce ta sai mota yayin da Mami ta biyo su a guje da hijabin ta,ta shiga baya in da ya kwantar da ita... Da gudu ya ja motar suka Kama hanyar asibiti da ita yayin da take kwance lamo tamkar matacciya a jikin Mami...
*hmmm..Allah sarki Bilkisu, Allah zai saka miki
.
Suna isa Nurses suka zo suka karbe ta,sai ER..In banda salati babu abin da Mami keyi,"mai zan ce wa Alhaji in abu ya sami yarinyar nan??"...
Ja'afar kuwa sai zuwa da dawowa yake yi,duk hankalin shi a tashe,zuciyar shi kamar zai faso don tsabar bacin rai da yake ji...Bayan awa daya likita ya fito,da sauri Mami da Ja'afar suka karasa kusa dashi..."Doctor lafiya,'yata ta farfado??",Mami ke tambayar sa a rude..
"Eh ta farfado amma Ku biyo ni ofishi na domin mu dan tattauna",inji likita...Ya juya,yana tafiya Mami da Ja'afar suna biye dashi..Bayan sun shiga,yayi musu nuni da kujeru dake gaban teburin shi yace su zauna..Zama suka yi sannan likita yayi gyaran murya ya soma magana...
"Toh a gaskiya 'yar ki tana da wani dan matsala da bai kamata ace tana dashi ba don qarancin shekarun ta..Don haka shine nike son na san musabbabin hakan,shin me ake yi mata ne da ya kai ga sawa 'yarki hawan jini?.."Hawan jini??!!",Mami da Ja'afar suka fadi lokaci daya.."eh hawan jini take da wanda kuma bai kamata ace tana dashi ba saboda karancin shekarun ta"..
"Inna lillahi wa inna ilayhir-raaji'un!, ayya 'ya ta ai dole ki samu hawan jini ko don ja'irin da ya muzguna miki ba tare da kinyi masa komai ba,in shaa Allah likita zamu kiyaye,baza mu dinga barin a bata mata rai ba",cewan Mami."Toh madalla,sannan a raba ta da duk abinda yake firgitar da ita saboda firgici ne yasa ta suma,please a kiyaye",likita ya fadi...
"Toh in shaa Allah, mungode likita",Ja'afar yace..."yawwa Ku gode wa Allah,ga wannan magungunan a siya mata,wannan"ya fadi yana nuni da sunan wani magani,"shi za dinga bata kowani lokaci jinin ta ya hau kafin Ku kawo ta asibiti".."toh Allah saka da alkhairi, zamu iya tafiya da ita yanzu?"inji Ja'afar..
"Ameen,eh zaku iya tafiya da ita, babu matsala in shaa Allah","toh sai anjima likita"suka fadi tare da mikewa bayan ya kira wata nurse cewan ta kai su inda Bilkisu ta ke..Suna isa suka ganta zaune a kan gado tana hawaye.."ya ta kiyi hakuri,ki yafe ni ki yafe ni ki yafe min",Mami ta fadi tare da rungume ta tana hawaye..
Rungume Mami tayi tana kuka mai karyad da zuciya.Ja'afar da sauri ya juyar da fuskarsa saboda saukan hawayen da yaji akan kuncin sa,ya bala'in tausayawa Bilkisu, karamar yarinya kamar ta amma wai tana da nawan jini??..hmmm,yayi ajiyar zuciya kana yace da Mami su zo su wuce gida,isha'i ya gabato..gashi ko maghrib basu yi ba..
Hannun ta Mami ta riko suka fita zuwa wurin da ake fakin motoci,suka shiga motar su,Ja'afar ya tuka su zuwa gida..Suna isa daidai ana sallame sallar isha'i,kai tsaye dakin ta Mami ta kaita sannan ta sauko zuwa dakin ta itama..Ja'afar shima yaje dakin shi don bada farali.
Bilkisu dai gode wa Allah tayi,domin tana tunanin lokacin mutuwar ta ce yayi,ba ta son ta mutu ba tare da ta neman wa mahaifiyar ta lafiya ba.Mikewa tayi ta tube kayan ta,ta shiga bayi ta wanke kanta fes sannan ta dauro alwala ta fito,bayan ta shafa mai, ta ciro wani jallabiya mai shigen rigar bacci ta saka,sannan ta dau hijabi ta sanya taje dakin Mami domin har yanzu bata gane ina ne alqibla ba.
Tana isa daidai Mami tana tada kabbara,sai ta yi maza ta tada kabbara ita ma.Suna idarwa suka yi addu'a sannan Mami ta juyo tana kallon ta da murmushi shimfide a fuskarta,'ya ta,ya jikin ki?",Mami ta tambaye ta tare da shafa kuncin ta,"alhamdulillah garau nike jin kaina Mami",cewan Bilkisu.."toh masha Allah, Allah shi albarkaci rayuwar ki Bilkisu na","ameen Mami, nagode da kulawar ku, Allah ya saka muku da alkhairi","ameen 'ya ta,ai da na kowa ne,oya tashi muje muci abinci"..Mikewa suka yi zuwa kicin..
Kulolin abinci suka kwaso,suka jera a kan dinning table sannan Bilkisu ta koma ta kwaso plates da robunan wanke hannu..Kana Mami ta bata abincin baba maigadi ta kai me..Zama suka yi kan kujeran dinning suna jiran Alhaji da sauran yaran..Ja'afar ne ya fara saukowa,sai Alhaji da Sultee suka y sallama suka shigo da alaman yanzu suka dawo daga masallaci..Ramlan shine na karshen fitowa..Kowa ya hallara a dinning kana Mami ta tashi zata yi serving,Ja'afar yayi saurin mikewa ya karba,murmushi Mami tayi ta bar mai,shi yayi serving kowa,suka ci suka koshi..
"Rabin rai,ina kuka je ne wai,da na dawo Sultan kadai na cimma a gida,yace shima ya fito daga daki ne bai gan Ku ba",cewan Alhaji.."hmm,asibiti muka je","asibiti??!,waye bashi da lafiya?",nan Mami ta labarta wa Alhaji dukkan abinda ya faru.Wani irin kallo Abba(Alhaji) yayi wa Ramlan,"kai wane irin yaro ne wai fisabilillahi!,meh yarinyar ga tayi ma?...meh tayi ma nace??!!.."Ab..bba..dakin Sultan fa na..na..naga zata shiga fa!,"dakin Sultan din dakin uban ka ne!,nace dakin uban ka ne!!?,"a'a Abba amma..","will you shut your mouth up!,ace yaro yayi laifi ayi masa fada ba za ya karbi laifin sa ba,kai wane irin yaro ne?",Ramlan ya wani murtuke fuska kamar hadarin kaji ala ana mai fada kan bare..
"Toh yau shine na farko kuma na karshe,in ka kuskura ka bari na kara jin ko da tsinke neh ka taba ta,sai ka yaba wa aya zakin ta,stupid kawai!",/"Abba kayi hakuri",cewan Ja'afar.."kai baza kace Abba yayi hakuri ba koh?!"..."Abbo yakuri",Ramlan ya fadi ciki2.."Allah ya shirye ka",Abba ya fadi yana mai takaicin halin yaron sa...
.
"Bilkisu na,zo nan",mikewa tayi jiki a sanyaye taje wurin Abba,bata ji dadin fadan da aka yi wa Ramlan a gaban ta ba.."kiyi hakuri kinji,ba zai kuma ba,kuma gobe zaki fara zuwa school in shaa Allah".."toh Abba nagode"....Mikewa Ramlan yayi ya wuce dakin abin sa,kowa ya bishi da idanu kana suka karkada kai lokaci daya........
Washegari,Mami ta sa Bilkisu ta shirya tsaf cikin jallabiya da dan karamin hijab..Wuraren karfe bakwai suka gama breakfast,dukkan su suka fits parking space..Abba da Mami suka shiga mota daya inda Abba zai ajiye Mami a wurin aikin ta sannan yaje ya duba shagunan shi..Ja'afar kuma ya shiga motar shi,ya bude ma kannen shi kofa domin su shiga,yace wa Bilkisu ta zo mazaunin gaba.Nan fa Ramlan ya soma kumbure2 kamar kumurci ya zauna a mazaunin baya shi da Sultee...Sallaman baba maigadi suka yi sannan yaja motar sai Bilal bn Rabah Islamic School,London street..
Suna isa, ya mika wa kowannen su #200,Ja'afar ya kasance mutum ne mai wadatan zucci." _thank you_ yaya",cewan Sultee."shh bana hana ka ce min thank you bah?","ohhh! Na manta neh,jazaakallahu khairan yaya"cewan Sultee..."yawwa my boy,a yi karatu fa,Ramlan a rage taurin kai",kwafa Ramlan yayi sannan ya juya ya wuce abinshi, Sultee ya bishi a baya...
*_Galaxy international schools_* da ke chanchaga suka wuce kai tsaye bisa ga umarnin Abba, yace ba zai hada su a makaranta daya ba..Suna isa ofishin _headmaster_ suka nufa kai tsaye inda Ja'afar yayi masa bayanin ya kawo sabuwar daliba ne kuma yana son a sa ta a class da ya dace da ita...
Jin yawan shekarun ta yasa shugaban makarantar yace za a sa ta a aji na 3(wato primary 3) zuwa nan gaba in tana da kokaro sosai,sai ayi mata tsalleken aji zuwa jss1.Sannan yace a saman mata _lesson teacher_ wacce zata dinga zuwa har gida domin koyar da ita abubuwan da aka koyar a ajujuwan da suka gabata..Godiya yayi sannan ya biya kudin makaranta da na litattafai da uniform a ofishin bursar dake kusa da na headmaster..Bayan ya gama,yayi sallama da principal da cewan Bilkisu zata fara zuwa sch washegari...
"Kanwa ta,ina kike son muje yanzu tunda sai gobe zaki fara zuwa sch",a cewan Ja'afar da yaga shirun yayi yawa."uhmmm,nima ban sani ba yaya",Bilkisu ta amsa.."toh bari muje yawo ta G.R.A gidan kanwar Mami","toh"..Hanyar by-pass suka bi sai GRA dake gefen _government house_,gaban wani tamfatsetsen gate suka yi parking,sauka yayi daga mota bilkisu ta fito itama..Kulle motar yayi kana ya kwankwasa gate din,sai da maigadi ya dau kusan minti biyar sannan yazo ya bude gate din..
"A'a Alhaji Ja'afar ne a gidan?",maigadi ya fadi yana washe baki,"eh nine fah,ya kwana biyu","lafiya lau,wace ce wannan kuma?","wallahi yarinyar aminin Abba ce,tana zama damu neh","oh...to..to..to..to,yayi kyau,yayi kyau,Ku karasa ciki suna nan,sannu yarinya","ina wuni baba",Bilkisu ta gaishe shi,"lafiya lau,Kin zo lafiya?","lafiya lau","toh madalli jeki,a fito lafiya"..karasawa suka yi zuwa falo, Ja'afar yayi sallama ya shiga sannan Bilkisu ta shiga itama..
"Oyoyo bros,idon ka ke ga??",wata budurwa kusan age mate din Ja'afar ta fadi tana saukowa daga bene.."wallahi nine fah,ya naga baki wuce sch ba bayan Xahra ta gaya min kin samu admission?","eh,ka san nan FUT na Bosso campus zana dinga lectures,so I choose to stay at home kawai na dinga zuwa lectures daga gida tunda Mommy ta siya min mota kuma","uhm yarinyar Mommy kenan",inji Ja'afar..
"Wace ce wannan kuma??"ta tambayi Ja'afar tare da yatsine fuska tamkar kashi ta gani..............................
0 comments:
Post a Comment