AMININ KWARAI Page 1-10
.
Na
Hauwa Hassan Nayaya
Gargadi gareku barayin basira duk wanda yayimin editing din novel koya sauya sunan,Ban yafe ba.
1⃣to5⃣
Kwance take kan makeken gadonta tayi daidai da kafafunta sai chatting data duqufa take,gashi sai faman murmushi take,jifa jifa kuma takan tuntsire da daria,hakan ya tabbatar da cewa tanajin dadin chatting din datake yi.
Al'adan Nasrin kenan inhar tana chatting da NY.
Ta maida hankalinta gaba daya ga wayan har batasan lokacin da mum tashigo dakin ba ji kawai tayi an fizge wayar a hannunta ay kuwa ba shiri ta juyo,sai duk kunya ta kamata,cewar mum,haba nasrin tuntuni kitashi ki yanka vegetables dinnan kinqi,kin shigo daki kin boye abinki sai faman hira mara amfani kike,bari Naufal yadawo xansashi kawai ya kwace wayar kowa ya huta,ay kuwa caraf nasrin tace haba mum pls kar muyi haka kinsan fa inayin duk aikin da kike sani fa sannan naga veggies din ba yanxu xaayi amfani dashi ba shiyasa banyi himman yi ba amma kiyi hkr xan tashi yanxu nayi,dan Allah kar kisa yaya naufal ya kwacemin waya pls mum,haba sweety ta I love u mum😘.Abin ma baiwa mum daria yayi tace to naji uwar iya magana da dadin baki wuce muje,Nasrin ta tashi tabi mum yayinda take godewa Allah a xuciyarta da baza asa yaya naufal ya kwace wayanta ba domin tasan tsaf xai iya.
Suna aikinsu a kitchen gwanin shaawa suna hirarsu yayinda mum ke tambayarta nasrin niko kinsan da irin mutanen da kike chatting kuwa?kinsan duniya ta baci yanxu,ta waya zaa iya batamiki tarbiya,abaki maita,asaki a abubuwa da dama,shin kinsan sharrin dake tafe da abubuwan nasara kuwa,uhmmm nasrin haryanxu ke yarinya ce,ki nutsu ki kula ki kiyaye ki yawaita addua tunda kin maidawa kanki chatting din yazama kmr ibadah,murya a sanyaye nasrin tace naji nagode sosai mum,insha Allah xan kiyaye Allah kara girma,mum tayi murmushi ta amsa da Amin.
*************
Asalin sunanta Nasrin Nazir Yunus,Ya' ta uku gun Alh Nazir da Hajia Nazifa,Naufal Shine babban dansu mai binsa kuma Nawas,sai Nasrin,Nabil sai auta Najwa,Asalinsu yan garin kano ne,amma a jos suke da xama a dogon dutse,Alh Nazir yanada kudi ba laifi,saidai duk da wannan bai bar ya'yansa sun tashi cikin rashin kwaba ko tarbiya ba,yaransa sun tashi cikin tarbiya da kaunar juna.
Naufal shekarunsa biyu kenan da gama karatu harya fara aiki,duk da yanada burin komawa yayi phd dinsa,Nawas kuwa yana final yr a Cambridge university dake london,yayinda nasrin ke final yr a secondary,nabil na jss3 auta najwa na primary 5.......wannan kenan.
Aman jini take tayi ba qaqqautawa saidai tayi mai isarta sannan ta daina,ta galabaita matuqa yanayinta duk ya sauya,hawayi daya nabin daya kamar famfo,Tayi wanke bakinta yayinda tayi flushing jinin,cikin muryar kuka me cike da damuwa nasrin ke cewa Aisha ya kikeso inyi da raina pls kibar bani hkr,nasan son NY ne xai kasheni,gashi bazan iya sanar mishi ba,Aisha in all indication ciwon xuciya na gab da kamani,tun yaushe nake DAKON SON NY?yaqi ya fahimta,lallai so ciwo ne,son maso wani.....bata karasa magana ba tare ya sarqeta sai amai kamar ranta zai fita.
Firgit ta farka daga mafarkin data kirashi mummuna,duk ta jike da zufa,tuni ta fara karanto addu'oi,ta dade a zaune tana addua tukun daga bisani ta koma ta kwanta cikeda mamakin mafarkinta duk da dai tasan tanason NY,fatanta Allah yasa yanajin me takeji game dashi.
Wai ma waye NY dinnan ne?????
Kubiyoni don sanin waye wannan handsome guy din😜dajin darasin da novel din ya kunsa....
Gareka na sadaukar da book dinnan yayana kuma aminina Nasir(Abu farhan)a duk inda kake ina maka fatan alkhairi.
.
Bayan an tashi daga school ne Nazira tace xata bi Nasrin gida domin ta nuna mata pic din NY,nan da nan nasrin ta hade girar sama data kasa,keee😳😳har saida nazira ta tsorata,meye hadinki dashi,kar kiga kina kawata idan har sunan NY bai fita bakinki ba to wlh kisani kawancen mu na dab da xuwa karshe👀👀ido nazira ta gwalalo a zuciyarta kuwa cewa take"gaskiya wannan NY ga dukkan alamu first class ne,bayan duk big guys dakeson kula nasrin bata kulasu amma wannan yasamu miqamin da ba wanda yasamu,dole nasan waye NY,inya min inmiki kwace inkin san wata bakisan wata ba"a fili kuwa nazira yaqe tayi😀tace kawata abin bai kai haka ba,Allah barku tare,Nasrin ta tabe bakiðŸ˜tace dadai yafi miki,bro dinmu yaxo daukan mu sai gobe✋ðŸ¼
Da suka isa gida ma nasrin daki tayi ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita,karar wayanta ne ya farkar da ita ta kalli agogo biyar da rabi😳lallai tasha bacci,a hasale ta daga wayan domin mai kiran bawani dasawa suke da ita ba tunda ta fahimci manufarsa a kanta,"hello yaya nasim barka da yamma",ay kuwa caraf ya amsa"barka dai sweet sis,na missing wannan baby voice dinki,hope duk kuna lfy,ðŸ˜ðŸ˜a daqile ta amsa lfy lau,yayita xuba ita dai sai cewa eh ko aa,ahaka tace mai xata kitchen ta taya mum aiki tun dawowarta school take daki,yayi mata sallama badon yaso ba.Ta jingina da pillow yayinda tafara tunano abubuwan rayuwa na ban mamaki da tausayi da dai sauransu,lallai Allah,Alhakim ne,duba yadda nasim ke sonta ita ma takeson wani,lallai wannan shine SON MASO WANI(littafin my khairat,luv u)ni kuma ummu arif nace koshin wahala ba😜.
😢😢hawaye ne yafara bin kuncinta,Ya Allah kasa na cinye wannan jarrabawar,Haqiqa so dafi neðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜(koni jidda na tausayawa nasrin)tana fama da DAKON SO(littafin kausar luv).
A haka Nabil yazo yasameta,yace adda nasrin mummy nakira,lallai kinsha bacci,har hajiyan su ya nasim taxo ta tafi😳nasrin tace da gsky yace wlh kuwa,tace tashi muje,da gudunta ta isa parlor gun mum,tagaisheta,mum ta amsa fuska a sake,tace ya naga kmr kinyi kuka,nasrin tayi yaqe wanda yafi kuka ciwo tace mum fa daga barci natashi shiyasa kikaga idona sunyi ja,mum wai hajyan su ya nasim tazo?mum tace eh,Nasrin ta kumace meya kawo ta???
Mum ta watsa mata harara tace shaqeni in fada miki,😞nasrin tace Allah baki hkr,ta tashi tai kitchen abinta ta hado tea ta haye sama abinta.
Asalin sunansa Nasim Aminu,mahaifinsa Alh Aminu abokin baban nasrin ne sosai tare suka taso,zumuncin su yaci gaba
Hakan yasa matansu da ya'yansu ma suka kulla abota,Sunan babar nasim Hjya Amina,Nasim shine dansu na biyu,yanada sis Nasima,sai twins dinsu Amir da Amira,sai Auta Amna.
Presently yana masters dinsa a mahatma gandhi university dake ghana inda ya karanci cardiology,tun nasrin na karama yake sonta amma yaqi furta mata shi anashi ganin abu ne mai sauqi,Nasim bafa sauqi inji ummu arif😜
***************
Lokaci na tafiya, soyayyar NY na karuwa kowanne rana a cikin xuciyar nasrin,yayinda kawancensu yaja baya da nazira domin nazira kishin nasrin take akan NY duk da batasan waye shiba(wahala girl)
A bangaren nasim ma hakan take,kullum son nasrin karuwa yake a ranson yayinda yake gani daya sanar da dad dinsa komai xaixo da sauqi,Ita kuwa Aisha saida tasan yadda ta janyo nasrin ajiki domin hakikanin gaskiya itake sonta tsakani da Allah ba nazira ba,inda suke gudanar da kawacensu mai ciki da amana da so da kaunar juna😊.
Lokuta da dama NY yakan tambayi nasrin yaushe xatayi aure,amsarta koyaushe daya ce"KAI NAKE JIRA"(littafin humaida)
Amma shi gani yake wasa take mishi,baisan cewa hakikanin gaskiyarta take fada mishi ba,
😢 kwalla ne kebin kuncinta yayinda ta tuno haduwarsu ta fari da NY,Ranar da baza ta taba mance taba,Tai murmushi tace ya Allah kaciremin son NY a zuciyata na huta(nima ummu arif nace ya Allah yaciremin son tuwo a zuciyata in huta😜),ta share kwallah yayinda ta nufi bandaki don gabatar da alwalar isha'i,nima ummu arif Ina biye da ita nace nasrin pls yaushe zaki fadama waye NY????Juyowan da zatayi naga hawaye ya wanke fuskarta ba shiri nabar dakin don nasan na fama mata inda yake mata ciwo,To wai waye NY dinnan neðŸ˜ðŸ˜
Masu karatu kucigaba da biyoni😊
Taku a koyaushe
.
Washe gari ya kama saturday ne,ba skul nasrin tun bayan datai sallan asubah ko karatun ma data saba yi batayi ba takoma bacci ba ita ta tashi ba sai wajen 10:00 na safe,ta tashi tayi wanka tasauko kasa.
Mummy tagani ita kadai a parlour sai kuma hayaniyan su najwa data jiwo a dadin yaya naufal,ta durkusa tagaishe da mum dinta sannan ta nufi dakin yaya naufal shima tagaidashi yayinda su najwa ma suka gaisheta,ta amsa cikin sakin fuska,caraf najwa tace Aunty Nasrin kinata bacci har Abba yayi tafiya,yace inkin tashi a gaisheki inya isa xai kiraki,tace ina yaje,Nabil yace kano yaje tace to Allah ya kaisa lfy ya kiyaye hanya dukkansu suka amsa da Amin,sannan ta nufi kitchen taje ta hado breakfast.
Takoma falo tazauna tafara cin abincinta yayinda mummy hankalinta ke kan tv tana kallon tashar MANARA TV,yadda ake baiwa nakasassu kafafu da hannaye,Nasrin ma shidin tafara kallo,tace umma gaskiya Shiekh Abdullahi Bala Lau yana taimakawa Al'ummar musulmai dayawa Allah dada taimakonsu yasa da niyya me kyau sukeyi,jiifa wai harda Christian da shia ma,Mummy tayi murmushi tace nasrin ay amfani ilimin da kudi kenan Allah yaqara musu himma da budi yasaka musu da mafificin alkhairi,nasrin ta amsa da Amin(nima jidda nace AMIN)
Nasrin bayan tagama breakfast duk da dai bawani abinci kirki taci ba tashi tayi takoma daki tafada gado,yayinda tunani biyu suka addabi xuciyarta,Nafarko shine meyasa Taga Aisha a mafarkinta alhali Nazira ce babbar kawarta,asalima bawani magana da Aishan suke ba,Na biyu kuwa shin dagaske ne son NY shi xai kaita ga halaka,in hakane gara tun wuri tasan abin yi.
Can kuma ta tuna ay mafarki ba gaskiya bane,ta tabe bakiðŸ˜
Tace komadai meye Allah yasa alkhairi ne.
Yinin ranar tayishi ne a daki har mummy ta fahimci tana cikin damuwa,Ta tambayeta tace kanta ke ciwo ta bata magani tasha tai mata fatan samun sauqi.
Da dare
Wayanta ta dauko ta kunna domin yinin ranar qin kunnata tayi,Ay kuwa saqon farko daya fara shigowa wayanta bai wuce na NY ba take taji wani farin ciki at same time baqin ciki,sai hawaye ta goge yayinda tafara karanta message din:
"Slm N-square,me yayi zafi yau najiki shiru,kodai sub ya karene,dama naji ance bashi kike ci kiyi sub din😂to wai dolene chatting din😜inafata kin yini lfy,NY"
Tazauna akan gado tayi dariya ma'ishiya kafin ta bude sauran text din,Tagama budewa tas sannan tai murmushi tace waima mexance da NY ne,saita fara replying kamar haka
"Wkslm,na yini lfya NY,inafata kaima haka,Ay ni in takaice maka sim dina special sim ne,bansa kudi banyin sub,amma haka nake kira da surfing net nonstop,nikadai akayiwa irinshi😎
Ay sub saiku😀"
Tana sending mishi tayi saa yana online ay kuwa sai yayi replying
"Hhhhhhhhhhhhhh
Sannu Zubaida👉ðŸ½ðŸ˜‚"
Itama tai replying
"Yawwa ZubairuðŸ˜,ya yau?"
haka dai hirar tasu ta cigaba cikin wasa da dariya,Nasrin dai ta tabbata son NY take domin duk sanda take chatting dashi,hatta magana bataso ayimata,saita tsinci kanta cikin nishadi da annashuwa,Anya zata iya rayuwa ba NY kuwa???(ni jidda nace tabbas xakiyi,tunda ba tare kukazo duniya baðŸ˜)
Wannan kenan..
Yau takama monday,Nasrin da wuri suka shirya bayan tayi waya da abbanta takuma turawa NY monday text(monday text😳ni ummu arif nace aiki yaganki yarinya)Sukai sallama da mummy yayinda Yaya naufal ya debesu ya ajiye kowa a makarantarsa shima ya wuce gun aikinsa.
Bayan anfito break ne nasrin ta kira kawarta nazira gefe ta labarta mata mafarkinta,tabe baki nazira tayi tace nasrin Who's this NY please,murmushi nasrin tayi wanda yake kara fiddo da kyawunta sannan tace Nazira I doubt if the combination of 26 alphabet can explain NY,cikeda da mamakin nasrin naxira tace uhmmmm abin naki babba ne,amma zanso in ga wannan NY din daya samu babban matsayi a xuciyarki ko kuwa ma ince a rayuwarki,for the second tym nazira takara cewa nasrin please who's NY,murmushi nasrin takuma yi tace yarinya zancen kikeso(wai anci da Abu farhan ya iyali😜)kinga tashi mu tafi class an ringing bell,Suka tashi suka nufi class duk da dai ba haka nazira taso ba,nima ummu arif nabisu a baya nace Nasrin pls Who's NY,juyowa tayi ta watsamin wani kallo,ay ba shiri nasha jinin jikina,kafa a sanyaye nabar wurin😞
Waye NY???????
Gaskiya sai masu karatu sun biyani xan fadi waye NY,ku gafa daga tmbya taimin kallon raini,xandai bita a hankali harsai munji waye NY😜
.
Washe baki Nasim yayi,ban dade da zuwa ba,nazo daxu baku nan shine nadawo,nabil yace kina bacci,nace kada ya tadaki,inkin tashi ma gaisa.
Kakalo wani murmushin dole tayi tace likita bokan turai,hope ka dawo lfy,Allah yasa angama a saa,Ya amsa da Amin cikeda jin dadin maganganunta.
Haka suka cigaba da hiran da mum da naufal,jifa jifa dai nasrin takansa baki,Bayan sun dawo daga sallan isha'i ne xasu je dinning cin abinci,nasrin tayi sama keee,cewar yaya naufal ina zaki😡tace watsa ruwa xanyi,mum tace bawani nan,xuwa dai xatayi tayi hira da maso wani,dam nasim yaji gabansa ya fadi,ita kuwa da gudu tayi daki..
Naufal ne yadawo table din ya zauna yace mum make things obvious to me,Mum ta numfasa tace Naufal ina matuqar tausayawa nasrin,domin da dadewa ta fada son wanda baison tana sonshi ba,ta dade
Tana dakon sonsa,maimakon abin yayi baya sai gaba yake,saidai bata taba sanin nasan halin datake ciki ba,amma ina tayata da addua.
Naufal a sanyaye yace mum waye wannan wanda takeso?shiko nasim mutuwar xaune yayi,ji yayi abincin yadawo mishi kmr magani,Mum tace ba kowa bane illah Nasir,Wanda yake xuwa dinnan,har ku gaisa tace frnd dinta ne,Naufal yace tabbas nagane shi,Nasir na burgeni mum bana fada miki ba,gashi ga dukkan alamu yasamu tarbiya,Allah sarki sis,SON MASO WANI KOSHIN WAHALA,Allah ya zaba mata abinda yafi alkhairi,Mum ta amsa da Amin Nasim ko cewa yayi bro tashi karakani gate natafi kaina na ciwo I need to rest,Mum tace nasim abincin fa,yace mum wlh nakoshi,kwanciya kawai nakeson yi,tace Allah ya sawaqe kagaida hajiyanka,yace to a hasale,naufal ya rakashi yaja mota sai gida.
Dukkansu basu lura da halin da yake
ciki ba,saidai sunyi mamakin tafiyansa.
************
Nasrin result yafito sai murna take,tana dada godewa Allah,ta hada walima a gida ta gayyaci yan'uwa da abokan arziki ciki harda NY.
A filin gidansu akasa canopy da chairs akayi decoration,wurin yafito yayi kyau sosai,Dashike Saturday ne ba aiki har abokan yaya naufal dana dad saida sukazo.
Taro yayi taro,wuri yayi kyau,ga abinci nan iri iri,uwar taro kawai ake jira,
can sai gata tafito sanye cikin doguwar riga kirar dubai yellow ce mai adon ja da baki ajiki saita nade kanta da bakin kashka mai adon yellow ajiki,tasa takalmin vinci da wata yar ubansun purse baqi,tayi simply make up tayi kyau matuqa,tana fitowa wurin aka hau tafi ahaka taje ta dinga gaisar d abokan abba dana yaya naufal da kuma kawayen mum da sauran yan'uwa.
Kafin taje tasamu wurin da aka tanadarmata ta zauna,kusa da ita wani sit dinne anyi shimfidar alfarma kmr nata,bakowa ta tanadarwa gurin ba illah NY domin yace da ita yana hanya.
Nan aka fara walima,Mlm sani shine yazo yafara yayi wa'azi mai ratsa jiki mai taken duniya budurwar wawa,sannan mlm khadija tazo tayi nata da dai sauran mallamai,gaskiya kowa ya qaru sosai,sannan jama'ar gurin sunyiwa nasrin da iyayenta addua sosai,Bayan nan ak fara ciye ciye da shan abubuwan sha,daidai lokacin ne NY yaceda nasrin gashi a bakin gate dinsu,ay kuwa cikeda da zumudin son ganin NY tanemo Nabil tace yaje ya taho da NY,yace lah adda nasrin dama zaizo,nandai yaje shigowa dashi yayinda MC yace kowa ya nutsu domin babban bakon Nasrin xai shigo wanda yataso tun daga wani gari xuwa nan don ya tayata murna,Yana shigowa tareda nabil kowa yayi kabbara yayinda murmushin fuskan NY ya fadada,Nabil yakaisa yagai da abbansu da frnds dinsa sannan yaje yagaida mum da frnds dinta,su yaya naufal da frnds nashi sukazo suka gaisa,yagaida sauran yan'uwa sannan nabil yakaisa mazauninsa tun kafin ya iso ya hangi nasrin azaune ta fadada murmushinta,sai yaga tayimishi kyau da kwarjini,ita ko jitayi kamar taje ta rungumeshi,yayi wani kyau da fresh ga sajensa ya kwanta luf,har yaje yazauna nasrin ta tafi wata duniyar tunani,saida ya matso daf da ita ya hura mata iska saitayi firgit,yar jos tunanin me kikeyine,kinga nafi gayun jos kyau koh😜tasa dariya,tace waima wayace kasa irin kayana yellow shirt,black trousers,watch shoes,answer meðŸ˜budan bakin NY yace yanxu nake shirin kiran nabil in akwai boutique nearby ya rakani in sauya kaya,dukkansu suka kwashe da dariya,tace NY baka da dama,nan suka gaisa tamishi godiyan halartar walimanta,NY gaskiya kacika alkawari,ngd kwarai matuqa,yayi murmushi yace haba nassy bby wat are frnds for,common let's cheer up,Nan aka kawo musu abinci iri iri,sukaci suka sha yayinda suketa tsokanar juna,Inka gansu xaka rantse masoya ne,(what a perfect match inji ummu arif👌)yan'uwa da abokan arziki duk sun xaci masoyane sai xuwa suke suna yimusu hoto,wasu suce perfect match,wasu suce romeo and Juliet da dai sauransu,NY dai bai kawo komai cikin ransa ba.
Aka gama cin abinci aka yi pics aka baiwa nasrin kyauta mai yawa,NY ma baa barshi baya ba yayimata kyautar wani sarka da dan'kunne na gold da wani Qur'ani izu sittin da wasu littafai dasuka shafi mata,taji dadi matuqa,iyayenta ma haka.
Nandai NY ya rufe taro da addua,kowa yafara haramar tfya gida ciki ko hardashi,yayi sallama da iyayenta da yan'uwa,har bakin motarsa kirar 4matic ta rakashi,NY ngd sosai,words can't express my gratitude to you,am most appreciative,Allah bar xumunci,yadda kaxo lfy Allah ya maidaka gida lfy,Thanks alot,yayi murmushi yace mrs godia nike da godia,irin karramani da kukayi,nagode ko nassy bby,sai munyi waya,ya daga mata hannu yaja motanshi yayi gaba,ta dade a tsaye tana murmushi kafin tayi cikin gida,shigarta keda wuya saiga cousins dinta sun taho a guje Nasrin kardai shine angonmu,kallonsu take cikeda murmushi yayinda hawaye ya wanke mata fuska😠sun fama mata inda yake mata ciwo,tashi tayi a guje tayi cikin gida ta haye sama sai dakinta ta murda key,Hasbunallahu wa ni'imal wakin kawai taketa fada,daga bisani ta daga hannu sama cikin shashekar kuka tace Ya Allah ka ciremin son NY a zuciyata na huta.
Ta goge hawayenta taje tabude kofa domin knocking ya dameta,Aisha ce da wata cousin dinta,a tare sukace nasrin pls waye NY????
Tayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,tace ummu arif naganki a labe shigo kuji waye NY,ay da gudu na karaso nazauna,yayinda nasrin tafara da NY........
.
Nasrin exams ya matso har sun fara practical,saboda haka duk wani damuwa tayi kokarin watsi dashi domin tasamu damar yin karatu saboda burinta bai wuce ace tayiwa waec da neco one sit ba,saidai duk watsi datayi da damuwoyinta NY na nan daram a ranta,wannan addua kawai takeyi.
Gashi ya karfafa mata gwiwa sosai don yanaso taci wannan jarabawar,domin duk sanda yashaida mata zaiyi jarabawa adduar datake mishi ko kannensa iyakaci,shiyasa shima baiyi kasa a gwiwa ba wajen yimata addua,domin data fadamishi xata fara exams nasiha da adduar dayayi mata ko yayanta naufal iyaka,kullum saita karanta text dinnan don dadinsa da takeji ga abinda ya rubuto mata nan kmr haka
"Nasrin ina mai matukar tayaki murna don ganinki a wannan matsayi,domin akwai dubu masu so sukai wannan matsayi har su rubuta SSCE amma ba dama,wasu sun fara sunada burin gamawa Allah ya karbi ransu,Wasu basuda halin biya,wasu iyayen naso amma ya'yan sunqi su maida hankali da dai sauran jarrabawa makamanta haka,kinga ko dole kiyi murna muma masoyanki mu tayaki,Sannan kada ki sanya rauni cikin xuciyarki ko wani tsoro ko fargaba kidauka cewa yadda kike rubuta normal exams haka xaki rubuta wannan ma,kuma ki dada addua kan yadda kikeyi,Abune na mai saa,Ina miki fatan farawa lfy da gamawa lfy,Allah yasa ku fito da kyakkyawan sakamako ba sakewa,Allah ya sakawa iyayenku danamu baki daya da gidan Al-jannah..
Bst of luck,NY"
NY ya sake samun matsayi babba a xuciyar nasrin.Ahaka dai har suka fara exams suka gama,Alhamdulillah,sunyi lfy sun gama lfy,Saidai nasrin tace sai sakamako yafito zatayi walima,yan iyayin ajinsu kuwa tuni an shirya walima,ita ko ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,Adduarta kullum Allah yasa suga Alkhairi.
***********
A yaune Nasim Aminu ya diro naija domin ya kammala karatunsa cikeda doki dason ganin nasrin,Direba na dauko sa daga airport yace ya wuce dashi gidansu naufal,yayi rashin saa nasrin ta tafi islamiya naufal baya nan,yagaida hjya ya wuce gida rai duk abace,yana isa dayaga mum dinsa yadda take haba haba dashi saiduk bacin ran yatafi,suka sha hira yaushe gamo,daga bisani ya tashi ya tafi side dinsa wanda angyara mishi tunkan yadawo,yaje yayi wanka sai bacci....wannan kenan...
Nasrin nashigowa gida daki ta nufa,ta kunna wayanta tanaso ta fadama NY cewa tagama exams lfy,domin tunda tafara exams yanayin chatting dinsu yaja baya domin yanaso ta nutsu tayi karatu,cikin saa kuwa taganshi online💃ðŸ»murna kamar me a gunta,
Nan tace mishi
"Slm Ma'abocin tsokana da barkwanci"
Ay kuwa nan yagani yayi murmushi sannan yayi mata reply kmr haka
"Wkslm mallamar tsokana da barkwanci ay koyi muke daku😜"
Dariya tayi sosai tukun ta kara cema
"Zaka fara koh😞,ay ngd,kamantani kwatata"
Dariyar shima yayi tukun yace
"Haba nassy baby na isa na manta dake,nabarkine kiyi karatun exams,kun gama ne???"
"Tace eh mun gama tun last week,muna jiran sakamako,hope kana lfy ka buya abinka,ko kudinka sun zo ne😜 "
Yace
"Hhhhhh kudi tukunna dai,ina lfy wlh,hope kema haka,gskya ina miki murna sosai na kammala exams dinki,Allah yasa kuga alkhairi,Nasrin inaso indan miki wani tuni,kinga ke mace ce,kuma iya gata iyayenki sun baki,saboda haka kada kisanya burin yin wani karatun boko mai tsayi,darajar ya'mace gidan mijinta,don haka inhar iyayenki sunyi miki maganar aure ki amince ki fidda mijin aure don samun kwanciyar hankalinki da nasu domin aure bai hana karatu muddin mijinki xai amince kicigaba,inma karatun suka miki maganar kicigaba,ki fara,sai kiyi aurenki kina cikin yi,amma kada kice saikin gama zakiyi aure,sannan kicigaba da xuwa islamiyarki domin ilimi addinini sau dubu yafi ilimin boko musamman gake diya mace,wacce wataran xaki xama maiyiwa ya'ya tarbiya,don haka ki dage gun neman ilimin addini shine abin ado ba boko ba,boko nan duniyane kawai,amma na addini na lahira ne,Sannan ki xamana mai cigaba da yiwa iyayenki biyayya,domin sun cancanci komai a gunki,infact u can even sacrifice your happiness for theirs as a good child,Iyayen sunsha gaban komai,pls ki nutsu kada ki biyewa kawayen xamani,duk da dai nasanki da wayau😜
Daga karshe ina miki fatan alkhairi a ko yaushe kmr yadda kikemin,Nasrin me cin bashi tayi sub😂😂😜"
Lokacin da nasrin tagama karantawa saida tayi kwallah,ji take kmr tace NY kai nakeso,amma takasa ta share hawayenta tayimai reply kmr haka
"Bansan iyakar godiyar dazanma ba NY,gaskiya kacika
🌹Aminin kwarai🌹
Nagode sosai,Allah ya saka da alkhairi,Fatan dakaimin,inaima fiye dashi,Ngd,Ngd,Ngd,Allah bar xumunci,Zanje nataya mum aiki a kitchen,ltr"
Murmushi yayi daya karanta yace Nasrin sarkin godia
"Nassy beb meye na godia,wat are frnds for,common karki damu,ki godewa Allah,agaida mum,ltr"
Haka dai nasrin ta kashe data d tasauka a whatsapo cikeda kewar NY,badon taso ba saidan inta cigaba da hira dashi a yadda takeji a tym dinnan xata iya fallasa sirrin xuciyarta gareshi.
Jiki a sanyaye ta tashi ta gangara parlour,amme wazata gani😳😳😳
NASIM,saukar yaushe ta furta a sanyaye....
,
A bangaren nasim kuwa,shirun da yayi bawai ya hakura da maganar nasrin bane,saidai mugun nufin daya kudirta yimata abisa bin gurbatacciyar shawarar abokinsa Bahar.
Hajiya ta bashi hkr acewarta wani hanin ga Allah baiwa ne,Domin bataso babansa yaji maganar nan because xai iya batawa da amininsa akan wannan maganar,amma me???
Nasim tuban muxuru yayi jira yake kawai Dad dinsa ya dawo ayita ta kare..
Wannan kenan
A yaune gidansu nasrin suka tashi da murna da farinciki kasancewar Nawas ya kammala karatunsa yau xai diro Nigeria yayinda Abba da naufal suka tafi Kaduna daukosa.
Mum dasu nasrin kuwa ana kitchen anata shirya abincin saukar Nawas,Nasrin ta xage domin tafi shaquwa da nawas akan naufal,nawas nasonta matuqa,shiyasa itama take sonsa,saidai tana baqin ciki saura kwana uku ta tafi skul.
Karfe biyar daidai na yamma su Abba sukay iso,suko su mum tun 4 suka kammala komai,gida sai qamshi yake,kowa yayi ado kmr masu xuwa biki😜Nasrin tayi ado cikin riga da wando pink da black,ta gyara gashinta tasa band pink,sai tayi kyau tafito kmr yar larabawa.
Ay kuwa tanajin horn itane tafara fita a guje,Tun kan naufal yayi parking nawas shima yafito ya taho gun yar kanwarsa abin kaunarsa,ya rungumeta qam kmr wani xai kwaceta,saiga su najwa da nabil ma,duk suka rungumeshi suna murna,nawas saida yayi kukan farinciki yace"indeed no place like home😊"
Nan suka shiga cikin gida,Abba yace su nasrin yau an mance abba,nasrin tai murmushi😊tace Abba kenan xancen kakeso.taje tahadama nawas ruwan wanka,tafito mishi da kaya mara nauyi sannan tafita taje suka shirya abinci bayan sunyi sallan isha'i.
Nawas nafitowa daga wanka yaga kayanshi already anfito mishi dasu,ga dressing mirror dinshi anshirya komai yayi murmushi yace lil sis I love you😘.
Kowa yafito ya hallara a Parlour domin yauma baa dining xaa ciba a tsakar parlour aka baje komai,Nasrin na maqe da nawas acewarta shixai bata abinci a baki yadda yake mata da,Abba yace Nasrin wai bakisan kin girma bane,tace Abba jst for today,nawas ma dariya yayi yace mudai kar a samana ido,Ahaka yadinga ba nasrin abincin abaki shima yanaci har suka koshi,naufal koh ya qula matuqa,yace da nawas tadai kusa tafya skul bare ka sangartar da ita irin daðŸ˜
Nawas qala baice mishi ba,mum na hira da Abba,shiko naufal da najwa da nabil suketa hirarsu,nasrin kuwa da nawas,sai kusan 11 suka watse a parlour nasrin ma bacci tayi,nawas ne yakaita dakinta ya shafeta da addua shima yayi nashi dakin.
Washegari sai ten ya tashi,yayi wanka yashirya yayi breakfast,yace su nasrin su shirya ashiga gari dashike Saturday ne,ay bada jimawa ba suka shirya sukaiwa umma sallama suka fita abinsu,nasrin ce a gaba sai najwa da nabil a baya yayinda dukkan su sukai dressing cikin milk and Brown,sunyi kyau abinsu,musamman nawas domin duk gidan shida nasrin sunfi kyau.
Yawo dai sunsha shi,sunje recreational centers iri iri,banda gidajen abokan nawas,sukai shopping sai sukayo gida ana kirayen kirayen magrib.
Ay kuwa sunayin dinner sai bacci dukkansu.
Washegari sunday Ranar da nasrin xata tafi makaranta,dama tuni mum tashirya mata komai,ta tashi jiki duk a sanyaye,tayi wanka tayi breakfast sama sama tashirya cikin wata doguwan riga casandra,tayi kyau duk da batai makeup ba,Su yaya naufal suka sa kayanta cikin mota yayinda idanunta suka kawo ruwa,taje tayiwa mum sallama bayan tasha kuka har saida tasanya mum kwallah,mum tayi mata nasiha sosai tafito nabil da najwa suka yo kanta da gudu suna kuka,ta rungumesu itama kukan take,dakyar naufal ya cirota daga jikinsu yasata a mota,suka ja suka tafi.
Naufal ke tuqin,dad na gefe nawas da nasrin na baya,nawas nata aikin lallashi,har mutuniyar tai bacci.
Cikin dan baccin ne datayi ne tai mafarkin NY yanata mata murmushi,itama murmushin takeyi mishi,ya matso daf da ita yace nasrin yau xan sanar miki abinda kika dade kinaso kiji daga gareni NASRIN ina......
Firgit ta mike,nawas ya riketa yace lil sis lfy,tai mishi murmushi tace eh lfy lau,A xuciyarta ko dadi taji gameda mafarkin nan ko kuwa me,itada tasan duk da ta nesanta kanta daga NY,tasan cewa sonshi na nan daram a xuciyarta,Shin NY zai iya zama nata,wata zuciyar tace eh nasrin,ay baa yanke kauna da rahamar Allah,Nasrin ta numfasa tace wato soyayya halittace,Ya Allah kazaba min abinda yafi alkhairi gareni,saiji tayi duk yan motan sunce amin,ashe xancen xuci yafito fili,Saitayi lamo kamar mai bacci
Sadness is
.
.
.
When the person you love,love someone else💔😢
Shin son NY na barin nasrin,me nasim yake shirin mata,kodai suna aure da NY,don jin yadda xaa kaya,kucigaba dabin jikar NAYAYA,Mrs Abdul 😊
.
Zeenat ce cikin wata irin banxar dressing batada da maraba da irin ya'yan christian dinnan,nasrin mamaki ne ya kamata sosai,xeenat ina xaki a daren nan???cewar nasrin
Wlh wani birthday din friend din Zaks zani,karki kulle kofa,inkin gama ki kwanta,nina wuce bye✋ðŸ¼
Nasrin sake baki tayi takasa cewa uffan,lallai xeenat tana cikin rudin duniya Allah ya shiryata da masu hali irin nata.
Shirya komai dazata bukata wurin xuwa skul gobe tayi,Tai Addua ta kwanta cikeda kewar yan gidansu da tsantar son NY.
************
Nasrin batasan yaushe xeenat ta dawo ba,ita dai ta tashi sallan Asuba taganta,Bayan tai sallah tai Karatu da Azkar,kitchen tashiga tahada breakfast tafito tai wanka,sannan tazauna taci abincinta ta koshi tayi dressing cikin wata jar doguwan riga hade da mayafinta tadau jakarta ta fita.
Tafita kome ta tuna kuma ta koma taje ta tashi xeenert,da kyar ta tashi domin daren jiya tasha syrup shiyasa ta makara,Nasrin sallama kawai ta mata tayi cikin makaranta.
Tana isa bakin lecture hall din saida ta tsaya tayi addua takuma godewa Allah da lecturer din bai iso ba,Ay kuwa tana shiga bayan tazauna saigashi duk da dai a tsarge take bisa ga kallon da students din ke mata,amma kuma saita basar tacigaba da sauraron lectures abinta.
Yinin dai sunyi shine a gajiye from one lecture hall to another,kasancewarsu na sabbin dalibai dole su gaji.Sai 4 suka kammala lectures din ranar,Agajiye ta isa hostel ta bude daki kasancewar xeenat bata nan, tea kawai tasha sai bacci.
Bata tashiba sai 7,da gudu tasauko tayi toilet tai alwala tayi sallah tana kan sallayan aka kira isha'i tayi tukun ta tashi ta nufi kitchen ta daura indomie ta nufi toilet again don yin wanka.
Tafito taci abinci tayi waya dasu Abba sannan tayi bitan karatun ta,11 nayi ta kwashe books din tahau gado tai addua sai bacci har lokacin ba xeenat ba alamanta.
***************
Ahaka nasrin tacigaba da rayuwarta cikin jami'a,duk nacin yarinya hakuri take domin nasrin taki ba Kowa fuska shiyasa batada qawa,inbanda xeenat da Daki ya hadasu gashi tana iya kokarinta na nunawa xinat cewa rayuwar data dauko ba mai billewa bace,amma xinat turn deaf ears to all that nasrin is saying to her,amma duk da haka bata gaji ba tana cigaba fatanta kullum Allah ya shiryata.
Kullum sai tayi waya da mahaifanta da yan'uwanta,NY kuwa yazo sau biyu kawo mata xiyara,xuwansa na biyun ne yayi mata sallama xai tafi kasar waje don yin wani two year course,Nasrin tayi mishi fatan alkhairi da farawa lfy da gamawa lfy,Allah kuma ya kikaye hanya.
So tun sanda ma yatafi sau daya kawai sukai waya because yanxu bata chatting saita koma jos,ita nesantar ta ma dayayi yamata dadi,Amma duk da haka son NY na nan daram xuciyar nasrin😢💔
A haka nasrin harta shafe shekaru biyu a skul tashiga na uku.
In anyi hutu brothers dinta ke xuwa daukota sumaida ta,Nasrin an waye😜in xata koma skul ba kukaðŸ˜da wasa da dariya😀take barin gida.
Bangaren Nasim kuwa ya zauna ya zurfafa tunani,inhar ya cutar da nasrin Allah bazai barsa haka ba gashi xai bata zumuncin iyayensu dasuka dade sunayi,bayaga haka gashi da sisters mata,sakayyar nasrin xata iya sauka kansu ko daya daga cikinsu😞
Da wannan tunanin nasim ya janye duk wani abu daya kudirta yiwa nasrin,sannan yayi alkawari bazai sanar da dad kan maganar ba,zai hakura Allah ya bashi mafiyintaðŸ‘ðŸ¼(ko kaifa nasim inji jidda)ðŸ‘ðŸ¼
Nasrin ce xaune a daki tagama assignment kenan xata tashi ta daura girki saiga xinat tashigo a buge,ita tarasa xinat wata irin diya ce asalima batasan me take karanta ba.ta tabe bakiðŸ˜tace Allah ya shiryata ta taimaka mata tahau gado sai bacci.
Exam yazo nasrin karatu take ba kakkautawa,cikin ikon Allah tafara a saa tagama a saa,Nawas yazo ya dauketa randa sukai hutu,Murna agun nasrin kmr me domin almost four month kenan rabonta da gida.
Suna isa cikin jos saiga kiran NY cikeda xumudin sonjin muryarsa ta daga ji tayi yace slm,nassy bby gani a bakin hostel dinku kifito😳😳😳
Da gaske kake NY ceawr nasrin,,,,,,,,,
Ina fata masu karatu suna jin dadin karatu,kucigaba da saurarona,taku a koyaushe Jikar NAYAYA,Mrs Abdul.
Asalin sunansa Nasir Yahya,haifaffan dan garin kaduna ne,shine da na farko a wurin mahaifansa,shiyasa suke matuqar sonsa,yanada kanne maza da mata,Bangaren tarbiya kuwa,koni daba gari daya muke ba na jinjinawa mahaifansa ballantana ace gari daya muke,indai tarbiya ne kam👌Allah yasakawa mahaifansa da gidan Al-jannah,domin hakikanin gaskiya yasamu tarbiya ba kadan ba.
Bangaren ilimin addini kuwa sai sam barka👌Domin NY mahaddacin Qur'ani ne da wasu littafan addini da dama,anma har yanxu nema yake,as it was said"learning never end"Bangaren bokon ma baa barshi baya ba wooo domin hes a smart philosopher,shiyasa yake matuqar so da girmama mahaifansa,domin sunyi mai dukkan gata.
Bangaren hali kuwa,A iya sanina dashi baida wani hali mara kyau,Chocolate colour ne shi,baida tsayi sosai,yanada dara daran idanu sannan ga saje daya kwanta luf gefen fuskarshi,bakinshi da hancinsa👌baida kiba sosai inyayi dariya gefen kumatunshi ya lotsa hakan na matuqar karamishi kyau,yadai hadu kmr jar fure🌹,ma'abocin wasa da dariya ne,zai fadama gskya komin dacinta,zai baka shawara ta gari,zai jaki da wasa da dariya don rage miki damuwa,inkina cikinta,uhmmmmm sisters to cut this long story short the combination of 26 alphabet can't explain NY😊😊😊
.
Nasrin ta goge hawayen fuskanta tace haduwata dashi nafari ko ince ranar dana fara ganinsa. .....
Tsaye nake a bakin titin tudun wada lokacin gabannin magriba narasa keke napep ga wani baqin hadari,hankalina yatashi matuqa,ga wayana ba charge bare in kira gida yaya naufal yazo yadaukeni,ina tsaya inata tunanin yadda xanyi har bansan sanda mota ta tsaya a gabana ba.
Ji kawai nayi ana yam'mata lift ne,Na leko nace aa mlm ngd,har yayi gaba anfara yayyafi sai gashi yadawo,yace sister pls kishiga i mean u no harm,I just wanna help,ga ruwa gaki mace wurinnan is not safe,kishiga kidaina jan aji karya tsinke,Nayi murmushi nashiga yaja muka tafi,saida yazo terminus yace ina muka nufa nace dogon dutse yace to madam shiru shiru,murmushi nayi nace kaikuma ogan surutu ba😃
Yace am Nasir Yahya,ni dan kd ne jiya naxo jos gobe xan koma,nasrin tayi mamaki kwarai dataga yasan jos din😠tace am Nasrin Nazir,ni yar jos ce,amma dai kana zuwa jos sosai ne,yace well gskya saita kama,tace ok nice meeting you,yace same..
Nayi tamishi nuni har kofan gate dinmu yayi parking,kafin na fita saida yamin nasiha,amatsayina na diya mace nadaina kaiwa dare a waje its a risk,nace mai sam bankaiwa dare yauma dai kaddara ne kawai,namai godiya muka exchanging phone numbers,na mishi fatan alkhairi nashige gida.
Mafarin friendship dinan kenan da NY wanda daga baya kyawawan dabi'unsa,halinsa suka sa kawacenmu ya rikide min yazama tsantsar so,uhmmm son maso wani koshin wahala,To su ummu arif,nana,aisha yaudai a sararamin a tayani da addua tunda kunsan waye NY😊😢
Jiki a sanyaye muka amsa da eh,kowa yayimata adduar alkhairi muka fita muka barta don xata gabatar da sallah..
Yan walima duk sun watse har an gyara gida,yayi shiru kmr baayi taro dazu ba,Nasrin ko ana nan ana bacci bayan ta kira NY tamai ya hanya dafatan isa lfy😞
Bata tashiba sai bayan magrib,ba shiri tayi toilet tayi wanka da alwala tafito tai sallah sannan tadan murxa cream tazira wata doguwan riga ta sauko kasa,da gudu ta isa gun Abba ta rungumesa harda bashi peck a cheek,nanta fara kwararo mishi godiya,yace nasrin its enough,Allah kara ilimi,tace amin.
Abba yayi gyaran murya yace nasrin inaso in tambayeki ki fadamin gaskiya,wanda yazo gunki dazu meye alakarki dashi,a sanyaye tace abba abokina ne,yace good ina kika sanshi,nanta labarta mishi haduwarsu ta fari,yace mata tashi kije,dama ya zata soyayya ce tsakaninsu yace ya turo magabatansa ya mata aurenta kowa ya huta domin shine darajarta tunda yasan bata da tsayayye domin bata sauraransu.Amma yanxu kawai abin daya dade yana saqawa ransa shi xai faru wato ya hadata da NASIM😳😳😳
Tab nasim,anya nasrin xata amince kuwa,muje xuwa..
0 comments:
Post a Comment