Bismillahirrahmanir Rahim
.
Wannan kirki raren labarine nayi shi dan fada karwa da nisha dan tarwa ban yishi dan wani ko wata ba Written by husba'ah fama
.
Wata yarin yace 'yar shekara 15 kafa fururu komai babu fuska kuma tasha Jan baki da hoda harda gazal ta fallo da gudu kanta daukeda tulo tadebo ruwa a guje ta fada gida Tana shiga ta saki tulun yafadi ya fashe Nidai gaskiya bazan yar daba hikenan ni banda kata bus hine fa ya bini har inda zan debo ruwafa inna yana cemin *YAR* *KWALLIYA* kafa ba mai fuska tasha ado hine nakamahi da danbe na fasa mihi baki hine dan bahida kunya ya biyoni gida Yasin bazan yarda ba inna kalli yanda bakina yake zubar jini inna Abu muguwace wlh Kayi hakuri kaji kaima da naka ina ruwanka da tsokanar ta kuma kasani sarai bazata barkaba Au abinda zaki ce kenan to shi kenan zan turo me rama min Kayi hakuri mana kai baka jin hakurine Ina kotsayawa beyiba yatafi Inna ki barhi ki barhi nace kaje ka kawo bindiga karhe kenan Yanzu Abu Wannan rayuwar kika zaba to shikenan zandena tsare miki wlh tinda ke bakida hakuri yanzu Wannan gabjejen kato kika kama da fada Inna hinefa ya nemi tso kanata fa Yanzu ruwan da kika debo ma gashi kin fasa tulon kaini inna ina zansa kaina Inna Wannan fa laifin tulun kine ina ruwanhi dani nan naso na ajiye hi hine ya fadi ya fahe sai hakuri Kamarya sai hakuri Abu girkifa zan Dora yanzu ya kikiso ayi To ni kome ma za ayi ayi tuludai yafahe nikuma na gaji bazan iya komawaba
.
Kin isa komawa kamar kinyi kin gama ga wani tulun can jeki dauka kidebo wani ruwan Kai inna kinemo wani ya debo kinga janbaki da hudana ya kare sonake na zagaya baya na siyo I dan har baki debo ruwan nan ba ba inda zaki Abu kin jini da kyau hikenan zan debo Abu ta dauki tulun tatafi Rake yauwa bari naga maya finda ke daure a kugunta ta kwance ta Ciro Hamsin ta mika wa me rake Yabata rake da canji tana tafe tana sha harta karasa rafi Yauwa wana kama wato jiya kika watsa min kasa kika gudu ko yanzu wana kama cewar Abu Ke Abu kinga diban ruwa aka turoni ba fada ba matsa na wuce cewar binta Ke binta me kike nufi ni wasa aka turoni kenan bari kiga wasa cewar Abu Hannu tasa ta ture tulun dake kan binta yafadi kasa yafashe Yauwa kinga wasa nan nafasa banza ko kinada abinyi ne Kaiiii ni kika fasawa tulu wallahi kinyi karya saina rama Abu kome kike takama dashi kin tara kin samu ni binta saina gyara miki zama Binta na gama fada tasa kafa ta daki tulun Abu yafashe Nanfa Abu ta daka tsalle ta dire ta kamo wuyan Binta suka kama fada da kyar aka rabasu Aina fada miki Abu ni Binta nice dai dai ke saina gyara miki zama Tohi kenan idan baki gyara min zamaba nizan gyara miki kuma saikin biyani tuluna kona daka ki a gurin nan wlh Allah ko Abu bazan biya ba kiyi abinda kika gadama koda me kika zo ni Binta na fiki haka kikace ko to hikenan Kallon ta Abu take tana gyada kai da buga kafa Banga wanda ze fi karfinaba ni Abu wai saiwata banza bazara iskar damuna binta wlh kintarowa kanki aradu da ka Hannun ta Abu ta kama ta sakar mata cizo dagudu tabar wajan Binta tabi bayanta da gudu haka suka yanka cikin unguwa dagudu harzuwa gidansu Abu Abu ta boye a bayan inna Inna ki matsa Wannan fadan ba naki bane kimiko min Abu na nuna mata abinda binta zata iya ni kika ciza dai ko cewar Binta Yar gidan marasa tsoro mekikeyi a bayana aina fada miki ni nadena bada hakuri kinga Binta gata nan zoki mata abinda kike so cewar inna Gadan gadan Binta tataho Kinga Binta tsaya Abu ina ruwan dana aikeki kidebo cewar inna Inna asara kika aika dankuwa ni Binta nice nan na fasa tulun *'YAR KWALLIYA* tafasa min nawa shine nima na rama wata tsiyarce cewar Binta Ahh babu bakomai kinyi daidai yanzudai kiyi hakuri Binta kibari idan tafito kuyita takare mutuwama tana tsoron idon ma haifi cewar inna Inna kenan kince haka ko to ina waje ba inda zanje kekuma Abu zaki fito kisameni hoda bawanka kidinga Wanka idan zakiyi kwalliya Binta tajuya ta fita Inna ki matsa kibar ni da ita kina jin metake cemin Karya tayi Abu gaskiya tafada yau kwananki nawa rabonki da kwanka Inna batun wankan nan kibarhi aikyan kwalliya kayihi batateda wankaba gawani kamhin turare na musamman dayake tahi a jikina gahi turaren babu a kasuwa me yafi raina shine zan tsaya inta batawa kaina lokaci wajan yin kwanka Dalla rufemin baki kazamar banza kazamar hufi ina kyau Anan *HODA BA WANKA* Baki tabude ta gir_giza kai ta dunkule hannu inna harda ke yasin duk wanda yasake ce min hoda ba wanka na dena raga mihi yasin cewar Abu Yanzu da kika dunkule hannu damben zakiyi dani nima cewar inna Jifa tayi da takalmin kafarta ta debo kayan Kwalliya ta zube a gabanta tadauki Wannan tashafa ta ajiye takalli kanta a madubi tayi dariya
.
Inna jiya da naje dan dali aka dinga tambaya waye yafesa turare nayi shiru tsabar kanhin turaren jikina hanci suka toshe Niko kayan nan ma bacanzasu zanyi ba Wanka kuwa nadena Kaza kankida motsi afakaice suka zageki baki saniba ba abinda kikeyi sai bugawa kitemaka ki ajiye kayan kwalliya kiyi Wanka kekanki zakiji dadi Tab tab aaah waii saidai wata Abun badai niba wanka nida hi munyi hannun Riga inna kifara sabon lissafi daga nan harranar sallah nida Wanka Haka kikace to Allah yashigoda yayanki da malam su insun isa dake Sa saki kiyi tinda ni kin rainani dan Allah ji yanda kika cika mana gida da tsami cewar inna Kinji ko inna kinji irin kamhin turarena ko hakama wani saurayi yajiyo kamhin yace yana sona nace bana son hi ni fako inna har bana son fita dik inda nabi ansan nice saboda turturarena cewar Abu Waiyoo waiyoo tasa kafa tayi koli da kayan kwalliya inna ban fada mikiba yau ake cin kasuwar gangare natafi Tayi fice warta Badan Allah yasa akwai sauran ruwa agidan nan ba da Abu ta gama dani cewar Inna Tafiya take a hankali tana tafiya tana yanga acewarta tafi kowa haduwa ga turaren jikinta yafi na kowa kanshi tana tafe tana cin gyada hannun takuma rikeda sandar rake ga wuwar danmara tasha a kugunta binda na labe tana kallon ta Abu nakara sowa inda Binta take Binta tariketa Wana kama yasin saina dagargaza bakinki zan kyaleki yanzu ina inna take balle kibuye a bayanta cewar Binta Yasin Binta kanki baya aiki kalli yanda kika rike min Riga a gaban mutane gasamari a gefe kalan ki zubarmin da mutunci a idonsu haba kidena abinda kuda zebiki Karsan kuda nice mangoro kobakijiba cewar Binta Janyota tayi zata daka bashiri ta saketa tatoshe hanci Abu dagaskene abinda ake fada kenan Wannan warin daga ina lallai kinci sunan ki huda ba Wanka sammin raken mana Abu taraba shi2 ta bata Yauwa nagode gyadar fa Tadiba tace Gahi kibarni zaki rakani cewar Abu Eh ni yanzu kawarkice gaskiya kinada hankali Abu Dariya tayi tace ko nasani suna tafe suna shirme harsuka siyo suka dawo
.
Atare suka shiga gidan Inna na ganinsu ta fara salati Abu mekika kuma yiwa Binta cewar inna Inna ai yanzu Binta tazama kawata cewar Abu Ina baze yiyuba ban yardaba wlh dama ya kike bare ankaraki da binta waye besan bintaba cewar inna Kinga Binta jeki gida zanzo na same ki cewar Abu To inna sai anjima cewar Binta Sallama Alaikum inna ina wuni Lpy kalau Nura sannu dazuwa kaga Abu tayi sabuwar kawa mara aji irinta Ke Abu yatoshe hanci inna meya yake bugawa haka cewar Nura Wacce inbanda *'YAR KWALLIYA* Fari Abu tayi da ido tareda juyawa New writer's Taku husba'ahfama
.
Yaya Nura a hekaima kaji kanhin tiraren nawa Dalla kanshi ko wari kazama kawai dubi yanda gidan nan yadauki warin jikin ki Wari karyama kenan Yasin kanhi kaji cewar Abu Yau sai kinyi Wanka bazan iya zama dake kina wariba wlh inna bani ruwan nan na kusa dake cewar Nura Banga abinda zesa nayi wanka ba Yasin kalan kanhin turarena ya tafi Nura ya dauki ruwan yasa a bandaki yakai mata soso da sabulo ya karyo bulala yarike Shiga kiyi wanka Yaya Nura ina ganin gir manka fa cewar Abu Yadaga bulala bashiri ta fada bandaki tayi zamanta Kayi ka gaji yaya ba wankan da zanyi cewar Abu Tana tawasa da ruwan kamar tana wanka tawanke fuska da kafa da hannu Kate makeni ina fitowa zan cika fukata da KWALLIYA na raka Binta tallar gurjiya hahhh Tabude ta fito ta harareshi tashige daki tayi KWALLIYA ta tafi gidansu Binta taje tasamu Binta ta fito tallar gurjiya A hanyarsu na tafiya Abu tayi ido4 dawata taci ado da KWALLIYA tayi kyau sosai harta bace Abu na kallon ta Ke mekike kallo cewar Binta Kinga yanda tayi kyau tafi yanta kayanta komai yayi Nanfa Abu tashiga yin irin tafiyar Kibar Wannan abin Abu kinsan daga ina take cewar Binta A'a cewar Abu Daga birni take haka suke tasu KWALLIYAR dasa kaya ba irin nakiba HODA BA WANKA
.
Yasin yanzun nan bakinki zeyi jini Binta nizaki cewa haka nifazanyi fada da duk wanda ya kirani da Wannan sunan kowaye hi cewar Abu Maida wukar nataba zuwa birni sau1 yanada kyau ginin su ba irin namuba kinga baze yu nabaki lbr ba saikin gani da idon ki cewar Binta Kai nima inaso naje zaki kaini dan Allah cewar Abu Inna inna ce matsala Abu damunje yasin cewar Binta Kinga bawata matsala ki kaini kawai inzaki kaini ya kika ganni zanyi kyau a birni ko cewar Abu Ehhh to ban saniba saikinje tukunna saboda gaskiya tsoro zaki basu kalle kifa tab cewar Binta Waike hikenan bakida magana sai kice na kalli kaina me zan gani kodai ciki baki kike min ne cewar Abu Ko daya KWALLIYAR takice abin tsoro ga kafarki Fari fat gaskiya bazan kaikiba saikin waye cewar Binta Abinda Binta tafada yabatawa Abu rai yasa tayi gaba ta barta a baya
.
Wani yarone yazo siyan gurjiya gun binta Binta zuba min gurjiya Karki zuba mai cewar Abu Tinda na ganka nadawo mekace min jiyama Meka ce mata Eh cewar Binta Shiru yayi yakasa cewa komai saida ya gano yayanshi yace ' *YAR KWALLIYA* nace Ohh me dadtin dankwali itace *'YAR KWALLIYA* cewar Binta Barshi dani yanzu nanuna masa kalata Yasin harni zaka tsokana ka gudu anhi kudin nahi Binta cewar Abu Binta ta ansa tace kuma bazan siyar maka da gurjiyan ba na karfine Gaya mihi binta waihi Wannan dame yake dakama ne naga saiwani jijjidakai yakeyi cewar Abu Kasa ta diba ta watsamai a ido Binta tasamai kafa ya fadi suka rufeshida duka abin mamaki kato a kasa mata na duka abinda mutane ke cewa kenan Yayan shina kara sowa ya daka musu tsawa Suka bar dukanshi suna Harar shi Lpy kaikuma meya kawo ka kasan muko suwaye cewar Abu Suwaye Ku inbanda kucakai marasa hankali dalla dubeki kafa furu furu komai be ganiba dubi kayan jikinki fuska saikace Aljana waike kinyi KWALLIYA Ap abanza yafi na tsohuwa kaga ka gaggauta barin gurin nan inba hakaba kuma hmmm cewar Binta Karkusake suce zaku yimin haukan da kuka saba danni bazan daukaba wlh Ko Binta mu gwadamai aiki dan nakula saimun koya mishi hankali cewar Abu Waige Binta tafara can ta gano dutsa tace haryanzu bakinka be mutuba ko tsaya ka gani Dutsen ta dauko da buga mishi a kai Banza a banza cewar Abu Jini ya fara zuba a kanshi Abu da Binta suka zuba a guje suka wuce gidansu Binta Umma ga gurjiyar ki yau an hana talla inji me gari cewar Binta Ke Binta waya fada miki cewar umma Umma Nifa ganauce ba jiyauba Gashi can ya baza yan *DOKA* A gari cewar Abu Kunga bana son shegan taka waca tsiyar kuma kukayi na sanku da kyau cewar umma Wani ne ya nemi tso kanar mu hine muka fasa mai kai cewar Binta Eh banjiba naji kamar kince fasa kai Allah na gode maka daka bani Binta nidai shikenan bakina baze zauna shiru ba saboda inada Binta cewar umma Kofar gidan su Binta aka siga duka da karfi Kufito mana dasu ko mushigo yara sun gagari kowa wlh yau zamu sharewa kowa hawaye kufito dasu cewar mutanan da suka zo Kuna jiko yara kunzama dan kuka mejawa uwarsa jifa Umma kinga jeki kiji dame suka zo idan da sulhune kusulhunta idan kuma akasin hakane kikira womu katkenan cewar Abu Kushiga ciki bari naji dasu
.
Wai baza a fito dasu bane Eh mumafa yan zama nine kofar suka bude suna kokarin shiga Haba dan samari gidan matan aure ne fa Nasani ina 'ya'yan Allah banin nan suke Binta da Abu Basa nan sun fita Karyama kenan ina ganin su suka shiga gidan nan dan haka ki fito dasu kawai mu baza mu hakuraba dan uwanmu suka fasawa kai gashinan sai zubar jini yakeyi yanzu haka yana Asibiti Allah yabaku hakuri kuje idan sun dawo nida kaina zan kawo muku su cewar umma Eh to na yarda dake saidai be kamata mu tafi haka ba bari mu bar miki sheda idan sunzo ki nuna musu Yadaga gora ze sauke mata dagudu tabar gurin ta shige gida tarufo kofa Yauni umma naga ikon Allah ina kuke Umma sun bar miki sheda banzaye sokaye sun yarda ba ma nan gamunan muna jinsu kuma cewar Binta da Abu Au kujin dadin kune a bar min sheda saboda kun amsa sunan Ku Binta da Abu ko Allah yate makeku suna nan suna jiranku kuna fita sai abinda hali ya yiwu cewar mama Basu isaba yanzuma ba barinsu zamuyiba narike muryar su zan ne mesu 1 bayan 1 cewar Abu Umma kawo mu kai miki dan dali cewar Binta Gashi nan kutafi amma dan Allah karku nemi tso kanar kowa kuma Ku canza hanya karsu ganku cewar umma To sai mun dawo suka fada gaba dayansu suka fita
.
Suna fita umma taji wani hadeden wari Umma taja dogon nun fashi Wannan wani sabon yayi ne kuma Abu irin Wannan bugawa haka nida Allah yasa kar Binta tadau Wannan halin na rashin Wanka Suna tafiya suna waka suna ciye ciye suna neman tso kana Abu ta gano bishiya tace Binta ajiye gorjiyar nan muhau bishiya kinga yanzu basu fara zuwaba zuwa anjima sai muje dan dali To muje suka tarar da yara a jikin bishiya suna wasa Kubar gurin nan Abu da Binta sunzo ko sokuke jiki yayi tsami cewar Binta Tinkan Binta ta karasa magana yaran suka bar gurin dan sunsan halin Abu da Binta Suka cire takalmi suka haye bishiya suna wasa kamar yara Wasu yan mata suka zo wucewa suka gano Binta da Abu suka kwashe da dariya Abu na ganin su ta sauko Binta ma sauko wa tayi Wakuke wa dariya Eh daku nake magana Abu ta fada tana dungure musu kai Karki sake dun guremin kai kinsan kowaye babana kuwa A garin nan
.
koma waye hi beda meniba abinda yasa kika kallemu shine yanzu ze Ja miki dukan tsiyama kuwa cewar Binta Jiki ko kayama baki iya sawaba ji hodar fukarki janbakin ma tsohon yayi ne amatse ciki asai sabo cewar Abu Kaji wai harkurace zata ce da kare maye jiki kalli kafarki kalli fuskarki ji wani wari mara dadi da kikeyi gaskiya kinci sunan ki HODA BA WANKA Nanfa Abu tayi kukan kura ta rufesu da duka Binta nadukan daya Abu ma na dukan 1
.
Duka sukai musu bana wasa ba harda yaga riga Cikin muryar kuka yarinyar tace saina nuna miki bakida wayo Saikin ga gatana Abu tace Jeki turo duk wanda kika gadama ni Abu ina jiran hi banza qazama Eh nice qazama idan ni kazamace ke kuma fa fada min cewar yarin yar Bakinki be mutuba ko Abu saimun zubar mata da hakwara tukun na cewar Binta Kuyi duk abinda kuke so lokacin kune yanzu nima lokacina nanan zuwa cewar yarin yar
.
Tana gama fada ta mike ta debi takal manta a hannu ta kalli kawarta da suke tafe tare Tace 'YAR KWALLIYA suka zuba da gudu Matsoratan banza kawai harni zakibawa tsoro da baban ki Wannan kalmarta zakiga me rama min yazama tamkar tatsoniya a gurina ni Abu naci dubu sai ceto Sukayi dariya Kinga dauki tallar mu karasa dandali yanzu kowa yazo zamusha kallo kai ni harnaji ma bana son zuwa cewar Abu Binta tace meyasa Tiraren jikina Akoda yaushe shine matsala ta dana je dandali daga kallo sai tohe hanci a gurin sama ri cewar Abu Binta tace dagaske kike Abu warin najan hankalin samari Abu tace bana son wula kanci binta wayace miki warine kanhidai nibama nason irin kallon da sama rin suke min nasani nafi matan dandali kyau da kanhin tirare sosai ma nice kadai nasan sirrin Nanfa Binta ta tafi tuna ni Ke tina ninme kikeyi Abu gaskiya nima zan fara fashin Wanka konima turaren jikina zefito kwana nawa zanyi banyi wankaba Abu tace yauwa yar gari kinga bake ba Wanka indai kinaso tiraren yazauna tareda ke duk inda kika higa ansan kin higo Binta tace To hi kenan nagode kawata Tadauko farantin gurjiya tace debi kici iya San ranki aikin bani sirri babba Abu tace Bakomai yiwa Kaine Binta amma ya zakiyi da umman ki idan tagane kin dena kwanka Kibari kawai nikaina bansan abinyi ba mutafiko kinga yamma tayi kar a fara bugawasa bama nan Abu tace ga aiki zan saki indan mun higa dan dali ki ki zuba ido kiga abin mama ki gurin sama rida yan mata To hikenan muje Abu Suka je dandali hakan kuwa akayi Abu nazuwa masu toshe hanci nayi masu dariya nayi Abu harda sake tafiya Kawata Abu gaskiya nima na rike sirrin nan hannu 2 Sukayi dariya suka tafa Suka sha kallo sukayi tsokana iya son ransu suka koma gida Daga ina kike Waye Wannan Abu tace tana daga kai taga Nura Daga dandali nake Yariko hannunta yawuce da ita ciki ya watsar da ita kamar kayan wanki Nura ya fara shin shine shin shine Yace Inna bana tunaninda Abu ta shigawanka tayi Inna tace Ko hmm zata aikata nasani Wannan nan gaba kadan nizan fara yimata Wanka da kaina
.
Abu tace Waaa niii tab bawanda ya isa dan bakin ciki turaren nawama rabani dahi za a yi Nura ya Wanka mata mari tafashe da kuka Inna abinda ya dace kenan kifara yi mata da kanki tinda ita bata yi Nifa bawanda zemin wanka Nifa yaya anyi walkiya na ganka bakin ciki kawai ka keyi dani dakaji kanhin tirarena saika dinga yamutse fuska saboda bakin ciki Tirare ko wari kinga kidena shiga cikin mutane kina kiran waikin fesa tirare dariya zasu miki Wannan warine warinma mara dadi qazama cewar Nura hi kenan Inna kina jinhi ko ni ya kira qazama tafara timami akasa Nura yace Inna kice mata ta tashi kokuma yanzu jikinta ya fada mata Bashiri ta mike tana gunguni harya fito fili tace nagaba yayi gaba kanshi kuma nayi bawanda ya isa yakwace Ehhhe Waye ze kwace inbanda Wanka Inna duk sanda kika tashi wankar *'YAR KWALLIYA* kitanaji kwalin sabulu saboda tsoro Inna saida safe Yana fada yayi fice warsa Allah yakaimu Inna kinji shi ko Yasin yaya kajawa budur warka Allah ya hadani da ita Kinga Abu bana son neman tsokana karki sake kitaba musu 'ya kisamu wanda yamiki badai itaba ki kwanta saida safe To Inna Allah ya kaimu WASHE GARI DA SAFE Abu ta fito tana hamma
.
Inna Allah dai yasa kin gama abinci dan yau yunwa nakwaso abaccin Bagai suwa ba komai sai Neman abinci baza kiciba saikin goge baki kinyi sallah tukunna cewar Nura Tamatso kusa dashi tace yaya a gidan nan kaine kwai matsalata yanda sauran suka tafi suka barini kaima zaka tafi ko ince kagaji kabarni Yatoshe hanci tinda tafara magana harta gama Nura yace Wai Wannan bakin naki Abu ai sai ya kashe me rai yaushe rabonki da goge baki AF anzo wajan nikaina na manta gawayin da gihirin na ban wuya Yasin hiyasa na dena wankewa yawan goge baki na kahe hakori Nura Yana nesa da ita yanda bazeji warin bakin ba Injiwa Yau saikin goge baki yaushe rabonki da sallah dan Inna tace rabonda taga kin kalli gabas harta manta cewar Nura Eh hakane yaya hadasu nakeyi hiyasa bata ganina Hadasu kamarya Abu Nasati1 nakeyi a rana1 sauran ranakun kuma ina hutu tafada tana dariya Nura yace Abin ma dariya yabaki ko Abu amma kin dena zuwa isilamiya ko Tab tsohon zance tin yauhe nadena zuwa bari kaji laifi nayi yace ze dakeni nikuma nace be isaba shine yasa yara suyimin waka waini *HODA BA WANKA* hine na sace mai tayar keke hine fa yake ne mana ruwa a jallo
.
Tana fada tana Sosa kai da jikin ta Inna haka lamarin Abu ya kara lala cewa cewar Nura Inna tace kaji da kunnan ka kakuma gani da idonka yazu kuma abin zekara finnada tinda ta hadu da Binta Ido yazare yace Binta gagare Ita dai yanzu kawartace sosai duk inda Abu take zakaga binta Cewar inna Dole nakara samiki ido Abu jeki kwanke baki kiyi Alwala kizo kiyi sallah a gabana kuma ma inbanda rashin hankali irin na Abu a i na akace miki hada sallah a keyi kowacce ana yinta akan lokacin ta kina jiko cewar nura Abu tace Yashiga tanan ya fita tanan bayan kai ba malami bane me zaka fada min nayarda bayan sanin ma nafika Na yarda jekiyi alwalar kizo Taje tayi ta zo gabanshi tace yaya na hutar dakai dama yau nake hadesu guri guda barima nayi ka gani Nura yace Ke bana son hauka fa sallar Asuba raka'a nawane Lallaima yayan nan nawane inbanda 2 Sallama Alaikum Nura yajiyo sallama daga kofar gida girgiza kai kwai yayi yatashi yatafi Nura ya Inna taku Lpy kalau cewar nura To Alhamdulillah megarine yace kuzo dakai da inna dakuma Abu Allah daiyasa lpy cewar nura Ehhhhhto lpy ba lpy ba saidai koma meye idan kazo fada kaji To gamu nan zuwa yace yakoma ciki Inna yarinyadai tasake ballo ruwa megarine yake Neman mu To Bakomai bari ta idar da sallah saimu tafi cewar Inna Abu tace Inna Nifa ba inda zani idan banci abinci ba Ehhhhe Waiba sallah kike yiba Abu cewar Inna Abu tace Inna kwantarda hankalinki na idar bani na bawa cikina tukunna Inna ta bata ta ansa tana hannu baka hannu kwarya harta gama Tasha ruwa Tace Inna saura kwalliya idan banyiba bazan iya sa kafata wajeba Nura yace kin isa waye ze zauna jiranki Inna tace kai kanka kasan hakan baze yiyuba kabarta tayi mutafi Abuta baje kayan KWALLIYA tayi kamar yanda ta saba fukarnan kamar Aljana Inna mutafi naga ma Warin bakinta yadoki hancin Nura Kaiiiiiii Abu baki wanke bakiba ko Eh ban wankeba bakina ko naka
.
Tayi gaba abinta sukuma suna binta a baya harsuka karasa fada kowa na gaida megari amma banda Abu Megari yace Ke Abu me yarin yata tai miki kika daketa jiya tareda bakuwar gidana Tawatsawa yarin yar harara tace kuma na dake ta nadaki banza ba uwar dayasa tace min HODA ba Wanka Ke Abu baban nawa kike fadawa haka cewar yar megari Anfada mihi ubanki ubanane cewar Abu Kaji yarinya mara kunya me garin kike fadawa haka Ayi hakuri yarin yace cewar Inna Abu tace Inna saboda ni karki fara karya niba yarinya bace hekarata goma shabiyar Inna nayimata alama tarufe baki amma ina zance kwai Abu take saki
0 comments:
Post a Comment