A DALILIN GATA Page 21-25
.
Kiran sallar ne ya sa suka ta shi dukan su domin gana wa da ubangiji, matan kuwa gurin Mata y'an uwan su majinya ta suka nufa, nan aka ara masu kayan buk'ata suka sauke farali. Zajlah ta dad'e tana kwarara ma mijin ta da kuma surukin ta addu'ar samun sauk'i da kuma cin wannan jarabawar daga ubangiji, saboda ba k'aramin tausayi suka ba ta ba, asara ta farat d'aya akwai tashin hankali ba k'arami ba. Bayan mazan sun dawo ne Abban Yusrah ya umurce su dasu koma gida tunda su mazan suna nan, sai dai kash cikin su ba wanda ya ji zai iya d'aga wa nan da can ba tare da ya ga halin da Dad yake ciki ba. Mum ce ta yi k'arfin halin furta' "Zajlah kuje gida ku d'an huta, in Dad d'in ku ya farfad'o za mu iso". "Mum gaskiya bazan iya tafiya ba, kuyi hak'uri Abba har muga ya yanayin jikin Dad, amma yanzu zanje gida in samo mana abinda za'a ci". Direba ya kai ta gidan, gaggauce ta dafa ruwan Lipton sannan ta soya k'wai da dankali sai ferfesun kifi da ta yiwa Dad. Wanka ta shiga ta yo wanda ko mai bata shafa ma jikin ta ba ta zura wata doguwar riga y'ar kanti ta d'auki wasu kayan buk'ata ta fice. Ko da ta isa asibitin kowa ya yi jugum ana sauraren farfad'owar Dad, bayan ta gaida su ne ta zube kayan da ta zo dasu, kowa sai sannu yake mata sa6anin Alamein da bakin magana ya mutu sai dai binta da yake yi da ido had'e da jin tausayin ta can k'asan zuciyar shi. Dak'yar ta samu Mum ta sha tea kad'an sannan ta had'a wa Saudat ta rarrashe ta ita ma tasha kad'an, sa6anin mazan da suka nuna ba za su ci komai ba, tana so ta had'awa Alamein yasha ko kad'an ne amma nauyin Abba take ji. Fahimtar hakan ya sa ya furta' "su Mum ne ake rarrashi su karya ba za'a had'awa yaro na ba?". Cikin zolaya yake furta maganar. Kai ta soke tana wasa da yatsun hannun ta, ganin cewa tabbas ita Abba ke jira ya sa ta had'a tea d'in ta kawo mai, zurum kawai ya yi yana kallon ta sannan ya kauda kai, hakan ya sa ta girgiza mai kai alamar kar yace bai sha, nan ya kar6a ya sha kad'an ya bata cup d'in. ********** *09:00am* likita ya fito daga d'akin da aka kwantar da Dad, su duka suka tunkare shi domin jin ya jikin nashi, nan ya gaya masu cewa ya farfad'o za su iya shiga su ganshi amma kar su cika shi da hayaniya. Cikin murna suka fad'a d'akin dukan su, sai lokacin Alamein ya san meke faruwa da Dad, saboda ko da Abba ya yi bayani yana nashi d'akin. Kowan nen su sai da ya zubarwa Dad da hawaye akan yanda ya koma cikin awa bakwai abin gwanin ban tausayi, lallai tabbas rayuwa ba a bakin komai take ba, rayuwa da lafiya ciwo da mutuwa duk ga hannun ubangiji suke, lokacin da ya d'oro ma d'aya ba wanda ya isa ya yaye ma sai Allah, an dai samu ya farfad'o amma ba uhm ba uhm-uhm sai dai ido, ga kuma 6angaren jikin shi da bai motsawa ko kad'an. Kukan da ya zo ma Mum ne ya sa ta fita daga d'akin ta jingina ga k'ofa tana rasgar kuka tamkar wata k'aramar yarinya, saboda hango tarin matsaloli masu tsabagen yawa a rayuwar su. Tunkarar Dad ya yi yana kuka zai fad'a saman jikin shi su Salis suka tare shi, Abba ne ya bada umurnin duk su fita daga d'akin, bayan sun fice ne ya je gab da d'an uwan shi yana magana ko zai kar6a mai sai dai babu nasarar ko da motsawar la66an shi, duk da k'arfin halin da yake yi sai da hawaye suka wanke dattijuwar fuskar sa. Fitowa ya yi daga d'akin yana mai shawartar su kan a wuce da Dad f.m.c Bk. Kowa ya yi na'am da maganar shi hakan suka yita rarrashin Alamein har suka fice su duka domin duba yanayin wutar da ta ci ma'aikatar, iya bincike anyi amma ba'a gano musabbabin wutar ba. ******* Su Mum kuwa gida suka fice domin yin shiri zuwa Bk. "Mum in shirya muje ko?", cewar Zajlah. "A'ah kuyi zaman ku ke da Saudat har muga yanda abin zai kasance, ke Saudat kishirya kayan ki ki koma can gidan su har mu dawo". "Mum kibari ni zan d'ebo kaya na in dawo nan har zuwa dawowar ku, Allah ya tashi kafad'ar Dad yasa ayi farar jinya". Hakan yasa Mum ta yita saka mata albarka. Da hakan ta fice ta d'auko kayan da za ta buk'ata ta rufe gidan ta dawo, Baban ta ta kira ta gaya masu abinda ke faruwa da sauran y'an uwa daya dace su san da faruwar abin. Bayan Mum ta kimtsa ne suka raka ta asibitin, acan ne suka had'u da Salmat, da Yusrah, sai kuma iyaye daga 6angarori da dama da suka cika asibitin tamkar ad'auke wa Dad ciwon da ke damun shi. Ba abinda ni kai na yak'ara firgitani tamkar yanda aka d'auko Dad za'a saka a mota kai kace gawa ce, nan matan masu raunin zuciya suka rik'a kuka. Bayan an wuce dashi ne da Abban Yusrah sai Imran, Alamein, Salis da wasu abokanen Dad biyu. Nan su Mama Asabe suka wuce jiki a sanyaye, Mamar Yusrah da Salmat da Yusrah duk gidan su Mum suka wuce.
.
Kwanci tashi yau Dad satin shi biyu a asibiti ana yi mai gashin jiki wanda ga alama sauk'i ke shiga kad'an-kad'an, wanda har yanzu bakin shi bai koma dai-dai ba abin ya zamo tamkar mai kariyar halshe. **** **** **** 6angaren su Zajlah kuwa ita da Saudat da Yusrah suke kula gidan, saboda tun lokacin da ta biyo su daga asibitin take gidan, sun je ganin Dad kusan sau biyar, haka ma su Mal Inuwa sun je sau biyu duba jikin na shi sai dai fatar Allah yakawo sauk'i. *** *** *** Yau ne aka sallamo Dad daga asibiti ba wai don ya murmure duka ba sai don ganin irin tsabagen kud'in da ake ci na jinya kuma ciwon sai dai hamdala ya sa Mum ta yi shawara da Abban Yusrah kan su nemi sallama aje gida a had'a da addu'o'i.

Ba hakan likitoci suka so ba, sai dai ba yanda za suyi hakan suka bashi sallama d'in tare da shawarwari na kula da yanayin jikin na shi. Hakan suka d'ungumo suka dawo gida wanda da murnar su Zajlah suka fito taryar su, sai gashi sunyi turus saboda sun zata za su ga Dad ko da da sanda ne ko kuma yana d'ingishi sa6anin ganin da suka yi an tallafo shi daga mota, dukan su sai da suka zubar da hawaye. Godiya Mum ta yiwa su Imran sosai na ganin irin yanda suke ba da kulawa ga ciwon Dad, kuma basu zauna ba tun faruwar abin kullum suna asibiti. "Lallai kun zama abokanen arzik'i, samun irin ku a wannan zamanin sai an tona, Allah ya yi maku albarka yasa ka maku da khairan", tana maganar tana hawaye. "Amen Mum, amma kakki damu wannan ba komai bane yi wa kaine, kuma Dad tamkar uba yake gare mu duk abinda muka yi mai ba fad'uwa ce a gare mu ba, fatar mu kawai a gare shi addu'ar samun sauk'i". Da hakan suka fice daga gidan suna masu tausaya wa zuwa ga Dad. Zajlah ta so ta kwana gidan amma Mum ta nuna mata tunda sun dawo ta tashi ta koma gidan ta had'e da yi mata godiyar d'awainiya da kuma kulawa da ta basuwa akan ciwon Dad, hakan dai ta had'a kayan ta ta wuce don ba hakan taso ba musamman da taga Yusrah ta dawo gidan da zama gaba d'ai. Hakan dai ta kakka6e y'ar k'urar da gidan ya yi sannan ta yi wanka ta kwanta, wata zuciya ke ce mata biki kyauta ba Zajlah ke fa sai da kika gyara inda za ki kwanciya sannan kika kwanta ya kama ta ki gyara wa bawan Allah na shi gurin, wata ke ce mata sassaucin da fa kika samu rashin lafiyar Dad ce amma yanzu in kika shiga sabgar shi zai iya wulak'anta ki, wannan shawarar ta fi duba wa ya sa ta yi kwanciyar ta. *** *** *** "Son ka ga har *10:00pm* ta yi kuma Dad ya samu bacci ka tashi kaje gida ka kwanta". "Mum kibar ni na kwana anan, ko na je gidan ba bacci zan samu yi ba". "Bazai yuyu ba Son ko matar ka d'azu na kora ta gida saboda haka kai ma ka fice gobe ka dawo". Ba don ran shi ya so ba ya fice daga gidan wanda ko sai da safe bai yiwa Mum ba, shi ala dole an 6ata mai rai. Ko da ya shiga gidan tsab komai ta gyara sa6anin d'akin shi dake fama da k'ura birjit, ganin cewa bazai iya kwana d'akin ba haka kuma bazai iya ta6a k'urar ba ya sa ya d'auko blanket ya dawo falo ya yi shimfid'a ya kwanta, da tunane-tunane fal a ranshi 6arawo ya yi gaba dashi. **** **** *Washe gari* Kiran sallar farko ya tayar da ita daga baccin duk da bata cikin tsalki, wannan sabo ne duk baccin da take yi da ankira sallah za ta tashi, alwala ta yi ta d'auko littafin ta na azkar tana karanta wa, sai wurin k'arfe *07:00am* ta fito domin samun abinda za ta dafa taci. Turus ta yi a falon ganin shimfid'ar shi alamar nan ya kwana, ji ta yi ba dad'i a ranta ko ba komai ya ci ta kyautata mai matsayin shi na mijin ta kodon gudun fad'awa fushin ubangiji, saboda tasan hakk'ok'in miji akan matar shi kuma tasan na mata akan mijin ta. A fili ta furta "insha Allah Alamein daga yau zan kula da hakk'in ka a kaina ko da ba zaka kula da nawa ba". Kitchen ta fasa shiga ta yi d'akin shi duk da gaban ta dake dukan uku-uku, ga mamakin ta tana tura k'ofar ta ji ta a bud'e turus ta yi ganin yanda d'akin ya yi uwar k'ura. Ita da na ta ta kasa kwana cikin shi ina ta ga na shi da tun auren su bai ga gyara ba, karfa ta mayar da mijin ta *KAZAMIN MIJI* (SIS JABO), duk tsaftar namiji ba kowa ne daga cikin maza zai iya gyaran d'akin shi ba saboda haka za ta tashi tsaye a wannan 6angaren. Gyaran d'akin ta shiga yi sosai, sannan ta fad'a toilet kayan shi k'anana ta saka a wash machine ta wanke sannan ta wanke toilet d'in, kayan wanki ta had'a ta fito dasu ta kaiwa Baba maigadi akan cewa don Allah yasamu mai wanki da guga yaba shi ya wanke, "aiko yaro na sana'ar shi ce zan kai mai ya wanke". Godiya ta yi mai sannan ta koma gidan ta d'auki turarukan d'aki ta je d'akin shi ta fesa, kitchen ta wuce ta yi masu girki ta saka mai a kuloli ta kai dinning table, Baba maigadi ta kaiwa sannan ta ci na ta ta fad'a wanka. ****** ****** 6angaren Alamein kuwa daga masallaci ya rok'i liman a saka Baban shi a addu'a sannan ya fitar da kud'i ya bada a raba sadaka, daga nan gidan su ya wuce domin duba jikin Dad. **** **** K'arfe *11:00am* ta kammala duka ayukkan gidan sannan ta fice zuwa gidan su Alamein, a gate suka had'u tana rik'e da kula a hannu kamar ta wuce komai ta tuna ta tsaya ta gaida shi, nan ya amsa ba yabo ba fallasa ta shige gidan shi ko ya fice zuwa gida.
.
Yana komawa gidan ya nufi dining table ya ci abinci kad'an duk da yana ganin yau ya ci dayawa akan tun fara ciwon Dad bai ta6a cin abinci irin yau ba, d'akin shi ya nufa domin ya yi wanka ya koma gidan su, yana tunkarar hanya k'amshi na tarbon shi har ya sadu da k'ofar, yana turawa ya yi turus yana kallon d'akin saboda yanda komai ya fito tsaf sai k'amshi dake tashi d'akin, saman gadon ya je ya kwanta yana ta tunane-tunane har bacci ya yi awon gaba dashi. **** **** Tana shiga gidan ta gaisa dasu ta bawa Mum Kular abincin da ta zo wa Dad dashi, "dama kenan jira kike yi gari ya waye ki fito tamkar wacce ke zaune saman k'aya", cewar Mum. Murmushi kawai ta yi saboda tana son zaman gidan musamman yanzu da Yusrah ke gidan saboda Allah ya had'a jinin su sosai. "D'auko kular muje kiga Dad jiki ya yi sauk'i akan jiya", masha Allah Mum Allah yak'ara sauk'i". Da hakan suka shiga d'akin ta ganshi ta yi mai ya jiki duk da ba iya kar6awa yake yi ba sai dai yayi alamar amsawa da kai. "Mum akwai zam-zam a gidan nan?". "Eh akwai Zajlah har galan d'aya da rabi". "Mum kawo rabin galan d'in muga". Bayan ta kawo ne Zajlah ta karanta (falak', Nas, Ikhlas) kowaccen su k'afa uku-uku sannan ta had'a da (Ayatul kursiyyu) had'e da wasu addu'o'i na yayewar lalura ta tofa. "Mum gasu nan ki rik'a bashi yana sha kuma ki rik'a shafe mai jikin shi dasu, insha Allah zansa a gayawa Ustaz Yusuf ko Ustaz Lukman su rik'a zuwa suna yimai addu'a, ba abinda addu'a ba za ta yaye ba sai in ba'a kai kuka gurin ubangiji ba, ubangiji Allah ya tashi kafad'un shi ya yaye lalura". Mum har da hawayen ta na jin dad'in kasancewar Zajlah a cikin zuri'ar ta, "tun farkon had'uwa ta dake jiki na ke bani ke alkhairi ce a gare mu". "Mum ba komai mudai dage da addu'a", da hakan ta fice daga d'akin ta koma falo gurin su Yusrah. *** *** *** *** Sai kiran azzahar sannan Alamein ya tashi daga bacci wanka ya fad'a ya kimtsa ya yi masallaci saga can ya wuce gidan su. Bayan an gaisa ne Mum take gaya mai abinda Zajlah ta yi da kuma shawarar da ta basuwa na kiran d'aya daga cikin Malaman su don yiwa Dad addu'a. Baiyi k'asa a gwuywa ba ya yi makarantar tasu Zajlah, da Ustaz Yusuf ya ci karo suka yi magana ya bashi tabbacin zai rik'a zuwa da safe Ustaz Lukman ko bayan isha'i. Godiya ya yi sosai had'e da d'auko kud'i ya bashi, nan ya nuna mai bazai kar6a ba sai dai gobe d'in in ya zo. **** ***** Yau sati biyu kenan ana kula da yiwa Dad addu'a had'e da mayar da ruwan zam-zam da Zajlah ta yi mai addu'a ruwan sha da kuma shafe mai jiki, jiki kam Alhmdulillah don yana magana yanzu kuma har yana iya takowa da k'afa daga d'akin shi zuwa gate abin sai son barka. *** *** **** D'an zaman da suka yi da Yusrah ya sa ta k'ara sanin kan waya sosai don har whatsap ta bud'e mata kuma ta saka ta group na gyaran jiki dana kwalliya, sai kuma group d'in musha karatu saboda gwada karatun littattafan soyayya, inda take samun littafai har ta rasa na za6a ta karanta. Tana bud'e data ta shiga whatsap ganin cewa ba'a turo *AL'ADUN WASU* (SIS BATUL) ba ya sa ta rufe data ta hau d'inkin ta da Yusrah ta kawo kusan turmi takwas. *** *** *** Soyayya mai tsafta da kulawar juna ake bugawa tsakanin Salmat da Salis tamkar su had'e juna saboda tarairaya.

*** ***
Inda kuma 6angaren Yusrah da Imran soyayya ta k'ullu sanadiyyar zaman da ta yi a gidan Mum shiko Imran yana saman hanyar duba jikin Dad kusan kullum. *** *** *** 6angaren Zajlah kuwa kullum sai ta gyarawa Alamein d'akin shi sannan in ta yi girki za ta ajiye kowanne kuma yana ci, kamar yanda inta gaida shi yake amsa mata cikin sakin fuska sai dai bayan hakan babu wata alak'a tsakanin su. Kamar kullum yau ma ta gama had'a breakfast ta d'auko ta kawo dining ta tarar dashi zaune ya had'a kai da gwuywa, ga alama yana cikin damuwa, bayan ta ajiye ne ta koma kitchen ta d'auki na ta kayan abincin ta yi falon ta. Kasa cin abincin ta yi sai juya cokali da take yi a plate duk jinta take yi ba dad'i, waya ta janyo ta kira Salmat suka gaisa sannan ta kora mata abinda ke damun ta. "Yanzu ne ya dace ki nutsi ku ajiye duk wani shirme da kuka yi a baya saboda mijin ki na cikin tsananin neman taimako da mai bashi shawarwari, saboda haka don Allah ki rik'a bashi kulawa ki ajiye komai a gefe". "Tabbbb Salmat yau ke da kan ki ke furta hakan?, ke fa kika ce in gyara mai zama amma yanzu ke ce mai yi mai yak'i". "Alamein d'in ne ya zamo abin tausayi shi da ubanshi, har dai yanayin da suke fuskanta yanzu dole a tausaya masu, amma kar kiyi saurin bada gari daga shawarwari ki zurma, don nasan ki da raunin zuciya sai anja aji", cikin dariya da zolaya take maganar. "Ke dai kika sani, Allah ya shirye ki", daga hakan ta kashe wayar ta bita da kallo tana nazarin kalaman Salmat. "Lallai ni shaida ce ciwon Dad ya sa Alamein ya sauya, saboda daga ranar da abin ya faru kawo yanzu babu hantara ko kallon raini, ko don yana ta lafiyar ubanshi ce bansani ba". A fili take ta maganganun ta ita kad'ai inda dai ta d'an ci abincin kad'an ta tashi ta mayar da kayan kitchen, turus ta yi a falo ganin yanda ta barshi hakan ta dawo ta tarar da shi tamkar ko yatsan shi bai motsa ba, kayan ta je ta ajiye sannan ta dawo kanshi ta yi tsaye saboda rashin takamemen ta ina za ta fara, don gaskiya har yanzu tsorace take ga kutsa kanta cikin lamurran shi. A duniya tak'i jinin ganin babban mutum cikin damuwa duk sai taji ta kasa nutsuwa a ranta abin yai ta damun ta, hannu ta kai za ta ta6o shi ko me ta tuna ta fasa oho, zaune ta yi nesa dashi kad'an saman kujerar da yake zaune, gyaran murya ta yi amma kuma a banza ko motsi bai yi ba. Tsoro ta ji sosai na ko ya suma ne a hakan, cikin sauri ta kai hannun ta saman kafad'ar shi ta girgiza shi kad'an ya zabura cikin razana, yana tayar da kan shi idon su suka had'e guri d'aya nan take bugun zuciyar su ya halba lokaci d'aya.
.
Ganin ya k'i d'auke idon shi akan tane ya sa ta yi saurin kauda na ta idon, saboda ba zata iya jurar kallon fararen idon shi da suka rine suka koma ja ba kan tsananin damuwa tamkar wanda ya ci kuka ya k'oshi, yatsun ta ta dinga wasa dasu kanta na nok'e k'asa. Hannu ya kai ya tallafo hab'ar ta had'e da yi mata alama da d'ayan hannun na me aka yi?. "Na ga tun d'azu baka ci abinci bane shiyasa", "Ayyah kar ki damu zanci yanzu, nagode da kulawa". Wata zuciya ke ce mai me zai hana ka gaya mata damuwar ka tunda ita ta kasa jure taka damuwar har tazo ta yi ma magana, d'ayar ke ce mai kakka tsaya gaya mata komai, me za ta iya yi akai? Salon ka ja ma kanka raini daga gurin ta tunda wuri haka. Tamkar guguwa haka ya ta shi ya nufi d'akin shi ya barta nan zaune sake da baki, "tabbas mai hali ba ya canja halin shi, irin hakan nake gudu shiyasa ba nason sa kaina cikin lamurran shi, ko ma miye Allah ya yaye", a fili take maganar ta ita kad'ai, da hakan ta wuce na ta d'akin. *** *** *** Zuwa la'asar ne ta gama ayukkan ta ta ji tana ra'ayin shiga tak'ara duba jikin Dad, har ta kimtsa ta fito ko motsin Alamein bata ji ba hakan ya sa ta ficewar ta. Tana isa gidan ta gayar da Mum haka ma Dad don jiki ya yi kyau sosai yana magana kuma yana d'an fita sai dai tafiya ba mai nisa ba. Abu d'aya ya yi mata tsaye a rai ganin yanda kwana ukun da bata zo gidan ba Mum ta kod'e ta jeme duk ta fita hayyacin ta tamkar wacce ta yi jinya. "Mum hala ciwo kika yi bansani ba?". "Wallahi a'ah Zajlah jarabobin rayuwa ce kawai da suka yi yawa". "Mum indai ciwon Dad ne ai Alhamdulillah don jiki ya yi dama sosai, sai dai a k'ara dagewa da Addu'a". "Tabbas a rayuwa anason bawa ya yawaita addu'ar Allah ya kare shi da miyagun k'addarori, to su ne suka hau kan Daddyn ku". "Tun lokacin da yafara wannan ciwon abubuwa ke ta kunno kai, wanda masu bashi da way'anda k'addara ta rutsa da dukiyar su suke ta kunnowa neman abar su". "To amma wannan ta su mai sauk'i ce akan wacce ta kunno kwana biyun nan, a rayuwa ana so mutum komai dukiyar shi yarik'a sayen kadara yana ajiyewa saboda ranar da lalura ta taso zai iya fitarwa ya saida yayi lalurar shi ba tare da wani ya ji shi ba". Zajlah dai zurum ta yi tana sauraren Mum, saboda har yanzu bata fahimci ina ta saka ma gaba ba, a tunanin ta irin dukiya ta Dad bazai ma yuyu ba ace cikin kashi d'ari an ta6a ashirin ba, amma dai bari ta saurare ta har takai k'arshe.

*** *** ***
*ASALIN MU* "Mu haifaffin garin Jega ne, ni da Dad d'in ku auren zumunci aka yi mana sanadiyyar mahaifin shi da mahaifi na uwa d'aya uba d'aya, inda tun muna yara iyayen su suka yi hatsarin mota suka rasu, hakan ya yi silar dawowar su gidan mu da zama shi da k'anen shi Muttak'a wato Abban Yusrah". "Hakan Baba na ya rik'a su amana had'e da basu tarbiya gwargwado duk da ba wani hali ne dashi sosai ba, ko da suka dawo gidan da zama dama mahaifiya ta ta rasu tun gurin haihuwa ta sai wata mata da Baba ya auro". "Daga baya soyayya ta k'ullu tsakani na da Kabiru wato Daddyn ku har muka yi aure, shekarar mu kusan bakwai da aure Allah bai bamu haihuwa ba sai daga baya aka samu cikin Son wanda haihuwar shi ta sa Kabiru ya d'auki son duniya ya d'ora mai kuma nan yaci sunan mahaifin shi wato Aminu. Haihuwar shi da wata bakwai ne Allah ya yiwa mahaifina Baba Sani rasuwa inda matar shi Aisha ta gama wanka ta k'ara gaba sanadiyyar bata haihu dashi ba, shi ko Muttak'a ya auro Balkisu mamar su Yusrah". "Hakan zama ya kasance tsakanin mu iya mu saboda bamu da wasu dangi na kusa, Son na da shekara biyar na haifi Saudat lokacin ne Allah ya k'ara bud'awa Dad hanyar samu yana bawa yaran shi kulawa da kuma soyayya wacce ko ni kaina na ta6a su to zan had'u da fushin shi ranar". Lokacin ne kuma arzik'in shi ya k'aru ta hanyar wani babban aminin shi mai kud'i wato Alh Ibrahim wanda yake shahararren mai kud'i sosai, kusan lokaci guda akayi auren mu da nashi, Allah cikin ikon shi matar shi ta samu ciki gurin haihuwa ta rasu ita da abinda ta haifa bak'in cikin hakan ya sa kaf ya had'a dukiyar shi ya ba Dad ajiya, saboda gaskiya babu wanda yasan dangin shi Sana'a ce kawai ta had'a su ko ga hira bai ta6a cewa ga dangin shi ba, don ko neman auren gidan mu aka shige mai gaba, wancan lokacin kurmi ya yi shirin tafiya da zai wuce ne Dad d'inku ke ce mai yaushe zai dawo? Gaya mai ya yi babu rana, sannan ya ce mai in Allah ya yi mai rasuwa ya bashi dukiyar shi kaf. Daga hakan Mum ta yi shiru hawaye na mata zuba cikin k'unar rai.
.
Zajlah ce ta ni sa had'e da rarrashin Mum ta d'auko mata ruwa tasha sannan ta cigaba kamar haka. "Da hakan ya wuce kurmi wanda bayan kud'in abinci da suturar jikin shi bai fita da komai ba dai-dai da gidan shi sai da ya saida sannan ya bar garin nan. Dad ya so ta6a kasuwanci da kud'in da Alh Ibrahim ya bashi ajiya na nuna mai hakan bai dace ba sannan yabar kud'in ma'ajiyar su ya cigaba da juya nashi gwargwado Allah ya bud'a mai hanyar samu ba laifi. Bayan shekara hud'u da tafiyar shi ne mummunan sak'o ya risk'e mu cewa Allah ya yi mai rasuwa sanadiyyar gobara data tashi gidan da suke zaune, wanda wancan lokacin Dad yaso share maganar sai da na takura shi kan cewa yashiga mota yaje kurmi don tabbatar da zancen, hakan ya sa ya shirya ya je wanda bai dawo ba sai da tabbacin duk wanda ke gidan bai fita ba sanadiyyar wutar dare data tashi ba zato ba tsammani. Bayan rasuwar shi da wata uku ne Dad ke maganar dukiyar margyayin wanda sai da aka nemi malamai had'e da takarda daya rubuta na tabbacin tunda baida kowa in ya rasu Dad ya d'auki kud'in, hakan ya sa kud'i suka zamo nashi. Da su ne ya bud'e company da sauran abubuwan shi na kasuwanci."

"Dad ba mutum ne mai son siyen kadarori ba, wanda kullum ina mai bashi shawara kan siyen filaye da kuma shaguna ya bada haya, maganar shi bata wuce yana da dukiyar da ba yaran shi ba har jikokin shi zasu ci su raga wani abu daga ciki". "To yanzu gashi karon farko k'addara ta sauka kan company, kud'in da aka aje account sune ake cirowa ana lalurorin yau da kullum, dai-dai da gida daga wannan da muke ciki sai naku babu ko da filin da za'ayi kiwon kaji a ciki, duk wannan ba shine tashin hankali ba sai tahowar labarin tabbacin Alh Ibrahim yana raye don Alh Taheer abokin Dad da akayi d'awainiyar asibiti dashi shi ya ganshi ra'ayul ayni a Abuja kuma ya bashi tabbacin yana nan tafe kwanan nan". (Ba Zajlah da ake ba labari ba ni kaina Jegal mai d'aukar rahoto ba k'aramar razana nayi ba, don sai da na zaga toilet, _lolx_). Cikin razana ta tayar da kai ta kalli Mum "yana raye fa? To ya akayi haka? Anya ko inda akace anyi gobarar nan yake?". "Tabbas an ganshi kuma shine, don har lambar Dad ya kar6a don ya kira su gaisa, sai dai ko da yakira ni na d'auka muka gaisa saboda Dad na wanka lokacin, bayani nayi mai kan cewa Dad na asibiti bai da lafiya, ba akan komai ba sai don gudun kar yakira Dad yasan da maganar yayi silar tashin ciwon shi farat d'aya a koma sabuwar jinya, to kinji babbar damuwa ta da kuma tashin hankalin mu ni da Son wanda muke neman mafita kamin abin yazo ga kunnen Dad". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hala Mum kud'in za su kai nawa?", cikin tsananin tashin hankali take maganar don jin take yi tamkar ita wannan musibar ta fad'awa. " kud'in wannan lokacin zasu kai million hamsin, kuma Son yace abinda ke cikin account ba zasu biya kud'in mutumen ba, sannan ba muda masaniya akan komai yanzu Zajlah har sai ya shigo garin nan munji daga gare shi". "Mum ina da shawara d'aya akai in har hakan zai yuyu, saboda a kammala kud'in mutumen kamin ya iso". "Zajlah ba muda wata mafita ta kud'i kuma babu wata kadara da zamu saida mu cika mai kud'in shi, shi ne abin dubawa". "Mum ko mu muke da kadara da zamu saka kasuwa a biya komai cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya ji mu ba". "Ta wacce hanya Zajlah?. "Mum gidan mu za'a saka kasuwa a saida mu ko mu dawo nan gidan mu zauna d'ayan part d'in da ba kowa a ciki". *** *** *** Maganganun ta ne yasa yaja birki ya tsaya don jin me za ta furta, abinda ta fad'a ne ya sa yaja ya yi turus, "me yasa duk iya tunanin mu ni da Mum bamu kawo hakan a zuwan mafita ba?, garin ya ya ta fi mu nazari da hangen nesa? Lallai tabbas ba girma ne hankali ba, ba shekaru ne tunani ba, dame yarinyar nan ke aiki cikin kwanyar ta?". Duk shi kad'ai ke yiwa kanshi wad'an nan tambayoyin sanadiyyar mafita da ya ji Zajlah ta samo wanda iya nazarin su basu kawo hakan ba. Mum ce ta janyo Zajlah ta rungume kan jin dad'i tana hawaye, sai albarka take saka mata wanda take jin tamkar ta maida ta ciki kan irin son da take yi mata da kulawa da dukkan damuwar ta. Suna hakan ne ya yi sallama ya fad'o falon, wanda daka kalleshi zaka hango walwala, farin ciki, annashuwa kwance saman fuskar shi, har k'asa ya durk'usa ya gaida Mum, cikin farin ciki ta amsa fuskar ta sake. "Sannu da zuwa", cikin sanyin muryar ta ta furta hakan sannan ta wuce zuwa d'akin Saudat da Mum ta gaya mata tana fama da zazza6i, kuma tana so ta basu guri su gana da junan su.
.
Bayan ficewar ta ne Mum ta kai duban ta zuwa ga Alamein had'e da furta "ka fara ganin irin alkhairin da nake hango ma a cikin zamantake warka da yarinyar nan? Wallahi na yi imani da Allah da wata ce ko siyar da gidan kace za kayi sai kunsha artabu da ita, in ma bata ce sai ka sake ta ba". "Wannan zamanin da ake ciki mun kawo ga6ar da yawancin y'an Mata basu cika yin aure saboda Allah ba, farko kana zuwa neman yarinya za kaji ana fad'in da wacce mota yazo? Daga hakan sai kaji iyaye na fad'in ai ko ki auri abinki ance yana da hankali da nutsuwa, nan ko nutsuwar kud'i ce ba nutsuwar Allah da Annabi ba". "Ina mai baka shawara daka rik'e yarinyar nan amana domin ta wuce k'ask'anci yanzu daga gare ka, ina sane da har yanzu babu wani cigaba a cikin rayuwar auren ku saboda bak'ar ak'idar da ka saka a zuciyar ka na k'yamatar talaka". Cikin razana da mamakin ina tasan irin zaman da suke yi yasa ya tayar da kai ya dube ta. "Kar kayi mamaki kuma kar ka zargi Zajlah da abinda ba haka bane, don tun auren ku wata magana data shafe ka bata tab'a had'a ni da ita ba". "Na dad'e da fahimtar hakan tun ranar da muka je gidan su yiwa mahaifin ta sallama, kuma ko kukan da take yi nasan da biyu take yin shi saboda akwai abinda kayi mata". "Yanzu dai dabara ta rage gare ka ta yanda zaka shawo kan matar ka ku zauna lafiya, don yanzu ka tabbatar da ita ba k'ashin yarwa bace". **** ***** Ko da ta shiga d'akin Saudat bacci take yi, hakan ya sa ta nemi guri ta zauna ta bud'e datar wayar ta ta hau whatsap, yanda taji ana comments kan wani novel ( *AL'ADUN WASU, BATUL MAMMAN*) ya sa ta yi ta tambayar farkon buk d'in, nan take aka tura mata saboda musha karatu akwai kula juna. Datar ta rufe sannan ta hau karatun littafin, sosai buk d'in ke saka ta nishad'i da walwala, dariyar tace ta tayar da Saudat daga baccin da take yi, had'a ido da suka yi yasa tasha jinini jikin ta saboda jiran saukar rashin mutunci kwando-kwando. Kafad'ar ta ta dafa had'e da furta "matar Brother me ya saka ki nishad'i haka kike ta dariya?". Cikin sanyin jiki ta gaya mata har da nuna mata buk d'in, "kai an baro ki baya ai ni yanzu kullum cikin zuba ido nake in matsu ba'a turo cigaban ba, saboda novel d'in yayi gaskiya ga dariya cikin shi sosai". "Aiko da zan iya dana ajiye karatun har tagama duka, saboda banson jira gaskiya matsuwa nake yi". "Ni ko nafi so ana yi ina biya kodon y'an comments dasu ke baka labari kuma ban iya karatu in yayi yawa". "Tabbb ai ina ga babu group d'in da suka kai musha karatu comments, kuma gasu da kula juna gaskiya, oh! kinga na manta, ya jikin ki?". "Ai naji sauk'i sosai don kan ya daina ciwo", hakan suka zauna suna ta hira wanda ni kai na Jegal nake mamakin hakan.

***** ****
Zaune yake jugum yana sauraren maganganun Mum had'e da nazari kan su duk jikin shi ya yi sanyi. "Abu na gaba shine ka dai ga yanda Allah ya sako mana jarabawa farat d'aya wanda bamu yi zato ba kuma bamu yi tsammani ba to ya kama ta ace ka natsu kasan me duniya take ciki, a wancan lokacin in har ina lurar da kai wasu abubuwan sai dai ka rik'a biyar zugar mahaifin ku na rud'in dukiya, yanzu gashi duk tak'amar ku da ji da kan ku da izzar ku ta rushe lokaci guda wanda baku da wata dabara sai yanda wanda ya baku ya yi daku". "A zamantakewar rayuwa ana so mutum yasan k'ima da darajar d'an Adam, ba akan komai ba sai don gama wa da duniya lafiya, wanda ka gani talaka haka Allah ya so ganin shi, ba don ba ya son shi ya yi shi hakan ba, sai dai ban-ban cewa tsakanin rayuwa da kuma hankalta". "Yanzu ka duba kagani yanda Allah ke baiwa kafiri kud'i ya hana wa musulmi, kuma fa ba don ya fi son kafiri d'in akan musulmin ba, a'ah don ya gwada k'arfin ikon shi ne da kuma tsara abubuwan shi yanda yaso. Da wuya kaga kafiri yana fama da talauci tamkar musulmi, ko yaushe za ka ganshi cikin jin dad'in rayuwa, to wannan jin dad'in na duniya shine ribar su gaba d'aya saboda lahira jahannama ce mazaunin su". "Sannan kayi nazarin wacce Sana'a ta dace ka fara, saboda yanzu zama haka kawai ba naka bane, don kaga kaine Babba kuma kaga yanda mahaifinku yake, ko babu ciwo akwai yanayin girma daya kamata kad'auke wa mahaifinka wasu abubuwan". "Ba matsala Mum bari zan binciki Imran da Salis gobe muyi shawara, daga nan asamu mai sayen gidan, in an kammala kud'in sai muga abinda yayi saura sannan asan Sana'ar da za'a kama". "To Allah yasa a fara a sa'a, Ameen ya furta a taka'aice had'e da dogon nazari na rayuwar shi. Duk wad'annan abubuwan da Mum ke jerowa har ga Allah yasan hakane, amma me yasa a wancan lokaci bai yi duba zuwa gare su ba? "Giyar kud'i", hakan wata zuciya ta bashi amsa. Lallai tabbas ya yarda da hakan, saboda yasan in can inda aka fito ne bazai tsaya ya saurari Mum ba har maganar ta tayi tasiri akan shi ba kamar yanzu. Bayan sun gama tattauna wa ne ya k'arasa gurin Dad suka gaisa ya yi mai ya jiki, sannan suka d'an ta6a hira, duk da ba magana mai tsawo yake iya yi ba sosai.
.
*WASHE GARI*
Wata shawara ce ta yanke a ranta bayan ta kira Salmat ta gaya mata abinda ke faruwa, inda ita ma ta tausaya masu sosai had'e da k'ara k'arfafa mata gwuywa kan abinda za tayi. Bayan ta gama breakfast ne ta jera a dining table sannan ta fad'a wanka ta fito ta kimtsa, sanin cewa yanzu yana gurin Dad ya sa ta shiga ta kimtsa d'akin na shi kamar kullum sannan ta fito ta ci abinci. *11:00am* Ta fita zuwa gidan Shema'u mak'ociyar ta, "yau wace rana Zajlah a gidan nan?", cewar Shema'u. "Kai Anty shaidar da za kiyi min kenan, yanzu fa zuwa na na uku kenan gidan nan, ai gara ni kefa zuwan ki biyu". Da hakan dai suka gama zolayar juna sannan suka gaisa, jugum ta yi kamar kar ta furta abinda ya kawo ta, sai kuma take tunanin duk duniya bayan Salmat babu wanda za ta iya gayawa halin da take ciki bayan Shema'u d'in, saboda ta yaba da hankali da nutsuwa irin tata, kuma ba mace ce mai yawan surutu ba ga alama za tayi rik'on sirri kuma gashi za ta girme ta da kusan shekara shida ko bakwai, sai da ta gama nazarin ta Shema'u na gurin kawo mata ruwa da d'an lemo ta dawo kenan take furta mata abinda ke tafe da ita kan ta yi mata magana da masu sayen kayan d'aki. "Ke ko Zajlah me zai kai ki siyar da kayan d'akin ki?, duka fa aure ko wata hud'u bai yi ba za ki siyar da kayan d'aki". Nan ta kora mata bayanin abubuwan da ke faruwa, sannan ta bata tabbacin za ta sa a nemo masu siya. "Kinga ko banyi mutunci ba wallahi ban shiga yiwa Mum Allah ya tsare gaba ba da abinda ya faru, Baban su Taheer d'ai yaje dubiya sau biyu". "Yanzu ko daga nan can zan shiga", "ina ga bara in d'auko hijab d'ina muje tare in dawo". Hakan suka fice zuwa gidan su Alamein, Shema'u ta yi jaje da Allah tsare gaba ta koma gida. *********** Su Imran suka samo masu sayen gida aka yi ciniki suka sai da inda Alamein ya nemi su bashi kwana biyu ya kwashe kayan shi daga gidan, da hakan suka fice zuwa gidan su shi da su Salis. Kamar yanda Shema'u ta yi alk'awari hakan ya sa ta nemo masu siyen kayan d'aki aka dace da masu siyen su cikin daraja Zajlah ta sai da, kayan kitchen sai kayan falo da keken d'inki kawai ta bari.

******
6angaren Alamein kuwa yaje gida gurin Mum sun tattauna yanda abubuwan suka kasance, sannan ya d'ora da gayawa Mum tasa a gyara masu d'ayan part d'in gobe da safe zai samu way'anda zasu kwaso masu kayan su, da hakan ya wuce gidan shi. Motsi ya ji a kitchen alamar Zajlah na ciki, yana son yashiga ya gaya mata ta kimtsa kayan ta zuwa gobe za su koma gidan Mum kuma yana jin nauyin yanda zai yi mata magana, saboda tun zamantakewar su maganar arzik'i bata ta6a had'a su ba, hakan ya sa ya tunkari kitchen d'in gaban shi na dukan tara-tara. Alamar mutum ta ji a bayan ta ta juyo ta ganshi tsaye ya jingina da k'ofa ya sako mata ido, "sannu da zuwa", cikin sark'ewar murya da in ina ta furta hakan. Da sakewar fuska ya amsa mata sannan ya d'ora da cewa "kar kiyi girkin dare saboda yau za mu yi parking kayan mu gobe a kaisu can, don an sayar da gidan kamar yanda kika buk'ata". "Ba matsala Allah ya kai mu lokacin", da hakan ya wuce d'akin shi. Bayan ta gama girkin ne ta ajiye mai nashi ta d'ibi nata ta ci, sai ta yi zugum tana so taje d'akin shi ta had'a mai kayan shi guri d'aya amma bata son abinda zai had'a ta dashi guri d'aya kuma tasan yanzu yana d'akin bai fita ba. Hakan dai ta daure ta nufi d'akin shi, ta fi minti biyar bakin k'ofa tana sak'a yanda za ta Shiga d'akin, jin motsin zai fito yasa ta k'wank'wasa k'ofar. Mamaki ya hana shi bud'e k'ofar ya yi zurum, sai da ta buga a na ukun sannan ya murd'a k'ofar ya ra6e gefe d'aya. Tsaye ta yi tana wasa da yatsun hannun ta sannan ta furta, "kayan kane zan had'a ma". Hanya ya bata alamar ta shiga d'akin, k'ofar ya rufe ya dawo ciki shi ma, ganin hakan ya sa gaban ta ya bada daram!, saboda ta zata fita zai yi don da shirin shi ta ganshi. "Hala kin kammala na ki kayan guri d'aya?", tambayar ce ta doki dodon kunnen ta. "Eh" ta furta a gajarce. "To bara in kama maki aikin saboda suna da yawa". "Ah da ka wuce kawai ai zan iya tunda ba girkin dare zanyi ba", ta furta hakan ne saboda ta fi so ya fita ya bata guri tayi aikin ta za tafi Samun sakewa, amma tasan zaman shi zai takura ta. Shi ma 6angaren Alamein gidan su ya yi niyyar zuwa ya turo Saudat a zuwan za ta kama ma Zajlah had'a kayan, to yasan in har ta zo to Zajlah za ta kama suyi aikin tare ne, amma da ta nuna za tayi ne ya sa ya fasa fitar. Nan dai suka zauna jigum ba mai magana, shi ya yi k'arfin halin bud'e wardrobe yana jido kayan shi yana d'orawa saman gado, sannan ya bata umurnin ta d'auko akwati na ta jera kayan a ciki, ba k'aramin mamaki ta yi ba ganin yawan suturar shi kama daga manyan kaya zuwa k'anana. 6angaren turarukan shi suka koma ana jibga su guri d'aya, ta d'auko wani turare za ta ba shi yasaka a wata jaka karaf hannun su ya had'u guri d'aya, wani shocked da suka ji ne ya sa cikin sauri dukan su suka janye hannun su kowane a tsammanin shi d'ayan ya rik'a, hakan yasa kwalbar ta sauka k'asan tiles ji kake yi tarassss, da sauri ta ja baya sai ga k'afar ta saman kwalbar da ta fashe ta watsu a gurin. K'ara ta saki da k'arfi ta rik'e k'afar tana yarfe hannu, da saurin shi ya zo gurin ta ya bata umurnin ta zauna bakin gado, dak'yar ya samu ta tsaya ya cire mata guntun kwalbar inda jini ke ta zuba, nan ya samu ya yi mata dressing gurin had'e da duban ta irin yanda take ta zubar hawaye tana cije le6e had'e da runtse ido. Nan ya barta ya je ya kwashe kwalbar ya k'arasa had'a kayan, sai murmushi yake yi shi kad'ai ganin yanda ta yi kuka had'e da shagwa6a tamkar wata k'aramar yarinya, hakan ya sa ya ji ta burge shi.
*washe gari*
Jakar ta ta hannu kawai ta d'auka ta fice daga gidan tunda ya gaya mata zai samu way'anda za su kwashe kayan duka akai gidan su, ko da ta fita ko ruwan Lipton bata sha ba saboda ya gaya mata kar ta kunna komai na amfanin girki, kuma Mum ta kira ta gaya mata cewa za ta yi girkin safe dasu. Karfe *10:00am* ta shiga gidan, bayan ta gaida Mum ta yi mata jagora ta k'ara duba jikin Dad had'e da gaida shi sannan suka dawo falo suka zauna. "Meke damun ki naga kina Jan k'afa?", Cewar Mum. Nan ta labarta mata abinda ya same ta da suna gyaran d'aki, jajanta mata tayi ganin abin da d'an sauk'i. "Ina Saudat halan? Banji motsin ta ba". "Ta ji sauk'i yau ta wuce skul, kinsan tun ciwon Dad bata koma skul ba, to suna ta shirye-shiryen exam ta k'arewa shiyasa yau ta je", "ok Allah ya taimaka". "Amein", ta furta sannan ta had'awa Zajlah kayan kari ta kai mata falon ta saboda tasan ba za taci tare da su ba. *********" 6angaren Alamein kuwa ba k'aramin mamaki ne ya cika mai ciki ba da ya shiga d'akin ta da sunan fitar da na ta kayan ba, saboda wayam ya gani ba komai kuma ya san dai ko da aka kawo ta da kayan d'akin ta, asali ma gaban shi aka had'a su saboda ranar Mum ta takura shi dole sai ya tsaya gidan har a k'are aikin sannan in fita zai yi ya fita. D'akin ya gani da alamar an d'auke kaya a gurin, to ko ta kai kayan ta ne wani gurin? Ko kuma ta sa ankai mata can gidan? Ganin bai samu amsa bane ya sallami masu kwashe kayan daga d'akin ta, saboda akwatunan tufafin ta tun safe ta saka almajirai suka kai mata, kujeru kuma da sauran tarkace dama ya sa an fita dasu. Ba'a gama ba sai kusan k'arfe d'aya na rana, saboda wasu na kwashe wa suna kai gidan su can kuma da masu had'awa. Dama part d'in da aka basu babban falo ne mai d'auke da d'aki biyu da suke fuskantar juna kowannen su ciki da falo sai toilet a cikin su, kamin a Shiga falon akwai kitchen da store, sai kuma 6angare d'aya toilet d'in tsakar gida. D'aki d'aya aka saka mata na ta kayan a falo sai katifa uwar d'aka, shi ma aka saka mai na shi kayan d'ayan d'akin. Da hakan aka kammala komai na gyara gurin. Zajlah da Saudat suka taya Mum girkin dare sai da suka gama ne sannan ta shiga part d'in su ta yi wanka akan tsabar gajiyar da take ji, abinci ta ci sannan ta je ta kwanta saboda dama Mum ta sako masu nasu wanda dashi ta shigo ta d'ibi na ta ta ajiye mai sauran. Bata fi minti goma da kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da ya shigo bai ji motsin ta ba hakan ya sa ya ci abinci ya yi wanka, jin ya yi yana son yaduba ya yanayin k'afarta yake, da hakan ya doshi d'akin ko da ya shiga tana kwance uwar d'aka saman katifa daga ita sai wata night gown mai d'an sharara sai dogon wando gashin kan ta ya bazu saman filon da ta yi matashi dashi, kallo d'aya ya yi mata ya kauda kai saboda wani abu daya ji ya tsirga mai, kuma bai ta6a ganin mace a irin yanayin da ya ganta ba, bakin katifar ya dawo ya zauna ya kai duban shi ga k'afarta yaga gurin har ya soma haushi kad'an, hannu ya kai zai ta6a gurin kuma ya fasa daga hakan ya zabura ya fice daga d'akin tamkar wanda aka tsikara.
*********
Tana tashi da asuba ta gabatar da sallah had'e da azkar d'inta sannan ta koma saman katifa ta zauna saboda ba aiki za tayi ba don Mum ta gaya mata da safe za'a kawo masu breakfast, tana so ta shiga part d'in su ta taya Mum aiki kuma tana ganin ta yi sauko dayawa, don tasan saurin karyawar su gidan k'arfe *10:00am*. Kud'in ta ta jawo ta irga ta koma maidawa ta ajiye a tunanin ta lokacin buk'atar su bata yi ba. Bugun k'ofa ta ji ya sa ta zabura ta fito ta bud'e, Mama talatu ce ta kawo masu kayan breakfast bayan ta kar6a ne ta gaida ta ta koma daga ciki, abinci ta ci sannan ta shiga wanka bayan ta kimtsa ne ta shiga gurin su Mum. ******** Bayan azzahar ne Salmat ta kawo mata ziyara, bayan ta gaisa da Mum ne take tambayar jikin Dad inda Mum ta gaya mata ya samu sauk'i sosai. Part d'in Zajlah suka koma aka baje sai hira ake ta zabgawa had'e da shawarwarin abubuwan da suka shafe su.
.
Akwana a tashi yau satin su biyu kenan a gidan su Alamein, wanda har yanzu babu labarin Alh Ibrahim sai dai a ko yaushe suna masu sauraren zuwan shi, jikin Dad kuma ya yi sauk'i sosai sai dai bai iya doguwar tafiya haka kuma bai cika son doguwar magana ba don in ta yi tsawo ji yake yi tamkar numfashin shi ya d'auke. Kusancin su ya sa abubuwa sunyi sauk'i sosai a zamantakewar su, saboda Alamein na ba ta kulawa gwargwado, kuma wani lokaci sukan had'u part d'in su Mum a baje ana ta hira, amma fa baza su iya hira tsakanin su ba saboda kowa tsorace yake da wani. ********* 6angaren Zajlah an samu k'aruwar wayewa a gare ta ta hanyar Anty Shema'u da kuma group-group na whatsap musamman na kwalliya da ake turo videos na kalar kwalliya iri-iri, wasu ma in an turo bata gane ba to gidan Shema za taje tayi mata bayani in ma ta kama ta zauna tayi mata to za ta yi mata da kanta. Tun lokacin da aka yi mata aure Mama Asabe da Mama Inno basu zo gidan taba sai kwana biyu da suka wuce, koshi don ta dame su ne kan basu tahowa kuma Mum tasa baki shiyasa suka zo, inda taji dad'in zuwan su sosai. ****** Yau saura kwana biyu auren Yusrah da Imran, su Zajlah babu zama musamman da Mum ta mayarda Yusrah gidan kacokan, a cewar ta ita za ta shirya abar ta, duk wani kayan had'in gyara na jiki ko na Mata a tare Mum ke had'a masu shi wato Yusrah da Zajlah, inda Zajlah ta fito real amarya sai wani k'amshi suke zabgawa ita da Yusrah. Kamar yanda Yusrah ta k'udurta ma ranta tun auren Zajlah haka ta gaya wa Mum cewa makarantar su Zajlah za'a yi mata walima saboda bata son bidi'o'in nan na raya Al'adu, ba k'aramin dad'i suka ji ba na za su ziyarci makarantar su, ko banza sun San cewa tsarin Malaman su da d'aliban na burge mutane da dama.
,
A gurin walimar ne suke jin labarin auren Ustaz Yusuf da kuma Ustaz Lukman sati biyu da suka wuce, inda matar Ustaz Yusuf ke basu tabbacin har mazan su sun zo auren kuma tare da gudummuwa, nan suka yi masu fatar alkhairi aka k'are walima kowa ya kama gaban shi. Washe gari bayan d'aurin aure ba'a gabatar da komai ba sai dare amarya ta tare a gidan ta dake ni'ima inda basu da wani nisa sosai da Salmat, Zajlah ne da Saudat suka tashi za su fice ta dafa kan Yusrah had'e da furta "muna jiran baby nan da wata goma, saboda ke ga su wance anji hud'uba ta sai wani tartsin yawu ake mana", tana maganar ne had'e da kallon Salmat tana murmushi. Sanin cewa tsokanar ta ne take yi ya sa ta yi shiru ta k'yale ta sanadiyyar yanzu baki ya mutu ko dogon surutu bata so. Da hakan suka watse suka bar Yusrah had'e da yi mata fatan alkhairi. ******* Bayan kwana uku ne da auren Yusrah Alh Ibrahim ya diro garin Jega, direct wayar Dad ya kira kuma akayi sa'a da babu kowa a tare dashi, kuma gashi su Mum basu yi mai bayanin komai ba. Wayar ya d'aga suka gaisa ba tare da yasan waye ba, daga baya Dad ke tambayar shi waye halan saboda bai gane mai magana ba, amsa ya bashi da cewa wani tsohon aminin shi zai kawo mai ziyara, ba tare da tunanin komai ba ya gaya mai address d'in gidan shi. Suna gama waya Mum na doso d'akin na shi, nan yake gaya mata zai yi bak'o duk da bai san waye ba, ya dai ce mai tsohon aminin shi, take nan gaban Mum ya bada rass, saboda jikin ta na bata Alh Ibrahim ne, ganin jikin ta ya yi sanyi ya sa yake tambayar ta ko lafiya, cikin yak'e take bashi amsa da ba komai, "bara inje ad'an tanadi d'an abin motsa baki wa bak'on", da hakan ta fice daga d'akin ba tare data jira me zai ce ba. Wayar Alamein ta kira had'e da gaya mai duk inda yake yayi sauri yak'araso gida. Lokacin yana tare dasu Imran suna process d'in wane business ya kama ta su fara, nan ya yi masu bayani da sauri ya wuce gida. A gate suka had'u da juna dai-dai yana waya da Dad yana gaya mai gashi ya iso gidan, nan Alamein ya tsaya suka gaisa Alh na ta mamakin girman shi, da hakan ya yi mai jagora cikin fargaba suka doshi hanyar shiga falon. Sai yanzu Mum ke nadamar rashin gaya mai da basu yi ba, ba akan komai ba sai akan matsalar ciwon da yakan iya tashi farat d'aya wata babbar matsala ta samu, saboda ko dawowar su Alamein gidan bata gaya mai ansayar da gidan su bane, kawai ta ce mai wani gyara ake yi gidan in an gama za su koma, wanda ga wancan lokacin take hango hakan a zuwan mafita sai yanzu take nadamar aikata hakan.

0 comments:
Post a Comment