A DALILIN GATA Part 11-15
.
Sun baro part d'in shi ne suka had'u da Mum har za su fice daga gidan, bayan sun gaisa ne take tambayar su shirye-shiryen da suke yi a game da auren. "Gaskiya Mum babu wani abu da za muyi, saboda yanzu haka daga gurin yarinyar muke ita ma babu wasu events a tsarin ta, walima kawai za su yi a islamiyar su". "Ni ma ranar assabar zan had'a k'aramar liyafa insha Allah. Ku cigaba da lurar da mutumen ku had'e da shawarwarin da suka dace, Allah yak'ara had'a kan ku yabar zumunci". "Ameen Mum, ai tsakanin mu da Alamein sai dai godiya don ya yi mana duk yanda ake yi", cewar Imran. Nan Mum ta wuce bedroom d'in Dad, ta bi shi da ido hankalin shi kwance yana karatun jarida. Gefen shi ta samu ta zauna sannan ta fara magana. "Ya kama ta a fara shirye-shirye, na ga ko I.V baka bugo ba gashi lokaci sai k'aratowa yake yi". "Kisa a buga ko Abban Yusrah yasa a buga don ni na fad'a maku bazan saka baki na a wannan auren ba har sai na ga cewa Son ya sauko yana walwala kamar kowa". "Yo ko yanzun ce ma akayi baya son maganar?, ni fa na rasa gane wane irin mutum ne kai, don Allah kayi hak'uri ka saka ma wannan auren albarka". Dak'yar da lallami ta samu ta shawo kanshi ya sauko har suna tattaunawa kan abubuwan da suka dace ayi na auren.

*******
Akwana a tashi wataran jariri ango ne, yau dai ga shi har ansaka Zajlah a lalle duk wani abu da za'a yi na al'ada 6angaren amarya da ango duk anyi, inda a 6angare d'aya Amarya tasha gyara daga wata shuwa dasu Mama Asabe suka d'auko musamman domin wannan rana. Yau ce ranar da za'a yi walimar Amarya a makarantar su, inda ba k'aramin jurewa Ustaz Lukman ya yi ba cikin Maluman da suka gabatarda walimar. Amarya tasha nasihohi sosai ga Malaman ta sai dai fatar d'orewar zaman lafiya ita da angon ta. "Yanzu Yusrah duba kiga wai wannan yarinyar ce Brother zai aure, da ace auren da yake so ne da events da za'a sai mun ture". "Ai ko hakan ba laifi, don ni dai abin ya burge ni sosai har ina tunanin in aure na ya tashi ni ma irin wannan walimar za'a yiman". "Ni kam wallahi ranar aure na sai an gwangwaje bazan yi irin wannan ba, kinga har Mum ta biye wannan abin wai ita ma za tayi liyafa gobe". "Ke inda Dad na son wannan auren ai wallahi da yanzu gari ya d'auka tun ana saura wata d'aya auren, amma duba yanzu wai gobe d'aurin aure amma abu shiru tamkar mutuwar sarkin gari". Dariya sosai Yusrah ta yi tana mamakin wannan ak'idar ta Saudat na k'yamar talaka, ta san da ace Zajlah masu kud'i ne to da duk yanda suka tsara abin ba za ta kushe ba. "Mu wuce gida Yusrah tun da an k'are". Maganar Saudat ce ta dawo da ita hayyacin ta. "Kibari mutane su rage sai mu gaisa da amaryar sannan mu wuce, kin ga yanzu jama'a sun mata yawa". "Don Allah ki wuce muje, ai dai tasan ba za'a rasa zuwa daga dangin Angon ba kuma munzo buk'ata ta biya ai shikenan". "Miye amfanin kiran sallar kurma?", ce war Yusrah. "Ban fa fahimce ki ba, ke sai ki rik'a je fawa mutum magana a dunk'ule". "Ke kuma ga ki ba cikakkar bahausa ba, to ina nufin miye fa'idar mu zo bamu gaisa da Amarya ba mu fice". "To ni dai ba don ta na zo ba, saboda yaya na nazo kuma babu lallai sai na tsaya". "Yo ai duk d'aya an cewa shege marar uba". Maganganun na Yusrah suka ishe ta ya sa taja bakin ta ta tsuke, ba don ta so ba ta tsaya har mutane suka rage sannan suka k'arasa gurin ta, cikin yatsinar fuska Saudat ke kallon su da d'ai d'aya sun sha manyan hijabayyen su har k'asa. "Kyawon zaman takewa ka samu abinda yada ce dakai, amma wasu da ka gansu kasan abin sai maneji". "D'an hakin da ka raina shi ke tsokane ma ido, kuma mutunci siyen shi ake yi ba shi ke kai tallan kanshi ba, mai hikima shi ke tauna magana kamin ya watso ta, wani ko maganar ke neman mak'alewa domin ya suturta ta shiko yana k'ok'arin hankad'o ta". Cikin muzan ta Saudat ta bi Salmat da kallo had'e da mamakin kalaman da ta feso mata tamkar dafin maciji. Yusrah ce ta tsaya suka yi gaisuwar mutunci har suna ta6a hira tsakanin su, daga nan suka fice su kuma suka shiga napep sai gida.
.
Yaune ranar Assabar misalin k'arfe *12:00* dubban jama'a suka shaida auren. *AL'AMEIN KABEER AL'AMEIN (A.K.A)* DA *ZAJLAH ABUBAKAR ZUBAIR (ZAZ)* Wanda ya samu halartar manyan bak'i daga gurare da dama duk da ba hakan Dad ya soba, musamman gidan su yarinyar da yake ganin k'ask'anci ne kamar shi yaje wannan k'azamar unguwar kuma ace auren d'an shi ake yi gurin. Dak'yar da lallami k'anen shi Abban Yusrah wato Alh Muttak'a ya shawo kanshi kan zuwa gurin auren. A 6angaren Alamein kuwa shi ma dak'yar da lallami Mum dasu Salis suka ciwo kan shi ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin dakakkiyar shaddar shi fara k'al wacce ta k'ara fito da kyawon shi na asali, sai dai daka dubi fuskar shi babu annuri sam a tattare dashi. Bayan gama d'aurin auren ne Imran ke yimai tuni kan gaisuwar da Ango da abokanen shi ke shiga yi gidan su Amarya, tur6une fuska ya yi tamkar wanda aka yiwa wahayi da mutuwa. "Kayi hak'uri A.K.A kakka bijirewa umurnin Mum in kayi hakan ba za taji dad'i ba kuma kasan da za mu fito sai da ta k'ara jaddada mana hakan". Da hakan suka d'an shawo kanshi suka shiga gidan su Zajlah shi da tsirarrun abokanen shi suka gayar da iyayen, sai yak'e yake yi wanda ya fi kuka ciwo had'e da wani tur6une fuska tamkar yad'ora hannu Saman kai yafasa da kuka. Muryar Salis ya ji had'e da wasu friends na su suna tambayar ina Amarya ta fito a gaisa. Zumbur yamik'e tamkar wanda ya zauna akan kunama, hanyar fita daga gidan ya dosa ganin hakan ya sa suka mara mai baya. Can na tsinkayo maganar wata daga cikin dangin Zajlah na giwa tazo na furta. "Gaskiya wannan Angon na da kunya akan wasu mazajen da za kaga sun shigo gaida iyaye an saka Amarya gaba har da su d'aukar hoto". "Gaskiya kam wannan na da sauran kunyar shi", inji wata mata. Da hakan sauran k'awayen Zajlah suka shiga gidan su Salmat suna ta yabon kyawon angon, har wasu na zolayar ta da cewa' "shiyasa ake mana 6oyon Angon ashe ansan mai tsada ne hakan, gaskiya kin more Allah yabada zaman lafiya". Salmat ce ta kar6e da Ameen had'e da cewa ai dole mu 6oye angon mu ga irin ku masu hangen kyawawan Maza. Da hakan dai suka ta zolayar juna wanda Zajlah tayi shiru ita d'ai tasan me take tunani a ranta saboda tana hango abubuwa da dama.

*10:00pm* Aka kai Amarya d'akin ta had'e da y'an rakiyar ta iyaye da abokanai har da dangin ta y'an giwa tazo, a unguwar G.r.a aka kaita gida ne d'an matsakaici mai part uku wanda yasha shuke-shuke na flowers sai k'amshi ke tashi. Nan dai dangi suka yi mata nasiha gwargwado had'e da lurar da ita muhimmancin hak'uri da biyayya, har wata na cewa duk da munsan abinda za mu fad'a duk malaman Ku sun riga mu. Da za su tafi ta ci kuka sosai har ta gode Allah inda take ta tunanin wace rayuwa za ta fad'a yanzu. Har k'arfe goma sha biyu bataji d'uriyar kowa ba, da hakan ta rage kayan jikin ta ta zazzagaya d'akin wanda ta jinjina ma mahaifinta da k'ok'arin da yayi duk da cewa yawanci siyayyar da kud'in da ta samu a musabak'a ne, ta ji dad'in ganin cewa har da keken d'inkin ta aka had'o mata dashi. Da hakan ta shiga ta watsa ruwa had'e da alwala ta yi karatun K'ur'an had'e da addu'o'in ta, ba ita ta kwanta ba sai wurin k'arfe d'ayan dare. ***** 6angaren Alamein kuwa ba yanda su Imran basuyi ba kan siyen wani abu da zai shiga dashi gida yak'i, Salis ya nuna zai siya kuma ya hana. Dai-dai da rakiyar da akewa Ango d'akin Amarya cewa yayi ya hutar dasu, hakan ya fice ya bar su nan da mamaki fal a ransu. Da shigar shi gidan ko ta kan Amarya bai bi ba yayi part d'in shi, kayan jikin shi ya rage yayi wanka duk da bak'ar yunwar da yake ji hakan ya dunk'ula ya kwanta don rabon shi da abinci tun goma na safe. ***** Kiran asubar farko ta tashi daga baccin, sallah ta fara gabatar wa sannan ta zauna zaman lazimi wanda bata tashi daga gurin ba sai bakwai na safe. Carpet d'in sallar ta ninke sannan ta d'an kimtsa d'akin, k'ullewar da cikin ta yayi ne ta tuna rabon ta da abinci tun la'asar d'in jiya. Bugun k'ofar da ta jine yasa ta saka hijab d'inta ta fito falon, kayan abinci ta gani jere a dinning table d'in. Gate ta nufa inda take jin k'arar ta bud'e k'ofa Sagiru k'anen Salmat ta gani da kula had'e da babban jug. Gayar da ita ya fara yi sannan ya mik'a mata kayan had'e da juyawa zai koma. "Kashigo mana daga ciki". "Aah zan ko ma islamiya ne ko yanzu break muka fito Mama ta aiko ni". "To mu shiga in baka kud'in mashin ko?". "Mama fa ta bani, ga ma mai mashin nan na tsaida waje zai ko ma dani". "Duk dai salon kar ka shigo ne, to ya yi ka gaida su na gode, ka gaya wa Salmat ina dubin ta". Da hakan ya wuce ta rufe k'ofar ta juya zuwan falon, abinda taci karo dashi ne ya saka ta razana wanda saura k'iris jug d'in yafad'i daga hannun ta. (Maryama ga shi na cika alk'awari, tun da ba'a bani wani novel sai na turo nawa, _lolx_. Masoya na masu kira na, masu kula ni private da kuma group nagode sosai Allah yabar zumunci. Daga yau zaku rik'a samun wannan buk sau biyu kullum insha Allah, luv y'all My fan's.) ® *SDY JEGAL* Dedicated to Anty ```Jidda Musa```. [2/5, 12:31 PM] *SDY JEGAL*: *ADALILIN GATA* *(16)* *DAGA TASKAR Y'AR MUTAN JEGA* www.sadijegal.blogspot.com ®NWA *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Tana doso falon karaf idon su suka had'e yana mai aika mata da mugun sak'on harara tamkar fararen idon shi su fad'o k'asa. Gaban ta ne ya yi mugun fad'uwa had'e da razana, ba k'aramin k'ok'ari ta yiba gurin rik'e kayan da ke hannun ta har za ta ratsa shi ta wuce part d'in ta komai ta tuna ta durk'usa har k'asa ta gaida shi, ba tare da ta jira zai amsa ba ta wuce kawai. Mamaki ne fal a ranshi sai kuma d'imbin haushi dake cunkushe da zuciyar shi na ganin ce wa ga abinci Mum ta aiko masu tun d'azu amma don rainin hankali ta kira gidan su akawo mata abinci. Wata zuciyar ke yimai tuni kan cewa ka gaya mata an kawo abinci? Ko kuma jiya da ka yi kwanciyar ka ka yi tunanin me za taci?.
.
Hannu ya bud'a alamar ba ruwan shi ko a jikin shi. Abin sai damun shi yake k'ara yi yanda ya ga wannan mitsitsiyar yarinya wai itace matar shi, a tunanin shi ma ko sa'ar Saudat k'anwar shi bata yi ba aiko k'auye an rage wannan bala'in. Hakan dai ya zauna saman dinning table ya d'an tsakuri abincin kad'an saboda tun ranar da maganar ta 6ullo bai k'ara saka wani abincin kirki a bakin shi ba, har wata rama ya yi sai tsawon da manyan ido. ****** 6angaren Zajlah kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba na mugun kallon da ya bita dashi, tun jiya take ta nazari ko za ta kamo makamar auren amma kash data had'a zaren zai tsinke. Saboda tun tashin ta ko a tarihi bata ta6a ganin angon da ya shigo gida daren amarcin sa bai waiwayi Amarya ba sai a kanta. Yanzun take d'ora abubuwa akan mizanin awo ko za ta samu wanne zai rinjayi wani, sai dai abin sai k'ok'arin gagarar ta yake yi. Ba komai bane wannan sai zuwan Mum gidan su da kuma zuwan su Imran, sai dai a tunanin ta mizanin awon ta zaifi rinjaye akan zuwan Mum. Ba akan komai ta karkata can ba sai ganin babu tausayi ko kad'an a k'wayar idon angon barrantana shi So ya samu mazauni ko da kad'an ne, kenan hakan na nufin Mum ce mai auren sanadiyyar gajeren taimakon da tayi mata, inko hakan ne wani taimako ya kusa zama masifa domin dai ita wannan bai dad'a ta da komai ba sai tarin k'uncin rayuwa, in ko hakan ne sam babu adalci a cikin wannan lamarin da sake ashe ranar walima k'anwar shi tadinga so ka mata magana, wanda a wancan lokacin har laifin Salmat ta so hangowa na mayar da martani da ta yi. Tabb lallai ko akwai aiki sabo wankan jego da ruwan fridge. K'arar da cikin ta ya yi ne ta dawo daga duniyar da ta lula, kular ta bud'e taga waina da miya ce sai kuma kunun tsamiya cikin jug. Sanin cewa ba ta iya canye ta ya sa ta dake ta fito daga d'akin, kitchen ta nufa ta d'auko plate da cup har ta dawo d'aki bata ganshi ba. Abinci ta ci sai da ta yi k'at sannan ta shiga ta yi wanka ta kimtsa had'e da k'ara kimtsa d'akin na ta. ****** *04:30pm* Sai hada-hadar shiri ake yi domin y'ar liyafar da Mum ta shirya da za'ayi a gidan ta nan cikin G.r.a d'in wacce za'a yi Mata zalla. Yusrah ta kira ta aike ta takaiwa Zajlah kayan da za ta saka. Duk k'awayen ta da dangi na kusa ko wa ya zo har da iyaye sun hallara gidan Mum. Wata dakakkiyar shadda kalar purple Mum ta aiko mata sai wani k'aton gyale mai kalar ash da takalman ta ash, Salmat ce mai take mata baya har zuwa masaukin da aka yi mata. Mum Faty & Jegal fan's su ne na farko da isowa gurin liyafa, su Bizzy, Yagani, Zainab, Sharubutu, Maryam, Mmn Eman, Hindatu sune kan gaba-gaba, Musha karatu group su ma sun hallara inda Fatima, Aunty Baraka, Maryama, Ummietta wabi, Mrs Zannah ke ta rabon ido, Mumbarin Jabo ma sun iso Innah Habiba da Yasmeeny a sahun gaba. Zauren karatu Serdeeyer, Meenah, Batul A. Go I sune a gaba, sai Zumunci group had'e da Greatest women inda khairat, ummen Alamein, fati salihu, Jamila sahabi suke jagorantar sauransu. Zahra B~B fan's duk ba'a barsu baya ba, Ashnur, Hauwa jidda, Anee fan's Anee, Ayusha, Zayyenab sun hallara su ma, sai kuma y'an Taskar Lubiee. Kallo ne ya ko ma k'ofar shigowa gurin sanadiyyar wasu Mata da suka doso gurin cikin ankon su na materials iri d'aya wato blue sai gwaggwaro da takalman su kalar sky, cikin nutsuwa suke tafiya har suka doso gurin, Stylish, Autar Hjy, Feedoh Deedoh, Munayshat, Miss Hafcy, Queen Miemie sai kuma Miemi Bee, Fulani ced'iya, Hauwa damary, Mrs Umar su ne suka fara ne mawa manyan su gurin zama sannan suka zauna, ba kowa bane wad'annan face Nagarta masu Nagartattar zuciya duk inda suka gilma kallon su ake yi tamkar wasu taurari. Da hakan akaci liyafa cikin farin ciki da walwala abin sai son barka.
.
Bayan an watse daga liyafar ne Mum ta tsaida ta gidan ita da Salmat a ce war ta su bari mutane su watse lokacin an gama gaisawa tasa direba ya maida su, duk da ba wani nisa ne dasu ba. Ad'an zaman da ta yi na awanni ne ta fahimci tsantsar son da Mum ke yi mata da kuma Yusrah wacce ta fahimci d'iyar k'anen Baban shi ce, sa6anin Saudat dake bin su da muguwar harara. Zuwa bayan isha'i ne Dad ya shigo gida, bayan Mum ta yi mai barka da dawowa ne take gaya mai cewa, "na fa tsayar da matar Son don ku gaisa". "Ai da kin bar ta ta wuce ba sai mun gaisa ba, tunda ke da kika k'ulla abin kin ganta kuma ta gan ki. Wai ma kina hankalce da yanda kika lalatamin rayuwar yaro?". "Haba Dadyn Alamein ban fahimce ka ba, me ya ka wo wannan maganar?, me yasa abu baya wuce wa a gurin ka?".
.
"Ba wai baya wuce wa bane, rai na ke 6aci in har na dubi yanda Son ya koma yanzu, walwala, farin ciki, nishad'i duk sun kau a rayuwar shi har wata uban rama ya yi duk ya zabge tamkar wanda ya kwanta ciwo". Murmushi ta yi irin na su na manya had'e da furta "Adalilin gatan da nayiwa Son in har muna raye za kaji dad'in abin, kai dai ka rik'a d'ora shi akan turba ta k'warai had'e da lurar dashi wasu abubuwan". Tana kaiwa k'arshen maganar ta fito zuwa falo ta janyo Zajlah sai falon Dad. Har k'asa ta durk'usa ta gaida shi cikin nutsuwa da girmama wa, har ga Allah yarinyar ta burge shi sosai, sai dai matsalar d'aya ce da Son baya son ta. Saboda shi fa duk abinda zai yi sanadiyyar farin cikin yaran shi yake yin shi, kuma in ba su son abu har ga Allah zai iya yafe abin nan duk son da yake yimai. Mum ce ta ta6o shi alamar yayi magana ya sanya wa auren albarka, hakan ya yi gyaran murya suka k'ara gaisawa ya sanya mata albarka had'e da fatar zaman lafiya. Da za ta wuce dubu goma ya ba ta, sai dai k'in kar6a tayi sai da Mum ta kar6ar mata. Mum kuma turarukka had'e da humra y'ar asali ta Maiduguri ta had'a mata, har za su wuce take tambayar ta ina wayar ta halan? Amsa ta ba ta kan ce wa wayar na cikin kayan lefen ta ko bud'a ta bata yi ba. "In kinje gida ki had'a wayar mana tunda can su Maman Sagiru sun hana kiyi amfani da ita, ko ba kyaso ki gaisa da k'awaye da kuma ni Mum d'in ki?". Murmushi ta yi ta soke kai, karaf Yusrah ta ce' "Mum ta bari gobe zan zo in had'a mata". "To anji sarkin iya yi", cewar Mum. Da hakan direba ya kai ta gida inda ta so Salmat ta shigo ta nuna mata ce wa dare ya yi, kuma ta san unguwar ta su sai a slow, amma za tazo ranar Alhamis ita da k'awayen su na makaranta. Warmers d'in da Mum ta ba ta ta d'auka ta shiga gida had'e da sauran kayan ta ita ko Salmat direba ya wuce da ita gida. ****** Bayan Zajlah ta shiga gidan ne ta ajiye kayan abinci a falon, bedroom d'inta ta wuce, saboda tsabar gajiya tu6ewa tayi ta fad'a toilet ta yi wanka. Kayan ta na lefe ta bud'e wanda bata ma san ya suke ba, akwatin k'ana nan kaya ta bud'e ta samu wata night gown mai d'an girma ta saka, hijab k'arami ta d'ora sannan ta fice zuwa falon, plate ta d'auko kitchen ta d'ibi abincin ta koma d'akin ta. Bayan ta gama ne ta je kitchen ta wanke abinda tayi amfani dasu sannan ta koma d'akin ta, alwala ta yo ta shimfid'a carpet ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi lazimi sannan ta kwanta. Tabbas ta dad'e tana tsara ma kanta irin rayuwar da za tayi ta farin ciki a gidan auren ta, da kuma kyautata wa duk wanda ta aura saboda samun lada a k'ark'ashin shi, sai dai kash tana ganin da wuya hakan ta kasance a yanda take ganin wannan auren. Gashi a tsarin ta tana son namiji mai tsayi kuma gashi ta samu sai dai a banza don bata gaban shi "ya Allah kakka d'ora min son wannan bawan Allah a zuciya ta". ***** 6angaren Alamein kuwa har akaci aka sud'e bai lek'a gidan su ba saboda dama ba mutum ne maison shiga gurin harakar mata ba. Yana shigowa gidan ya ci abinci daya gani a dinning table sannan ya shiga part d'in shi, wanka ya yi ya nemi guri ya kwanta da tunane-tunane fal a ranshi har bacci ya yi awon gaba dashi.

*WASHE GARI*
Bayan ta gabatar da sallah ne da abubuwan da suka dace tayi wanka ta shirya cikin atamfar ta kalar lemon green fitted. Bakin gado ta zauna ta zabga uban tagumi komi ya cunkushe mata, sai tunani take yi dama haka rayuwar auren take ko kuma nata ne yazo a hakan? Duk iya nazarin ta ta rasa gane wane matsayi take dashi a gurin Angon. Jin hayaniyar mutane a falon ne ya sa ta janyo gyalen ta ta yafa ta fita, saboda tana tunanin Yusrah ce kamar yanda ta yi alkawari za tazo jiya. Tana fita karaf idon ta cikin nashi yana dariya k'annen shi sun saka shi tsakiya. Gabanta ne ya yi mugun fad'uwa saboda annurin fuskar shi daya kau cikin second uku. "Laah Brother kace Amarya bata ta shi ba, ga shi har ta tsantsara kwalliya", da saurin Yusrah ta taro ta had'e da zaunar da ita, d'an zamewa ta yi k'asa ta gayar dashi, ya amsa ba yabo ba fallasa saboda k'in amsawar zai sa Yusrah ta dame shi. Breakfast ta had'a mata da kanta tana tarairayar ta sa6anin Saudat dake binta da mugun kallo. Zumbur ya mik'e ya wuce part d'in shi saboda bazai iya kallon kayan haushi ba. Bayan ta gama karyawa ne suka shiga hirar duniya ita da Yusrah har tana tambayar ta matsayin karatun ta. "Gaskiya iya primary school kawai nayi saboda na fi son islamiya akan bokon". "No wonder! Biri ya yi kama da mutum", cewar Saudat. Harara Yusrah ta dinga zabga mata had'e da yi mata alamar gamon ki da Mum, sanin za su iya komawa ta gayawa Mum ya sa ta yi shiru, wayar ta ta fitar tana latse-latse. Hakan ya tuna ma Yusrah maganar had'a ma Zajlah wayar ta, nan ta gaya mata taje ta d'auko wayar ta kawo mata. "Ina fatar kin saka charge". "Eh na saka tun jiya", ta ba ta amsa. Wayar ce ta had'a mata har da layi biyu cikin kwalin wayar da credit, Mtn da Etisalat.
.
Ba number kowa a wayar hakan ya sa Yusrah ta saka mata ta ta number data Mum, ko kad'an batayi gigin saka mata ta Saudat ba sai kuma number Alamein da ta yi mata saving da (HUBBY), lambar ta shiga kira sau biyu tana tsinkewa sai ana ukun kamar bazai d'aga sai kuma ya d'aga. "Brother number Madam kenan". Bata jira me zai ce ba ta tsinke wayar, wayar ya bi da kallo had'e da furta "lallai yarinyar nan ta samu sake, don ma ta samu shekaranjia Mum ta ce nakar6i lambar ta mu rik'a zumunci shi ne za ta wani zak'ewa da baiwa wata lamba ta", za mu had'u ne". Bayan ta nu na mata duk abinda ya kama ta tasani take gaya mata su shiga kitchen suyi girki tunda an kawo komai na amfani a store.
.
Suna cikin girkin ne Alamein ya fito daga part d'in shi ya yi waje sai ga shi ya dawo falon had'e da Imran da Salis, sai wani dake aiki company dayace zai zo taya shi murna. Falon suka zube dukan su inda Saudat ta gayar dasu ta cigaba da latsar wayar ta. A tare suka fito daga kitchen d'in ita da Yusrah, gyalen ta ta k'ara janyowa ta rufe jikin ta saboda wannan shi ne karo na farko da Maza za su ganta ba hijab a jikin ta, har k'asa ta durk'usa ta gaida su had'e da yi masu sannu da zuwa, nan suka amsa cikin sakin fuska da walwala. Part d'in shi Yusrah ta wuce ta kawo masu ruwa da lemu, itako Zajlah ta koma kitchen domin k'arashe aikin. "Tabbb da sallamo wata k'anshin girki yadoki hanci na sannan a kawo min ruwa da lemu, kawai abari in na yi lunch na danne da ruwan", Salis kenan sarkin barkwanci. Hakan suka kwashi dariya duka falon sa6anin Alamein dake wani cin magani. Abincin suka jera ma su Imran a falon bayan sun gama, suka wuce da na su part d'in Zajlah saboda ta gayawa Yusrah ba za ta iya cin abinci gaban Mazan ba saboda bata saba ba. Ba k'aramin dad'i Alamein ya ji ba da suka wuce part d'in ta, saboda a tunanin shi in har zai cigaba da ganin ta falon zuciyar shi za ta iya tashi ya kasa cin abincin, don ko yanzu zai ci ne saboda tabbacin ba ita tayi girkin ba Yusrah ce. Bayan sun gama cin abinci ne har da santin su suka tashi za su wuce, su Zajlah ne suka fito domin suyi sai an jima nan sukayi godiya suka ba ta kud'i wanda ta kasa kar6a saida Yusrah ta kar6a suka yi masu fatan alkhairi da d'orewar zaman lafiya. Saudat ce ta ce su sauke ta gida ita ta gaji da zaman gidan, shi ma Alamein makulin mota ya d'auko domin suje tare tunda sun ce za su biya su gaida Dad. "Ai kai mun yanke ma fita har company sai nan da wata d'aya", inji Imran. "Saboda ga mai laifi an yanke mai hukuncin gidan yari ba", cewar Alamein. Dariya sukayi sosai sannan suka fice daga gidan har Saudat d'in, akabar Yusrah da tace sai marece za ta koma, wanda hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Zajlah ba.
,
Hira suka shiga yi sosai ita da Yusrah, saboda gaskiya yarinyar ta yi mata ba tada girman kai irin na masu kud'i, kuma ga alama za ta girme ta kad'an. Tunani take tayi a ranta kan ta tambayi Yusrah asalin ya auren su yake ko kuma ta k'yale ta, saboda gaskiya har ga Allah abin na damun ta sosai. Bayan sun yi sallar La'asar ne suka shiga kitchen domin girkin dare, duk da tana tunanin mawuyacin abu ne yaci abincin ta don tana tunanin k'ila ko d'azun bai ci ba. "Me ya kama ta mu girka abincin dare?". Maganar ce ta dawo da ita daga hayyacin ta, ta kai duban ta zuwa gare ta ta sauke ajiyar zuciya. "Me kike ganin yayan ku ya fi ra'ayi da dare d'in?, duk da ban tunanin in ya shigo zai ci abincin". "Ko da wasa kar kiyi tunanin tunda ba shi yagan ki yace yana So ba za ki rage shi da wani abu na kyautata wa, a tunani na ta hakan ne za ki janyo hankalin shi zuwa gare ki". "Nasan ce wa watarana Brother zai yi alfahari da auren ki *ADALILIN GATAN* da Mum tayi mai. Saboda har kullum in dai namiji zai jure ya auri Mace ma'abuciyar ilmin addini to tabbas babu shi babu dana sani, yanda tarbiyar yara ke ta6ar6arewa yanzu ka samu mai d'ora yaran ka akan hanya ma abin alfahari ne". "Amma yanzu abinda mutane basu gane wa musamman Maza har kullum burin su shi ne su auri Mace wayayya kuma y'ar boko, basu san ce wa da wayewar waje k'ara ta gida ba".
.
"Nasan matsalar Brother mai sauk'i ce, saboda shi kwata-kwata matan ne basu burge shi, asali ma ko taro ake yi muddin akwai Mata gurin bazai halarci taron ba, ni kai na da nake k'anwar shi ta jini sai shekaranjia ne Mum ta matsa mai ya kar6i lamba ta, kin ga ko irin shi bazai yi wuyar shawo kai ba tun da idon shi basu bud'e da soyayyar kowace Mace ba". "Saboda haka ki dage ki janyo hankalin mijin ki, in zama ya yi dad'i za ku dace sosai da Brother, kar ki biyewa zugar k'awaye". Hakan dai ta yi ta tsara mata irin abubuwan da ya dace tayi da way'anda basu dace ba har suka k'are girkin. Zajlah ta kai duban ta zuwa ga Yusrah had'e da furta. "Ni yanzu abu d'aya nake so ki samo min customers na d'inki tunda kin ga ba karatu nake yi ba sai dai zaman gida". "Ba yanzu ba kam sai an gama kula da yaya na sannan, kuma ai ni ban tabbatar kin iya d'inki ba, kar in kwaso atamfofin k'awaye na ki yanka ba dai-dai ba Brother ko ya biya su", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. "Ke dai ki samo za kiyi mamaki". Da hakan suka kammala ayukkan had'e da kimtsa gida sannan Yusrah ta yi haramar wuce wa, leda ta cika mata da kayan sha fa cikin na lefen ta, kuma ta had'a mata da dubu biyu cikin kud'in da su Salis suka ba ta, dak'yar ta karb'i kayan tayi mata godiya. *** *** *** *** Alamein na shigowa gidan ko takan abincin bai bi ya wuce part d'in shi, duk da kamin ya fito daga gidan Mum ta yi mai nasiha dai-dai gwargwado kan kula da hakk'in yarinyar mutane wanda ya nuna mata zai yi insha Allah. Sa6anin yanzu yana doso gidan ya ji gaba d'aya ranshi duk ya 6aci shiyasa ya k'i kula abincin ya wuce kawai. Kuma dama bai saba da cin abincin kowa ba sai na Mum, don ko yanzu sai da ya sa Saudat ta d'ebo mai abinci ya ci sannan ya fito. *** *** *** Tana jin shigowar shi tana part d'in ta wata zuciya ke ce mata ta fita tayi mai barka da dawo wa, wata na ce mata kar kije ya maki wulak'anci. Gaskiya ba k'aramin fad'uwa gaban ta ke yi ba akan irin muguwar hararar da yake zabga mata. Da hakan ta yanke shawarar zaman ta d'akin ta, wanka ta yo had'e da alwala ta gabatar da shafa'i da wutri ta yi addu'o'in ta sannan ta kwanta duk da irin tsoron da take ji. Tunani kawai take yi anya za ta iya biyar shawarar Yusrah kuwa?, saboda a tunanin ta ko kyautata wa mutum na tafiya ne da samun fuska, kawai dai ta yanke ma kanta in har ta ga fuska za taci gaba da kyauta ta mai, da hakan 6arawo bacci ya yi awon gaba da ita.
.
Yau ta kama Alhamis dai-dai da kwanan ta biyar kenan a gidan Alamein, wanda sai ta wuni ta kwana basu had'u dashi ba, kuma har ko yaushe ta yi girki za ta ajiye mai sai dai yanda ta ajiye hakan za ta zo ta d'auke shi sai dai ta bayar sadaka wa almajirai. Tun safe take hada-hadar tarbon k'awayen ta da suka yi mata alk'awarin kawo mata ziyara yau d'in. Tana gama ayyukkan ne ta yi wanka ta shirya cikin wata shadda brown fitted gown, ko minti biyar bata yi da shirin ba sai ga su sun zo su hud'u Salmat ce cikon ta biyar d'in su. Hakan suka baje sai hirar makarantar suke ta zubawa, wanda a ciki ne suke gaya mata Ummulkhairi ce matar Ustaz Yusuf ya yin da Safiya ake maganar ta da Ustaz Lukman. Da la'asar ne suka ta shi wuce wa ta rik'e Salmat kan ce wa sai zuwa marece za ta wuce, da hakan suka fice suka bar ta. Hira suka dasa tsakanin su inda Zajlah ta kwashe yanda maganar auren ta ta kasance ta gaya wa Salmat, hak'urin nan dai da Yusrah ta ba ta shi Salmat ta ba ta had'e da nuna mata muhimmancin biyayya. "Ni yanzu ba ma wannan ke damu na ba irin yanda zan yi in tafiyar Baba saudiya ta yi, saboda ko ganin shi ban yi barranta na in gaya mai zan je gida". "Hakan za ki jure gaskiya, kuma ki rik'a kula da gyara mai part d'in shi in har ya fita tun da ya zama dodon ki, Allah ni wannan in ni ce cikin wata d'aya zan gama dashi". Murmushi kawai Zajlah ta yi, da hakan suka yi girkin dare suka k'are. Ba yanda bata yi ba kan Salmat ta tsaya har a gama magrib sannan ta wuce tak'i, "in ma na tsaya wa kika ajiye da zai kai ni in nayi dare? Ga wannan unguwar ta ku kuwar ka banza, ko misk'ilin mijin ki za ki sa ya mayar dani?". "Ina nagan shi ni kaina barranta na insa ya mayar dake, ke dai ayi ta sha'ani". Suna cikin hakan ne sai ga Alamein ya shigo gidan, saboda falo suke tsaye suna maganar za ta wuce.
.
Ba k'aramin mamaki ya yi ba yanda ya jiyo maganar mutane a falon, saboda yau kwanan shi biyu ko motsin ta bai jiba, abincin da yake gani saman dinning ne ke ba shi tabbacin tana gidan, ba don hakan ba da yace ba mutum a gidan. Ba don suna gab da k'ofa ba da ko sallamar shi ba za su ji ba, saboda iya la66an shi sallamar ta tsaya, gaida shi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa, Direct hanyar part d'in shi yayi, "am ji mana Malam". Muryar ta daki kunnen shi cak ya tsaya ya juyo yana yi mata kallon raini had'e da 6acin rai tattare a fuskar shi na jin haushin Malam data kira shi. "Baban mu zai wuce saudiya zuwa jibi in kai bai da darajar da ko gaisuwar surukai kaje yi mai to y'ar shi na da buk'atar zuwa ta gana da mahaifin ta", cikin isa da gadara Salmat ke gaya mai maganar, don ita ba ta hak'urin wulak'anci. Ba k'aramin k'ok'arin ta Alamein ya gani ba na tsaya ta gaya mai magana a gadaran ce, saboda ita ce Mace ta farko da hakan ta ta6a had'a su har ta dubi k'wayar idon sa ta so ka mai magana. "Kin san ce maki aka yi da aka ta shi d'aura auren a k'afa ta aka d'aure igiyoyin uku akace duk inda zan fita tana manne dani da za ki ce min za taje gida, in ta iya ta biki kuje tare kar ta dawo gidan ba damuwar Alamein bace". "Wannan sunan ga alama kuskure akayi gurin rad'a ma shi, ina ga wanda aka k'udurta daban wannan ya fito a fatar baki daban, saboda kwata-kwata sunan bai dace da mutane irin ku ba". "Amma ina mai baka shawara daka canja takon zamantakewar aure saboda in kai ba'a ta6a ganin ka aka furta ana son ka ba, to Zajlah har masoya sai da ta ture, ba'a kawo ma ita saboda rashin mashin-shi ni ba, darajar iyaye ka ci". Ba ki sake ta barshi ta fizgi hannun Zajlah wacce ta zamo mutum mutumi tana kallon Salmat ta kasa ta6uka komai, falon suka bari don ta taka mata. Sai da suka kai gate sannan ta ja ta tsaya, "yanzu ke har wannan namiji ne za ki tsaya shakkar tunkara don kina son fita?, Allah in ni ce wannan sai dai mu gasa juna wanda ya gasu shi zai yi bayani, kin ji ance in masara ta ji wuta ita ke fad'i". "Allah ran da duk kika jibgu hannun mutane ba ruwa na, kinga haka ranar kika so kawa k'anwar shi magana". "Tabbb su jibga manya, ke ni fa zan iya d'aukar rainin hankali daga talaka d'an uwa na ban d'auka ga mai kud'i ba wallahi, saboda abin sai yayi yawa in kayi sake, don mutum bai ga uba na yawon maula gurin shi ba barranta na ya wulak'anta ni". "Kuma yanzu kin ji da kunnen ki abinda ya furta, saura kar ki shirya kije ma Baba ban kwana, ni wallahi da ni ce to ya bud'e shafin yawo sai inda mai ya k'are". Sosai Zajlah ke mamakin rayuwar Salmat don kwata-kwata bata yo halayyar Mama Inno ba, don tun suna yara ba ta d'aukar raini. Hakan ta sa kai ta fice daga gidan had'e da jadda da mata ce wa sai sun gan ta kamin wu cewar Baba. **** **** ***** Fadeel ya shiga damuwa sosai saboda tabbatar da ya rasa yarinyar har abada, domin akan idon shi aka d'aura auren ta da wani, ya san ba k'aramar asara yayi ba saboda samun nutsuwa irin ta ta ga y'an matan yanzu abu ne mai wuya, da hakan ya hak'ura sai dai har kullum yana fatar samun Mace natsattsiya tamkar ta, Fadeel kenan da Zajlah ta yiwa nasiha da zai mari Mum. Ustaz Lukman ma hakan ya yakice Zajlah daga zuciyar shi har ya furta wa Safiya k'awar Zajlah yana son ta saboda gudun yakuma nauyin baki.
.
Yau dai abinda ta k'udurta data gama girkin breakfast gidan Mum za ta je tayi mata wuni, hakan ya sa ta gama girkin ta cikin lokaci ko ta kan Alamein bata bi ba ta fice saboda sanin cewa yana company. Da shigar ta gidan Mum ke ta tarairayar ta, bata san ina za ta d'ora taba kan murna ita dai yarinyar ta yi mata har ga Allah don tana ganin mutuncin ta sosai. Ganin cewa Mum ta shiga kitchen ne ya sa ta bi ta domin taya ta girki, "ai da kin koma falo kawai, saboda ba girki ne zan yi ba Daddyn ku ne kawai zan yiwa ferfesun kifi".
.
"Ba komai Mum kawo in d'ora". Hakan ta ba ta girkin saboda matsa mata da tayi kan ta ba ta, suna hira da mai aikin Mum ita ko tana aikin har ta kammala. "Ni fa har yawu na sun tsinke da wannan girkin naki, duk gida ya d'auki k'amshi haka", cewar Mama Talatu. "Kai Mama ai ban ma iya girki sosai ba saboda ko da na tashi gidan mu ban san mahaifiya ta ba sai mahaifi na, Mama Inno kuma bata cika ba mu girki sosai ba duk da mu ma ba zama muke yi sosai ba kullum muna islamiya". "Duk da hakan na san zai yi dad'i gaskiya, don kin fi waccan sangartacciya da ko ruwan Lipton bata iya dafa wa ba sai d'an banzar girman kai da raina mutane". A rayuwar ta ta k'i jinin cin naman musulmi d'an uwan ta, saboda sanin illar hakan, duk laifin ka gare ta ba za ta iya zaman zagin ka a bayan idon ka ba. "Allah ya kyauta Mama, a yita hak'uri. Wai ma ina Saudat d'in tun shigowa ta banji motsin ta ba?". "Yanzu za ki gan ta tun da azahar ta yi, dama tana zuwa health makaranta, auren nan ne ya sa ta kwana biyu bata je ba". Da hakan har ta kammala girkin ta fito falo, har k'asa ta durk'usa ta yiwa Mum sannu da hutawa, hannun ta ta rik'o ta zaunar da ita gab da ita. "Haba Zajlah har yaushe wai za ki daina jin nauyi na? Na gaya maki ki saki jikin ki tamkar kina gaban Mama Inno, ko Mama Asabe zance ne?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. Da hakan dai ta samu tana jan ta da hira har ta d'an saki jikin ta, nan Zajlah ke gaya mata tana so gobe taje gida yiwa Baban ta bankwana zai wuce saudiya jibi. "Ba matsala Zajlah zan shirya gobe muje tare in ya so in baro ki can ki wuni ko, ina fatar kin gaya wa Son batun tafiyar Baban na ki?". Tunawa da cewa jiya Salmat ta furta mai maganar ya sa tace' "eh Mum yasan da maganar". Tana shigowa falon ta yi turus ta tsaya tana wani shan k'amshi, da murnar ta ta taryo ta duk da tsorace take saboda gudun hantara, hannu ta mik'a ta kar6i litattafan da ta rungume had'e da furta "sannu da zuwa, ya makarantar?". Yauwa ta furta a tak'aice, duk da taso yi mata wulak'anci ganin Mum ya sa ta yi shiru, don ta san ko ta sha giyar wake ba za ta fara ba. Littafan ta kar6a ta wuce d'akin ta, (ni dai Jegal da ido na bi ta saboda mamakin ko mahaifiyar ta bata gaida ba). "Wai Zajlah ki na da ra'ayin makarantar boko ne ko ya ya?", "a ah Mum an ce boko da wuya kuma ni iya primary kawai na tsaya, sai dai ba laifi ina gane k'ananun abubuwa".
.
"Kuma Mum ni yanzu d'inki kawai na sa gaba, in dai ina sa mu ba laifi nasan zan rage kewar wasu abubuwan". "Au kice da mad'inkiya nake zaune, da fatar kin iya kar ki 6ata kayan mutane a tarar da Mum ranko", tana dariya take wannan maganar. Yanzu ta fahimci Mum na da dad'in zama ga kuma raha da take da, tabbas albasa bata yi halin ruwa ba. "Mum hala Dad bai shigo ba?, yau yunwa nake ji sosai wallahi, ko break ban yi ba a skul". "Kira shi kiji in ba yanzu zai shigo ba sai kici na ki, kin san yau ko yayan ki nan zai ci abinci tunda ga matar shi nan gidan". Jin cewa Brother zai zo gidan ya sa ta hak'ura har sai da suka dawo. A tare suka shigo gidan wanda ya sa ya yi turus ya bi ta da kallon mamaki, sai kuma ya basar ya k'araso cikin falon, don dama ko ta kan gidan shi bai bi ba ya yo gidan saboda ya samu abinda ya ci. Durk'usawa ta yi ta gaida Dad sannan ta yiwa Alamein sannu da zuwa, Dad ya kar6a ba yabo ba fallasa sa6anin Alamein dake yak'e wanda ya fi kuka ciwo. Falon Dad suka wuce saboda nan ne gurin cin abincin su, sa6anin Mum data tsaya suje tare da Zajlah aci abincin, inda ta nuna ma Mum ak'oshe take duk da yunwar da take ji tasan da nauyi taje cin abinci da surikin ta, duk da ta hango su a gurin su ba komai bane, kuma ita ma da tana gida tare da Baban ta take cin abinci. Tsinkayo muryar Mum tayi tana ba Talatu umurnin ta had'a abinci ta kai mata falon ta. Hannun ta ta rik'a ta kaita falon ta, sai da Talatu ta kawo komai sannan ta ba ta umurnin taci abinci kamin ta dawo, da hakan ta fice zuwa falon Dad.

0 comments:
Post a Comment