A DALILIN GATA Part 6-10
.
"To wai Dad wa ye ya isa har ya d'aga hannu ya kai wa Mum mari kuma ya zauna lafiya a garin nan?". "Son ni ma wannan shi ne abinda nake tambaya, amma nasan ba wanda zai bamu wannan amsar sai ita kanta, kuma nasan mu shekara muna tambaya ba za ta gaya mana ba".
,
"Dad mushiga daga ciki muji ko za ta gaya mana d'an gidan uban waye shi". Ce war Saudat. Hakan suka d'unguma sai bedroom d'in Dad domin sa mun amsar tambayoyin su. "Mum Alamein ta shi kigaya min wane isasshe ne zai d'aga hannu duk garin nan yadakar min Mata?". Wani guntun murmushi ne ta saki a fuskar ta had'e da girgiza kai alamar ina tausayin tsarin ku. "Wannan shi zai tabbatar muku ce wa duk abinda kayi na alkhairi ko na sharri za ka had'u da makaman cin shi ko mai dad'ewa". "Kuma kai da kake ta da jiyojin wuya me za kayi akai ko da na gayama wa ya mare ni? Ko ka manta shi wanda ka mara yana da y'ay'a kuma sun san darajar shi". "Me kake tunani a wancan lokacin in har ace ko da ka mare shi wani d'an shi na gurin? Ko kana tunanin dukiyar ka za tasa in har suna gurin su k'yale ka?". "Mum ni fa mutumen laifi ya yimin, har ta ya ya zai zo yana tafiyar ganin dama a saman titi". "Haka zalika nima laifi nayi yaron ya mare ni". Cikin damuwa Dad ya bi ta da kallon mamaki, ya rasa ga ne ita wace irin Mace ce da batasan y'ancin kanta ba. Durk'usawa ya yi gabanta ya d'ora hannuwan shi saman k'afafun ta tamkar yayi kuka yake ji ya furta. "Don Allah Mum ki gayamin ya akayi hakan ta faru? Kuma in kin san waye ki gayamin shi please and please Mum?". Murmushi ta yi sosai har hak'oran ta suka bayyana, sannan ta kwashe ko mai ta gaya masu had'e da yaba halayyar yarinyar. Sai lokacin suka saki fuskokin su har Al'amein na furta "wallahi ya kuru da ya aikata wannan d'anyen aikin da ya had'u dani". "Inna san waye shi ko in ban sani ba? Ko kuma inna gaya maku waye shi za ku d'auki mataki?". Da hakan dai ta k'ara janyo hankalin su had'e da k'ara lurar dasu kan muhimmancin girmama na gaba dasu, wanda Dad ke zaune yana sauraren su. ****** Duk abinda aka saka ma rana zai zo indai da rai da lafiya. Yau ne ake shirin gabatar da musabak'a ta gari wadda za'a gabatar a makarantar su Zajlah saboda kasancewar makarantar ta su ce babba kuma itace kan gaba a duk sauran makarantin nen garin su. Daga kan y'an izifi biyu aka fara har zuwa kan izifi sittin wanda aka share sati d'aya ana gudanarwa tsakanin makarantu biyar dake garin. Inda aka k'are kuma makarantar su Zajlah ta zamo gwarzuwa a musabak'ar wanda har da Zajlah da Salmat acikin gwarzayen, saboda Zajlah ta yi haddar izifi talatin inda Salmat ta yi izifi ashirin. Bayan kwana ki bakwai ne aka gabatar da ta Jaha a garin Birnin kebbi, daga nan akayi ta k'asa gaba d'aya inda Zajlah ta zo ta d'aya a cikin y'an izifi talatin Salmat kuma ta biyu a cikin y'an izifi ashirin. Sun sa mu kyaututtuka da dama wanda ya had'a da kud'i da keken d'unki Zajlah harda kujerar Makkah wanda sanadiyyar hakan har da guntun hawayen ta na farin ciki. Ko Malaman su kaduba lokacin za kaga farin ciki kwance fal a fuskokin su musamman Ustaz Lukman dake kula da 6angaren masu haddar da kuma wani abu da yake ji kwance k'asan zuciyar shi akan Zajlah. Mahaifin ta farin ciki fal a ran shi harda hawayen shi, ji yake yi ina ma ace yana gani da idon shi yaga wannan rana ta farin ciki da y'ar shi ta zamo gwarzuwar shekara. Hakan suka tarkata suka dawo gida farin ciki fal ransu, sai mak'ota ke ta shigo masu murna da Allah sanya alkhairi. Sun samu kud'i sosai musamman Zajlah da tazo ta d'aya, har gida Ustaz Lukman ya biyo su had'e da kyaututtukan da suka sa mu mota ta kawo masu har k'ofar gida. "Za ku sa mu shigowa makaranta ranar assabar?", ce war Ustaz Lukman. "Ustaz a bamu sati d'aya mana mud'an huta sannan mu shigo". "Sati d'aya ya yi yawa gaskiya saboda bazan jure...... Sai kuma ya canja akalar maganar. "Shikenan Zajlah ku shigo zuwa ranar Larba, tunda kunga yau ta kama Assabar". "To Ustaz mun gode sosai". Da hakan suka shige gidan su Salmat d'in.
.
Kamin su shiga gidan ne Salmat ta kai duban ta zuwa ga Zajlah had'e da furta. "Yau kin yarda da abinda nake cewa Ustaz Lukman son ki yake yi?". "Ke dai ina ga aure kike so shiyasa kullum maganar ki ba ta wuce ta So ba". "Kina ji fa yau har da furta cewa bazai juri rashin ganin ki ba, sai ya juya maganar saboda kar mu gane inda ya dosa". Dundu ta sakar mata had'e da janyo gashin kanta sai da ta yi k'ara, da hakan suka shiga gidan. Mama Inno ce ta tarye su dukan su ta rungume sai albarka take saka masu har da guntun hawayen ta. "Zajlah yau burin ki zai cika da yardar ubangiji saboda ya yi maki hanyar samun kud'in da za ki kula da matsalar idon mahaifin ki". "Wallahi Mama ina jin tsabar kud'in da nasamu tun a can matsalar Baba ce nafara kawo wa, sai kuma samun abin Sana'a da zai raba mu da yawon bara". "Don ko babu kud'in zan soke matsalar bara tunda na samu keken d'unki zan tashi da koyo har in iya". "Gaskiya kam kinyi tunani mai zurfi, yanzu sai abubuwa sunyi sauk'i ku had'u ke da Salmat kuje koyon d'inki". Da hakan aka shigo da kayan da suka samu gidan su Salmat, inda kowannen su ke da keken d'inkin sai Salmat dake da kud'i dubu d'ari biyu Zajlah ko na da dubu d'ari biyar da kujerar Makkah da shugaban k'asa ya baiwa duk wanda ya yi na d'aya a matakin haddar su tun daga izifi biyu har zuwa izifi sittin. **** Tun lokacin da yarinyar ta hana ma saurayin marin ta take kwana kuma ta tashi da ita aranta, saboda yarinyar ta burge ta sosai, sai tunani take yi ina ma ace y'ar tace ke da halayyar wannan yarinyar. Hakan take gurin Fadeel wanda duk yanda ya so yafige yarinyar a cikin zuciyar shi abin ya faskara. Duk inda zuciyoyin mutum biyu suke da tunanin ta suke kwana kuma suke tashi, duk inda suke farautar ta domin su ganta abu ya faskara. ******* Falon ta shigo ta d'auki remote domin canja tashar, abinda ta ga an nuno ya hana mata canjawa sai gata zaune jagwaf saman kujera. "Saudat! Saudat!! Saudat!!!". Gigice ta fito daga d'akin ta ta fad'o falon saboda kiran da Mum ke ta k'wala mata. Plasma d'in ta bi da kallo saboda itace Mum ke nunawa da yatsan ta, ita dai bata ga komai ba bayan yarinya tana rero karatun Qur'an cikin baiwa kowane harafi hakk'in sa had'e da tajweed. "Mum me ke faruwa halan? Ban fahimci me kike nuna min ba fa".
,
Nan Mum ta yi mata bayanin yarinyar. Hakan itama Saudat ta ji yarinyar ta burge ta sosai. "Ina so kishirya zuwa anjima ki rakani makarantar su yarinyar nan, dama na yita neman ta duk inda nake sa ran ganin ta bangan taba". "Yanzu Mum me za kije kiyi mata? Sai kita neman yarinya tamkar wacce ta k'ulla maki wani abin arzik'i". Mugun kallon da Mum ta bita dashi ne ya sa taja bakinta ta tsuke. *05:00pm* Dai-dai wannan lokacin Mum ta faka motar ta k'ofar makarantar, da Ustaz Yusuf ta fara cin karo k'ofar makarantar. Nan ta yimai bayanin abinda ke tafe da ita, mashin d'inshi yahau yayi mata jagora har k'ofar gidan su Salmat, godiya ta yita yimai har da fitarda kud'i taba shi saidai bai kar6a ba yajuya yakoma. Mota ta hakimce tana wani yatsinar fuska saboda k'ofar gidan da taga sun tsaya wai nan Mum tazo kuma gurin k'aramar yarinya. "Fito mushiga ciki mana". "Shiga ki fito Mum zan jira ki a mota". Fad'a ta dinga yi mata sannan ta fito har da wani handkerchief tana toshe hanci. Gidan suka shiga inda Mama Inno ta yi masu tarbar da ta dace duk da batasan su waye ba. Bayan sun gaisa Mum ke yi mata bayanin gurin Zajlah tazo. Nan Mama ta kira su daga d'aki suka fito. Durk'usawa sukayi har k'asa suka gayar da Mum, bayan ta amsa ne take ta yabon musabak'ar su data gani ana ta haskowa a cikin kowace tasha. Nan ta d'ora da gaya mata itace ta hana wani saurayi ya mara. Har ga Allah ta manta da abinda ya faru sai yanzu data tuna mata. "Laaah Haj wallahi ba komai, ai yiwa kaine don ni ma zanso a daraja nawa iyayen". Da hakan Mum ta basu dubu goma-goma suna ta godiya, itako ta fice daga gidan.
,
Da sannu Fadeel ya binciko gidan su Zajlah wanda karo uku kenan yana zuwa k'ofar gidan su amma sai jikin shi yayi sanyi yaka sa tunkarar ta yakoma. Yau dai da k'arfin gwiywar shi ya tashi na tunkarar ta yaga ya mata gaskiyar lamari ce wa yana son ta. K'ofar gidan ya zo, amma a tunanin shi na zai iya tunkarar ta yau sai gashi abin ya gagara, ta gaban shi suka zo suka wuce ita da Salmat domin zuwa koyon d'inkin su gidan wata mata dake k'arshen layin su. "Ni fa Zajlah abin nan ya fara d'aure min kai, in har kin lura kusan kwana uku kenan duk muka wuce zanga wannan motar". "Kuma fa abin mamaki ba a ganin na cikin motar su waye saboda duhun glass d'in motar". "Ke kika damu da wannan motar, ni fa zan iya ce maki ban ma ta6a lura da motar ba sai yau dakika yi maganar". "Ai ke dama ba komai kike lura dashi ba, inaganin wataran sai halaka ta hau kan ki bakisan za ta zo ba". "Au dama in abu zai same ka zaka san da zuwan shine?". "Ba hakan nake nufi ba, amma dai ana so ka lura da yanda abubuwa ke tafiya saboda tsaro". Dariya sosai Zajlah ta yi, da hakan suka isa gidan da suke koyon d'inki. ****** Yau ne aka aje kan za'a yiwa Baban Zajlah aiki a idon shi, Malam Inuwa, Zajlah da Salmat ne suka yi mai rakiya zuwa Birnin kebbi. Asibitin Sir Yahaya ce aka yi mai aiki kuma aka gama cikin nasara wanda sai da suka had'a shi da medical glass saboda rashin ganin abinda ke nesa dashi. Je kaga murna fal a gurin Mal Abubakar inda yake alfahari da y'ar shi k'waya d'aya tak da Allah ya bashi, wacce ta zame mai y'a d'aya tamkar da dubu.

*****
*Wacece Zajlah?* Mal Abubukar d'an asalin k'auyen giwa tazo ne shi da matar shi Basira, auren zumunci ne aka yi masu domin mahaifiyar ta da mahaifin shi ne uwa d'aya uba d'aya. Sun ta so tare da Mal inuwa ne tun shigowar shi garin Jega sanadiyyar Sana'ar kayan gwari wanda daga baya har ya samu matsakaicin gida ya saye a kusa dashi ya dawo nan da zama. Allah ya had'a kan matan su wanda inka gansu zaka rantse da Allah y'an uwan juna ne. Basira ta rasu ne tun ranar da ta haifi Zajlah wanda bata ko saka yarinyar a idon ta ba. Lokacin ita kuma Mama Inno ta haifi Salmat da sati biyu, nan ta kar6i Zajlah ta had'a da Salmat tana shayar dasu. (Asalin sunan Zajlatu ne k'awaye ne suka tak'aita shi da Zajlah, abinda sunan ke nufi rayuwa kyakkyawa kuma mai sunan tana daga cikin tabi'ai, me neman k'arin bayani akan asalin sunan da tarihin mai sunan zai iya searching da *KISASUT TABI'AT*, amma da larabci). Sun shiga tashin hankali sosai musamman Mama Inno da Mal Abubakar, dole suka dangana saboda wanda yafi su son ta ya kar6i abarsa. Zajlah na da shekara takwas a duniya Baban ta ya makance sanadiyyar ya jima yana gani bishi-bishi sai bai d'aukin abin wata matsala ba har abin ya ta6a idon duka ya daina gani, tun yana iya lalurar kan shi har abin ya gagare shi. Lokacin ne sauran tsirarrin dangin shi suka guje shi sanadiyyar ganin ya zama wata lalura a gare su, wanda shi ba hakan yazauna dasu ba don mutum ne mai taimakon dangin shi duk da shi ma ba wani hali ne dashi ba. Sanadiyyar makarantar shi ne Zajlah ta dawo gurin shi da zama domin taimaka mai da wasu abubuwan da ba za'a rasa ba. Zajlah yarinya ce mai kimanin shekara goma sha shida zuwa sha bakwai, chocolate colour ce ba wata kyakkyawa ce ta azo a gani ba sai dai manyan idon ta da gashin girar ta shike fitar da kyawon ta, yarinya ce mai shape sai dai batada k'iba irin sosai d'in nan. Kamin abubuwa suyi tsanani ansaka su makarantar boko iya primary daga nan basu cigaba ba sai makarantar Arabic dasuka mayar da hankali akan ta. Saboda kowaccen su ta yi sauka uku sai kuma hadda da suke yi har Ustaz Lukman ya saka su acikin musabak'a, wanda sanadiyyar ne har duniya tasan da zaman su inda iyayen su ke alfahari dasu.
.
Mamaki fal a ran Saudat na miye silar zuwan Mum gidan su wannan kucakar yarinyar, ga shi tana so ta tambaye ta sai dai kuma bata ga fuskar tambayar ba. Bayan sun dawo ne direct bedroom d'in Dad ta wuce, zaune yake k'asa saman carpet ya jingina jikin shi da kujera yana karatun jarida. "Daddyn Alamein hutawa kawai ake yi"?. "Ba dole ba tunda yanzu kin rage So na da tattali na, ina ga aure zan zo in yi ko zan samu mai bani kulawa", yana maganar ne d'auke da murmushi a dattijuwar fuskar sa. Murmushi Mum ta yi sosai had'e da tattara hankalin ta guri d'aya ta k'ara matsawa gab dashi. "Shikenan fad'uwa tazo dai-dai da zama, ka ga inka nemo mata sai a had'a da naka auren dana son ad'aura rana guda". "Yaushe Son ya nemi mata banda labari? Yaron da ko mata bai cika kulawa ba ina yaga macen da yake so?". "Sanin hakan ne ya sa na nemo mai mata da kaina, yarinya y'ar asali y'ar gidan mutunci mai ilmi". Wata irin zabura ya yi ya kai duban shi zuwa gare ta.
.
"Kina nufin Son ne za ki yiwa auren dole? Ko ni da nake uban shi ba'a yimin auren dole ba barrantana shi da yake cikin k'urciyar shi", yana maganar ne cikin fad'a-fad'a. "Dad'i na dakai duk yanda ake magana cikin kwanciyar hankali indai aka ta6o yaran ka cikin second d'aya za ka birkice". "Duk duniya ba ni da farin cikin da ya wuce na yara na, babu takura ko matsi tsakanina dasu duk abinda suke so shi nake so saboda haka babu maganar ki za6ama son abokiyar rayuwa sai ranar da yaganta da kanshi yakawo ta". Suna cikin maganar ne sai ga Alamein da Saudat sun shigo d'akin, bayan sun gaida mahaifan sune suka nemi guri suka zauna. Sai da ta tattara hankalin ta a gare shi sannan ta fara magana cikin hikima da basira. "Alamein matsayi na na mahaifiyar ka data shayarda kai kuma ta raine ka da gudun 6acin ranka in na nemi wata alfarma gurin ka za ka iya yimin ita?". "Haba Mum miye duniya bazan iya yi maki ba? Duk duniya banda tamkar ku ke da Dad sai kuma Lil". "Da kyau Son! Mata na nema ma mai hankali da nutsuwa ga ilmi wanda nake fatar inka amince aure nan da wata d'aya indai har iyayen yarinyar basu yi mata miji ba". Yanda kasan ana kid'a ganguma haka zuciyar Alamein ke bugawa, cikin abinda bai wuce second biyar ba zufa ta wanke mai fuska duk da sanyin A.c da fanka da suka yalwata d'akin. "Aure kuma? Mace? Ni da kaina? Bazai yuyu ba, miye abin so ga Mace d'in? Me zan yi da ita? Tauyewar rayuwa kawai". "Anya zan iya bijirewa buk'atar Mum? Duk k'ask'anci na nasan darajar mahaifa na, in na yi mata hakan banyi biyayya ba", duk a cikin zuciyar shi yake wannan tunanin. Ka aure ta kawai in ya so daga baya ka mak'ala mata wani sharrin ka sake ta kawai. "Bazan so in zamo mai rayuwar auri saki ba shiyasa tun farko Mace ba ta gabana". Duk a zuciyar shi yake ta sak'a wad'annan maganganun da ya rasa samun mafita akai. "Mum ina fatar ba wannan maganar ce silar zuwan mu gidan su wannan kucakar yarinyar ba? Me Brother zai yi da wannan mitsitsiyar yarinya, kuma ma y'ar talakawa haba Mum". Maganar Saudat ta dawo dashi hayyacin shi daga tunanin da ya cunkushe mai zuciya. "Y'ar talakawa fa? Duk yanda naci buri akan auren Son da bak'i daga k'asashen waje a hakan zan tozarta?". "Alamein". Kai ya d'ago ya kai duban shi zuwa ga Mum had'e da saka handkerchief yana sharce zufan da ke karyo mai ga jiki ta ko ina. "Amsar ka nake jira in har ka amince shikenan, in ma baka amince ba ka gayamin bazan tilasta kaba, sai dai ina hango alkhairi tattare a zaman takewar ku". "Mum na amince". Da hakan ya mik'e ya fita daga d'akin zuciyar shi tamkar ta fashe. "Alhamdulillah! Allah na gode ma, yanzu sai ayi haramar zuwa neman aure". "Ke kuma fitsararriya da kike maganar y'ar talakawa ce na gaishe ki y'ar k'aruna, a hakan dai ta fiki mutunta mutane, ta shi ki 6ace min dagani". Cikin 6acin rai Saudat ta mik'e sai da ta kai k'ofar fita ta furta "Allah yasa anmata miji kuma har an saka rana", sannan ta fice da sauri. Murmushi Dad ya yi had'e da ce wa "wannan auren kan ki za ki d'aurawa shi saboda babu mai son shi". "Saboda son kai da rashin hango abinda nake hangawa ba, amma nan gaba za ku gane inda na dosa.
.
Cikin sauri suka gaggauta shiryawa suka hau hanyar makaranta. Suna fita suka ci karo da mutumen kamar kullum sai dai sa6anin kullum yau ya fito ya jingina da motar yana waya idon shi akan su tamkar maye. Hakan suka gilma ta gaban shi suka wuce, sallamar da ya yi ce yasa Salmat ta ja birki ta tsaya had'e da rik'e hannun Zajlah dake neman fincikewa. Amsa sallamar ta yi sannan ta nemi ci gaba da tafiya, ganin ce wa in ya k'yale damar shi ta k'arshe za ta wuce, nan ya furta. "Don Allah ki taimakamin da number k'awar ki ina so zanyi magana da ita, na yi tunanin bai dace in tsayar daku saman hanya ba shiyasa nake neman lambar muyi magana a tsanake". Tana ta yar da kanta karaf idon su suka had'e take hoton abinda ya faru ranar ya dawo mata tangaragan, da sauri ta kauda kanta had'e da furta. "Malam kayi hak'uri banda waya kuma an yimin miji, sai an jima". Hannun Salmat ta fincika da k'arfi suka fice wanda Salmat sai mamakin ta take yi fal a ranta. "Haba (ZAZ) wannan abin dame yayi kama?, ke ce fa a kullum ke yi muna nasiha kan ce wa wulak'anta d'an Adam bai da kyau amma ga shi yanzu kin yi da kan ki".
.
Nan Zajlah ta ba ta hak'uri had'e da ba ta labarin abinda ya faru, sannan ta d'ora da ce was' "a ganin ki wannan ko mijin aure na rasa ya dace da rayuwa ta?". "Duk da hakan ya kama ta ki yi masa uzuri don baki sani ba ko godiya zai yi maki, ko kuma yana tafe da wani abu mai muhimmanci". "Ko ma miye yanzu shi ta sha fa don ba ya gaba na". Da hakan suna tattauna wa har suka kai makaranta. **** "Daddyn Alamein banji kace komai ba har yanzu kan maganar yarinyar, wallahi ina hango alkhairi ne tattare cikin wannan auren in har ta yiyu". "Me kike so ince? Ai magana na hannun ki saboda yanzu ke ce mijin ni ne matar, tun da har kika iya k'udurta neman auren ba da yawu na ba". "Haba abin bai kai haka ba, yanzu ya kamata mukai k'arshen magana kan turawa gidan su yarinyar, in kuma har kana ganin abar maganar ne wallahi ba matsala sai abar ta". "Tu da kin yi magana da Son har ya amince ni me zance? Yanzu ki fara bincika wa kiji in har ba'a yiwa yarinyar miji ba sai kiyi k'ok'arin samun wa'anda za ki tura ayi maganar don bazan sa kai na ba cikin abinda yaro na bai so ba". "Shikenan ba matsala za'a yi yanda ya dace tunda Abban Yusrah na da rayuwar shi, kuma ko da ran ka shi ne waliyyin shi". Da hakan ta fice daga d'akin ta shirya sai gidan su Zajlah. Bayan sun gaisa da Mama Inno ne ta sako mata buk'atar da ke tafe da ita kan tambaya in ba'a tsaidawa Zajlah miji ba kan za su turo manya domin ne mawa yaron su ita. Nan Mama ke tabbatar mata ce wa Zajlah ba tada miji, har suka ajiye kan ce wa za'a turo manya, da hakan Mum ta fice daga gidan. **** Yana batun fice wa ne suci abinci Mama inno ta tsayar da shi take gaya mai abinda ke faruwa. "Kin ga abinda nake gudu, shiyasa nake matsawa Mal Abu kan ce wa yasamu mata yayi aure tunda ya samu lafiya kafin yaran nan su samu mazajen aure, ga shi har an fara zuwa neman su bai da mata, kuma bai dace ayi auren d'aya daga cikin su bai da iyali ba". "Yo in haka ne abar min maganar zan tuntu6i k'awata Asabe in har ta amince sai ayi auren nan da sati d'aya tunda dukan su ba yara bane kuma tana da hankalin ta da nutsuwa, kasan ita ma mijin ta rasuwa yayi". "To shikenan sai munji daga gare ki duk yanda kukayi". Da hakan ya sa kai ya fice zuwa mazaunin su yana mai labarta wa Mal Abu maganar neman auren shi tunda ya k'i nemo wa da kanshi had'e da gaya mai za'a zo neman auren Zajlah. "Ba komai Mal Inuwa Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alkhairi, na gode sosai da karamci Allah yabar zumunci". Amein ya furta a tak'aice. Saboda hakan yake jin Mal Abu tamkar d'an uwan shi na jini. ****** *BAYAN SATI BIYU* Anyi auren Mal Abu da Asabe wanda ta tare gidan, suna zaman su na fahimta akan su duka ba yara bane, kuma Asabe Mace ce mai hak'uri da sanin ya kama ta don bata san inda take aza Zajlah ba kan kulawar da take ba ta. Cikin hakan ne Zajlah da Salmat suke zama duk gidan da suke so tsakanin wurin Mama Inno da wurin Mama Asabe. A 6angare d'aya kuwa k'anen Baban Alamein wato Alh Muttak'a Mum ta nema had'e da d'ora mai nauyin maganar auren Alamein, domin halayyar su ba d'aya ba shi da Dad, mutum ne mai karamci da iya zama da mutane. Wanda karamcin shi da sanin halayyar shi ya sa yana tunkarar su Mal Inuwa da magana take nan aka ba shi Zajlah, saboda a tunanin su yaron gurin shi ne ke son ta.
.
Ustaz Yusuf ne da Ustaz Lukman ke tsaye suna tattauna wa akan tafiyar da tsarin makantar su kan musabak'ar da za'ayi nan da next year. A tsayen da suke ne suna tattaunawar d'alibai ke wuce wa ta gurin suna gaida su ciki kuwa har da su Zajlah. "Wai har yanzu baka tunkari yarinyar nan da maganar cewa kana son ta ba?, kasan fa ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kar wani ya yima shigar sauri". "Bazai ma kawo ba saboda ina nan da shirin tunkarar ta kwanan nan insha Allah, akwai abubuwan da nake jira ne da komai ya kammala zan tunkari mahaifin ta". "To Allah yataimaka yasa kuma rabon kace, da na yima murna sosai saboda hankali da nutsuwar yarinyar". A hakan dai suka k'are tattaunawar suka shiga cikin makarantar domin fara karantar da d'alibai kamar kullum.

******
Tun ranar da aka sanarda shi maganar tsayar da ranar auren shi da wacce bai sani ba ya shiga tashin hankali marar misaltuwa wanda daka kai dubanka zuwa gare shi za kasan ya fice daga hayyacin shi. A kullum tunanin shi da wanne ido zai kalli friends d'in shi da kullum yake cika bakin kan cewa Mace ba ta gaban shi, wanda a kullum maganar shi bata wuce shi aure baya gaban shi. K'arar rufe k'ofa ce ta dawo dashi hayyacin shi wanda kan tsabar tashin hankali idon shi har sunyi ja, guri ta nema ta zauna sannan ta fara magana. "Yanzu Brother kana gani za ka zuba ido a d'aura ma aure da wannan yarinyar? Wallahi talakawa ne sosai kuma da ka ga yarinyar za ka shaida cewa ko boko batayi ba, ko kusa baku dace ba wallahi". "Ya kama ta in ma aure ake so kayi to a baka dama ka zak'ulo yarinya mai class ba kamar waccan kucakar ba". A kasalance ya tashi daga kwancen da yake ya saka filo a bayan shi ya jingina da gado, ido ya sako mata tamkar yayi kuka. "Ni ba ma yarinyar ce ta dame ni ba kamar auren da za'a yimin a dai-dai wannan lokacin da ban shirya ma abin ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba bazan iya bijirewa buk'atar Mum ba a gare ni zanyi mata biyayya insha Allah". "To Brother Allah yaba ka iko, kuma yasa auren ya zamo alkhairi a gare ka kamar yanda Mum ke furta wa". A tak'aice ya amsa da Ameen. "Amma ya kama ta ka gayawa su brother Imran saboda fara shirye-shirye, kaga sati biyu ya rage har auren". Wayar shi ya d'auko ya mik'a mata had'e da bata umurnin ta kira Imran da Salis ta gaya masu yana neman su yanzu. Cikin mintunan da basu wuce goma ba suka iso gidan, Mum suka fara biyawa suka gaida sannan suka wuce part d'in shi saboda ba suda shamaki da gidan. Bayan sun shiga d'akin ne suka tarar da Saudat na rarrashin shi kan ko tea ne yasha Wanda duk ya fara jemewa, dak'yar yasha tea d'in kad'an sannan suka gaisa. Nan Saudat ke labarta masu abinda ke faruwa, kowannen su mamaki fal a ran shi. Sai dai jin cewa za6en Mum ne suka ga cewa lallai gata ne aka yimai. Nan dai suka tattauna yanda abubuwan za su kasance, amma ya jajirce kan ba za'a yi komai ba bayan d'aurin aure, a hakan suka biye mai saboda sanin hali. ***** 6angaren Zajlah kuwa mamaki ne fal a ranta kan ce wa an tsayar da maganar auren ta da wanda bata sani ba, kuma har yanzu bai zo gidan su ba, to wannan waye shi? Tasan dai ba wanda suka gani a mota bane. Koda jiya ankawo kayan sa Lalle har da lefe duka, anan take jin ana fad'ar cewa mijin bai Nigeria sai ana saura kwana biyu aure zai dawo. "ZAZ mu gayawa Mama ta fitarwa y'an ajin mu da ta su alawar da kuma malamai". "Wannan aikin na kine, ni dai inkin shirya ki fito mu wuce kinga ko jiya mun kusa makara har Ustaz Yusuf na mana fad'an mun fara rashin mayar da hankali yanzu". "Ke kam yanzu da mayar da hankali da rashin mayarwa duk uwar su d'aya ubansu d'aya, saboda dole ki jingine makaranta". Muguwar harara Zajlah ta sakarwa Salmat wanda yasa cikin sauri ta fad'a d'akin Mama Asabe ta d'ebo iya adadin alawar da zasu baiwa y'an ajin su da malamai suka fice. Ustaz Yusuf ne ke rarrashin Ustaz Lukman kan tashin hankalin da ya shiga sanadiyyar alawar da Salmat ta kawo masu had'e da bak'in labari a cewar shi. "Tun ba yau ba nake lurar da kai kan ka gaya mata muradin ka a kanta amma ka tsaya sanya ga abinda ya faru yanzu". Magana kan ta kasa yin ta yake yi saboda sai ya bud'a ba ki ya kasa furta komai. A hakan ya buga mashin d'in shi ya fice daga makarantar da ya ga ta koma mai tamkar
.
Bai gasga ta maganar ta ba har sai da ya tura manyan shi da maganar aure aka tabbatar mai cewa auren ta saura sati biyu. Har ga Allah ya so yasa mu yarinyar a matsayin abokiyar rayuwar shi, har kullum yazo kwanciya muryar tace ke yimai amsa kuwar maganar da ta yi mai, a tunanin shi duk wanda ya sa me ta ba k'aramar sa'ar rayuwa yayi ba. Fadeel kenan yaro ga Alh Ibrahim da Haj Fatima wanda yataso cikin gata da jin dad'in rayuwa har yake tunanin zai iya taka kowa ba tare da antakura shi ba. Sai gashi yanzu ya yi sanyi sosai tamkar ba Fadeel ba sanadiyyar soyayyar da ya d'orawa Zajlah tun ranar da ta rik'e mai hannu had'e da yimai nasiha kan abinda ya kusa aikatawa, sai gashi kuma ashe ba rabon sa bace.

*******
Imran ne had'e da Salis suka zo k'ofar gidan su Zajlah, bayan sun gaisa dasu Mal Abu ne suka yi masu bayani kan cewa abokanen Ango ne ya turo su gurin Zajlah ne. Da hakan Mal Inuwa ya shiga gidan shi ya gaya masu su shirya suna da bak'i saboda suna gidan shi. Shimfid'a aka yi masu a zaure ya fito ya gaya masu su shiga daga ciki. Zaman su bai wuce minti biyar ba Zajlah da Salmat suka fito nan suka gaisa duk da basu san su waye ba. Sarkin tsokana ne Salis ya yi gyaran murya had'e da furta. "Amaryar mu ya kike?".
.
Nok'e kan da tayi ne ya bayyana cewa ita ce amaryar, a ranshi yake k'iyasta lallai Mum ba k'aramin gata tayi wa Alamein ba saboda Zajlah ba tada makusa ko kad'an, don ga alama inta sa mu guri za tafi haka fresh. Gyaran murya Imran ya yi ya kai duban shi ga Salmat yana mai tambayar ta abubuwan da za suyi na aure. "Gaskiya babu abinda muka shirya sai walima wacce za'a yi cikin makarantar mu ranar juma'a ana gobe d'aurin aure". Wani dad'i ya ziyar ci zuciyar su Salis duka sanadiyyar jin ra'ayin su d'aya da Alamein. Yanzu sun sa mu hujjar da za su kare kansu ga friends d'in su koda sun dame su da tambayar ya akayi biki babu wasu events, za su basu amsar amaryar ustaziya ce. "Ashe Ustaziya zamu aura bamu sani ba, to Allah sanya alkhairi ya had'a hankulan ku", cewar Imran. Waya Salis ya fitar yana kira tak'i shiga yakai duban shi ga Imran yana mai cewa' "ka ga wayar mutumen ta k'i shiga yana yuyuwa network ne ba kyau, kuma gashi ya ce yana so yaji zazzak'ar muryar amaryar shi". Ido d'aya ya kashewa Imran saboda ganin ce wa bai fahimci inda yadosa ba har yana batun magana ga shi yana gudun ya kwafsa mai. "Tun da ba'a sa mu wayar shi ba sai ki ba da taki number a tura mai ku gaisa kamin yadawo". "Wallahi banda waya, saboda su Baba sun hana mu rik'a waya". Ba k'aramin dad'i yaji ba da amsar da ta bashi, saboda ya san ko number ya kar6a ko kallo bata ishi Alamein ba, asali ma za ta iya zama silar samun sa6ani tsakanin su. Dubu hamsin suka zube masu domin hidimar aure inji Ango a cewar su. Da hakan sukayi sallama dasu suka fice had'e da yaba hankali da nutsuwar yaran. ******* Tabbas yau ya tabbatar da cewa a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, "gaskiya ba k'aramar asara nayi ba da ban sa mu Zajlah a matsayin mata ba, saboda ban zaci wannan risk'in ba ko kad'an". "Ko da ance wani bai auren matar wani Allah bai k'addar to aure tsakanin mu ba dole inyi hak'uri in fawwala ma Allah lamari na, takan yuyu ba ita ce alkhairi a gare ni ba". Duk a zuciyar shi yake wannan tunanin yana cikin tsananin tashin hankali, a hakan ya tashi ya yi nafila raka'a biyu had'e da addu'o'i ta ke yaji nutsuwa ta sauko mai.

Suna koma wa gidan ne Salis ya saka Alamein gaba da surutu har yana ce mai, "Gaskiya friend ka gode ma Allah da wannan gatan da Mum tayi ma, wallahi ta za6o ma Mace mai hankali nutsuwa da ilmin islama, ko fa waya ba'a bari ta rik'a gidan su wallahi hakan ya burge ni sosai". "Saboda waya ga budurwa ba k'aramar illah bace, itace jigo na farko dake fara taka rawa a lalacewar tarbiyyar yara". "Duk wannan kai ta shafa kuma matsalar kace ba tawa ba, ina ruwan k'wai da aski, kuma in ka zo ne kacika min kunne da surutu sai in ta shi in ba ka guri, saboda na ga ka zo da sabon salo kiran sallah da usur". "Wa ne ni in takura Ango, ai sai dai ni in d'aga in ba ka guri". Hakan ya gama zolayar shi suka fice daga gidan. (Ina so inyi kira gare mu iyayen yara akan sake ma yaran mu domin amfani da waya, muna ganin tamkar burgewa ce ko wayewa to gaskiya wannan bai yi ba. Ba'a ce kar ku bari yaran ku suyi amfani da waya ba, sai dai ya kama ta ku saka ido akan kowan ne tako na yaran ku saboda kaucewa fad'awa hatsari. Kar kice ai shiriya ba a hannu na take ba ga Allah take, kulawar ki zai sa Allah yadubi zuciyar ki ya tallafa maki gurin d'ora tarbiyyar yaran ki akan hanya madai-daiciya. Gare ku y'an mata, ina mai kira zuwa gare ku daku tsalkake zuciyar ku akan mu'amala da waya domin sharrinta ya fi alkhairin ta yawa. Ya Allah don darajar sunayen ka tsalkaka, don k'udurarka don iradarka don k'arfin mulkin ka ka shirya mana y'ay'an mu Maza da Mata.)
0 comments:
Post a Comment