A DALILIN GATA Page 16-20
.
Falon Dad ta koma ko da ta shiga har sun gaji da jiran ta sun fara cin abincin sai santi suke yi, guri ta samu ta zauna ta saka abincin ta fara ci. "Mum baki ta6a ferfesun kifi da ya kai na yau dad'i ba, ga shi ya ji garlic sai k'amshi ke tashi". "Kawai Son ka fito ka gayan cewa matar ka ta fini iya girki, shiyasa har gaba na kake kasa hak'uri sai ka yabi girkin ta". Cak su duka suka tsayar da cokulan su daga cin abincin, kallo ya koma gurin Mum, Dad ne ya kasa hak'uri ya furta. "Yanzu kina nufin wannan mitsitsiyar yarinyar ce ta yi wannan girkin?, lallai Son kana kwasar ragwada, sai dai har yanzu banga ka fara kaurin wuya ba". Yana maganar yana Shafa wuyan shi alamar tsokana. Shi dai kawai basar da abin ya yi yana dariya yana nok'e kai, sai tunani yake yi ashe kan shi yayi wa da baicin abincin ta. "Gobe ma zanje gidan su yarinyar saboda mahaifin ta zai wuce saudiya, don haka kai ma Son ka shirya don kai za ka kaimu gobe d'in ni da ita". Ji yake yi tamkar yafasa ihu saboda yanda Mum ke son kusancin shi da yarinyar, shi ko har ga Allah ko ganin ta bai son yi, hakan dai ya kar6a ba don ran shi ya so ba. **** **** **** 6angaren Zajlah kuwa abincin ta ci sai da ta k'oshi sannan ta kai kayan abinci kitchen, d'akin ta dawo ta hau gyaran shi duk da ba wani gyara ne a d'akin ba, har toilet ta wanke ta shimfid'a sabon blanket ta feshe d'akin da air fresheners sannan ta dawo falon ta zauna, don jin take yi ba ta da ra'ayin fita falon gidan saboda kar ta had'u da Alamein. Tun daga k'ofar shigowa falon wani dadda d'an k'amshi ya tarye ta, ko da ta shigo falon ta gan ta kwance saman 3sitter barci ya yi awon gaba da ita. D'akin Mum ta za ga ko ina fes dashi sai k'amshi ke ta shi, a ranta take ta saka ma Zajlah albarka had'e da hango alkhairin da ke tattare a cikin auren. Sai la'asar Mum ta ta da ita ta gabatar da sallah ta kuma fad'awa kitchen suka yi girki ita da Mama Talatu, bata wani samu sakin fuska daga Saudat ba shiyasa take mak'ale da Mum ko Talatu. Har k'arfe 09:00pm ba labarin Alamein ba bu alamar shi, kuma wayar shi ma ta k'i shiga dole direba ne ya maida ta duk da ba nisa da gidan sai dai shirun unguwar. Kulolin abincin da ta zo dasu ne ta ajiye a falon ta wuce part d'in ta, saboda ba yunwa take ji ba sai da ta ci gidan sannan ta fito. ******* Alamein kuwa da gayya ya k'i ko ma wa gidan, saboda yasan da ya je dole shi zai dawo da ita gidan, sanin cewa Mum za ta iya ne man shi a waya ya sa ya kashe ta duka. Akan idon shi ta shigo gidan ta ajiye abincin sai da ya tabbatar ta shige sannan ya fito ya ci abincin ya ko ma d'akin shi. Kwata-kwata bai son abinda zai janyo alak'ar had'uwar su ko da ta second biyu ce, kwance ya yi yana ta tunanin yanda wai kamar shi za'a yi mai auren dole, don bai ga abin so ga Mace ba. Wasu lokuta in har yana tuna lokacin degree d'in shi yanda friends d'in shi ke rud'ewa in suka ga Mace abin har haushi yake bashi over, don ganin yake yi rashin abinyi ke sa ka 6ata lokacin ka ga Mace. In har bai manta ba akwai lokacin da wata Lubna ta mak'ale mai tana bibiyar shi wanda shi ba ta ko gaban shi, ranar ta tarar da shi zaune dasu Imran kawai ta rungumoshi wait gaisuwa ce, marin da ya kifa mata ne ya dawo da hankalin tsirarun mutane dake gurin nan take aka ta mata dariya tun ranar bata k'ara kula shi ba, da wannan tunanin bacci ya yi awon gaba dashi. (Alamein asuba ta gari inji Jegal, _lolx_.) *** **** **** *WASHE GARI* Misalin k'arfe *11:00am* Mum ta kira Alamein kan cewa ya d'auko Zajlah ya biyo ya d'auke ta su wuce, rasa ina zai saka ran shi ya yi ta yanda zai gaya wa Zajlah ta shirya su wuce d'in, wata dabara ta fad'o mai take ya lalabo lambar ta da Yusrah ta kira shi da ita. Text message ya tura mata kamar haka ( *ki fito Mum na jiran mu*).
.
Ta dai ji wayar ta ta yi k'ara kuma ta d'auko taga alamar abu a sama amma bata gane miye ba, saboda bayan saving number da call ba abinda Yusrah ta ko ya mata, asali ma bayan Yusrah da Mum ba wanda ya ta6a kiran ta a waya. Ba sarwa tayi kawai ta fad'a wanka. Bayan ta fito ne ta kimtsa tana zaune saman mirror tana taje kanta aka banko k'ofar d'akin da k'arfi wanda sai da ta razana da sauri ta zabura. Gashin kan ta ya kama da k'arfi ya fizgo cikin rinannun ido yake nuna ta da d'ayan yatsan. "Ke wace irin dak'ik'iya ce da zaki banzatar da ni a mota fiye da minti ashirin?, waye bawan ki ko wa kika ajiye?, kinsan ba don darajar Mum ba wallahi baki yi darajar ko da takalmin Alamein su ta ka wannan k'azamiyar unguwa ta ku ba". Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta ga shi har lokacin yana rik'e da gashin kanta. Wayar shi da Mum ta k'ara kira a karo na uku ya sa ya sake ta had'e da kai mata muguwar harara. Nan ya d'aga kiran had'e da ce mata ga sunan zuwa, cikin tsawa ya ce mata "fice muje banza kawai dak'ik'iya". Hijab d'in ta ta janyo daga saman gadon ta saka suka fice wanda har lokacin hawayen idon ta basu kafe ba. ®
.
Gaban motar ta je shiga saboda gudun ta zauna baya yace ta mayar dashi direban ta, ashe duk da hakan bata tsira ba harara ya bi ta da ita had'e da furta "baki yi matsayin da zan zauna gaban mota ni da ke ba sai dai ki koma baya, jahilar banza kawai". Sum-sum ta ko ma bayan mota ta takure sai zuciyar ta ce ke mata wani tuk'uk'i. Da hakan har suka iso gidan, Mum ta fito sai dai ta ce dole Zajlah ce za ta shiga gaba ita ko ta zauna baya, akan ta matsa ne ya sa ta fito had'e da durk'usawa ta gaida ita. Tallafo ta ta yi cikin sauri had'e da tallafo ha6ar ta sai ga hawaye shaaa, "me ya same ki Zajlah? Son ne ya 6ata ma ki rai?", duk cikin rud'u take tambayar ta. Kai ta girgiza alamar ba komai, "haba Zajlah yau fa ranar murna ce gare ki za ki je gida kiga iyayen ki, ni da na zata ina fitowa inga bakin ki har kunne kan farin ciki" murmushi ne d'auke a fuskar ta alamar zolaya. Hakan ya saka Zajlah ta d'an murmusa "Mum fa ba komai ina d'auko hijab ne zan saka naji abu ya fad'a man a ido, kuma na duba banga komai ba sai wani zafi da nake ji a cikin idon". Sannu Mum ta mata had'e da saka bakin ta ta bushe mata idon sannan ta rik'a hannun ta ta saka ta gaban motar ta rufe sannan ta shiga baya ta zauna. Unguwar su Zajlah ya nufa wato Birnin yari, ran shi 6ace sai wani cin magani yake yi, har suka isa ba wanda yace uffan har Mum d'in saboda kowa da abinda yake sak'awa a ranshi. Sai dai tunanin Mum har yau babu wani cigaba tsakanin zaman takewar su kawai Zajlah na 6oye mata ne, lallai tabbas yaro man kaza. Da hakan suka iso gidan inda Zajlah bata ko jira su ba ta fad'a gidan su Salmat, Mama Inno ta tarar zaune tsakar gida tana gyaran wake, saman ta ta fad'a tana razgar kuka wanda ya sa ta kayar mata da gaba. ********* A can 6angaren Alamein kuwa Mum na fitowa daga motar ya je zuwa juya akalar motar shi ya koma gida Mum ta bishi da harara. "In ita gidan za ta wuni sai aka ce ma ni ma nan zan wuni?, wato ka fi k'arfin ka fito mu shiga ka gaisa da mahaifan yarinyar nan ko?, wai kai sai yaushe ne za kayi karatun ta nutsu a rayuwar ka?". Cikin 6acin rai ta kama hanyar shiga gidan ta bar shi, dole ba don yana so ba ya rufe motar ya mara mata baya da handkerchief saman hancin shi yana yatsinar fuska tamkar Wanda ya shigo cikin jeji.

*******
Mama Inno ta tallafo ta had'e da jera mata tambayoyin meke faruwa wanda amsa tak'i fitowa sai dai ambaliyar hawaye. Suna hakan ne sai ga Mum ta shigo gidan da sallamar ta had'e da murmushi a fuskar ta, hakan ya sa Zajlah ta fad'a d'aki. Shimfid'a Mama Inno ta yi masu had'e da yi masu kyakkywar tarba cikin fara'a da sakin fuska, Mum ta furta "kin ga y'ar tawa da sangarta muna kawowa k'ofar gida tana fasa kuka, ita da ya kama ta yau ta zamo cikin walwala baki har kunne", cikin zolaya Mum ke furta maganar. "Yo ai kad'an kenan daga aikin Zajlah, ba dai shagwa6a ba har dai in tana gaban Baban ta". D'agowar da Mum za tayi ta ganshi k'erere saman kan ta, muguwar hararar da ta zabga mai ya sa ya janye handkerchief d'in da ya toshe hanci dashi, sannan ya d'osa na gefen ta ya zauna tamkar mai tsoron zama saman allura. "Mu shiga can wurin Mal Abu d'in?". Maganar tace ta dawo dasu hayyacin su su duka biyun. D'aki ta shiga ta d'auko hijab had'e da sako Zajlah gaba suka shiga gidan na su. Nan aka gaggaisa inda suka tarar Baban ta bainan yana gurin Sana'ar shi ta kayan gwari, Mama Inno ce ta fita ta samu yaro don yakiro su Mal Abu. Cikin minti goma sai gashi sun iso, nan dai aka gaisa suka yi mai Allah sanya alkhairi da fatar zuwa lafiya adawo lafiya. Dubu ashirin Mum ta ajiye sannan ta yiwa Alamein alama da ido yaba da nashi, hannu ya saka gaban rigar shi ya kwaso kud'in da shi kanshi baisan nawa ne ba ya ajiye, saboda a matse yake da subar gidan. Shi ya fara ficewa sannan Mum ta kai duban ta ga Mama Asabe tace' "ga y'ata nan ku kulamin da ita zuwa dare Son zai dawo yaje da ita", cikin jin dad'in irin kulawar da Mum ke bata Mama Inno ta furta "za ki samu y'arki lafiya in ma murnar ganin Baban ta baisa ta k'ara k'iba ba". "Ai ko in hakan ta kasance zanfi kowa murna da farin ciki". Da hakan dai suna ta walwala Zajlah ta raka Mum har gurin mota sannan ta dawo gidan. "Zo nan Zajlah inga me ke damun ki, na ga idon ki sun kumbura". Kusa dashi taje ta lafe tana wani zuba shagwa6a. Mama Inno ce ta kar6e da cewa "wacce ta shigo da kuka gidan har ta kayar min da gaba, ashe duk tsabar shagwa6ar zuwa gida ce", nan dai suka ta tsokanar ta ita ko sauraren su kawai take yi. ***** **** 6angaren Alamein kuwa har suka kai gida fad'a Mum take mai kan abubuwan da yake yi marar dacewa musamman ga sirikan sa, tun tana fad'an har ta dawo rarrashi tana mai nuna mai irin yanda Zajlah ke mutun ta ta bai dace ya wulak'an ta na ta iyayen ba. Zurum ya yi yana sauraren ta tamkar mai d'aukar darasi, (ni dai Jegal na ce Allah yasa maganar Mum ta shiga kunnen ka Alamein).
.
Lokacin Salmat ta dawo daga islamiya saboda yanzu ta daina zuwa ta marece da safe zuwa la'asar take dawowa gida. Tana shiga gidan ta ci karo da Zajlah je kaga murna tsakanin su tamkar sun dad'e basu had'u ba, d'aki suka fad'a aka bud'e shafin hira. Bayan sun gaisa ne Salmat ke ce mata "ina gadararren mijin ki?, ina fatar kin fara gyara mai zama yanzu?".
.
"Hmm! Bari ke dai Allah ya had'a ni da miji marar tausayi, ai ni wannan auren nan kallon auren k'addara nake yi mai", nan dai ta kwashe yanda zaman su yake da yanda ya yi mata d'azun ta gaya mata. "Tabbb sai kika tsaya kallon shi gashin ki ya zamo linzami agare shi, wai ke wace irin Mace ce?, ni fa in mutum ya siyi mutunci wallahi zan nuna mai nice na raini mutuncin har ya girma, sa6anin ka nuna min rashin mutunci in nuna ma cikin shi nayi na haife shi". "Salmat ya kike so na yi ne?, wallahi ko Mum ban iya gaya wa irin zaman da muke yi dashi, nasan komai yayi farko zaiyi k'arshe watarana sai labari". "Lallai ko yarinya za ki zama goro ko abin saye, tunda kin za6i siyar da farin cikin ki ga wanda bai san darajar d'an Adam ba". "Ko dai ba za ki rama abinda yake maki ba to kiyiwa kanki gatan rashin d'aukar raini, saboda in kince ba za ki motsa to kin zama shara kenan duk abinda ya d'auko zai sauke shi saman kan ki". "Ni fa kinsan ko Mace y'ar uwa ta ban iya sa'insa da ita bare namiji, don haka kawai ki taya ni addu'a ita ce kawai mafita gare ni". "To Allah ya kyauta kuma ya dasawa Alamein bala'in son ki a ranshi". Suna had'a ido ta yi mata gwalo tana dariyar k'eta. Da hakan dai suka rik'a hira wanda Salmat ta so ta lurar da Zajlah muhimmancin k'watar y'ancin ta ga Alamein amma abin ya ci tura. D'inkin da aka ba ta na ashobe ta kwaso kusan turmi goma sha biyu ta jibge ma Zajlah had'e da furta "ga d'inki nan kije dasu kiyi ko za ki rage nisan gadin gida, gobe nake so in ba Sagiru su ya kai maki ki ragen aiki". "Zan dai d'auki goma inje dasu, sauran kuma kya k'arasa tun da ke kika yi had'ama kika kar6i kayan mutane". "Yi hak'uri matar Alamein, uwargida kuma amarya daga ke babu k'ari". Share ta kawai ta yi ta fad'a kitchen domin kama ma Mama Asabe girkin dare, ita ko ta fice gida tana mata dariyar shak'iyan ci. *** *** *** *** Babu abinda yake tunawa ran shi yayi mugun 6aci sai tunanin komawa d'auko waccan kucakar yarinyar da Mum ta mak'ala mai. Tabbas ba abinda Mum za ta sa shi ya kasa yi mata, kuma yaji fad'an da tayi mai d'azu sai dai ranshi ke 6aci ko yarinyar ya tuna da ita. Murmushi yayi sosai saboda samun mafitar ba sai ya je d'aukar Zajlah ba kuma abinda zai yi Mum ba za ta ta6a sani ba. *** *** *** Kud'i Zajlah ta fitar dubu goma ta bawa mahaifin ta inda dak'yar ta samu ya kar6i kud'in, a cewar shi na mijin ta da Mum sun isa, duk da hakan sai da ya tambaye ta inda ta samu kud'i. "Baba abokanen shi suka bani dubu ashirin cikin su na ba ka goma na ajiye sauran saika dawo in yima dafuwa". Murmushi ya yi dajin dad'in yanda take kula dashi tun bata kai hakan ba. ******** *09:00pm* Aka aiko daga waje wai anzo d'aukar Zajlah, kayan ta ta had'a hadda d'unkunan da Salmat ta jona mata, har da guntun hawayen ta na rabuwa da Baban ta. Salmat ce ta d'auko mata kayan ta domin ta taka mata daga nan ta wuce gidan su, da biyu ta yi rakiyar saboda tana so Alamein ya yiwa y'ar uwarta ba dai-dai ba a gaban ta tayi mai tasss, sai dai sa6anin hakan suna fita suka ganshi jingine ga mota da fara'ar shi kamar kullum. "Ustaziya barka da fitowa", Salis kenan yaro mai kamala da ganin mutuncin manya. Nan suka gaisa har yasa Zajlah ta kira mai Baban ta su gaisa, ko da ta dawo hira ta 6arke tsakanin shi da Salmat domin hali ya zo d'aya kowa akun kanshi ne gurin surutu. Har k'asa ya durk'usa ya gaida Baba had'e da yimai fatar alkhairi, shi ma kan shi kud'i ya ba Baban suna ta yimai godiya. Mota ya bud'e mata ta shiga ya kai duban shi ga Salmat "to sai na ganki alhamis d'in banda karya alk'awari". Cikin jin kunya Salmat ta shige gidan, shi ko ya shiga motar ya ja suka fice. Mamaki ne fal a ranta, lallai ta tabbatar da Alamein bai san darajar aure ba, wato ya fi k'arfin yazo d'aukar ta sai dai yaturo abokin shi, irin haka ne shaid'an ke samun kutsawa zuk'atan masu raunin imani sai daga baya azo ana fad'in wane da matar abokin shi yake mu'amala alhali abokin ne ya bashi wannan damar. (Allah ka tsalkake mana zuk'atan mu ka k'ara mana k'arfin imani, kasa mufi k'arfin zuk'atan mu).
.
Har suka kai gida ba wanda yace da wani uffan, kowa da abinda yake sak'a wa a ranshi, fitowa tayi daga motar bayan maigadi ya bud'e masu gate sun shiga godiya ta yi mai sannan ta nufi hanyar shiga falon da kayan ta Salis ya rik'o mata wasu. A falon suka tarar da shi zaune yana kallo yana latsar waya, part d'in ta ta wuce ta kai kayan sannan ta dawo d'aukar na hannun Salis, abinda ta ji ne ya sa ta ja birki ta tsaya. "Yanzu don Allah A.K.A abinda kake yi a tunanin ka ya dace?, don kawai kar kaje d'auko yarinyar nan sai ka kira ni kace inje in d'auko ta wani aiki kake yi kallon ne aiki ko kuma chart da kake yi?". "Salis ya kake so inyi da rayuwa ta ne?, ka duba kaga yanda damuwa tayi min yawa, abubuwa duk sun ja baya, ko company sai ku ne ke kula dashi". "Wallahi in na ga yarinyar nan har wani k'unci ke ziyartar zuciya ta, na rasa ina zan tsoma kaina inji sanyi". "Hak'uri za kayi, muzgunawa yarinyar tamkar rashin bin umurnin Mum ne, kuma ni banga illar Zajlah ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa, don Allah ka sassauta mata dame za taji? Auren dole ko rashin bata kulawa da baka yi?". "Ko ma miye ita taja wa kanta, da ace da Mum taje da buk'atar neman auren tace ba taso ai da ta hutar da kan ta, to nasan kwad'ayi ya kawo ta shiyasa". "Ai ko da kaga iyayen ta kasan mutane ne masu wadatar zuci da neman na kansu, kwata-kwata wannan abin bai dace ba wallahi". Ganin cewa baza ta iya jure sauraren maganganun ba yasa ta fad'a falon ta yiwa Salis sai da safe ta kwashi kayan ta ta koma part d'in ta. "To yanzu duba don Allah alama ta nuna ta ji me kake fad'a, kasan dai ba dad'i". "Kai ni fa ko a gaban ta zan furta abinda nayi niya don ba tsoron ta nake ji ba". Ganin in ya yi gabas yayi yamma ne yasa ya yimai sai da safe ya fice daga gidan rai 6ace da halayya irin ta A.K.A.

*** *** ***
6angaren Zajlah kuwa tana shiga d'akin gado ta fad'a tana ta razgar kuka cikin damuwa da tsananin 6acin rai. A rayuwar ta bata ta6a saka ma ranta auren mai kud'i don taci kud'in shi ba, asali ma tafi hangen auren rufin asiri ta samu talaka d'an uwan ta da zai san darajar ta da k'imar ta, saboda yawancin masu kud'i basu cika d'aukar talaka wata tsiya a doron k'asa ba. Hakan ta ci kukan ta har ta gode Allah ba mai rarrashi. Alwala ta yo ta yi sallah had'e da kaiwa Allah kukan ta kan yakawo mafita acikin wannan aure na ta, bayan ta gama ne ta dunk'ula ta kwanta had'e da tunani iri-iri har bacci ya yi awon gaba da ita. *** *** *** *WASHE GARI* Bayan ta gama sallah ne ta kimtsa d'akin ta, wanka ta yi ta shirya sannan ta nufi kitchen tea ta had'a iya cikin ta sai k'wai biyu data soya, bayan ta karya ne ta koma d'akin ta ta kwashi turamen da tazo dasu ta nufi d'ayan k'aramin d'akin da aka saka mata keken d'inkin ta da sauran komatsan ta, zaune ta yi ta fara yankan d'inkin sai da ta yanka turmi hud'u sannan ta hau keken ta fara. *** *** *** 6angaren Alamein ko yana dosowa falon k'amshin wainar k'wai ta doki hancin shi, sai dai yaja ya yi turus da yaga dinning table d'in wayam sa6anin kullum da yake tarar da girki a gurin. Yau har ga Allah yaso yaci girkin ta kodon fad'an da Mum ta yimai ce wa kar yadawo gidan ta cin abinci in har ba matar shi ce taje mata wuni ba da tasan cewa babu mai bashi abinci ba. (Tabbb ni dai Jegal nace jin dad'in ferfesun kifi ne yasa Alamein zai la6a da fad'an Mum ya kwashi girki, sai ga shi ran Zajlah ya 6aci yau bata ajiye ba, lolx). Zaune ya yi turus a falon yana tunanin mafita, ga shi yana so yaje office cikin lokaci saboda wani meeting da zasu yi da wasu dasu ke da share a company d'in. Ga shi shi ba gwanin girki ba don ko ruwan Lipton bai iya dafawa ba. Kitchen ya fad'a ya yi sa'ar ruwan lipton har sun fara hucewa, hakan ya zuba madara da sugar kad'an ya sha ya fice daga gidan. *** *** *** Zajlah ko na can na fama da d'inkin ta, har wani nishad'i take ji na ganin ta samu abinda zai rage mata damuwa, don har ga Allah ta manta wani 6acin rai data shiga jiya. Jin cikin ta na k'ugi ne ya sa ta ajiye d'inkin ta shiga kitchen macaroni ta yi jallof d'inta da dama ta saka a kula ta d'auki plate da cokali ta koma d'akin. Bayan ta zuba ta ci ne ta tsinkayo kiran azahar, nan ta yi sallah sannan ta hau d'inkin ta.
.
Kwanaki hud'u sun shud'e ba wani cigaba tsakanin zaman Alamein da Zajlah sai ma abinda ya k'arasa kwa6e wa, don yau kusan kwanan su biyu basu had'u da juna ba. Alamein ya fara shiga takura saboda ga shi ba gwanin yawon restaurant ba, asali ma yana iya cewa tun tashin shi bai ta6a cin abincin waje ko na wani aure ba sai dai na gidan su. A hakan yake buge-bugen shi in ya fita office yasha lemo da biskit, sai kuma maltina rabon shi da abincin kirki tun ranar da Zajlah ta wuni gidan Mum. **** **** **** Yau tun safe ta taya Mama Inno aikin gida saboda tana so taje gidan Zajlah, k'arfe *11:00* ta gama kimtsawa ta shiga gidan su Zajlah ta ja Naja'atu domin ta raka ta, saboda tun auren Zajlah ba ta jin dad'in fita ita kad'ai. Naja'atu y'ar k'anen Mama Asabe ce mai kimanin shekara tara a duniya, tun auren Zajlah Mama Asabe ta ji gidan ya yi mata shiru dayawa ta shawarci Mal Abu ta d'auko yarinyar ta dawo hannun ta da zama. Keke napep suka samu suka shiga sai G.R.A, gidan su Alamein ta fara shiga ta gaida Mum saboda karamcin dattijuwar, da murna ta tarye ta kamar ta had'iye ta, nan suka had'u da Yusrah ita ma ta zo ma Mum hutu kwana biyu. Tare suka rangad'a sai gidan Zajlah har Mum na mitar Yusrah ba ta gajiya da zuwa wurin Zajlah, basu had'u da Saudat ba akan tana makaranta.

*** *** ****
Zaune take saman tela ta duk'ufa d'inkin saboda yau take so ta k'arasa ta samu ko d'an mak'ociyar ta ne Shema'u ta aika yakai wa Salmat d'inkin, saboda Salmat ba ta da waya haka ma iyayen mata, su Mal Inuwa ne kawai suke da kuma Baban ta ya wuce saudiya kwana biyu da suka wuce. Jin sun shigo falon ne tsit ya sa direct suka yi part d'in ta, ganin su ba k'aramin farin ciki ya saka ta ba, da gudun ta ta rungume Salmat ta saki ta rungume Yusrah sannan ta saki baki tana kallon su. "Daga ina kuka had'u haka ba sanarwa sai dai ku diro ma mutum ba shiri?", tana maganar ne d'auke da murmushi a fuskar ta. "Allah ne kawai ya had'a mu don mu d'ebe maki kewa yau, Mum na shiga gaidawa na tarar da ita a gidan". "Ai ko gaskiya na ji dad'i sosai da ganin ku", hannun Naja'atu ta rik'o had'e da tambayar ta lafiyar gida, yarinya mai surutu ta yita zubawa har da bata labarin da Baba zai wuce su Mama da Anty Salmat har da kuka suka yi, dariya sosai yarinyar ta basu yanda ta zak'e tana bada labari da kwatan ta yanda su Salmat suka yi. D'inkin Yusrah ta janyo tana dubawa had'e da furta "anya Sis ke kika yi wannan d'inkin?, ko wata ke zuwa tana taya ki?", cikin zolaya take maganar. "Tabbb ka ma kan ki ai wannan oga ce a gurin d'inki, tare fa muka fara koyon d'inkin amma yanzu ko wacce ta koya mana ta wuce ta musamman breast cup tamkar ta auna su". "Kai Salmat ki rage sharri fa, ni dai kawai d'inki ke birge ni shiyasa na mayar da hankali na iya". "Kin manta ana gab da auren ki da muka je gidan Zainab mai d'inki muka tarar ta saka wani style gaba ta zuba tagumi akan ta kasa had'a shi sai da kika kar6a kika had'a?". "Na tuna uwar k'wakk'wafi". Keken ta hau ta k'arasa had'a rigar sannan suka koma d'ayan d'akin a falon ta, lemo da ruwa ta kawo masu sannan aka zauna dasa wata sabuwar hira. "To ku tsaida hirar hakanan kuje kitchen ku ne ma mana abinda za muci, saboda ni dai na gaji bazan iya girki ba". Salmat ce ta bi ta kallo had'e da "furta matar nan dad'i ya maki yawa, mu da muke bak'i mu za mu ne mawa kan mu abinci, to tsaya ma da bamu zo ba waye zai dafa maki?". "Manta kawai barta ta huta, nasan gajiya biyu ce saman kanta ga ta Brother na, ga ta keken d'inki", tana maganar had'e da kashewa Salmat ido d'aya. "Ku dai kunga bone wallahi, tahowa zanyi in gayawa su Baba duk ayi maku aure, saboda na fahimci inda kuka dosa". "Kai rufa mana asiri, mu fa yanzu ake renon mu komai bamu sani ba", cewar Yusrah. "Shi ne naga da rarrafe kuka zo gidan nan k'arewar raino, ku dai yi sauri ku fitar da Maza musha shagalin biki". Salmat ce ta furta "ni kam bazan yi aure ba sai kin haihu hud'u tukuna", "Tunda haihuwar kashi ce, wallahi da kin shiga uku in na haihu hud'u kina gida, Allah sai dai mu bada ke sadaka koda a lima mai ne". Dariya suka yi sosai nan Yusrah ta kama hannun Salmat suka fice zuwa kitchen domin samun abinda suka girka. Ita ko Naja'atu ta janyo tana ta ba ta labari sai dariya take yi, ji take yi tamkar farin cikin ta yad'ore hakan. ®
.
Suna tashi daga office ya ce ma Alamein suje yau gidan shi zai je duba ajiyar shi, jin hakan ya sa Imran yace shima baza'a barshi a baya ba. Hakan ta sa suka d'unguma su duka suka biyo shi, wanda sai fargaba yake yi in ba abinci za suje ci ba, duk da babu abinda basu sani a zaman takewar su ba, sai dai yanzu yana jin nauyin suje gidan ba su da abinda zasu ci. Dabara ce ta fad'o mai na kawai ya nuna masu zai biya gurin Mum yakai mata sak'o, saboda sanin in dai daga office suke direct suka yi gidan to abinci ne na farko da Mum za ta tarye su dashi. Sai dai kash ba yanda bai yi ba Salis ya kafe kan cewa shi fa sai ya je yaga ajiyar shi sannan in zasu wuce su biya su gaida Mum d'in. *** *** *** Abinci suka yi kusan kala uku suka saka a kuloli, saboda cikin su ba wanda yasan cewa ta daina yin girki da Alamein, asali ma Salmat ce ta sa ayi girkin haka a cewar ta gidan Amarya har kullum bai rasa bak'i. Bayan sun k'are girkin ne suka kimtsa gurin sannan suka koma falon ta, abin dariya ko da suka shiga Naja'atu na ta zuba bata lura da Zajlah ma bacci take yi ba. Dariyar su ce ta tayar da ita daga baccin da ya d'auke ta, zama suka yi suna dariyar ta suna furta "neman kud'i da wuya yarinya". "Ai ni ba kud'i ne nake nema ba, rage zango ne nake yi saboda ban aikin komi". "Ashe in aka bada kud'in wannan d'inkin in d'auka kenan", cewar Salmat. Yusrah ta ce' "Sis ni ma zan kawo customers kwanan nan tunda na ga ke expert ce a 6angaren d'inki". Hararar su kawai ta yi ta fad'a toilet ta yi wanka. Bayan ta fito ne ta kimtsa Yusrah ta saka ta gaba da cewa sai ta yi mata kwalliya don tasan yanzu Brother bai nesa da dawowa, hakan ta saka ta gaba ta yi mata make up had'e da wani nad'i tamkar an d'aura gwaggwaro. (Saura k'iris waya ta ta su6uce ta fad'i, sai dai na rik'e ta gam saboda gudun rasa wacce zan kawo maku rahoto, tabarakallah ahsanul khalik'een kawai nake na natawa, _lolx_). Baki Salmat ta saki tana kallon Zajlah had'e da furta "lallai make up na fitar da 6oyayyen kyau, to ni ma ba za'a barni a baya ba azo a tsantsara min tawa".

Da dosowar su gidan k'amshin abinci ne yatarye su, mamaki fal a fuskar Alamein sai dai kawai ya dake kuma ya basar. Falon suka shiga sai dai wayam ba kowa sai dariyar su ce ke tashi daga falon Zajlah. Masauki suka yiwa kansu suka zube a falon. Hayaniyar da suka jiyo a falo ce ya sa Yusrah ta lek'o, da d'an sauri saurin ta ta iso falon tana mai fad'in "oyoyo Brother na", cikin sakin fuska ya amsa ta sannan ta gaida su Salis. D'akin ta koma ta gaya masu wanda Zajlah kamar kar ta fito sai dai mutuncin su Imran gare ta sun wuce ta yi masu haka, gyale ta janyo ta yafa sannan ta tunkaro hanyar zuwa falon. Duk zumud'i da zagwad'in ta na saka Salis a idon ta sai gashi wata kunya take ji tana dabai baye ta, jin batajin motsin Salmat bayan taba ya sa har za ta bud'e k'ofar kuma ta juya ta saka ta gaba suka fito falon. Gaisawa suka yi wanda Salmat da Zajlah d'in ko ta kan shi basu bi Ba, shi ko kallo guda ya yi ma Zajlah ya ji wani abu ya tsirga mai take ya mayar da kanshi k'asa yana latsar waya ganin cewa tana tare da y'ar uwar ta mai tsiwa. Kamar kullum falon ta suka koma suka ci na su abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon su dukan su. "Ka d'auki ajiyar ka mu wuce, in kuma baka ta shi ba ni in fice", a fad'ar Imran. Salmat ya nuna da yatsa "kaga ajiya ta nan", kallo aka bita dashi wanda ya yi silar k'ara jin kunyar ta tamkar ta nitse. Zajlah kanta ta yi mamakin faruwar hakan, inda Alamein ke dubin me Salis ya hango a wannan fitsararriyar. Da hakan dai suka ke6e suka k'ara tattaunawa tsakanin su, inda soyayya mai k'arfi ta d'inke tsakanin su. Sai da suka yi girkin dare suka ci sannan kowa ya kama gaban shi. Alamein ko anci darajar Yusrah don ita ke saka mai abinci wanda Zajlah bata nuna mata cewa ita kad'ai ke girkin taba, kuma tasan ganin mutane ya sa shi kan shi yaci abincin.
.
Awanni sun shud'e, kwanaki ma haka, wanda yanzu auren Zajlah da Alamein ke cikin wata na biyu amma ba wani canji tsakanin su kowa sabgar gaban shi yake yi, inda Zajlah d'inkin ta kawai ta saka ma gaba don tana samun customers da dama ta gurin Salmat, Yusrah da kuma Shema'u. *** *** 6angaren Salmat kuwa magana ta yi nisa tsakanin ta da Salis inda manya suka shiga gida har an saka ranar auren su. Aikin ta ta gama cikin lokaci saboda za taje gida wurin ganin Baban ta daya dawo daga saudiya jiya. Ba tada niyyar gaya mai komi saboda dama yanzu kusan kwana biyu sai taje gidan Mum, wani lokaci ta shiga gidan mak'ociyar ta Shema'u, ko yanzu a waya ta kira Mum ta shaida mata za taje wuni gida, hakan ya sa tace taje kawai ita ma za tazo daga baya. Bayan ta kimtsa ne ta fita sai da takai saman titi sannan ta samu keke napep ta shiga sai gidan su, da murna ta fad'a gidan ta gaisa da Mama Asabe, gurin Baban na ta taje ta lafe tamkar wata mage, bayan sun gaisa ne yake ta ba ta labarin Makkah yana saka mata albarka har da guntun hawayen shi. "Haba Baba miye na kuka a ciki?, ai wannan abin farin ciki ne a gare mu duka". "Dad'i ne yayi man yawa Zajlah yanda na tai Makkah ta sanadiyyar ki, lallai tabbas y'ay'a mata rahama ne, gashi Allah bai bani d'a namiji ba amma kin zame min tamkar d'a dubu".
.
"Ba komai Baba, adai yi ta saka mu a addu'a, Allah yasa anyi hajji kar6a66e", "Ameen" ya furta a tak'aice. Ferfesun kifin da ta yi mai ne had'e da alalen dankalin turawa sai so6o da jinja data had'o mai ta zube gaban shi. "Zajlah Duke ina zan kai way'annan kayan? ai sun yi yawa", yana maganar farin ciki fal ranshi. "Baba ba komai kaci sai ka k'oshi, nasan ka yi kewar abincin Nigeria". Naja'atu ce ta zo tana furta "Baba in baza ka iya canyewa ba ni zan taya ka, kaga ma yau komai banci ba". Dariya ta basu sosai. Kayan aka d'iba akace ta kaiwa Mama Inno ta dawo sannan ta fice. Sai zuwa bayan la'asar ne Mum ta iso ita da sarkin jin kai wato Saudat, sai wani sha k'amshi take yi tana yatsinar fuska tamkar anyiwa zawo yayyafi, saura k'iris Zajlah ta kwashe da dariya ganin yanda take yiwa fuska. Kaji ne dak'wa-dak'wa Mum ta soyo ta zo ma Mal Abu dasu, ba k'aramin dad'i Zajlah ke ji ba ganin yanda Mum ke tarairaya da ita da kuma mahaifan ta, godiya suka zuba sosai wanda har suka sa Mum na jin nauyin hakan da suke yi mata. Basu wani dad'e ba suka fice daga gidan. D'aki suka wuce bayan wuce war Mum suna hira, inda magana d'aya ga ta biyu Salmat ta ce Salis kaza. "Ke tsaya! Wai ke nan nuna min za kiyi kinsan soyayya kenan?, sai wani zak'ewa kike yi ba kida hira sai ta Salis". "Habawa yarinya sunan ki sorry, gaskiya har tausayi kike ban da baki san dad'in "So" ba, yarinya da kin more rayuwarki". "Rashin sanin gard'in So wani lokaci ya fi sanin So d'in kwanciyar hankali, ni kinga yanzu hankali na kwance, ke ko kullum la66an ki basu huta da furta Salis kaza ba". Dariya Salmat ta yi sosai, inda a 6angare d'aya take tausaya wa rayuwar auren Zajlah da take ganin an tauye ta dayawa, saboda wannan auren sunan shi farin cikin uwar miji k'uncin surukar ta. **** **** **** Bayan sati biyu ne dubban mutane suka shaida auren *SALIS YUSUF* *&* *SALMAT INUWA* Wanda aka gabatar da biki cikin farin ciki da walwala tsakanin ango da amarya duk da ita ma ba wasu events akayi ba. Kullum Zajlah na saman hanyar gida tun ranar da aka saka Salmat a lalle har yau da za'a kai ta gidan mijin ta unguwar ni'ima. Mum, Yusrah da Saudat sun yiwa Zajlah kara sun zo auren, duk da auren ya zamo tamkar 6angare biyu a gurin su saboda amintakar Alamein, Imran da Salis d'in sun taso tare ne tun primary skul d'in su, inda abotar tasu har ga iyaye ta kai. Hakan aka dunk'ula Amarya aka kai ta d'akin mijin ta, sai dai fatar Allah yabada zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba. Sai da kowa ya watse ne daga ita sai Salmat d'in ta duk'ar da kanta dai-dai kunnen Salmat d'in ta furta "to uwar soyayya kamin nan da wata goma muna jiran muga d'an soyayya". Kasa magana ta yi sai hawaye dake yi mata zuba na kewar gida da iyaye, suna hakan ne Imran ya rako ango nan suka yi raha da zolayar juna sannan Zajlah ta bi Imran ya sauke ta gida.

*** ***
Bayan kwana biyu Mum na zaune suna hira da Dad take gaya mai tana ganin fa kamar har yanzu babu wani cigaba tsakanin Alamein da Zajlah. "Koma miye Haj Hasana laifin ki ne, saboda kin tauyewa yaron nan rayuwar jin dad'i sosai, don haka gobe zan kira shi yasauwak'e ma yarinyar wannan auren". Bud'ar bakin ta ke da wuya za tayi magana ya yi mata alama da bai son jin komai daga gare ta, da hakan suka je suka kwanta kowa da abinda yake sak'awa a ran shi. K'arfe *02:00am* wayar shi ta d'auki k'ara kamar kar yad'aga saboda baisan lambar ba kuma da fargabar waye zai kira shi da wannan tsakiyar daren. D'agawar shi dai-dai take da furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un", wanda ya yi dai-dai da zaburar Mum daga baccin da take yi, wayar ce ta ku6uce mai inda ya tafi luuu ya fad'i k'asa a sume.
.
Jijjiga shi Mum ta yi had'e da salati a bakin ta inda ko motsi baya yi, waya ta janyo ta kira Alamein sannan ta fito harabar gidan da kukan ta domin kiran direba da maigadi, har part d'in Dad suka shiga a rud'e, duk iya dabarar da za suyi sun yi amma ko motsawa baiyi ba, kukan Mum dana Saudat kawai kake jiyowa wanda gida duk ya hargitse ya koma tamkar safiya.

Gigice ya lalabo makullin motar shi ya sauko ya bud'e falon ya fice, inda ya tayar da maigadin shi don yabud'e mai k'ofa, hankali tashe yake yimai bayanin abinda Mum ta gaya mai. Motsin da ta ji ya yi yawa ne har an bud'e falon an fice ya sa ta yaye labulen window d'in ta, cikin tashin hankali ta hango yana yiwa maigadi bayani. Hijab d'inta ta zaro daga cikin wardrobe ta saka ta fito, tana kawowa gate d'in yana ficewa da motar. Baba maigadi ta tambaya abinda ke faruwa, nan ya yi mata bayani kamar yanda Alamein ya gaya mai. "Baba don Allah ka kula da gidan bara in k'arasa a k'afa". "Haba y'ar nan ki duba fa kiga dare ne, kuma ke Mace ce kiyi hak'uri ki koma zuwa safe muji yanda abin ya kasance". "Baba wallahi bazan iya zama ba har sai na ga wanne yanayi Dad yake ciki, da ganin yanda Alamein ya fita kasan abin sai a hankali". Ganin da gaske ta kama hanyar zuwa gidan ne ya sa ya rufe gate d'in ya mara mata baya. Suna kawowa motar direban Dad na kunno kai a guje, inda ta Alamein ke daga waje ko rufe ta bai yi ba. Mum ce da Saudat suka fito a rud'e inda idon kowa cikin su har sun kumbura, maigadin su ta ba umurnin ya shiga motar Alamein yakai ta asibiti saboda ba za ta iya zama ba, don direban su da Alamein suka wuce da Dad. Nan Zajlah da Saudat suka fad'a motar aka fice dasu sai asibitin Aisha Buhari, wanda ko da suka isa har an shiga A&E dashi sai direba ne da Alamein ke kai kawo a wurin, wanda duk iya nazarin shi ya kasa gano miye silar wannan abin. Juyawa ya yi zuwa ga direba had'e da je fo mai tambayar silar wannan abin.
.
"Wallahi Yalla6ai yanda ka ganshi hakan Haj ta kira mu muka tarar dashi, bamu San takamemen meke faruwa ba, sai dai ka jira k'arasowar Haj kaji, Allah dai yata shi kafad'ar Alh", yana maganar yana shartar majina. Da hanzari Mum ta fito had'e da tambayar su abinda ake ciki, Alamein ya bata amsa cikin k'arfin hali cewa tun shiga dashi ba wanda yafito har yanzu. "Mum wai miye silar wannan tashin hankalin?, saboda ni dai a sani na Dad ko hawan jini bashi da barranta na inyi tsammanin shi ne ya ta shi". Nan ta kwashe abinda tasani ta gaya mai. Wayar ce ya buk'aci gani inda aka yi sa'a Mum ta fito da ita, kar6a yayi ya binciko last call d'in wayar ya kira, kawai Mum ganin shi ta yi zaune da6as a k'asa sai hawaye ke biyar idon shi. Mutum mutumi ya koma saboda magana kan ta bai iya ta sai dai kaga la66an shi na motsi sai ido da yake saki tamkar sabuwar gawa, hawayen da bakin dake motsawa kawai zai tabbatar ma yana raye ba don hakan ba sai dai kace a sume yake. Cikin tashin hankali Mum ta dafa kafad'ar shi had'e da jero mai tambayoyi cikin rud'u da firgici, wanda shi ko bin ta kawai yake yi da ido. Cikin tashin hankali Zajlah ta samo ruwa a cup gurin masu jinya ta zo gab dashi tana jijjiga kafad'ar shi, addu'a ta yi sosai a ruwan ta bashi ya sha kuma ta dinga Shafa mai su a fuska tana mai k'ara karanto wasu addu'o'i tana tofa mai, inda gaba d'aya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye kan tausaya wa yanayin da suke ciki. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai Mum ke furta wa wanda ta fara jin nutsuwa na sauko mata. Sa6anin Saudat dake wata irin gunza tana fisgar gashin kanta tamkar wata sabuwar kamun hauka. Ajiyar zuciya Alamein ke sauke wa kad'an kad'an saboda wani sanyi da yake ji yana sauko wa tun daga saman kanshi har zuwa yatsan shi. Hannun ta ya janyo da take rik'e da kanshi tana tofa mai addu'a ya d'ora saman k'irjin shi dake dukan tara-tara, ruwan ta kuma d'ora mai a baki ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya ya zube a jikin ta tamkar gawa. K'arar da ta saki ne ta janyo hankalin mutane da dama suka yo gurin, wasu nurse ne guda biyu suka tallafe shi aka shiga d'ayan d'akin dashi na kusa da Dad. (Wayyo ni Jegal meke faruwa haka?, zuciya ta duk ta cunkushe saboda rashin sanin takame-men me ke faruwa da d'a da uba)
.
Babban tashin hankalin su rashin sanin takamemen abinda ke faruwa, suna hakan ne Dr ya fito daga d'akin da aka shiga da Dad, cikin rud'ani suka tare shi kan cewa ya ake ciki? "Ina son ganin wani daga 6angaren marar lafiyar amma kuma namiji ba Mace ba", daga hakan ya shige office ya bar su tsaye tamkar gumaka a chochi.
.
"Mum me zai hana a kira Abban Yusrah a gaya mai abinda ke faruwa, tunda ga Alamein shi ma akwance". Wayar Dad dake hannun ta ta mik'a mata alamar ta kira. Alh Muttak'a ta gani rubuce nan ta kira kusan sau uku sai ana hud'u aka d'aga, bayan ta gaida shi cikin nutsuwa ta kora mai bayanin abinda ke faruwa, nan yace gaya nan zuwa. Suna hakan ne direba ya kawo wayar Alamein da ake kira dake cikin mota, Zajlah ce ta d'aga wayar suka gaisa take kora ma Salis abinda ke faruwa, nan ya ce mata shi ma gayanan zuwa . Kusan tare suka iso asibitin, Imran, Salis da kuma Abban Yusrah, ga alama Imran da Salis sun san me ke faruwa amma ganin tsananin tashin hankalin da ake ciki ya hana masu furta komai. Office d'in likitan suka shiga nan yake ce masu "sanadiyyar abinda ya samu Alh wanda ko mu bamu san miye ba ya yi silar mutuwar 6arin jikin shi had'e kuma da hawan jini na farat d'aya wanda ke barazana da rayuwar shi". Su duka ukun "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" suke furtawa, cikin tsananin tashin hankali Abban Yusrah ke furta "wannan wane irin tashin hankali ne dake neman rayuwar d'an uwa na?, ya Allah ka tada kafad'ar Yaya". Imran ne ya yi gyaran murya had'e da ce ma Abban Yusrah "Abba wannan abin yana da nasaba ne da k'onewar ma'aikatar Dad gaba d'aya wacce ba'a san miye silar hakan ba, yanzu hakan daga can muke wanda har yanzu wutar ke ci". "Shi ne ma kiran da muka yiwa Alamein domin yasan yanda zai gayawa Dad maganar cikin kwanciyar hankali, ashe an samu wanda ya gaya mai har ya yi silar jefa wad'annan iyalai cikin tashin hankali". "Innalillah" Abban Yusrah ke ta nanata wa wanda shi ma ga alama ita ce tayi tasirin samun nutsuwar shi da yanzu shi ma ya zube a sume. "To yanzu likita me ake ciki akan ciwon na shi?". "Za ku jira nan da awa hud'u domin samun farfad'owar shi sannan a hau mataki na gaba". Hakan yasa suka fito jiki a mace tamkar wa'anda k'wai ya fashewa a ciki, cikin k'arfin hali Mum ta tunkare su domin jin me ke faruwa. Ganin cewa 6oye mata bai da wata fa'ida ya sa cikin nutsuwa da lallami had'e da nasiha suka gaya mata me ke faruwa. Ba k'aramar bajin ta ta yi ba gurin aro juriya ta yafa ba, bayan "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai "Hasbunallah wa ni'imal wakeel" kawai take nanatawa. Zajlah kanta ba k'aramar gigita ta shiga ba na jin k'addarar da ta sauko ma wa'annan iyalin ba, k'arfin hali ta yi sosai sannan ta tunkari Saudat domin rarrashin ta ganin irin yanayin da ta shiga. Likita ne ya fito daga d'akin da aka shiga da Alamein, cikin sauri suka tunkare shi had'e da jero mai tambayoyi na jin wanne yanayi yake ciki.
.
"Za ku iya shiga ku duba shi, amma plxxx banda hayaniya saboda yana buk'atar hutu". Haka suka rik'a rigen-gen shiga d'akin. Kwance yake kanshi yana kallon ceiling wanda kallon ne kawai yake yi amma bai da takamemen abinda yake kallo, saboda tunane-tunane da suka dask'are zuciyar shi wanda yake jin tamkar ma ta dai na aiki. Sannun da suke jero mai ya d'an dawo dashi hayyacin shi wanda ba bakin sai ido kawai da yake bin su dasu, sai kai da yake kad'awa alamar amsawa. "Mum kinji me ya samu Dad? Mum Dad ya mutu ko? Shike nan yanzu ba mu da komai? Mum kisa a kashe wutar da takama a company". Sambatu yarik'a yi tamkar wani zautacce, hakan yasaka Mum ta fasa wani irin kuka mai cin rai. Da saurin ta ta zo ta toshe mai baki had'e da girgiza mai kai alamar yayi shiru inda ita ma sai hawaye ke sauka akan budurwar fuskar ta, ruwa ta kuma bashi tana dafe da k'irjin shi tana tofa mai addu'a, Zajlah kenan yarinya mai zuciyar tausayi. Wayar Imran aka kira had'e da gaya mai cewa an samu nasarar kashe wutar amma fa ta lashe komai na ma'aikatar wanda ko fallen takarda ba'a fita dashi ba, hakan ya yi dai-dai da kiran sallar asuba. (Hakan ya sa ni ma dole na dakata domin gabatar da farali).

0 comments:
Post a Comment