JININ JIKINA Page 21-25
.
***
ƁBayan wasu kwanaki FARIS yanzu sam hankalinsa bayakan baby boo kusan zance baya kiranta kullum itake kiransa, da takirasa saiya shirgamata karya kan aiki yamasa yawa yana gajiyane shiyasa baisamu ya kirata, abunka da mata da miji idan yafaɗamata haka saima tausayinsa datake ji ita a ganinta aikin ne yamasa yawa."
"Hakafa rayuwarsu ke gudana yanxu a kalla faris yana neman shuɗe sati ɗaya a nijeriya."
"Zuwansa gidansu baifi a irgaba kullum suna tareda Faty duk tahanasa sakewa saikara rura wutar tsafinta take kotakota yanxu faris baya hankalinsa itake controlling dashi, ga ta matsa masa kan suyi aure, yabata hakuri kan jiran Dad yake da zarar yadawo za'yi komai, da waɗannan kalaman yasamu ya kwantar mata hankali."
"yauma kamar kullum suna tare suna hiransu cikida so da kauna, faris kenan da faty."
"Wayarsa dake aje gefensa ne yaɗau ruri yana neman agaji,sharewa yayi not minding yadauka ko yasan mai kira."
"Uhmmm honey kanajina faty ce ke faɗar haka."
"ina jinki swthrt Faris yaceda ita."
"Wannan kuɗin da kace zakaban ɗinnan 1million naira ko kamanta ne tana faɗa tana fari da ido."
"No ban manta ba let transfer it now to your account kinji koh?."
"Fari da ido tayi tace naji honey."
"In less than 3mins Faty taji alert a wayarta, dake da E banking yayi amfani."
"Full of suprise take kallonsa she could not believe it, idan ko hakane maganin boka share kukanka na aiki 1million naira tayi exclaiming, hugging ɗinsa tayi tabasa peck a cheek tace i loɓe you Faris, ina sonka, da sonka nunfashina ke fita kazamo wani gurbi na rayuwata i can't live without you pls karka bar rayuwata kakasance dani har abada tana magana tana shishigewa jikinsa kamar mage."
"fuskarta ya ɗago ya zubamata oily eyes ɗinsa yanamata wani shu'umin kallo haɗe da killer smile ɗinsa wanda ni Neerat nakasa fassara kallon mai wannan, faty yakira cikin muryansa mai sanyi."
.
"ɗagowa tayi tana kallonsa itama danata salon kallon tace na'am."
"Alkawari na miki xan kasance da ke no matter what kinji, kada kidami kankai wannan kyautar ba komai bane idande wake nayisa kai koma wa wani nayi, so yanxu kimanta da wannan muyi hiranmu kinji."
"Kai ta gyaɗamasa alamar taji maganarsa, hiransu sukacigaba dayi kamar ba gobe."
***
Mum ne da 'yan matanta suna ta faman aiki tarar Dad kasancewar yau zai dawo."
"Mum nikam ya faris ya komane humaira ce ke tambaya."
"Fareeda tace banajin ya koma sabida munyi waya da Muskan jiya tace vai dawo."
"Mum ce tayi saurin karɓan zancenda fareeda keyi tace kina nufin Faris yana nan amma baixuwa ko gaisuwa muyi anya lafiya kuwa? kuma yabar min daughter acan ita ɗaya kudaukomin waya nakirasa yanxu."
"Wayan sukamikamata ta gwada kiransa saidai rashin sa'a takira kusan sau biyar amma ba'a ɗagawa, layin muskan takira cikin sa'a kuwa ta daga."
"Gaisawa sukayi da mum, bayan sungama gaisawa ta tambayi lpyrta tace tana lpy, bawani matsala mum tasake tambayarta, tace ba komai, kunyi waya da faris inji mum, eh munyi tawa mum karya ɗan kare mijinta, toh yayi kyau ki kulla da kanki, kuma kimaida hankali kan karatu kinji, naji mum na gode, ba komai 'yata ,hira suka ɗan taba kan sukayi sallama."
"@2:00pm Dad yadawo family'nsa sunyi murnar dawowansa, tarɓansa sukayi cikin girmamawa, bayan ya huta yayi wanka suka cikamasa gabansa da abinci kala kala, dukka yaran da mamar kowa naso ya farantamishi, sosai yaco abincin sai albarka yaketa samusu yana kuma yaba abinci."
"Daya gama cin abincin suka koma falo, nan yabaiwa kowa tsarabarsa, murna suka hauyi suna masu farinciki da kyutarda mahaifinsu yamusu ta sabuwat waya."
.
"hira sukasomayi da matarsa dakuma 'ya'yansa, cikin hiransu ne mum take sanar dashi zuwan Faris, yace toh yayi kyau, ina ita Muskan ɗin ya barta, mum tacemasa ai tana makaranta shiyasa basuma zo tareba, yace toh yayi kyau sunma yi kwana biyu basu gaisa da muskan ba ɗan baida lokaci."
"Wayarsa yacire yakira muskan, sun gaisa lpy yamata nasiha sosai kan xaman rayuwa da kuma kab karatunta, godiya tawa Dad sukayi sallama."
.
"FARIS @ 4:00pm daidai wannan lokacin suka rabu da faty, rabuwarma da kyar sukayi, sabida yana zaune hankalinsa na a kan giɗa yau yana son zuwa duba su mum."
"Motarsa yake tukawa a hankali cikin nutsuwa, amma kuma yanajin kamar yayi missing ɗin wani abu daban, duk da idan suna tare da faty yakan manta kowa da komai amma yau yana ɗan tunawa da wata ko wani abin mai muhimmaci a wajensa."
"Wayarsa ya ɗauko yana driving yana ɗan duddubawa can ya danna lambar baby boo."
"Wayar na Hannunta tana game yasoma ringing, ganin handsome ɗinta ke kira yasata ɗagawa da sauri tace Assalamua'alikum mijina abin alfaharina."
"wa'alaiki salam dafatan kin wuni lpy?
"Lpy mijina, ya aiki?
"Aiki alhmdullilah, ya karatu? da fatan kina kula da kanki? "
"Sosaima mijina, saidai zuciyata cike take da kewarka, i miss you my handsome pls kadawo gida mijina tafaɗa a sahagwaɓe."
.
"Wani yarrrrr yaji duk tsigan jikinsa ya tashi wani iri yaji, ɗan maganarda tayi a shagwaɓen duk yaji jikinsa yayi sanyi, wani irin feelings yasoma ji na fusgarsa."
"Uhmmmm baby boo zandawo ƙwannan karki Ji damuwa yafaɗa adan daɓurce, yakara da faɗin zankiraki anjima kinji."
"Toh mijina ka kula da kanka tamasa blowing kiss ta waya haɗe da hanging ɗin wayar, tana murmushin jin daɗi."
"Shikam duk ta rikitasa gashi ta kashe wayar, shima murmishin yayi yaji wani daɗi na shigarsa fiyeda in da faty yayi hira."
"Cike da jin daɗi ya isa gidan, amma yana karasawa text na faty ya shigomasa waya, yana dubawa yaga text ɗin kamar haka."
_*honey bayan tafiyarka yanxu Daddy'na yakefaɗamana tare suka dawo da Daddy'nka, Pls ka daure kasanardashi maganata da kai*_.
"yana gama karantawa yayi murmushi, ya fita cikin motar ya kullo, nufi cikin giɗa."
***
Suna zaune dukkansu a falon kasa suna ganin wani series film a zee world _king of heart_ da ka gansu zakasan suna jin daɗin kallon, ana cikin haka suka jiyo sallamar Faris."
"Assalamua'aikum"
"Wa'alaikum salam dukkansu suka amsa haɗe da basa izinin shigowa."
"Sgowa yayi fuskarsa ɗauke da murmushi, yakarasa har inda suke zaune, zama yayi ya kwashi gaisuwa, nan su fareeda ma suka gaida shi ya amsa fuskarsa a sake."
"Dad ashe ka dawo faris ne yayi tamvayar."
"Eh son ɗazu na dawo, mummy'nku take sanardani kaxo bayan tafiyana."
"Eh naxo yin wani aikin ne dama kai nake jiran zuwanka ma tuntuni."
nikuma faris? Dad yayi tambayar very exclaimed."
"Eh Dad."
"ALLAH daiyasa lpy kake nemana."
"Wata magana nakeso muyi ne shiyasa."
"TOH inajinka faris faɗa toh."
"Juyawa yayi ya kalli fareeda da humaira dake kallo abinsu, yace fareeda kutashi kubamu waje zamuyi magana da Dad."
"baki suka turo gaba suna gunaguni suka mike, harara humaira ta wurgamai itakuma fareeda baki ta murguɗamasa, duk ya gansu amma ya share kamar bai gansuba."
"Suna barin wajen ya juyo yace em..em...emm dama nace Dad sai kuma yayi shiru."
"Ido Dad da Mum suka xubamasa suna sauraronsa, shiiru kusan na 3mins sukayi duka, shi faris yana tunanin ta'ina xai soma faɗawa dad yaje nemasa auren faty, sukuma dad da mum daban abinda suke sakawa a ransu."
"Dad ya gusar da shirin nasu dacewa faris lpy kayi shiru? ko dai wani abinne ya faru tsakaninka da muskan? kayi magana kasamu a duhu."
.
"Jin maganar dad ne ya dawo dashi duniyar tunaninda yake, gaining courage yayi yasoma magana."
"Dama ba komai bane kuma muskan batayi wani abinba kawai Mum, Dad kunsan ina namiji allah ya halittamin auren mace 1,2,3,-4 shi........."
"DAKATA Mum tafaɗa cikim kakkawsar murya karka kuskura ina ruwanmu da wani 1,2,3,-4 dakake irgawa tsayama tukun ban fahimci mai kake nufi....."
"DAD Ne ya tari nunfashinta ta hanyar dakatarda maganarta, yace haba zainab kya barsa ya karasa maganarsa tukun kikasan mai zai ce haba zainab ki rinka baiwa kanki hutumana."
"TACE toh shikenan inajinsa yakarasa toh tafaɗa a kifule."
"Yawwa son inajika kacigaba."
"FARIS yace toh dad dama ba wani abin bane, nasan muna zaman lpy da muskan tana bayamin bukatuna da sauke dukkanin hakkina da ya rataya a kanta, tana farantamin kuma gsky ina alfahari da ita matsayin matarda na aura, banso ace zan iya rayuwa da wata bayan itaba amma kaddara ta riga fansa dad aure nake so nayi kuma fatima ce 'yar wajen abokinka ita nakeso kanemamin aurenta, bawai zanyi aure ɗan banason muskan ba ko kuma cin fuskarta a'a kawai dai cika sunnah xanyi, yana kawowa nan yayi shiru yana mai tsunkuyar da kansa."
"Ai kamar jira mum take ya gama ta amashesa tace lalle wuyarka yakai yanka nasan za'a rina wai anci zanen mahaukaciya, sabon salo gemu a kafaɗa, toh buɗe kunnuwarka da kyau kaji wlh middin ina raye bakai ba auren wannan 'yar iskan yarinya maras kunya kawai tun wuri ka janye wannan kaxamin batunka dan baxai taɓa yuwa ba kadai jini da kyau, tana kaiwa nan ta tashi fuuuuuuuu ta bar wajen tana binsa da wani mugun kallo da yasa cikinsa ɗuran ruwa sabida abinda ya gani cikin idon mahaifiyartasa."
"Mikewa dad yayi shima ya dafashi yace son kayi tunani idan ma baka hayyacinka kadawo tun wuri sabida nima ban goyi bayan aurenan ba, gajidai mai nace maka kuma idan dan wannan kakejirana toh gobe ka kama hanya kabar nijeriya ka koma london maganar nan ya mutu understand."
"NOOOOOOOOO yafaɗa da karfi this house is hell, why? dad nazata zaka goyi bayana but kaima kayi turining back to mie,pls dad ku barni nayi auri faty i so much love her."
"KA Mutu inji mum dake saukowa nace kama fita kabani waje i don't want to see this your useless face and that your stupid mouth talking here kafita kuma baza ka auretaba."
"Hanyan fita ta nunamasa, jiki sanyaye ya tashi ya kama hanyan fita har yakai bakin kofa Dad yace and gobe kabar nijeriya nace kadai jini da kyau.
"ko kulasu bai yiba yafita zuciyarsa namasa zafi zuciyan maza ya baci."
"Motarsa yashiga not minding da gate man din horn yake dannawa kamar zai pasa kunuwar 'yan gidan gateman na hangamemasa gate @360 ya ja motarsa."
"Mum rai bace ta wuce dakinta..........
Hakama Dad bayan yabi shima NASA ran s bace........
*****
"ɗaki Mum ta wuce rai bace, shima Dad biyota yayi."
"A bakin gado ya ganta zaune tayi tagumi ta tafi duniyar tunani, zuwa yayi yazauna kusa da ita yayimata side hug sannan ya kira sunarta ZAINAB."
"Na'am ta amsa sa amma bata ɗago ta kallesaba."
"Look at mie we need to talk huh! "
"Alhj ina jinka ta ɗan ɗagowa a karonnan."
"Kidaina ɗaga hankali kan abinda yaron nan yafaɗa bai isaba yayi kaɗan yace zaiyi wannan auren nasan matsalar ki muskan ce, toh ki kwantarda hankalinki ba'abinda zai faru da ita, ko kin manta nace itama ɗiyatace zan zamemata uwa kuma uba wannanfa alkawarine dana ɗauka kuma saina cika, ZAINAB idan harɗai ina nunfashi a doron kasa muskan bazata yaɓa yin kuka ba insha Allah Bazan bari FARIS ya sata bakin cikiba, wannan auren ban goyi bayansaba matata idan har hakan shine kwanciyar hankalinki da farincikinki kinji koh."
"Fuskarta sake kuma ɗauke da murmushin jindaɗin zancen mijinta tace na goɗe mijina a kullum ina alfahari da kai kasancewarka matsayin mijina uban 'ya'yana."
"Bakomai matata ina son ganinki cikin farinciki, kwanciyar hankalinki shine nawa."
"Peck ta kaimasa a cheek tace amma wani hanzari ba guduba nifa wannan al'amarin yaban mamaki."
"Wani al'amari kenan inji dad da faɗa."
"Gani nake kamar faris baya hayyacinsa anya kuwa ba wani abin a kasa."
"Kai ya jinjina maganar ki gsky ne nima haka nake gani sabida bantaɓa tunanin faris zai iya furta waɗannan maganganun ba musamman yadda nasan yakeson muska da alama akoi abu a kasa."
.
"tayani gani mijina nasanfa halin yaron nan kumafa dacan yarinyar na sonsa amma shi kullum cikin tsanarta yake, kai gsky da sake kasan mai hankali shiyake ganin ɗingishin ƙkwaɗo."
"gasky kam karmuyi sake yanxi yakikeganin za'ayi sabida nace masa yatafi london a gobe kina tunanin zaitafi kuwa?."
"Ina ai ban tunanin haka, wannan yarinyar fatima idonta a ɓuɗe suke nasan duk yadda za'ayi idan shi faris yaje yafaɗamata bamu yarda da zancenba, toh daga nan zatace zatayi wani abu akanmu kaga tunda dama gwanda mu mike tsaye, nafiloli zamu sake kan wanda muke a da sa'annan zamu sami malamai suyita saukar Qur'ani da yanka ana saɗaka koya kace.?"
"Excellent matata haka kawai zamuyi kuma muja shi faris jikinmu mununa mun yarda da auren kinga haka zaiyarda damu aikinmu zaitafi mai kyau."
"Haka za'ayi, abuna kuma biyu muskan zamanta can ita ɗaya kaga ba daɗi nace ko zata dawo itama sai amata nata neman tsarin a amata saukar al qur'anin itama."
Toh sai gobe zanwa su anwar magana su sata a jirgi saita dawo ko? "
"Eh haka za'ayi , nan suka sauya hiransu da tasu salon soyayyar."
***
Allah ne kaɗai yakaisa giɗa sabida wani irin tukinda yake, koda yashiga gida da gate man ya hangamemasa gate ya shige @360 parking ɗinma yayisane kawai sabida akarkace yayi, rai ɓace yafita yanufi cikin gida, ɗakinsa direct yanufa, kayan jikinsa ya rage yashige toilet, shower yasakarwa kansa idonsa runtse yana cikin jacuzzi ruwa na sauka a dukkanin ilahirin jikinsa,yana jin daɗin ruwan, duk haushin su Dad yakeji kamar ya shakesu ya huta kawai haka yakeji a ransa yana ganin hakkan shizaifi samamasa farinciki a halin yanxu."
"Ya ɗau tsawon lokaci a haka kan yayi wanka yafito, ya shirya cikin kananan kaya, fitayayi bayan yazari key yaɗau mota ya fice,hanyan gidansu faty yaɗauka dancan kaɗai yakeji idan yaje zai ji sanyi cikin ransa."
"Ya isa gidan yasanar da faty ta shirya tasamesa kofan gidansu yanajiranta."
"Cikin shirin wata doguwar rigar material blue ta fito tana rankwasa tana yauki harta karasa wajensa."
"Shikam faris ganinta dayayi kawai ya nemi ɓacin ransa ya rasa sai ma murmushi dayake kamar bashibane wanda ya murtuke fuska ɗazu."
.
"Gaisawa sukayi data shiga motar,ya amsa yacemata fita zasuyi zuwa gari, tace ba matsala suje."
"Suna tfy suna hira abinsu anan ne ta tambayesa ko yasanar da Dad maganarsu yacemata eh yasanardashi yace daya kammala abinda yke zaisami daddy'nta suyi magana, farinciki tayi sosai harta kasa boyewa."
"shidai kallonta yake batasan karya yamataba, shikuma yama rasa dalilinsa na mata karya."
Da haka sukaje wajajen shakatawa dayawa sai dare sukadawo ya ajeta gidansu shima ya wuce gidansa.....
***
_*2 days later*_
Bayan kwana biyu Da maganarsu Dad kan ɗauko muskan da za'ayi, yasamu yakirasu Anwar yasanar dasu su sata d jirgi tadawo gida."
"Sunyi komai shida aliyu yadda Dad ya bukata sunsama mata viza,."
"FARIS kam tunranda su Dad sukaki amincewa su nemamasa auren faty yaɗaina zuwar musu gida ko kiransu a waya ya daina yi sam kuma su ko sunkira baya picking wai yana fushi dasu. kuji wani zancefa anan."
"Fanin su Dad ma dasuga abin na faris yayi kamari suka kyalesa sunsan baya hayyacinsa ne, kuma har yau su fareeda basuda masaniya kan abinda yake faruwa a gidan."
***
" Ranar Wata alhamis tana zaune a falo tayi tagumi tafi wata uwa duniya can tana tunani, ba komai take tunawa ba illah faris, ya canza kota kota gashi yaki yadawo, gashi kullum cikin kawomata korafi yake da zarar tace bayakiranta saiyace aikine yamasa yawa ita a gsky yanxu tasoma gajiya zuciryarta tasoma mata hasashe kan ba gasky faris ke faɗamata ba, takasa sakewa kwanan tana yawan yin mafarkai iri iri."
.
"Tana yawan ganin faris dawata mata fuskarta baki kirin gashitana neman halakasa,itakuma muskan duk lokacin ta dososu wani farin haskene ke bayyana kuma da zarar ta dososu ko wancan matar tayi niyan kashe faris ɗin idan wannan hasken muskan ya bayyana saita kasa yin komai."
"Toh fa muskan wannan abin shi kedamunta gashi takasa gane mai wannan mafarkin ke nufi, tana cikin wannan tunanin ne tajiyo sallamarsu Anwar, take ta komo hankalinta taɗan daidata nutsuwarta waje ɗaya ta amsa su haɗe da basu izinin shigowa."
"izini tabasu suka zauna, bayan sun gaisa, tawuce taɗaukomusu abin motsa baki, hannunta ɗauke da tire da jug saikuma kofuna da plate cike da snacks ta zo dashi, a gaban kowannensu ta ɗirarmasa kan wasu kananan stools tace dasu bismillah."
"Sai da suka ɗan taba abin da takawo musu tukun suka tamabayeta ya zaman kaɗaice? ya makaranta kuma? duk tace abgodewa Allah zaman kaɗaici kuma tana fama."
"Anwar yace faris ya makale acan yaki yadowo kuwa, sai Aliyu yace nimadai abinda nagani."
.
"Murmushi tayi tace zai dawo insha allah bada daɗewaba coz nasan yayi missing ɗina kamar yadda nima nayi missing ɗinsa kunga duk inda yake hankalinsa na gida na tabbata."
"Suma murmushin sukayi Aliyu yace toh sarauniyar iya magana da soyayya kyafaɗamana haka ai dama tunda kika kasance matar faris kam."
"Anwar ne ya amashesa da faɗin faɗi kanka tsaye abokina gori takemana da wayancewa."
"la muskan tafaɗa tana mai rufe fuskarta da hannu biyu alamar taji kunya tace nifa ba gori nakemuba."
"Toh muskan munji faɗar Anwar, yace dama gaidaki mukazo yi saikuma visa da muka tahomiki dashi inji Dad yace gobe zaki 9ja yana maganar ya ciro visa card ɗin yamikamata."
.
"full of suprise take kallon card ɗin a ranta tace 9ja Allah dai yasa lafiya ne, murmushi ta kakaro tace musu na gode insha Allah yau zan shirya."
"Toh suka amsata Aliyu yace gobe zamuzo mukaiki airpot insha Allah."
"Toh ba komai sai kunzo Allah ya kaimu."
"Ameen, muzamu wuce sukace da ita suna mikewa."
"Har bakin kofa tarakasu ,tamusu godiya yadawo ciki, tana sake sake cikin ranta, waya taɗauko takira fareeda kozata bata information amma kash wayar baya shiga haka ta gwaɗa na Dad shima, duk saida ta gwada wayar 'Yan gidan amma batasaminsu, hakura tayi kawai."
"Tashi tayi taje ɗaki tasoma haɗa kayayyakinta na tafiya duk wani abinda tasan zata nema tahaɗa su a babban troley'nta cip cip."
****
Washegari jumma'a kamar yadda su anwar sukace zasu zo ɗaukarta toh suncika alkawari sunzo sun ɗaukota sun kaita airpot."
"Kafin jirginsu yaɗaga saida suka kira Dad a Waya suka haɗashi da muskan sukayi magana."
_Readers karku manta duk wannan abinda ake faris baida masaniya akai_
"basuɗau lokaciba a maganar dadukayi da Dad wanda ni neerat banji abinda sukafaɗaba amma sai ganinta nayi tana murmushi alamar maganan da sukayi yamata daɗi kenan, wayar ta mikamusu lokacinda ake bukatar pasinja su shiga jirgi tamusu sallama tawuce abinta.."
"baifi 30mns ba jirginsu yaɗaga zuwa nijeriya."
.
FARIS zaune gaban kanin mahaifinsa Usman duk ya korowa kawunsa bayanin komai game da son auren faty daya ke son yi dakuma yadda suka kaya dasu , kawu usman yaji jawabansa yakuma tambayesa kan yana son karin auren dawata manufa koko matarsa ce tamasa wani abin?,Kamar yadda yafadawa Dad yanason karin auren ne sabida cika sunnah kuma yana sha'awan yin mata Biyu haka yadafadawa Shiva kawun. Kawu yace toh masha Allah idan dai dan wannan ne zaiyiwa Dad magana,gdy FARIS yashiga jerowa kawu yasan idan dai kawu yawa dad m.agana zai iya amincewa shiko idan akamai haka angama masa komai na Rayuwa.
Kawu yace gdy ya isa ai yiwa kaine kuma FARIS ai kai dana ne kaima karkaji komai kaji. Toh yace kawune ya umarcesa da yatashi yatafi shima zasa wani gun yanxu daganan yawuce wajen dad din."
'farinciki ne ko murna duk FARIS na ciki yana driving yana..murmushi harda bude wakar backstreet boys yana marming din wakarsu ta _I want it that way_ har ya isa gida."
"Faty da kawarta meemah yau sundau hanyar kauyen bebeji sabida itafa faty haka kawai take jin bata aminta da abinda FARIS ke fadamata game da maganar aurensuba gani take kamar karya yake mata idan yace wai aiki ne yawa dad yawa, shiyasa ta fadawa meemah su koma wajen boka share kukanka ko, zaisan *meke faruwa*(cute xarah ce )."
"sun shiga cikin jejin kamar yadda suka saba yau ko tsoro babu tattare da faty, karkashin bishiyan da yake bullowa suka tsaya take sukasoma babbako ashar masu zafi, wata irin iska ce ta kada tana juyawa boka na a samarta yana saukowa kasa take suka jiyo dariyar boka hahahaha yana wani mugun dariya inda iskar ta tsaya shikuma sai gashi zaune yana wannan muguwar dariyarsa hakora duk sun rine gasa baki so irritating idan kungansa fans.
"shegu, marasa imani, hatsababbu abinda boka kefadi kenan wasu faty."
"Sannunku dazuwa yanunamusu waje su zauna, ba musu suka zazzauna, boka yace."
"nasan zaku dawo basai kunfadi mai ke tafe dakuba nasani ansami matsala wajen iyayen yaron wancan karon bamusamu munyi aiki kansuba amma yanxu zamuyi, wata kwarya yaja yakawo gabansa cike da ruwa ya umarci faty da ta matso ba musu ta matso kamar yadda ya bukata wasu yarensa yasoma karantowa wadda ni neerat bansan mai yakefadaba tsiiiiii wasu kibiya biyu suka wuntsilo bakin kwarya atsorace faty ke gwalo idanu tana ganin abin al'ajabi, dariya boka ya bushe da ita yace."
"kinga wannan yanunamata cikin kwaryan waye wannan ya tambaya yana nunamata cikin kwaryan?.
"faty da tacika da mamaki tace."wannan ai mummy ce mahafiyar FARIS tafada maganar na rawa abakinta."
"wannan fa yanunamata dayan."
"Dad ne ai tafada still getting suprise."
"toh yayi kyau inji boka sa'anan yace wadannan suke kawomuku cikasss sabida a halin yanxu sun hana dansu auren ki amma yanxu zanyi maganunsu zuba ido ki gani."
"kibiyar da ya ajiyesu guda biyun yadaga yajefa cikin ruwan take dayan ya sami dad a bakin zuciyarsa dayan kuma yasami mum gefen zuciyarta amma basu kula da hakanba boka yace ."
"kinga wadannan kibiyoyin dana harba musu yasamesu toh aiki yayi yanxu bazasu bijirewa auren kuba tashi ki tafi komai yayi daidai hahhhhhh yasake barkewa da dariya."
"kudi masu yawa ta ajiyemasa cikin kwaryansa ta taso suka kama hanyan fita daga jejin da meemah."
"saida suka fita cikin daji suka shiga cikin mota sun soma shiga gari tukun faty tasoma baywa meemah lbrn abinda ya wakana."
**
Dad, mum zaune a falo tare dasu fareeda sun shirya tsabb zasu dauko MUSKAN takusa sauka, suna cikin hirane lokacinda boka ya harbo kibiyoyin kirjinsa ya rike a daidai lokacinda kibiyar ta samesa, mum madai taji abu ya dan tabata amma ba kamar ta dad ba."
"ruwa dad yace humaira ta mikomasa a firij mai sanyi, saida yasha wannan ruwan yadanjin dama -dama yace su taso su tafi batare da yafadamusu abinda yaji bakin zuciyarsa."
"isarsu airport yayi daidai da saukar jirgin su MUSKAN, lokacinda ta fita a jirgin ido tarinka warowa tana dudduba su mum, can nesa ta hangosu lokacin suma sun hangota da gudu ta nufesu hugging din mum tayi tace I miss you so much my mum, I miss you to daughter mum tafada itama, murmushi dad yayi wajen dad ta koma ta kama hannunsa tace i also miss you dad, kanta yashafa yace my daughter I miss you too, ke baki ganmu bane fareeda tafada tana wurgomata harara cikin wasa, sorry my sisters tamatso wajensu hannayensu takamo dukka tace."
"You know i love you all babes kawai ganin dad da mum ne yasa nayi mantuwa ban fara hogging dinkuba, kun hakura ammatas? Murmushi sukayi tare da hugging dinta suna dariya duka."
"da kyar Dad yasasu suka shiga mota, suka kama hanyan gida."
"da isarsu.MUSKAN tawuce daki tawatsa ruwa sukuma sukaje shiryomusu abinci, bata dau lokaciba ta shirya tasamesu a falo dukkansu sukaci abincin suna hira harsuka kammala, koda suka kammala kamar rufe bakinsu dad akayi(kodashike ai rufewan akayi ) ko maganarda sukayi. Niyan sanar da ita sunkasa yi hira kawai sukayi tayi."
"sai kusan bayan sallah'n magriba kawu usman yazo shi gidansu FARIS ya tarar da Dad a gida da fara'arsu suka tarbesa, bayan sun gaggaisa hardasu MUSKAN yake tambaya dama tare suke da FARIS ne? Mum ce tace dashi ai yau tazota ita, yace toh yana da kyau, cewa su MUSKAN yayi subasu waje zasuyi magana da dad, ba musu suka mimmike suka nufi nasu dakin."
"bayan tafiyarsu ne kawu usman ya dubi yayansa da girma ya soma koramasa bayanin yadda sukayi da FARIS yakuma rokarwa FARIS dad yaje sunemasa auren faty tunda sunnah zai cika."
"Ajiyan zuciya dad ya sauke yace ba matsala gobe ma kuwa zasu yanxu zai kira daddyn faty yasanar dashi batun."
"mum dai najinsu amma itama bata jin zata iya hanasu auren, amma can kasar zuciyarta kuma tanajin zafin faruwar haka."
"Gdy kawu usman yawa dad hade da musu sallama ya tafi."
"Cikin mum da dad ba wanda ya yi yunkurin tambayan wani mai dalilin sa na barin ayi auren shiru kawai sukayi duka."
"da kyar dad yayi gaining courage ya dau waya ya kira daddyn faty yasanar dashi abinda yakeso, daddyn faty dayafi kowa murna naganin zai aurar da diyarsa yace ba matsla sai sunzo, nan sukayi sallama."
"kawu usman yakira faris ya fadamasa yadda sukayi da dad harma da amincewarsa wow! FARIS yakasa boye farincikinsa sai gdy yake zubawa kawu, kawu yace dashi yaje yasami dad yamasa gdy shima toh yace dashi."
"suna gama waya da kawu yakira dad yanemin yafiyarsa hade damasa gdy yace zai shigo gobe insha Allah, dad yasanar dashi MUSKAN tama zo yasa su anwar susata jirgi tazo, FARIS yace ba komai sai ya shigo kawai."
"lokacinda ya kira faty dan yasanar da ita already daddynta ya sanar da ita amma tayi birisss ta saurari shi FARIS din daya fadamata tayita murna kamar da gaske harda kukan munafunci, shikam dariyama ta basa da tayi kukan, hira suka sha ta love kamar su cinye kansu ko suzama tsuntsu su ga junansu. "
**
Washegari kamar yadda su dad suka fada haka akayi sunje sun nemawa FARIS auren faty an basu, take suka bada sadakinta naira dubu dari , akasa Rana sati daya mai zuwa za'a daura auren."
"Alokacinda aka sanar da FARIS wane yasa ruwa akasa yasha dan murna kasa boyewa yayi a fuskarsa."
"yaje sa gidansu bayan sun gaggaisa da mahaifansa da yan uwansa ya mike yace bara yaje su gaisa da MUSKAN, dad yace idan kaje kasanar da ita zance amma kamata yadda zata fahimta kaji son, FARIS yace insha Allah, yasa kai yawuce a dakinsu fareeda ya sameta zaune tana game a wayarta."
"sallama yayi, ta amsasa ba tare da ta dago kallesaba, shikuma bai kulataba dan yasan fushi take dashi waje yasamu ya zauna kusa da ita jikinsu na gogar juna suna iya jiyo numfashin junansu ga Sansanyan kamshin turarensu da ya hade a dakin, kansa ya kwantar bisa kafadarta a hankali yamata whispering (rad'a) a kunnenta wanda ni dai neerat banji mai yaceba, haryanxu ignoring dinsa tayi, dayaga da gaske take yasa sa saukowa har kasa ya kama hannayenta yace."
"Am sorry baby boo i know you have the right to ignore me but just know d fact that I so much love and miss you too as you did, kiyi hakuri gani gabanki ina mai neman yafiyarki matata, would you forgive me yatambaya yana kanne mata ido daya."
"she couldn't stand anymore denying it she miss him, all she can is that let her make him understand his fault but she loves him so much, baki ta murgud'a masa ta dauke kai daga ganinsa "
"Dariyane yaso kwace masa amma ya danne yace plss baby boo, har yanxu she's not ready to talk to him, FARIS fa yaga idan ba using da love styles dinsa yayiba he could not get his baby boo bak, dan haka ya mike kamar fita zai yi ai bata ankareba taji saukar bakinsa a nata kissing dinta yashiga yi romantically yana sarrafata yadda yakeso duk iya kokarinta tayi ignoring abinda yake mata but takasa, itama shahada tayi kawai tashiga..maidamasa martani, sun ma manta inda suke harsaida FARIS yacimma burinsa suka fada duniyar ma'aurata.
"Alokacinda ya gamsu, ya dawo hankalinsa yace am sorry i don't mean to do that kinji yi hakuri my baby boo, murmushi tayimasa kawai, umurtanta yayi da su yi wankan tsarki akoi maganar da zaiyi da ita, ba musu ta biyemasa shida kansa ya sabeta yakaita toilet wankan ma shiyamata yawa kansa, koda suka fito saida ya tabbata ta shirya yaja hannunta suka nufi part dinsa ta kofan baya sukabi sukaje su."
"bayan ya canza kaya shima yadawo inda take yayi yazauna kusa da ita baby boo ya kira sunarta."
"Na'am ta amsa sa cikin sanyin muryanta."
.
"magana yasoma mata kamar haka, kinsan ina sonki kuma har cikin kundun zuciyata, kuma akidayaushe burin na bai wuci na faranta miki na ganninki cikin jindadi da Kwanciyar hankakiba, I never wish naga ranki a bace koba kya cikin kwaciyar hankali, so dayawa nakan cemiki ke kadai zuciyata ta aminta dake kuma ke kadai nake son rayuwa da ke karkashin inuwar aure daya kuma ki kasance uwar 'ya'ya na you know it right that bantaba jin son wata diya mace cikin zuciyata idan ba keba banida burin naga ina rayuwa da wata idan ba keba, kinzama *jinin jikina* zuciyata da ruhina, numfashi yaja yayi shiru daya kawo nan yana mai jin tausayin baby boo baisan yadda zai sanar da ita ba OMG! ya furta cikin ransa how will i tell her this, how will I convince her, how will she know that wat am capable of doing is not intentionally gosh yadafe kansa yace c'mon be strong enough oya FARIS gain courage huh! Duk maganar nan a ransa yake shi kadai, iska ya furzar a bakinsa mai zafi hade da daci."
"musfar i don't understand what you are saying go straight to the point and said it clearly so that I will understand MUSKAN ce tayi wannan maganar."
"oh baby listen to what i will say and just know is not intentionally huh!."
"yeah ok all ears musfar inji MUSKAN."
"uhmm em...emm gaining courage yayi yace dama aure nake so nakar... Makalewa maganarsa tayi sakamakon ganin MUSKAN ta mike a guje tayi hanyan waje da gudu."
"MUSKAN! MUSKAN!! MUSKAN!!! FARIS ne ke kiranta yana binta amma ina tuni ta fice daga part dinsa, da gudu taxo tawucesu mum zaune a falo, suna ganin ta tawuce suma suka rufomata baya, itakuma tana fadawa dakin ta banko kofar da karfi ghamb! Ta fada gado tana rusa kuka mai tsuma zuciya."
"d'akin suka shiga dukkansu harma dashi uban gayyan duka, a kid'ime mum tasoma tambayarta lpia? Tambayoyi tarinka jeromata amma kodaya bata sami amsar daga bakin MUSKAN ba a dole suka koma kan shi FARIS da tambayar nan ya sanar dasu abinda ya wakana tsakaninsa da MUSKAN, damn it! Mum ta furta you see huh! Now get out of here ta umarcesa dayabar dakin badan yasoba yafita amma yaso ace ya sami ya lallashi baby boo."
"fareeda, humaira, totally speechless suka tsaya baki sake suna ganin, da jin ikon Allah yanxu Ya FARIS dama abinda yake shiryawa no wonder amma koma wacece zai aura zataci ubanta kwafa sukayi duka, Dad yace su fita zaiyi magana da MUSKAN fita sukayi ransu duk a dagule suka bar mum da Dad."
"d'ago MUSKAN mum tayi daga kwanciyar tazaunar da ita tana mai fuskantarta zuciyarta cike da tausayin 'Yar tata, haka shima Dad,."
"Da kyar suka sami karfin guiwa suka soma mata da nasihohin suka sanar da ita yin wannan auren shine mafita daya garesu idan ba hakaba zata iya sa mijinta yasoma bibiyar matan banza idan ta hanasa auren yin haka kuma sam ba yida amfani Dan da kishiyar waje gomma ta gida, da ire -iren wadannan kalaman nasu da nasihanda sukamata hade da kalamai masu taushi da zagi dasukayi amfani dasu sukasamu suka shawo kanta ta fahimcesu hade da rage damuwa , dan sun nunamata itace tasu suna sonta kuma baxasutaba yarjewa FARIS ya musguna ko wulakanta ta sabida yayi amaryaba, duk da abune mai wuya gareta Dan mata akoi kishi mussaman idan akace kishiya za'amusu toh ita MUSKAN kishin mai zafine sabida jitake kamar mutuwa zatayi barinma dataji wacce FARIS zai aura wayyo tarasa inda zata sa kanta if only zata iya bijirewa maganarsu Dad da tayi hakan amma yazatayi da kauna da hallacin da sukamata a rayuwa hakika idan ta bijirewa maganarsu tazama butulu."
"saida suka tabbatar da tadan sami nutsuwa tukun sukamata saida safe suka tafi nasu dakin."
"ka.mar jira su fareeda suke su mum su fita suka fada dakin, tambayar.MUSKAN suka soma wacece FARIS zai aura, tana a kwance ko kallonsu batayiba tace dasu FATY, what! Suka hada baki wajen fada both fareeda and humaira, faty fa kikace lalle biri yayi kama da mutum but ya akayi su mum suka yarda da hakan no fareeda that girl is up to somthn bahaka su dad yarda kuna idon a tsatsaye she is a witch, an evil, monster zaginta fareeda da humaira sukayi tayi harsaida suka gaji dan kansu suka daina amma sun dau alkawarin sai tagane kurenta dasu take zance."
"FARIS kam duk yarasa mai yakemasa dadi duk lissafinsa ya dagule haka ya kwanta da tunanin abin yi."
.
_ranar yadda sukaga dare haka suka ga rana MUSKAN nacan takasa bacci kwana kuka tayi tajin zafin mijinta zai kasance karkashin inuwar aure da wata wayyo taci kuka ta koshi, FARIS ma kusan shima kwana zaune yayi dan zuciyarsa ba dadi sam yake ji, su mum ma haka bangarensu, haka su fareeda duk haushi ya cikasu da sunada yadda zasuyi apasa aurenan da sunyi, Amarya faty kuma cikin jin dadi da farinciki ta kwana Allah Allah take gari ya waye tasamu tasoma preparation danji take kamar sati dayan yamata yawa bazai Zo ba take ji_
.
Kwanaki sunata shudewa hakama ranaku abubuwa da dama sun faru cikin wadannan kwanakin har zuwa yanxu da ake gobe daurin auren FARIS da faty, duk iya kokarin MUSKAN na ganin ta had'iye mai ke damunta takasa kullum cikin kuka take dama -dama ma dasu fareeda ke dan debemata kewa suna tayata hira da k'wantar mata hankali da kalamai masu taushi, ba a bar su mum da dad a baya ba awajen kula da farantawa MUSKAN rai, tunda incident d'innan yafaru tsakanin MUSKAN da FARIS batasake kulasaba, duk hanyanda zata hadasu kauracewa take haka da zarar yashiga d'aki ta tabba shi dinne zata kwanta kamar mai bacci haka zai kare wa kyak'yawan fuskarta da jikinta kallo wani sa'in ya bata peck (light kiss )a kumatu ko a lip ko ya gyramata kwanciya yatafi."
"Su faty amarya anyi events kala -kala na keche raini akayi duk event din ta hade da ita da angonta, ta gaiyato kawayenta daga kasashe daban -daban kuma duk yan duniya ne, haka shima FARIS ya gayyato abokansa amma basukai na faty yawa ciki harda su Anwar da Aliyu wanda da kyar yasamu suka yarda zuwa auren dan su afad'arsu suna yin MUSKAN ne ba faty ba."
"events sunyi ba karya saidai dangin FARIS kodaya ba wanda ya hallaci event din kama daga mum, MUSKAN su fareeda da yan uwa sabida duk cikinsu ba wanda yake murna da wanga auren."
"sanin ba wanda zai kulasa yasa bai ma yimusu maganar zuwaba, faty kam taji dadin rashin zuwan nasu ma hakkan shi Yafimata alheri a ganinta."
"A gidanan 9ja zasu xauna FARIS yasake gina tangamemen gida tsarin gidan hak na turawa sabida mr fauzy ne yayi zanen gidan tsaya fadin tsaruwan gidan da girmansa bata lokacine amma gidan yakai gida kowacce mace da part dinta kuma gidan upstair ne, a nan nijeriya zasu tare da zama saidai shi FARIS idan yagama cin amarci zai koma bakin aiki ansamowa MUSKAN transfer daga can tadawo da karatu Nile University dake abuja fadar Dad abarta anan sabida zata fi samin nutsuwa."
"Yau jumma'a misalin karfe 2:00pm aka daura auren faty da FARIS akan sadaki naira dubu dari auren da manya -manyan yan siyasa da kasuwa suka hallata sai dai ko kotan mutannenda suka hallacin daurin auren MUSKAN faty bata samuba."
"Andaura aure lafiya lau ango sai washe hakora yake wani dadi yake ji wanda shi kansa baisan na meyeba, abokansa sai faman tsokanansa suke da yimasa tsiya."
"A cikin guest house na daddy akayi reception na maza."
"lokacinda MUSKAN taji an daura auren FARIS wani irin kukan bakin ciki ta rushe dashi duk yan uwa sunyita rarashinta da kyar ta tsaida kukan amma can cikin zuciyarta *Hawayen masoyi* (sis rabi'at sk mash &Mr smile ) shike zuba daga idanunta."
"Wow! Amarya faty basai na tsaya fad'a muku yadda zata kasanceba danyin haka bata lkc ne amma baki haryakasa rufewa dan murna ko kunya bataji yadda take abu kamar ba amarya bane."
"Da dare andauki amarya aka kaita gidan mijinta dake ashokoro, yadda part nata ya hadu hmmmm ba karya komai nata ja da baki kamadaga kushin, kayan kitchen, pent ds."
"lokacinda kowa ya watse aka barta da kawayenta nan suka bude babin hira harda ita kamar ba itaceba amaryan sabida lullubinta ta yane tazauna acikinsu sunta shan hira kuma duk akan zaman da zatayi da MUSKAN suke munafunci iri -iri da abuba da dama suke kunsawa faty akai yadda zata maida MUSKAN mowa wajen FARIS suke fad'amata sai babbake dariya suke kamar gidan rawa haka gidan ya koma."
"kafin FARIS yatafi wajen amaryansa dad yace yabiya yadau MUSKAN itama yau zata koma gida kuma yahad'ata da humaira sutafi tare sabida zaman kad'aici taji dad'in hakan dukda bason komawa takeba."
"An ajiyesu ansake musu nasiha kamar sabon auren Dad yace yamasan MUSKAN batada matsala saidai kai FARIS ka kula kazama adali mai adalci tsakanin matanka, ire -ire wadannan nasihan yarinka masa, saida ya tabbata yamasa nasiha sosai yabasu izinin tafiya,yabawa MUSKAN key mota sabuwa pill kirar KIA Yacenatane kyauta yabata harda kuka dan murna tayitamasa gdy, ba'abar mum abayaba itama tayimusu nata nasihan ankai ruwa tukun akaraba MUSKAN da mum da fareeda tana matsar kwalla suka kama hanya taki zama a gaba a bayan mota tazauna tare da humaira."
"kamar FARIS yasan *bad'akala* (kwaishe) da ake a gidansa baiyi gigin gayyatan abokai su rakasaba daga shi MUSKAN da humaira kadai suka hanyan gidansa."
"lokacinda suka isa gidan tundaga waje har suka doshi falon suna jiyo muryansu, bangaren MUSKAN yanunawa humaira yace taje ta tajirasu itakuma MUSKAN babban falon gidan dake kasa yanuna mata yace tajirasa yana zuwa ba musu duk suka bi umarnin sa."
"A lokacinda ya isa kofan d'akin faty kamar kunnensa ya fashe dan yadda suke ihu suna babbake dariya, rai yahada fuskarsa a murtuke ya bankaje kofar, a rayuwa ba abinda FARIS ya tsana kamar hayaniya, ido curu -curu suka a lokacinda suka hango FARIS ko wacce tasoma tattara kwarmatsonta suna shirin barin gidan, angrily yace faty tasamesa a falon kasa bai jira mai zataceba yajuya yabarta a d'akin, mchwww! Duk sukaja tsaki itakuma tabi mijinta, duk fita sukayi kowa tayi gidan ubanta."
"Duk ya tarasu a falon tunda faty tashigo taga MUSKAN tasoma wani shu'umin murumushi tana wani rankwasa da juya ido,zama tayi kusa dashi jikin FARIS ta shige da gangan dan ta bakantawa MUSKAN rai amma ko kallon inda suke MUSKAN batayi, shikuma tunda faty ta shige jikinsa yaji wani rin yarrrrr a jikinsa gawani dan iskan kamshin turare dayake fitadaga jikinta rikitasa take yanemi nutsuwarsa yarasa da kyar ya daidaita yasoma musu nasiha kamar yadda addinin islama ta tadana a gurguje yasamu ya kammala bayan yace da zarar yagama sati daya a d'akin faty girki zai koma 2-2days, ba abinda MUSKAN tace dasu haryagama yatambayeta ko tana da wani abin fada tace babu, yace toh ta wuce d'akinta saida safe, baby mujemana faty tace dashi ok toh haka tana kallonsu suka wuce faty rungume dashi, dan bakin ciki dayawa MUSKAN yawa kasa kuka tayi kawai murmushin takaici tayi ta wuce nata part din."
"wow! Part na MUSKAN yaci uban na faty nesa ba kusaba duk da iyayen faty sun narka arziki amma bai kai wanda aka narkawa MUSKAN ba ita kallon nata komai ligh purple da pink falo da kitchen d'akuna kuma Golden haka babban royal bed dinta na duka dakunan side dinta golden ne komai nata yayi wanne yar wata sarki ko shugaban kasa haka dakinta yake, ta sami humaira harta sauya kaya zuwa na bacci itama haka ta sauya ta dauro alwala tazo tayita nafiloli, saida ta idar suka soma dan taba hira da humaira ko abinda yafaru bata fadawa humaira bacci tasoma ji tacewa humaira su kwanta dan gobe zasu makaranta kasancewar itama humaira a nile University tuke karantu, kuma ita MUSKAN a goben zata fara fita School din."
"Amarya da ango kam saidai muce sam barka sabida suna shiga d'aki ba kunya faty tasoma romancing din FARIS abunka da mai nema tuni ya biyemata da kyar yasasu sukayi sallah'n raka biyu da ya wajaba nan ma ita ta nemi yahada kwanciya da ita."
.
_waiyazibullah ya Allah ka tsaremu daga irin halin mata kamarsu faty, ace anyi mace ba kamun kai ba aji, ko kunya, yaku yan mata da manya mata mu na lura muzama daya daga cikin matan da Allah s.w.t yake suffantasu da matan hurul ayn, mukance masu alkunya da kamun kai..Allah yasa mudace AMIN YA RABBI_
"Ango FARIS fa an angwance duk da ba a Virgin yasami faty ba but bayida nacewa sabida yadda tsafi ke dako dashi."
"saida suka sami nutsuwa bayan sundibi kusan tsawon awa 2-3 suna abu daya, wanka ma duk tare sukayi suna zuba love abinsu."
"ko da suka gama duk abinda zasuyi suka nemi lafiyar gado."
Su amarsu ta ango saidai muce asuba ta gari............
**
Washegari tun sallah'n asuba da sukayi MUSKAN batasake komawa kwanciyaba azkar tarinka yi harsaida taga gari yadanyi haske nan dinma ba baccin ta komaba kitchen ta nufa dake bangarenta tasoma had'a breakfast na gidan gaba daya, Irish potatoes ta fere ta soya sa da eggs dinta ga peppers soup nata na chicken sai shayinta dayasha kayan kamshi ta hada ta juyewa su FARIS a warmers tazuba nasu da humaira takaimusu dining suma FARIS takaimusu part din faty a bude ta tara suma a dining ta ajiyemusu tabar dakinsu."
"data koma tahada komai na kitchen datayi amfani dashi ta wanke tasss tayi mopping haka falonta ta kunna turaren wuta na yan Maiduguri dana kaimata gudumawa duk gidan ya bulbule da kamshi, ganin har kusan 8:00 yasa bata koma bacciba dan dama 9:00takeda lectures, d'aki tawuce tayi wanka data fitone ta tada humaira tace tayi wanka itama, humaira da bacci bai ishetaba ta mike a wahale tayi wanka tafito tasami MUSKAN ta shirya tsabb cikin wata super lemon green dinki zamani akawa rigar tadaura zaninta kwass abinta tasha ado kamar wata amarya sai shining take like a star, baki wangale humaira take gininta tace mata kai aunty kinyi kyau, na gode tace da ita kiyi maza kishirya yanxu kusameni a falo toh ta bita dashi kawai, Itama atamfa tasa amma ita d'inki riga da skirt tayi kyau itama, a falo ta sami MUSKAN, dining MUSKAN taja suje suci abinci full of surprise tace MUSKAN yaushe kika tashi har kinyi breakfast and all those work, hmmm kekike bacci ni nagama komai nasu FARIS ma na kaimu-humaira bata bari ta karasa maganarba tace kardai kucemin ke kikamusu girki? Of course yes ni namusu ta bata amsa, you are stupid wlh yanxu har girki zaki musu Allah kinbatan rai nikam, sorry lil sis amma kinsan hakkina ne na musu and kinga ni fa duk abinda suke kansu sukewa kuma fadar ubangiji da nasu mum nake bi if not am not gonna do it babe."
"Toh naji yanxu muci abincin mutafi school karmuyi missing lectures ko, toh MUSKAN tace bayan ta zuzzubamusu abincin da tea suka soma ci.,"
"inless than 20mins suka kammala komai suka fito a sabuwar motanta da dad ya siyomta KIA tajazu suka tafi school kota kansu FARIS basubiba."
"toh su amarya kuma sai 11:00suka tashi wanka suka chaba ita da angonta dasuka fito sukaga warmers a kan dining nan suka baje suka kwashi girki abinsu."
"koda suka gama garden na gidan suka fita shan iska suna zuba love wane su cinye junansu ko fita yau FARIS baida niyan yi idan baki sunzoma wajen amarya ma hira ka'dan suke taba ta sulale wajen mijinta ."
"FARIS baidamu daya duba MUSKAN ba kuma baiji motsintaba koda yamma dasuka dawo basu haduba suma basu nemesaba, nan ma indomie dinsu suka dafa da eggs sukayi pilling suka ci nayanxu kam basu kaiwa su faty ba.
•••••
Lives moved on haka rauywarsu ta kasance har 1week koda FARIS zai koma d'akin MUSKAN ranar ma faty bata kyalesaba har saida yabiya mata buka tarta taga ta mantar dashi MUSKAN har tasake jansa suka kwana tare, kullum haka take da zarar randa tasan girkin MUSKAN ne saitayi abinda FARIS bazasa wajen MUSKAN ba."
"ita dai MUSKAN na gani ikon Allah amma ko ajikinta bata taba nunawa koda a fuskaba and bata sakewa humaira ta gane komai dake gudana, kuma ko mum takira ta tambayeta ya zamansu? da Matsala? Duk saidai tace masha Allah ba komai shiyasa mum ke kara son MUSKAN cikin ranta."
"duk kwanakinda suke shudewa FARIS basu cika haduwa da MUSKAN ba watarana su hadu yaxo shiga gida tana fita ko yana fita tana shiga, girkima yanxu taciresu kowa shi ke nasa, karatu ya kankama yanxu suna second semester exams zasu fara duk hankalin MUSKAN na akan karatunta dad'inta ma daya course dinsu daya da humaira kuma aji daya suke shiyasa kullum zaka gansu da laptop ko test books agabansu suna karatu."
"duk iya zamansu ba wanda ke zuwar musu gida sai zaryan kawayen faty dasuka maida gidan kamar gidan ubansu, kullum suna cikin zuwa gidan."
"Abun FARIS fa sai addu'a sabida aikin ma yanxu saida suka yomasa transfer yadawo gidan Nigeria da aikin."
Yanxu almost getting a month da aurensu faty while MUSKAN kuma tana 3month 2weeks da auren FARIS."
"yau kamar kullum ba school humaira tafita unguwa while faty itama taje gidan wata kawarta, MUSKAN kadaice a gida tana zaune batama jin dadi 2days kasala da yawan bacci sun mata yawa ga yawan kwadayi tarasa mai yasameta tana cin gautanema yanxu dan tashin zuciyar da yake damunta karar tsayuwar mota taji cikin ranta tace Allah yasa humaira ce dan ni nagaji dazama ni daya wlh."
"FARIS ne yashigo bayan ya Parker motarsa ya shiga cikin gida yunwa yakeji yaje part na faty bata nan duk iya bincike yayi amma ba abinci a part dinta, haushi duk ya cikasa har ya zauna komai ya tuna oho ya mike yayi hanyar dakin MUSKAN da sallamarsa yashiga ta amsa masa amma bata waiwayi inda yakeba."
"gefenta yaje yasamu yazauna yace MUSK- bai karasa tamike a guje tayi hanyan kitchen sink tasamu tasoma kwarara amai wane hanjinta zasu fito waje kamshin turarensa kadai dataji shi yasata amai."
"A guje yabiyota kitchen din bayanta yaje yatsaya duk ya kidime yanajin yadda take amai saiji yayi tausayinta ya darsu cikin ransa he cannot stand any more zuwa yayi, yayi hugging dinta yana bubbuga bayanta yanata fad'in sorry har saida tagama ta kuskure bakinta tana juyawa ta kwace jikinta daga hugging din da yamata binta yasoma dayaga tana tafiya yana kiranta amma ita ko juyawa batayi ba harta kai falo ta zauna.
"shima biyota yayi yasoma tambayarta bata da lapiyane taki amsasa dayaga haka yace ta tashi suje asibiti, tabb nan fa tace ba inda zata, dayaga da gaske take, yabata rai shima forcefully yasoma janta bayan yaja hijabinta dake kan kujera tana tirjewa yana janta saida yadakamata wani irin tsawa daya tsoratata ba shiri tayi tsitt haryasa a mota ya kama hanyar asibiti."
"suna isa asibiti basu wani sha wuyaba suka sami ganin Doctor kasancewar FARIS yasansa, Doctor yama MUSKAN wasu yan tambayoyi duk ta amsamasa nan yasa wata nurse ta karbi fitsarinta a gwada."
"in less than 30mins nurse din tadawo da result na fisarin, Doctor yana gani yakaranta yana ganawa yace wa FARIS congratulations matarka na dauke da juna biyu na wata daya da yan kwanaki."
"FARIS daya tashi daga zaunenda yake yayi hugging na MUSKAN yana bata peck ta ko ina yama manta asibiti suke saida tadan cijesa a kunne yadawo hankalinsa, gdy da kyauta ya ma Doctor da nurse din, bayan doctor yakaranta musu jawabai da ya kamata suka kama hanya, yama rasa idanda xaisa kansa duk da FARIS ba a hankalinsa yakeba but yana son baby musamman daga MUSKAN wacce takasance *JININ JIKINA* he can't deny it he loves it and yakasa boyewa."
"tun a hanya yasoma sayesayen kayan kolama sabida Doctor yafadamasa mata masu ciki na kwadayi itadai MUSKAN ido take binsa dashi kawai bata magana."
"kafin su karasa gida saida yayi siyesiye dayawa, suna Parker mota faty na shigowa gidan itama ganinsu tare kuma FARIS yazaga yana budewa MUSKAN kofa yasa faty fitowa a harzuge tayo wajensu da saurinta amma ina kafin takarasa MUSKAN takama hanyan shiga cikin gida FARIS kadai ta tarar ko sannu dazuwa babu tace baby daga ina?."
"Daga asibiti yabata amsa."
"doing what at hospital? Tasake tambaya "
"MUSKAN ce ba lafiya nakaita ganin Doctor."
"And sukace mai yake damunta."
"Enough! Ya kina ta min tambaya kamar wacce take a lawyer."
"yes dole na tambaya i wanna know what happen to her."
"okay fine kinaso kiji ko toh ciki ne da ita she's taking my baby."
"WHAT! Tafada da kakkausar murya CIKI Noooooo bazai yuba I have to do something bazata zauna da cikin nan ba da gudu tadau motarta ta fita a gidan @360."
"shikam FARIS ko kallonta baiyiba yasa kai ya shige cikin gidan ".
0 comments:
Post a Comment