RAHAMA DADDY'S GIRL Page 41-50
.
Da shigowar ta dakin ta ta wuce da yake abinka da mai karamin ciki ga kuma gajiya sai bacci, Ba ita ta tashi ba sai k'arfe 7 na safe, Fajir yaji shigowan ta yayi tsammanin ta shigo dakin amma yaji shiru hakan ya tabbatar masa da bacci tayi, Da safe kuwa koda ta shigo yana wanka dan haka bakin kofar toilet din taje, "Na tafi!" Haka kawai tace ta fucewar ta, Mamaki ya shiga sam Salma bata dauke shi da muhimmancin ba, ita dai ta iya kishin hauka amma bata iya tsare nata hakkoki ba, jiya bata san ya ya kwana ba, bata san ya yawuni ba haka ma yau, hakan ya k'ara Kona ransa. Haka suka kwana biyu curr ita Salma fushi take dashi akan ya hanata Mota ya bawa Rahma a cewar ta, Shikuwa al,amarin ta ya matuk'ar daure masa kai, taja mai ciwo ta dau fushi kuma dashi, Duk wata wahala tai Rahma ce kanyi ta, Abinci da zaici ma itace, ruwan wankan sa wanda Salma bata taba hada mishi ruwa wanka ba, gyaran dakin sa da komai, Rahma kuwa tagama fadawa kogin son Fajir, wanda take tausaya ma kanta wani sa'in sai taji kamar zuciyar ta zata buga. Wannan kenan. Kamar kullun yau ma a falo yake zaune Rahma na bare masa lemo, Salma ce ta shigo tana zuwa ta fad'a jikin Fajir, "Honey, Baby yana son lemun," Ta fada tare da nuna cikin ta, Bakin ta ta bude ya saka mata wanda ya fara sha ta lakume tare da kwanta wa ajikin sa, Da sauri _sauri gaban Daddy's girl ya fara bugawa, tsantsar mamaki bayyane a fuskar ta yaushe suka shirya?????? Kina bacci! Abin da na fad'a kenan saidai ashe bata jini ba.....!
.
Dama ita suka maida 'yar tasha? Lallai kiyayyar da Fajir yake mata ba karama bace, Duk wahalar nan da take ashe ya shirya da matar sa? Lallai kuwa ya cuceta shi sam baisan zuciyar ta ba, duk soyyayar da take nuna masa bai hango komai ba?? Ina fa ya hango, nikuma nace!! Salma ta bankowa Rahma harara ganin ta tsure su da Ido, "Malama bakyaji ance ki bani lemon?" Rahma ta maida hankalin ta kan Fajir, girar sa ya daga alamar Yess, Cikin Salma yake shafawa wanda ta bude shi a fili, Rahma kan ta ta duk'ar taci gaba da bare lemon, "Honey wane suna zamu sawa Babyn nan?" Ta fada tare da k'ara hade kanta da fuskar shi, Murmushi yayi kana yace, "Me kike so?" Bakin ta ta hada da nashi ta danyi kissing enshi, Kana ta juyo kan Rahma, "Wai bazata bani lemon ba?" Fajir ya dago ya kalli Rahma da idanun ta suka kawo ruwa, "Indai wannan lemon kike jira toh abinda yake cikin ki ya zube," Tana kaiwa nan tabar falon tare da had'iye kukan ta, lallai tabbas tasan abin yi, Fajir kuwa haka kawai yaji baiji dadin hakan ba, Salma ko baki ta saki, "kaji muguwa,?" Fajir da kansa ya bata lemon sai iskanci take zuba mishi. Abinda Rahma bata sani ba kuwa a daren ranar suka shirya wanda Salma ce ta sameshi da kuka cikin ta yana ciwo, Wannan duk shi ya kawo shirya war su, kuma dai akace Al'amarin Miji da Mata sai Rabbi. Rahma kuka taci wanda yayi sanadiyar kumbura idonta, tana kwance a daki taji an turo k'ofar, Fajir ne ya shigo cikin sanyin jiki, a gefen gadon ya zauna, A hankali ya tashe ta ta zaune tare da kama hannayen ta biyu wanda Rahma taji kamar wayar wuta ta kama sanadiyar wani irin shock da takeji, "Rahma!" Ya Kira sunan ta, bata iya amsawa ba sai dago Ido da tayi, Yaci gaba da cewa,"Zaman da kukeyi da Salma baya mun dad'i, koba komai yayar kice, so Ina so Ki dauke ta kamar Falmata(Yayar Khady ce diyar Mama Safiya) barin ma yanzu da take dauke da Juna biyu bana so wata rigima tana shiga tsakanin Ku, So Ki zauna da ita kamar Itace matsayi na a wajen ki," Rahma ta cire hannunta daga nashi, "A matsayin ka?
.
Bangane matsayin ba," Ta fada cikin wata irin murya, cikin rashin kulawa yace, "Eh ni ba Yayan ki bane? So Ki dauke ta itace Yayar ki," Wani murmushin takaicih Rahma tayi, kai a zaton ka har yanzu kana Yayana ne? Shi fa auren ina kayi dashi? Baka san zuciya ta ta dad'e da kamuwa da tsananin son ka ba? Meyasa zakayi min haka? Kaine kake zuwamin a mafalki a koda yaushe, bazaka so ni ba meyasa kake sa zuciya ta tana yaudarar kanta? Wannan duk acikin zuciya take maganar ganin tayi shiru tana kallon sa dauke da murmushi at dsm tym hawaye ya cika idon ta, "Rahma!" Ya Kira ta wanda yasa ta dawo daga maganar zuci da take, "Yahh Ina ka ajiye auren mu?" Karan kanta bata san tayi maganar ba shi kuwa Fajir fargaba ya shiga yi kada dai ace Rahma son aure take masa. Kauda kanta tayi a gefe kana ta mik'e tayi hanyar toilet, "Kada kadamu Yahh zanyi koma me kake so," Tana kaiwa nan tayi toilet, da bango ta jinjina tasha kukan ta, shikuwa kukan ya tsaya saura ta, ya dad'e kana ya tashi jiki a sanyaye, dole yasan abin yi kafin lokaci ya kure masa. Kwana biyu da faruwar hakan, akayi rasuwa a gidan Sarki wato karamin gida, wata tsohuwa ce ta rasu, dan haka kaff dangi ana can, Sai bayan la'asar Rahma ta fito da niyar komawa gida, Dama Fajir yazo da ita toh a yanzu Motar Islam take so ta karba. Salma kuwa tun azahar tabar wajen, Rahma taje yiwa Mai Martaba Sallama Daddy ma yana a wajen duk da har yanzu fushi take dashi, A kalla a sati bazaifi sau biyu da zata Kira shi ba, Acan ta same Fajir shima yaje Sallama ganin hadari ya rikide garin da alama gab yake da ya tashi, Tare suka fito nan yace in ta tashi tazo su wuce, Aikuwa suna isa gida ana gwabcewa da ruwa ha'in da na'in, Umbrella enshi ya duba dake a gefe Kwara daya ce dan haka yace, "Ungu kije sama ki dauko min wata," Baki ta zumbure, "kai Yahh sai naje zan dauko mata wata?" Fitowa yayi ya bude leman tana ganin haka ta zo da gudu ta kankame shi, kar ruwa su taba ta, "Ke ki kuma zan dauko miki wata," "Tsoro faa a motan," Yanda ka kankame sa sosai yasa jikin su ya fara bada wani reaction kamar an zuba acid cikin base, tafiya suka fara a kamkame, saidai basu kai ko Ina ba iska yayi sama da leman, "Wayyo Yahh sanyi!" Ganin duk ta rirrike shi ta hana su tafiya yasa cafff ya dauke ta, Sai a falo ya dire ta fuska a daure ya wuce d'akin sa, Ita ma da gudu tayi daki ta fad'a toilet, Wani irin take ji ajikin ta duk ilahirin gabban jikin ta sun amsa ma wannan sakon da jikin su ya tura, Da kyar ta cire kayan ta hada ruwan zafi a jacuzzi ta kwanta aciki, Daga lokacin bata kara ganin Fajir ba, Saidai taje makokin ta dawo a Motar ta, Yau kam part en Baban ta ta nufa dan Father yayi mata fada sosai kuma taji fadan dan haka tayi can dan ta bashi hakuri, Tana shiga ta nufi upstairs zuwa dakin shi, saidai tana fara takawa taci karo da Sadiya tana takawa da kyar da tutsetsen cikin ta, Da sauri da sauri gaban Rahma ya fara faduwa, Me take shirin gani? Badai ciki ba? Kam.. ai wlh wannan Matar bata isa ba, Rahma da ta tsura mata Ido har ta Iso gab da ita, Sadiya tayi murmushi na karfin hali tace,"a,ah Rahma ce a yau dinnan," Rahma da taji kamar ta watsa mata ruwan zafi bata san lokacin da zuciyar ta ta ingiza taba tasa hannayenta duka biyu ta bangaje Sadiya daidai lokacin da Daddy ya fito daga dakin, Sadiya yayi ka ka ka ta fadi k'asa a rub da ciki, ita kan ta Rahma saida taji ihun Sadiya sannan ta fahimci abinda ta aikata, daidai lokacin da Mamam Jodan ta shigo gidan, Daddy cikin gaggawa yazo ya kama Sadiya, koda ya dago ta tuni jini ya balle mata, Maman Jodan tazo da sauri ta kama ta tana salati, Rahma ta tsoro ya shige ta da k'arfi Daddy ya finciko ta, wani irin kyakkyawan maruka biyu ya bata wanda yasa taga Daddy ya dawo mata gida hud'u, cikin tsananin bacin rai Daddy ya k'ara fincika ta a k'asa, "Fice ki barmin gida, marar hankali da natsuwa kije kada ki k'ara zuwa nan har sai kinyi hankali!"
,
A guje tabar gidan tana kuka kamar wadda numfashin ta zai fita, ikon Allah ne ya kaita gida, Daki ta fad'a tayi kuka har tabawa kanta tausayi, Bata fito dakin ba saida safe da yunwa ta kusa illata ta, tana so ta Kira Daddy ko Father saidai fargaban me zai biyo baya takeyi bata so ace mata Sadiya ta mutu. Fajir kuwa tun zaman su cin abinci yake mata wani kallo Rahma fuskar nan tata a kumbure, Da kyar ta samu ta had'iye shayin da take sha, Salma ta kalli Fajir tace, "Honey meyasa babu Maltina ta anan?" Fajir ya kwala wa Zahura kira da sauri ta hawo Saman dauke da Maltinar wadda ta kasance ta roba, Nan ta ajiye ta koma k'asa, Ba,afi mintuna ukku ba Salma ta ajiye cibin da take cin abincin, Fajir ya fake ta da ido, Kallon sa tayi kana taci gaba da cin Abincin, kara ajiye cokalin tayi tare da rike cikin, "Menene?" Inji Fajir bata amsa ba, Ta sauka a kasa tare da rirrike cikin ta Sosai, "Owhh wayyo Fajir zan mutu!" Da sauri daga Fajir har Rahma sukayo Kanta, Nan ta shiga ihu tana murk'usu tare da rike cikin ta, Cikin firgici Fajir yace,"innalillahi wa inna alaihir raji un, Rahma jeki dauko min keys," Da gudu Rahma tayi sama, saidai duk inda tasan yana ajiye mukullan bata gansu ba, Da sauri ta dawo ta shaida bata gansu ba, Fajir yayi sama dan ya duba shima din baigan su, rudewa tayi masa yawa, Koda ya dawo har Salma ta suma a wajen tuni ta fara zubar jini, Da sauri yace Rahma ta dauko key na Motar ta, A 360tayi part enta saidai sam bata gansu ba saida ta jiyo shi yana kwala mata kira kana ta hango su a gefen gado da sauri ta je ta jawo Motar saidai babu Iska a Motar ganin idan suka tafi ciki zasu shekara basu kai ba yasa Fajir ya ajiye Salma cikin haushi ganin duk motocin gidan basu da amfani, Da sauri ya nufi part en Salma cikin sa,a yaci karo da jakar ta a falo, Nan ya zaro na Motar ta. Salma banda nishi babu abinda take Rahma kuwa kuka take ganin yanda Salma take cikin jini, Ita ta zauna da ita a baya har suka Isa asibiti Da sauri aka karbi Salma, Daga Fajir har Rahma ko wannensu kamar ya rusa ihu, Bayan kamar mintuna talatin likitan daya ke ciki ya fito tare da kiran Fajir zuwa Office, "Abortion!" Fajir ya fad'a cikin tsananin Mamaki, likitan ya dafa kafadar shi yace "Calm down my frnd,ba komai bane dan yanzu munyi mata wanke mara kuma zata samu lafiya inshaAllah, saidai kaje ka tambaye ta me tasha acikin awa daya da suka wuce dan acikin abin sha tasha gubar, sanadiyar jinkirin kawo ta da kukayi shi yaja dole cikin ya zube," Cikin rudewa Fajir ya bar falon, Dakin da aka kai Salma ya shiga, Salma na ganin shi ta fara kuka "Fajir an cuceni an zubar min da ciki Allah ya isa wallahi," Hawaye yaji suna son zubo mishi tabbas ta bashi tausayi, "Salma me kika sha acikin awa d'aya?" Salma ta kara fashewa da kuka tace,"wallahi yau banci komai ba abincin da muka ci sai kuma Maltinar da nasha," "Maltina?" Ya fada tare da mik'ewa, Da sauri ya fice waje, Rahma dake a waje da sauri ta bishi, Baice da ita komai ba sai wani irin huci da yake kamar zaki, Suna isa gida taga ya dauki kwalbar Maltinar da ruwa ya fita, Ita kam daki ta wuce tayo wanka, yau kam abu yayi mata zafi iya zafi. Tana zaune anan ta jiyo parking din Fajir, Yana shigowa tun a falo ya fara kwadawa Zabura mai aiki kira, da sauri tazo tana ban hak'uri, Kwalbar ya nuna mata, "Waya baki wannan ki bawa Salma," Shiru tayi yayin da jikin ta yake rawa matuk'a, "Bada ke nake ba?ko sai na harbeki!" Ya fada cikin tsawa, Nan take ta zube k'asa zaune, "ranka shi dad'e, gimbiya ce ta bani tace idan zan kai abinci na bawa Mai daki," "Gimbiya? Rahma ce ta baki?
.
Wallahi idan kika mun karya sai na illata ki," Nan take ta fara kuka, "wallahi itace kuma cewa tayi idan ban kaiba zata koreni, dan Allah kayimin Rai kayimin Afuwa,!" Nan ta zube tana sharban kuka cikin tsawa yace ta biyo shi, Rahma na ganin Fajir ta taso da sauri,"Yah Salma fa...." Shiru tayi ganin ya jefo ta da kwalbar Maltinar, "Rahma dama bakida imani? Wace irin muguwa kike? Kin kashe Matar babanki a jiya yau kuma kin kashe d'ana kuma zaki kashe mata ta? Wace irin zuciya ce dake? Me kika sa acikin lemon nan da kika bada abawa Salma?" Cikin wata irin murya yake maganar mai firgita mazauna wajen. Rahma cikin rudani ta zaro ido "Yah wallahi bani na bata ba," Matar ya kalla nan ta kara sadda kai tace,"a,a fa gimbiya, dazu da safe kika bani a kitchen kikace idan ban bata ba zaki koreni, ni kuma banyi zaton wani abu bane aciki ba na kai mata," Da sauri Rahma tazo ta kwashe wannan Matar da Mari saidai ko hannun ta bata ajiye ba Fajir ya dauke ta da wani irin gigitaccen Mari, Dafe kunnen ta tayi ta kafe shi da Ido, "Fajir! Nizaka mara? Ni zaka kira da marar imani? Me kake nufi da na kashe Matar Daddy? Na zubar wa matar ka ciki? Duk ni kadai wannan aikin?" Wani murmushin bakin ciki tayi tare da zubar da wasu hawaye, Wani mugun wawan Mari ya k'ara kai mata wanda sai da tayi zaman 'yan bori a k'asa, "Kin zamemin Bala,i kin zame ma kowa Masifa! Haka ake gata?? Toh wallahi Bari kiji yanda kika zubar min da ciki sai kin bar gidan nan, mai mugun hali, bana kaunar koda da kwayar zarra ne, an riga da an cuceni had'ani zama da ke!" Yana kaiwa nan ya nufi hanyar dakin sa, Rahma kam kuka ya kafe a idon ta tsabar rudani da bakin ciki, A hankali taja k'afar tayi D'aki, key din motar ta kawo ta dauka ko dan kwali babu akan ta, haka da Jan kafa ta fice zuwa inda motar ta take, Ta dad'e zaune acikin har Fajir yazo ya k'ara fita tana nan zaune ta hada kai da sitiyarin Motar, tunani take so tayi ko yaya ne amma sam kwakwalwar ta ta cushe, Haka taja motar ba tare da tanada isasshen iska ba, da kyar ta isa wajen kanikawa aka zuba mata iska, acan bayan motar ta hango sauran canji ta basu, Titi ta hau sosai tana zuba gudu ta kamar zata tashi Motar, Tun sha biyu take gudun so take sai lokacin da hankalin ta yadawo kana ta tsaya ko zatayi tunani har gashi rana na batun faduwa bata samu yin hakan ba. "Fice ki barmin gida, marar hankali da natsuwa kije kada ki k'ara zuwa nan har sai kinyi hankali!" "Kin zamemin Bala,i kin zame ma kowa Masifa! Haka ake gata?? Toh wallahi Bari kiji yanda kika zubar min da ciki sai kin bar gidan nan, mai mugun hali, bana kaunar koda da kwayar zarra ne, an riga da an cuceni had'ani zama da ke!" Wad'an nan kalamai sune ke mata yawo acikin kai, "Daddy!" Ta fad'a tare da sakin murmushi, "Fajir! Meyasa na so ka alhali ba,ayi ka domin ka so ni ba?
.
Meyasa zuciya ta ta yaudare ni? Salma meyasa kika rabani da Yaya na Mijina meyasa baka kasance *RABO* a gareni ba? Islam meyasa baki zamemin *wata k'awar* da zaki hana ni kaunar Yayan ki ba? Tabbas *duk abinda kayi* shi ake maka amma ni mai na aikata da rayuwa ta ta kasance *Mimie da Mami?* Jodan shine na farko da *Yacuceni* da ba,asani auren Fajir ba gashi sanadiyar hakan Narasa yanda zanyi nayo *Yakana*hakan yajazamin garari acikin *duhun daji* ni *Rahma*ya zanyi???? Idanun ta taji suna kokarin rufe kansu nan take ta suma ba tare da ta tsaida motar ba bada bata lokaci taji kamar an zare numfashin ta. ********* "Mumy zan zo wajen ki ya fiye min dad'i," Aisha ta girgiza kai tana wani irin murmushi tare da fitar da wani haske a hannuwanta, "Rahma ashe kin girma, naji dadin ganin ki a yau dinnan saidai har yanzu nan wurin babu ke! Ki jirayi lokaci, abinda ya faru dake ba komai bane acikin halin rayuwa, ki kasance mai hakuri da juriya a duk inda kika samu kanki, albarka tana tare dake!" Rahma wani murmushi ta saki kamar yadda taga mahaifiyar ta tayi, "Mum bazaki zauna dani ba? Daddy fa yace inzo wajen ki," Aisha tayi dariya mai matuk'ar kyau, "Daddyn ki yafi son ki da rayuwar sa, ki koma garesu amma kafin nan ki tabbatar kin koye biyayya kinsan darajar Kauna kinsan meye hakuri," Rahma ta yunkura dan ta riko hannun Aisha, Sai taga tana ja da baya tana dariya, fararen tufamin ta suka shiga zuba kyalkyali, hannuwa ta shiga daga ma Rahma, daga nan bata kara ganin komai ba.
.
"Lahhh inno! Inno taho ki gani, kahiragga ta tashi!" Yaron ya malala da gudu yana kiran Innar sa, A hankali ta bude idon ta tare da kura ma saman dakin Ido, Tayi tayi ta gano acikin Ina ne take amma sam ta kasa gane hakan, da kyar ta mike tsaye tare da rike kanta da ke bala,in Sara mata. "Wagga! Ke Wagga taho Ku gani Yarinyar ga ta tashi" Wata tsohuwa ce ke magana tana tattafa hannun ta, wata Mace ta shigo itama tashigo da gudu tana fadin, "Awo wallah ko ta tashi, kai Idi shek'a da gudu ka kirawo su dawuda," Aikam yaron da ke tsaye daga shi dan karamin pant wanda a kalla ya kai shekaru goma ya falla as guje yabar dakin, Rahma ta jingina a bangon dakin tana mamaki Wace duniya kuma take????? Tsohuwar nan ta shigo da kwanon ruwa ta riko kan ta tana kokarin bata ruwan, Kauda kanta tayi gefe tsohuwar nan ta ajiye kwanon, "Ah toh ke Jimma taho ki bata ruwan ko tana sha, in banda ma Dauda daga ganin kahira ya dauko ta," Rahma bata gano me suke fada ba, dan haka kokarin komawa tayi ta kwanta, Saurayin da ya shigo dauke da kwasa sabe a kafadar sa yasa ta kin komawa ta kwanta, Karasowa yayi wajen ta, "Inno kun bata maganin?" Innar tace "Ina hwa mun ka bata tunda ko ruwan taki sha, in banda ikon Allah mutum ya kwana goma a kwance baici komai ba kuma hat akawo mai ruwa ya tsaya yin kuri," Dawuda da yasan jininin Innar tashi dan haka ya nufi wani lungu ya dauko Leda nan ya zazzage maganin ya ballo su, mika mata yayi, "Aun hu kisha," Kawar da kanta tayi, ya k'ara miko Mata, da kyar ta amsa ta sha maganin tare da ruwan na kwano, wad'an da suka kasance faro faron fura ne mai tsami, Komawa tayi ta kwanta, sai bayan la,asar sosai ta kara tashi, Matar da ake kira Jimma ita ta kama ta tashiga bayi, nan Jimma tace tayo arwala, Ganin tayi tsaye alamun bata san meye arwalan ba yasa tayi saurin rike bakin ta da tatuna Inna tace musu kafira ce, Jimma tace "toh yi zaman Ki taho ki kwanta," Da dawuda ya dawo yaga Rahma a zaune da alama inda aka daure mata kan ya daina ciwo, Kyakkyawan Murmushi ya bata kana ya zauna gefe, "Jimma tayi Sallah kuwa?" Jimma ta girgiza kai tace,"Inna hwa tace ba Musluma bace kalli gashin kanta da da harrutttan ta,(farce)" Dawuda yayi dariya yace, "Bari dai mu Bari har tagama dawowa cikin hankalin ta sannan mujiya dan nidai batayi min kama da kahirrai ba, kuma ai gashin kanta bana doki bane gayu dai na ankayi mashi" Jimma dai batace komai ba sai "uhm kam" Ita kuwa Rahma iyakar ta ido. Tsawon kwana biyu kenan da farkawar ta amma ko kala bai fito daga bakin ta ba, Inno tayi fad'a har ta gaji cewa an ajiye mata Christan acikin daki su ala dole ganin yanda akayi squeezing gashin kanta tare da faratun ta da suka yi yawa sai irin shigar ta wannan shi yake tabbatar musu da cewa Rahma ba Musluma bace, Dawuda ne kadai ya musa da yake shi yayi zama a birni acan yayi Almajiran ci, Fitowar Rahma daga daki ne yasa Dawuda dake zaune a turmi ya juyo, Inna kuwa labari take bashi na rabon gadon su, jin yayi shiru ne yasa Inna dagowa ta kalleshi, ganin Rahma a tsaye tana zubar hawaye ne yasa ya taso yayo kanta, "Mallama mihhwaru dake haka?" Kuka ta shiga Sosai kana ta dube shi,"Ina ne nan? Su waye Ku?" Dawuda yace,"Alhamdulillahi Inna Wagga diya ta warke, toh taho ki zauna bisa tabar ma sai kiji," Rahma zaunawa tayi a gefe, Inna ma turmin ta jayo ta zauna, "Mallama ni suna na Dawuda, nidai bansan mihhwaru dake ba naje can gangaren gona nigga neki kwance a kasa, naji tsoro ganin babu kowa wajen, Dana duba sai na hango motar ki ta kone kurmus a cikin haki ta bugi wani icce, toh anyi sa,a karshen wata ne likita tazo garin ga, dan haka ni dauko ki nikkai ki can, an dubaki akayi maki allura nissai miki magani, shina hwa Abbaki hwarka ba har tsawon kwana shida, amma yanzu tun gashi ke tashi sai Ki hwada muna wacece ke?" Rahma ta zaro ido tare da maimaita tambayar"wacece ni?"
..
Gidan ta kara kallo ta kalli Dawuda ta kalli Inna, so take ta tuna wacece ita amma sam ta kasa, "Dama baku sanni ba? Dan Allah ku daure Ku fadamun suna na, Wace ce ni?" Daga Inna har Dawuda tsananin tsoro da mamaki ya kamasu badai ta fad'a a kogin ciwon *Mantau ba?* Hmmm Lallai kam tayi loosing memory nata, toh waye zai tuna mata???? Wane gari ne ta same kanta??? Taya tazo nan???? Readers Ku taimaka Ku fadiwa Rahma. [9/24, 5:55 PM] Aunty Queen Mamu: *RAHMA* _(Daddy's girl)_ *Na* *QUEEN MERMUE* *35* Nan take Rahma ta rikice matuk'a, a iya sanin ta bata san wacece ita ba, Ganin haka yasa suka tausaya maka, Suna suka saka mata inda Inna tace a dinga kiranta da Yalwa, Dawuda kuwa yace saidai sunan birni wato Rukayya, Haka rayuwa ta kasance wa Rahma a garin Dan kaiwa dake k'arkashin kauyen Tubako shi kuma take karkashin k'aramar hukumar Silame,dake jihar Sakkwato, Da yake Dawuda saurayi ne matashi kuma mai ilmi, dan Abirni yayi zama ko yanzu dogon Hutu yazo har acire amfanin gonan, nan ya shiga koya mata addinin sa Salla da kuma karatu, Rahma kamar sabuwar haihuwa haka ta koma komai sai an nuna mata, a yayinda Jimma da Inno suka maida ta Ruke, Inna na ganin ta warke tasa ta dinga biyar Jimma zuwa rafi daukar ruwa, haka kuwa akayi kullum zata dauki tulu suje daukar ruwa idan sun dawo zasu raba aiki wannan abinci wannan kuma gyaran gida, Inno kam mace ce mai yawan Masifa ga kuma son tsafta, dan haka abu k'adan zata dora kwandon bala'i, Sosai Rahma take zage dantse tayi aiki ga kuma tsoron Inna da take dan har korar ta taso yi saida Dawuda yashiga tsakani, Jimma ce kadai take samun sauki a wajen ta da yake sarakuwa ce a wajen Inno Mijin ta yana birnin legas, Sosai Rahma tayi baki amma ga Mamaki kuma sai tayi jiki tare da samun na tsuwa, Shakuwa mai k'arfi ta shiga tsakanin ta da Dawuda, Tofa wata sabuwar inji 'yan caca. *********** Fajir yana dawowa daga Asibiti ya wuce Gidan Sarki, Sam bai nemi Daddy ba acewar shi Rahma dole ta Kira shi, Bayan sun gaisa da Mai Martaba nan yake tambayar sa ko ya dubo gwaggwon su, Sadiya kenan wadda ta haifi twin's saidai itace babu lafiya amma yanzu ta ji sauki har an maidota gida. Nan Fajir yayi murna saidai yayi Mamaki da yaji Sarki yana tambayar Rahma bata zo ba, Karya ya zuga masa da cewa ai tana nan zuwa anjima, daga nan ya wuce karamin gida dan dubo Lafiyar 'yan biyu da Mamar su. Nan ya hadu da Daddy yayi masa Barka ganin Daddy bai tambaye shi ba'asin Rahma ba yasa shima baiyi masa zancen ba. Kwana biyu kenan da tafiyar Rahma ba tare da Sun sa Ina ta dosa ba, An sallamo Salma daga Asibiti wanda kullun cikin kukan karya take, so take ta k'ara sa ya tsani Rahma dukda bata san takamammen Matakin da ya dauka akan Rahmar ba, Haka rayuwa ta kasance, Sam Fajir yakasa samun na tsuwa na ganin Daga Daddy har Father kai kaf gidan babu Wanda yayi masa Maganar gashi kullum yana zuwa amma bai taba cin karo da ita ba, Su dai acan suna fushi da Rahma ne yayin basa tambayar ta akan abin da ta aikata, shi kuwa ganin shirun ya zata ta fadi abinda ta aikata masa ne shiyasa suke nauyin tambayar sa, saidai har yau babu Wanda yace ya jikin Salma, Part din Rahma ya shiga a yau ganin sa abude yasa ya shiga har daki, Wayar ta ya hango yashe ak'asa hakan yasa yayi saurin kara dubawa, Wayar har ta danyi kura kuma akashe, Wayar sa ya zaro dan kuwa al,amarin ya fara bashi tsoro, Islam ya Kira daga can ta daga,"Hello Yahh! Barka da yini" "Lpy qlau, Islam kina Ina ne haka?" "Yah Ina school, kasan muna exams" "Ohk yaushe zaki koma gida?" "A hostle nake kwana yanzu but saura 2days mu kammala ai jiya na shiga gida," Jin taje jiya yasa yace,"oh da yaushe?" Kafin ta bashi amsa sai kuma ta jefo sa da tambayar da ta rikita shi,"Yahh Ina Rahma ne nayi ta kiran ta a kashe Daddy ma yace fushi take ya Kira a kashe kuma taki tazo ganin Twin's" Fajir yace"am Bari inzo Bari na duba," Katse wayar yayi tare da zaunawa akan gadon dakin, Tsoro ne fal a zuciyar sa, tunanin sa ya bashi ko tabar kasar ne ta tafi gun Mama Sadiya? Passport inta ya shiga bida sai kuma ya ganshi hakan ya tabbatar masa bata je ko'ina ba, Hakan dai ya daure ya Kira Mama Sadiya, Tambayar d'aya ce, "Ina Rahma ta shiga wayar ta akashe?" Haka Mama Safiya ta tambayeshi, duk wani Family da yakira sai an jefo sa da tambayar, Tuni kan sa ya dau zafi, Wayar Daddy ya shiga Kira, daga can ya dauka tare da fadin "ya akayi Fajir?" Cikin rashin sanin abin cewa Fajir ya shiga kame kame, Saida Daddy ya k'ara tambayar kana yace,"am Daddy dama Rahma nake nema," Cikin rashin fahimta Daddy yace,"Wace Rahma kuma?
.
Tazo nan ne?" Fajir nan take yaji hanjin cikin sa sun kulle da sauri ya katse wayar, jikin sa ya bala'in mutuwa kwanta wa yayi akan gadon yana jiyo kamshin Rahma, Baiyi aune ba yaji parking mota a harabar Gidan, ta window ya leka gaban sa ne ya fadi hango Daddy ya fito a Motar, Da sauri ya nufi kasan, Yana isa falo wayar shi ta shiga ringing ganin Daddy yasa ya isa karasowa, Bayan sun gaisa ne Daddy yake tambayar zancen, "Fajir Ina Rahma ne? Tsawon Sati Ina neman ta a waya ban samu ba," Fajir ya sadda kai ne,"Daddy nima fiye da Satin kenan ban sameta ba, na zata ko gida taje akan abinda ta aikata mun," Cikin rudewa Daddy yace "ban fahimce ka ba? Tsawon Sati bata nan gidan ko yau ta fita?" Nan Fajir ya kwashe labarin komai ya fad'uwa Daddy, tare da shaida masa ya Kira kowa bata je ba kuma passport enta yana nan. Daddy wani irin Fargaba ya kama shi, tabbas kwana d'aya da faruwar fadan sa da Rahma ko bacci baiyi a ranar ba, babu abinda yake ji sai fargaba idan ya tuna da ita amma dan yafi karfin zuciyar sa ya nuna mata cewa shine babba akan ta koda ya kasance maiyi mata kuskure hakan yasa ya danna zuciyar. Shawarar Fajir suka bi, direct Fadar Sarki suka wuce dan azaton su Father yanada masaniyar inda take, Mai Martaba hankalin sa yayi matuk'ar tashi lokacin da Fajir yake masa bayani, Nan ya fara fad'a,"wallahi duk Wanda yayi sanadiyar halaka ta bazan yafe masa ba," Yana kaiwa nan ya bar fadar ransa a baci. Abu yaci tura anyi nema dangi kaf babu mai labarin Rahma, Masarautar ta hargitse Dan kuwa babu mai gano kan Sarki, Anyi cigiya gidan talabijin, redio har a kamfanonin MTN da duk wata kafa ta yada labari amma shiru kake ji, Sarakunan garuruwa suka bada cigiya tare da kyauta mai tsoka, Daddy tuni ya kwanta ciwo, kuka babu Wanda baiyi ba acewar sa shine Sila, Haka yakasance a gun Fajir yayi danasi abinda yayi matuk'a, bai taba Jin son Rahma ba sai alokacin da ta nisan a gareshi, wani irin so mai tsanani yake shigar sa haka zai wuni ya kwana ya kwana d'akin ta. Salma hankalin ta ya tashi ganin irin tsananin tashin hankalin da Fajir ya shiga, duk iya kissa da kisisinar ta kasa ciwo kan lamarin, ********** Duk inda suka ratsa sai anyi sha'war yadda suke hirar tare da dariya da alama suna cikin tsantsar farin ciki, Rahma ce kan jaki Dawuda yana Jan akalar Jakin, Yanzu duka Fadin kauyen ansan da kaunar su wadda inno ce kadai bata mara musu baya ba, Dagacin garin da kanshi yace zai zama Waliyin Rahma, toh a yanzu da take a wata na shida da batan ta hakan yasa aka tsaida auren su Saba ga wata mai zuwa, Rahma kam sam babu abinda take tunawa na rayuwar ta abaya tuni ta tashi daga Rahma izuwa Rukken Inno kamar yadda 'yan kauyen suke kiran ta. Yau garin kowa Murna yake, duk yaron da kagani zaka gamu dashi Falle da gudu, Rahma dake kan jaki wanda akasan ta ciyawa ce suka yowa Inno ta kalli masoyin ta Dawuda tace, "Dawuda ya nigga kowa na shek'a gudu haka sai murna suke waye ya shigo garin?" Dawuda da hakoran sa suka ki rufewa yace,"ai yanzu da mun kai hakin ga gida can mun kayi, wata Hajiya ce mai rabon kaya duk shekara nan taka zuwa, sanadi kuwa ance hatsari ta samu acan titin malke sai dan garin ga yat taima ka mata shina hwa duk shekara sai tazo garin ga," "Kai gaskiya muma muje mu samo namu," Daga nan suka ajiye ciyar dabbobi a gida suka wuce babban fili dake a gaban kofar gidan dakaci, Da yake mutanen garin ba yawa ne dasu ba dan haka cikin tsari ake rabon kayan, Atamfa ce ake bawa Mata da dubu goma, maza kuwa yadi da buhun shinkafa sai dubu ashirin,ga masu aure, Marar aure kuwa Shinkafa da yadi da dubu goma, Ana haka har Rahma ta shiga dakin da ake kira a rubuta sunan ka kana ka fita kabada takardar sunan ka, sai abaka. Koda ta shiga dakin wasu hamshakan hajiyoyi ne guda biyu zaune a gefe sai Namiji wanda shine mai rubutun, Da shigowar Rahma Matar daya ta kafe ta da Ido, "Ke zo nan," Rahma saida ta dan zabura kana taja kafa tayo wajen su, Matar ta cire glishin idon ta, "Meye Sunan ki?" Rahma cikin yar fargaba ko laifi tayi ne ta amsa da,"Ruke!' "Wannan garin kike?" Rahma daga kai tayi, Matar ta kalle 'yar uwarta wadda tun lokacin da Rahma ta shigo bata dago kanta ba da rubutun da take a waya, "Hajiya kinga wannan Yarinyar kuwa? Yanzu kalle fa da kin bude makarantar anan ai da bata zauna anan ba," Wadda aka kira da Hajiya ta dago kanta, "Ke wannan garin kike?" Rahma kam ta kagu da tambayoyin su, da kyar ta kada Kanta, Hajiyar tace,"Ina ne gidan ku?" "Gidan Innon margayi Sale," "Oh Inno..!"

0 comments:
Post a Comment