RAHAMA DADDY'S GIRL Page 31-40
.
*'Yan Tsakar INADA KISHIYA nagode muku sosai inajin dadin zama daku Rabbi yabarmin Ku ya karbi addu,oinku, mugun tare ake,* Salma ta zak'e ta fara magana cikin yayyafin masifa, "Honey wallahi ka jawa waccan Yarinyar kunne idan ba haka ba sai na tattaka ta a gidan," Fajir ya juyo ya kalli Rahma, nan take ta marairaice fuska,kara kallo Salma yayi data rike konkoso,"me sukayi miki?" Salma cikin fada take cewa,"shiga daki na sukayi haka kawai suka dora min kwandon dariya, dan haka kayimun katangar karfe tsakanin mu," Fajir ya bata fuska ya kalli Rahma da Islam yace,"akan me zaku mata dariya? Sa,ar Ku ce?" Rahma tayi caraf ta murguda baki tace,"Shi kenan munga abin dariya bazamuyi ba? Kuma fa bada ita muke ba,Islam ce take bani labari," Fajir yayi wa Islam kallon hakane? "Eh labari muke fa kuma dama kasan Aunty Salma bata son muna gaisawa kai ne ka tursasani amma daga yau zan daina kuma zan fadawa Maman Fada duk yanda akayi tunda so take taga ta shiga tsakanin mu," Islam ta fice daga falon, Fajir tuni kanshi yayi zafi yana tsoron masifar Salma yana tsoron masifar Kakarshi Maman Fada idan taji wannan labarin dan haka ya ballawa Rahma harara, yana hararar ta ita kuwa ta bankawa Salma harara, "Kagani ko?
.
Harara na take" Fajir haushin su yaji duka dan haka baice komai ba ya nufi dinning table ya zauna dan yunwa ce karan kanta ta fiddashi sai ga wannan hayaniyar, Rahma kuwa tana shiga daki suka tafa da Islam, Islam ta kalle Rahma tace,"ai wannan shegiyar matar tashi yafi son ta da kowa, wallahi muddin kikayi wasa zasu maidaki yar kallo, bakar kazama da ita," Rahma tace,"ni Ina ruwa nada Mijin ta iya abinda nasani bana kaunar ta kuma sai na gallaza mata a gidan nan," Dariya Islam tayi tana harhada kayan ta,"Allah yasa zaki iya da ita, Bari in wuce naga waccan tsohuwar tana danna min kira," "Oh dan Allah ki gaida min dasu Yah yace weekend zai kawo ni," Islam tace"toh matar Yaya," daidai lokacin da take fita daga dakin, Ta falon ta biyo ta wuce batace dasu komai ba har takai bakin kofa Rahma na bayan ta, Rahma dake sanye da leggings sai yar bes bata rufe cibiyar taba tabi hanyar fita, Wani irin tsawa Fajir yadaka mata, "Ke Ina zaki haka?" Juyowa tayi ta tumbure baki, "Ita zan raka," "Dawo ki zauna," Salma ta watsa mai kallon Ina ruwan ka? Kunnen uwar shegu tayi dashi ta nufi hanyar ta, Islam da take a corridor tayi saurin girgiza kai alamun kada ta biyo ta, hannun ta ta dora a kunnen da nufin suyi waya, Hakan yasa Rahma ta dawo ta zauna kan table en, Abinci suka fara ci Salma sai faman kushe abincin take. Da maraice Rahma ta shiga kitchen da niyar dora girkin dare, Shinkafa ta dora, wanda duk a Google take kallo, bayan ta dahu ta dora miyar tumatir, bayan ta hada komai miyan ya dahu ta zuba a flas store ta shiga dam ya maida shinkafar da ta rage daga wadda ta dibo, tana shirin fitowa ne ta hango Salma ta shigo kitchen en, cikin sand'a ta bude kullun ta lasa miyar, drawer ta jayo ta fidda gishiri ta tattake ta afka shi cikin miya, ta kulle kamar yanda ta gani ta fice daga kitchen en, Rahma dariya tayi saida cikin ta yayi ciwo, lallai Salma ta debo ruwan dafa kanta, Zubar da miyar tayi ta hada sauce na kwai da kifi, Bayan Isha suka fito cin abinci, Salma tana faman yauki a dole za,a dizga Rahma gashi Fajir baya wasa da abinci, Salma ta ya kune fuska ta fara saka abincin, haka ta tula ma Fajir da yawa, tana bud'e flax daya sai taga ba miya bace, kallon Rahma tayi,"Ina miya ne?
.
Ko kina nufin shima sauce din zaici?" Rahma ta tabe baki tace, "da abinda kika gani zakiyi aiki, kuma ba dan ayimin sharhi yasa na girka ba," Fajir yace"is ok Honey zubamun zanci haka nan," Salma ta mike cike da haushin Rahma, ita kuwa Rahma sai wani kayataccen murmushi take sakar mata ta harde hannaye a kirji ta dora k'afar ta daya kan d'aya, irin I'm d winner dinnan. Lafiya qlau suka ci Abincin duk da ita Rahma ba komai taci ba, Da dare kuwa Salma ta shige da Miji suka bar Rahma adakin ta, (kaji sokuwa keda girki wata da kwana da miji) Rahma tayi games har ta gaji Sam bacci yaki daukar ta, ta kira Daddy kuwa yaki dauka, karfe d'aya daidai agogon yace, tsoro taji yana kama ta ga kuma baccin da take son yi, Kuka ta fara a hankali, "Ribfff!" Faduwar jikar ta da ta dora akan madubi, da gudu ta fito daga dakin a tsorace, Bata tsaya ko Ina ba sai dakin Fajir unfortunately basu datse kofar ba, Tana shiga dakin kafin su ahama kunnu lamp din dakin, kuka take sosai, cakk ta tsaya da kukan, tsoron da tayo wa guduwa ya fiye mata akan abin da idanun ta suka gano. "Wayyo Allah Daddddyyyy!" Abinda ta fad'a kenan dai dai lokacin da..... [
.
Abinda ta fad'a kenan dai dai lokacin da taga wannan abun, da k'arfi ta juya tabar d'akin jikin ta ya shiga rawa haka kawai sai taji haushin Salma, da koke koke da wake_waken ta na ban tausayi bacci yayi awon gaba da ita. Rahma canji take gani a yanzu sosai, agaban ta Salma Fajir suke zakewa suna soyyaya wani lokacin ko kallo basu isheta ba wani lokacin kuma tayi tsaki, A yanzu ta daina Jin tsoron bacci ita kadai haka ta daina yin girkin sai Salma ce ke shiga tana yi, Rahma batada kwanan miji a yanzu gatanan dai kullun cikin zama d'aki. Mama Sadiya kuwa da tazo Sam bata fahimci zaman da suke ba ganin Rahma bata nuna komai ba, cikin 'yan dubarun ta na babbar mace ta shiga bugun cikin ta koda matsala, Rahma babu kawai tace, Yau take Salla a wajen Rahma dan ta tambayi Fajir tafiya gida kuma yace taje, yasani sarai tare yakamata suje amma ganin bazai iya ba yasa yace aiki zaije, Cikin murna Rahma ta shiga falon, saidai abin da tagani ya bala'in daga mata hankali, Daddy ne kwance akan cinyar Sadiya sai faman soyayya suke basu ko ji shigowar ta ba sai ji sukayi tace,"Daddyyyyyyy,"ta fad'a cikin sanyin murya, cikin halin ko ajiki na dan kinganni da matata Daddy ya amsa mata,"oyoyoyo My Dota!" Cikin bacin rai ta zauna d'ayar kujerar, "Ina wuni," Ta sowa yayi ya zauna a kujerar ya dan jawota jikin sa,"Lpy qlau My dear nayi missing naki Sosai," Murmushi ta kakaro tace "Me too dad" Daga haka ta zauna shiru, Sadiya dake zaune kamar gunki tace,"Rahma amare ya mai gidan naki?" "Badai kinsan inda naki yake ba? Toh meya dameki da nawa?" Rahma ta fad'a cikin daure fuska tare da duban wayar ta, Daddy yayi saurin cewa "Rahma!" Ko baki bai rufe ba itama tace"Daddy!" Baice mata komai dan a ganin shi bai kamata kada tayi fushi gashi shi dai yasan irin rashin ta da yayi na Sati biyun nan, ko bacci da kyar ya saba da yinsa ba tare da yaje dakin ta ba, da yawa yakan je ya dauki story book ya karanta kamar tana jinsa. Allah kadai yasan irin son da yake yiwa Rahma Sarai yasani a yanzu rayuwar ta bazatayi mata dadi ba, dan haka yake kokarin ganin ta shaku da Fajir wanda shine zai haddasa soyyaya a tsakanin su, kamar yanda take tun lokacin da take karama batada abokin shawara kamar shi so yake Fajir ya maye gurbin sa ta wannan hanyar. Jin yayi shiru ne yasa Sadiya mik'ewa tabar falon, ba kadan taji haushin maganar Rahma ba, amma toh ya ta iya???? Rahma kallon Daddy tayi cikin sanyin jiki taga yanda duk yaji babu dadi, "Daddy I'm sorry bana son matar nan ne, haka bana son Salma, yazanyi dasu?? Yazanyi nadaina ganin su?" Daddy sosai ya kalleta, yanzu ya gano abu biyu, na farko tana taya mahaifiyar ta kishi ne, na biyu kuwa karan kanta take yiwa kishi, lallai yasan yanda ya nuna ma Rahma Kauna da wuya ne ta yarda a hada kaunar ta da wani, Rahma ta mike tsaye cikin sanyi ta fidda jakan ta, turaruka masu kamshi ta fidda kusan guda shida, daidai nan Islam ta shigo a guje, Duka suka maida hankalin su kanta, Tana shigowa ta fad'a akan kujera tana haki, Daddy ya kalle ta yace,"lafiya haka Maryam?"
.
.Islam ta kalle Daddy a daburce tace,"Daddy Ya baraq ne, bansan me yasha ba Ina zuwa ta wajen nan ya biyo ni," Daddy yayi dan gutun tsaki kana yace,"Yaron nan sai nadaukar masa mataki wlh," Rahma ta kalli Daddy da alamun tambaya tace, "ya barak da nasani? Wani abu yake yasa,?" Islam tayi caraf tace,"au baki sani bane? Ai tun tuni yake shan abinsa har Mai Martaba yasani," Rahma ta tabe baki tace"uhm Allah ya kyauta! Ahm Daddy ga wannan, zanje cikin gida gun Mama," Daddy karba yayi yasa mata albarka, kana ta dauki wanda ta warewa Father da kuma Maman Fada, Tare da Islam suka fita, acan suka hango Barak a tsakar gidan yana ta hauka, Barak kanin Jodan ne, da yake duka 'ya'yan Abdullahi saidai Allah ya shirya, Rahma suna shiga ta wuce Fada, ganin Su waziri a wajen Fada yasa ta dan tsaya dan tasan bazata samu damar ganin sa ba, waziri yashiga ya shaida mai ai nan take yace abashi wuri zai hana da Matar sa. Rahma mugun walakanci tayiwa Sadiya wanda sai da ran Daddy ya sosu haka ta kwashi motar ta tabar gidan tana masifa da rigima. Haka rayuwa ta kasance mata, A halin yanzu laifin mahaifin ta tafi gani.
'
Rahma bata Jin dadin zaman gidan a yanzu ita ba gwana bace a fagen dagar waya saidai yanzu tana daurewa a karatun novels. ******* Masarautar kuwa, Abdullahi ne zaune a gaban k'anen Mahaifin sa, Abba ya kalli Abdullahi yace,"Yanzu kana tunanin daga ni har kai mun isa mu tsaida Yaya ga abinda yayi niya? Toh lallai kuwa Abdullahi ka haukace, yanzu duk wannan abun da ya faru da'yar sa da kuka cuta ma shine ba tsoron Allah zaka zomin da wannan zance? Toh bari kaji in gayamaka, ko ni aka bawa Sarautar wannan gida zan cire ta na damkawa Umar ita, bale har inje inyi magana ince a hana masa, a kull ka k'ara tada zancen nan sai na fadima Ubanka shida kake shakkarsa, sam baka san girma ya hau kanka ba a haka kuma kake tunanin sarauta, kadai kan ka kawai ka sani baka san kowa ba, fice ka bani waje!" Da karfi Abban ya fad'a sumi sumi Abdullahi ya fita, lallai ta sarke mashi duk inda ya duba babu nasara, Jekadiya ita kadai ce mai Fatan taimaka mishi dan haka ya k'ara sama ranshi ko ana sharo ko ana mazuru sai ya kai. Ga Jodan da yake son fiddawa da k'arfin tsiya, Bayan ya sanar da Jekadiya yanda sukayi nan take tace masa kada ya damu, zata maida tafiyar tata zuwa Niger a gobe in yaso kudi kawai zai maido mata a yau, da haka ya koma gidan sa ita kuwa ta wuce Fada. ******** Rahma zaune a falo tana kallo tana chart, Fajir ne ya fito shi kadai, da alama Kwanan nan Salma bata zama wata kila aiki ta fara zuwa dan kuwa ta lura kullun sai shida take dawowa, Ido ta bishi dashi zaunawa yayi a dayan kujera, gaishe tayi cikin sanyin jiki, "Rahma!" Ya Kira sunan ta cikin natsuwa tare da hade hannun sa duka a kafafun shi, da alama magana ce babba yake son yi da ita, "Na,am" ta amsa tare da kallon inda yake, Saida ya danyi shiru na mintuna kana yace,"bakya Jin dadin zama gidan nan ko", Tabbas kowa ya kalleta yasan bata Jin dadin zaman duba da yanda ta kara tsukewa duk dan mugurjin na da tayi a baya ya zube, Cikin gamsasshiyar amsa tace,"Eh!" Dan kauda kan sa yayi kana ya k'ara duban ta yace,"nasan da hakan, kwata kwata ma ko abincin kirki bakya ci, bansan me kika sawa ranki ba," Cikin jin haushin maganar sa tace,"duk da nake marainiya kuma ni kadai acikin gida ban taba kukan maraici ba ban taba rasa kulawa ba," Ta karashe zancen tana mai tamke fuska tare da kawar da kanta. "Abin yi! Ke kadai ce wadda Father zai iya yiwa favour a nan take, kinga ni bana son ki a matsayin Mata, haka bazan iya kallon Ki a wani matsayin ba Wanda ya wuce kanwa ta ba, mai zai hana kisamu Father da cewa bakya so na, a raba auren, na tabbatar zaiyi miki abinda kike so," Cikin tsananin Mamaki Rahma take kallon sa, ba wai haushi ya bata ba a,a zancen sa ne ya bata haushi, cikin gatse tace masa,"naga kafi yawan zuwa can mezai hana kai kafada masa!" Kallon ta yayi, shi har ga Allah wayau yake son yi mata kamar yanda suka tsara da matar shi, shidai Sam bai ma son zaman ta a gidan baya son cuta mata haka baya iya faranta mata, Daurewa yayi yace,"Kin riga da kinsan ni bazai lamunce mun ba kamar yanda kika san babu saki a duk auren da ya hada, Amma ke Ina ji ajiki na zai iya raba auren mu kasancewar ya banbantaki da kowa, nifa jiye miki zama anan nakeyi gwara a wurin Daddy zaki fi samun kwanciyar hankali." Cikin bacin rai da kai k'ololuwar raini Rahma ta mike tsaye,"Lallai Salma ta iya bada shawara, toh kace ban bata matsayin Jekadiya ta ba bale ta aiko da sakon ta a wajena," Fajir shima cikin bacin rai ya mike,"kee! Rahma kisan yanda kike magana agabana sam na rasa yanda raini ya shiga tsakanin mu, duk rainin ki toh kidaina saka mata ta aciki," "Oh my gosh!" Ta dage goshin ta tare da fadin hakan, cancikin makoshi tace,"na manta rako su akayi," Daga nan ta fice falon, sam baiji me tace a karshe ba amma ya fahimci ta gama rai na shi, da wata ce da tuni ya saita ta, amma ko ita din ba barin ta zaiyi ba. Rahma ranta yayi zafi sosai, wannan kiyayyar dame tayi kama?
.
Ita tun tashin ta ba,a taba furta mata Kalmar rashin so ba sai akan Fajir, lallai ya kamata ta gyarawa Salma zama. Salma na dawowa ta tarar Fajir baya nan, Rahma kuwa tana Jin ta ta fito da gudu ta nufi falon, Tsayawa tayi bakin shiga falon daidai lokacin da wayar ta take ringing, "Eh gata nan ta dawo, ita kadai ce, Eh tun dazu na gyara dak'in," Ta danyi shiru kuma kana tace,"lah Yah ba gayama ta zanyi ba," "Toh! Kai Yah dan ta ganni da wannan kayan wane zargi kuma,?" Can kuma ta bubbuga kafa ak'asa tace,"Yah duk ka canja wlh, ba damuwa zan canja," Rahma da take tsinkayar Salma labe a bayan labule ta lallab'a irin bata son a ganta dinan ta dauki chajan wayar ta tayi daki, Salma ta fito a rikice, ganin Rahma daure da towel da, shin dawa take waya haka? Fajir ko? Chabb lallai anyi babban munafiki me sukayi a d'akin?shiyasa tun dazu ta Kira shi yaki dauka, gaban ta ya bala,in faduwa tayi dakin sa da gudu. Nima dai nayi dakin da gudu. me Rahma take shirin shirya wa
.
Saida akayi Isha,i ya shigo can ya hango Salma hakimce a falon k'asa tana ta kumbura kamar fulawa ansa yeast, Bai kula ta ba yayi Saman shi dan a uzurce yake yana so cin abinci da yake ko da Rana baici abincin ba, Salma ta shigo dakin cikin kububuwar ta ta tsaya akan sa lokacin da yake rage kaya, "Me kacewa Rahma a waya dazun?" Kallon banza yayi mata dan shi kam ya fara gajiya da hali irin na Salma, Cikin basarwa yaci gaba da cire kayan sa, "Me kika san kin aike ni,"shi azatonsa sa shawarar da sukayi take nufi, Salma cikin masifa tace, "Bangane ba? Me kake nufi? Ni zaka yaudara ai wallahi bazata sabu ba," Shareta yayi zuwa falo dan cikin sa nayi masa kuka, Mafisa Sosai Salma takeyi wadda shi baisan asalin abin da takeyi wa masifa ba, Har a dining ta bishi ganin ya kyale ta yasa ta sakar mishi kuka, Azahirin gaskiya Fajir baya son ganin kukan mace kota halin kaka bale Salma da yake Jin son ta sosai, dan haka ya daure yace, "Wai menene? Bana ce kifita harkan Yarinyar nan ba? Ko so kike ta raina mu ne?" Salma ta goge hawayen ta tace,"toh ba kai bane kake waya da ita ba," Cikin kaguwa yace,"ni babu wayar da nayi da ita" At dsm tym yaja ta sukayi daki, wanka ya shiga kafin yazo suyi bacci. Daga haka ya kashe zancen. Rahma kuwa tun da ta fahimci Salma akwai ta da saurin zargi duk wani abu da zai kawo zargi shi take aikatawa. ******* Jekadiya ce zaune a gaban Abdullahi sunyi tsuru tsuru, ko wanne su yana jimamin abinda suka jiyo daga hamshakin mashahurin gawurtaccen bokan nasu, abinda ya faru kuwa shine, Bayan Jekadiya tayi tafiyar zuwa kasar Niger ta zayyane ma boka duk buk'atar su, nan take ya duba a madubin sa, abinda ya bayyana kuwa shine Sam Abdullahi bazai gadi sarauta ba. Abdullahi yaso ya karya ta wannan bokan dan shi kam kota halin kaka ne bazai Bari aba Omar sarauta saidai kuwa duk su rasata.
*******
Yanzu zaman Salma da Fajir zaman rashin yarda ne abu k'adan sai ta tsare shi da tambayar tsiya wanda wannan abun ba karamin haushi yaka bashi ba. Yau Salma babu zuwa Aiki weekend, dan haka tana part enta tana sharban bacci dayake ba adakin Fajir ta kwana ba. Rahma ce ta kwankwasa dakin sa shima bacci yake, a hankali ya bud'e idon sa yace" waye," Cikin yar k'aramar muryar ta tace "nice" "Shigo" Shigowa tayi daure da towel duk da akwai pant da yar breziyar ta a jikin ta,"ya akayi ne?" Ya tambaye ta cikin muryar bacci ba tare da ya juyo ya ganta ba, "Yah wanka zanyi a toilet enka" Cikin magagin bacci yace,"naki fa?" "nawa ba ruwan zafi," Har yanzu bai juyo ba yace,"kije kasa mana," "Kai Yah wankan har k'asa," Bata jirayi amsar shi ba ta shiga toilet en, shikam baccin dama damunsa yake ko maganar da yake mata acikin baccin ne dan haka bai kara bi takan ta ba yakara kan bargo, Rahma ta shiga tayi cire kayan ta tayi wanka, pant enta ta wanke tayi hanging in shi, breziyar kuwa sai da ta kawo dakin taje gefen gado ta 'yar da ita, Daga haka cikin addu,ar kada ya tashi har sai Salma ta shigo tayi dakin ta. Salma da ta fito daga ita sai daura kirji ta nufi dakin dan ganin ko ya tashi, Shikuwa daidai lokacin ya shiga toilet yin wanka, acan ya hango pant dan karamin tsaki yayi, "Wannan iskanci fa," Ya fada acikin ransa dan daganin pant en yasan ba na Salma bane, Salma tana shigowa ta zauna a saman gadon jin wanka yake yi yasa ta tashi dan ta koma har ya k'are, abu taji ya rike zanin nata, aikuwa tana dubawa ta hango yar k'aramar breziya kamar ta masu kirgan dangi, Gaban ta ya bala,in faduwa sai a lokacin takara kallon gadon ganin yanda duk aka yakushe bedsheet din, Tana dago kanta shikuwa ya fito rike da pant en da niyar ya kaiwa Rahma dam a zaton sa ko mantawa tayi, Salma ta kalli breziyar ta kara kallon pant din ta kara maida idon ta akan gadon at dsm tym ta dubi wankan da Fajir ya go gashi sai faman goge kai yake da towel. Tabdi jam, ni kaina saida na hango yak'in da za,ayi.
.
Salma wani irin kallo ta bishi da shi, Shikam Sam baisan me take nufi da kallon ba dan haka ajiye towel din yayi da yake goge kansa, bakin k'ofa ya leka ya kwala wa Rahma kira, Salma na tsaye kai kam ji take kamar ta dambata dashi, Rahma ta shigo tana waya a kunnen ta saida ta shigo kana ta katse wayar, Kallon kallon aka shiga yi, Pant din ya nuna mata,"meye na ajiye min wannan acikin toilet?" Dan bude Ido tayi kana tace,"oh mantawa nayi da na wanke," Jefo mata yayi, Salma tayi saurin jefa masa breziyar, cikin masifa tace,"me wannan kuma yake nufi? Pant a toilet bra akan gado? Fajir me kake son kace" Ta fada cikin tsawa, Wani kallo yabi Rahma dashi, Tumbure baki tayi kana ya tambaye ta ta bashi amsa,"Yah ai kai kace nayi wanka na anan kuma mantawa nayi da kace in dauke daga nan," Bata rufe baki ba Salma tayo kanta ai kuwa da gudu Rahma tayi waje tare da banko kofar tana dariya, Salma so tayi ta rage zafi akan Rahma amma ta tsere dan haka ta juyo gun Fajir wanda ya tamke fuska, "Fajir alk'awarin ka kenan? A iya nan ya tsaya? Tunda wuri haka zakaci amanata, karasa da wacce zaka kwana sai wannan mitsitsiyar Yarinyar?," "Salma!" Ya Kira sunan ta cikin kakkausar murya, "Meyasa baki da hankali? Wane irin maganganun banza kike son fada min? Toh wallahi Allah kishiga hankalin ki ganin Ina daga maki kafa bawai shi zaisa ki maidani sa,anki ba!" Cikin fushi itama taci gaba da cewa,"eh dole kace haka kagama lalata da k'anwar ka,! Malam kana tutiyar sa,a dan wlh ba girmeni kayi bale kazo ka zuba min rainin hankali, ashe dama haka kake? Aini bansan munafinki boye kake ba sai a yau banza mai...." Bata karasa ba ya kwashe ta da gigitaccen Mari, wani irin ihu tayi ba,abun tace zata rama ba nesa ba kusa ba tasan bazata ci riba ba, "Allah ya isa mugu, dan iska mai lalata,." Da gudu tayi waje sanadiyar belt enshi da ya dauko yayi Kanta. Ranshi yayi masa zafi da yasani bai bar Rahma ta shiga toilet din ba, can kuma wata zuciyar tace kaida gidan baka Isa kayi iko da matar ka ba sai ita? Tsaki yayi a bayyane,bai taba sawa Salma hannu ba tun lokacin da ya taba Marin ta kafin suyi aure bai kara ba sai a wannan lokacin dan haka ya shiga tuhumar kansa da rashin kyauta mata. Rahma dake labe tana Jin duk abinda ya faru ta fito tana kukan munafinci, abakin d'akin sa ta tsaya dan tasan tana shiga zai Koro ta dan dole yaji haushin ta ta hada shi rigima da abar kaunar sa, "Yahh! Dan Allah yi hakuri kabawa Aunty Salma hakuri ni bansan zai mata zafi ba, kuma naga ai k'anwar ka nake ko bacci zanyi a dakin ka kamar yanda nake yiwa Daddy," Cikin raunanniyar murya take maganar tana shan Kuka, Wanda azahirin gaskiya gwalo take masa a bayan k'ofar, Jin bai kula taba yasa ta kara sheshshekar kukan, "Yahh in bata hakura ba zan kira Daddy yayi mata magana,!" Tausayinta yaji tare da ganin rashin laifin ta, dan haka cikin yarda da ita yace, "Jeki abinki basai kin kira DadRahma ba, zatayi hakuri," Rahma ta banko masa harara tare da dage hanci tace,"tana hakura Ina kara kunna wutar," Abinda ta fad'a a badini a zahiri kuwa cewa tayi,"tohm Yah na," Daga haka ta juya tare da fadin "yesss!!" Tayi dakin ta, Rawa ta shiga yi tana kada dan karamin kugun ta, can kuma sai ta tsaya tana wani tunanin, Toh wai ita meye nata na hada rigima haka? Ita dai ba Mijin Salma take so ba haka zalika ba wai zaman daram take so ba toh meye nata aciki? Haka dai ta shiga tunanin shin ko zatayi yanda yace a raba auren su? Wata zuciyar tace a,a Hamma KB da take so har ansa date auren shi,ita fa ba burin ta Fajir ya so ta ba, a,ah ita so take ya fifitata akan Matar sa. Ni kuwa nace da wane dalilin???? Yau kusan kwana biyu kenan Salma na fushi ta Kira Yayar ta ta sanar mata yanda akayi, Yayar tata kuwa duba da irin son da Fajir yake mata tace Samm wannan kisisina ce ta mata, Haka Fajir yazo lallashin Matar sa tare da fad'a mata dalilin yin wankan Rahma a dakin sa, Bawai ta yarda bane saidai ya rufe ta da dadin baki dan haka sai zuciyar ta tazama 50-50wane kason taji ta yarda in wani kason kuma yace an maidaki sauna. Sati daya yanzu da faruwar hakan sabon kishi ya kullu tsakanin Salma Fajir da kuma Rahma Fajir, Rahma babu abinda take bakin ciki a yanzu irin yanda Fajir duk ya wani kara zuzucewa akan Salma, sai suyi ta abubuwa a gaban ta, Hakan nasa ta kuka sosai taji kamar taje a raba auren ta huta, Yau kam kamar kullun zaune ta samesu a falon ita kuwa DVD take so ta dauka zuwa dakin ta kasancewar tata tasamu matsala, Ganin suna zuba soyyayar su babu kunya bale tsoron Allah yasa ta wuce direct ta cire socket din duk da kallon yana aiki kuma cassette ne aciki, Salma ta kara manna ma Fajir wani Hot Kiss a goshi da yake kwance yake akan cinyoyinta, Rahma nan take taji wani kololon bakin ciki ya taso mata bata kallon inda take tafiya har tayi nisa Salma ta kwala mata kira da "kee!" Rahma bata juyo na taci gaba da tafiya, "Honey kalli ikon mallaka ina kallo ta dauke DVD," Fajir ya ware murya yace,"Rahma!" Tsayawa tayi abakin kofar, "zo nan," Bata Musa ba ta dawo din, "Akan me zaki dauke DVD? Kinaji kuma tana kiranki kinyi mata banza?" "Aidai Ina ganin ka shedi zanen suna na, dan haka banga dalilin da ya hana ka sanar da matar ka sunan yanka na ba," Cikin izza take maganar taci gaba da cewa,"kuma ke Bari kiji, koda wasa kika ga nayi abu kikayi kokarin kai kara na sai na ballaki a gidan nan, saniya kawai kuma in ke kika siya wannan kizo ki kwata," Fajir kallon Mamaki ya bita dashi,Salma kuwa mik'ewa tayi a tsaye "Jarr..... Ni kike gayawa haka? La,ila hwa illallahu, lallai Fajir ka cuceni had'ani da wannan Yarinyar," Fajir kuwa hannun Salma ya kamo, "haba Honey meye ki kyaleta yarin ta ke damunta," Hannun ta ta fisge,"ai kace haka Yarinya ta kallan ta kira ni da saniya kai kuma kace yarin ta?" Rahma kuwa tsaki ta saki,"tunda bakya iya kwatar Bari naje inada abin yi," Salma kan Rahma tayo da k'arfi yayin da Fajir yayi saurin kamata, "Kabar ta!" Rahma ta fad'a cikin tada murya,"Ina gaya miki Salma koda wasa kada kiyi tunanin kaskantaccen hannun ki zai tab'a ni ya zauna lafiya, idan kuma kina ganin wasa ne shi Mijin naki yayi ganganci barin ki," Tana kaiwa nan tayi watsi da DVD da karfi akan tiles din, Cikin fushi kuma ta dauki setlight ta maka ta a TV, aikin mahaukaci ta shiga yi a falon komai ta samu watsi take dashi. "Niii!!!! Ni zakice ki doka?, Hmmm wallahi zaki gane ta sai na maidaki abar tausayi anan," Fajir d yaja Salma zuwa dakin sa ita kuwa tsoro ne yaka mata dan a zahiri tsoro ne da ita sai bakar masifa. .
.
Where are you AMNOOR, a gaskiya banida bakin godiya a gareki, kwacokam Buk kika sadaukar wani Queen
.
Lallai wani al,amari yana shirin faruwa Anan. Haka rayuwa ta kasance wa Rahma a iya yanzu ko taje gida bata zuwa part din Daddy dan gudun taga matar shi ran ta ya baci, Sam Daddy ya fita harkan ta ita kuwa fushi take dashi mai tsanani, Wani abu da baku sani ba shine, tuni Rahma ta fad'a a tarkon so, son wanda batada muhalli a zuciyar sa, son wanda bai san tanayi ba, dan haka yanzu abubuwa sun jagule mata, Salma kuwa sabon luv aka bud'a tsakanin ta da Fajir, wanda yafi na baya kasancewar tana dauke da Juna biyu, Wanda take neman zubar dashi kota halin kaka, kasancewar bata shirya haihuwa ba ga kuma aiki da bata dad'e da fara somawa ba. Duk da tasan idan Fajir ya gano zata samu matsala dashi, da yake da yawa tayi ta zubar da cikin ba tare da yasan tana da cikin ba, saidai wannan lokacin akasi aka samu a gaban shi likita ya tabbatar tana da juna biyu, Sabuwar ririta da kulawa ba,a magana. Rahma abu yayi mata zafi Sam bata kaunar ganin Salma tare da Fajir, abu mafi muni shine duk ta kwanta bacci shi take gani, hakan yasa ta tattara nata ta bar part enshi, Duk da haka fadan ta da Salma na nan, Yau ma a kitchen Salma ta sameta bak'ak'en maganganun maras dad'i ta gaya mata, har da cewa ta likewa mijin ta, hakan ya tunzura ran Rahma lallai yau dinnan sai ta Haukata Salma, Da safe Salma na zaune a falon Fajir daa yake bacci yake kuma a ka'idar sa ba'a tashin sa, Salma tasan da hakan duk lokacin da tayi gigin tashin sa toh fa sai ya zuba ruwan masifa, Shi take jira ya tashi, Motar shi take son dauka Tesla model 3, wadda tun ajiya tagayamai da ita zataje sunan babbar k'awar ta, Rahma taji lokacin da sukayi zancen dan haka tun 8ta shirya cikin Dubai Gift, dakin a nufa wanda Salma ta tsura mata Ido tana son taga yakoro Rahma, Dariya Salma tayi dajin wannan abun da zai faru,ganin Rahma ta wuce sai yanga take, Rahma kuwa tana kai dakin sa a hankali ta taka inda yake ajiye keys ta dauko na Motar Tesla Model 3, saida ta dan Jima aciki sai ta fito sai da takai bakin k'ofa ta shagwabe murya yanda Salma zata jiyo ta tace,"uhm Nidai naki wayon, kayi bacci kawai sai mu hadu acan," Ta dan yi shiru kamar wadda ake bawa amsa, can kuma ta kara bubbuga kafa tace, "Haba Yah! Na fayi wanka kadai bari in nadawo ko kazo anjima ka dauko ni," Da dan gudu ta fito tana gungunin Shagwaba, sai kuma ta tsaya tace,"na,am!" Komawa tayi dakin kana ta fito da gudu tana dariya tayi down stairs, Salma dake zaune kamar dutse ta mike tana mamakin shin ko daman ya tashi,? Dakin ta shiga da k'arfi, ganin ya k'ara sa blanket ya rufe har fuska tasa ta yaye bargon, Hmmm kaji munafiki, abinda ta fad'a a ranta, Da karfi ta doki k'afar shi,"stop pretending kama tashi, wato ni kamaida sauna ko? Da nice na tashe ka ai ruwan Masifa zaka zuba mini, toh wallahi duk nasan wani shiri da kuke, daga kai har ita nafi k'arfin Ku walakanta ni," Fajir da ya cika ya cika kamar ya fashe shiru kawai yayi mata, Sam bai ma fahimci zancen da take ba, Cikin tsananin takaicih ya watso mata idanun sa da suka zama jajaye, "Waya ce ki tashe ni?"
.
Cikin amon murya ya fadi hakan. Takaicih ya ishe Salma ga shi zata makaro a wajen aiki, "Ka bani key na Motar," Rike da keankwaso tana karka dawa, Tsaki yayi ya koma ya kwanta, Fincikoshi tayi da k'arfi,"Fajir! Wallahi kada kace zakayi wasa dani, kabani keys nace, ni zaka maida yar tasha ko kuma bansan abinda kake aikatawa bane?" Baice komai ba ya nuna mata drawer da Hannu, kanshi ke tsananin Sarawa kamar zai cire gashi nan take ya fara jin sanyi na kama shi, Komawa yayi ya kwanta, ita kuma ta bude tana neman key din, ganin bata ga na Tesla model 3 Gashi ta makara yasa ta dauki na Fiat Tipo ta fic tare da tuhumar boye abinsa yayi, Saidai tana kaiwa downstairs ta hango an wangale ma Rahma get ta fita da Tesla model 3 d'in, wata irin Ashar ta zuba, lallai dole taje ta dawo ayi wadda za,ayi. Da yake Sam bata had'a aikin ta da komai ba. Rahma kuwa, unguwar kawai ta zagaye tana hango Salma ta hau titi ta juyo da kan motar zuwa Gida. A hankali ta tura kofar tare da boye keys din a bayan ta in case of yatashi daga barcin, ganin har yanzu yana nan dunkule yasa taje ta ajiye su, Har zata fita sai ta kalli agogon hannun ta, ganin 9:30 bai tashi ba yasa ta tattako zuwa inda yake, Tun daga nesa take jiyo nishin sa, da wani irin huci mai zafi, da sauri ta karaso wajen ganin yanda yake makarkata ya tsora tata, "Yahh what is happening to you?" Hannun ta ta dora akan forehead nashi, zafi radau, da sauri ta girgiza shi,"Yahh please wake up!" A hankali ya bud'e idon sa ta suka ja na wucin gadi, Wani irin zafi yake ji acikin su kamar ana zuba mishi yaji, ga sanyi da yakeji ajikin sa, higher fever ne mai k'arfi ya kama shi anan take, Rahma tuni ta fara hawaye, "Yah zan kira doctor? Yah !" Tashi tayi da nufin fita taji ya kamo hannun ta,juyowa tayi cikin sanyin jiki, Da kyar ya bude bakin sa cikin muryar rashin lafiya ya fara magana, ganin bata jiyo abinda yake cewa yasa takai kunnen ta zuwa bakin sa, "Rahma ke debo hot water, zaki ga magani a toilet zartan, ki dauko towel kizo," Da gudu ta shiga toilet din, ruwan zafi ta zuba a baho, sai ta shiga neman maganin, acan cikin glass drawer ta hangon shi, for hot temp ne ta dauko, sai da ta duba procedure kana ta rage ruwan ta zuba 3drops, karamin towel ta dauko ta fito, Yana jin ta ya fara kokarin yaye bargon sa, karasowa tayi ta ajiye a gefen sa ta shiga taimaka masa ya gyara kwanciyar sa, Towel din tasa a ruwa tana daddana masa kamar yadda ya umurce ta, Gaban ta taji yana faduwa lokacin da take shafa kirjin sa, boxer ne kawai a jikin sa ko singlet babu, Nan take ta fara dan daburcewa, haka kawai taji wani abu na ayyanuwa a cikin zuciyar ta, wanda ni kaina naso ganin menene amma babu dama, Da kyar ta Ida gogar jikin ta maida bahon a toilet tare da tsane towel din ta shanya. Dawowa tayi a wurin sa da Hannu ya nuna mata inda yake ajiye maganukan sa ta dauko, Nunu mata yake tana balla masa, ta koma a store ta dauko ruwa masu dimi, ta shin sa tayi ya jingina a gadon har zata bashi sai kuma ta juya ta ajiye maganin, "Yah jirani," Da gudu ta fita dakin, yana mamakin yanda ta maida gudu tafiyar ta, tea ta hado masa ba mai yawa ba saidai yayi tick sosai, Da kyar ta lallab'a shi yasha, "Yahh kasha mana, Daddy yace ba kyau shan magani ba'aci abinci ba," Da haka ta samu yasha kana ta bashi maganin, Taimaka masa tayi ya gyara kwanciyar sa ta rufa masa bargon kana ta maida maganin ta dauki cup din tayi waje, Bacci mai k'arfi ya kwashe shi, Ita kuwa Rahma duk bayan mintuna goma sai ta leka dakin. Tana ganin 2 tayi ta dauki abinci wanda Irish ne ta hada da hanta sai kayan ganye, koda ta shiga ya tashi sai dai idon sa a rufe, Durkuso tayi a gaban shi, tana kallon fuskar shi, Acikin ranta take yaba kyakkyawar fuskar shi, hancin sa gashin idon sa, sai kuma ta tsurawa Lips enshi Ido, batayi aune ba taga idon sa abude da sauri ta mike tsaye tana Sosa k'eya, "Am.. abinci Yah," Idon sa ya lumshe ya k'ara bude wa hakan ya k'ara tafiya da imanin ta, Ruwan wanka yace ta hada masa, Bayan ta fito ta kamashi har toilet ya shiga sannan ta dawo, Rahma gadon ta dan gyara da yake ita fa idan aiki ne batada kuiya ga kuma saurin yin abu dan koma kamar ta tashi sama take yinshi alamun batajin nauyin jikin ta, nikam cewa nayi toh Ina taga jikin bale taji nauyin sa???????? Abinci yaci Sosai kana yayi Sallah ya koma kwanta wa, Ganin ta gyara dak'in sai kamshi yake yasa yaji dadin hakan, Rahma tana komawa daki ta Kira Father, Nan suka gaisa ya tambaye Fajir nan ta shaida masa baida lafiya ne, budar bakin Mai Martaba sai cewa yayi"Bacci yayi kuka tashe sa?" Mamaki tambayar ta bata sai tace,"Father idan an tashe sa yake rashin lafiya?" Father yace,'ai wannan ya zamar masa jiki muddin yayi nauyin bacci aka tashe sa ta hanyar tsawa ko bubbuga sa toh fa sai yayi kwanaki yana fama da ciwon kai, tun rasuwar mahaifinsa da aka tashe sa yana bacci aka gaya masa, haka lokacin da mahaifiyar sa ta bar gidan nan yana bacci hidimar sa ta tashe sa, shine fa ya zame masa jiki," Rahma shiru tayi kana tace, "Father dama mahaifiyar sa bata mutu ba?" Father yace,'wayace maki ta rasu dama? Bata kasar nan ne tun lokacin kuma har yanzu," Rahma zatayi magana yace,"Zan dauki waya, ki tabbatar dai yana cin abinci da maganin sa dai_dai," Daga nan ya katse wayar, Rahma tausayin shi taji ya kamata,
.
Salma kuwa Bayan an tashi daga aiki ta biya gidan Yayar ta dake anan Kano, Nan suka shirya yanda zata zube cikin ta hanya mai kyau tare da cimma wata manufa tasu, bata dawo gidan ba sai 9:pm.
0 comments:
Post a Comment