A WATA MASARAUTA Page 21-30
.
Saima taji labarin Safeenat batasamu zuwa makarantaba saboda bata da lafiya, Ba jakadiya k'adaiba gaba d'aya hankalin iyayen Safeenat saida yashi , Domin abbansu Safeenat fitowa yayi daga gida yana salati yashiga motarsa nufi neman Bilkisu." Safeenat kuwa kuka tashigayi kwana d'aya babu Bilkisu babu labarinta, Saitafara tunanin ko prince Adnan ne yasanya a d'auketa, domin d'aukar fansar abunda taimasa, Wata zuciyar kuwa na gargad'inta da bazai iya sanyawa a d'auke ta ba." Bilkisu kuwa ya kulleta a d'aki yayi tafiyarsa, sai dai duk bayan a'wa biyu zaizo domin ganin koda tayi nadama tafad'a masa inda Abdullah yake, Amma babu alamar nadama a fuskarta, sai dai ya tarar da ita tana games a wayarta hankalinta a kwance babu damuwa a tareda ita, haushinta ya lunlub'eshi yace "wato ita wannan yarinyar batada niyar nadama tafad'i inda takai Abdullah kenan?" Ya kai hannunsa zai fisge yawar dake hannunta k'irar 1phone tayi saurin b'oye wayar a bayanta, Ganin zai iya murd'eta ya kwace wayar a hannunta , tatura wayar cikin rigarta, shi kuma ganin ta tura wayar a rigarta, yayi mata wani kallo, Yace "shed'aniya ni babu abunda zanyi dake, kidaina wani tura waya a riga, wato d'azun kinji dad'in nahad'a jikina da nake shine yanzun kike Neman nasanya hannuna a cikin rigarki, saboda kina jarabanbiya, to Allah yakiyayeni babu abunda nake iyayi dake, kitafi can kinemi dai dai dake, ninafi k'arfinki babu abunda zanyi dake, Yaja wani dogon tsaki malama kifito mun da Abdullah nasakeki kikama gabanki ." Ta kallesa taja wani dogon tsaki, tayimasa kallon sama da k'asa, Tace "mezanyi dakai, dibeka, me gareka wadda harnake sha'awar had'a jikina da kai, tanuna masa d'akinsa dayi wani kaca kaca da kaya tace " k'azami kawai." Tace Abdullah bazan fad'i a inda yakeba domin har yanzun bangaji da ganinka cikin k'unci da bak'in cikin rashin ganin Abdullah ba." Yace "a she kema zama bek'aremaki a gidan nan ba kenan, Domin mundun bakibada umurnin a sake Abdullah ba nima kisani bazan tab'a sakinki ki koma gida ba, Kuma kisani abincin da nake kawomaki daga yau na daina, Sai dai kizauna da yunwa idon kikaji wuya zakiyi bayani da bakinki inda kikai Abdullah, Ganin yanda yake magana sai wani cincira yake cike da b'acin rai da bak'in ciki, kamar ba Adnan d'in da tasani ba, Dariya tashiga yimasa tana nunasa da hannu tana dariya harda rik'e ciki, Haushi da bak'in ciki ya kuma lunlub'esa, Ya d'aga hannu alamar zai daketa meya tuna oho sai ya sauke hannun yana cizon yatsa, Sai yafita d'akin a fusace yaja k'ofar d'akin da k'arfi yasanya makulli ya kulleta yayi tafiyarsa." Ganin ya kuma kulleta bayada niyar sakinta bare takoma gida, Duk hankalinta yatashi tana tunanin jakadiya, tasan yanzun duk inda take tana cikin tashin hankalin rashin ganinta kwana d'aya dabatayiba Idon kuma tayi yunkurin shedawa maimartaba to Tabbas hukuncine zai hau kanta watak'ila harta rasa rayuwarta, wadda idan hakan yafaru bazataji dad'i a rayuwarta ba." zubur tamik'e tsaye da tuna da Safeenat tasan yanzun labari ya kai a kunnesu na b'atanta Suma tasan tabbas basa cikin kwanciyar hankali a wannan lokacin." Wayarta ta d'auka takira fadawanta tace tana buk'atar a sakar mata Abdullah yanzun nan, Suka amsa mata da to angama ranki ya dad'e, Suka sakesa, suna kewar juna domin d'an zamanda sukayi da Abdullah sunshak'u dashi sosai, Wadda shi kuma Abdullah beso aka sakesaba ko dan saboda kalar abincin dayakeci irin na masarauta, Sai yashiga tunani a zuciyarsa, gaskya betab'a ganin masarautar da fadawa suke daula haka, sai a wannan masarautar, inama shima a maidashi cikin fadawan yaci gaba da rayuwasu, da ya bautawa masarautarsu Bilkisu, Domin zama taredasu ya fahimci me'ake nufi da sarauta, Kuma ya fahimci k'aramci da daraja d'an Adam irin na masarautarsu Bilkisu A haka dai yabar wurin fadawan, yana kewarsu, yana mai tsinewa Adnan a rayuwarsa domin yasan shine silar sanyawa a sakesa, domin yaga kwana biyu beganshiba, saikace a tare a ka haifemu." Yaja wani dogon tsaki yayi tafiyarsa." Adnan yana k'ofar gidansu Abdullah yana kwantarwa da mahaifan Abdullah hankali a kan cewa insha Allahu gobe Abdullah zaidawo gida, ba b'acewa yayi ba yanan cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali, Begama rufe bakinsaba sai ganin Abdullah yayi a gabannsu yana dariya, yayi kyau yayi k'iba har wani shek'i yake, yana masu dariya, yanufi mahaifansa ya rungumesu cikin jin dad'i, suma sai murna sukeyi naganin tilon d'ansu, Prince baki yasaki yana kallon Abdullah yana mamakin kwana biyu, yaga yayi kyau kuma yayi k'iba. Gefe yajanyeshe yana kallonsa cike da mamaki,樂 yace "Abdullah wai meke faruwa ne?" ina fatan muguwar yarinyar bata sanya anyimaka illah ba?" Yakaiwa Adnan harara yace gaskiya ka daina cewa gimbiya Bilkisu muguwa, domin ita ba muguwa bace, illah maison alkhairi da daraja d'an adam, Ni wlh a baya d'aukar da nake mata wata wuk'antanciyar 'yar talaka marasa galihu a she ba haka abun yakeba, Adnan yasaki baki da hanci yana kallon Abdullah cike da mamaki,
.
Yace "gimbiya kana nufin Bilkisu 'yar sarki ce?" Abdullah yace kwarai kuwa, 'yar sarki ce, wadda mahaifinta da masarauta gaba d'aya suke alfahari da ita saboda kyawawan halayennta da kuma daraja d'an adam." Adnan yace " 'yar wace masarautarce?" Waye ubanta?" Kuma A wane gari suke gudanar da mulkunsu?" Duk a jere yajerawa Abdullah wad'an nan tambayoyi, Abdullah ya wurgamasa harara, yace " kobaka tambaye niba nad'aukoma labarai da d'umi d'uminsu, Zakasan kowacece Bulkisu amma kabarni nashiga gida nahuta zuwa anjima sai muhad'u kasha labari." Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa yabar Adnan a nan tsaye yashiga tunani, Saida Abdullah yakai k'ofar gida ya waigo yaga Adnan tsaye yana tunani, Yace gaskya prince baka kyautamun ba, dakasanya a kafito dani daga cikin daular mulkin gimbiya Bilkisu, Domin gaskiya da bakai bane danace kamar kanajin bak'incikin ganina a cikin daular masarauta Yana kaiwa nan yashigewarsa gida Yabar prince Adnan tsaye yana tunani."
.
Prince Adnan kasa tafiya yayi a k'ofar gidansu Abdullah, Domin gaba d'aya Abdullah mamaki yake bashi lokaci d'aya ya firgice masa har yake iya fad'a masa Magan ganu a kan Bilkisu, Motarsa Yakoma ya zauna yana tunanin sauyawar da Abdullah yayi, Kiran sallar azahar ne yafito dashi daga cikin motar, yanufi masalanci dake kusa da gidansu Abdullah domin yayi sallah, Yasan dolene Abdullah yafito domin yayi sallah, daga nan yabafashi labarin kowacece Bilkisu, 'yar wace masarautace shine kawai abunda yakeso yasani a bakin Abdullah." Shiru kakeji har a'ka kammala sallah bega Abdullah ba, dibe dibe yashigayi koda zaiganshi amma beganshi, Yanke shawara yayi yashiga cikin gidansu kai tsaye yayi masa dabarar da zai fanyace masa komai a kan Bilkisu, Domin yanda yaga kan Abdullah namasa rawa ko aika yaro yayi yakirashi yasan bazai fitoba." Kaitsaye yanufi gidan tare da sallama, Mamarsu Abdullah ya tarar tsakar gida tana arwala, Ya durkusa k'asa ya gaida ita, ta amsa masa cikin fara'a da sakin fuska, Tace "Adnan dawowa kayi ne?" Yaufa bazaman lafiya amininka yadawo, Adnan yayi murmushi ya sosa kai, yace "Ummu yana ciki kuwa?" Ummu tace "yana d'akinsa shiga katashesa lokacin sallah yayi yana kwance, Adnan ya mik'e yashiga d'akin Abdullah dake kwance saman makekeyar katafarsa yana shak'ar barci, Adnan yashiga tashinsa yana bunbugar k'afarsa, Abdullah yabud'e idonsa a hakanli yakai dibonsa ga maitashinsa yana cikin jin dad'in barcinsa, Ai kuwa yayi ido biyu da Adnan Zurbur yamike zaune yana mai kallon Adnan Yace "dama nasan kaine, domin babu mai katsemin jin dad'in duniya sai kai, To yanzun da katasheni me kakeso naimaka?" Adnan yayi murmushin dole domin a xahirin gaskiya maganganun da Abdullah yake fad'a masa sunayimasa ciyo a rayuwarsa amma baya nuna masa, saboda yana buk'atar yabashi labarin Bilkisu wadda ya dad'e yana nema." Danne zuciyarsa yayi, yace "sorry abokina tashi lokacin sallah ne yayi kana kwance kanata shak'ar barci, Kuma kasan kwana biyu nayi missing d'inka, Bilkisu ta d'aukemun kai." Jin ya ambaci sunan Bilkisu Abdullah yamik'e zaune yana murmushin jin dad'i a fuskarsa, Wadda yabawa Adnan mamaki." Abdullah yace "wlh kuwa nima nayi missing d'inka abokina bari nayi sallah kasha labari da d'umi d'uminsa." Adnan yayi murmushin dole, yace "yawwa my friend ayi mana addu'a." Dariya yayi ya d'auro alwala ya shinfid'a darduma tayar da sallah, Adnan na kallonsa." Bayan ya idar da sallah ne Ummu tagabatar masu da abinci, Damun shinkafane yasha kayan lambu da busanshin kifi, Adnan yakai dibansa ga abincin, yaga kalar abincin da Addah take dafa masu duk ranar juma'a, Filet d'in abincin yajawo a gabansa yana mai had'iyar yawu, Soma cin abincin yayi yana mai kallon Abdullah domin ya matso yafad'a masa asalin wace ce Bilkisu, Yana gudun yafayiwq Abdullah maganar, Yace yafasa gayamasa, domin ya fahimci dawowarsa wani rashin mutunci yakeji dashi, Besan abunda ya hango a masarautar su Bilkisu ba, Wadda shi a masarautarsu basu dashi." Ya kuma kallonsa yace "abokina baka bani labarin zamanda kayi da fadawa ba?" Abdullah yayi dariya yace "bari kawai prince nasha wuya, Kuma daga baya nasha dad'i, domin kuwa abincin damukece tare da fadawa kamar abincin da sarki yakeci, Bari kawai prince ai mulki da daraja d'an Adam na masarautar su Bilkisu, Sannan kullum cikin farin ciki muke kwana mutashi cikinsa sab'anin nan, Prince yayi saurin katsesa zuciyarsa nayimasa tafasa, yana yabun kirkin wata masautar da batasuba, kuma abunda yakeso yafad'a masa bashi yake fad'a masaba Yayi karfin halin yimasa magana yace "friend abunda nakeso nasani shine, Wace ce Bilkisu?" Kuma a wane gari take?" Waye mahaifinta?" Abdullah yayi dariya yace "Bilkisu Abdurraham yola kenan, haifanfiyar 'yar yolace, Mahaifinta Abdurrahaman yola shike mulkin garin yola ma'ana shine sarkin garin yola, Najiya a bakin fadawanta cewa mahaifin Bilkisu duk a cikin 'ya'yansa yafisonta, domin kyawawan halayenta da kuma daraja d'an Adam, Kuma Batada girman kai irin ba 'ya'yan sarauta, Asalima bataso a san cewa ita 'yar sarkice, Wannan dalilin ne yasa taxab'i karatu a garin, domin babu wadda yasan ko ita wace ce bare adinga bata girman da zai hanata karatu cikin kwanciyar hankali." To kaji tak'aitancin tarihim gimbiya Bilkisu." Magana yakeyiwa Prince amma hankalinsa gaba d'aya yatafi tunanin Bilkisu, Dayaji cewa 'yar sarkin yola ce, To 'yar wacece a cikin matan maimartaba?" Tunawa yayi da fuskar Bahijja, tabbas tun farkon ganinsa da Bahijja yaga tanayimasa kama da fuskar dayasani, Sai a yanzun yagane bada kowa take masa kamaba face Bilkisu, Kodai d'akinsu d'aya da?" Zurbur yamik'e tsaye sai maganganu yakeyi kamar wani zaranre, Yana fad'in tabbas k'auwar Bahijja ce, Domin sai a yanzun yatuna Bahijja tanada k'auwa wadda take bimata, domin su biyu ne 'ya'ya mata a wurin Ammi, Kuma yasan Bilkisu tun tana k'aramarta ganeta ganeta kawaine beyiba, Yaja wani dogon tsaki wadda sai da Abdullah yazabura ya mik'e tsaye, Yadafasa yace "prince lafiya kake kuwa?" Naji kana wasu maganganu dangane da Bilkisu kodai kunada alak'atane da masarautar su Bilkisu ne?" Domin da alamar hakan a fuskarka, Adnan yace ban tabbatarba sainayi bincike, Ya d'auki key d'in motarsa yayi ficewarsa, yabar Abdullah a tsaye yana mamakin d'an uwanka amma bakasan d'an uwanka bane, saboda rashin sadarda zumunta tsakaninka da d'an uwanka babu wadda yasan juna saida idon kun had'u a hanya katuru kudinga yiwa junanku rashin mutunci saboda babu wadda yasan juna a tsakaninku, Allah yabamu ikon sada zumunci." Abdullah yayi murmushin jin dad'i yace "Allah yasa idan kabincika kagano 'yar uwarka ce, Danafi kowa jin dad'i domin gaba d'aya zan tattara kayana nakoma masarautarsu Bilkisu da zama."
.
Prince tafiya yake hankalinsa gaba d'aya baya jikinsa, Sai tunanin Bilkisu yakeyi yana mamakin rayuwa irin nata, Bilkisu kuwa tun lokacinda tasanya fadawanta suki Abdullah take dibun prince shima yazo yafitar da ita cikin wannan gidan, amma shuru takeji bezoba, Durk'ushe take tana mai zubar da hawaye, idan tatuna halinda jakadiya take ciki a yanzun na rashinta datayi, tana tausaya mata domin tasan hankalinta a tashe yake yanzun, Tsayowar motarsa tajiyo, da sauri tayi tashare hawayenda ke zuba a fuskarta, domin karyaga nadama a fuskarta, Tashi tayi daga tsugunnen datake tayi saurin hawa kan kujera ta kwanta tarufe idonta alamar barci takeyi, Tanajinsa lokacinda yasanya key yabud'e k'ofar d'akin yashigo ya ganta a kwance tana barci cikin nutsuwa, Matsowa yayi kusa da ita ya tsora mata ido yana kallonta cike da tausayi, ganin yayi takoma masa Bahijja sak, murza idonsa ya kumayi domin ya tabbatar da gaskyar ita d'ince ko kuwa gizau take masa, ita d'in daice yagani kwance tana barci cikin kwanciyar hankali,. Sai gani yayi tak'ara masa kyau da gwarjini, ya kai dibunsa a agogon gwal dake d'aure a hannunta yaganshi da tambarin masarautar yola, a nan take tausayinta ya lunlubeshi ya durk'usa saiti kujerar da take kwance yasunkuyar da kansa dai dai saiti bakinta ya kaimata kiss a baki, sai ganin yayi tabud'e idanunta, zurbur tayi tamik'e zaune tanaimasa kallon tahuma, tace "to Allah yakamaka, mekakeso ka aika mun?" Rayfen d'ina zakayi kome kake nufi?" Shi kuma kunya duk ta lunlub'esa, amma sai ya wayance ya mere baki, yace mezanyi dake?" dibeki, dan Allah malama kitashi na maidake inda na d'aukoki,domin inada abunyi, yana kaiwa nan yanufi hanyar waje yabarta a nan zaune." Ganin yafita, itama ta mik'e tabi bayansa, ta tarar dashi har yashiga motarsa ita kad'ai yake jira, Tana zuwa wurin Taja tayi tsaye jikin motar taki shiga, shima ita yake kallon cike da mamaki, Saida suka d'auki kusan minti 30 yaga batada niyar shiga motar, Bud'e murfin motar yayi yafito yana huci, yace "dan Allah malama idan bakitashi tafiya ba, ki kauce kibani hanya na wuce, domin ni inada abunyi, Bata kallesaba kuma bata d'aga daga inda takeba, Ganin zata b'atamasa lokaci yaja hannunta yabud'e murfin motar ya turata a ciki, Yazagaya mazauninsa yashiga yatayar da motar suka bar gidan, Kallonsa takeyi cikin k'asaita mulki tace "a she kasan abunda nake nufi?" Ya zama Dole abud'ewa gimbiya mota idan tazata shiga, Be tankamata ba domin ya fahimci neman magana take dashi, yaci gaba da tuk'in motarsa." Hanyar makaranta yanufa da ita, zai ajiyeta a inda ya d'auketa, Tsayarda motarsa a cikin makarantar yayi daidai da gaba d'aya d'alibai sunfito lacture motar prince na tsayawa sai a kan idon Safeenat dake zaune tayi tagumi tana tunanin Bilkisu Atake gaban Safeenat yafad'i da tahango Bilkisu a cikin motar prince, Wata irin k'ara tasaki tazubar da littafan hannunta, wadda taja hankalin d'aliban makarantar gaba d'aya a gareta domin ganin meke faruwa?" Wurin Bilkisu tanufa da gudu, ta rungumeta tana zubar da hawaye, Kallo d'alibai suka bisu dashi, suna mamakin ganin Bilkisu tafito a motar prince, domin suna da labarin b'acewarta yau kwana biyu kenan, Safeenat tamaida kallonta a wurin prince dake tsaye a bakin motarsa, Tanunasa da yatsa idanunta cike da hawaye, Tace "wannan azzalumin ne yad'aukeke?" Wlh Allah saiya sakamaki, Ta kuma rungume Bilkisu tana kuka tace "sister ina fatan beyimaki komaiba. Bilkisu ido cike da hawaye ta kalli Safeenat ta kuma juyawa ta kalli mutanen dake kallonsu jira sukeyi suji dalili, Tace " jama'a kudibesa, tayimasu nuni da prince dake tsaye cike da mamaki, Ko wannesu ya maida kallonsa a wurin prince Tace shine yasace ni, da kansa bawai sanyawa yayi a saceniba, a matsayinsa na d'an sarki meye hukuncinsa?" Kowa shuru yayi, rike da baki, yana kallon prince cike da mamaki, Ta kuma matsawa kusa da shi ido cike da hawaye tace " nace banasonka, kakirani a waya, katuramun sak'on text duk a kan nayi hakuri nasoka, domin ka fahimci cewa ni 'yar sarkice, Nanumaka bana ra'ayinka, bana iya soyayyah dakai, shine kasace katafi dani gidanka domin kayi rayfen d'ina, To Allah yafika azzalumi mai mugun nufi, Allah zaice gaba da tsareni daga shairinka, Aikuwa a nan d'alibai kowa yasaki baki da kunne, suka had'a baki sukace fed'e樂 to Allah ya kyauta Amma dai prince kabamu mamaki樂 kowa ya kama gabansa yana fad'in albarkacin bakinsa, Safeenat tamatso kusa gareta ta dafa kafad'arta tace sister ina fatan beketa maki haddiba?" "tanunasa da hannu tace "Allah yafishi, Allah ya kwaceni a hannun azzalumi irinsa, Amma kasani bazan barkaba har saina d'auki fansar saceni dakayi kwana biyu batare da hakkina ba, Prince mutuwar tsaye yayi yana mamakin makirci irin na 'ya mace, yanuna kansa cikin sarkewar murya yace " rayfen nizanyi rayfen d'inki?" Me gareki wadda zaibani sha'awar da zaisanya nai maki fed'e?" To bari kiji ni har yanzun banganki a mace ba. Amma idon hakan kike buk'ata zan aikata maki basai kin had'a dayimun k'azafiba. Idanunsa sunkad'e sunyi jajir alamar ransa yab'aci sosai, yashiga motarsa yayi tafiyarsa Tok'i yake yana tunanin tuzarcin da Bilkisu tayimasa a bainar jama'a, Ya kaiwa sitiyarin mota doka, had'i da Jan wani dogon tsaki, Tambas zand'auki mataki a kanki Bilkisu, Ba 'yar uwata kikeba ko ciki d'aya muka fito dake saina d'aukar maki mataki mai muni, Wadda yafi fed'e ciyo."
.
Gudu yake a kantiti kamar ba'a hanyacinsa yakeba, Allah ne kadai yakawosa gida lafiya, Aguje yashigo da motarsa ya ajiyeta parking space, a can ya hango Bahijja da Fahad suna tattauna maganar aurensu, Ganinsa dasukayi yashigo ba a hayyacinsaba duk Kansu sukashi mamaki meke damun?" Fahad yace "kwana biyun nan yarasa abunda kedamun prince kullom cikin k'unci yake ba fara'a a fuskarsa, duk yashigo gida baya kula duk wadda ke masa magana, yanzun diba kigani yanda yashigo gidan nan kuma a haka zai rab'amu yawuce batare da yayi makowa maganaba a cikinmu Bahijja tace "wlh kuwa nima hakan nakeganinsa kullum cikin damuwa, Basu gama rufe bakinsuba yanufosu idanunsa sunkad'e sunyi jajir, Kallon tuhuma suka bishi dashi gaba d'ayansu, suna jiran suji tabakinsa. Ya k'ak'aro murmushin dole, yad'an saki fuskarsa yace "amarya da ango kunan zaune ashan soyayya, Fahad betanka masaba, sai Bahijja ce tace masa "zaunan kowa yayi aure yabarka, baka daniyar yin auren, sai fama kake da bak'in rai tsakankanin nan gidan nan kowa maganarka yakeyi anrasa abunda ke damunka, Sai a lokacin Fahad ya kallesa yace, Idan kaga dama memartaba na nemanka. Ya kalli Fahad yayi dariya domin a yanayinda yayi masa mgana ya fahimci fushi yakeyi dashi. Ya kuma maida kallonsa a Bahijja yace Anty Bahijja na tambaye?" Bahijja tace "ina saurarenka Adnan Allah yasa nasan amsar tambayarka, Yace "waini ina k'auwar nan taki Bilkisu?" Bahijja tace "Allah sarki Bilkisu baiwar Allah, tana nan lafiyarta k'alau anan garinma take karatu, Adnan yace ce wata yarinya ce mukahad'u da ita a makaranta naji ina mutuwar sonta, Kamarku d'aya da ita sak, Duk damuwarda kukaganni nashiga kwana biyun nan, duk a kantane, Ina tunin a raina cewa kamar Bilkisu ce domin kamarku haryab'aci, kinsan tunlokacin da Bilkisu nak'ara rabona da ganinta. Fahad yace "ina zakasanta tunda bakason zumunci, Farkon ganinka da Bahijja ai kasa ganeta kayi sai daga baya sannan kaganeta, Adnan yayi murmushi a zuciyarsa yanason ya tabbatar da Bilkisu 'yar uwansa ce?" Itace k'auwar bahijja kuwa?" domin yasan kalar hukuncin da zai d'aukar mata, dan yayi alk'awali da rayuwarsa tunda tayimasa k'azafin yatashi yin rapean d'inta, A gaban bainar jama'a to tabbas tunda hakan takeso zai aikatashi a kanta, ko kuma yayi mata abunda yafi rapean ciyo." Yace Anty Bahijja don Allah kid'an nunamun photo nan Bilkisu a wayarki nagani, domin na tabbatar da k'auwatace tashiga birnin zuciyata. Dariya sukashiga yimasa gaba d'ayansu, Fahad yace Ashe soyayya ce take neman ta zautarmun da d'an uwa, muka rasa gane kansa a gidan nan, Bahijja ya takamomasa photo nan Bilkisu tanuna masa tace kaganta nan, Allah yasa dai itace tanemi zarar dakai, Yayi dariyar da tafi kuka ciyo shekad'ai yasan abunda ke zuciyarsa, Ya amshi wayar yashiga diba photo nan Bilkisu, Ganin photo Bilkisu dayayi ya tabbatar da ita d'in daice, yayi saurin mik'ewa tsaye yana fad'in tabbas itace itace wlh, Gaba d'ayansu dariya suke masa a ganinsu ya zare a soyayyar Bilkisu. Cikin dariya Bahijja tace zauna mana Adnan muyi magana. Sai a lokacin ya nemi wuri ya zauna, Tareda cewa Anty Bahijja kuna kama da ita sosai, Inason natuna da wani abun shin Ku biyu ne 'ya'ya mata a wurin Ammi ko?" Bahijja tace kwarai kuwa, mu uku ne 'ya'ya a wurin Ammi yaya Abdulraham shine babba sai ni, sannan kuma Bilkisu ita k'arama a d'akinmu wadda gaba d'aya halinta ya babbanta da nakowa a familynmu, Saboda kyawawan halayanta maimartaba yafi sonta a cikin 'ya'yansa. Yacije baki yace Anty Bahijja inason Bilkisu kuma aurenta zanyi, Wlh idan bansamu Bilkisu ba zan iya rasa rayuwatah. Kitaimakeni Anty Bahijja kibani Bilkisu. Dariya sukadinga yimasa gaba d'ayansu lokaci d'aya duk yafita hankalinsa a kan soyayya, Fahad yadafa kafad'arsa yace "ka kwantar da hankalinka Adnan indai Bilkisu ce kasanyawa rayuwarka tazama matarka, Yanzun katashi katafi kaji kiranda maimartaba yake maka daga can kafad'amasa k'udirinka a kan Bilkisu. Mi'kewa yayi yanufi sashin maimartaba, a zuciyarsa kuwa yana Addu'ar Allah yasa kudirinsa ya cika."
.
Dashigarsa sashin maimartaba, Ya tarar dashi zaune rik'e da jarida a hannunsa yana karatu. Sallama yayi masa jiki ba gwari yashiga cikin d'akin, Yanemi wuri ya zauna a k'asan gefin k'afar maimartaba , ya sunkuyar da kansa k'asa, yace "Allah yataimakeka Allah yakara maka lafiya ranka ya dad'e gani yarima Fahad yace kana nemana. Maimartaba ya maida kallonsa akan Adnan yaga duk yarame masa yayi bak'i. Sannan yayi kyaran murya yace "Adnan waimeke damunka?" Kwana biyu na lura dakai bakacikin hankalinka?" Meke damunka wadda mu mahaifanka bazaka iya fad'a mana shiba, Tun shekaran jiya nasanya d'an uwanka Fahad yakiramun kai domin mutattauna akan tafiyar da zamuyi a gobe zuwa yola, domin nemawa Fahad auren Bahijja, Amma dazarar antukari d'akinka sai aji kofa a rufe harka fita." Ina kake zuwa?" Meke damunka wadda a matsayinmu na mahaifanka bazaka iya fad'a mana Shiba?" Adnan yasunkuyar da kansa k'asa yace "ranka ya dad'e tuba nakeyi, Munkun fara jarabawa karatu ne yake hanani sukuni kwana biyu nan, kayi hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwaba, tuba nakeyi. Maimartaba yayi murmushin jin dad'i Yace "meye shawararka na tafiyar da zamuyi yola gobe Neman auren Fahad da Bahijja?" Banida wani buri a rayuwata illah naga na aurar daku lokaci d'aya dakai da d'an uwanka, amma kai har yanzun ba kasamu matar da kakeso ba, Mamynka tasha nema maka 'ya'yan k'awayenta amma gaba d'ayansu bbu wace tayi maka a rayuwarka, Adnan yakuma sunkuyar da kansa k'asa yace Allah ya taimakeka ai nesa tazo kusa, Murmushi jindad'e yayi, yace "Allah yasa cemun zakayi kasamu matar aure, danafi kowa jin dad'i, Sai na had'aka da d'an uwanka na aurar daku gaba d'aya. Adnan yayi murmushin jin kunya, yace "kusan hakan ne ranka ya dad'e, Maimartaba yace "Alhamdulillah. 'Yar waya?" A wace unguwa take?" Waye mahaifinta?" Adnan yayi murmushi ya sunkuyar da kansa, yace Allah ya taimakeka k'auwar Bahijja ce Bilkisu, tare muke karatu da ita, kuma munfahimci junanmu tana sona Nima inasonta, Abba ka taimakamun karnasa Bilkisu. Maimartaba yace Alhamdullah abu yazo gida kenan, amma naji dad'i sosai Allah yasa abukanin arzikinkune. Murmushi yake yana cike da jin kunya ya amsa da Amin Abba, Mikewa tsaye yayi zaitafi d'akinsa, yace Abba natafi sai da safe, gobe tafiyar safe zakuyi kuwa?" Maimartaba yace "tafiyar safe nakeso muyi in Allah ya yarda. Allah ya tsareku Abba ya kuma kaiku lafiya dawo mana dakai cikin koshin lafiya. Cike dajin dad'i Abba ya amsa da Amin Adnan. Yafito yanufi d'akinsa shekad'ai yasan abunda ke cikin zuciyarsa. Shigarsa d'akin yacire kayansa, yana mai dariyar mugunta yana fad'in gimbiya Bilkisu kenan kinshigo hannuna zanwula k'antaki yanda naga dama, domin ba d'igon sonki a cikin zuciyata ko d'aya, kuma dole kiyi biyayya saboda kina k'arkashin inuwar aurenah, Zanyi amfani da wannan damar na aure ki domin nad'auki famsar abunda kika aikatamun a gaban bainar jama'a. Ya kuma yin murmushin mugunta, yacije baki, yace "nalura da idanunki saikin buk'atar d'a namiji, da wannan zanyi amfani, na azabtardake azaba mai tsanani, saikinyi danasanin aurenah rayuwarki." Yayi kwanciyarsa yana tunanin mugunta iri iri a rayuwarsa." Maimartaba sarki Bashir mahaifinsu Adnan yasauka garin yola lafiya, Inda yasamu tarba da karramawa a masautar yola, Yayi farin cikin karramashi da akayi, Daga nan yashiga fad'awa mai martaba abunda ke tafe dashi." yazo neman auren Bahijja da Bilkisu, Sarki Abdulraham yaji dad'i kuma yayi farinciki da zuwan nasa, yace " aidakayi zamanka ba saikazoba ko aike kayi ya wadatar, kuma Bahijja da Bilkisu 'ya'yankane duk yanda kazartar da hukunci a kansu dai dai ne, ba saika taso tun daga kano zuwa yola nemawa Fahad da Adnan aureba. Amma wani hanzari ba guduba, 'yarka Bilkisu karatu takeyi bansaniba ko Adnan zai iya jiranta harta kammala karatun nata sannan daga baya sai ayi bikin nasu, a lokacin ta mammals karatun nata. hakan naga yafi. Sarki Bashir yayi murmushin jin dad'i yace Bakomai hakan da katsara yayi dai dai zanje na shawarci Adnan idan yanada ra'ayin barinta karatu bayan anyi auren saitaci gaba da karatun dama kuwa makarantarsu d'aya. Murmushi sarki Abdulraham yayi yace "hakan shine daidai idan ya amince sai ayi auren gaba d'aya, Nima zankira Bilkisu domin naji ra'ayinta a kan hakan, A haka sukayi sallama suka rabu cikin farin ciki da kewar juna. Bilkisu kwana biyu hankalinta ya kwanta ta natsu karatunta tasanya a gaba, domin sunkusan fara exam, tsakaninta da prince sai dai kallo, itama mamaki yakebata domin gata gashi sai dai yarab'ata yawuce itama hakan, Tana mamakinsa amma a zuciyarta bata yarda dashi ba domin tasan a kwai wata kullanliya dayake kullawa a rayuwarsa, Ita kuma ta d'auki d'amarar duk abunda yake nufi tafishi jinsa.
.
A haka suka cikagaba da zama da prince a makaranta babu be kula wani daga cikinsu, Abu d'aya yake damunta dashi a kullum idan suka had'u sai yayi mata wani kallo nasama da k'asa sannan yacije baki yayi tafiyarsa, abun yana bata mamaki amma bata kulashi." Seefana tace "sister naga mutumin naki kwana biyu nan ya daina kulaki?" Kodai yaga baya iyawa da fitinarki ne?" Domin kema idan yayimaki bakyaleshi zakiyiba, Bilkisu tayi dariya tace " nasan bazai barniba domin inaji a rayuwata da kwai abunda yake shiryawa, domin nasan halin Adnan sarai baya barin bashi, Wayar da kecikin jaka ta d'auki ruri, ita takatse masu maganar da sukeyi da safeenat, Sauri bud'e jakarta tayi domin tasan Abbantane ke kiranta domin ringing d'insa daban ne tasanya masa, Takara wayar a kunnenta tare dayin sallama ta gaidashi cikin fara'a dajin dad'i, Abba shima cike da farin ciki yake amsa gaisuwa gimbiya Bilkisu, Bayan sunk'are gaisawar Abba yake shaida mata da tashigo mota gobe yana son ganinta akwai maganar da yakeso yayi da ita, Bilkisu tayi mamaki sosai take tambayarsa Abba lafiya kuwa?" Ina Ammi nah take?" Yayi murmushi yace "Ammi ki lafiyarta k'alau gata a kusani, taja wani dogon ajiyar zuciya, Tace Abba bata wayar mu gaisa naji muryanya, Abba yamikawa Ammi waya suka gaisa, sannan zuciyar Bilkisu tayimata sanyi, Tace "insha Allah gobe zamuyi asubanci mutafo tareda fadawa gaba d'aya, Abba yace "yawwa gimbiya Allah yayi maki albarka, yakawoki lafiya, tace "Amin Abbana sukayi sallama, Bayan ta k'are waya da Abbanta, takira fadawa take shaida masu gobe su zama cikin shiri yola zasu tafi, kuma tafiyar safe take buk'ata suyi, su tabbatar da sunwake motocin da zasuyi tafiyar dasu, Suka amsa mata da angama ranki ya dad'e, Takashe wayarta tasanya a jaka, Takai dibanta ga Safeenat tace "sister gobe fa yola zantafi Abba yana nemana amma ina ganin kwana d'aya zanyi saboda munkusan fara jarabawa, Safeenat tace "sister Allah yakaiku lafiya ya kuma dawo dake lafiya, Bilkisu ta amsa da "Amin." Ashe duk maganar da sukeyi a kan kunnen Abdullah da yazo giftawa ta wurin yaji Bilkisu na waya, tana fad'in to Abba insha Allahu gobe da sansafe zamuyi asubanci mutafo tare da fadawa." Ai kuwa Abdullah yaja gefe d'aya ya tsaya inda bata iya ganinsa saida ta kammala wayar, Har maganar da sukayi da Safeenat duk a kan kunnensa, ya fahimci gobe yola zata tafi kenan?" Aikuwa yashiga jin dad'i domin bazai yarda ba dashi za'atafi baza'a barshi garin Kano ba, Juyawa yayi ta bayanta yayi tafiyarsa gida yashiga harhad'a kayansa gobe sai yola, domin ba zai yardaba k'afarsa k'afar fadawa ko a but ne ya amince a sanyashi a tafi dashi yola, Wasa wasa Abdullah beyi barciba Allah Allah yake safiya ta waye masa yagansa a mota sunmik'i hanyar yola,. Dakyar yasamu asuba tayimasa tun kafin mahaifinsa ya fito zuwa masallaci Abdullah yarigashi fitowa rataye da jakar kayansa yayi saurin bud'e gida yanufi masaukin fadawa, Yana isa k'ofar gidan ya tarar da motoci Jere har basa k'irguwa, sunbi layi alamar ba'a jima da gama wankesu ba, Yakai dibunsa a gaba d'aya motocin saida gabansa yafad'i, A zuciyarsa kuma yace "Alhamdulillah Ashe inada Rabin zuwa masarautar su Bilkisu, Yadiba gabas da gamma gudu da arewa bega alamar mutum ko d'aya ba, Ya fahimci cewa suna masallaci sallah sukeyi, A can ya hango wata mota rab'e gefe d'aya ya rataya jakar kayansa yanufi motar yayi tsaye, ya kai dibansa a cikin motar yahango rubar ruwan faro, Yabud'e murfin motar ya d'auko robar ruwan yayi arwala ya tayarda sallah a bakin motar, domin da zarar yashiga masallaci to kafin yafito suna iya tafiyarsu subarsa, Bayan ya k'are sallah ya bud'e murfin motar yayi shigewarsa gidan baya rungume da jakar kayansa, ya d'au minti biyar a motar, saiyaji zafi yayi masa yawa, yashiga zuge glass d'in motar domin iska yashigo masa, Aikuwa anan take sanyin asuba mai had'e da iska mai dad'i yashiga ratsashi, dama besamuyin barci jiyaba, Abdullah yasaki baki da hanci sai kwasar barci yakeyi rungume da jakar kayansa."
.
Gimbiya Bilkisu ta shaidawa fadawa cewa da zarar sun kammala sallar asuba zasu wuce, Haka kuwa suna k'are sallah kowannesu ya shiga motarsa suka nufi gidan Bilkisu domin d'aukarta suwuce. Koda suka isa gidan Bilkisu tareda jakadiya har sun kammala shirinsu tsaf suka fito sukashiga mota suka d'au hanyar." Abdullah nacan cikin motar mutane yasaki Baki da hanci sai kwasar barci yake harda yawun barci Saiji yayi ankwankwasa murfin motar a zabure ya farka cikin gigin barci yake fad'in ankawo yolar?"
.
Bud'e idonsa da zaiyi yayi arba da wani k'aton soja bak'i sed'ik dashi dawani k'aton ciki idanunsa jajir,sai wani huci yake, ya kai dibansa ga Abdullah yace "ubanwaye yashigo dakai cikin motanah?" Abdullah sai da cikinsa ya d'uri ruwa, yafito cikin motar ya maida idonsa a k'ofar gidansu fadawan yaga bbu motocin da yagani d'azun har sunyi tafiyarsu yola kenan, yad'ora hannu a kai ya kurma ihu, Soja narik'e da kwalar rigarsa yana cewa "yakama b'arawo cire belt d'in wandonsa yayi yana neman zugawa Abdullahi shi, Abdullah saibada hakuri yake gashi bayada wuyar sakin fitsari, Aikuwa soja na d'aga belt daniyar zugawa Abdullah, sai ga fitsari yadinga zuba a wandonsa yarik'e belt d'in, mutane ne suka zagayesu suna tambayar abunda ke faruwa aikuwa Abdullah yanasamun sa'ar soja ya gantsaramasa cizo a hannu soja yakwatsa ihu, yasaki Abdullah ya yana diban hannunsa, Shikuwa Abdullah ya zuba da gudu yabar jakar kayansa a motar soja
.
Gudu yake akan titi yana motsa jininsa, Dama haka al'adarsa take, dazar yayi sallar asuba tunkafin safiya tawaye, kafin mutune sufara firtuwa, Prince yake gudun a kan titi domin motsa jininsa, Yauma hakan takasance gudu yake a kan titin, saiji yayi mota ta bangajeshi, tayi sama dashi ta yafar akan titi, Tundaga lokacin Be kuma sanin inda kansa yakeba, Mai motar kuwa Yakama gabansa yayi tafiyarsa, yabar prince kwance cikin jini kota ina zubar masa yakeyi, Gimbiya Bilkisu tareda fadawanta a kan hanyarsu ta barin gari, Sun iso daidai wurin da abun yafaru, Ganin mutane sunyi cincirindo a tsaitsaiye yasa ta kai dibanta a wurin taga mutane sun tsaitsaya alamar wani abun suke kallo, Tayi saurin d'agawa fadawa hannu alamar su tsaya." tabasu umurni sufita suga meke faruwa?" taga mutane tsaitsaiye a kan titi?" Wasu daga cikin fadawan suka fito, suka nufi wurin da abunyafaru, sukaga mutum a kwance cikin jini, anrasa mai taimakamasa." Sukayi saurin nufo Bilkisu dake cikin mota a zaune, suna shaida mata, da cewa Hatsarine ne yafaru ranki ya dad'e, wadda kuma abun yafaru a kansa yana buk'atar taimakon gangawa domin duk mutanen dake wurin tsoron tab'asa suke. Tayi saurin bud'e murfin mota tafito, tana bada umurni da a d'aukeshi a nufi asibity dashi, Nan take fadawa suka tallebesa a kasanyashi a mota suka nufi asibity dashi, Asibitin kud'i suka nufadashi, Bilkisu tabada ATM CARD d'inta akaciro mata kud'i ta dank'awa d'aya daga cikin fadawan kud'in, tabashi umurni duk abunda ake buk'ata yayi amfani da kud'in asaya. Takoma warta mota tayi zamata tareda jakadiya." Likitoci suka kawowa prince taimakon gangawa, suka tallabesa suka nufi d'akin da za'a dibashi. Prince kwance cikin jini kamar bayada rai saiwani numfashin wahala yake fitarwa, Likitoci tsaitsaye a kansa domin ceto rayuwarsa, Babban likitan yabada umurni da akiramasa d'aya daga cikin wad'anda suka kawosa, Fadawa suka nufi ofishin likita yake shaida masu majinyacinsu yana buk'atar asanyamashi jini da gangawa, Idan ba hakan ba yana iya rasa rayuwarsa a kowane lokaci, domin jininsa yakusan k'arewa ajikinsa, Dan haka aje cikin 'yan uwansa a nemo wasu daga ciki wad'anda jininsu yayi daidai danasa sai a d'ebeshi a sanya masashi, Fadawa suka fito suka nufi wurin gimbiya Bilkisu suna shaida mata abunda likita ya fad'amasu, jini ake buk'ata asanyawa mutumin da suka kawo, A razane tafito a motar tana kallonsu, d'aya bayan d'aya tace, to Ku meye amfaninku da bazaku bada jininku a sanyawa musulmi d'an uwanku domin ceto rayuwarsa ba?" Kallo suka bita dashi cike da jin tsoro, Fahimtar haka da tayi daga garesu yasa, Tarab'asu tawuce cikin sauri tanufi ofishin likita, Tura k'ofa tayi tashiga tareda yimasa sallama, bata jira amsawarsa ba, ko kuma ya bata umurnin zama ba, Taja kujera ta zauna, Likita saibinta yake da kallon mamaki, Yace malama lafiya?" Daga ina haka?" Takai dibanta a wurin likita tace " yi hakuri docter banyi maka bayanin koni wacece ba, wlh duk a rud'e nake, Marar lafiyar damuka kawo yanzun, wadda ke buk'tar jini cikin gangawa, shine nazo domin a d'ebi jinina a sanya mashi, domin idan akatsaya Neman 'yan uwansa zai iya rasa rayuwarsa, Don Allah docter kayi Sauri ka auna jinina idan yayi daidai danasa a sanyamashi. Likita yatsora mata ido cike da mamaki, yace "idan son samune munfi buk'atar asanya masa jinin namiji a kan na mace, Saboda mace tana haihuwa kuma tana zubarda jini duk k'arshin wata, Mik'ewa tsaye tayi cike da b'acin rai, tace "dakata Docter ✋ kaifa kace yana cikin mawuyacin hali mutuwa ko rayuwa?" Amma kakeyimun wani dogon zance, magana d'aya nakeso kafad'amun, Ana iya d'ibar jinin mace a sanyawa wani koba'a d'iba?" Docter yace ana d'iba amma idan mace ta jima bata haihuba, Bilkisu tace "toni bantab'ayin aure ba bare na haihu, Docter sanyamun abun d'ibar jini, kad'iba kak'arawa bawan Allah karya rasa rayuwarsa. Da Sauri likita ya d'auko kayan aiki ya kwantar da ita kan gado yashiga d'ibar jininta. Bayan minti talatin ta tashi daga kan gadon, fadawa sai sannu suke jera mata. Ganin likita tayi a gabanta yana mata sannu had'i dayimata tambayoyi, Babu abunda kikeji a jikin?" D'aga masa kai tayi tace "banajin matsalar komai docter. Yace "Alhamdulillah mund'ebi jininki roba biyu, Asanya masa wadda insha Allahu munasaran farkawarsa nan da awa d'aya, Tace "Allah yabashi lafiya." Likita ya amsa da "Amin." Ya kuma kallonta yace "amma ke matarsa ce ko?" Domin a zamanin damuke ciki babu wadda zai iya taimaka maka da jini sai mahaifiyarka, ko kuma matarka, kodai wani d'an uwanka koshi d'an uwanka najini, Bilkisu tayi murmushi tace niba matar sabace, ba kuma 'yar uwarsa bace, Asalima bansan koshi wayebane, Domin har yanzun banga fuskarsaba, tsoho ne, ko yarone, bansaniba, taimako nayimasa saboda Allah domin duk wadda ya taimaki wani Allah zaitaimakesa." Pls 'yan uwana kutaimakamun da addu'a idanuna ciyo yakemun sosai
.
Bilkisu ta sauka garin yola lafiya, Inda dukkanin wad'anda ke cikin gidan masarautar yayi murna da farin cikin dawowarta. Bayan tayi wanka tashirya taci abinci, ta sauko k'asa tanufi sashen maimartaba domin taji Neman da yakemata, Ta Tarar da maimartaba kishin gid'e a kan kujera, Tayi sallama tashiga. Tasamu wuri a k'asa gefen k'afarsa ta zauna, ta sunkuyarda kanta k'asa tace "Allah ya taimakeka Allah ya k'ara maka lafiya, Gani nazo ranka ya dad'e Allah yasa ba laifi tanayiba, Maimartaba yayi murmushin nan irin nasu na manya, Yace "aibakya laifi Bilkisu, Domin kina kiyaye duk wani abuda kikasan zaib'amun rai, Dan haka nafifitaki a cikin 'ya'yana. Wato Bilkisu wata shawara nakeso muyidake wadda maganar waya bata isa, Saikinzo gani gaki. Bilkisu kinsan d'an sarkin kano, Fahad shiyakeson Bahijja, Ta girgiza kai. To satinda yawuce mahaifin yaron wato sarki Bashir, yazo da kansa ba aike yayiba, yazo neman aurenku keda Bahhija. Saida gaban Bilkisu yafad'i Yaci gaba da cewa Kema d'ansa Adnan yaganki a makaranta, yanunamun dacewa, harkun fahimci junanku, dan hakan nayanki hukunci aurardaku gaba d'ayanku keda Antynki Bahijjah. maimartaba magana yakeyi amma gaba d'aya hankalinta bayajikinta, musamman dataji ya ambaci yabadasu gaba d'ayansu, Idanunta ne suka cika da hawaye tasunkuyarda kanta k'asa yadda Abbanta bazai iya ganin hawayentaba, Maimartaba tunda yafara yin magana yake kallon yanayinta yalurada lokaci d'aya tacanza masa daga k'arshe hawaye take zubarwa, Yace subahanallahi Bilkisu laifi?" Meyasanki zubarda hawaye?" Goge hawayenki kidaina kuka, Idan maganar aure ce bakyaso daki zubarda hawayenki k'ara afasashi, Nima abunda yak'arabani kwarin gwaiwar yimasa alk'awalin badake, yazomun da mgnar cewa kunfahimci junanku a makaranta dake da yaron. Amma wallahi Bilkisu mundun bakyaso to alk'awari ne bazan maki auren dole ba, Kanta a sunkuye k'asa sai zubarda hawaye take, Gaba d'aya tausayin mahaifinta duk yagama lunlub'eta, a zuciyarta, Wato domin ya faranta mata rayuwa yana iya ruguza alkharin dayayiwa sarki Bashir nabayardasu dayayi gaba d'ayansu, Abba idan yayi haka kuma har abada sarki Bashir bazai kuma yarda da maganarsaba, Sannan kuma idan yayi hkan, yaya k'auwarsa sarki bashir Amminmu zaji dad'i wadda suke uwa d'aya uba d'aya, da sarki Bashir, Zai iya zamantuwar rugujewar zumcinsu, Maimartaba yace "gimbiya Bilkisu kenake saurare, kukan da kikeyi nameye?" Takuma sunkuyar da kanta k'asa tace"Abba karatuna banaso nayi aure batareda na kammala karatunaba, Abba inaso nayi karatu sosai domin nataimaka 'yan uwana mata takowace hanya, Abba yace "nasan kudirinki a kan karatunki, gimbiya Bilkisu, Nayiwa sarki Bashir bayanin karatunki, Yace zai tambayi Adnan d'in idan yaji yagani ya amince zaibarki idan akayi auren saikici gaba da karatunki Idan kuma be aminceba to lallai bazan auran dakeba sai bayan kin kammala karatunki har lokacinda burinki yacika, gimbiya Bilkisu, Murmushin dole ta k'wakwalo tayi, had'ida kallon mai marmarba, Tace nagode Abba, Yace "goge hawayen kitashi kitafi kikwanta kihuta nasan kinsha gajiyar hanya, Tamik'e tsaye had'ida yimasa sai anjima, Tafita daga d'akin, Tafiya takeyi kamar wadda kwai yafashewa a cikin domin gaba d'aya batacikin hankalinta, da kyar tasamu ta isa d'akinta cikin mawuyacin hali. Akan gadonta tafad'a tasaki wani wahalallen kuka mai tsuma zuciya, Tana magana ita d'aya kamar wata zaranriya, Ashe dama Adnan d'an uwanane yake wulak'antani hakan?" Meyake nufi da turowa Neman aurena?" Wani sabon salon wulak'anci dacin zarafi zaikuma yimun bayan ya aureni?" Domin a bakinsa yasha furtamun bayasona, bayason ganina, Me kama danima idon ya ganta sai ya hukuntata, Sannan ace da wannan zanyi rayuwar aure?" Takuma b'arkewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya, Tana danasanin had'uwarta da Adnan a rayuwarta gashi yanzun yana neman ruguzamata rayuwa." Adnan kuwa gaba d'aya yasusuce baya da maganar kowa sai ta Bilkisu, Anty Bahijja ke k'ara kwantar masa da hankali akan cewa Bilkisu insha Allahu takusan zama matarsa, Likita ya turo k'ofa yashigo had'ida yimasu sallama yanufi gadon Adnan domin ya ciremasa rubar jinin da ke hannunsa, Doctor yakai dibansa ga Adnan yayi murmushi yace " Adnan angon Bilkisu ina fatan ba abunda kemaka ciyo domin munasan ran sallamarka nan da zuwa gobe, Adnan kwance yake amma jin doctor ya ambaci Bilkisu yayi zumut ya mik'e zaune, Yana murmushi yace doctor kokasan Bilkisu ne?" Kaga mundace da juna ko?" Gata fara kyankyanwar yarinya mai dogon hanci, ga k'aramin baki,
.
Yace "doctor kaga Bahijja yayi nuni da Bahijja yace kamarsu d'aya da Bilkisu na, Amma Bilkisu tafita kyau, Gaba d'ayansu dariya suke masa ganin yanda soyayyar Bilkisu ta kusa zautar dashi, Bahijja tace, ayye Adnan yanzun Nice Bilkisu tafini kyau?" To lallai bazan baka aurantaba nafasa, Aisai ganinshi tayi durk'oshe a gabanta rik'e da k'afafunta, yana fad'in "yi hakuri Anty Bahijja ki aura mun Bilkisu wlh idan narasa Bilkisu zan iya rasa rayuwata, Sai a kunnen maimartaba, yace bazaka rasa ranyuwarka ba Adanan indai akan Bilkisu ne domin munyi mgana da mahaifinta yabaka Bilkisu amma dasharad'in sai ta kammala karatunta."
.
Adnan yace "dady kataimakamun karnarasa Bilkisu wlh idan narasata zan iya rasa rayuwa, A yanda nakeji Bilkisu itace rayuwata rashinta a gareni komai zai iya faruwa dani, pls dady kataimakamun. rik'e yake da k'afar dady yanayimasa magiya, Maimartaba ya dafashi ya mik'ar dashi tsaye, tareda rungumeshi a jikinsa, cike da tausayin d'an nashi, ganin yafad'a tarkon soyayyah. Yace "Adnan nafad'amaka ka kwantar da hankalinka Bilkisu tazama matarka, Koyanzun idan kashirya za'a d'aura maka aure da Bilkisu amma da sharad'in zaka barta tacigaba da karatunta, Idan kuma baka buk'atar matarka tadinga yawun makarata to kak'ara hakuri har lokacinda ta kammala karatun nata sai ayi bikin naku. Pls Adnan kadaina damun zuciyarka da yawan damuwa, Domin kaji bayanin da likita ya yimuna akan cewa ciyon zuciya ne yakeson kamaka saboda yawan tunanin da kakeyi, Adnan yace "dady nayarda a aura mun Bilkisu zanbarta tacigaba da karatunta daga nan har k'asar waje idan tana buk'ata, wlh dady nayimata alk'awari zankaita domin tayi karatunta, Ya juya ya kalli Bahijja dake zaune duk tausayinsa yama lunlub'eta, Yace dady ga Anty Bahijja nan itace shaidata zanbar Bilkisu tayi karatu." Dady yace "toshikenan tunda ka amince zamuyi waya da mahaifin nasu, sai nafad'a masa yanda mukayi dakai kaga daga k'arshe sai a sanya ranar aurenku lokaci d'aya tare da yayanka fahad gaba d'aya. Murmushi yayi harsaida hak'oransa suka fito, cike da jin dad'i yace nagode dady." Gaba d'ayansu suka sanya dariya." Bilkisu ce keshir shirenta domin komawa makaranta, ta kamalla shiryawa, tsaf. amma zuciyarta cike take da kunci domin tun jiya kobarci bata samutayiba, saboda tashin hankalin maganar da Abba yayi mata na auren Adnan, D'akin maimartaba Tanufa, domin yimashi sallama, Tura k'ofar tayi tareda sallama, Ta isa kusa dashi ta durk'usa k'asa tareda sunkuyarda kanta, "tace Abba barka da hutawa. Allah yataimakeka Allah ya tsare mana lafiyarka Abba nashirya zan koma makaranta. Abba yatashi daga kwancen dayake, yana mai murmushi a fuskarsa yace "gimbiya Bilkisu harkinsherya?" Sai makaranta yanzun ?" To Allah yakaiki lafiya, Allah ya tsaremumke a duk inda kike , Ina alfahari dake Bilkisu a cikin 'ya'yana domin jajircewarki a kan karatunki, Allah yabaki ilimi mai amfani." Tasunkuyar da kanta k'asa tana mai zubar da hawaye, tace "Amin Abbah. Maimartaba cikin rashin jin dad'in ganin hawayenta yace "Bilkisu mekikeyiwa kuka?" Meke damunki?" Tun lokacin da nayimaki mgnar auren d'an gidan sarki Bashir naga kinshiga wani yanayi natashin hankali bayan kuma ance kunfahimci junanku tun a makaranta, Bilkisu waimeke damunki ne?" Takuma sunkuyarda kanta tana mai shinshikar kuka, data tuna da cewa wai Adnan ne zaicewa sun fahimci juna dashi. yabiyo ta wannan hanyar ne domin wata mummunar manufa tashi, ya aureta don yaji dad'in wulak'antata, amma tayi alk'awari a rayuwarta bazata tab'ayiwa mahaifinta musuba, kuma bazata tab'a sanyashi yaji kunya a idon jama'a ba, bazan tab'a barin Abbanah yazama mai magana biyu, amma zata nemi alfarma a wurinshi, wadda tasan zaiyimata ita. Tasunkuyar da kanta k'asa, tace " Abba babu abunda yake kedamuna, Amma don Allah Abba ina Neman alfarma a wurinka. Cikin yanayin tausayi, yace "fad'i Bilkisu ina saurarenki, Tace "Abba don Allah katausayamun koda sun aikoma da cewa A d'aura aurenmu tare da Anty Bahijja, Abba don Allah kataimamun kar d'aura dani, Harsai na kamalla karatuna sannan. pls Abba kataimamun ta kuma fashewa da kuka, Abba yace "share hawayenki Bilkisu bazantab'ata yimaki abunda bakyasoba, Tunda kinfi buk'atar saikin kammala karatun naki sannan kiyi aure, to shikenan sai ayi na antynki Bahijja daga baya sai a yinaki bikin, Hakan yayi maki kuwa? D'aga kai tayi had'ida yin murmushi jindad'i, tace "ngd Abbah Abba shima murnushin yayi yace "daina yimun godiya burina shine akullum naga nafarantamki rai yanda kema kike k'okarin farantamun nawa ran, . Tashi kitafi kar dare yayi maki a hanya. Tamik'e tafita had'ida yimasa sallama, Adnan jiki yayi kyau ansalameshi a asibiti, Dashigarsu gida ya fad'a d'akinsa ya yayi wanka yayi kwanliya ta d'aukar hanka, Sauri kawai yakeyi isa makaranta domin yayi ido biyu da Bilkusu, Motar Abbansa yashiga wadda tafi motarsa komai, da shigarsa motar ya kalli fuskarsa a madubi yaga yayi kyawon da betab'ayin irinsaba murmushi yayi a ransa kuma sai cewa yake dole ne idan Bilkisu ta ganni taji itama takamu da matsanancin sona, Yaja motar yanufi makaranta, domin Neman Bilkisu, Dashigarsa makarantar mazaje group sai kuwa sukeyi naganinsa, amma be kulasuba sai waige waige yakeyi shidai burinsa yayi ido biyu da Bilkisu."

0 comments:
Post a Comment