*Daga sahal dan sa'ad Allah ya yarda da shi yace''wani mutum yazo wajen manzan Allah S A W,sai yace,ya manzan Allah,nuna min wani aiki wanda idan na aikatashi Allah zai soni mutane zasu soni?,sai manzan Allah S A W yace: KA GUJI DUNIYA(dadin dake cikinta da qyale qyalenta) Allah zai soka,sannan KA GUJI ABUN HANNUN MUTANE MUTANE ZASU SOKA*
*_ruwayar ibnu maaja_*
Sam taqi dubansa,hidimad gyara gurin da suka kammala cin abinci kawai takeyi,ya san tana sanen rayi haka
''idan kinsan wata baki san wata ba yammata,duk abunki sai na dan more kan na tafi''ya fada cikin zuciyarsa yana danne danne waya,kansa ya dago kamar wanda ya tuna da wani abu da gaske ya dubeta
''af,maryam,taimakamin ki dauko mim wasu takaddu cikin cupboard please''kamar ba zata je ba haka taji saboda kunyar idon mami amma sai taga mamin ma ta sauko daga kan dining din ta koma cikin falo tayo zamanta kan kujeru,ba tare da tace komai ba ta miqe ta nufi inda ya aikata din.
Ta kusa aqalla minto goma tana dube dube cikin dakin nasa amma sam bata ga abinda yake fada din ba,dole ta juyo ta fito don ta sanar masa,a kusa da maminta tadda shi yana zaune yana nuna mata abu a waya,ta dan rusuna kadan''ban gansu ba''tace da shi,ba tare da ya dago ya dubeta ba yace
''ki sake dubawa dai da kyau,suna nan ciki ko locker din mirrow dina''a yanzu kam jikinta ya fara bata aiken bogi ne,don iya dubawa tq duba ko ina din,amma sabida bata son musu yasa ta miqe ta koma.
Ko minti biyu batayi da komawar ba ya dafe kai yana fadin
''af,na manta asge na sauya musu gu shi yasa ta kasa ganinsu,bari naje na dauka''ya fada yana satar duban mami,bata ko dubeshi ba har ya miqe yayi hanyar dakin,binsa tayi da kallo tana murmushi can qasan ranta tana fadin''dama ai bazan hanaka kebewa da matarka kuyi sallama a abdallah'',tattare itama ya nata ya nata tayi ta haye sama abinta
A hankali cikin sanda ya tura qofar dakin ya shiga,tana duqe ta duqufa neman takardu
''har yau maryam ke yarinyace na yarda da hakan ba wuya a miki wayo''ya fada cikin xuciyarsa
jingina yayi da qofar ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta son ranshi,sai datq gaji da dubawa kana ta dago,ta juyo da niyyar fita amma hankalinta na kan gado tana dubawa ko nan ya ajjiye,dalili kenan da yasa bata ganshi ba har sukayi karo,baya ta ja da sauri,tana yarfe hannunta tace
''na duba ko ina ban gansu ba nikam''.
Hannun nata ya kama yana fadin
''ba wasu takardu dama,son ganinki kawai nakeyi dama kafin nawuce,ma tabbata idan ba haka ba bazaki bari na ganki din ba sai a gaban mami''
so take ta qwace amma ya gwada mata qarfi irin na 'yan maza sai da ya kaita gefan gado ya zaunar da ita kana yayi tsalle ya fada gadon,kwanciya yayi ruf da ciki,kanshi ya dora saman cinyarta ya saka hannayenshi ya zagaye qugunta,ya gama kanainaye jikinta bata da ikon motsi
''ummm,baby,har yau bansan matsayina a gunki ba baby kin barni cikin duhu fa?''ta dan hadiye wani abu,yana nufin yace har yau bai fuskanci komai daga gareta na ko so yake sai ya qureta ya sata fadin abunda bata yi niyya ba
''ka riga da ka san matsayinka tuni a gurina ba tun yau ba''shiru ya danyi kana yace''na riga ni kuma da na manta baby,pls ki sake gayamin''.
Shiru ta sake yi don ya sakata cikin kokwanto biyu,idan ta buda baki abinda duk zata gaya masa ta tabbatarwa kanta qarya take a yanzu,idan kuma ta fadi gaskiyar wanne kallo zai mata,jin taqi cewa komai ya saka shi juyowa da sauri ya koma rigingine duka akan cinyar tata yana kallin fuskarta,sai tayi saurin runtse idonta,murmushi yayi ya saka yatsanshi ya lakace mata hanci
''yar qauye kawai,shi kenan tunda kin barni cikin duhu,idan kuma na mutu kafin na dawo burinki ya cika kenan ko?''
bata san lokacin da ta bude brown oily eyes dinta ta watsasu cikin nashi ba tana zazzaro su,shima kallon nata ya tsaya yi can qasan zuciyarsa wani sanyi na ratsashi
''mutuwa kum....''sai ta kasa idawa ganin yana sake fadada murmushinsa yana lumshe ido,idanun nata ta sake ja ta rufe ba tare da ta qarasa din ba
''a hakan ake so ace ba'a sona?,bansan lokacin da kika koyi yima kanki da kanki qarya ba''.
Bugun zuciyarta ya qara gudu jin yadda ya kama tafin hannunta yana mata tafiyar tsutsa,wani abu take ji yana bin jikinta,da hanzari ta janye hannun ba tare da ta bude idon ba,yana qoqarin sake kamowa tace
''ka bari,ba dadi''
''da dadi''ya fada cikin wara iriyar murya
cikin lokaci qanqani gaba daya yake son burkita mata tunani,hot kises ya dinga aika mata da su wadanda bata taba koda kin labarin irinsu ba,romancing dinta yake sosai kamar ba abdallah,duk da jikinta na amsar saqon amma a tsorace take matuqa hakanan bakinta bai mutu ba da fadar kalmar ''ka bari abdallah,bana so,ka bari don Allah''
ko kadan bai saurareta ba sai da ya ragewa kansa zafi,kallonta yayi idanunshi sun juye tamkar bugagge muryarshi ta koma can qasa sosai,a rufe idanunta suke gashin kanta da ribbom din ya dade ta zamewa ya warwatsu har fuskarta,wata kasala yakeji sosai a jikinsa don haka ya koma ha kwanta kamar dazu kanshi bisa cinyarta kwanciyar rigingine yana maida numfashi.
A hankali ta dinga bude idonta kamar mai tsoron cin karo da wani abun,ta dube abdallah dake kwance daidai kan cinyarta,idanunsa na a rufe numfashinsa na sauka a hankali,ta rabbatar bacci ne ya daukeshi,so take ta miqe amma ta kasa saboda gaba daya ya sakar mata nauyinsa,sai ta miqa hannunta ta dauki ribbom dinta ta hada gashinta guri guda ta dauki dankwalinta ta mayar,fuskarsa taci gaba da kallo,wani kyau baccin yayi masa sosai kamar ba mai bacci ba.
Ta riga ta yarda kyau kam Allah ya bawa abdallah shi,irin kyawun da ba kowa Allah ke azurtawa da shi ba
kusan awanni daya da rabi ya samu yana baccinshi tana zaune tamkar mai gadinsa duk motsinsa na kan idanunta,a haka taji an soma knockong qofar,ta fara qoqarin tureshi daga jikinta jin muryar mami ne amma qememe yaqi,tamkar ma yana sane sai ya sake kanannadeta abinsa yaci gaba da baccinsa,a hankali mamin ta murda qofar jinta abude yasa ta dan turo kadan tana sallama,amsa mata maryan tayi sai ta leqo da kanta,karo na biyu ta soma yunqurin maida shi gefe ta kasa cikin jin kunya,murmushi mamin ta mata kana ta mata alamar tayi shiru ta zauna kada ta tasheshi ta ja qofar ga rufe musu,ta sake kallon fuskarsa gumi taga yanayi duk da sanyin rabar dake dakin,tattausan tafin hannunta ta saka tana share masa tare da hura masa iskar bakinta,caraf taji an kama hannun naga an riqe,tsoro da kunya suka kamata sai tayi wuri wuri da ido,ya bude idonsa a hankali ya sumbaci hannun kana ya tashi zaune yana ambaton ''la'ilaha illal lah muhammadurrasululluh sallallahu alaihi wa sallam'' yana miqa
ya dubeta tana qoqarin miqewa yace mata
''sannu baby am sorry na danne miki cinya ko''bata ce komai ba tana qoqarin fita cikin zafin nama ya rigata isa bakin qofar ya saka key ya qulle,ta kalleshi cikin alamu na tambaya kafin ta furta tambayar ma ya bata amsar
''babu inda zaki je,idan kinga kin bar dakin nan nazo tafiya ne''sai ta bata fuska kana tace
''to waishin ma ni matarka ce?,bayan kace temporary ne''
girarsa ya dage kana yace''yes har yau matata ce ke,dole kici gaba da yimin abinda nakeso kafin lokacin da maryara zata iso''kasa magana tayi shi kuma ya zare key din ya jefa aljihun three quater dinsa
''daga tashina a bacci kinsani magana my mero'',jin ya ambaci sunan meron ua sake hasalata
''ai ba meron bace,sabida haka kada ka sake kira mana sunanta,kayi qoqari mu rabu lpy''shikam da yar qaramar dariyarsa ciki ciki ya zari towel dake saqale kan murfin cupboard ya shige toilet
A darare take zaune gefan gado tana bin dakin da kallo a haka ya fito ya sameta,da sauri ta dauke kanta don yaune karo na farko data taba ganinsa haka,rigar wankan jikinsa ya kunce zaren dake riqe da ita ta fadi a gun ya zama daga shi sai gajeran wando,cikin qunquni tace
''nikam naqi jinin rashin kunya''
a hankali ya tako gabanta ya durquso inda take a zaune har tana jin qamshin sabulun wankanshi da ragowar dumin dumin ruwan da yayi amfani da shi
''me kike fada?''ya tambayeta da wata iriyar murya ta daban,baya ta dan ja tana sake tsuke fuska don kusancin nasu yayi yawa
''nikam babu abinda nace''dagowa yayi yana dariya
''da kin sake kin maimaita yarinya yau da kinga yadda ake ruwan rashin kunya,yau da saidai mami tayi jinyarki ni kuwa na gudu abuja kinga ko fada ba zata samu damar yi min ba''sarai ta fuskanci me yake nufi,wai gabuntar dan fari ke damun Abdallah ko tabarar auta?,ta rasa wanne ne daga ciki,sai kuma ta tuna cewa itama 'yar farin ce take ta bawa kanta amsar saidai tabara ce kawai irin ta auta.
Babu wanda ya sake cewa dan uwansa komai har ya kammala shiryawa,itakam sai dauke kanta kawai tayi wani sashen don harkarsa yake kamar shi daya ne cikin dakin,wannan karon ma t.shirt din ya sanya saidai baqa ce long sleeve haka ma three quater dinashi baqine,wani kyau suka yiwa farar fatarsa,ya fesa turarrurrukansa,ga tunaninta ta dauka zai bude musu qofa ne su fice sai taga ya soma sauko da wasu tsadaddun akwatuna baqaqe masu kyau qana nan set ne guda uku ya ciro biyu babban da qaraminsu ya ajjiyesu
''bismillah madam,a hadamin kayan tafiya''ya fada yana dauki pillow daga saman gado ya jefar a saman rugs din dakin ya kwanta rub da ciki yana kallonta
''ammafa mami tazo nemanmu dazun kana bacci'',girarsa ya dage
''ba matsala nasqn ba wata damuwa bace indai mami ce,bamu da damuwa da ita'' qi tayi duk don ua qyaketa ta fita hakan yasa ya janyo wayarsa ya kira mamin ya tambayeta
''a'ah,ba wani abu ne,dama baqi ne suka zo matan baffa salisu ne kuma sun tadda kana bacci,har mun gaisa ma sun wuce sauri suke suna zasu''
''ok mami''ya fada ya katse wayar yana duban qwayar idonta
''sarkin kuka,komai kuka komai kuka,bayan qiri qiri baki da gaskiya''ya fada cikin zuciyarsa yana murmushi,bai ce mata komai ba har ta gaji da kallon da yake mata ta miqe ta isa ma'ajiyar kayanshin don yanzu kuma bata da wata dabarar ta kubce masa.
Tsaye tayi a gun,ta rasa ma wanne zata dauka masa,kaya ne bila'adadin iya ganinta,a sanyaye tace
''wanne da wanne zan dauka maka''
''na baki zabi,nikam,bani da ta cewa''ya fada yanajin dadin yanayin da suke,ji yake kamar ya riqe lokaci suyita zama a haka,a hankali ta dinga zaban kayan tana shiryawa cikin akwatin,tsit dakin yayi lokacin da take aikin,duk wani kotsinta yana binta da ido don,ba qaramin burgeshi take ba,komanta cikin nutsuwa,ta gama da suite suite ta saka masa yadi biyu shadda biyu tunda tasan tafiyar tasa majority sai yafi amfani da suite din,sannan ta saka masa na shan iska,ta kammala ta rufe qaramin kuma ta saka masa sauran tarkace na buqatar yau da gobe,shi kansa yanayin yadda ta tsara masa kayan ya burgeshi qwarai,komai a tsari,ta gama shima ta zuge tana fadin
''an gama'',sai da ya lumshe idonsa ya bude kana yace
''thank you verry much,shukran jazilan''
ya tashi ya zauna soasai yana fadin
''bari na qarasa daya nau'in godiyar ko''kafin tace komai ya jawota jikinsa,irin saqonnin dazu ya fara aika mata har suka so sufi na dazun zafi,nauyin da saqon nasa ya mata ya sata sakin kuka amma bai fasa ba don yana jin shine hanya daya data rage masa na samun sauqin abinda yake ji cikin zuciya da gangar jikinsa.
Kukan wayarsa ne ya ceceta,da qyar ya iya miqa hannu ya dauka,sunan mami ya gani na yawo ya daga kana yayi shiru
''abdallah,maryam tayi baquwa fa''bazai iya magana ba don yasan da yayi din tana iya harbo jirginsa don haka yace
''uhmmmmm''tuni ma ita ta kashe bata jirayi amsar sa ba,ya dubi maryam da ta dunqulr guri guda,duk da abinda yake ji sai da ta bashi dariya,sai kace wanda yake shirin yin mai gaba dayan duka ta wani tsure
''raguwa kawai,abinda baikai ya kawo ba kin gaza daukeshi''ya fada yana miqewa itakam ko daga kai ta kalleshi bata iyawa saboda azabar kunya haushi da tsoro
ya fito yana tsane jikinsa har yau tana nan inda ya barta,wayarta itama ta dauki tsuwwa da sauri ta daga hindatu ce ke kiranta
''adda maryam,jiran kusan minti arba'in''
tayi qoqarin daidaita muryarta saidai duk da haka a sanyaye take
''gani nan hindatu''ta kashe wayar ta miqe tana daidaita kanta
Sai data juya baya kana tace cikin cool voice
''bani key din zan fita ana jirana''
''dubeki,a hakan zaki fita,shiga toilet kiyi wanka''
ido ta zazzaro duk da bata kallonshi,kamar yasan zaro idon tayi kuwa yace
''eh,ko ba zakiyi ba kije ki daura alwala muyi salla azahar tayi mu samu ladan jam'i nasan yanzu masallaci sun riga da sun idar''
son fitar take don haka ta koma ta daura alwalar,kaya ta samu ya ajjiye mata da ido ta dubi kayan ya fahimci tambaya take
''ki sauya kaya na jikinki sunyi squeezing da yawa ko''ya bata masa ba tare daya dubeta ba,ba musu don itama ta yarda haka dinne ta debi kayan ta koma toilet ta canza ya jasu suka bada sallar azahar,suna idarwa ko ko addu'a bata tsaya yi ba ta dauki key din dakin da ya dora sama dressing mirrow,shima baice komai don yasan yau kam ya samu dama mai yawa,binta yayi da kallo har ta fice
A falo ta taras da hindatu da mami nata hira abinsu kamar wadanda sukayi shekara da sanin juna
''sai yanzu adda maryam har ina shirin kkmawa inda na fito''inji hindatu da sauri ta mata alamar don Allah tayi shiru don hindatu qanwar abdallah ce yanzun ta bata kunya,ashe mamin ta kula suka hada ido kunya ta kamata,sai yanzun ta gane wayo wato abdallah ya mata da ya sata canza kaya,tunda mami ai zata iya gane ba da su ta shiga ba,mamin gwanar kawaice da basarwa sai kawai ta miqe ta koma samanta ta basu gu
ajiyar zuciya ta saki tayi harr da idanunta,hindatun dai tace
''ko kunya bakwaji adda maryam,kubar mamanku zaune ita daya ku qule daki kuna cin soyayyarku''ido ta zare mana
''yi mana shiru mara kunya 'yar lukuta kawai,wai hindatu haka kika koma?,kina kallon kanki a madubi kuwa,lallai jabir shima da shi da ya barki kika yi qiba irin haka''
dariya tayi''ni da shi duka bamu ganin qibarmu,amma kowa sai ya ce mun zama 'yan lukutaye ni da shi''
''eh gaske''maryam ta fada tana kallon hindatun yadda ta koma,tayi bul bul ta sake zama fara,hira tayi hira qarshe ma dakin,maryam din suka koma,sai da suka shafe aqalla kusan awanni biyu suna hirar yaushe gamo.
Har kusan qarfe uku na rana suna hira kafin tayi haramar tafiya,a falon suka sake taras da mami hannunta dauke da poil paper ta nufi dakin abdallah hindatu tayi mata sallam,cewa tayi ta jirata ta koma sama ta dawo dauke da turaruka ta bata,hannu bibniyu hindatu ta amsa ta mata godiya kana maryam ta rakota.
Wata sabuwar matrix ash colour taga ta saka muqulli ta bude,baki maryam ta kama
''ah,lallai yarinyar nan jabir na shagwabaki,yanzu shikam ya yarda ya bawa hindatu mai shegen rawar kai mota take ja?''dariya hindatu tayi
''kai adda maryam,an girma da yanzu,idan da rabo ma nan da wata bakwai sai kizo suna''
duka ta dan kai mata
''eh lallai hindatu baki da kunya,laifin jabir ne''sai da ta shiga cikin motar ta zauna kana tace''zan biya gida fa na gaida mama,me zan ce mata?''take kewar gidan duk ta kamata,tana son taga mamanta sosai,watanni kusan nawa ta share rabonta da ita,tun ranar da aka fiddota zuwa fidan mijinta
''kice ina gaidata sosai da sosai,sannan nima ina nan zuwa''
''amma adda maryam duk ranar da zaki din zaki biyo min ko don Allah''ta fada taba yin kalar tausayi duk don tazo mata din,murmushi tayi
''kai hindatu''
''eh mana,baki fa taba zuwa min ba adda''
''to naji,zanzo insha Allahu''
''yauwa adda ta''ta fada tana dariya ta eufe murfin motar kana ta tada ta taja,bata bar gurin ba tsayawa tayi taga irin driving din hindatun,sai da ta fice a daga gidan kana ta saki yar qaramar dariya tana girgiza kai
''hindatu,hindatu''abinda ta fada kenan cikin zuciyarta ta juya ta koma cikin gidan.
Kitchen ta shiga kai tsaye da zummae dora musu girkin dare,saidai abun kunya ta tadda mami harta kammala ta adana cikin warmers baaba uwani na gyara kitchen din,cikin kunya ta fito ta koma dakinta,wanka ta shiga tayi kana ta fito ta sauya wasu kayan,doguwar riga ta sanya ta atamfa wadda ta kamata daga sama daga qasa ta bude sosai,ta mata kyau qwarai cikin ragiwar dinkunanta ne na fitar biki da bata kammala sakawa ba.
Mami na gaba abdallahn na gefanta,security din abdallah ne guda biyu riqe da akwatunansa,yayin da ita kuma ke binsu a baya a haka suka isa harabar gidan inda dalla dallan motocin da gwamnati ta sakewa abdallah guda biyar ke jiransa wadanda da su zasu rakashi airport su kuma su wuce abujan su hadu a can.
Duk suka shafa addu'an da mami ta gama jero masa kana ta dan matsa don basu damar sallama,hakan yakeso don dama tun dazun idanunshi na cikin nata,moment nasu na dazun kawai ke masa kai kawo,ji yake kamar ya dawo da hannun agogo baya,hannunshi ya miqa mata idanunshi fal so qauna da bege,a kunyace ta miqa masa nata hannun,cikin motar ya janyota a tausashe,saura kadan ta fada cinyarsa ya rungomota jikinsa kana ya miqa hannu ya rufe murfin motar driver najin haka ya kunna motar ya jata,mami na can suna magana dasu ibrahim sai gani tayi har motocin sun fice.
Gam gam ya hade hannayensu waje guda kana ya kwantar da kanshi kan kafadarta,yadda bata ce komai ba shima haka,kowannensu da abinda yake saqawa ranshi a haka har suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake nan kanon dabo
Ahankal motocin suka koma tafiya kasancewar sun fara shiga cikin airport din,sai a sannan ya fara magana
''ina fata zaki cika zuciyarki da soyayyata kamar yadda tawa take cike da taki kafin na dawo,duk da na sani cewa ko a yanzun ma nasan cike take din saidai dama da aka hanata,abu daya da zan gaya miki maryam am sorry to say bazan iya cika miki alqawarin da na daukar miki ba,bazan iya sakinki ba maryam har *ABADA* ke din tawa ce''ya qarashe maganar yana daga kansa dagq kafadarta,wata farar envalope fara qal ya ciro daga aljihun suit dinshi ya bude tafin hannunta ya saka mata,dai dai lokacin da motar tasu ta tsaya aka bude masa murfin.
''Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo dani,kimin addu'a don muhimmin aiki zan gabatar wanda koda shine aiki na qarshe da zan aiwatar insha Allahu sai na gabatar da shi,alhj hamza ya jima yana cutar da society dinmu,ya dade yana ha'intar qasarmu yana lalata rayuwar matasa maza da mata,yana shigo da mugayen makamai da qwayoyi,in sha Allahu wanann karon qarahensa yazo,ki saka ni a addu'o'inki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam''
wata muguwar faduwa gabanta taji yayi,a hankali ta furta
''Allah ya tsare,Allah ya bada sa'a''saidai bata san ya ji ba ko baiji ba don ya fice da hanzarinsa ganin sun kusa makara yana baiwa driver din da ya daukosu umarnin ya fara maida masa ita gida sannan su kama hanya,binsa tayi da kallo shi da security dinsa har ta daina ganinshi,drivern ya dawo ya rufe murfin kana yaja motar
Batasan dalili ba kawai dai taji zuciyarta ta hade envalope din da ya bata tayi tsakiyar hannunta tana jin qamshi na fita daga jikinta
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣8⃣
*Daga abu hurairah R.A yace:Manzan Allah S A W yace''na haneku da yin hassada,domin hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cin karmami(yayi,itace)*
Cikin motar laqwas jikinta yayi gaba daya,tana jin wani abu mai kama da kewa na shigarta kamar wadda aka cirewa wani muhimmin abu daga sassannin jikinta
Dakin ta ta wuce kai tsaye ta fada gado tayi ruf da ciki,kasala take ji da canjin yaynayi cikin jikinta,sai taji gidan ya mata fayau kamar ita daya ce a ciki,ganin matuqar taci gaba da zaman a haka kasalar zata rufeta da gasken ya sanyata miqewa ta fito kai tsaye tayi sashen baaba uwani
A tsakar gidacta tatar da ita kan tabarma tana gyara zogale,kan tabqrmar ta isa itama tasa hannu tana tayata suna hirarsu,qarar wayarta ya katse musu hiran kiran raliya ne,tana murmushi ta daga sanan ta mata sallama
''maraaba da dawowan diyana''cikin sauti mai dauke da farinciki ta maida mata amsa
''uwar gida kuma amaraya agidan muhammad nasir''
dariya itam tayi cike da nishadi
''a wannan kirarin ai sai ku,ku da ludayinku ke kan dawo''
sai da suka gama zolayar juna kamar yadda suka saba sannan suka fara gaisawa
Hira sukayi mai tsawo wadda har baaba uwani ta kammala gyaran zogalen ta kwadanta basu gama ba
Har bayan magariba tana gun baban suna hirarsu,sai sallamar mami kawai sukaji
''zuwa nayi na duba dama,nayi zaton bai dawomin da ke ba''
kunya ta kamq maryam din ta sunkuyar da kai tana murmushi,tana idar da sallar isha'i ta yiwa baba sallama ta koma bangarensu
Ta kammala shirin naccinta tsaf ta haye gadonta,saidai ko guda baccin da take da muradin yi bata ji alamunsa,wata iriyar kewa da madaici na daban take ji na damunta,juyi take tun daga farkon gadon zuwa qarshensa,tayi hakan yafi sau a qirga,tana son qaryata kanta kewar abdallah take saidai ta gaza,sai ta tsinci kanta da muradin jin muruarsa saidai ko kadan ba zata iya kiransa ba,hasalima bata tunanin akwai lambar wayarsa cikin wayarta,ta miqe a hankali ta jawo side drower ta ciro envalope din da ya bata dazun,dawowa tayi kan gadon ta kwanta ruf da ciki,a hankali ta farketa,kudi ne sababbi fil a miqe yan dubu dubu masu yawa suka fado,yar qaramar takarda ce maqale jikin bandir na kudin,ta cirota ta budeta,karo na farko da idaninta suka ci karo da kyakkyawan rubutu wanda bata yaba ganin kamarsa ba
''kiyi amfani da su idan buqata ta taso miki,love you so much my sugar''
dunqule takardan tayi ta dorata saman kudin
Ta sake bude cikin envalope din take taci karo da wata takardar fara qal mai adon furanni wadda ba shakka itake tashin qamshin nan,ajjiye envalope din tayi kana tasa hannu biyu ta ware nadin da aka yiwa takardar,sallama ce a farkon takardar cikin kyakkyawan rubutu da harshen larabci
_qoqarin mantawa da wanda kake so is like trying to remember some one you never meet,i know we feel d same baby saidai bansan me ke yawo cikin zuciya da ruhinki ba,dont let your ego stop u from doing whats right,duk abinda nayi nayi ne saboda ke,duk abinda kike gani na miki laifi a akansa saboda ke na aikata,sonki ne sanadi baby,i cant express my feelings a kanki baby,ban taba sanin haka so yake na sai a kanki,zan iya cewa kai tsaye ke kika koya min so,nasan kina tunanin na auroki ne kan tilas,ba haka bane na aureki saboda sonki da qaunarki da nake,nayi tsammani zaki qini zaki qi sona hakan ne yasa ban nemiki kai tsaye ba,but sorry for hurting u baby_
_kalmomi na sun bata ranki hakan ya sa kika riqeni,na sani na kuma san na fada,but banda ke baby baki ciki amma duk da haka am sorry again for my words and action last time,ina sonki baby ina sonki,am not with you to play games,ina fatan komai zai gyaru kafin dawowata,bazan iya jurar rasaki ba bazan iya ba,zanso ace ko yaushe kina tare da ni,baby ina da qarfin buqata tun ba yau na na sani,idan kika qi ni bazan iya sakinki ba duk tsanani matuqar ina raye amma ina fatan bani dama nayi aure,koda babu komai tsakaninmu ganinki da zamanki a matsayin matata kawai ya wadatar da ni,ke ta dabance baby ki yarda,inajin komai nawa daban duk lokacin da muke tare,am feeling safer when iam wrapped up in your arms then ever before,duk lokacin da nake kusa dake baby am overwhelmed with happiness,kin soni kin ceceni kin kubutar da ni kin kuma tserar dani,shin wannan ba so ne ba baby?bai isa a kira waannan so ba?,so mai ma kuwa mai tsada,so mai cike da sadaukarwa da fansa?,kin min abinda 'yammata da yawa suka kasa min,na haqiqance u are what i have been waiting for my whole life,so na haqiqa so na gaskiya,kina sona ba tare da kinsan ma kina sona din ba baby_
_alhamdulillah finally a found someone who loves me just for me,ba don wani abu da nake da shi ba,but ban manta ba i promise sai na ninka sona cikin zuciyarki fiye da da,nasan nayi nasara duk yadda kika kai ga boye hakan alredy na ganahi cikin idanuwanki koda zaki qaryata ni,abu na gaba shine ki fadamin shima na tabbatar miki cewa sai nayi nasara nayi alqawari,TO THE MOST BEAUTIFUL GIRL IN D WORLD,AM SORRY BABY,_
Lumshe idanunta tayi tana jin wani abu da bata taba jin irinsa ba na ratsata,gaba daya abdallah ya gama kasheta,muguwar kasala ce ta lullubeta,sai ta ninke takardar ta lalubo jakarta da take ajjiye muhimman abubuwanta zata jefa ciki idanunta suka sauka kan takardar,takarda ce data dauketa washegarin daren da abdallah ya fara cuta,sam ta mance da ita,da sauri ta daukota ta bude ninkin da tayi mata,rubutune mai kyau kamar wancan saidai bai kai yawan wancan ba
_idan da kina da masaniyar tun yaushe na fara sanki ba zaki nemi abdallah ya rabu da ke ba,na soki a lokacin da bakisan akwai mai sonki ba cikin duniya,maryam tun kina 'yar secondry school na fara sonki,cikin kulawaata da sa idona kika kammala universty dinki,can you remember sau nawa kike zuwa registration ace miki an dau nauyinki saboda hazaqarki cikin dalibai?,zaki iya tuna samari nawa kika yi suka tafi basu sake dawowa ba?,har kina tsammani ko matsala ce daga gareki,kin kusa auren jabir a lokacin bani qasar nan ban sani ba na tafi jinya na gubar da naci london,cikin qurarren lokaci na samu labarin hakan ina can,sauran qiris na rasa raina san da na samu labarin zakiyi aure amma da yake Allah na sona ya tsinke lamarin,dalili kenan da na nemi sabon mai dafa min a binci saboda na sani bangarenki ne........._
Iyakar rubutun dake ciki kenan saidai tasirin da ta yuwa zuciya da gangar jikinta mai yawa ne har ta kasa zama ta miqe tsaye,da gaske abdallah yake?shekaru nawa nufinsa yana tare da sonta,abdallah ya dade tare da ita ba tare data sani ba
A hankaki wasu abubuwan da suka dinga faruwa da ita a baya suka dinga fado mata,sautari akan tsaya da mota ta alfarma da niyyar rage mata hanya,a lokacin haushi da takaici na kamata ne don tana tsammanin 'yan kama wuri zauna ne kawai wadandq suke barewa duniya gyada taci keson hilatarta,saidai bata taba katarin ganin fuskar abdallah cikinsu ba,duk cikin nashi salon game din ne kamar yadda ya mata kan ABDUR RAHIM?.
sai kawai taji murmushi ya subuce mata
abdallah?
abdallah?,wanne irin mutum ne kai abdallah,basira da wayinka sun isa,you have play good game with me''ta samu kanta tana fada cikin zuciyarta,sai ta koma bakin gado ta zauna tana tuna abubuwa masu yawa a wancan lokacin,tasha ganin abubuwa masu yawa da suka sa ta dinga jin tsoro har take ganin ko jinnu gareta
Wayarta dake silent taga tana haske,ta miqa hannu ta daukota daga gefan pillow,baquwar number ce,sai data daga kai ta kalli agogo qarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare ,ta maida kanta kan wayar tuni har kiran ya tsinke,tana shirin maida wayar wani kiran ya sake shigowa,da tayi kamar ba zata daga ba daga qarshe ta daga din ta kara a kunnenta kana tayi shiru don tantance waye
''assalamu alaikum''muryar abdallah ta daki dodon kunnenta,kasa zama tayi sai ta sulale ta kwanta ruf da ciki saman gadon saboda wani makami da ya aikowa zuciyarta,sake maimaita sallamarsa yayi wanda wanann karon sai da ta lumshe idanunta,lebanta ne suka amsa ba tare da ko wane harafi ya fita ba
''baby nasan kina jina,zuwa yanzu na tabbatar kin karanta saqona''itama so take ta dan rama ko yaya ne kafin ya dawo kano,muryarta low sosai wanda ko kai dake dakin babu lallai kaji me take fadi
''ban duba ba,don bani da time na duba takardu''murmushi ya saka mai sauti da wata 'yar shashsheqa wanda har sai da ta jiyo shi,tsigar jikinta ta zuba
''baby,baby,baby,kullum kina yiwa kanki qarya me yasa?,i know tuni saqona ya isa,ko kice eh ko kice a'ah,na kira ne dama naji muryarki ko zan iya bacci,sai nakejin dama mu koma qauyen ni'ima muyi zamanmu,atleast acan zamu dinga kwana daki daya,idan da rabona ma sai in kwana cikin ni'imtacce jikinki,baby na kasa mance moment namu na dazun ina jin kamar ya dawo,i want feel you beside me,i want to feel your lips......on my neck and.....baby i want.... Iwant''ya fadi kamar mai tsoron magana
''i want to run my head along your chest,kiss your lips....''ai bata iya jumurin sauraronsa ba ta katse kiran nasa ta jefa wayar gefanta bayan ta tsura mata ido
Tana kallin kiran nasa amma bata jin zata iya dagawa yaci gaba da horata babu gaira babu dalili,shi dole sai ya tada zaune tsaye,sai da ya hada mata missed call kusan goma sanann ya haqura,qarfe saya da kwata ta sauka a gadon ta shiga bandaki ta daura alwala tayi nafila raka'a biyu ta kwanta,tunani ne fal kwanyarta ta kama wanann ta saki wancan,cikin haka tunanin mero ya fado mata,sai taji ranta ya baci,tana son sanin haqiqanin me tsakaninsa da ita kafin komai ya daidaita,a uziyya tayi ta kori tunanin daga ranta don haka dabi'arta take bata kwana da kowa cikin ranta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Ta makara sosai gun tashi kuma mami bata tayar da ita ba,bakinta ta wanke da fuskarta ta fito falon bata tadda mami ba sai baaba uwani tana ta gyara kitchen,nan ta tsaya sunq gaisawa har mamin ta sauko,tayi adonta cikin dogowar riga mai zubin buba saidai ready made ce wannan,bayan sun gaisa mamin ta gaya mata ta shirya hajiya laila na zuwa anjima zata fara mata gyaran jiki,ita gaba daya kunya ma kamata take duk da ta sani mami bata dauketa suruka ba amma akwai kunya tsakani,ta amsa mata da to sannan ta koma daki.
Ta daura towel tana shirin shiga wanka saqo ya shigo wayar sai ta dawo ta duba,number din dazu ce wadda ta tabbatar ta abdallah ce
''baby jiya kin kusa kasheni wlh,sauran qiris na gayawa mami yadda kike gara mata yaro,ina gaya miki damuwa ta kika gudu kika barni,me yasa baby?,i need your help baby''
bata shirya ba amma sai da murmushi ya subuce mata,ya tuna mata ma,take ta kira mamanta,hira sukayi sosai wadda ta qara mata kewar gidansu
Cikin kwanakin gyara sosai maryam kesha wanda ko bazawara aka yiwa hakan sai ta tsere ma sa'a,itadai maryam nata ido,wannan qauna da mami kewa abdallah ba kadan bace
🍃🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Zaune suke su biyu cikin fallen dakin nata wanda yafi kama da kango,idan ba kyakkyawan sani kayi mata ba zaka tsammaci mahaukaciya ce sabun kamu,tuni ta saje da su tabi sahunsu kamar yadda habiba ta shaida mata,ta tsotse ta rame kamar wadda kullum ake diba ana kada miya,ga uban ciki a gaba ya fito yayi tsororo kamar dosana shi akayi babu kyawun gani.
''yanzu habiba babu wata hanya kenan ta kubuta''ta tambayeta cikin damuwa
''bana zaton zahariyya akwai''
dariya sukaji ana babaka musu a razane suka daga kansnsu,malam na hayi ne tsaye bakin qofar dakin yana shigowa
''kuna batawa kanku lokaci ne amma babu wadda ta isa ta kubuta daga gareni,mutane ne ku masu son zuciya,kun bijerewa Allah kuna neman biyan buqatarku kan wani mummunan qudiri naku,yadda kuke da baqar zuciya nina haka nake,kunga kenan zamu je ta tadda da mujemu,a sannu sannu mata ire irenku zasu ci gaba da shiga masibu kala kala,walau a nan duniya ko a lahira,irin mu muna nan da yawa Allah ya ajjiyemu saboda ire irenku,haka gaba dayq mu da ku kuma sai munje lahira za'a hukunta mu baki daya,ni dama na riga na sani bani da rabo a lahira,kunga ai gwara naci nawa tun anan''ya juya ya fice yana sheqa dariyarsa.
Hada kai sukayi suka fashe da kuka kowacce da irin tata nadamar,sun qi Allah bayan ya musu ni'ima,idanunsu ya rufe basu ganin baiwar da yayi musu da tarin ni'imominshi a garesu sai yanzu da ya karbe abinsa,dama ya fada cikin littafinsa mai tsarki''idan kuka gode min zan qara muku,idan kuma kuka kafirce to haqiqa azabata mai tsanani ce'',sun yarda sun dauki hudubar shaidan,wanda dama bashi da burin da ya wuce batar bayan dama ya sani cewa tun can dama shi batacce ne,kuma dama yayi wa Allah alqawari sai ya batar dq bayinsa kamar yadda yazo cikin wasu surori na qur'ani lokqcin da Allah yace ya fita daga aljanna la'ananne ne shi
''kuma la'anata tana tare da kai har zuwa ranar qarshe''
sai shaidan din yace
''ya ubangiji ka jinkirta min izuwa ranar qiyama''sai Allah yace an jirka maka,har uzuwa rana da lokaci sananne,sai shqidan yqce da ubangiji
''na rantse da isarka da buwayarka sai na batar da su gaba daya,saidai bayinka daga cikinsu tsarkakakku''sai Allah yace da shi
''haqiqa bayina baka da wani iko a kansu sai wadanda suka bika dagq cikin batattu,kuma haqiqa jahannama ce makomarsu gaba dayansu,tana da qofofi guda bakwai''a wani gurin kuma shaidan din yace
''zanzo musu ta tsakaninsu data damansu data hagunsu mafi yawansu zaka samesu marasa godiya''
haka ya sake fada a wani gurin cewa
''sai na batar da su,sai na sanya musu buri sai na umarcesu su canza halittar Allah(kamar bleeching yana daya daga ciki)
shi yasa Allah da kansa yake fada mana
''haqiqa shaidan abokin gabarku ne ku ruqe shi abokin gaba'',muna mantawa ne da ranar mutuwa ranar tonon asiri ranar hisabi,ranar da duk wata rai saita bi ta saman siradi ta wuce wanda qarqashinsa wutar jahannama ce,aikinka mai kyau gaskiyarka zumunci da ruqon amana ne kawai zai qetarar da kai cikin salama
Son zuciya ya mana yawa,muna biyewa soye soyen zuciyoyinmu baka iya hana zuciyarka aikata mummuna wanda hakan ke kaimu ga halaka,Annabi muhammad S A W yana cewa''an lullube aljanna da abinda rai baya so(kamar salla azumi zakka,zumunci,da sauran ayyukan alkahairi da bamu son yi ko muke jin wuya gun aikata shi)an kuma lullube wuta da sha'awe sha'awe(kamar zina,caca,cin dukiyar marayu,annamimanci,sata da sauran abubuwa da rai kejin dadi yayin aikashi)''
Allah ya sake cewa ba don falarlarsa da rahamarsa ba da duka munbi shaidan face 'yan kadan
Allah kasa mu dace duniya da lahira
Sun jima cikin alhini da jimantawa kansu kafin habiba tace
''zahariyya nifa na gaji,anya ba kashe malam zamuyi ba?''duk da yadda taso ga neman mafita amma sai da shawara ta tsoratata,don bata manta ba irin wannan kuskuren taso aikatawa ya kawota ga wannan matsayin da take ciki yanzu
''habiba,in sake yunqurin aikata wani kuskuren kenan?''
''kashe malam,zahariyyq rage mugun iri ne cikin al'umma,bakiji abinda yace babe,malam fa bazai taba shiryuwa ba,shin kin san shi mutum nawa ya kashe cikin wannan qazamar harkar tasa?(hmmm,sai yanzu data ritsa da su suka san qazama ce)''
cikin rashin gamsuwa ta girgiza kai
''wannan shi da Allahnsa amma mu dq muke neman kubuta kuma inamu ina kisa,shawara daya ce kawai tunda mu bamu tsaya munyi karatun addini ba boko muka sa a gaba,ba wasu addu'o'i garemu ba kawai kullum mu dinga karanta masa fatiha ba adadi,ai Allah yana jinmu,kuma nasan da yardaraa wata rana zamu kubuta''
take ta yarda da shawarar zahariyyan don tafi tata fidda maslaha
*mrs muhammd ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣9⃣
*An karbo daga Abdullahi dan amru dan Aas Allah ya yarda dasu baki daya,haqiqa Manzan Allah S A W yace''yana daga cikin manya manyan zunubai mutum ya zagi iyayensa(uwa da uba)'',sai sahabbai suka ce ''shin mutum zai iya zagin iyayensa?'',sai Manzo S A W yace''eh,a zagi mahaifin mutum,mutum(wanda aka zaga) shima ya zagi mahaifinsa(mahaifin wanda ya zageshi din),ya zagi mahaifiyarsa shima(ya rama) ya zagi tasa(wanda ya zageshin)''*
_ruwayar bukhari da muslim ne_
Itakanta ko ba'a gaya mata ba tasan ta canza,wani santsi da qamahi fatarta ke fitarwa na musamman,wani lokaci har shanshana kanta takeyi kota tsaya kallon kanta a madubi,magani masu kyau mamin ke bata na ainihin 'ya'yan itatuwa ba gamje gamjen bature ba,tana jin naiyinta da kunyarta haka zata karba ta sha tana rufe ido,mamin takanyi murmushi tace
''babu kunya tsakaninmu maryam diyata ce ke kamar yadda nasha fada,namiji kuwa dan son gyara ne bashi da kunya ta wanann bangaren,balle abdallah da ina kula da rawan kanshi,idan kika zaune kara zube cikin lokaci qanqani zaki wargaje fes babu kunya zai dauko miki wata,shi yasa har yau ina alfahari da lambar yabo da na karba agun daddyn abdallah har ya mutu yana yabamin,so haka nakeso ki zama gurin abdallah koma kifi haka,koda akwai wata ma kisha gabanta''
kunya ta kuma kamata duk da maganar ta taqarshe ta dan haifar mata da fargaba
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Tun ranar bai kima kiranta ba,har ta dinga zaton ko fishi yayi,cikin ranta take jin ba dadi idan fushin kuwa yayi,can qasan ranta ake tsinkularta ta kirashi taji muryars amma da zarar tayi kamar ta kira din sai kunya da nauyi su hanata
Kusan tara na dare ne suna zaune ita da mami da baaba uwani,baaban ce ta musu sallama ta wuce bangarenta mami ta duba agogon kana ta miqe ta haura sama bayan ta ce da maryam tana zuwa,kallo take amma batasan ya akayi idanunta suka kai kan hotkn abdallah window size dake kafe a can kusurwar falon ba,sai ta kafe hoton da ido,a hankali wani abu ya dinga motsa zuciyarta,ta miqa hannunta ta duba call history inda num dinsa take wadda ko serving bata yi ba,ta shiga canki camkin ta kira ko a'a,kamar wadda aka tankwabi hannunta ta danna kiran gakin ya soma tafiya sai ta qyaleshi.
Daidai lokacin da yake cikin dakin hotel din da suka sauka,shi da manyan yaransa ne guda biyu,a gaggauce yake shiryawa cikin wadansu baqaqen kaya samfurin kayan jami'an tsor,duk da kqyqn qiki ne amma ba qaramin kyau suka yi masa ba,yana cikin daura belt dinsa bayan ya sanya bindigarsa a aljihun wandon na baya yaga shigowar kiran,bai lura ba sosaj ya dauke kai yaci gaba da sanya boot a qafarshi baqi don muhimmin aiki ne a gabanshi bai saba qa'idar lokaci komai nasa a tsare yake
Tana dab da tsinkewa ya kai hannu da niyyar dauke wayoyin nashi ya kashesu don bazai fita dasu ba,ba dasu zaiyi amfani ba already ya gama maqala na'urar da zasu dinga communicating da abokan aikin nasa a jikinsa,mamaki ya kamashi ganin sunan *honey sweet* bisa screen dinshi,katse kiran yayi kana ya kirata
sai da gabata ya dinga bugawa kafin ta amsa kiran,a kasalance ta kara wayar a kunnenta hade da yin sallama,duk da kuzarin da yake da shi sai da yaji an zare masa shi tas,shi da yake ta shiryawa a gaggauce yana basu order din baison bata lokaci sai gashi yana shirin kwanciya saman gado,yaran nashi suka kalli junansu da lamar tambayar ya haka?a tsakaninsu saidai babu damar furtawa oga suka ja bakinsu suka tsuke,alama ya musu da su fita su jirashi a qofar dakin yana tsoron kada ya tafka abun kunya a gabansu,don tunda yaji muryarta komai ya kwance masa.
Shima dai a kasalance ya amsa mata sallamar,daga nata bangaren ma wani dafin ya kuma zuba mata,shiru ne ya ratsa tsakaninsu tana jiyo saukar numfashinsa,ya shiryawa sata tayi magana koda bata so,ya santa da qin yarda da gaskiya ta wannnan bangaren,saida yayi dariya ciki ciki sannan yace
''Allah sarki baby,kafin kice komai nasan kewata ke damunki kika kira kiji sweet voice nawa ko?''
gabanta ya dan fadi ta zaro ido kamar tana a gabansa ne,sai data cire wayar daga kunnenta ta sake dubawa shidin ta kira sanann ta maida kunnenta
''sai kace wata kai,niba wannan yasa na kira ba,dole ce ma ta sani kiranka''
murmushi ya saki mai sauti wanda ya kusa wucewa da imaninta
''attitude naki din nan yana burgeni,kina da jarumta da yawa,aiki ne ya cushe min shi ya hanani kiranki my suger''wani sanyi taji yana ratsata har sai data cure gu daya,rake idea din yadda zata bagarar da shi yazo mata
''hmmmm,gida nakeson naje naga mama''
shiru ya danyi kana ya sake sanyaya muryarsa
''nima zanso kije ki ganta din,amma sorry baby,gaskiyq ina kishinki da yawa,na tabbatar idan zaki din saidai driver ya kaiki fa,kinga kun kadaice daga ke sai shi cikin motar....har zuciyata ta fara zafi ma wallahi da tuna hakan da nayi''
ta hade rai don gaskiya tana matuqar son ganin maman
''amma fa ka sani yaushe rabona da mama,tun ranar da kasa aka fiddani a gidan''ta fada cikin shagwabar da batasan tayi ba ma,shikam tuni taso sauya masa lissafi don sai da yayi ajiyar numfashi kana yace
''shine kuma sai kin illatani da muryarki?''
''me kuma nayi?''
''kinfi kowa sani,gaskiya my kiyi haquri idan Allah ya dawo dani na miki alqawarin kaiki da kaina ki wuni har dare sai nazo na daukeki kinji?''
hawaye taji kawai na silmiyo mata,don haskiya ta qagu taga mamanta,tayi kewarta sosai,sai kuma yqce sai ya dawo sanann zata je,bayan shi kullum sai yaga tashi maman saidai idan baya gari,kasa magana tayi shima shiru yayi yana saurarenta,can qasa ya jiyo kamar sautin kuka,da hanzari ya miqe ya zquna yana fadin
''ya salam,maryam me yasa kika maida hawayenki masu araha irin haka?,daga cewa sai na dawo zaki je?''
''eh,ai baka kyauta ba,banson rashin adalci fa abdallah ka san halina sarai''cewar mami data amshi wayar bayan ta maidata handsfree,sam maryam bata san ma ta iso ba sai da ta qaraso gabanta
kanshi ya dafe
''shikenan mami nikam abdallah bawan Allah,naga ta kaina an hade min kai''
''har hanci da goshi ma zamu hade maka indai zaka dinga matsantawa irin haka''
''mami ina da kishi sosai kin sani,dole idan zata je mami driver ne fa zai kaita,mami banason wallahi yani ya kalleta''
''oh abdallah,halin naka dai yana nan,to zuwa kam sai tajeshi haka kawai,wake raba da da uwa,yaushe rabon da tq gansu,haba abdallah''
''shikenan mami na yarda mata taje,amma ba kwana ba,yauwa......baaba sule ne zai kaita,kuma don Allah ta saka hijabi don Allah''ya fada a sanyaye,wani mugun kishinta yake ji yana yi kamar yasan gyaran jiki ake mata dan ubansu
kama bakinta mamin itama tayi kana tace
''iyeee,sannu fa ubana''marairaicewa yayi
''mami pleaseeeeee.......''
''ya isa''tayi saurin tsaida shi
''taji zata saka,ince ko shikenan?''
''i love u my mommy''ya fada cikin murmushi
''me too my son''ta fada itama,tana shirin katse wayar yace
''yauwa mami.....i need your prayer mami zami fita aiki kan mutumin nan kimin addu'a mami kamar kika saba,i know ita ke kaini ga yin kowacce iriyar nasara''maryam dake gefe duk dai taji ba dadi wani kewa da karayar zuciya na son kamata
addu'a tayi masa sosai y
hannayensa a sama kamar suna tare ta gama suka shafa su duka,sai yaji wata nutsuwa da dukka qarfinsa sun dawo.
Miqawa maryam wayar tayi dom suyi sallama
''baby....ki kulamin da kaina''
''kanka kuma?''
''eh i mean you,nine ke kamar yadda kece ni,byee love u much more''ya fada ya katse wayar sai ya barta da waya a kunne,a sanyaye ta cire wayar bayan ta sauke ajiyar zuciya
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Cikin atamfa excellent ta shirya pure cotton,duk da mai qaramin kudi ce amma ta matuqar amsarta,kalar blue black dark blue and navy blue da sea green ce,sai ta samu kanta tana aiwatar da umarnknsa duk da ba'a tuna mata ba,hijabi ta sanya blur black wanda ya rufe ilahirin jikinta,mai hannu ne hakanan yayi matching sosai da atamfar ta,ita kanta data kalli madubi sai taga tayi masifar yin kyau,hakanan tana jinta compertable sabanin mayafi,duk da cewa dama ita gwanar hijabince musamman sanda tana gida
baaba sule dinne kuwa tana fitowa suka gaisa da kanshi ya bude mata motad duk da bata so kunya ce take rufeta,don aqalla ya kusa sa'an abbanta
Ta dinga kallon unguwar tasu,babu shakka gida akwai dadi,baka gane hakan sai randa aure ya daukeki daga cikinsa ya kaiki wani gu,komai rashin sukuni na gidanku randa ka barshi sai kaji kana kewa da begensa,ta samu gidan auren da ya ninka gidansu nesa ba kusa ba amma bata daina kewar gidansun ba,may b home is nothing but two arms holding you tight when you are at your worst
Cike da zumudi ta saka kai cikin gidan da saurinta saboda yadda jama'ar unguwa keta binta da kallo,suna ganin ta sake zama ta daban,wata ma yaranta ke kai mata gulmar maryam tazo sai a hau leqe saboda ta tsaya suna magana da baaba sule ashe mami ta cika boot da kaya bata sani ba sai yanzu yace ta turo yara su kwashe
Farinciki ya cika,zuciyarta ganin gidan qal a share sabanin da da iyakacin tsaftar qofar dakinsu ne zuwa,cikin dakin nasu,lubabatu ce kan tabarma zaune da qananun qannensu wadanda suke daki daya da da qatuwar farar takarda ta shimfideta kan tabarma ta zana alifun ba'un har zuwa ya'un manya manya da alamu tana koya musu ne shi yasa ko sallamarta basu ji ba,kafin ta sake maimaita sallamar ta hango isyaku ya fito daga dakin uwarsa kanshi tsaye yabi takan takardar ya take rubutun kana yayo hanyar waje,lubabatun ce ta yunquro da sauri ta cafko wuyanshi ta baya
''wannan iskancin naka isyaku ya isheni wallahi yau sai jikinka ya gaya maka''
Da sauri maryam ta qarasa don kada abun ya kwabe tana banbare hanunta daga wuyan isyaku wanda keta kici kicin qwace kansa cike da rashin kunya
''sakeshi lubabatu kinji sakeshi''sai a lokacin taga maryam din ba musu ta sakeshin ya kuwa fice abinsa da gudu,ta saki fuskarta daga daurewar da tayi tana fadin
''sannu da zuwa adda maryam''
''yauwa lubabatu,karatu ake yi ne?''ta dubi yaran kana tace
''eh,makarantar dare suke zuwa malaminsu yace su tabbata sun iya zuwa anjima zasu je kuma naga basu iya ba''farinciki ya kama maryam ganin an fara samun ci gaba a harkar karatun yaran
''da kyau kin kyauta kuwa lubabatu''
yaran suka zuba mata ido suna shakkad zuwa gurinta,ko dama can ita ba mafadaciya bace bata dai shiga shirginsu ne saboda gudun rashin kunya irin tasu,su kuma suna ganin a yanzu ta zama yar gayu kada ta makesu idan suka matso gurinta tunda haka jamila ke musu sanda tana aure gidan jabir
sai ta bude hannayenta tana fadin
''kamar baku ga yayarku bane,ku taso mu gaisa mana asiya''
ai kuwa har rige rigen zuwa suka dinga yi,sai taji farinciki ya rufeta,zaman lafiya babu abinda ua kasihi dadi haka dan uwa,baka da kamarshi cikin duniya,hamsin hamsin ta fidda ta raba musu su biyar tace su sayi alawa
Ganin har suka gama budurinsu,aka gama shigowa da kayan da mama ta hadota da su samfurin kayan masarufi babu wanda ya leqo daga matan gidan ya sanyata tambayar lubanatu wadda gaba daya maryam ta karanci nutsuwa sosai a tattare da ita
''ina wai matan gidan ne?''
''au...''ta fada tana murmushi tare da dafe bakinta
''na manta ban gaya miki ba,sun fara zuwa makarantar matan aure qarfe tara na safe zuwa daya na rana mamata da maman hindatu(maman maryam din)ke zuwa,ya hindatu ce ta sanyasu''
cike da nuna kara tace
''inna hadiza fa?''
sai da ta kalki qofar dakin nata kana ta tabe baki
''tana ciki tana bacci,tata makarantar kenan''ta fada tana bushewa da dariya,daquwa maryam ta mata
''mamarki ce itama''daki lubabatu ta shiga ta daukowa maryam maqullin dakin maman tace
''adda ga key din ko''ta karba kana ta budr dakin maman ta shiga
ta bi dakin da kallo ya sake kyau ya canza,cike yake da tsafta da qamshi,wani kewar dakin ta kamata,sai ta cilla mayafinta da jakarta saman kujera,kai tsaye ra shige dakin maman ta fada gadonta data yi kewarsa matuqa
Tana son gadon umman nata tana jin dadin kwanciya a kai,gadon da tasha dabdalar quruciyarta a kai har yanzu katifarshi ce a kai,duk da canza kayan daki da taga umman nata tayi amma bata canza abarta ba,ta sake juyawa tana tuna rayuwarta cikin gidan quruciyarta zaqi da madaci kala kala,a haka bacci yazo ya sureta.
Can cikin barcinta taji kamar ana kiran sunanta,a hankali ta dinga bude idonta har ta budesu tarwai kan fuskar mamanta,farinciki ya kamata,yaushe rabon data ganta,tana tsaye cikin unifaorm ash colour doguwar riga da hijabi,sun mata kyau kuwa unifaorm din sosai
''ki tashi kiyi sallah kina ta bacci har anyi azahar''sai ta miqe tana mutstsuka ido
''ashe har kun dawo mama''
''eh kina ta bacci har girki akayi aka gama baki sani ba,halan bacci kika koyo''murmushi tayi ta miqe zata fice a dakin tace
''sannunku da dawowa''
''yauwa''maman ta amsa tana rataye jakar makarantar ta data daukota daga falo gami da cire hijabinta ta linke ta saka a sif
Duk inda tayi maman kallonta take,godiya take wa Allah cikin zuciyarta,farinciki fal ranta,lallai addu'a bata faduwa qasa banza,duk wanda ya kalli maryam din koda makaho ya shafata yasan ba a wahala take ba,babu shakka Allah ya share mata hawayenta na shekara da shekaru wanda ya jima yana zuba,hirarsu suke gwanin sha'awa da maman bayan baaba huwaila ta aiko mata da abincin rana don girkinta ne,bata zauna ba sai data shiga dakin baba huwailan suka gaisa,kayan dakin mama datq cire ne jere a dakin nata,ba laifi sunyi kyau kam,cike da sanyin kiki da nadama ta dubi maryam
''na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun lokaci bai qure min ba ni da yarana,maryam na cutar da ke a baya na kuma so na sake cutar da ke amma da yake ALHERI ne cikin zuciyarki sai Allah ya kareki ya kuma sanya kika mana zarrah a rayuwa,maryam don girman Allah ki yafe min ni da yara na gaba daya''
sam magiyar da take mata bata yi matq dadi ba,ko da can baya ta sani cewa shedan ke rudarsu da duhun kai,bata taba riqar baaba huwailan ba
''baaba,tamkar mahaifiya kike a gurina,nikam dama ban riqe ki ba,na yafe miki Allah ya yafemu baki daya''
Data zo cin abinci duka qannenta ne kewaye da ita suna hirarsu abinda bai taba faruwa ba tsakaninta da su ba tarihin rayuwarta,nan take jin duka baaban su ya maidasu makaranta,sosqi taji dadi don babu gatan da zaka yiwa yaro da ya wuce ka bashi ilimi(har kullum haka iyayenmu ke gaya mana,burinsu kenan (rabbirham huma kama rabbayani sagirah)
maryam ta dubi mama''ni ka ban ma ga baaban ba''
kubrah tayi caraf tace''baaba yana kasuwa,sai shida zai dawo''ta juya ta kalli mama
''kasuwa kuma mama''
''eh,kin manta da shagonsa da abdallah ya bude masa cikin kwari?''
''abdallah,a cikin kwari?,yaushe abdallahn yayi haka ba ta taba sani ba,koda mami bata taba mata magana makamanciyar wannan ba''cikin zuciyarta tayi maganar amma a fili sai tace
''au na manta fa''
''ai kullum malam sai ya yiwa yaron nan addu'a,yanzu kam qlhmdlh malam ya dauje duk wani,nauyi na gidansa da a da baya iya daukeshi,abdallah kam ba baya ba wajen alkhairi,abu daya zaki mana maryam ki wanke mu kiyi zaman aure mai cike da biyayyar miji,duk yadda kika zauna da mijinki kina nuna masa irin kalar tarbiyyar da kika samu kenan,kibi mijinki maryam ki riqe abdallah hannu biyu,bawai don arziqin da yake da shi ba,a'ah ko daya,kinfi kowa sanin cewa ba wannan ne gabanmu ba,nagartattun halayen abdallah kadai sun isa su sama masa kowacce kalar mace ta gari,ina fata kin fahimceni''kanta ta gyada
''na fahimta mama''
''Allah ya albarkaceku ke da shi baki daya''
''ameen ameen mama''ta fada cike dda jin dadin addu'o'inta
kafin ta rafi sai data tambayi yan qannenta me suke so ta saya musu kowa ya fadi abinda yakeso wanda bai wuce sabon unifoarm,jakar makaranta da lunch boxs,excercise book,lubabatu ce mai registration na placemen da sauran tarkacen kayan karatu,bata bar gidan ba sai data hadasu da lubabatun da kulu sukaje aka siyo,murna da tsalle kam sun sha shi,ko idon inna hadiza bata gani ba bare jamila ko binta,tana tsammanin ma basa gidan don idan banda isyaku data gani dazun da take shigowa gidan babu wanda ta gani cikinsu
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[8:18pm, 10/9/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣0⃣
*Daga abi musa al asha'ari R.A yace:Manzan Allah S A W yace da ni''ya Abdullahi dan qais,shin bana nuna maka wata taska daga cikin taskokin aljanna ba?LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH''a ruwayar nisa'i ya qara da ''LA MALJA'A MINALLAHI ILLA ILAIHI''*
*Daga abu hurairah R.A yace: Manzan Allah S A W yace ''duk wanda ya fadi SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI sau dari za'a kankare masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi''*
_ruwayar bukhari da muslim_
Bata bar gidan ba har baaban ya dawo,a tsaitsaye suka gaisa saboda an soma kiran sallar magariba ya daura alwala ya fice yace yana dawowa,itama alwalar tayi ta shiga dakinsu tayi sallah,tana idarwa kiran hindatu ya shigo,a dokance take cewa
''Allah yasa adda baki tafi ba,gamu nan ni da jabir''
''da daddaren nan''
''wlh,daga asibiti muke kuma akace kina gida''
''ina nan ban tafi ba baaba nake jira,sai kun iso''ta fada sanan kowacce ta kashe wayarta
Tana dakin baaban ita da shi bayan baaba huwaila ta ajjiye masa kwanukan abinci ta fice,hira suke yi abinau gwanin dadi,abin ya faranta ranta sosai,ashe akwai lokackn da zata ga rana irin wannan?,lallai komai yayk farko zaiyi qarshe,basu damu da yadda inna hadiza keta kai kawo bakin qofar dakin ba,baaban ya dubeta bayan ya ajjiye carbin hannunshi
''maryam,ina fata zaki yafemin,na dade ina daukan haqqinki,na yi watsi da duk wani haqqi naki da Allah ya doramin,tun kina mitsitsiyarki na watsar da duk wani haqqi naki da Allah ya dora min,gashi daga qarshe ta inuwarki muke samun rufin asiri,ki yafemin maryamu,haqiqa na dau darasi a rayuwata,na qiku don kuna 'ya'ya mata,ina neman dq namimi,ido rufe,sai gashi yarin yana daf da lalacewa,Allah ya sa baiyi girma mai yawa ba,duk da haka har yau na kasa saitashi kan hanya madaidaiciya saboda na riga da na batashi na nuna masa gata,duk da haka na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun da wuri,a yanzu ne nake ganin budi cikin harkokina da nake yalwatawa iyalina nake daukan duk wani nauyinsu bakin gwagwado,kimin afuwa maryam''
Itakam bata jin dadin yadda mahaifinta wanda yayi sanadiyyar zuwanta duniya ke faman roqonta haka
''nikam baaba wallahi abunda kamin bazan taba iya biyanka ba,banga wani da zaka yimin ba na riqeka,komai qaddara ne kuma nasan haka lah ya qaddara dama zanyi rayuwata''
''duk da haka,na sani maryamu ki yafe min''
''na yafe maka baaba har abada duniya da lahira''
''na gide madyamu na gode,Allah ya albarkci rayuwarki,ki sake yimin godiya gurin yaron nan abdullahi,babu shakka babu abinda zamu iya cewa da shi,tsakaninmu da shi fatan alkahairi ne''
har yanzu mamamin abdallah bai saketa ba,yaushe ya shiga jikin yan gidansu ne wai haka?,yaushe suka saba soaai har yake musu alkhairai bai taba nuna mata ba ko sau daya
Suna cikin dakin suka jiyo shigowar hindatu,shigowarta ne ya tunowa da baba sabon babur da jabir din ya siya masa ya dinga zuwa kasuw ko wata guda ba'a rufa ba yace maryam din ta tayashi godiya
Nan cikin dakin itama ta ahigo bayan sun gama gaisawa da mama suka sha hirarsu da baban,har kusan qarfe tamwas da rabi suna tare,tuni ta kira baaba sule tace ba sai yazk daukarta ba don hindatu tace su zasu maidata
har soro suka rakosu baaba huwaila da yan qannesu,a tsakar gida sukayi sallama da baaba,suna kallo su jamila da binta na leqensu ta window
cikin mota suka tadda jabir din,hannunsa ya dunqule yana mata jinjina irin ta sarakai''Allah yaja da ran antinmu,Allah ya taimakeki uwar gidan abdallah mai nasara''dariya ya bata ba kadan ba
''haba jabir,ka mance cewa ka girmeni irin wanan gaisuwa haka?''
''ai yanzu kece babba,ko kin mance kin bani 'yar qanwa,gimbiya hindatu,wadda ba qaramin yabawa da zaben da nayi nake ba har yau''dariya ya bas gaba dayansu har suka fara taciya suna hira abinsu
sai da suka fara biyawa ya yiwa hindatu siyayya ya hada harda maryam din kana suka ajjiyeta a gida sannan suka nufi nasu gidan
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
kwana bakwai mami bata bari an dakayar da gyaran da ake mata ba,tamkar ana shirin canza mata fata,ita kanta mai gyara ta yaba yadda gyaran ya karbi jikin maruym di sosai da sosai,baaba uwani kuwa zama take kawai tana kallon maryam din
''gaskiya meramu anya ba canza miki fata hajiyar nan me gyaran jiki take ba?''duk sanda ta fadi hakan dariya take basu ita da mami
Kusan tun ranar da sukayi waya da abdalla kan zuwanta gida basu sake samun kiranshi ba,ana gobe kwanaki bakwai din da ya diba zasu cika mami ta nemeshi don taji goben zai dawo,saidai ta nemi layin nasa yafi sau goma bata sameshi ba,har cikin dare tana iransa bata sameshi
da safe ma hakan ce ta faru,damuwarta ta kasa boyuwa ta tadda maryam a kitchen tana goge freezer tare da sake jera kayan ciki don mamin ta hanata yin kowanne aiki
''ni kam maryam kina samun abdallah a waya kuwa''maryam din ta waiwayo ta dubi mamin sai ta rasa amsar da zata bata,don ita kanta tasha kasa kunne cikin dare lo da rana taga ko zata samu koda texs nasa,Allah ya taimaketa tin kafin tace wani abu mamin tace
''sam ba'a samun wayanshi,na kira na kira duka akashe''
jikinta taki yayo sanyi gaba daya,gabanta ya dan fara faduwa kada kadan ta juyo gaba daya ga mamin tace
''to mami ni cewa nayi ko chargy ne babu a wayoyin nashi?''
kai ta girgiza
''bana jin haka,saboda ba cikin wani qauye bane cikin tsakiyar abuja ne fa,kusa da villa,kinga ta yaya za'a rasa chargy a wayoyi?''
sbiru ya sake ratsa tsakani,bayyanar damuwa kan fuskar maryam wadda ita kanta batasan ta bayyana bayasa mami riqe hannunta
''kada ki damu in sha Allah he is safe''
kai ta gyada asanyaye,sai ta kasa qarasa ci gaba da aikin ta biyo bayan mami ta fita a kitchen din ta koma dakinta ta kwanta
Maganganunshi na qarshe ta dinga tunawa
_''Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo da ni,kimin addu'a don muhimmin aiki zan gabatar,wanda ko shine aiki na na qarshe da zan aiwatar in sha Allahu sai na gabatar da shi,ki sakani a addu'o'inki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam''_
Wani irin juyi tayi cikin matsananciyar faduwar gaba ta tashi ta zauna sosai kan katifarta,sai taji kanta ya sara ta dafe goshinta da sauri kana ta maida jikinta fuskar gadon ta jingina
kusan wuni tayi sukuku zuciyarta ba dadi,duk motsin da tayi maganansu ya qarzhe a airport ke mata amsa kuwwa a kunnenta,ko falon bata sake fitowa ba saboda rashin kuzari,mami keta leqota don kada ta takure ranta ta sa damuwa,ta karanci wani kalarson abdallan mai qarfi cikin zuciyar maryam din,da taga ta leqo ta sai ta qirqiri murmushin dole,gaba daya walwalarta ta ragu,ta dinga kiran layin abdallah a jejjere kamar wadda aka bata aikin yi amma ko da wasa bata shiga ba is switched off computer keta faman gaya mata,
Cikin kwana biyu duk yadda taso hana kanta damuwa zuciyarta tace batasan wannan ba,bata taba jin damuwa irin ta wannan lokacin ba,bata taba jin ta damu da wani abu a rayuwarta ba kamar wannan lokacin
cikin kwana na uku ta gaza daurewa
fitowarta a wanka kenan wanda tun safe ta kasa yinsa sai kusan daya na rana ta samu tayi,mai kawai ta shafa ta fesa turare ta zira doguwar riga ta nade kanta da mayafinta,takalmanta plate ta jawo ta saka kana ta fito,babu kowa bangaren don mami ta fita asibiti don haka ta fito waiting parlour ta zauna tana kallon shigewa da ake tayi da sabbin furniture bangaren nene a da,bata cikin nutsuwarta batasan wa zai zauna anan ba bata kuma damu data sani din ba,abinda ke cunkushe kadai a ranta ya isheta jarraba
number din hisham ta laluba ta kirashi,daga yanayin yadda taji sun gaisa har yana zolayarta ta tsinke da lamarin,sai kawai ta fasa tambayarsa ta kashe kiran,lambar abdallah ta sake trying wanda ta maida kiran tamkar ibada a gareta saidai amsar daya ce kamar kullum is switched off,ita kanta ta fuskanci yanayin damuwa kan fuskar mamin duk da bata kai tata ba,jin zuciyarta take kamar ana hura mata wuta
son abdallah
kewar abdallah
duk su suka mata rubdugu,kalamansa na qarshe a gareta ke sake sanya mata karaya,kawai sai ta zame a gun ta kwanta rub da ciki,batasan ya akayi ba ta tsinci kanta ne kawai tana kuka tuquru,bakinta na fadin
''kada ka yimin haka abdallah,kada ka guje ni,kada ka tafi ka barni''take furtawa a hankali cikin kuka,Allah ya taimaka mutanen dake aikin kafa kayan furniture din sun kammala sun fice
Kuka tayi mai yawan gaske har yasa idanunta suka kumbura baya ga zafu da radadin da suke mata amm hakan baisa ta haqura ba,sai da bacci ya lallabo ta taimaketa ya saceta,bacci ne mara dadi wanda tana yinshi tana sayke ajiyar zuciya ma kukan da ta yi
Hannu taji kan wuyanta a hankali ta soma bude kumburarrun idanunta wanda hasken daya cika falon yasa ta gaza budeshi gaba daya,mami ta gani tsaye a kanta tana fadin
''bacci kuma a waiting parlour maryamu?''ta tambayeta ba tare data lura da yadda idanunta suka sauya kala ba
''tashi ki koma daki idan baki gama ba kiyi a can amma nan ai yayi waje''
sosai tayi qoqarin tashi amma ta kasa,ga zaton mamin magagin bacci ne don haka ta kama hannunta don tayata tashin,zafin da taji da hucin zazzabi ya sata furta
''subhanallahi,maryam me ya sameki haka?''sai a lokacin ta lura da yadda idonta ya suntume fuskarta tayi jawur
''ya salamu ya Allah,maryam''mamin ta fada a rude,zare wayar hannun maryam din tayi don ta miqar da ita,number din abdallah ta gani kan scrren din wayar,sai ta dubi maryam din
''abdallah dai maryam?duka a kanshi kika yiwa idanunki haka?,sai kace an ce miki ya mutu ne''kalmar mutuwa data ambata wa abdallan sai ta sake karyar mata da zuciya,take taji ko,mutuwar ma yayi ne tunda gashi mami ta fada?,sabbin hawaye suka soma tsiyayowa,sai mamin ta dafe kanta don ta fuskanci abinda ya sakata kukan
''babu abinda ya samu abdallah maryam,tashi maza mu shiga ciki ki je ki watsa ruwa ki karbi magani,zafin zazzabin nan yayi yawa kada ya zama wani abun kuma daban''
mamin ce ta taimaka mata har ta shiga toilet kana ta fita ta bar mata dakin ta haye samanta don tayi wanka,itama ta hada mata magungunan da zata sha da zai saukar mata da zazzabin,zuciyarta fal da fafinciki jinjinawa da yaba tsaftatacciya kuma ingattaciyar qauna kuma mai qarfi da ya samu daga gun matarshi,wanda tayi imanin koda bafa duniya zai samu kyakkaywan kulawa a rayuwarshi
Ta kammala watsa ruwan ta canza kaya,da qyar ta iya bada sallar azahar da la'asar da suka shigeta ta dawo ta nade a gado,har yanzu zazzabin tana jinsa cikin qashinta,a haka mami ta taras da ita
Sai data tilastata taci abincin da ta shigo da shi sannan ta bata maganin ta sha,tana nan a gurinta har bacci ya sake daukarta sanann ta fita dakin
Bata farka ba sai da wani amai mai zafi ya farkar da ita,da gudu ta miqe kanta na sarawa ta shiga bandakin ta dinga kwarashi,mami wadda ta idar da sallar magariba tana jiran isha ta dawo falin qasa ta zauna saboda maryam din ta fara jiyo kakarin amai,da hanzarinta ta shiga dakin,ita ta wanke gun data bata din ta maidata gado ta kwantar tana mata sannu,ta taba jikinta kana cikin damuwa tace
''maryam anya ba ciki gareki ba kuwa?''
duk da tana cikin ciwo sai da tambayar tq bata kunya,tayi qasa da idonta tana girgixa kai,sake matsowa mamin tayi tana lallabarta
''kada kiji kunyata idan shine ki gayan kada na yita baki magunguna muyi asararsa don Allah''
nan ma kai kadai ta iya girgiza mata ta kasa hada ido da ita
''to shikenan,allura dama zan miki naji zazzabin yaqi sauka''
sam bata qaunar allura,da kayi mata allura gwara ka zabga mata mari,ita ta sani ciwonta ba na magani ko allura bane,da sauri cikin murya ta marasa lafiya tace
''don Allah mami ba yanzu ba,a barshi sai anjima zai iya sauka''ta fahimci allurar ce bata so don haka ta qyaleta ta sake bata wasu magungunan
Ranar kam har kusan biyu na dare ana fama,qarshe dai allurar da bataso mamin ta mata,bayan tasha fama da ita kafin ta tsaya din,sai kusan uku saura na dare ta samu bacci ita kuma mamin ta koma dakinta
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
A daddafe ta tashi tayi sallar asuba sakamakon baccin daya cika mata ido,duk da zazzabin ya sauka baki daya sai ciwon kai dake son matsanta mata kuma,da qyar ta gama sallar ta kwanta saman daddumar zuciyarta babu dadi,duk wani minti idan ya wuce sai taji kamar yana sake nesantata da abdallah ne
A hankali taji an turo qofar dakin,ta daga kai tana amsa sallamar da akeyi,mami ce cikin hijabinta da carbi a hannunta da alama idar da sallarta kenan itama,tayi qoqarin tashi zaune don gaisheta mamin tace a'ah yi kwanciyarki,a haka suka gaisa ta duba jikin taji babu zazzabin,shuru tayi bata ce mata kan nata na ciwo ba din kada ta daga mata hankali
''yanzu maryamu jinkirin dawowar abdallah yasa kika matsantawa kanki da damuwa haka har da ciwo?,lallai ba shakka gaba guduwa zaki dinga yi kibi mijinki kuna barina kenan?''ta fada cikin tsokana da zolaya,kunya ta kama maryam sosai,ita kanta batasan tana misbehaving har haka ba,batasan ya akayi abun ya hudata haka ba har yake bayyana kanshi da kanshi ba tare da ta sani ba.
''a'ah daina jin kunyata,ni hakan dadi ya yimin sosai,Allah ya qara hada kanku,aikin da yayi ne ya tsaudashi jiya kafin na kwanta saiga kiranshi,amma alhamdulillahi an samu nasara ya kama dukkan jama'ar daya shirya kamawar sai mu yiwa Allah godiya''
hakanan taji wani sanyi na sauka tun daga kanta har tafin qafarta,a gida ko a waje abdallah jarumi ne tabbas babu kokwanto,a hanakali cikin zuciyarta ta dinga fadin alhamdulillah
''sai ki kwanta kiyi naccinki sosai,kiyi bacci harda minshari ko''ta sake fada cikin zolaya,murmushi tayi tana sake sunkuyar da kanta mamin ra mata sallama ta fice
Ta lumshe idonta tana jin wani shauqi na kamata,duk da ciwon da kanta yake murmushi sai daya subuce mata,ta dan dafe kanta idanu a lumshe,a hankali bacci mai dadi ya sureta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Sannu a hankali taji yanayin baccin nata na sauyawa,ta dinga bude idanunta a hankali har ta kammala budesu tas,yana zaune gefan gadon nata sanye da baqar jallabiya mai hula irin ta maza ya zuba mata idanu kamar wanda aka bashi aikin zana fuskarta,wani abu mai kama da farinciki taji ya ratsata
''welcome dear''ya fada a nutse
''an tashi lpy gimbiya?''ya tambayeta idanunsa har yanzu na kanta,kasa amsawa tayi sai cusa kanta da tayi cikin hijabinta,yayi maganar amma taqi dagiwa sabida haka ya tashi tsam ya koma gabanta yana qoqarkn dago fuskarta amma ta qiya,shima bai sakar mata qarfi ba ya qyaleta yana fadin
''kin daga min hankali da yawa baby,tun asuba na baro abuja duk sabida nazo na ganki amma kin min rowar fuskarki,shikenan na gode''ya fada yana miqewa zai fice a dakin,sai ta bude ido daya taba satar kallonshi tamkar ta tsaidashi tana kallo ya fice a dakin a hankali kamar wanda aka qididdigewa iya takun da zaiyi
Kunya da tsoro ranar suka hanata sakewa ko fitowa,sai taci gqba da kwanciyarta kan gado abinta mami na kulawa da ita a tsammaninta jikin da saura,tana son ta fito ko zata sake ganin fuskarshi amma kunya ta hanata,tana jiyo muryarshi a falo lokaci lokaci shida mami suna maganar bangaren nene da ta ga ana sawa sababbin furniture
_WASHEGARI_
Tas ta jita ta warke sosai,ko guntun ciwon kan ma babu shi,qarfe tara ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,muradin ganin abdallah take,shi kuma kamar ya sani tun jiyan bai sake leqota ba duk da ya turo mata guntun sms
_sorry dear na zama busy kan wani abu,see u later_,iya abinda ya turo kenan
Ta shirya cikin atamfa riga normal da zani rafa,tayi lite make up kana ta feshe jikinta da turaruka masu dadi,ta daura dankwalinta bayab ta gyara gashinta kai azabar santsi ta hadeshi da ribbom madaidaici,haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar,ba qarya ta mata kyau matuqa,muryarshi da jiyo a parlour ta haifar mata da fargaba,sai ta koma bakin gado ta zauna ta fasa yunqurin fitar da takeyi,ta dauki wayarta ta fara danne danne kanta a qasa
Raliya take turawa tex don taga missed call dinta na kiran data mata tana bacci
A hankali taji ana taba qofar kana aka turota,cikin qananun sakanni tattausan qamshi ya buwayi hancinta,qamshi ne mai kwantar da rai tamkad zai saka bacci a nata bangaren wani shauqi ya qara mata,kallo daya ta masa ta sauke idanunta qasa,kunya take ji sosai,ga wani maganadisu dake fisgarta cikin idanunshi,wani kyau na musamman taga an qara masa,gani take kamar mami ta gaya masa sirrinta,nauyin hada ido take da shi,yayi kyai sosai cikin light blue din shadda,babbar riga da yar ciki da wando,fadan irin kyawun da shaddar ta masa ma bata baki ne,shadda ce yar ubansu sai maiqo take tasha bugu,a hannunshi riqe da hularse,a gogone baqi a hannunshi na fata na kamfanin armani sai takalminsa half cover irin na maza,sai ya tashi sak dan kano don ba baya bane su wajen iya wankan shadda suna sahun gaba,ba qaramin amsarsa shigar tayi ba,do da wuya ya sanya kaya komai rashin kyawunsu suqi amsarsa ,fuskarsa cike da murmushi mai bayyana sirrin kyawunshi
''amincin Allah ya tabbata a gare ki baby,ina fata kin wayi gari cikin qoshin lafiya,af kice ma anko mukayi''ya fada cikin zolaya,sai a sannann ta dubi kalar atamfar da ta saka blue ce da baqi,duk da blue din ya dan dara nashi turuwa da kadan
qarasowa yayi bakin gadon ya tsugunna kana ya dafa cinyoyinta,abinda taji a jikinta shima shi yaji,sai tayi saurin zame hannun nasa,dauke hannun yayi yayi murmushi yana yiwa hular hannunshi kari ba tare da ya dubeta ba
''am too busy jiya naso inzo in sake tozali dake,ina daya bangaren can ana jeran amaryata''
sai tayi dumm ta rasa yadda zara fassara maganarshi
Ya miqe ya isa gaban madubinta ya daidaita hular bisa kanshi kana ya sake dawowa inda take
''wanne saqo kike da shi gun imna wuro,qauyen ni'ima zamu je,yau idan Allah ya nufa zan zama angon mero''
batasan lokacin da ta daga kanta ba,ta yi masa wani birkitaccen kallo ido cikin ido,wani irin zazzafan kishi baqinciki da takaici ya lullubeta
''naga kina duba na maryam idan da magana kiyi''ya fada yana sake matsowa kusa da ita tare da riqo hannayenta ya sanyasu tsakiyar tattausan tafin hannunsa,a zafafe ta fusge hannun nata kana cikin tsananin fushi da bacin rai da kuma masifa tace...........
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[4:28pm, 10/10/2017] Huguma👑: [3:31pm, 10/10/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣1⃣
*An karbo daga Anas dan maalik R A yace: Manzan Allah S A W yace''dukkan dan adam mai kuskure ne,mafi alkhairin masu kuskure sune wadanda suke tuba(idan sun aikata kuskuren kuma bazasu sake komawa ba)''*
Tace cikin wata iriyar murya mai dauke da tashin hankali
''jeka.....jeka nace,kaje tunda ka fadi abinda kake son gaya min lallai saqonka ya isa''tayi maganar cikin zafi da juyewar kalar qwayoyin idanunta
ya sake matsota yana fadin
''to kima me nayi don Allah maryam,ina cewa ke kika bada damarcda,zan qaro auren ko?,tunda na baki dama na ganin canji kafin dawowata saidai har naje na dawo din banga wani canki ba,it means abdallah jeka auri ero ko?''
Idanunta cikin nashi tana dubanshi kuka takeson tayi saidai ta kasa
''dama kana sonta din abdallah na dade da sanin hakan,toma meye donta ka aureta,hakan na nufin yankewar numfashin maryam da qarewar rayuwarta aduniya?''ya fuskanci ta fara ficewa daga saitinta,don haka sai ya miqe yana sake saba babbar rigarsa yana shirin ficewa tare da cewa ''Allah ya kyautq,Allah ya baki haquri,sai mun dawo''
tsintarta kawai yaui a gabansa tana tura qofar hadi da jingina jikinta da qofar,hawayen da bataso su fita su suka soma turereniya kan kuncinta.
Ta jingina kanta da bango kana ta saki kuka,muryarta a shaqe cikin raahin sanin me yake fitowa daga bakinta tace
''idan kana so ka tafi kaje,amma banu inda zaka fita abdallah sai ka tsaga qirjina ka cire zuciyata ka tafi da ita,wananna wanne irin so ne?,wanne irin horo ne wanan?,na gaji.....na gaji abdallah da irin wanann horon,me yasa kake ma zuciuata irin wanann hukuncin?,me yasa ka kasa gane qirjin maryam cike yake da so da kuma qaunarka?,kasan matsayinka a cikinta kuwa?''
Kasa tsayuwa yayi har sai da ya qarasa inda take tsayen yasa hannayenahi duka biuun ya dafe shima qofar ya yiwa maryam din rumfa,numfashinsa na fita da sauri,wani irin nau'in farinciki da baiyi tsammanin akwai irinsa cikin duniya ba ya mamaye ilahirin jiki jini tsoka da zuciyarsa yace
''abdallah ya dade da sanin ya dasa qauna cikin zuciyar maryamunshi,irin qaunar da ko mutuwa kayi bata barin zuciya ta huta,abu daya abdallah yake da muradon ji daga bakin mace qwaya daya tal aduniya shine *NIMA INA SONKA ABDALLAH KWATANKWACIN YADDA KAKE SONA K......*
*NIMA INA SONKA ABDALLAH FIYE DA YADDA KAKE SONA,FIYE DA YADDA KAKE TSAMMANI KO HASAAHE CIKIN ZUCIYARKA*,ta fada cikin tare numfashinsa ba tare da ta barshi ua kammala fadar abinda zaima fada din ba,kasa daurewa yayi sai da ya ji duminta ajikinsa,sai da yaji hucin numfashinsu na gauraya guri guda,gaba daya ta narke a qirjin nasa tana sake cusa kanta cikin qirjin nasa,tsaiwa ce ta gagaresu ya jata gefan gadon suka zauna,bai janata kuka na don shi kansa badon kada ya nada yammazqn ba dira kanshi zaiyi a kafadarya ya sha kukanshi saboda tsabar farin cikin da yaji yana kewaye duniyar subhana da shi
A hankali kukan ya soma jan baya sai ta janye jikinta ta dubeshi da brown oily eyes dinta da a yau suka sauya kama
''abdallah......mero fa?''ta tambayeshi tana jan majina,dariya taso qwace masa dik da haka sai da murmushi ya wadaci fuskarsa,ta tsareshi da ido sosai da alama kishi ne ya bude fagenshi cikin zuciyarta,sai da ya lakuce mata hanci kana yace
''gaki nan,ai kece *MERO NA*kuma kece *MAIRAMU* hakanan kece *DIYANA* duka''
kunya ta kamata,wai haka abdallah ya qware wajen buga game ne?,bata tsammaci a fili tayi maganar na sai da taji yace
''yes abdallah good player ne,sanna kuma winner ne,yau nayi winning,the game is OVER today''shigewa jikinsa tayi yama boye kanta aqirjonsa murmushi kwance kan fuskarta,hannunahi duka ya sanya ya marabceta zuwa jikinsa yana fadi cikin dariya dariya
''ashe haka kike da kishi maryam?,amma fa kin danji kunya kadan,kishi da 'yar qauye?,ya akahi kika aminta abdallah zai iya duban wata mace dina ma burgewa ma balle a kai ga batun so,macen ma irin mero,kin manta da su abida salma saddiqa zubaida da sauransu,basu isheni kallo ba sai mero?''
Kuma fa haka me,but ya akayi ta kasa tunanin hakan kishi duk yabi ya rufe mata ido ,ba shakka taji kunya,sake duqunqunewa tayi a jikinsa
''amma fa ta bangare guda kin burgeni haka nan kin gama biyana''ya fada yana lalubar kunnenta son so yake maganar ta koma ta sirri tsakaninsu
''yadda kika nuna kishi na na tabbatar cewa ni din ba qaramin dan gata bane''
Tayi har da ido duk da bai ganinta,can qasa muryarta tace
''amma daurin auren wa zaku a ni'ima,kuma waye zai zauna a bangaren nene na da''
''daurin auren mero,amma fa meron qauye,kuma a ni'ima din sannan bangaren nene na da anan zata zauna nata ne''
sai ta miqe daga jikinsa,hawayen ta na som dawowa
''abdallah ya zaka yimin haka,dai da zuciyata ta gama kamuwa da qaunarka zaka qara aure,bazan iya ba....bazan iya sharing wata da kai ba Allah,ina kishinka fiye da yadda kake zato''ta fada tana girgiza kanta tare da yunqurin sauka daga gadon,wayyo farinciki ya kamashi kamar yayi adungure,tuni ya riqota yana girgiza kai shima ya birkitota ta fada jikinsa ya rungumeta tsam
''Allah na gode maka da ka bani mai kishi na,nasan ba komai ya jawo hakan ba face tsatsar qauna,calm down madam,maro zata auri labaran ne nata nacan qauye na daukota ta zauna nan ne tare da mami ta dinga tayata da aikace aikace da kula da gida,tunda mamin tace tana sonmu tana son zama da mu amma ta rantse gidan mu zamu tafi,ba zata zauna tare da mu ba gudun shiga haqqinmu,labaran kuma na bashi aiki cikin kamfanoni na na nan kano,kuma banyi qarya ba *YAU ANGON MERO NAKE AMMA MERO DIYA NA* don na tabbatar yau ba zaki tsallake tarkona ba saikin fallasa min da bakinki qaunar da kike son binneta cikin ranki bayan akwai mamallakinta,shi yasa nayi miki adon angwayen don nima ango ne,haka daga yau ba zaki sake kwana gidan mami ba sai cikin gidanmu,gidan da na fara ginashi tun daga sanda na fara tizali dake a rayuwata,don ke dama na ginashi na dana jeshi dalili kenan da yasa a china na muku shigar sauri na zabi *gadon amarcinmu* don ni kadai nasan wanda zaifi dacewa da gidan,a lokacin mami na ganin na miki shishshigi batasan tanadi na yiwa kaina ba''
''wato abdallah mugun dan duniya ne?,ya iya buga qwallo son ranshi cikin hikima kuma ya saka ta cikin raga ba tare da golan ya sani ba''maryam ke gulmarsa cikin ranta bayan tayi luf a qirjinsa,tashi yayi ua fidda babbar rigar jikinsa ya dorata saman madubi bayan ya je ya sakawa dakin key,ya cire yar cikin ma daga shi saura farar vest dinshi qal da dogon wandon shaddar,gadon ya dawo ya haye yana fadin
''yau kam nima zan more soyayya mai 'yanci''sai ya kuma bata kunya ta cusa kanta tsakani cinyoyinta,sam ta kasa hada udo da shi,kowanne sakon kunya yake sata turata ciki,anan ya lalace yana gaya mata yadda take da tasiri cikin zuciyarsairin girman matsayinta,da irin yadda yake ji game da ita,yadda sonta ya dade da illata zuciyarsa,duk inda ta duqa sai ya hanata,yace ta barshi yau ya bararraje ya fidda duk wani feelings da yake ji game da ita,daga qarshe tallafe kumatunta tayi tana kallonshi,tayi imanin ya zauce cikin so kamar yadda ita ta zauce,saidai tsakanin shi da ita batasan wanda yafi wani ba,sau biyar hisham yana kiransa yana katsewa,qarshe ma ya daga yana fadin
''kaga malam idan zaka kama hanyarka ka wakilceni shikenan,nikam a inda nake yanzu ko mami,nasan zata min uziri''da yaga yaqi daina kiran nasa sai ya kashe wayar baki daya ya jawo bedside ya wullasu ciki yana jan tsaki ya sake dawowa sukayi zaman dirshan saman gadon suna kallon junansu cike da shauqim bege da qauna
Itama mamin ba ta nemi ko daya daga cikinsu ba kamar tasan tsiyar da abdallah ya qulla,cikin dakin sukayi sallar azahar har ma da la'asar,babu wanda yayi tunanin wani abu waishi abinci a cikinsu,wani irin shauqi ke dawainiya da su wanda gaba dayansu basu taba zaton akwai irinshi ba,a haka ma maryam na doddojewa saboda tsoro da gudun kada a tafka abun kunya cikin gidan suruka,ya qaraci fitinarsa sau biyu yana wanka tana kallonsa,
Sai da suka idar da la'asar maryam tace
''ya kamata ka tafi haka,kaga kada mami taga rashin,hankalinmu''kamar ma ba da shi take ba sai ua dira kansa saman cinyarta yayi kwamciyarsa yana fadin
''babu rashin hankali,tsakanin miji da mata sai Allah ita kanta mamin ya sani,nasam ta mana uziri,uziri kam dole ne ayi mana musamman ni Allah sarki da na jima ina faman rainon soyayyarki tun kima qwaila''ya qarshe maganar cikin salon zolaya
ta fara tura bakinta tana qoqarin tureshi
''ni daga ni,nikam ba qwaila bace ko a da dinma''yadda ta turo bakin ba qaramin sha'awa ya bashi ba,bai iya haqura ba sai da tsotseshi tas,abdallah na haukata ta iya yau da salon soyayyarshi tana zaton na gaba sawa zaiyi ta manta kowa da komai
cikin haka sukaji ana knocking,aka rasa mai magana tsakaninsu,murya qasa qasa tana zare ido tace
''mami ce fa''
kafada ya daga ya ware hannunshi kana ya miqe ya nufi qofar,ido ta sake zarowa ta biyoshi da sauri tana roqonsa qasa qasa saitin kunnanshi kada ya bude sai yasa rigarsa
''sai na cire wanann ma na zauna da boxer ki da kanta ma idan mami ce anjima zata kaimu gidanmu''kunu tasha tana miqo masa rigarsa kana ta fece bandaki ta saka maqulli ta buya,bai kuwa saka rigar ba ya budewa mamin,ita kanta sai da taji kunya ta kamata,ta kautar da kanta sanan tace
''ba kai nake nema ba diyata nake nema,kasan bata gama warkewa ba akwai sauran magungunanta da zata sh''
shima sai ya hau sosa kai don ya gama fuskantar inda mamin ta dosa
''mami ki kawo sai na bata''
hararasa tayi gafara min ni na wuce,haka zaka dirka mata maganin bata ci komai ba tun safe?,baka iya kula da mutum ba sai sakarci ka iya''ba shiri ya matsa ma ta shigo,ta kalli gadon da suka yamutsashi don akai suka yini salla ke sauko da su ta dauke kanta tana kiran sunan maryam din,gyaran murya ta yiwa mamin kamar maiyin wani abu a bandakin
sai ta samu gefan kujera ta zuan bayan ta ajjiye maganin kan madubi,shima gefan madubin ya jingina yana fadin
''kinsan kuwa mami cikin wadanda na kama tare da alhj hamza da yaranshi harda adnan?,mami ashe yana daga cikin manyan yaranshi,duka poising da naci sau biyu har da hadin gwiwar alhj hamza din''salati mamin ta saka tana tafa hannayenta
''kai Allah ka tsare mana imaninmu ya Allah,wadan nan mutane wadan nan mutane sun cika butulu,amma dama hausawa sunce idan zaka gina rakin mugunta ka ginasho gajere wataqila kai zaka fada,yanzu gashi su suka fada din,nene kam ba ita ba labarinta har yau ita da zubaida,yanzu don Allah meye ranar wanann?''
kanshi a duqe yake jijjiga kai,har yau yana jin takaicin yadda mutanen suka ci amanar mahaifinaa da mahaifiyarsa,har yau yana tuna yadda babanshi da mamanshi suka hada gwiwa aka auro nene gidan cikin halin qunci da wahala ita da yayanta amma yau da ita akayi yunqurin rusa su badon Allah baya bacci ba ya basu kariya da kariyarsa,kasa cewa komai yayi don idan ya tuna su bacin ransa ne ke tashi qwarai da gaske,badon mami tace ya qyalesu ba dukkanau sai ya nemo su yayi shari'a da su har igiya tayi saura,amma gashi a yau ya samu adnan wanda ko tantama baya yi hukuncin kisa ne zai rataya awuyansa sabida irin barna da kisa da suka dinga yi
shuru shiru maryam bata sake motsawa ba,babu yadda mami batayi ta fito ba amma ta kasa,shi kuwa abdallah na gefe yana musu dariya,da mamin ta gaji tilas tace
''aishikenan gasu nan idan kin fito din kyasha,ki tabbatar da kinsha kuma sabidayau hajiya lailan tace kisha shi''ta juya ga abdallah dake masu dariya
''ka shiga tsakaninmu ko,zaka dara da kyau musamman idan na saka ranar tarewarku nan da watanni goma''
''lokacin ta haihu kenan ta gama wankan jego'' 🙄,ya fada qasa qasa yana duban sama
''me kace?''mamin ta tambaya,da sauri yana dariya yace
''babu komai mami,Allah bani na shiga tsakaninku ba,kunyarki dai kawai take ji''
''gafara min,ka maidani wata kakarka ko,tamu ce ni da kai''ta fadactana rabeshi ta fice qasan zuciyarta cike da farinciki,ta tabbatar cewa irin qaunar da take sha'awa danta ya samu ga matarsa ya gama samunta sai godiya ga Allah,abdallah kam ta sani bamai wasa bane gun kula da nunawa iyali soyayya tuntuni ta sani halinshi ne a qidarsa ce
Wanka kawai ta zarce da yi bayan ta ji fitar mamin,kayan jikinta ta maida don ta tabbatar abdalla yana dakin,towel ta rufawa kanta sabida jikqewa da sumar tata tayi,yana tsaye bakin madubin hannunshi daya ya dafe amdubin da shi dayan kuma yana ruqe da yar kwalabar maganin yana karanta rubutun lrabcin dake jiki,ta qarasa gaban madubin da sauri da niyyar tattare magungunan don batason ya gane na meye,ajjiye kwalbar yayi ya zare towel dake kanta yaci gaba da goge mata ruwan gashin nata na burgeshi tare da bata sha'awa
''baby kici abinci gaskiya kisha maganin nan''
''na ciwon kaine kuma ya riga da ya sauka''ta fada akunyace
dariya ya saka kana yace
''eh kam gaskiya ne,na gani ai''
ta tsargu don haka tace
''qarya nayi kenan?''ta fad tana hade rai din kada ya bullo da wani abun,ai kam bai fasa ba sai da ya ja habarta yana dariya yace
''gaskiya na sake tabbatar da irin son da mami na kemin,ya Alah ka sake jamin da ranta ka qara mata lafiya da tsawon rai mai amfani,kice gyarani kawai take yi ni ban ma sani ba,i luv my momma''sai kuma tayi shiru bata data cewa don ta tabbatar ya gani
sai ya leqa fuskarta bayan ya jawota ua rungumeta ta baya kana ya dora habarsa kan kafadarta yana cewa
''kina zaton Abdallah bai iya larabci ba ko yammata,zan baki mamaki kamar yadda na saba,kwanan nan zan daina magana dake da hausa''
dariya ta subuce mata
''ni din ma akace ban iya bane?''
''i know baby na,ke din gwanace ta kowanne bangarr tunda kika iya sace zuciyar abdallah tun ruwanki bai isa alwala ba shi kuma da ya tashi ramawa sai ya haukataki baki daya ko?''diddira qafarta ta shiga yi cike da shagwaba taba kukan qarya,anan ya lalace yana ta faman kallonta,don ba qaramin kyau tayi masa ba ji yaje kamar ya hadiyeta ya huta
Bai fita adakin ba kuwa sai da aka kira sallar magriba,yana fita ta rufe da key don tasan idan batayi da gaske ba ma yana iya cewa adakin zai kwana mata tundavyaga mami mai dauke kai ce wunin sur ta fita a harkarsu tana cikin mutanen dake ta aikin bangaren mero
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Tun kafin ta tashi abacci yake ta faman doko mata kira tazo yana son ganinta,har qaryar bashi da lpy ya mata,tana jin kiran nasa ta shareshi don haka jiya ya dinga buga mata qofa har ya bata kunya don baaba uwani ta jisu tana ji tana gaya masa qila tayi bacci ne
Takanas ya tashi ya taho dakin nata ya soma buga mata,cusa kanta tayi qarqashin fillow tana kuma qudunduna cikin bargon,qasa qasa yake kiran sunata
''wayyo abdallah wallahi kunya kawai kake bani,tun jiya kasa na kasa hada ido da mami na''haka ta dinga fada cikin zuciyarta,likimo taci gaba da yi har ta daina jin bugun nasa
Qarfe tara da rabi ta fito a wanka taba gaban madubi daure da zani ta lulluba towel a kanta ta ji ana knocking,sai da ta tambaya taji baaba uwani ce don haka kai tsaye ta bude mata ta juya tana fadin
''shigo baaba yanzu nake shirin zuwa kitchen din nasan kina can kina aiki ke daya,yau bacci ne ya danneni wlh''
''wani baccin zaki sake kuwa yanzu yanzun nan''taji muryar abdallah,kafin ta waiwayo tuni ya rungumeta ta baya hannu daya yasa ya sakawa qofar muqulli,ya sake matseta gam ajikinsa yana lalubarta
duk inda ta ruqe hannunshi sai ua zame har sai da yayi iya yinsa kana ya saketa,zatq gudu toilet yace
''wallahi kika gudu ina da spare key idan na bude ki zaki dandana aguna''tilas ta tsaya yana dubansa ya birkice gaba daya,sai ya koma gefan gadon ua zauna,ya dauki kusan minti ashirin kafin ya daidaita,ya sake kallonta tana zaune kan dressing chair ta juya masa baya
''kinsan jiya da qyar na iya bacci kuwa baby,kuma kika hanani ko duminki naji ma''
A shagwabe tace ''kayi haquri,mami sai taha rashin kunyarmu yayi yawa a matsayinmu na hausa fulani,kuma kunya kaga wani yanki ne daga cikin imani''
kai ya gyada
''alright,naga kamar tsoro na kike baby tun yanzun,idan shine ma pls ki cire shi a ranki,don ni mitum ne da keson maida matarsa ta zamar masa tamkar qawarshi,jeki saka kayankin kizo mu gaisa''ba musu ta bude kayan sawarta ta ciro atamfa,a hankali ya tashi ya isa gareta ya ruqe hannun ya maida atamfar yana fadin
''atamfa atamfa dai baby,yau kam ba atamfa nakeso ki saka min ba''yayi maganar idonshi akan kayan nata yana lalubawa,wani material ya ciro mata dinkin fitted gown,orange ne da adon baqi,ta dubeshi bayan ta marairaice
''yayi tsiraici da yawa wannan,kuma kasan bamu kadai bane cikin gidan''ya tubure mata shi au yakeso ta saka masa,da qyar ta lallabashi ya haqura ya sauya mata wani lace riga da skert tare davalqawarin koda anjima ne zata sa masa wannan din
Toilet tayi nufin shiga ta saka kayan yace sam bai yarda ba shikam,sai baya ya juya mata ta sanya underwears,bata kai ga fara sanya kayan ba ma ya juyo shi tana ji tana gani ya shiryata cikin lace din,ba qaramin kayu kuwa tayi ba,zagayata yq dingayi yana qare mata kallo kafin daga bisani ya jata cikin jikinsa yana shaqar qamshinta,sun jima a haka ba tare da ta hanashi ba kafin daga bisani ya fidda mata mayafi yace ta saka
Da qyar ta iya zuwa gun mamin ta gaidata ta kasa hada ido sam da ita,ita kuwa murmushin take,dadi take ji cikin ranta da Allah ya bata suruka mai kunya ba irin surukan zamqni ba da idanunsu ke tsakar ka,suna ganin ai an dade tare da suruka an zama daya idanunsu ya soye don haka babu wata kunya tsakaninsu,qarshe zamewa tayi kitchen gurin baaba uwani
Suna kitchen suna aikin girkin rana ita da baaba uwani,duk da yadda abdallah yaso hanata taqi,sabida ta sani sarai idan ta biye masa kadan daga aikinsa suyi wunin daki bai ko jin kunyar idin mami,ga gidan yau ba laifi akwai mutane,murya ta jiyo cikin falo tamkar ta inna wuro,da azama ta fito falon nan sukayi kacibus,ita dince kuwa,farinciki ya kama maryam din don ma kunyar mami ta hanata sakewa,ita inna wuron ta yo gaba ne sabida anjima kadan za'a taho da mero amarya,hidima sosai mami ta dinga yi da inna wuron,ina kasa ina ka ajjiye ta,jinta take kamar babbar yayarta,mutanen nada wata irin qima da matsayi mai yawa a idanunta,ba zata taba mancewa da su ba,alkhairinsu mai tarin yawa ne a gareta ita da iyalinta,daki guda aka bude nata daya daga cikin dakuna hudun dake corridor din dakinsu maryam
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[4:09pm, 10/11/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣2⃣
*Daga abdullahi dan mas'ud R.A yace:Manzan Allah S A W yace''idan kuka kasance ku uku,kada mutum biyu(su kebe)su gana (su ware cikon dayan da suke tare),har sai sun cakudu da wasu mutanen(sun fi uku kenan),saboda dalilin haka(kebewar tasu su biyu su barshi shi kadai)zai iya bata masa rai/baqinciki''*
_ruwayar bukhari da muslim_
_MASOYANA NAGA SAQONNINKU,SAIDAI,BAN KAI GA DUBAWA BA WAYAR TAYI RESTORE DI SAQONNIN,SABODA HAKA AYIMIN AFUWA NA RASHIN GANIN REPLY,INA GODIYA YABAWA TARE DA JINJINAWA QAUNAR DA KUKE GWADAMUN TA BAN MAMAKI,ALLAH YA SO KU KAMAR YADDA KUKA SONI_😍
Abdallah ya kasa ya tsare,shikam yace an takura shi saboda baqin da auka dinga yi cikin gidan sun hanashi ganin maryamansa wadda tana cikinsu ana hidima da ita,duk da mami ma ta hanata yin wani abin saboda gyaran jikinta
Gab da magariba aka iso da mero gidan,a qalla mutum ashirin 'yan rakiyarta,kai tsaye suka fara da kawota gurin mami,maryam ce ta kamata ta mata iso saman mamin
''masha Allahu,Allah ya sanya albarka,ku kaita gidanta ta hita tunda dai mina tare ai babu damuwa''cewar mamin din haka ta sauko da ita suka nufin sashen sa yake a yanzu mallakinta
Bakin yan uwan meron harda na labaran yaqi rufuwa,kowa sam barka yake yana fadin ashe wani jinkirin alkhairi ne,gashi llkaci daua ta sanadiyyar wannma nawam Allah mero kin shiga daular da duk cikin ahalinmu ko a tarihi babu wanda ya taba shigarta,ya baku mazauni ya miki kayan daki ya bawa mijinki aiki ai babu abinda yayi saura tsakaninku face biyayya da fatan alkhairi''cewarsu,kallo kam sin shashi din lungu da saqo na gidan cikindaren banu inda basu leqa shi ba,itakam maryam wami abun su bata dariya wani anun su bata mamaki
maryam ta yaye lullubin da meron ta qudundune kanta aciki tana fadin
''to ai ba kowa adakin daga ni sai ke ko,sai ki bude kan hakanan kisha iska''itakam ko kadan bata ma kin zafi sai sanyi sanyi da take ji sakamakon ac data ratsa dakin,ta yaye mayafin tana kallon maryam,ita din ma kallon meron take tana murmushi tare da fadin
''umm,su mero amarya''murmushin itana tayi tana fadin
''yauahe rabon da kimin daiya mairamu?,da kin dauka zan auri yaya abdullahi ne ko?,ai ko wani abi gaya min ba nasan yafi qarfina,a wautata dai na soshi da farko,daga baya indo ta ankarar da ni,duk abinda fa kika ga munayi tsarawa mukayi,shiri ne kawai harda hadin bakin inna wuro,amma ba gaske bane''
Dariya ta kama maryam tace
''wato harda inna wuro kuka so haukatani ko?,to shikenan nina zan rama,nan da watanni zan bawa labqran qanwata ya aura kema kiji yadda akejin kishi''dariya ta qyalqyale da shi sannan tace
''kiyi haquri adda mairamu,wallahi ina sin labaran dina,musamman ma yanzu da mukayi aure''dafa ta tatyi tace
''kada ki damu nima wasa nake miki,Allah ya bar kowa da masoyinshi''
''ameen adda''
''yau kuma na zama adda kenan ko?''ta fada cikin sigar tsokana''fuskarta ta rufevtana dariya
''eh ai innata cectace duk abinda ban san ba na tambayeki kada nazo nayita yin shirme,tunda kin girmeni''
jinjina lanta tayi tana murmushi,mintuna kadan suka qara maryam din ta miqe tana fadin zata ta kwanta sai da safe din qila angon ya kusa shigowa don tana jin lokacin da ya kira meron a wayar da ya siya mata yar nokia mai torch,ta tambayeta me take da buqata ta kawo mata
girgiza kanta tayi kamar zatayi kuka,banu komai adda ni kawai tsoron kwana nake anan,murmushi tayi don ta fuskanci me take nufi
''hmmm,ni dake duka jirgi daya ya debo mu ai,ban san me ke a ciki ba balle na taimaka miki''ta fada cikin zuciyarta,amma a fili sai tace
''kada ki damu ai yanzu labaran din zai qaraso,bake daya zaki kwana ba,kiyi,haquri kinji''a sanyaye tace ''to,amma wayata ba caji ko zaki ara min igiyar cajinki''
''bara naje na dauko miki minti biyu''ta fadi tana juyawa tare da ficewa daga bangaren
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Shida mamin ne tsaye cikin falon hannunshi dauke da kayan bacci na maza,tun dazun yake mata rigima ahifa nazai koma bangarenshi ba
''hooo abdallah,to wai ya kakeso ne da ni,na gaya maka an kwashe maka kayanka dagadakin sabida duka dakin baqi ne a ciki,gobr zasu koma garinsu ko so kake na koresu daga dakin kai ka shiga ka kwanta bayan ga bangarenka can,abinda yasa dama ban barka ka koma daga dawowarka ba gyara ne akeyi kuma an riga da an kammala an maida komai muhallinsa''
cikin shagwaba kamar wani qanqanin,yaro yace
''amma mami for god sake sai kace maye za'a kaini can ni kadai na kwana''
''ohhh,da can da kake kwanar mayen ne kai,ko wani abun ya gutsiri namanka?''
kai ya mirgina
''Allah mami ki rage sona,ina ma laifin kive in kwana dakin maryam tunda ita kadai ce,kawai sai a kaini qarshen gida ni daya tal kamar maraya''
dariya taso kamata amma sai ta dake
''anzo gurin,dama abinda yake ranka kenan kakeson fada,to anqi din,ko kunyar baqi ba zaka ji ba ka tsallakesu ka tafi dakin matarka kwana?,kaga kaina ciwo yake ka wuce sashenka kaje ka kwanta har abinci nasa an kai maka,idan kaqi kuma ka kwana a parlour shikenan''daga haka ta kama step din bene ta haye tana masa dariya cikin ranta
Sai data haye baki daya sanan ha dawo da kallonsa parlour din,yaja qwafa cikin zuciyarsa yana cewa ''duk a gama boye maryam din da yi masa wasa da hankali zasu gamu ne sai ya bata punishment''haka ya juya ya fito ba haka yaso ba cikin ransa
Cikin sa'a ya hangota tana fitowa daga bangaren meron,da azama cikin qwarewa irin tasu ta SS ya labe,sam bata lura da shi ba tana gyara yafen mayafin doguwar rigar jikinta taji an kamota baki daya anrungume tsam,ta tsorata sosai ta bude bakinta da niyyar yin magana
''kina yin magana sai na cinye lips dinki''ta saki ajiyar zuciya jin muryar abdallah ne,sai ya tuna mata lokutan baya da yake tsora tata irin hakan
Luf tayi a jikinsa ta saki ajiyan zuciya ta lumshe idonta,wani yanayi take ji na daban,dumi qamshin jikinsa gami da qamshin mint mouth fresh dinsa tare da maganar da yake mata cikin kunne suka kashe mata jiki,kwanciyarta a jikinsa ya bashi daman sa hannunshi yana shafa kafadarta zuwa yatsun hannunshi
''ina zaki je?''
muryarta low tace''charger zan daukowa mero''
''kishiyarki''ya fada cikin sigar tsokana,sai ta saki murmushi tana sake narkewa a jikinsa
''yanzun ki qyale wata mero muje mu kwanta,yau sashen mami a cike yake ya mana kadan''
ta dan zaro ido
''amma babu kowa a dakina ni ai,ni kadaice''
''i know,amma duk da haka ya mana kadan tunda tare nakeso mu kwana''
''amma mami fa.......''
''shshshshsh!''ya fada yana dora yatsanshi kan lebensa bayan ya juyo da ita da sauri suka koma suna fuskantar juna,idanunsu cikin na juna ya riqe qugunta
''bana son musu,just say yes...''sai ta sauke qwayar idonta,a hankali ta furta
''to''
''good mero na,bari naje na dauko miki kayan barcinki,nasan kina da buqatarsu''ya fada da sauri yana zaunar da ita kan kujerun dake waiting parlour din ya shige bangaren mamin
white night gown ce qal da ita mai santsi da taushi armless,rigar iyakacinta cinya,sai wandonta da ya tsaya qasan gwiwa,yana fitowa daga cikin corridor din da dakunan suke yaci karo da mami na saukowa daga step din benan
''au,baki tafi ba kenan''yayi saurin boye kayan baccin a bayansa yana fadin
''no.....nazo daukan wani abu na ne da aka manta shi ba a hada min ba cikin kayana(maryam)''baki ta tabe tana fadin
''alright,sai da safe''
da sauri ya amsa mata ya fice yana dariya hannunshi a baya gudun kada ta leqa taga maryam din bata nan tabiyo sahu
Tsaf sashen yake a gyare fes komai daidai,ya zube musu kayan baccin nasu gefan gado yana dubanta
''madam muje muyi wanka ko?''
kai ta girgiza
''nikam ban jima da yin wanka ba basai na sake wani ba''
''bazaiyiwu ba,ko an gaya miki bansan yadda kike tsarin wankan ki bane,koda kinyi da magariba idan kika zo yin bacci sai kin sake hakane?''
shuru tayi,ganin haka yasa ya fara cire kayan jikinsa,tayi qasa da kanta don batason ganinshi haka,yana kallonta cikin ransa yana fadin
''zaki sani yarinya'',da kansa ya shiga ya hada musu ruwa mai dumi da turarukan wanka kala kala cikn bathtube kana ya fito,yadda ya barta haka ya taddata bata yi wani shirin yin wanka ba,saiji tayi kawai anyi sama da ita kai tsaye ya shige bandakin da ita,bai direta ba sai da suka shiga ya ajjiyeta kana ya zagaya bayanta,zif dinta ya soma ja zai zuge sai ta hade jikinta guri guda tana fadin
''zanyi wankan,amma sai ka gama,ka barni idan ka gama na shigo nayi nawa''
ya sauke hannunta yana sake zuge zif din yana fadin
''ai daga yau babu wanda zqi qara wanka ba tare da dan uwanshi ba,daya daga cikin qa'idan rayuwar aure na kenan,sabida sunna ce ta ma'aiki,na san kin sani''
Tsori duk sai ya kamata,ta yaya zata iya tsayawa haka gabanshi?
''please abdul''
ta fada cikin rawar murya don tuni har ya kai zif din qarshe
''no maryam''ya maida mata amsa yana sabule rigar anan,ta sake sunqulewa guri guda tamkar qasa ta tsage ta shige ciki haka take ji,ya zura kansa ta kafadarta ya kai bakinsa saitin kunnensa
''ci gaba da yimin musu zai jawo na miki abinda bakyaso ne,wanan abun da kike tsoro,kinga shikenan na kashe boss din mun huta ni dake baki daya''
hawaye ya soma sauka kan kuncinta bai kuka ba don yana tsaye ne a bayanta,ga qoshi ga kwanan yunwa,cikin muryar kuka tace
''naji amma pls ka barni,da underwears dina''duk da mood din da ya shiga sai da ta bashi dariya
''a garinku kika taba gani anyi wanka da underwears?....''
''please...''tayi saurin katseshi,shiru ya danyi kamar bazaice komai ba kana daga bisani ya saki ajiyar zuciya
''alright,amma fa gaskiya kin tauyeni maryam''
kusan dai abdallah rabin wanka yayi,fatar ta kadai ta tsone masa ido,sai sheqi santsi da qyalli take,ai a ranar ya bawa idonshi abinci sosai,gyaran da tasha gun haj laila ya gama rikitashi,kusan awanni hiyu suka kwashe cikin bayin yana bawa idonshi haqqinsa,duk da bai tabata ko kadan ba don ya fuskanci a tsure take sosai
Da ido tabi kayan baccin,abdallah dan garari ne qarshe,bata da daman musa masa tunda itama ya mata alfarma,kuma da sharadin zai mata abinda take gudun indai ta kuma yi masa musu,don haka ta karba ta koma toilet ta saka su,ta kalli kanta a madubi ba shakka ba qaramin kyau suka yi mata ba,saidai kunya ta lullubeta,dukka hannayenta da singalalin qafartava waje yake,haka nan ana iya hango saman qirjinta sabida net ne mai kama da code lace a gun,ba yadda ta iya haka ta fito tana rabe rabe,sai Allah ya taimaketa ya tayar da sallah lokacin da ta fito din,tayi hamdala ta haye gado taja tattausan bargon dake kai ta lulllube jikinta tana satar kallonshi,cikin nutsuwa yake sallarshi da cika qa'idoji sharudda da dokokinta,kallo daya zaka masa ka tabbatar ya samu ilimin addinin islama bada wasa ba,hakan na daya dah cikin abinda yasa take sake ganin qimar mami take sake qaunatar shi kansa abdallan,don ada ta yiwa 'ya'yan masu kidi kudin goro,saboda yawancinsu idan iyayenka nada arziqi mulki ko sarauta nasu damuwa da zuwa islamiyya,gani suke sunfi qarfinta,amma kuma ai baka fi qarfin shiga wuta ba ko?
don kaje gaban Allah kace rashin sani ne ya saka aikata ba daidai ba sam ba hujja bace a gun Allah,tunda ga makarantu na addini nan ko ina
Ganin yana niyyar sallamewa ya sata maida idonta ta gimtse don kada ya kamata tana satar kallonshi,murmushi yayi don tuni jikinsa ya bashi kallonsa takeyi,baice komai ba har ya kammala da dukka addu'o'insa kana ya miqe ya isa gadon yana jan bargon gami da cewa
''malama mai,baccin qarya a tashi a bani,abinci naci''da sauri ta damqe bargon bayan ta bude idonta,sai da ya tuntsire da dariya ganin yadda ta haqiqance wai ita bacci take amma daga jin anja bargo har ta zabure ta miqe,ya sakar mata bargon ya koma gefan madubi ya zauna bayan ya harde hannayensa ya zuba mata ido yaga ta yadda zata tashi,ai kam kasa tashin tayi qarshe sai ta yayimi bargon ta yafashi ta cukuikuye kana ta soma yunqurin tashi
''nikam a haka nakeson ki tashi''ya fadi yana boue dariyanshi,marairaice tayi
''amma fa babu mayafi kuma yakayan yan gajeru ne''
girarsa ya daga
''yes,haka nakeson in ganki,ko kinfison naje na kalli wasu?''ya fada yana dage gira.
Sai ta hade rai ta cuno baki kishin ya motsa,miqewa tayi ta sauka daga kan gadon sai ta tsinci kanta da sauya taku,binta yayi da kallo kamar ya hadiyeta haka yake ji har ta fice a dakin ya kasa dauke idonsa daga hanyar,ba kyau na fuska kawai Allah ya mata baiwa da shi ba har diri na jiki duka ta samu,shikam Allah ya zaba ya bashi bashi da abinda zaice da ya wuce alhamdulillah
Cooler ce mai dauke da friede rice da coleslow,sai farfesun hanta daban,kusan tare suka ci abincin saidai shi ya dinga bata tana karba cike da kunya
''kunyarki tayi yawa maryam,amma.....na kusa tsige miki ita''haka ya fada yana wane kashe mata idanu
cikin jikinsa ya janyota bayan ya kashe wutar dakin yana sansanar qamshin jikinta,wani qamshi yake ji na tashi a jikinta da bai taba jin irinsa ba,sai da ya gama sansana iya son ranshi kana ya hautsinota suka dawo fuskantar juna
''hira nakeso muyi irin ta ma'aurata my dear na''ya fadi bayan ya hade tafukan hannunsu cikin juna,sai ta sunne kanta a qirjinsa tana murmushi,batasan haka zama da masoyi yake da,dadi ba,sai,yanzu ta sake tabbatarwa tabbas a baya batasan farincikin zuci ba sai yanzu
''maryam''ya kira sunanta tamkar mai rada,bai jira amsarta ba ya dora
''gobe ne zamu shiga wata rayuwa,rayuwa ce da bamu taba sanin ya take ba sai a labari,rayuwa ce da bamu taba dandana irinta ba sai a mafarki,zama zamuyi na dindin din,ina son don Allah maryam ki riqe amana ta,ina sonki da yawa ina qaunarki fiye da yadda kike hasashe ko zato,zuciyata bata taba dandanar soyayya wata diya mace ba baya ga mami na sai akanki,kinsan gausawa sunce zo mu zauna zo mu saba,ni yarima ke sarauniya,inason mu gina masarauta mai cike da ni'ima nutsuwa da kwanciyar hankali,ina so matata ta kasance tamkar qawata,qanwata,yayata mahaifiyata mahaifina da kuma 'yata ta yadda ta kowanne bangare daga cikin mutanen nan da na lissafa zata iya taka rawa a gurbinsu''ya zarce da gaya mata ra'ayinsa da qa'idarsa me yakeso da abinda bayaso,ya kammala yana maida numfashi yayin da maryam tayi shiru har yanzu kanta na kwance a qirjinsa
Babu shakka abdallah mutum me mai sauqin ra'ayi da hali qwarai da gaske,tasha jin ana fadan halayen masu sunan,sai yau ta sake tabbatarwa hakan suke,yau din da Allah ya hadata zaman aure da mai irin sunan,wata qila sun samu tabarrakin sunan da ya zamto babu sunan da Allah yafi so irin abdullahi sai abdur rahman,dama ya bata ta fadi nata dukkan ra'ayin yaci mata alwashin kiyayewa shima,saboda zaman tare kowa,nada haqqin akan dan uwansa,bawai shi kadai ke da haqi ko keson kyautatawa ba,Allah ya fada cikin qur'aninsa mai girma cikin suratul baqara''walahunna mislul lazi alaihinna bilma'aruf,suna da(su mata)kwatakwamcin abinda ke kansu na kyautatawa(akan mazansu,ma'ana yadda zata kyautata maka kaima akwai kawatankwacin hakan a kanka)
itakam kasa fada tayi sai da ya matsanta mata kan haqqinta itama ta fadi din
''qaunarka kawai abdul idan ka bani ya isheni rayuwa,ka soni har mutuwarmu,ka riqe amana ta,kada ko tozarta qaunar da nake maka''
''har *ABADA* har *ABADAN* maryam banjin akwai abinda zai sa na tozarta tukuicin qaunar da kika yimin,idan dai wanan ne matsalarki ki goge shi daga babin matsala daga ciki kundin rayuwarki''ya fada yana shafa gashin kanta da ya sauka har kafadarta
wani irin bacci sukayi mai cike da qauna da tsantsar bege cike da shauqin juna
🍃🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Da safe sai guduwa tayi don ta fuskanci abdallah na son sake tsareta wai tayi wanka ta shirya anan,ita kuwa batason abinda zaisa mami ta gane bata kwana a dakinta ba,duk da tasan babu ruwan mamin ba nunawa zatayi ba ama abun da kunya tusa gaban suruki
shigarta waitin parlour din taci kark da kibrin yana fitowa daga sashen nasu,ta sake kallon agogo qarfe shida saura na safe,da,sauri ya qaraso gareta
''yauwa dama ke nake nema na rasa yadda zanyi na ganki''da mamaki kan fuskarta ta kalleshi
''lafiya?''
sai ya hau sosa kai
''ah...mero...mero ke nemanki,tana daki''
mamaki ya cikata saidai bata ce komai ba ta nufi bangaren nasu
gabanta ne ya dunga faduwa ganin meron nafa rusa uban kuka,duk da ita kanta ta tsorata amma sai ta danne ta qarasa inda take,sai kuwa ta sake qara sautin kukan nata,take ta gane abinda ya faru da ita,bata iya cewa komai ba ta taimaka mata tare da koya mata wasu dabarun data fusknaci meron bata sani ba,ta tausaya mata tsoro ya sake cikata,jikinta duk yayi sanyi saidai bata nunawa meron ba din kada ta karya mata gwiwa,haushin labaran ya kamata,me yasa sam su,basu da haquri,atleast ai ya bari yan uwanta su koma
Kukan mero yaqi qarewa,zama tayi ta dinga mata bayani sannu a hankali ta fahimceta,ta samu ta daina kukan bayan digon bayani data mata,duk da ita ma ba sanin wani abun tayi ba ga kunya na yadda zata mata bayanin,bata kai ga tafiya ba kiran abdallah ya shigo wayar ta,da sallama tare da sanyin jiki
''shine kika gudu ko?,idan kin gama da maryar labaran din kicewa mami na fita amma bazan jima ba zan dawo,shima gashi nan muna tare ki gayawa amaryar tasa''kunya ta cikata
kada dai ace ya sani abdallan,kamar kuwa ya san me take tunanin yace
''ba wani,abu yace da ni ba,nina fuskanta da kaina,naga kuma yana buqatar training,so kada kunya ta ta qaran miki akan ta da''ya qaraahe maganar yana dariya ciki ciki
A sanyaye ta sauke wayar a kunnanta,ji take ma kamar ita yakewa dariyar,ta dubi mero dake kwance hajaran majaran ta miqe
''maigidan naki sun fita da abdallah,zan je mu gaisa da su mami,amma dole ki dinga qarfafa jikinki kada ki nunawa su inna wani abu kin fahimta''kai ta gyada mata ta yi mata godiya ta fice
Tuni har sun tashi,kasancewar mutumin qauye ya saba da tashin wuri,baya malalacin baccin nan na bayan sallar asuba,Allah ya taimaketa mami bata fito ba,don haka anutse suka dinga gaisawa daga bisani ta shige dakin da inna wuro take.
*mrs muhammad [truncated by WhatsApp]
[3:19pm, 10/12/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣3⃣
*Daga jabir dan Abdullahi R A yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa ''((idan mutum zai shiga gidansa sai ya ambaci sunan Allah yayin shigar tasa da yayin ci abincinsa,sai shaidan yace:baku da abinci baku da gurin kwana(a cikin gidan),idan kuma ya shiga ba tare da ya ambaci sunan Allah ba yayin shigar tasa sai shaidan yace:kun samu gurin kwana,idan bai ambaci sunan Allah ba yayi da zaici abinci sai yace(shi shaidan din):kun samu gurin kwana da abinci))*
Tana dakin suna ta hirarsu da inna wuro mami ya shigo dauke,da kwando wanda ta zuba kayan breakfast a ciki na inna wuron,da sauri maryam ta tashi ta amsheta kamta aduqe tana gaidata,ta amsa mata asakekamar kuma ba aurukarta ba yadda dai sjka saba,zama tayi itama aka soma hirar da ita duk da maryam taja bakinta ta tsuke,saboda kunyar mamin,sai ta tsugunna tana hadawa inna wuro tea.
''ni inna wuro dama zamanki kikahi wlh damu,da kiwa,naji dadi sosai''inji mami,kama bakinta inna wuron tayi
''rufani ki saya ni bintu,ina ni ina zaman maraya,wannan ao saiku,dubi fa don Allah wai wannan ruwan ahine karin safenku,ina kuwa zakuyi qwari''ta fada tana nuna tea din dake hannun maryam tana figita mata,dariya ta basu,baki daya,kai imna wuro nanu dama,duk yadda mami taso ta yadda tayi zamanta aje a taho mata da tsoho alhajinta sam ta qiya.
''amma dai inna ai kya zauna har a raka mairamun taki nata gidan anjima ko,ku gano nata dakin''maryam dake gefe gabanta ya fadi,sai walwalarta ta ragu,tsoro ne fal ranta
''nan fa daya,nifa yau sai qauyen ni'ima bintu''da qyar tasha kanta amma fa saidai a rakata taje ta gano don babu faahi yau zata koma,ta bar tsohonta shi kadai a gida(hmm,mata irin na da kenan masu iya tattala miji da bin umarni)
''kema sai ki zauna ki karya don hajja laila ta iso yau takeso itama ta koma audan din,tana can gun takwararki ana mata gyaran jiki da qunshi,sai kije can ki samesu don nan ba zaku sake na saboda mutane''kamar an dira mata dutse haka taji ta amsa da ''to''
''sannunki bintu,ke dai kin zama uwar kowa kenan,kin kama kowa kin riqe kamar yadda hausawa suke cewa da na kowa ne,arziqinki na kowa ne,Allah ya albarkaci rayuwarki data yaranki,da za'a samu ire irenki cikin al'umma su wadata da an bar kukan yunwa qunci da talauci,Allah ya jiqan mai gidanki''inji inna wuro
''ameen ameen inna,ai shi arziqi da Allah ya baiwa dan adam tamkar ka dauki wani abu ne mallakinka ka baiwa,wani kace ya amfana ya kuma amfanar da wasu,muma aro Allah ya bamu da rabon mu aciki da rabon wasu,ma'ana ka ci ka ciyar da wasu,ruwanka ka ci kai kadai ka tashi ran qiyama cikin wahala,don Allah na narka dukiyar ne ya dinga maka azaba da ita,abinda ka bayar shine rabonka don shi zaka taras a cikin littafinka ranar gobe qiyama,wanda kaci kuma banza ne don na wani ka yiwa ba bare a rubuta maka ladar ka ciyar da dukiyarka ga wani,kai kanka baka da tanbas din dawwama cikin dukiuar,wataran Allah na iya karbe kayansa ya baiwa wanda yaa dama,ko ka muti kabar zuriya to baka aikata alkhairi na wa kake zaton zai kula maka da su?''
''wannan haka yake binta,Allah kasa mu dace''inji inna wuro,maryam na gefe tana jinsu ita kanta addu'a takewa mamin cikin zuciyarta,ko bata taba mata komai ba ta haifa mata *GWARZON MIJI DAYA TAMKAR DA DUBU ABDULLAHI BAWAN ALLAH*,bare babu irin halaccin da bata mata ba,mami mutum ce wadda samun kamarta zaiyi wuya
ruwan shayin kawai ta sha taji cikinta gaba daya ya cushe don haka ta fice tabarsu adakin,dakinta ta koma tayi wanka ta saka baqar doguwar riga don kada kayan ta su baci garin lalle,can ta tars da haj laila tana hada lallen qunshi,tuni mero an shige cikin dilka da kurkum ga bayaga halawa da aka sha.
Ita kanta kasa gajiya tayi da sabawa fatarta sabulu saboda wani irin santsi da taji tana yi na ban mamaki,itakam dama ko ba'a gama gyaran jkkin nan ba a yau zata cewa haj laila abarta haka,tana kallon yadda mero keta fama ina ga ita,fitowarta kenan haj lailan ta miqa mata wani anu cikin cup sai qamshin citta da kanunfari yake tace
''shanye diyata''haushi ma kamata yayi bata ce komai ba tayi kurba uku ta faki idonta ta fita da shi da niyyar zubarwa
cikin garden na gidan ta shiga ta daga zqta fara zubarwa taji an riqe hannunta,a hankali ta dago kanta sai suka hada ido,sanye yake cikin suit baqi da ja saidai yar saman ya cireta tana singalalin hannunshi,da alamu har ya dawo daga fitar da yace mata zaiyi
sai da ya mashe mata ido daya sannan yace
''shigowata kenan naga wani haske ya cika gidan nan,ina waiwayawa naga ashe kece,shine na biyoki ina fata banyi laifi ba''ya fadi maganar yana qoqarin amshe cup din daga hannunta,tana qoqarin boyewa ta bashi amsa
''um um,ko daya bakayi laifi ba''
ganin yana qoqarin maida abin babba yana son ya rungumeta yasa ta sakar masa cup din a sauqaqe,sai ya leqa ciki yana fadin
''hala wanann abun dadi ne mami ta baki ko,Allah yayi da rabo na kenan nasha?''ya tambayeta yana kallonta,wani irin kyau yaga tana fitarwa,tambayar kawai yayi amma bai gane me yake fada
da sauri ta girgiza masa kai
''a'ah,kada kasha''
''why?,muba muta ne bane''yayi tambayar yana dan zaro ido gami da dage gira.
Sai kawai taga ya dangwalo ya tsotsa
''hmmmm,gaskiya da dadi''ya fada yana kaiwa bakinsa,kafin ta qwace har ya kurba,ta karbe kana ta zubar
''na gaya maka mazq baku sha,idan poising ne kuma fa?''
sai taga ya saki murmushi mai fidda sauti kana ya harde hannunsa a qirji
''sai abun ya zama abun alfahari a gareni,masoyiya ta bawa masoyinta guba sabida tsabar qauna,kuma zaqinta zanji dear na,ballantana ma na sani ke din ba zaki iya ba,saboda wasu ma da suka yi yunqurin bani naci kin kawar da hakan,ko kin manta har asibiti kika je aka tabbatar miki da irin nau'inta da kuma qarfinta?''
ido ta zaro,wai abdallah aljanine ko kuwa yana da su ne?
murmushi ya kuma yi,ta bude bakinta da niyyar yin magana,sai yayi azamar qarasowa gabanta,yasanya tafin hannunshi ya rufe labbanta yana kallon qwayar idonta tare da cewa
''yi shiru da bakinki,ki adana duk wasu tqmbayoyi da kike da,su,wannan hiran na daya dagq cikin hirarrakin da na tsara mana,cikin gidan mu na qauna,a kan gadon soyayya,a kuma qirjin masoyi''ya qaraahe maganar yana kashe mata ido.
kunya ta kamata sai ta zame bakinta tana murmushi ya sake matsowa kusa da ita yana yin qasa da murya saitin kunnenta
''ina fata kin tanadarmin salo salo na soyayya da,qauna wadda zaki shayar da ni,kinsan abdallah dan soyayya ne,yana son soyayya musamman ga matarsa''ya fada yana qoqarin janta jikinsa,gabanta ya shiga faduwa,ta faki idonsa ta zille tayi hanyar fita,baiyi yinqurin binta ba don ya tabbatqr da mutane a wajen amma sai ya matso uadda zata iya jinsa ya biyo bayanta
''ki gama zulle zullenki yarinya,awa,nawa,ne ya rage?''hakan da ya fada sai ua sata tsayawa ta juyo ta dubeshi idonta har ya cika da qwalla,dariya ya sa mata tayi hanzarin ficewa daga gun.
Zuwa la'asar gaba daya hajja laila ta gama da kyawunta,tamkar buga qunshin akayi aka dayeshi,banu kuskure ko daya aciki,ja ne amma har saman hannu da saman qafa,abinka da fara ya fito kuwa yayi marun,kyau kam basai an fadeshi ba ya gama yi,tuni yan kawo mero sun tafi don yaci ace ma zuwa la'asar din sun kai gida,saukowarta kenan daga saman mami dauke da wata leda wadda wani arnen codenet ne a ciki da aka fidda wa dinki na garari,kudadr mamin ta saka masu yawa ta siyawa maryam din sabida wannan rana,sallama akayi aka shigo falon qasan,raliya ce janye da hannun fadil(yaronta)sai hindatu da lubabatu da kulu,baaba huwaila da hajiya atika.
Cikin dakinta suka shiga ita da raaliya hindatu lubabatu da kulu,baaba hadiza da hajiya atika kuwa suna sama gun mami,mami ce tasa duka suka zo don yi mata rakiya,hira suka dinga yi wanda zuwansun ya rage mata fargaba sosai,lubabatu da kulu nata kallen kallen gidan mami don yau ne zuwansu na farko,sun tabbatar cewa Allah ya yiwa adda maryam din baiwa ba qarama ba.
Raaliya ce ta shiryata tsaf cikin codenet din orange da yellow,kana ta dora mata alkyabba da mamin ta hadota cikin kayan,yellow ce mai ratsin fari,fadar irin kyawun da tayi ma bata baki ne,su kansu tsayawa sukayi kallonta,kai tsaye gin mami suka fara zuwa kana suka fice suka barta ita da ita,kallonta mamin take cike da farinciki,burinta kam ya gama cika a yau,hannu ta miqawa maryam din ba musu ta bata,gefeanta ta zaunar da ita kana tace
''maryam,da farko abinda zan fara cewa dake shine kiyi haquri,don babu wani abu da ya wuce haquri da mace zata riqe wanda zai,zame mata jagora kuma madogarar gidan aure,haquri maryam shine komai a rayuwa,kiyi haquri a duk yanayin da zaki tsinci kanki a gidan aurenki,duk wata mace da kika gani zaune gidan aurenta wallahi ba za'a rasa wata matsala da take fuskanta ba komai qanqantarta,ta wata ne tafi ta wata,qila wadda kikewa hangen ta haye ta huta da zata buda miki cikinta wallahi saikin tayata kokawa,komai dadinki da mimi wataran sai kun samu sabani,donko tsakanin harahe da haqori ma ana sabawa,na biyu riqe sirri ki riqe sirrinki ke da maigidanki maryam,koni idan bai zama dole ba bana buqatar jin sirrinku ke da abadallah,ku riqe amanar juna,ku riqe sirrin juna,ku zauna da juna cikin amana''nasiha ta dinga mata irinta tsakanin da da uwa,kuka sosai ta dinga yi har sai da mamin tace
''a'ah,ai kuma zaki batawa abdallahn kwalliyar me akayi kenan kuma uhm.....maza share hawayenki,duk da haka kowacce mace ta saba yau hashi kowa na zaune agidanta''.
Da kanta ta kama hannun maryamun har harabar gidan ta sanyata cikin sabuwar range robber baqa wul wadda kyauta ce mamin ta yi mata,tukuici ne ta bata,kadan daga cikin irin abubuwan da take ji zata iya yiwa maryamu,yadda ta kama hannun mamin itama sai ta karya mata zuciya har sai da ta share qwalla,motocine kusan shida don akwai yayar mami da qanwarta,sai yayar marigayi alhj abdulkareem mai nasara da qanwarsa,tana nan tsaye mamin har motar ta daga suka fice daga gidan kana ta juya ta koma ciki,tun daga lokacin ta soma jin kewar maryamun,bangare daya ga abdallah dake shirin tafiya shima,babu shakka kewarsu zatayi ba kadan ba,don ma ga mero nan,amma kafin su saba su maye mata gurbin maryamunta ai ba nan kusa bane
Sai da suka fara zuwa gidansu suka kaita gun mama da malam mamuda mahaifinta kafin su wuce da ita gidanta.
Wani irin yadine ajikinsa orange colour mai bala'in kyau da taushi,dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,fuskar nan tashi tayi wani irin kyau na musamman,hisham ke riqe da wata iriyar jaka da aka qawata ta da rubutu mai kyau suna tafe yana masa tsiya har suja qarasa gun mami,tana falon nata tana sallah ya tura qofar suka shiga,kujera suka samu suka zauna suka jirayeta har ta idar,sai data shafa addu'a kana ta tashi ta dawo kan daya daga cikin kujerun itama ta zauna,hisham ne ya fara magana
''mami gashi na kawo miki shi,ayi masa nasihar zaman aure''mirmushi mamin tayi tace''ka kyauta kuwa,shi yasa nake sonka hisham badai hankali ba''
harararsa abdallah yayi''jimin dan rqimin wayo,kana nufin zan iya tafiya banzo ga mami na ba?''
dariya ya masa don ya fuskamci yanayin fuskarshi har ya canza ya kuma san ba wani abu ne ya tabashi ba sai barin mamin da zaiyi.
''abdullahi''ta kira sunanshi da salon da bata taba ba,take ya dago idonsa ya kalleta,sai ya kasa civgaba da kallon nata ya duqar da kanshi,son ya hango magana zata masa bata wasa ba
''shi aure da kake gani girma ne da shi,daraja da shi qima gareshi,sunna ce guda ta wanda akayi duniua da lahita dominsa wato annabi muhammad S A W duk wanda ya wulaqantashi baya tare da annabi na tabbatar kuma bazaka so haka ba,a duk sanda ka dauki yarinya,aka rqbata da uwa da ubanta da inda ta taso tavgirma,aka rabata da danginta aka rabata da duk wani wanda ta saba da shi aka baka to ka tabbatar da xewa amana ce aka baka mai girma,kasan sarai hikuncin wanda ya tozaratar da amana ko yaci amana ko?,ka tuna ko yauahe cewa matarka ba siyanta kayi ba,ba baiwarka bace 'yace 'yantacci ya mai yanci,kada ka dinga mu'amala da ita irin mu'amalar bawa da ubangidansa,a'ah,ka mu'amalance ta wani lokaci kamar 'yarka,ka tsawatar mata ka bata shawaea ka tausasa mata kaja girmanka,ka mu'amalanceta wani lokaci kmar mahaifiyarka,ka tausasa mata,ka kyautata mata,ka girmamata,ka mu'amalanceta wani lokaci kamar qanwarak,ka qaunaceta ka kauda duk wani abu da zai cutar da ita ko ya,bata nasabarta,ka dorata kan hanya madaidaiciya,ka mu'amalanceta kamar qawarka,ka gaya mata damuwarka,kayi shawara da ita,kuyi wasa kuyi dariya,matarka duka tana da wannan mtsayin a gareka''.
Ta dora da cewa''na tabbata har yau kana iya tuna mu'amalata tsakanina da mahaifinka wanan kawai ya isheka madubi,ya iaheka littafin da zaka dinga karantawa ko yaushe koda ban ce maka komai ba game da zamantakewa da iyali,abdallah ka guji zalunci,Allah da kansa ya fada cewa ya haramta zalunci abinsa kansa,kuma ya haramtashi a tsakaninmu,ka kyautatawa matarka,ka sauke duk wani nauyi da Allah ya dora maka,yadda kake da haqqi a kanta haka itama take da haqqi a kanka,ban yarda ka take mata haqqinta ba abdallah,iya wannan nasan ya,isheka nasanka nasan tarbiyyar da na maka,don Allah abdallah kada ka watsamin qasa a ido,kayi zama zama na haqiqa da matarka,Allah zai tsadaku ranar gibe kan yadda kuka sauke haqqin jilunanku,wallahi wannan gaskiya ne babu ko tantama aciki''
idanunshi tuni sun hama hada ja,zuciyatsji zafi take masa,karo na farko da zai rana gidan kwana shi da maminsa,a hankaki ya miqe daga mazauninsa ya isa gabanta ya durqusa kangwiwoyinshi,kana ya cire hular kansa
''mami kisa kin albarka,kici gaba da yi mana addu'a,insha Allahu zanci gaba da zama abun alfahari a gurinki''
hannunta ta dira saman kanshi kana tace
'' *BARAKALLHU LAKA,WA BARIK ALAIKA,WAJAMA'A BAINAKUMA FILKHAIR*'',ta amshi ukar da kanta ta maida masa ita saman kansa,sai ya kasa jurewa ya dora kansa saman cinyar mamin yana ajiyar zuciya,tausayinsu ya kama jisham,babu shakka ba qaramar qauna nace tsakanin wannan da da uwar ba,sai ya,kasa zama shima ya tashi a hankali ya fice,uwa ba wasa ba.
Mamin bata masa magana ba don ta saba da irin hakan,majority tun yana yaro idan zuciyarsa na quna haka yake ya dira kansa saman cinyarta har sai ya huce,don bashi da qawa a lokacin ko aboki da ya wuce maminsa(yana da kyau iyaye ku zama kune abokai ko qawa na farko wanda suka matuqar shaquwa da 'ya'yansu kafin kowa,ta hakane zaki samu damar yiwa diyanki kalar tarbiyyar da kikeso mai kyau ba tqre da wasu sin samu damar ruguje miki ba,bawa yara damar shaquwa da aboki fiyr da iyaye da rashin jansu a jiki babbar illace,da abokin nan ko qawarnan zwta dinga shawara,ita zata dinga gayawa damuwarsa bake ba,kinga kenan zai iya dorashi kan irin tasa tarbiyyar,amma idan akwai shaquwa tsakaninku kece mutum ta farko da zai fara dinga gayawa matsalolinsa da damuwarsa kafin kowa,saidai idan kuma yayi aure Allah ya bashi mace ta gari sai ki koya masa neman shawara daga matarsa,saidai idan duka su biyun tunaninsu baikai nan ba ko mas'alar tafi qarfinsu,a kuka don Allah iyaye,tarbiyya abace mai tsada da wuya,amma a qarshenta kuma ke uwa ke zaki fi kowa mora da jin dadinta koda baki duniya kuwa).
Ita ta riqo hannunshi suka sauko qasa,ya zama kamar ba abdallah ba,qwarin rai da qarfin zuciyar nan duka babu,har dariya ta dinga masa kan cewa ya girma fa,ya kamata ya koma abdallahn sa,nan da ten months yana iya zama daddy,abinda ya sashi dariya ya kuma bashi kunya kenan,bakin freezeer suka isa ta bude ta ciro wata qatuwar leda ta sake jansa har suka fito harabar gidan inda motocin security dinsa guda uku data abokansa guda uku ke jiransa,cikin motar da za'a kaishi ta bude masa da kanta ta sanyashi kana ta miqa masa ledar''Allah ya tsare hanya,a sauka lafiya''ta fada kana ta rufe musu qofar ta koma ciki,a varanda ta tsaya har sai da taga ficewar motocin duka.
Mus'ab abokinsu ke tuqa motar,usman na gefansa baya kuma hisham ne da abdallahn,cikin salonvtsokana hisham din yace
''idan bakason rabiwa da mamin kawai mu maidaka gida sai a yiwa maryam waya ta haqura kawai''harar ya galla masa bayn ya sauke ajiyar zuciya
''mami da maryam duka rayuwata ne hisham,ka sani,ba sai na maka dogon bayani ba''tsokanarsa suka ci gaba da yi tare da yi masa shaqiyanci kala kala irin na abokan ango har suka iso unguwar.
0 comments:
Post a Comment