Alhj hassan,Alhj Hussain,Alhj isma'il 'yaya ne ga Alhj usman mai nera, matar sa daya tak Hajiya Zeenatu ita ce uwar 'ya'yansa. Sun kasance suna zama ne a cikin garin zamfara. Wannan family Kansu a hade yake, hakan ne ma yasa suke zama a gida daya sai dai kowa da nashi part Saboda gidan babban gida ne sosai , iya haduwa gidan yahadu, kasancewar Alhj usman mai nera hamshakin mai kudi ne sosai gashi ya kasance shi mutum ne mai son jama'a da taimakon talakawa. Haka ma duk 'ya'yansa ba bare a ciki, domin ko wannesu Allah ya hore masa dukiya,dukiya kuwa abinda ake kira dukiya domin duk wanda yaga family din yasan dala ta zauna ba sai an gaya masa ba. Alhj Hassan shi ne babba matarsa Hjy Fatima 'ya'yansa biyu maza faruk da Hafiz. Alhj husain shi ma matar sa daya Hjy zainab, sai dai har yanzu Allah bai basu Haifuwa ba. Alhj isma'l matansa biyu Hjy saratu da Hjy khadija 'ya'yansa hudu duk maza,Hashim,yusuf,'ya'ya ga HjySaratu. Salim,Ali 'ya'yan Hjy Khadija. Zaman da suke zama ne mai hade da hadin kai da kwanciyar hankali ba'a cika jin kansu ba.
.
faruk shi ne mai dan girma a cikin 'yayan,akalla yanzu yana shekara 9, yana primary 5 ne a yanxu. Amma idan yana fitar da lafuzzan turanci,kamar a secondry yake,gashi kyakkyawa fari tas dashi ga natsuwa da hankali,shiga rai shi yasa a familyn duk anfi ji da shi. Faruk ne zaune yana jiran fitowar momy (zainab )ummanshi ce ta aiko shi da dan wake yakawo mata. Yauwa dana, kace mata na gode,ya mika mata kulan ya fita,tayi zaune domin taci, sai dai yajin yau ba yawa, kiranta a waya tayi maman faruk ya akayi yau yajin ba yawa.....naga alamar so kike ki cutar muna da baby shiya sa na fara rage yajin,ko dan kinga mijin baya nan ne...ai bai ko san da cikin nan ba....ke haba meyasa,kinsan indiya yaje,idan nagaya masa bazai ma bari yayi abinda yaje yi ba sabida tsananin murna,kinsan mun shekara goma da aure ba haifuwa,haka ne fah Allah ya bada masu albarka,amin,amin nagode.
.
Yau ne Alhj Hussain (Daddy)zai dawo daga indiya,Momy sai shirshiryen tarbonsa ta ke,ta kammala abinci ta shirya tsaf tayi kyau sosai tana sanye da wani blue din material mai ratsin fulawa pink jiran isowar sa kawai take,da yake yace mata karfe 1:00pm zasu sauko gashi yanxu daya saura, tadan kishingida Kafin ya iso. A cikin barcinta da bai riga yayi nisa ba taji sallamar sa,da saurin ta tashi ta rungume shi,tamai sannu da zuwa,sai kallon ta yake yanda ta kara mishi kyau....yadai kallon fa, kinga yadda kika kara kyau,haske,cika, ko ni dana je indiya albarka...um um fah,Allah kuwa,kunnensa ya tara a bakin ta, gaya min meye sirrin,ni dai ba wani sirrin muje kaci abinci akwai lbr mai dadin ji,da gaske ?eh. Ya gama cin abinci yayi wanka suna kwance suna firar ya bayan rabuwa...yauwa baki fada min lbrn ba,to rufe idonka na gayama, tooo....,wannan wane irin lbr ne haka da sai na rufe idona, kai dai nace ma ka rufe,to na rufe, Allah ya karbi addu'ar mu da muka dade munayi domin yanxu ina dauke da juna biyu .....da gaske!! Allah kuwa,tana magana ne a cikin jin kunya,rugumar ta yayi yana mata kiss ta ko ina,yayi sujjada yana mai cewa "Allah na gode ma da kasa zan ga kwai na a dunya,Allah ka bamu masu yawa masu albarka, kuma kasa muna da yawancin rai.
.
Amin mjina.....bari naje na gayama family wannàn abin farinciki....ai kowa ya sani,ya akayi su ka sani, domin na san ki da kunya baza ki iya fada ba ,zazzabi ne mai tsanani nayi kamar bazan yi rai ba,sai da muka je asibiti,bayan an dubani suka ce ina dauke da juna biyu,baka ga yanda family ke murna ba hardai Hajiya da Alhaji....to ni meyasa ba'a gayamin ba sai yanxu? Saboda ina so ne na baka surprise,zaka fi farin ciki, kuma nasan idan na gayama baza ka bari ka, karasa abinda kaje yi....Allah kuwa da ranar zan dawo ba shiri. Haka rawu taci gaba domin yanzu momy haifuwa yau ko gobe. Faruk ne da sallamar sa tare dan rissinawa ya gai da momy,ta amsa sallamar tare da amsa gausuwar.
.
Halan dai anzo ayi magana ne da kanwar?eh mommy. Da yake tun lokacin da cikin mommy ya fara girma kusan kullum sai ya zo ,wai magana su ke yi da kanwarshi ta cikin cikin,ni Billy giro abin har mamaki ya ke bani. ya naga kamar ranka a bace faruk,wasu ne suka bata min rai a school wai baza ki haifa min kanwa ba sai dai Kane,ni kuma ai nasan Allah shi ne maiyi ......kuma a kullum nayi sallah sai na roki Allah ya bani kanwa...to kasan da haka kake bata ranka a banza faruk, ni ma kawai na tsinci kai na ne da ance kane zaki haifa min sai inji raina ya baci tunda kannaina duka maza ne ina so na sami kanwa.......haka ma wasu na can na neman da namji,basu samu ba....to Allah dai ya ba ka kanwa amin mommy. Hanun sa ya dora a cikin momy,yana mai cewa. "Kanwa ta wai sai yaushe xaki fito a daina mun gori,mu rika yawo tare'yan ajinmu su dai na minkurin kanwa,nima na rama...hmm kai dai kullum baka gajiya kana magana da abinda bai ko xo duniya ba.... lah kinga umma tana motsi ...duk abin nan da akeyi a idon daddy ne sai dai ba wanda ya ganshi,murmushi kawai ya keyi,ya jingina a bakin kofar. Umma ce ta fara hango shi tsaye yana kallon su cike da sha'awa....a'a Alhj kai ne a tsaye sai faman kallon mu kake nida dana....danki mai kanwa ..ai inaganin idan baki haifi 'ya mace ba,bansan ya faruk zai yi ba. Allah dai ya taimaka ki haifo macen,amin ya Allah.
.
Amma akwai ki da abin dariya mimi,kinga yadda kika Fuske...ya baxan fuske ba kina min zance marar dadin ji, wanda ko a mafarki bana so haka ta faru.....da wasa nake miki fah,ya zanyi wanann tunanin nace yayan ki bazai aure ki ba, wannan soyayya haka...ni dai zancen ya isa haka,ko abin motsa baki ban kawo miki ba,duk kin bi kin birkita min lissafi,afwan cewar Zainab. Momy ce zaune a falo Mimi kwance a saman kafafunta tana game a waya,nikuwa Mimi yaushe zaku fara waec da neco?a wannan watan mommy...amma baki da abinyi sai danne,dannen waya,ai Mommy duk dare kafin nayi barci sai nayi karatu,haba mommy na, ai kinsan bana wasa da karatu,haka kam amma ki kara dagewa kinji,inshaAllah mommy. Abba!wai wa zai kaini school yau,kasan fa jarabawa ce damu bana so nayi latti,yayanki zai kaiki,wanne daga cikinsu?Hafiz kuma a kullum shi xai rika kaiki..Abba why?shi ya zabi haka,hmm lai ma yaya Hafiz yayi hakanne don yana tunanin zan soshi,to meye abin yi tadan yi shiru kadan kafin ta samo amsa...yes hakan zanyi yayi dai dai. ...Tana magana ne a cikin zuciya. Kome zata yi oho,muje zuwa....
.
Tafe suke ba mai magana a cikinsu. Hafiz ya katse shirun,yadai Mimi shirun fah,ina dan revising ne shi ne kaji shirun yayi yawa...ok yayi Allah ya taimaka,ameen yaya shima murmushi yayi yaci gaba da driving dinsu. Haka suke kullum basu cika wani surutu ba soboda revising dinda take yi,kuma tayi hakanne domin kar ya takura ta,amma shi abun yana dan damunsa sai dai yabar abun ne a zuciyar batare da ta fahimci hakan ba. Kamar kullum yau ma zai kai ta school yake tambayar ta. Mimi meyasa kullum bita kike kamar wacce bata karantu ba ,bayan nasan ba haka kike ba, da kinyi karatu zaki fahimta, basai kin sake ba,amma yanxu kullum sai kinyi bita...uhm ..eh.. am ina so ne in kara fahimta. Yanayin maganar ta ya gane cewa da gangan take bita kullum,kaddai ace yarinyar nan bata sona shiyasa take min haka..a'a dama haka take bata cika son damuwa ba idan za'a je school, dayan bangaren zuciyarsa ne ke bashi amsa. Zee!!..ya akayi,mimi mutumen ki ya fara gano ni...kamar ya ya Mimi? kinsan nace miki kullum revising nake a mota har mu iso,to ya fahimci yi ne kawai nake don kar ya ta kurani,gaya miki yayi?
.
A'a yanayin fuskar sa ne ya bani amsa...nikuwa Mimi me zai hana ki fito fili ki fada mashi cewa faruk ke sonki,na tabbata idan yaji zai hakura. Kinsan bai riga da yace yana sona ba....amma ai duk wanda yaga yanda yake baki kulawa yasan akwai so mai tsanani,gsky ni kaina tausayi yake bani ranar da zai furta min ince a'a,ina jin nauyi sosai a matsayin sa na yayana. Kinga kawata ga shawara,yaushe ne yaya faruk zai dawo?kesan daga shekara sai shekara yake kawo muna ziyara saboda yanayin aikinsa,inaga yayi wata 7 da kawo muna last ziyara,kenan saura wata biyar kafin yazo....tab amma da saura dai kika ce,kuma kinsan kafin wannan lokaci zai iya furta miki, abinda nayi tunani ki matsa ma yayanki akan yadawo kina son ganinsa,na tabbata a yanda yake sonki zai dawo..zee kinsan ban cika son matsa mishi ba...kinkuwa san dalilin haka,sai kin fada. Ba makawa yanayin yadda kuke gudanar da soyayyar ku da yaya faruk, idan Hafiz ya gani zai fahimci Ku masoya ne, na gaske,kwarai kuwa zee shawarar tayi,kinga abu yazo cikin sauki.
.
Allah ya biyaki zainab,shiyasa nake sonki...Ameen Mimi. Kwance take a daki ta na tunanin yadda zata bullowa yayanta faruk ba tare da ta, takura mishi ba....karar wayar ta ya katse mata tunani koda ta duba faruk ne wani sassayyan ajiyar zuciya tayi tare da murmushi kamar yana ganin ta. Hello yayana,hy my mimi,ya exam, Alhamdulillah,ki na dai karatu sosai ko? eh yaya sosai. Sai da suka dan taba fira take cewa "yaya ni gsky nayi missing dinka da yawa idan kai bakayi missing dina ba...haba! Mimi Allah nima nayi missing dinki, ai nakusa na dawo...to amma yaya har wata 5 fa,haka ne Mimi yau da gobe cikin ikon Allah sai kiga har lokaci yayi. Amma kiyi hkr kinji Minima to yayi yaya Allah ya kaimu lokacin ameen my Mimi shiyasa nake sonki kina saurin fahimta. Haka suka cigaba da firar su ta masoya kamar ba zasu aje waya ba. Mimice da Zainab a karkashin wata bishiya suna jiran azo a dauke su daga makaranta.
.
Hafiz ne tafe a cikin mota ya iso inda suke yayi fakin,mimice ta tashi tana cewa "yaya sannu da zuwa,yauwa...barka da wuni yauwa sannu zainab. Yaya faroooook!!!! da gudu ta tafi ta fada jikinsa shima haka rungumeta yayi,yana cewa my Mimi!!! Sai faman sauke numfashi take tare da janye jikinta. Yaya da wani yace min ga ka can da sai nayi gardama kafin na juyo,sai Allah yasa nice na fara hango ka, Mimi kenan wannan gudu haka baki ji ciwo ba dai ko?a'a yayana...ai ko naji ciwo bazai dame ni ba tunda gaka a gabana.....su Hafiz ne da Zainab suka karaso,Hafiz ya mika ma faruk hannu suka gaisa. Ita ko Zainab sai cewa takeyi ai ke har kin bamu tsoro wlh.....yaya faruk sannu da zuwa yauwa Zainab ya exam mun gode Allah,to Allah ya bada sa'a, ameen. Hafiz ashe har yanxu mimi bata san ta girma ba...Allah na sani yaya .. to meyasa kikayi gudu haka idan kika jiwa kanki ciwo fa ...ai kaine yaya kamin bazata,tana magana ne a cikin shagwaba, shi ko faruk sai kallonta yake yanayin yanda take shagwabar ta,yana birge shi.
.
Yaya Hafiz dama kasan yaya ya dawo?a'a nima yanzu na ganshi...Mimi kenan kamar yadda kika ganni bazata shima haka ya ganni. Amma yaya shine kaki karasowa kayi fakin nesa damu, to ai kin hango ni duk da nesa nake daku....yaya...
.Mimi yakoyi yanayin yanda tayi magana ne, a shagwabe ,su dukansu sai da abin yabasu dariya, Mimi sai faman kallon sa take yayi kyau,ya kara haske dagani yana cikin koshin lapiya. Meye tambayar ki mimina?yaya meya sa kadawo tun lokacin dawo war ka bai yiba?kece Mimi.....ni kuma...daga kansa yayi alamar eh,to ai kace min nayi hakuri,haka ne. Mimi nakasa jurewa ne, ace kin nemi alfarma ban miki ba,Mimi a duk duniya bani da wani buri sama da inga na faranta miki,Mimi fata na a kullum ki kasansce cikin farin ciki da walwala babu wata damuwa a tattare da ke. na gode yaya na gode kwarai da kulawar ka a gare ni Allah kuma yasaka ma da Aljannat fiddausi,ameen Mimi Allah yasa mu dukan mu mukasance a cikinta. su dukansu suka amsa da Ameen.
.
Bayan sun dawo ne,Mimi tayi wanka tayi kyau sosai kamar ba indiya,sanye take da riga da siket English wear ta yafa wani karamin gyale Kalar kayan,tana saukowa ne zuwa falo,anan ta sami mommy zaune. Mommy nah,ashe yaya faruk ya fita,to zai zauna ne yayi ta jiranki har sai kinfito,yadai ce ki same shi a dakin sa,to mommy bari naje. Kwance yake yana sauke gajiyar tafiya daga shi sai singlet da shortniker,bacci yanason ya dan dauke shi. Sallamar Mimi yaji,Mimi ina zuwa, sai da yasaka jallabiyar sa,sannan ya bude daki, tsaye yayi yana kallonta ba tare da ya bata hanya ta wuce ba. Kwata,kwata ta canza masa domin wani irin kyau yaga ta kara, sai murmushi take dimple dinta na lutsawa...my Mimi tsokanan ya isa haka,wannan murmushin ai sai in manta hanyar gidanmu...aah yaya,to ai a cikin gidan naku kake,kaga baza ka manta ba. Yaya, aka ce kace insameka,dama abinci naso kikawo min amma har naci,sai dai barci da nake sonyi,ok yayi bari naje wurin kaka musha fira kenan,ayi barci lafiya,ok bye my Mimi. Ta tafi shiko yashiga dakinsa. Written by Bilkeesu giro [4:54PM, 10/3/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro 18kakaaaa!!!....gani a bayan ki yau baza ki tsorata ni ba,ai ba tsorata ki zanyiba,nayi ta sallama ne baki amsa ba shine nakira da karfi ko zaki ji. Kaka ina Alhaji yayi wai, bacci yake,watakilma kin tashe shi da wannan kuwar taki,kaka ai gara ma ya tashi ya ga amaryashi sabon jini,takarasa maganar ne tare da shiga daki. Alhajina ashe ka tashi da barcin...an wuni lafiya,lafiya Kalau mimi,ina abokin ki,barci yake,koda yake bai jima da shigowa ba.cewar Alhaji. Shi ne ni kika zo kika tayarnmin da miji amma shi kin barshi yana bacci?eh kaka, shi dan hutu ne....ai kuwa shima yanzu zanje in tashe shi tana magana ne tare da dauko maya finta. Koda Mimi taga dagaske take ta rirrike kaka tana cewa kaka don Allah yi hakuri Allah ya gaji dayawa,cikin marai rai cewa take magana. to zaki sake tada min maigida? a'a amma ai kinsan nima matar sa ce,...kamar yadda shima din faruk mijina ne ba,kaka kenan nikadai ce matarsa bana zama da kishiya......
.
Domin tuni na sa yayana ya miki saki ukku....ayya ai ni bana sakuwa....Sallamar Hafiz da Ali ce ta katse musu fira,kuma da alama Hafiz ya ji abinda suke cewa sbd yanayin fuskarsa yanuna. Kaka ce ta amsa sallamar,bayan sun gaisa ne Mimi ke tambayar Ali, "yaya Ali ina takwarata,ina fatan lafiya kalau take,lafiya lau, tace ma a gaida ke,ina amsawa,shi yaya Hafiz yaki gaya muna wacece antinmu...hmm Mimi kenan kena ke so amma a cikin rashin sani na fada sonki domin dana san faruk ke sonki da bazan fara ba,sai dai saukin abin ban furta miki ba....yaya yadai naga ka zurfafa, tunanin me kake,ba komai Mimi. Kaka ni zan tafi,to a gaida mutan gida,za suji inshaAllah. Daddy inaso inje shan ice cream na dade ban je ba,Mimi ni bana iya yawon nan yau ki je faruk ya kaiki...shan zakin ne yata shi ko...mommy pls ki banni inje,ai baxan hana kiba jeki tunda daddyn ki, yace kije...thank u my mom tayi mata kiss a kumatu ta fita a guje. Da isar ta,ta banki kofar dakin bako sallaam fito daga wanka kenan yaji an banki kofar dakinsa bako sallama,dagowar da zai yi yaga waye, sukayi ido hudu da Mimi.
.
Da sauri ta dauke idanunnta akansa domin bata saba ganin sa,a haka ba. Dagashi sai towel ga gashin kirjin sa duk ya kwanta luf ,luf dashi,gabanta sai dukan uku,uku yake domin tasan yau fada ne rabonta. Wai ke Mimi! yaushe ne zaki yi hankali ki daina gudu!da har zaki shigo min daki ba sallama! bayan kinsan ba abinda na tsana irin a shigo min daki ba sallama,sai kace dakin arna,get out of my room!stupid girl kawai. Gabaki daya ta rasa natsuwar ta,da kyar ta samu ta iya cewa "yaya am so sorry pleasedajin maganar ta yasan kuka take,nan take yaji bai kyauta ba. Mimi kuka kikeyi?yi hakuri raina ne ya baci da yawa,gaya min me ke tafe dake, tayi shiru ba amsa, yaxo dab da ita Mimi magana fa nake miki,am sorry fadamin mekike so, dama.... ta sakeyin shiru hawaye na zuba a idanunta domin ta tsani fada a rayuwar ta har gara ma a daketa da ayima ta fada.
0 comments:
Post a Comment