Jawota yayi, ya rungumeta yana dan bubbuga bayanta,alamar rarrashi,har saida ya tabbatar ta sauko sannan ya sake tambayar ta,nan take cemishi daddy yace inzo ka kaini wurin shan ice cream. Har yanzu shan ice cream na nan baki daina ba ko? ya dan lakuci hancinta yana murmushi ita ma haka, sannan yace "jeki shiryo ki zo mu tafi. Suna hanyar su ta dawowa ne take tambayar sa"yaya ni meyasa ba'a bari ina driving da kaina? kibari idan kika gama secondry school sai ki fara driving da kanki kinji,to yayana ai nakusa, domin cikin wannan watan zamu kammala. To Allah ya kaimu,Amin, yaya yaushe zaka koma ne? sai bayan wata daya' amma kamar yayi yawa,a yadda kasa ba zuwa, eh haka ne ina son in huta da yawa ne...right! ni kuma sai in ganka da yawa kenan shiyasa nake kara jin sonki a cikin zuciyata mimi har nake tunanin bazan iya rayuwa bake ba...nima haka yayana i love you so much more .
Mimi!!tashi baccin ya isa haka kinsan yau ranar family meeting ne,ina so mu karasa aikin mu cikin lokaci,to mommy. Dayake duk za'ayi family meeting kowa da kalar abincin da zai kai, bayan angama meeting kowa shi zai dibi abincin son ransa, suna masu ci cikin zumunci da yarda da kuma aminci. Kowa ya hallara a babban falo, Alhaji Hassan shi ne ya bude taro da addu'a,Alhaji ne, ya tashi yana cewa "dama yau rana ce wacce muke tattaunawa akan abubuwa da dama ciki harda warware matsalolin mu da suka shafi wannan family, sai dai yau Alhamdlillahi babu matsala ko daya inshaAllah fa ce alheri da na zo muku dashi. Alherin shi ne za'a sa ranar daurin auren Mimi da faruk,wadan da dama kowa yasan suna son juna sosai da sosai. Duk da haka nasan zaku yi mamaki sosai saboda ba wanda ya kawo auren su kusa,nima a daren jiya nayi wannan tunani ya kamata a yi auren nan kafin faruk ya tafi tunda Mimi ce yake jira kuma ta kare karatun ta, na secondry, in yaso idan mijin ta ya amince ta ci gaba da karatu, sai taci gaba. Gaba ki daya falon yayi tsit kowa na saka abu a cikin zuciyar sa kuma da alama abin yayi matukar yi musu dadi,akasin faruk wanda tun lokacin da aka fara zancen zufa ke karyo masa har yanzu. Ko meye dalili oho,muje zuwa.....
.
Ina fatan wannan hukunci da na yanke yayi? gaba dai falon ya dauka sai cewa suke"yayi gsky hakan yayi daidai Allah ya tabbatar da alheri.Amin Ko akwai mai magana a cikin masoyan?cewar Alhj hassan.Eh Abba, faruk ne ya furta hakan tare da mikewa tsaye,fadi maganar ka muna jinka. Don Allah famly kuyi hakuri da abinda zai fito bakina musamman ma Alhj da Mimi nasan zaku fi kowa jin haushi da kuma mamaki akan abin da zan fada. Alhj inaso ayi hkr a janye aure na da Mimi....saboda me! alhaj hassan ne cikin kakkausar murya yake magana, faruk kana da hankali kuwa?meye dalilinka.....Abba wlh bana son Mimi.....INNaLILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN falon ne ya dauka da hakan sai da kowa ya mike saboda tsananin mamaki akasin mimi wacce ko mikewa ta kasayi tana nan zaune kamar gunki,idanunta na kan faruk ko kiftawa basayi saboda tsananin mamaki.
.
Tas!!Tas!!Tas!!kake ji Abba ya wanke faruk da mari uku masu kyau cikin tsananin bacin rai...ka ga kyale shi haka, faruk fada muna dalilinka na cewa baka son Mimi,alhj nima haka na sami kaina da bana son Mimi a cikin 'yan kwanakinan nayi duk yadda zanyi in maida son yaki amma wlh ina son Mimi abaya shiyasa banaso ayi auren nan nasan wahala kawai zatayi.....Hauka! to bari kaji in gaya maka aure ba makawa sai anyi in yaso ka kasheta, dan rainin hankili..a'a alhj hassan cewar abban Mimi, baza ayi haka ba tunda baya so shikenan....wlh ba makawa auren nan sai anyishi kuma cikin satin nan inshaAllah. Kuma ka bace ka bamu wuri,koda abba ya juyo ya ga Mimi zaune shar hawaye na zuba a idonta,kuma har yanzu idanun ta na kan faruk ...Mimi !mimi! Abba ne ke jijjiga ta,ko motsi taki, fa ce hannuta da ta nuna faruk dashi, amma sai ta kasa furta komai ganin sukayi ta zube kasa sumammiya innalillahi wa inna ilaihi raji'un kowa yayi kanta sai yayyafa mata ruwa ake, da kyar suka samu ta farfado aka wuce da ita cikin gida. Faruk sai kuka yake sosai akan rashin fahimtar sa da ba'ayi ba.Hafiz yaja shi zuwa dakinsa. Hafiz wlh na kasa gane wannan al'amari da zuciya ta tazo min dashi...... sai kuma wani irin kuka ya kwace masa. .
.
Hafiz nasan yanzu Mimi zata yi tunanin na cuceta....to kai meyasa baka bar abin a ranka ba watakil ko son zai dawo bayan anyi aure, hafiz bana tunanin haka,kuma bana so kyautawa ta da Mimi ya dawo rashin kyautatawa, domin idan na aureta a cikin rashin sonnan bansan mai zai faru ba,ban taba tunani cewa soyayya ta da Mimi zata dawo hakaba,faruk addu'a ya kamata kayi domin wannan al'amari na zuciyar ka yana da ban tsoro da al'ajabi. Mommy, yaya ya cuceni, yayi min ilar da har in mutu bazan mantaba,me nayi maka da zaka min haka.. ashe da gaske ne cewar zainab namiji ba dan goyo bane,mommy yaya yasa na tsani maza a duniya, Allah ya...kul!! kar ki kuskura ki kara tunanin furta wanna mummunar Kalmar....wayyo Allah mommy na yazan da raina.... wani irin kuka ya kwace mata mai tsanani. Kiyi hakuri Mimi dama haka rayuwa take soyayya na zama ki,haka kuma ki kan koma so kiyi hkr kinji, ki rungumi kaddara,tajawota jikinta ta rungume, tana mai kara rarrashin ta. Faruk baka kyauta wa family din nan ba,faruk me ya hada ka da mimi da har zakayi wannan furucin da ba Mimi kadai taji zafinsa ba. Umma wlh mimi bata min komai ba kawai haka naji a zuciyata bana sonta.....da kin kyale dan iskan yaron nan marar mutunci, wanda hankalinsa kadai ake gani amma baya dashi...a'a Alhj kada zafin zuciya ya debeka kayi wa yaron nan baki.
.
Abbah don Allah kayi hakuri nasan nayi kuskure,ko kallon inda faruk yake baiyiba ya tafi abinshi. Faruk kodai wata ce kagani kanaso?ko daya umma ,abin sai kace tabin jinni, ko wani abu ya hadaka da wani ne ko sabani akan mimi ko yace yana sonta kaci mai mutunci,umma gsky babu,hmm faruk kenan mai hankali bazai ji wannan zance ya yadda dashi ba,dole akwai wani a bu kasa,umma...faruk, tashi kawai kabani guri. Zainab kizo akwai magana,ok sai nazo kenan,ta aje wayar tare da share hayen da suka zubo mata. Barka da wuni mommy yauwa Zainab yau kece a gidan namu?eh mommy, to ya mutan gida lafiya lau,jeki Mimi na daga ciki. Mimi ya ake ciki ne? naga duk kin ya kuce...Zainab aure za'ayi min da Wanda baya so na,aure Mimi?kuma da wanda baya sonki?kwarai kuwa zainab,waye wannan, yaya faruk,dama kuna da wani dan uwa ne faruk bancin faruk dinki,shi dai da kika sani zainab,shine guda ba kari,kuma shi da kansa yace baya sona..... What!!Mimi meyake nufi da haka....cin amana, mana har sai kin tambaya bayan ke da kanki kin taba nunamin halin da namiji naki yarda .....innalillahi wa innailaihi raju'un amma yaya faruk yaci amanar soyayya....ganin nake kamar wata ya samu,tunanin da nake kenan mimi.
.
Wato Mimi kin nuna masa so, ba ko dan ajin nan na mata,matsalar kenan, zainab,ai ya fahimtar dani yanzu,amma nasan abinyi. Koda Zainab ta fito suka yi kicibis da Hafiz zai shiga dakin mimi,tsaya wa yayi yana kallonta batare da ya bata hanya ta wuce ba. Sai yaga tayi mai kyau sosai fiye da kullum....yaya Hafiz ina so zan wuce,oh sorry Zainab,sannan ya bata hanya ta wuce. Yaune ranar daurin auren Mimi da faruk,anyi matukar yin taro kamar ba'a mutuwa,bayan an daura aure ne za'ayi walima,baxa su samu damar yin wasu buku kuwa ba,domin basu da isasshen lakaci, saboda zasuyi sammako zuwa London. Zainab ce ke shirya Mimi sai tsokanar ta take,amarsu ta ango kinga yadda kikayi kyau kuwa na tabbata ko makiyin ki yaganki sai ya sake kallo ,meye amfanin haduwar, miji baya so...hmm ni bana son kina zancen nan fa...Allah, to na daina. Kina birge ni mimi ta yadda kika cire damuwa a cikin ranki,kamar ba abinda ya faru.
.
Zainab na fahimci idan nasa damuwa a raina bani da wata riba face rashinta,na fiso in maida lamarina a wurin ubangiji, da yaddar Allah inhar da gaske yaya keyi na yadaina sona inshaAllh idan na dage da addu'a zai soni. Zainab ko London muka je zanyi harkar gabana ne,zan nuna kamar dama can bamu shakuba, amma zan masa duk wata biyayya da mata take ma mijinta. Mimi kenan meyasa zakiyi haka.... so kike in shishshige masa in yaso ya kara jin haushi na ne...hmm zainab muma daina maganar nan pls, saboda raina kara baci yake. Bayan angama walima, Mimi da Zainab ne a daki, suna kallon fotunan da suka dauka a waya,Mimi wannan foton duk yafi kyau,bari a turama yaya faruk yagani tunda bai ganki ba....a'a Zainab karki tura...da sauri zainab ta tashi domin ta gudu.
.
Ita ma Mimi biyo ta tayi aguje,Zainab na kai wa bakin kofa taci karo da mutum, gata rungume a jikinsa, sannu,sannu take tada kanta, saboda tana fargabar waye, koda ta dago idonta taga Hafiz, da sauri ta janye jikin ta, cikin jin kunya, har bata son hada ido da shi shiko gogan wani farin ciki ya ziyar ceshi sai tunani yake ina ma ace mallakin sa ce...... yaya hafiz yi hakuri bada sani na bane...no zainab,ba komai ai ya wuce Mimi, faruk yace "tunda safe ne tafiyar ku,daga kai tayi alamar taji,domin dariya ne sosai ta keji,saida yafita sannan, ta fara dariya sosai tana nunin zainab,shi ne dai dai dake...kinga banaso to ni inaso,kanki ake ji,kin tura foton? ai dama wasa nake miki....a'a ai tunda kin tura a kirjin yaya Hafiz zai je wa yaya faruk ko? Mimi!!...Zainab...yayi zan rama ne, cewar zainab. Mimi ce agaban mommy da daddy su nayi mata nasifa akan tabi mijinta sau da kafa,nasifar ta ratsa ta, hakan ya sata kuka sosai,kenan dai zantafi in barku mommy zanta fi gurin wanda baya sona ni kadai ke sonsa mommy.....yi hakuri kinji mimi ya isa,tashi muje cikin gida ki musu bankwana.
.
A filin jirgi,Mimi sai kuka take mai cin rai ta rirrike abba,tana cewa,"Abba na fasa auren tunda shi baya sona.....kaka ki gaya ma su da gaske nake na hakura....Alhaji don Allah ka taimakamin kajenye auren nan nafiso na zauna daku, haka take binsu tana kuka amma bawanda yace mata kala saboda ta basu tausayi har basu san me zasu ce mata ba,baba Bashir kadai ne yayi karfi halin yaimata magana, yi hakuri Mimi nasan cewa, yayanki bazai cutar da ke ba, amatsayinki na kanwa a gare shi, ki yi hakuri kinji, daga kanta tayi alamar taji tana, mai share hawayenta. Zainab ce ta rungume ta suna jin kamar kar su rabu, faruk ne yaxo, ya ja hannuta su ka shiga jirgi,suna masu yi musu bye bye. A cikin jirgi ne faruk ke kallon Mimi yana magana a cikin zuciyar sa"yau wai Mimi ce ke kukan bazata bini ba, bayan ada kuka take zata bini,lailai nayi kuskure. Bayan sun isa ne,Mimi sai kallon gidan take yayi matukar birgeta gashi da fadi,mutun zai sakata ya wala,haka ta fada a cikin zuciyarta.
0 comments:
Post a Comment