ya nuna mata dakinta, shiko ya tafi nasa dakin,wanka tafarayi, ta kwanta domin ta samu ta sauke gajiyar tafiya, bacci barawo ya dauke ta. Koda ta tashi,ta samu ya aje mata takeaway gashi dama tana jin yunwa sosai,ta zauna taci saida ta koshi, bata da abinyi kuma tana fashin sallah,tashi tayi tana yawata wa,a cikin gidan anan taga wurin wasan basket ball gashi ko a gida wasanda sukeyi kenan hakan yayi matukar yimata dadi, ai ko saida tayi ball sannan ta koma ciki,ganin marece tayi. Wuraren karfe goma na dare tayi shirin bacci kenan,taji motsin shigowar sa,"wai yanzu naji dama, ni kadai a gida tun dazu sai kace maiya,kwantawarta keda wuya ya shigo dakin da sallamarsa ,ta amsa sallamar tare da gaishe shi, ya mika mata ledar hannusa tare da amsa gaisuwar,ba yabo ba fallasa. Gasashiyar kaza ce da hollandiya milk a ciki,taci sai, dai ba sosai ba, domin taci ragowar na dazu,tasa saura a firij,tayi kwanciyar ta,sai safe.
.
Ba ta farka ba sai wuraren karfe goma na safe, tayi wanka,ta shirya cikin wasu kana nan kaya,riga da siket, rigar iya cibi, sai siket dinma ma iya cinya tayi kyau sosai,saida ta gyara ko ina fes,sanna taje kici neman abinda zata ci, ba komai a kicin din,illa kayan tea,sauran kazar jiya ta dumama ta hada da tea ta ci. Kwance take falo tana game da wayarta,da tagaji ne da game ta kunna tv, tana kallo. Yau sati daya kenan amma ba abinda ya canza kullum abinci saye take ci,ga kadaici na damunta,tun zuwanta bata yi waya da kowa ba,sabida bai saya mata layin canba,shi ne ta yanke shawarar idan ya shigo xata masa magana. Bashi ya shigo ba sai karfe tara da rabi,tana kan sallaya tana karatun Qur'ani taji shigowarsa,saida da takara minti talatin sannan,ta je dakinsa da sallamarta,sai da yabata izini sannan tashiga. Zaune ta same shi bisa gado yana dan wani aiki da laptop,daga shi sai singlet da wando. Yaya sannu da aiki,yauwa sannu yabata amsa ne batare da ya ko kalli inda take ba.
.
yaya dama cewa nayi me zai hana a siyo kayan abinci,akan wane dalili? ganin nayi zaifi sauki,gashi kuma nagaji da cin abincin sayarwa,ni da nake siya bance miki naga gaji ba sai ke,da ci ne kawai naki,dan kin raina ni ko? yaya meye raini anan kuma,ganin nayi siyen kayan abinci yafi sauki,saboda kinfini fini sanin abinda yakamata ko?mamaki ya bata sosai ganin a hasale yake magana, Allah ya huci zuciyarka,ta furta hakanne tare da fita daga dakin a tsorace domin ganin take ko dukanta zai iya yi. Ta koma dakinta cike da mamaki,tana cewa"rashin so bala'i ne, idan ba haka ba wannan maganar ce zata hasala shi,ina ma ace yanzu ne kake so na ba a lokacinda nake gidanmu ba,amma sai lokacin da zan yi rayuwa a gidanka zaka ji baka sona,yaya meyasa zuciyarka ta zo maka da wannan al'amari? Wanda ni bazan iya jureshiba,why?yaya. Kuka take sosai,tana rokon Allah ya sauya mata wannan al'amari,cikin sauki, tana cikin kuka ne bacci barawo ya saceta. Ba ita ta farka ba sai asuba,tayi sallah taji baza ta iya komawa bacci ba saboda yunwar da take ji,kici ta nufa domin ta hada tea,ga mamakin ta sai taga kayan abinci makil ,wato dama jiya yaya ya siyo kayan abinci,shi ne yayi tamin fada,kamar ma ba zai siyo ba. Nan take, tahada musu breakfast mai rai da lafiya, gida duk ya kamsashe,a dining table ta jera komai,sannan taje tayi wanka,ta shirya ne cikin super Holland riga da siket sun dan kamata kadan, tayi daurin dankwalinta, mai kyau ta jashi baya, gaban gashin ya kwanta sosai,ta sake sauran gashin a bayanta. Ta fito das,das,da ita sai kamshi take,dakinsa ta kwankwasa sai gashi ya fito da shirin fita,saida yaji wani abu da ya ganta,tayi kyau sosai,cike da murmushi ta gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa.
.
yayana breakfast na jiranka,batare da ta tsaya jin me zai ce ba,ta juya hade da jawo jelar gashinta zuwa gaba, wato ta maida shi saman kafadar ta,hakanne yabashi damar ganin show me your back,tafiya take kamar wacce ba qashi a jikinta,tana wani irin laudi,ga hips da Allah yabata duk da haka bata kiba ba rama,ya salam,Allah yayi halitta anan, tun randa nake da mimi ban taba ganin tayi kyau irin wannan ba,cewar faruk. Abinci suke ci amma sai mamakinta yake kamar wacce bata da damuwa a tattare da ita.Da zai tafi har bakin mota tarakashi. Haka sukaci gaba da rayuwa har tsawon wata ba wani sauyi,kwalliya nan tanayinta yadda ya kamata,abincin ta lafiya ko makiyinta yaci bazai ce baiyiba,tana masa biyayya dai dai iyawarta, gata da tsafta,uwa uba tana ibada ba dare ba rana. To ni Mimi mena rageshi da shi,amma nakasa miado sona,ko dai zan hakura da kaine yaya....a'a Mimi gajen hakuri bana ki bane,ki tuna fa a kwai Allah,kici gaba da hakuri da kuma addu'a, cikin ikon Allah sai ki ga komai yadawo daidai. Tana magana ne da zuciyar ta, haka ne fa,tayi maganar ne a fili. Faruk ne zaune a falo yana kallo,kamshin turaren ta ne ya dawo da hankalinshi wurinta sanye take da doguwar riga ta kanti baka mai dogon hannu, anyi mata kwalliya da fararen duwatsu,ba dankwali a kanta,tayi matukar yin kyau.
.
Sai dai yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa a tare da Ita. Zama tayi akusa dashi, yana saman kujera ita tana kasa,tafara da cewa. "Yaya kaje a bainar jama'a ka tozartani baka dubi zumuncin da ke tsakanin mu ba,ballantana har kaji kunyar mahaifina, agabansa ka furta cewa baka sona, hawaye ne shar ke fita a idonta amma hakan bai hana ta cigaba da maganar da takeyi ba,yaya idan har wani laifi naima meyasa baka kira ni a gefe ka gaya min ba har saida kaje a cin jama'a, kasa iyayenmu a cikin bacin rai da bakin ciki,nayi hakurin wannan, amma bazan iya jure wannan ba ..... Ya isa mimi!....ya isa haka!... wai me kikeson cewane da har sai kin bata min rai kafin ki fada?yaya tun lokacinda muka zo banta taba fita ba, bantaba waya da kowa a gida ba, ko da yaushe ina cikin kadai ci, yaya, ya kake so nayi da rayuwata ne...kuka take sosai shiko faruk duk gabadaya tausayinta ya lullube shi, jikinsa yayi sanyi sosai. Mimi pls kiyi hakuri tun zuwammu da kwana biyu na saya miki layi, koda naje kai miki nasamu kina bacci,shi ne na saka, a cikin drawer,Allah na manta in gaya miki amma kiyi hakuri,kinji, Yaya kana nufin Abba bai taba tambaya ta ba,Mimi ko nakira Abba baya daga wayana yayi fushi dani kuma inajin kunyar kiransu daddy,sai su Alhji da kaka kawai, amma sukan tambaye ki,sai dai, akanyi rashin sa'a bana gida.
.
Yaja hannunta suka je dakinta,drawer din ya bude ya dauko layin. Miko wayarki a saka layin,ta dauko wayar ta bashi,yauwa yanzu kinga sai a kira daddy ko?eh yaya,ringing daya tayi aka daga wayar,tare da amsa sallama,daddy Mimi ce, mamana aikinsan muryanki bata bace ,ya can din?lafiya lau,ya yayanki yana lafiya?lafiya lau. Daddy nayi mising dinku dayawa ina momyna,ga momynki,Mimi injin dai kunan lafiya dai ko?Allah mommy, lafiya kalau muke to in jin dai kina masa biyayya, yadda yakamata, Allah momy ina masa,to kici gaba da yimasa biyayya kinji,inshaAllah komai zai bi daidai,sun dade sosai suna waya,sannan takira su kaka suma ta gaisa dasu,yaya gaskiya akira abbah tayi maganar a cikin shagwaba. Kirashi mana,amma nasan ni bazaiyi magana dani ba,yaya zai yi magana dakai....hmm Mimi kenan bakisan Abbah ba ne idan yayi fushi....Ya daga wayan fa,Abba barka da wuni,a'a 'yata Mimi kece?eh Abbah nice,ina fata dai yayanki baya cutar dake?bayan min komai.....amma don Allah kayi hakuri da abinda yayi,Mimi bawai banyi hakuri bane,inaso in kwatar miki 'yancinki ne...ko bakya so?inaso abba ...to ki barni dashi kawai so nake sai yagane kuskurensa,ga ummanki, tanaso ku gaisa,bayan sun gaisa ne,umma tayi,tayi mata nasifa akan taci gaba da hakuri,sannan ta aje wayar,tana mai kallonsa,idanuwansa sunyi jawur,kingani ko nagaya miki....kayi hakuri yaya,jawoshi tayi jikinta ta rungumeshi,tana kara kwantar mai da hankali.
.
Shima rungumeta yayi,yana shafar gashin kanta,har ya fara wuce gona da iri,saurin dakatar dashi tayi,da cewa"yaya muje muci abinci,bahakan ya soba amma ba yadda iya dole yatashi suka je cin abincin,da suka gama ne suka koma kallo,har wuraren karfe goma. Mimi tashi muje muyi bacci dare yayi,wani iri taji zancen abinda bai taba yi mata ba,tashi tayi suka jera kowannesu ya shiga nasa daki,toilet tashiga tayi wanka,sanna ta fito tayi shirin kwanciya,tana kokarin kwantaya taji yana nocking kofanta,me kuma yaya yake bukata cewar mimi.Tashi tayi ta bude masa kofan, tsaye tayi tana jiran taji kome yake bukata,yanayin kallon da yake mata ne ya tunatar da ita tufafin da ke jikinta, da ita da babu duk daya ne,da sauri tajuya domin dauko hijabi,idan kinsa hijab din kizo muje dakina. Bayan sunje dakinsa ne ya umarce ta da tayi arwala,"yaya ina da arwala,to zo muyi nafila mugodewa Allah,hadi dayin addu'a Allah yasa ma aurenmu albarka,raka'a biyu sukayi ya juyo ya dafa kanta yana addu'a. Written by BilkeesuSai da yayi mata tambayoyi akan addini ya tabbatar bata da matsala, sannan,ya dauke ta chak ya aza bisa gado,tare da cire mata hijab,anan yafara gwada mata iyawarsa,sai rokonsa take yayi hakuri,Mimi bazan iya bane pls kibanni nayi,ciga ba yayi da shafarta ta ko'ina har yana kokarin rabata da kayan jikinta,yaya pls....bakinsa yasa a cikin nata yana tsotsa, sai da ya tabbatar ya kashe mata jiki sannan ya fara addu'a saduwa da iyali,wata irin kara naji Mimi tayi,wacce ni Bilky giro,sai da na bar dakin aguje ban shiryaba. Sai da safe na samu na dawo dakin, bacci suke abinsu rungume da juna. Faruk ne yafara tashi cike da farin ciki yake kallon Mimi,duk yaji taba shi tausayi yarinya 'yar shekara 17 ya kasa hakurin bari har ta qara girma. Daukar ta yayi zuwa toilet domin suyi wanka,ya hada mata ruwan zafi da dettol ya sakata a cikin bahon wanka,qanqameshi tayi alamar taji zafin ruwan sosai,yaya da zafi tana magana ne a cikin shagwaba,sorry my Mimi,sai da yagama yimata gashi sanna sukayi wanka,suka fito,suka gabatar da sallah..
.
Shi da kansa ya hada musu breakfast,sukaci,Mimi kwanciya ta koma yi,akasin shi da yake shirin zuwa aiki,yagama shirin sa tsaf sannan ya dawo gun Mimi,yadai Mimi ko akwai abinda yake damunki?yaya zafi nake ji a gun,oh no Mimi sorry ba laifi na bane,nifa a sannu na biki,kece very tight,amshi wannan magani ko zaki ji sauki,bayan tasha maganin ne ya lallaba ta, har saida tayi bacci sannan ya fita. Ba ita, ta tashi ba sai wuraren karfe 12pm.wanka ta komayi,sannan ta gyara ko'ina na gidan tsaf,gida sai kamshi yake. Kici taje domin samun abu mai sauki wanda zata girka ,kuskus ta datafa da stew da naman kaza,sanna da dafaffen kwai,ta kai kan dining table ta jera,tana jiran dawowar sa. Wayart ta dauko takira zainab,ringing daya biyu ta daga wayar,hello Zainab Mimi ce,lah Mimi ashe,akan jiku,ya amarci,Alhmdlh,
kinji ni shiru ko zainab?har wata fa ba kira,nace ko dadin auren ne?hmm zee kenan har akwai abinda zai sa inmanta da ke in ba gushewar hankali ba,to har amin baiko ba kira kuma nasan bazaki rasa jiba,yaya ya manta bai gayan min ya aje min layi a daki ba,ni kuma ban tambayesa ba sai jiya,Allah zee banjiba dawa akayi,na baki gari ki canko,nadaisan ba kya son Habib dashi akayi ko kuwa?hmm an barki baya Mimi,da yaya hafiz akayi,dan girman Allah!da gaske nake miki zancen nan,bayan tafiyarku komai ya hadu,soyayya zamzam kamar wadanda sukayi shekara, amma nayi matukar murna wlh, Allah ya kara dankon soyayya,Amin mimi na gode,sannan suka aje waya,tana mamaki yanzu ace yaya faruk ko yagaya min,ko da yake bazai yi tunanin banji ba.
.
Bushi ya dawo ba sai wuraren 3pm,sai faman sauri yake,saboda yabar Mimi ba abinci, bai kuma yi tunanin zata iya dafawa ba,bai zame ko ina ba, sai dakinta,kwance ya sameta akan kafet din sallah tana bacci,da alama tana gama sallah tayi bacci domin ko hijabi bata cire ba. Durkusawa wa yayi cike da tausayinta, yana mai shafar fuskarta tare da bata kiss,kamshin turarensa ne ya tada ita, a hankali take bude idanuwanta cike da jin bacci,yaya ka dawo?sai yanzu nasamu damar dawowa, meeting ne ya tsaishe ni,kiyi hakuri na barki da yunwa,ba haka naso ba,ba komai yaya,abincin zaka fara ci,ko sai kayi wanka,kin dafa abinci ne?daga kanta tayi alamar eh,i hope kinci?banci ba kai nake jira,haba mimi tayaya zaki jirani bayan kina jin yunwa,yaya nafi jin dadin cin abinci da wani,amma dai irin haka ai sai ulcer ta kamaki,ki daina dogon jira haka kinji,naji, to tashi muje muci abincin,amma cire wannan hijab din. Ta cire hijabi suka tafi. Yau shi da kansa yake bata abinci a baki,tana lafe a saman jikinsa,sai wani kara narke masa take,sai da suka koshi sannan sukayi wanka. Kwance suke a bisa gado rungume da juna,ba kaya a jikinsu sai bargon da suka lulba dashi, da alama wanka sukayi,Mimi na shafar gashin kirjinsa,shiko yana shafar gashin kanta,koma wa yayi kan dukiyar fulaninta da suke rikitar dashi ko yaushe,anan tafara jin yana so ya wuce gun..."um um fah yaya,kin manta yau fa sati daya kenan,kuma kice zaki hana ni,gashi kinsan gobe ne tafiyata,yanzu yaya ni kadai zaka bari, a'a zan kayo miki wata kanwar abokina da take karatu anan,a hostel take zama,idan na dawo sai ta koma,hakan yayi miki?daga kanta tayi alamar eh,yanzu za'a barni nayi ko?kunya taji sosai har da rufe idanunta,nan suka faranta ran juna.
.
Kwance take duk jikin ta ya mutu,shi ko faruk sai shirin tafiya yake. "Mimi yau bazaki taya ni shiri ba,yaya Allah jikina ne ya mutu, ni bana son kayi tafiyannan, mimi kenan to ya aka iya,tasowa tayi domin ta taya shi tsarin kayan da zai sa, kwana nawa zaku yi?kallon ta yayi kafin ya bata amsa, sati daya, haba yaya shi ne baxa ka tafi dani ba,wai sau nawa zan gaya miki ba zai yiyuwa ba,sbd bani kadai zanyi tafiyar nan ba,meza ku jeyi a China din?zamu dauki lecture a gun wani shahararren doctor,to yaya.....to yaya me?so kike sai na bata miki raine kafin intafi ko?sadda kanta tayi kasa,cikin yanayi na son tayi kuka,tana mai ci gaba da tsara mai kayan. Ta gama tsarin kayan amma ta kasa tashi a gun,faruk ya lura da haka,zowa yai ya tasheta daga durkushen da take,Mimi kiyi hakuri wani lokacin zamu yi tafiya tare kinji, daga kanta tayi alamar taji,nan ya fahimci kuka take sonyi, rungume ta yayi Mimi kar kiyi kuka mana,kinsan bake kadai zaki zauna a nan gidan ba,to ai Ita ba kai banecikin kuka take maganar, nasani amma ai hakuri zaki yi.....karar wayarsa ce ta katse su,kinga Mimi ni kadai ake jira. Har bakin mota ta rakashi, yashiga yana mai yi mata bye bye hadi da jefo mata kiss,ita ma haka, tana kuma yimai addu'ar, zuwa da dawowa lfya da kuma samun nasara akan abinda suka jeyi,har sai da ya bace ma ganinta,ta koma daga ciki.
.
Zaune take a falo tana kallo,taji nocking tashi tayi ta bude kofar,wata yarinya tagani kyakkyawa da ita ba laifi, sai dai bata da fari sosai,kuma baza ta wuce tsaran mimi ba"zaki iya shigowa cewar Mimi tare da bata hanya,bayan sun zauna ne bakuwar ke cewa"suna na khaleesat,nice kanwar abokin mijinki,wato yaya Hashim, wow nice name,nikuma suna na mimi, Sannuki, ya karatu?Alhmdlh, kiyi hkr na jima ban shigo ba,ba komai,ai ban ma zaci zaki shigo yanzu ba,tashi tayi ta kawo mata abinci,tana ci suna fira kamar dama sun san juna. Bayan tagama cin abinci ne ta nuna mata masaukinta,tana mai cewa"sai dai banganki da kayan sawanki ba,suna a mota ta na bari,wai koda banan gidan bane,kinga yanxu zan dauko ba tantama,haka ne fah. Washe grin ranar, Mimi ce a kicin tana hada musu abin karya warsu,sai ga khaleesat tazo ta sameta,tana mai cewa,ke kadai ke aiki ba gayyata,ba haka bane naga zaki je school ne...wace school? yau fa weekend,kinga sam na manta,iyye sbd hutawa,wane hutawa,kawai mantawa dai nayi,ko kuma dan ba kya zuwa school ba,ai idan bana zuwa,yayana yana zuwa aiki,eh kuma fa,tare suka kammala hadawa,dama sunyi wanka,sun gyara ko ina fes fes,sai suka zauna ma ci.
.
Haka suke rayuwar su abin sha'awa,kamar 'yan uwan juna. Yau sati daya kenan da zuwan khaleesat wanda yayi dai dai,da yaune faruk zai dawo,sun shirya mishi lafiyayyen abinci. Zaune suke a falo suna fira,firar da baza ta wuce ta salim ba wato saurayin khaleesat koyaushe bata da fira sai ita. "ke khalee kodai zowa za'ayi a muku aure a huta, baki da aiki sai maganarsa,koyau
she kuna manne da juna ta waya......hmmm Mimi kenan, ke da kunyi aure amma ko yaushe cikin waya,sannan wannan uwar kwalliyar da kikaci duk fa don shi ne, khalee kenan, to ai ni mijina ne idan banyi masa ba wa zanyiwa,gsky kam,ni har birge ni kukeyi,da gaske?Allah kuwa. Nan dai suka cigaba da firar su......... cikin firar ne suka ji ana nocking kofa,aiko ba shiri Mimi ta tashi ta bude kofar,jikinsa ta fada ta rungumeshi,yaya
na sannu da zuwa,shima rungumeta yayi tare da kaimata kiss a kumatu,suna masu karasowa cikin falon,amma ga alama Mimi ta manta da khalee na nan falon, domin sun soma fita hayyacin su ba tare da sun bar falon ba,ganin haka ne yasa khaleesat yin gyaran murya,faruk ne ya fara juyowa,yana mai cewa "a'ah, khaleesat ya kike, ya karatu?yana mai sosa keyar sa na alamar jin kunya yayi maganar. Lafiya kalau, ya hanya? alhmdlh,Mimi duk kunya ta hanata juyawa sai kokarin take ta janye jikinta daga nashi,shiko yaki ya sake ta,sai da ya gama gaisawa da khalee sannan suka shige daga ciki.
.
Wanka zaka fara yi ko abinci zaka ci?abinci zan fara dashi domin yunwa nake ji,to yayi bari na kawoma,kunci abincin ne?a'a,to me zai hana inzo muci gabadaya,no kaidai bari in kawo ma naka,takarsa maganar ne tare da fita,sai da ta gama jera masa komai da tasan zai buqata,ta fita domin suci nasu,a daki ta sami khalee kwance,"har kin kwanta,to taso muje muci abinci ko,suna cikin cin abincin ne khalee ke cewa"yau fa zan koma school bazan qara ko kwana daya ba, me kike sonyi a school wannan sauri haka, gashi gobe weekend,kinsan mun kusa fara exam fa,hake ne,na manta. Lallai kina futawa da yawa,hmm ke kullum baki da aiki sai cewa mutum yana hutawa, ai koni result kawai nake jira yafito na fara karatu,yaya faruk zai bari ne?eh akwai wani lokaci dana tambayesa ya kuma amince,anan ma yace zanyi karatu inshaAllah, to Allah ya taimaka,Ameen.......suna cikin magana ne sukaji faruk na qwalawa Mimi kira,ta amsa kiran ne tare mikewa cikin sauri. Yaya gani,kun karasa cin abinci,eh munkare,to muje kitayani wanka,bayan sun fito ne,take fadamasa cewa yau khalee zata wuce,saurin me take haka?kasan sun kusa fara exam, ok yayi Allah ya taimaka.
.
Yaya please katashi muje muyi ball,Mimi me yasa kike son muyi ball?kullum sai munyi nida khalee,amma tunda ta tafi ban sake yi ba,sbd baka bari,Ita khalee har tana da lokacin ball,ksan morning lecture takeyi,sai muyi ball da maraice....yaya meyasa baka bari,sbd yanayin jikinki yanuna kina da ciki,kai yaya har naji kunya wlh,kunyar me Mimi?ai ni yarinya ce ban isa ba,Mimi kenan..... yau wata mu biyu da zuwa london fa,kinga kenan cikinki wata daya,amma bani da tabbacin ko ya kai wata daya sai na aunaki,yaya to muje shan ice cream,kinganki Mimi ba kya bari mutum ya huta......oya tashi ki shiryo muje.....yeeee! Yaya thank u,ganin yadda ta tashi da gudu ne, yasa ya dakatar da ita,cikin tsawa"Mimi!juyowa tayi ba tare da ta karaso ba,zo Mimi,cikin sanyi murya yake magana. Mimi pls ki daina gudu kinji,sbd cikin nan bai yi kwari ba,zai iya zubewa ako wane lkc,idan kuma ya zube a dalilin ki zamu iya samun matsala,pls take care, yaya kayi hkr inshaAllah hakan bazai sake faruwa ba.
.
Bayan wata daya da faruwar hakan. Mimi ce a bisa lilo sannu a hankali take yi,tana mai rera waka cikin natsuwa,karar budewar gate taji da alama faruk ne sbd lokacin dawowarsa ne,hakanne yasata tashi domin ta tarboshi kamar yadda ta saba,da Isar ta gun ya ware hannayensa,fadawa jikinsa tayi tana yi mai sannu da zuwa,tare da amsar jakar hannusa,suka karasa daga ciki,sai da yayi wanka sanna suka zauna cin abinci,budewar kula keda wuya taji wani irin amai ya tunkarota,aiko ba shiri ta haura sama domin zuwa toilet,faruk na biye da ita har toilet,sai sannu yake mata,ba iyaka,da ta gama,ya dauko ta ya aza abisa gado,yana mai yimata sannu, Anan yakawo musu abinci domin suci,"yaya ni baxan iya cin wannan abincin ba,asali ma shi ne ysa ni amai,to me kike son ci?fresh milk,ai bazakiji kin koshi kamar abinci ba, eh nidai kawai abanni nasha,tashi yayi ya dauko,ya tsiyaya a cup ya mika mata,tana gama sha sai bacci abu ga mai ciki. Haka yake fama da ita kullum, bata iya cin komai sai fresh milk, ga yawan bacci,amma hakan bai sa ta rage bashi kulawa kamar yadda ta saba ba.
.
Akwana a tashi yau cikin Mimi yakai wata uku. Kwance take a bisa kirjnsa sai zuba shagwaba take, "Yaya yaushe zamu je gida ne?not now,yayi maganar ne a takaice,meyasa yaya?Mimi inaso ne sai cikin nan ya fara kwari, sbd bai zaunu da kyau ba,irinshi yafi saurin kawo matsala, yaya pls kayi hakr mutapi ,inshaAllh baza'a samu matsala ba,kibari nan da wata daya mugani, to Allah ya kaimu,Ameen. Tashi ki dauko fresh milk kisha, domin daganin cikinki yunwa kike ji,tun dazu ma nake son tashi amma kasala ta hanani, ta karasa maganar ne tare da mikewa,garin dawowa ne tayi tntube da center capet ,da sauri yatashi ya tarbo ta, kar ta kai qasa,"sannu bakiji ciwo ba dai ko?girgiza kanta tayi alamar a'a. gama shan fresh milk na aunaki inba matsala,tana gama sha ya duba, ba matsalar komai,wani irin ajiyar zuciya yayi,yana mai cewa "Alhmdllh. Ita dai Mimi sai kallonsa take cike da mamaki,faruk ya lura da hakan, Yadai kallonfa....hmm nidai yaya mamaki kake bani,kasa cikin nan a ranka sosai,ko ranar da kamin tsawa akan nayi gudu Allah sai da na firgita,aida da kinji yadda gabana ke uku uku sai kinfi mamaki,to ai yaya sa abu a rai da yawa yafi kawo Matsala,haka ne Mimi nima na tsinci kaina da son haifuwa,sai gashi kin samu ciki ba jimawa hakan yayi min matukar dadi,sai dai cikin yana da 'yar matsalar da ba'a cika son yawan motsa jiki ba,shiyasa kika ga na fiye damuwa akansa.
.
Yaya dama duk sabon ciki haka yake?a'a sbd bai shiga da kyau bane......karar wayarsa ta katse su,yana magana akan tafiyar su Nigeria nan da sati mai zuwa, wani irin dadi Mimi taji har ta matsu bai karasa wayar ba,yana ajiye wayar,take tambayarsa,yaya amma zamu dan dade ko?akan me?zamu daiyi sati, haba yaya kabari mu danyi ko wata daya mana,noo ina da anbinyi da yawa, sannan ai idan lokacin haifuwar ki yayi a gida zaki haifu inshaAllah kinga kenan zaki sha gida hadda style, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba. Yau ne sati daya ta cika,su Mimi sai shirye,shiryen tafiya ake,"wannan zazzadin haka mimi sai kace wacce tayi shekara bata je gida ba,na fa yi kokari yaya sbd ban taba irin wadan nan watanin bana gida ba fa,to naji kiyi sauri kinsan fa karfe goma zamu daga, to yaya.....
.
Allah sarki yau zanga su kaka. Karfe 10am cif su ka daga sai Nigeria.
.
NIGERIA Koda suka sauko daga jirgi har sun samu su umma sunje tarbonsu, wani irin dadi Mimi taji kamar ta ruga da gudu, amma ba hali sbd rikon da yayi mata,yasan idan ba haka yayi mata ba zata iya gudu,suna isa ta fada jikin umma,shiko faruk ya dan rissina yana gai shesu. Yauwa sannuku ya hanya Alhmdlh umma,har yanzu son jikin na nan kin wani lafe a jikin ta,sai kace mage,cewar momy,he Momy..... ba wani haka ne, cewar faruk,gabadaya suka dau dry suna masu shiga mota.
.
Bayan sun isa ne sukaje ko wane bangare ita da faruk,suka gaishe su,da suka je bangaren su kaka ne,kaka sai cewa take"wai dan kunjin nan naki bai fara fita bane?kai kaka.... wai dama yaya ya fadi,shi ne naga kowa sai kallona ake....wannan farin ciki Mimi bazan iya boye saba,amma yaya akwai kunya kowa sai kallona yake, tayi maganar ne a cikin shagwaba, Yo ke har wata kunya ce da ke jifa yanda kuka wani makalewa juna,dagani haka kuka je kowa ne bangare, ai shi zaki gayawa haka kaka,yo shi namji ne fa,ba haka nake nufi ba,ta yaya mutum yace baya son auren, amma sai makale min yake baya ko jin kunyar kalmar da ya fada kafin ya bar gidan,tana magan ne a cikin zuciya,kuma da alama faruk ya fahimci me take nufi, domin ya janye jikinsa daga nata,ba tare da yace komai ba. Zaune suke a falon su Mimi, suna fira,da alama abinci suka gama ci.......karar wayar mimi ce ta kaste musu fira, koda ta duba, Zainab ce, ta dagar wayar tana cewa"Zee......ba wani zee, kinzo gari ko ki gaya min saida yaya Hafiz ya fadamin, sorry pls so nayi nabaki surprise ki ganni kawai a gidanku,ai na riga ki domin ni yanzu haka ina bakin gate gidanku...da gaske? Allah kuwa,da gudu ta tashi tare yadda wayr a saman kushin, ta nufi hanyar fita.....Mimi!Mimi!! Mimi!!!yaya pls ina zuwa. Batare da tsaya ba,ta ci gaba da gudu ga gate din akwai dan jayawa.
.
Momy kin ganta ko,ta kuma san matsalar da kenan fa,yi hkr faruk bari ta dawo ai zata gane kurenta, Ba a fi minti 3 ba sai gasu sun shigo Ita da Zainab,sai da zainab ta gama gaishe su, sannan momy ta fara da cewa "wai ke Mimi meyasa har yanxu kanki yana rawane,har da xa'a kira ki, kikaqi dakatawa,sai magana da kika jefowa mutane sbd rainin wayo!,Momy pls kiyi hkr....ai bani zaki bawa hakr ba,faruk zaki bawa hakr,shiko faruk tun shigowar ta, da yayi mata kallo daya bai sake ba,sbd yayi matukar hasala sai huci yake. A tsorace Mimi taje gurinsa tana mai bashi hakr,daga kansa kawai yayi alamar yaji,batare da ya ko kalle ta ba. Zainab muje daga ciki,bayan sun shiga ne Zainab ke tambayar ta,"me yake faruwa ne Mimi?kinsan ina dauke da junabiyu shi ne ya hanani gudu,sai akayi rashin sa'a na manta nayi, ke kuwa gashi baki da abinyi in farin ciki ya sameki face gudu,wlh kuwa, ni abun yana damuna, inaso indaina amma abu ya faskara,kiroqi Allah sauki mana,haka zanyi,inshaAlla
h,nan dai suka cigaba da firar su,a cikin firar ne Mimi ta dan fara jin marar ta nayi mata ciwo amma bata so Zainab ta fahimci hakan,tun tana jurewa har abin ya faskara,anan Zainab ta fahimci halinda Mimi take ciki. " yadai Mimi? marata zainab....na shiga uku, sannu ko,bari inje ingaya ma su momy......a'a kar ki fada don Allah bari mugani zuwa anjima ko zata daina,tun tana bisa gado har ta sauko kasa sbd ciwon ya tsananta,Mimi pls kibari na je.......oh no!Mimi jini fa ke zuba a jikinki...ba shiri zainab ta fita da gudu domin ta fada ma su faruk.
0 comments:
Post a Comment