Momy!....yaya faruk!......Mimi ba lafiya,kafin kace me faruk har ya haura sama,koda yatafi yaga halin da mimi take ciki sai cewa yayi"shi ke nan kin kaini kin baro,Mimi why!why Mimi!!....cikin ya zube ko faruk?Momy cikin ya zube Mimi ta min asara,innalillahi wa innailairaji'un
,faruk hakr zakayi...yanzu a dauke a kaita dakin duba marassa lafiya ka dubata,momy ai wannan jinin da ya zuba kadai ya isa ace cikin ya zube,ba sai an wani duba ta ba,wanka kawai ya kamata tayi zan kawo magani, yanzu,momy ce ta taimaka mata tayi wanka,bayan ya dawo ne, yayi mata allura hadi da bata magani,ya kwantar da ita,sannan ya kama hanyar fita daga dakin.....Mimi ce ta dakatar da shi ta na mai riko hannusa. Yaya pls........bana son jin komai daga kareki Mimi, ya fita abinsa,bai zame ko ina ba sai bangarennsu a dakinsa,da isar sa, kaya kawai ya cire ya fada toilet ya sake showertun daga saman kansa har kasa,ko zai ji sassauci, Bayan ya fito yayi zaune saman gado,ya dafe kansa da hannayensa,yana fitar da hawaye masu zafi. Ita ma mimi inbanda kuka, ba abinda take,tana tunanin yadda zata shawo kansa ya fahimci cewa Ita kaddara idan Allah ya rubto ba makawa sai anyita, dukda dai tasan da laifin ta aciki, amma ai ba da gangan bane,tana cikin haka ne su Momy suka shigo,saurin rufe idon ta tayi domin bata da abin cewa........ da dai kin bude idon da yafi,fada kan ba makawa,sai kinsha shi tunda ke ba kya aikin hankali,Momy inda take shiga ba nan take fita ba,ji take kamar ma ta dake ta,.....haba fadan ya isa haka,ki barta da zafin zubewar cikin mana, kinsan cewa Mimi yarinya ce,yakamata ki bita a sannu,umman faruk ai yarinta ba hauka bane.
.
Amma ai kya duba mata, Mimi har nawace,she is 17 years old, har yauzun bata ko shiga 18 ba fa,haka na sami faruk a nakinsa,wai kuka yake yi wanda yakamata ace ya rungumi kaddara,har nayi mamaki ina hankalinsa yatafi, hmmm uman faruk abinda da ciwo,kinsan faruk idan yasa abu a ransa,sawa yake dawa.....to baga irinta ba,.......amma dai abbanta baya nan ko?baya nan sa'ar da taci kenan,domin nawa fadan ma mai sauki ne. "Mimi kukan ya isa haka kinji,Allah ya kawo wani tsayayye mai albarka,ameen umma nagode,kina jin yunwa?a'a umma a qoshe nake koda abin ya faru, to kicire damuwa a ranki indai faruk ne zai sauko, daga kanta tayi alamar taji, tana mai share hawaye,nan suka bar dakin ita da Momy, ya rage daga Ita sai Zainab,wacce tunda abin ya faru ta kasa cewa komai, gani take kamar itace sila.......Zainab kidaina tunanin a dalilinki ne abin ya faru dama can haka Allah ya rubuto,sai da ta nisa kafin tace,"to Mimi Allah dai ya sauwaka, amma......No Zainab kar kice komai pls,kawai A barwa Allah komai. Yau kwana uku kenan Mimi bata sa faruk a idonta ba,kowa gdn yazo dubata amma shi tun lokacin bai sake dawowa ba, hakan bai hanata kiransa a waya ba yafi a qirga,domin ta bashi hkr,sai dai baya dagawa,ganin haka ne ya sa ta koma tura masa text,amma duk daya,hakanne yasa ta yanke shawarar zata je ta sameshi a dakinsa ko zai hkra. Sai da tayi wanka,ta shirya ne cikin wani tsadadden less, ash color yayi mata kyau sosai,dinkin riga da siket ya dan kamata ba sosai ba,sai zuba kamshi take.
.
Koda ta fito ba kowa a falon,bata zarce ko ina ba sai bangaren su faruk,ta nufi dakinsa tana mai nocking,amma shiru kamar ba mutum a ciki,har zata sake nocking sai taji muryashi yana cewa, yes!ta shiga ne tare da sallamar ta,ya amsa sallamar ba yabo ba fallasa,yaya barka da wuni, barka dai,yaya dama nazo ne akan inkara baka hkr don Allah kayi hkr inshaAllah......."hakan bazata sake faruwa ba,faruk ne ya karasa maganar tare da cewa dama nasan haka zaki fada, amma ba kya aiki da hakan,ba haka bane yaya inaso ka fahimci cewa idan Allah ya rubuto abu ba makawa sai ya afku,sannan da bakin ka fada cewa "cikin nan yana da matsala,wata qil Allah ya hango wahalar da ke tartare da shi,shi yasa ya mun sauki,amma ka kasa gane hakan, kamata yayi mu roqi Allah da ya sauya muna da mafi akhairinsa,Mimi! Pls get out of my room,ba musu ta tashi ta fita,ganin yadda ya hasala. Bayan kwana biyu da faruwar hakan,Mimi ce ke saukowa daga kan bene zuwa falo,ta samu Momy zaune tana waya da daddy,Mimi sai cewa take "Momy bani shi mu gaisa,ai ya ma katse wayar, Ashe kinyi waya da daddyn ki,bayan faruwar zubewar cikinki? eh Momy,amma ga alama bai miki fada ba?haka ne Momy ai yaya faruk bai gaya ma kowa ga dalilin zubewar cikin ba,keda umma kawai kuka sani sai Zainab,gaskiya ya kyauta ana son haka a rayuwa,Allah ya biyaka faruk,Ameen momy.
.
Ni kuwa Mimi banga kina shirin tafiya ba,gashi naji kamar faruk yace gobe zaku tafi,gobe Momy?eh mana bai gaya maki ba,sati daya fa yace zamuyi kuma ai bamu yi sati ba, kika sani ko canza shawara yayi,may be ya canza shawara, tayi maganar ne cikin rashin jin dadin zancen. Saida ta bari Momy taje kicin, sannan ta tashi domin zuwa jin zancen tafiyarsu,tana isa bangarensu ta samu ya dawo kenan daga wani guri,sannu da zuwa yaya, kamar bazai amsa ba,sannan yace "yauwa sannu,dakin ya bude tare da cemata bissmilla,shiga tayi ta ta zauna shiko yana rage tufafin jikinsa,ya dawo daga shi sai singlet da short niker, Inajin ki me kuma kika zo dashi yau,batun tafiya ne yaya naji ance gobe zamu tafi amma sai baka gaya min ba,haka ne amma ai ba dake zanyi tafiyar ba, meyasa yaya? Sbd baki da wani amfani agare ni,sosai ta kalleshi,sannan tace "bani da amfani fa kace yaya?yanda tayi maganar har saida ya kusa dry,anan take kuma ya sha toka,ai gsky na fada,na daya dai ko cikin kika kara samu zubaddashi zakiyi,sbd yarinta na damunki,sai naga,gara na tafi ni kadai,tunda akwai 'yan mata in inada buqata, abinci ko ba matsala ta bane,kin ga baki da wani amfani kenan...tabbas bani da amfani,sbd sha'awa ta kawai kake basona ba, ta fita batare da ta ji me zai ceba. Dariya yake sosai yana cewa"my mimi,hatta ma sha'awa da so baki banbanta su ba.
.
Tana isa dakin ta,ta fada saman gadonta ruf da ciki tana fitar da kuka marar sauti. Shiko faruk yana nan yana kallonta a laptop dinsa domin yasa camera a dakin,tana cikin kuka sai momy ta shigo,saurin share hawayen ta tayi domin batason Momy ta gane,zo muje kici abinci,sai da suka fita daga cikin dakin, ya rufe laptop,yana mai cewa "Mimi nima banso ace nayi tafiyar nan ba da ke ba,lalura ce kawai. Washe garin ranar. Faruk ne tare da umma,Abba,Hafiz
, da alama tafiya zai yi suko suna masa fatan Allah ya kiyaye hanya. Hafiz muje karakani a other pert nayi musu bankwana. Bangaren su Mimi suka fara zuwa,ba kowa a falon,faruk ya haura sama zuwa dakin Mimi. Bacci take abinta daga ita sai rigar bacci fara tas, bazata wuce iya cinya ba, gashin kanta duk ya baje har zuwa fuskar ta,sannu a hankali yake yaye mata gashin da yazo gun fuskar ta,tare da jaye pillown da ta rungume,ya maye gurbin pilon,Mimi taji abin kamar a mafarki,ta Kara rungume shi kamar za'a kwace mata shi,..... sallamar Momy yaji,tana mai cewa ai zata shiririta ka indai Mimi ce....Momy bacci take bana so tashi,sannu,sannu yayi maganar kamar mai shinfidar yaro, to jeka dai Hafiz na jiran ka,"yace lokaci na tafiya, sai da ya bata kiss sannan ya tashi,yana cewa "har yanzu bacci masu ciki bai sake ta ba fa Momy, da dane, da yanzu ta tashi, lallai kam,cewar momy.faruk ya fita tana masa Allah ya kiyaye hanya. Yaran nan kamar basu ne aka samu 'Yar matsala abaya ba,amma yanzu cikin ikon Allah soyayyar su ta yanxu, harta fi ta da.
.
Koda Mimi ta tashi daga bacci, sai kamshin turaren faruk ta ke ji a jikinta, Dakin momy taje,da sallamarta tasamu ta sallame sallah kenan,"momy yaya ya shigo ne? ya shigo domin kuyi sallama,ya samu kina bacci ya tafi abinsa.....zuwa ina? ina kika san zai je? wai da gaske yake ba zai je dani ba,ta karasa maganar ne cikin kuka. Daga gani wannan kukan har da yunwa a cikinsa tashi kije kisamu abinda kika ci,tunda kikayi sallar asuba kina nan sai faman bacci kike har 11am, Momy Allah yaya bai kyautamin ba...Mimi jeki inaso inyi lazimi. Tashi tayi ta bar dakin,tana mai cewa a cikin ranta "lallai yaya har ni zai yima haka,wato da gaske yakeyi kenan,ba komai zan rama ne. Sai da tayi wanka sannan tayi lokacin kari,fresh milk ta dauko tana sha har sai da taji tayi makil,sannan ta tashi taje bagaren su kaka,ko zata rage jin zafin abinda faruk ya mata. Sallama dai masu gida,wa Alaikissalam,...to fa kinzo ba sauran hutu...karki damu ni bacci ma zanyi, amma dai tukuna ina mijina?ya fita,amma kike a dakinsa kina kyro magana,gyaran dakin nake....haba kaka bari na gyara mana tunda nazo,a'a yi baccinki ai har na kammala,don Allah kaka sai anyi sallah zaki tasheni... to naji 'yar iya yi, murmushi kawai mimi tayi batare da tace komai ba.
.
Yau sati Biyu kenan da taffiyar faruk, kullum yana kiran Mimi amma bata daga waya, da yaga haka ne sai ya kira Momy yace aba Mimi, ansar wayar kawai take bata tare da ta aza a kunnen taba, sai taje daki ta aje, har sai ya gaji ya kashe,sannan ta mayar ma Momy da wayar, ba tare da tasan abinda ake ciki ba. Zaune suke a falo suna kallo Mimi ke cewa"Allah momy yunwa nake ji,a'ah to waya hanaki cin abinci?tashi tayi taje ta bude frij amma ba fresh milk, Momy babu fresh milkai da gangan na kyautar da ita sbd na fahimci ba kya cin abincin in akwai ta, Allah Momy bazan iya cin komai ba sai Ita,shiyasa. Ashe ko aiki ya same ki,pls Momy.....ba wani in zakici abinci kici. Tashi tayi taje bangaren su faruk,tana tunanin baza'a rasata ta ba.Da sallamarta ta shiga,sai dai waya umma take amma, hakan bai hanata amsa sallamar ba, tare da tambayarta me yake damnta, sbd fuskar ta nuna akwai dmw. Umma fresh milk nake so in za'a samu pls, sosai makuwa Mimi,....gashi wai zaku gaisa ta mika mata wayar ta fice,batare da gaya mata waye ba. My Mimi wannan horo haka, ai yayi yawa, pls am so sorry,wani irin hausin sa taji. Hmmmm me kuma kake so kace dani yanzu, bayan bana da, wani amfani a gareka.....dai dai umma ta fito gashi bata so taji, mika mata wayar kawai tayi,har kun gaisa? eh umma,to ga fresh milk,ta amsa tayi gdy ta fita.
.
Tana dawowa kawai sai ta fada jkn Momy, tana magana a tsorace,"wayyo Momy motsi nake ji a cikin cikina,ke Mimi kodai yunwa ce... hannun Momy ta jawo ta aza a cikinta, mamaki qarara a fuskar Momy, tana cewa, "Mimi dama cikin ki bai zube ba ne,domin wannan cikin daganinsa yayi wata biyar,tashi muje asibiti. Haka kuwa akayi domin doctor ya gaya musu wannan cikin kadan ya rage ya cike wata biyar, sai dai da alama cikin ya zuba,ha kan yasa ya kwanta,amma yanzu komai zai zo normal inshaAllah,cike da farin ciki suka dawo gida. Nan take family kowa ya sani sai murna ake, akasin faruk da aka kira wayarsa, a kashe take,amma tuni abban Mimi ya sani,domin har ya kira ta yana taya ta murna. Zaune take tana shafar cikin ta wani irin farin ciki, ke ziyararta,tana cewa"Allah na godema, dakasa cikin nan bai zube ba, naso ace yaya, na nan, da yake ganin banida wani amfani,naga ya zaiyi,ya zaiji,me zai ce mun.
.
Bayan sati daya da faruwar haka. Mimi ce kwance abisa 3 seater,bangare su faruk tana bacci,umma ko tana yanka kankana,sallamar faruk taji,ta amsa sallamar ne cike da mamaki,umma sannu da aiki yauwa sannu....amma meyasa baka kira zaka dawo ba,Allah umma wayata ta fadi,yau sati daya kenan,ganin aiki yayi min yawa shiyasa ban yi lokacin sayen wata ba. Umma me za'ayi da wannan kankanar haka da yawa?kasan yau ne meeting.... eh shiyasa ma na dawo da wuri domin ina son in halar ci meeting din. My Mimi..... bacci take fa karka tashe ta, me yake damun Mimina wai duk ta rame...... har ka tambaya bayan kasan ciki ne da Ita,ciki Umma? dama bai zube ba?dan guntun tsaki umma tayi,sannan,tace "zafin zuciyar ka ai bazai bari ka fahimci ya zube ko bai zube ba,tunda ko duba ta bakayi ba,Allah umma a lisafina cikin bai wuce 3 month ba,Sam na manta yakai 4month har da sati koda muka zo amma don Allah umma ayi hkr,da kuskuren da nayi na rashin duba ta,mu dai fatan mu Allah ya sauke da lafiya, sassanyar ajiyar zuciya yayi,kafin yake cewa "Ameen umma. Kallon mimi yake cike da sha'awa taqara,haske,smooth, kyau,ga qirjinta da yaqara cika,sai wani irin abu yakeji.......umma ce ta katse shi,tana mai cewa,"ko kana bukatar abinci akawo ma?a qoshe nake umma' sai dai ko zuwa anjima.
.
Kowa ya hallara a gurin meeting Alhaji ya bude da addu'a, bayan haka suka fara tattauna wa akan lamurran family,ciki harda magana akan asa ranar auren Hafiz da Ali rana daya. Duk abin nan da ake faruk hankalinsa na kan Mimi, ya matsu a qare ya gana da Ita,domin ya fahimci,har yanzu fishi take dashi. Aiko ana gamawa ya riko hannuta da sauri,"Mimi pls kiyi hakuri da abinda nace miki ranar,wlh wasa nakey miki,asalima bako London naje ba....ok yanzu tunda kaji cewa cikin yana nan, shine zaka cemin wasa kake,bana son wani kwantar min hankali da zakayi,na riga da nasan cewa baka sona,sha'wa...no Mimi kar ki fadi haka,wallahi tuni na dawo gareki Mimi inasonki so na har abada,ai nasaba jin wannan yaya, sai ka zanxa wani salon. Mimi ba lallai bane ki iya ganin yadda nake sonki, ba lallai bane kisan yadda na dauke ki ba, ba lallai bane kiji yadda nake kewar ki ba,domin ta zuciyata ne Kadai zaki iya gani,pls Mimi ki duba min fa,tunda naje nake kiranki a waya, amma ba kya daga wayar,kinaso kicemin wannan duk don cikin ne?...... sai kawai kuka yaci karfinsa,saurin dago kanta tayi domin bata zaci abin zai ga kuka ba,sai taji gabaki daya ya bata tsusayi,"yaya ka daina kuka please,indai nice na hkr,rungume juna sukayi suna kuka,Mimi I love u,love u too,yayana, Tafi raf raf family ya dauka, har da su shewa,gaba ki daya sun manta a gaban family suke maganar,domin faruk bai ko bari aka fita ba ya riqo hannun Mimi.
.
Karfe shida na yamma ranar, Mimi ce ke waya da faruk,yana gaya mata anjima da karfe 8pm zasu fita,Ita ko sai tambayr sa tayi, zuwa ina kenan yaya?ki shirya kawai ko ma ina ne zaki gani,to Allah ya kaimu lokacin,Ameen,sannan suka katse waya. 8pm ta shirya tsaf shi kadai take jira,dakin Momy taje da sallamar ta, ta sameta tana addu'a zama tayi, tana jiran ta har ta qare,banyan ta qare ne ta juyo gareta, yadai har kinyi sallah kin shirya,?eh umma yanzu shi kadai nake jira bana son yazo ban shirya ba duk sai na kasa shiri cikin natsuwa,lallai kam haka yafi......sallamar faruk suka jiyo,Momy ce ta amsa sallamar, ya rissina ya gaisheta, lfya lau faruk....kinyi zaune kina kallonsa tashi ki dauko maya finki kutafi mana, tashi tayi ta dauko suka tafi. Tafe suke cikin mota sai kallon kallon suke wa junansu, faruk ne ya fara da cewa, my Mimi kinyi kyau sosai, sai kace amarya,yaya kenan kai kuma sai in kira ka da ango Kennan, domin kyan da kayi in ma akwai abinda yafi ango to ka ka kai,kamar kuwa kin sani domin yau angoncewa xanyi da kyakkyawar amarya ta Mimi. Ihm yaya dai shiyasa kace zamu wani gurin, au kina tunain zan iya hkr ne har muje London,ai nafayi qoqari gsky,murmushi tayi kafin take cewa,yaya amma wannan hanyar ta zuwa gidan kace ko?cewa zakiyi ta zuwa gidanmu ce,domin duk muka zo Nigeria nan zamu riqa sauka
.
Wani hadaden gida naga sun shiga iya haduwa gidan ya hadu,Mimi sai cewa take wow yaya amma anqara gyara gidan nan?a kwanakin nan nasa aka gyara shi, gida sai kace a qasar waje,cewar mimi,ya bazan gyara gidan haka ba tunda matata kyakkyawa ce kamar balarabiya, uhm yaya kenan, ka daina kuda ni haka da yawa, ai sai kasa kaina ya qara girma. Nan dai suka shiga daki, ya bude musu gasashiyar kaza da fresh milk da Hollandiya milk sunyi sanyi har sun gaji. Sannu a hankali take ci har ya gama ci bata gama ba, Mimi bazan iya hakr labulabun nan naki ba fa,jawo ta yayi jikinsa yana bata har sai da ta qoshi,daga nan aka janza salo,sai aikawa junan su sakwanni suke,daga gani sunyi missing din junansu sosai,mimi ce tayi karfin halin cewa lets go to the bed pls, nan suka kashe wuta,dole na fita na basu guri,na dai san an faranta ran juna. Basu suka koma gida ba sai 11pm. Sai da suka qara kwana biyu sannan,suka koma London,cike da kewar mutanen gida.
.
Akwna a tashi ba wuya a gurin Allah,yau cikin Mimi wata tara,haifuwa yau ko gobe, sai dai cikin yayi girma sosai,tafya ma da qyar take yinta. Kwance suke suna bacci wuraren karfe 12am a cikin baccinsu ne faruk yake jin wani irin nishi kamar a mafarki,koda ya farka baiga Mimi ba, ba shiri ya nufi toilet domin yana zaton can nishin ke fitowa,Mimi ya samu a durqushe riqe da qugu sai zabga salati take. Mimina meyasa baki tashe ni ba, yaya ka taimakamin zan mutu, bazaki mutuba Mimi, daure domin kingin tsirif ki haifu,rufe bakinsa ke da wuya,santalelen da ya fito, jawur dashi, sai dai da alama,akwai wani domin, Mimi bata daina nishi ba, "Mimi qara trying akwai wani tafe, subul kuwa kyakkyawa yarinya ta fado,murna a gurin faruk ba'a magana, sai sannu yake mata,hadi da godiya. Nan take ya shirya su tsaf da uwar har 'ya'yan,tea ya hada mata mai kauri tasha,sannan tayi feeding din yaran. Tun a wannan daren ya kira gida ya fadi,sai kiranta ake a na mata barka da ta sauka lfy. Sbd tsananin murna,Abban Mimi ji yayi kamar yayi tsuntsuwa yazo yaga jikokinsa.
.
Saida suka qara kwana biyu ya tabbatar da lafitlyarsu sannan suka dira Nigeria,murna a gun family ba'a magana,ga yaran akwai shiga rai'yan tubultubul dasu,kyawawa masu kama da iyayensu. Ranar suna yara sukaci,Muhammad Ammar, da Nana Fatima,wato sunan mahaifiyar faruk, ana kiranta da Islam. Bayan sunyi arba'in ne akayi bikin su Zainab da hafiz,Ali da zeenatu,anyi biki bidiri sosai abin ba'a cewa komai,su salim,Hashim,Yusuf sai casu ake,dama school ne yahana kuji su,yanzu kuma sun kammala. Da aka gama buki faruk ya kwashi matar sa da yaransa suka koma London. Bayan shekara biyu. Mimi ta fara zuwa school,da yake faruk ne yace sai yaransa,sunyi kwari zata fara zuwa.
.
Yau ranar weekend ranar da suka kebe domin wasa, a gurin basket ball suke ko wannensu ya yi shirin wasa,dasu har 'yayansu,ammar da Islam. Ball aka jefa bayan ta tsaya,sai suka cema ma yaran,duk Wanda yayi na daya da dauko ball za'a bashi ice cream,oya!one!two!!three!!! gooo!!!,aiko suka tafi da gudu,suko suna kiran sunan yaran, yadda zasu qarajin qarfin gudu, faruk shine mai ammar, Mimi ko Islam. Ammar!Islam!Ammar! Islam!Ammar!yee
ee! islaaam,da gudu ta fada jikin Mimi sai murna take tayi ta daya,1,0 kenan oya kusake zuwa muga wa zai na daya, faruk ne yayi magana tare da jefa ball,wannan karon Ammar ne yaci, faruk ya dauke shi sama, ya dawo dashi,Ashe hakan da aka yi masa ya birge Islam, abu ga yara, nima daddy amun irin na Ammar, a'a momyn ki zata miki,a'a fa banda haka yaya, kin taba ganin inda 'yan wani gd sukyi yima 'yan wani gd tawai,ni ba ruwana da haka kawai a mata, don kasan bazan iya irin yadda kayi ba shiyasa, tayi maganar a cikin shagwaba, tare da bubbuga qafafunta a kasa, Cike da sha'wa ya kalleta yana cewa "yara na kallonki,su suce me kenan,ai nima yarinyace, to naji, ya dauki Islam Itama ya mata,to saura ni,dry yake sosaimimi ki bar ma yara wannan,muje inmiki naki a daki. Shiga sukayi cikin gd suka ba,Celina yara wato mai kula da yaran.suko suka shiga daga ciki. Daga hannayen ki sama, amma fa ki rinste ido, ok,sai da ya cire kayan jikinsa gaba daya,sannan Ita ma yacire nata,ta bude idonta tana mai cewa, yaya ba haka nake nufi ba, ni haka nake nufi,rungume ta yayi tare da hade bakinsu wuri daya,suna masu shafar jikin juna ta koina,tsayuwar ta gagare su, suka fada saman gado tare da jaw bar go suka rufe jikinsu,nan suka,lula duniyar ma'aurata, Amma fa ni bangansu ba Asea ce tabani lbr,kar kuga laifi na. Bayan sunyi wanka ne, na koma leqawa na same su rungume da juna, faruk ke cewa, Mimi ke ta,dabance,domin a duk lokacin da nake kasancewa tare dake,na kan manta komai a duniyar nan,Nima yaya banajin akwai wani da namiji,da ya kaika,shiyasa ako wane lokaci kazo min da buqata, bana iya hanaka. Mimi ina sonki, yaya nima ina sonka.qara rungume juna sukayi, suna masu farin ciki da jin dadin zancen ko wannensu, tare da fatan Allah yasa su kasance tare har,Aljannah fiddausi. Ni A.y.s nace ameen.
.
ALHAMDULILLAH Na gode Allah da yabani ikon kawo qarshen wannan littafi lfy. Kuyi hkr da kurakuren da nayi, kuma ina godiya ga 'yanuwana, masoyana,da Abokaina. MashaAllah.
0 comments:
Post a Comment