ALWASHI Page 11-15
.
***Cikeda mamaki Hafsat ta kalli mami saboda jin abinda tafada,
"Kidaina mamaki Hafsat sannan kuma narokeki dan girman Allah kada ki k'i amsar bukatata domin yin hakan na iya zama dalilin faruwar abubuwa da dama ciki kuwa harda dawwamar bacin rai da bakin ciki acikin zuciyata..."
Sunkuyar da kai Hafsat tayi tai shiru takasa yin magana acikin zuciyarta kuwa tunani takeyi shin shi yaron mamin da take burin hadata dashi shine yaganta yake sonta ko kuwa kawai mamin ce keda burin yin hakan a matsayinta na mahaifiyarsa domin ita tunda take zuwa gidan bata taba ganin daya daga cikin yaran mamin ba kuma surayya kadai ta sani har suke yin waya da ita,
"Hafsat ya naji kinyi shiru? Kodai bakya son dan nawa?"
Muryar mami ta katse mata tunaninta da takeyi,
"Mami to ai bai taba ganina ba kuma nima ba taba ganinshi nayiba.."
Murmushi mami tayi,
"Hafsat kenan ni awurina duk wannan ba wani abu bane kuma abune mai sauki domin na isa da dana duk abinda nasashi baya k'in bin umarni na, matsalar dai kawai kece idan baiyi miki ba,ga hotonshi nan akafe abango ta bayanki, juya ki gani..."
Waiwayawa Hafsat tayi cikeda mamaki ta kalli wurin domin tunda take shigowa bedroom din mami Allah bai taba bata ikon damar kallon wurinba bare har taga hoton,
Hadadden saurayi tagani zaune akan kujerarshi ta office wanda abisa dukkan alamu acikin office dinshi akayi masa hoton,
Farine kyakkyawa mai daukar hankali wanda baduk macece zata ganshi takau da idonta a lokaci guda ba,fuskarshi zagaye take da saje mai hadeda kasumba,bakaken suit ne ajikinshi wadanda sukayi mutukar amsarshi domin sun sake haska farar fatarshi,
,
Manyan idanuwanshi farare tatass ta zubawa ido har ta gangaro izuwa kan dogon hancinshi mai tsini wanda yake daf da bakinshi dan madaidaici mai dauke da zagayayyun lips wadanda suka kasance jajaye jur,
Ita kanta bata san tsawon mintunan data dauka tana karewa halittar yusleem kallo ba,
"Masha Allah, tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu wanda ya kawata halitta da surar wannan bawan nashi.." Ta fadi hakan acikin zuciyarta wanda har lokacin takasa dauke idanuwanta daga kallon hoton,
"Hafsat..." Taji mami takira sunanta sai lokacin ta iya tunawa ma da ashe mamin na zaune wurin, cikin sauri ta dauke idonta daga kan hoton ta sunkuyar da kai cikeda jin kunya,
"Hafsat ko baiyi miki bane?"
Shiru Hafsat tayi bata amsaba tasake sunkuyar da kanta kasa,
Juyin duniya haka mami tayi tana tambayar hafsat amma taki amsawa tayi shiru,
Murmushi mami tayi,
"To Allah dai yasa hasashe na yazama gaskiya hafsat idan har kuwa hakan ya tabbata to nasan zanfi kowa farin ciki....."
Dan murmushi hafsat ta kuma yi cike da kunya,
"Insha Allah zanzo gidan gobe goben nan muyi maganar da umminki kafin asan ta inda za afara kuma"
Mami tafadi hakan cikin jin dadi, ita hafsat yanzu sai taji tana jin kunya da kuma nauyin mamin shiyasa taji duk zaman ta takura,
"Haba hafsat ai tsakaninmu babu yar surukunta, ki dauka cewa kece yata ba yusleem ba, ko aurenku ya tabbata karkiji kunyar sanar dani laifinsa matsawar yayi miki ba daidai ba.."
Shiru hafsat tayi takasa cewa komai,har mami takaraci maganarta ta gama bata iya daga ido ta kalleta ba daga karshe ma sai cewa tayi zata tafi duk kuwa da cewar ba wannan lokacin tayi niyyar tafiyar ba amma wannan maganar da sukayi da mamin itace ta tilasta mata barin gidan.
Ko drivern gidansu bata zauna zaman jiraba sai mami ce tasa drivern ta yakaita gida,
Hatta ummi saida tayi mamakin ganinta a lokacin saboda bata zaci zata dawo dawuri hakaba,
Tambayarta ummin taringa yi akan dalilin dawowarta da wuri haka bayan kuma ba haka tasaba dawowa ba idan taje,
"Hafsat ko unguwa hajiya siyaman zataje ne shiyasa kika dawo?"
"A'a Ummi babu inda zataje tana nan.."
"To meya faru?" Tasake tambayarta,
"Babu komai, tace zatazo wurinki gobe ma"
"Amma dai lafiya ko?"
"Ehh lafiya lau"
"To shikenan Allah yakaimu.."
Acikin zuciyarta ta amsa amin din bata bari ummin tajiba,
Ita kanta bazata iya fassara yanayin da zuciyarta ta karbi yusleem ba kawai dai tanajinta cikin nishadi wanda bata san dalili ba,
Daren ranar tayishi ne batare da tayi isasshen bacciba.
Washe gari da safe misalin karfe 11 daidai nasafe mami tayiwa gidan sammako lokacin Alhaji sa'id na nan ko fita baiyiba,
Jin zuwanta yasa Hafsat jin wata irin faduwar gaba duk sai taji jikinta yayi sanyi dan dakyar ma ta iya zuwa suka gaisa daga nan ta koma daki ta kule bayan ta gabatar mata da ruwa,
"Hajiya kubra yau dai zuwana yasha banban da wanda nakeyi ada domin dalilin zuwana yau shine neman auren yata nazo.. Wato Hafsat"
Murmushi hajiya kubra tayi ta kalli mami,
"To ai bakiyi min gwari gwari yanda zan ganeba"
"Kamar yadda nafada miki nazone in nemarwa dana yusleem auren yarki Hafsat idan har babu alkawarin wani akanta domin wallahi ina mutukar kaunarta kuma ina son inhada jini da ku.."
Murmushi hajiya kubra tayi,
.
"To ai kema yarkice, amma yanzu abinda nake ganin za ayi shine abbanta yana nan bai fitaba bari inje insanar masa"
"To shikenan"
Tashi hajiya kubra tayi tafita zuwa part din Alhaji sa'id mintuna Kadan sai gata tadawo,
"Hajiya to bismillah zo mu karasa wurin alhajin"
Tare suka shiga suka iskeshi zaune kan kujera hannunsa rikeda jaridar weekly trust,
Gaisawa sukayi da mami tayi masa bayani kamar yanda tayiwa Ummi nan Alhaji sa'id yace babu komai indai har Hafsat din ta amince domin ba za ayi mata doleba kawai abinda za ayi shine suje su daidaita ita da yaron,
Cikeda farin ciki mami tayiwa Alhaji sa'id godiya ta mike tafita acikin ranta tana ganin yanzu saura abu daya yarage shine tashawo kan yusleem....
*
***Falon hajiya kubra mami takoma tazauna tana jiranta zuciyarta cikeda farin ciki wanda kana iya gane hakan karara idan har ka kalli kan fuskarta,
Tana nan zaune har ummi tafito daga sashen alhaji nan sukayi sallama ta rakata tatafi, saida Hafsat taji fitar mami sannan tafito daga daki tazauna akusa da ummin tana dan kallonta domin jin karin bayani amma kuma sai dai kunya takeji,
.
"Mamin naku tatafi yanzu nakaita wurin abbanku sunyi magana akanki keda danta, abbanki yace yaron yazo ku daidaita mutukar kun amince kuna son juna to shi bashida wata matsala..."
Shiru Hafsat tayi ta dan sunkuyar da kanta kasa tana murmushi,
"Nida naso kema kiyi karatu kamar yar uwarki amal to amma kin san kowa da yadda Allah yake tsara masa rayuwarsa.., sai dai muyi fatan Allah yasa hakan shine yafi alkhairi"
Har dai ummi tayi maganarta tagama Hafsat bata iya cemata ko uffan ba.
Cikin farin ciki marar misaltuwa mami taje gida tana shiga ta nemi wurin zama ta zauna tafara lissafin abubuwan da ya kamata ta siyo ko ta hado domin bata bukatar bikin nan yawuce watanni biyu masu zuwa kacal,
Paper da pen ta dauko ta zauna tana rubuta abubuwan da takeso tasiyo da adadinsu,
Yusleem ne yaturo kofar falon ya shigo yana sanye da farar riga jersey da blue din trouser hannunshi rike da key din motarshi,
A kusa da mamin ya zauna ya jingina kamar yadda yasaba domin shi haka dabi'arshi take kamar wani mai sarauta akoda yaushe cikin iko yake,
"Mami ina kwana..?"
Dagowa tayi ta kalleshi bayan tacire farin medical glass din dake kan fuskarta,
"Sai yanzu katashi ko? In ba hakaba yaushe za akira karfe 12 da safiya..." Takarasa maganar tana murmushi,
"To ai mami weekend ne.."
"Ehhh tunda weekend ne sannan kuma kai kadaine baka da mata ai dole kayita bacci har rana ta fito"
Murmushi yayi yana shafa kasumbar dake fuskarshi,
"Mami yunwa nakeji wallahi dan yunwar ce ma tafito dani daga gida"
"To me zakaci?"
"Abani tea banda bread, soyayyiyar agada da dankali amma banda egg"
Murmushi Mami tayi tana kallonsa,
.
"Ai matarka zata sha tsaraba kai idan katashi karyawa baka karyawa da abu guda biyu kuma abin haushinma idan anbaka ba na kirki zakaci ba"
"Mami wallahi nima ina son infara cin abinci dayawa amma narasa meyasa bana iyawa, but ina tunanin nanda 2 weeks zanje london so zan biya ta chairo naga dr dina"
"Da dai yafi maka amma mutum yarinka cin abinci kamar wani karamin yaro..."
Bai kara maganaba yaciro wayarshi daga aljihu yasoma latsawa, mikewa mami tayi tafita takira kuku ta fada masa aikin da zaiyi tadawo wurin yusleem tazauna,
"Wai mami rubuce rubucen me kikeyi ne haka?"
"Ai zan fada maka, kwantar da hankalinka.."
Murmushi yayi yatashi yakoma kan 3 sitter ya kwanta,
Mintuna kadan kuku yashigo dauke da faranti wanda ya dorowa yusleem kayan breakfast din akai,
Akan center table ya dora mishi yajuya yafita, tashi yusleem yayi yaja table din gabanshi ya hada tea yasoma karyawa yanayi yana kallon mami wacce ta dukufa akan rubutun da takeyi,
Saida ya kammala sannan mami ta dago ta kalleshi,
"Yusleem ya maganar auren da nace ka nemo, har yanzu baka samo yarinyar da tayi maka ba ko kuma yaya?"
Dama tun shigowarshi saida jikinsa yabashi maganar aure mami zatayi masa,
Sai da yadan ja lokaci sannan yace,
"Mami meya faru kuma?"
"Babu abinda yafaru inaso ne inji idan har kasamo sai afara maganar auren idan kuma baka samoba to ni nasamo maka..."
Sunkuyar dakanshi yayi yana nazari batare da yace komai ba, tabbas shikam yanada farin jinin yanmata domin babu wahala yanzun nan budurwa tace tana sonshi sai dai kuma sam shi baya bukatar auren ne,
.
"Yanaji kayi shiru?"
"To mami ai nazaci mun gama maganar nan"
"Dawa? A'a bamu gamaba, nidai ina son kasani nasamo maka yarinyar da zaka aura nanda watanni biyu dan haka saika fara dukkan shirye shiryen da yadace amma wannan karon kasani banyi maka aure dan ka sakar musu yarinya ba,
Sannan kuma inaso ka sama mana visa mutafi umarah domin muje inyi maka addu'a akan Allah yarabaka da wannan aljanar da take tareda kai kuma yasa ayi auren nan cikin sa'a yasaka albarka aciki"
Tunda mami tafara maganar baice uffan ba har tagama,
"Ina fata kaji maganganun da nayi maka kuma sun shiga cikin kunnenka?"
"Ehh naji"
"Yawwa to Allah yayi maka albarka Allah yasa ayi cikin nasara"
Bai amsaba yatashi yafita mami tarakashi da ido,
Kamar yadda mamin tafada acikin lokaci kankani yasamo musu visa suka tafi umarah addu'a sosai mami tayi masa kan auren da zatayi masa bayan sun kammala umarah ne yawuce London yabarta anan bayan tafiyarshi da kwana uku itama tawuce dubai domin karasa hada lefenshi da siyan sauran abubuwan da za ayi amfani dasu abikin dan hatta kayan da amarya zata saka duk saida tasai mata,
.
Saida ta kammala siyayyarta tsaf sannan tadawo Nigeria shikuwa yusleem har lokacin bai dawoba, dawowarta babu jimawa tatura wakilan yusleem sukaje nemar masa auren Hafsat agidan Alhaji sa'id wanda basu tahoba saida ranarsu, domin Alhaji sa'id ya yanke ranar aure saboda ya fahimci cewar Hafsat din tana son yusleem,
Wannan abu ba karamin dadi yayiwa mami ba dan tsananin dadi aranar da daddare taje gidan tayi godiya,
Aminanta da kawayenta ta gayyato suka kai lefen Hafsat wanda tsayawa fadar kayan ciki bata lokaci ne, domin mami ta yiwa Hafsat lefe na alfarma irin lefen da tunda yusleem yake aure ba ataba yin irinshi ba,
Yanzu gidajen guda biyu ko ina shirin biki sukeyi gadan gadan, Alhaji sa'id ya sakarwa ummi kudi domin yiwa yartata siyayya, ita dai Hafsat bata katabus saboda har yau bataga angonba kuma shima bai gantaba tana jin tsoron kar yaganta ya rainata yace batayi masa ba domin tasan dama auren hadin mami ne,amma shikam bata tunanin akwai wata ya macen da zata ce baiyi mataba,
.
Yusleem kuwa tunda ya Lula yatafi bai dawoba gyaran gidanshi ma wanda za ayi sai yaronshi na office yasa yatsaya akai akayi aka gama aka gyara gidan tsafa aka sake fenti,
Saida biki yarage saura kwana takwas sannan yadawo lokacin hatta kannenshi su Abdul da surayya har sun zazzo daga makaranta, mami taso tayi masa fada amma kuma dayake acikin farin ciki take sai ta shareshi taci gaba da harkokinta,
Surayya kam kanwar yusleem tattarawa tayi takoma gidansu Hafsat saboda acewarta ita abangaren amarya take ba bangaren ango ba, Hafsat ba karamin dadi tajiba domin dama ita kadaici kwal agidan take harkokinta domin Alhaji sa'id bai bar amal tazo ba duk da tayi niyyar zuwa amma yahana,
Surayya ce taraka Hafsat akayi mata komai kama tun daga kunshi gyaran jiki da gyaran kai wanda duk mami ce tadauki nauyin yin hakan,
.
Ana igobe daurin aure yusleem yaje gidansu Hafsat din wanda wannan dinma mamice ta tilastashi, kamar zaiyi kuka yashirya yatafi bayan sallar isha,
Surayya yayiwa waya tana dauka taji yace,
"Ke turo min wannan yarinyar"
Sarai surayya tagane abinda yake nufi amma sai tayi fuska tace,
"Uhm yaya wafa?"
"Oho miki" yafadi tareda katse wayar,
Kallon Hafsat tayi tana murmushi,
"Angonki ne yazo yana waje yana jiranki"
Saida gaban hafsa yafadi saboda jin abinda surayya tace,hijabi tadauka ta kalli surayya,
"Zo ki rakani dan Allah"
"Zan dai kaiki amma ina zuwa dawowa zanyi"
"Nayarda"
Fita sukayi gaba dayansu, afalo suka iske su ummi ita da jama'arta wadanda sukazo suna yan aikace aikace,
.
Kanshi yana durkushe akasa yana latsa wayarsa dan haka ko fitowarsu bai ganiba bare yaga zuwansu, surayya ce ta kwankwasa masa glass din dake saitinshi hakan yasashi yin kasa da glass din yana kallonta, gaban Hafsat ne yashiga dukan tara tara haka kawai domin gani tayi yusleem yafi kyau afili kuma tabbas shine mutumin da yake taimaka musu lokacin da tana gidan marayu domin yataba zuwar musu sau daya sun ganshi,
"Ina wuni.." Hafsat tace dashi tana kallon kasa,
Ko kallonta baiyiba ya amsa da "lafiya"
Daga haka babu wanda yakara magana acikinsu ganin haka yasa surayya tajuya zata tafi dominated tabasu wuri nan yadakatar da ita yadauko rafar yan dubu dubu guda daya ya mika mata yaja motarshi yayi gaba,
Hafsat ji tayi ko ajikinta balle abin ya dameta,
Washe gari aka daura auren Hafsat da yusleem da misalin karfe 2 narana akan sadaki naira dubu hamsin.
*
***Aranar da aka daura auren aranar alhaji sa'id yace aje akai Hafsat gidanta duk da hajiya kubra bata so hakaba domin ita taso ace sai washe gari za akaita amma tunda ga abinda alhaji sa'id yace dole babu yadda ta iya dan haka aka fara shirin kai amarya dakinta,
.
K'arfe 9 daidai aka fito da Hafsat din daga sashen alhaji sa'id bayan ya kammala yimata nasihar da ta dace duk wani uba yayiwa'yarsa a lokacin da za akaita gidan miji, haka itama hajiya kubra ba abarta abaya ba wurin yiwa Hafsat fada akan tabi mijinta kuma ta kyautata masa,
Inbanda kuka babu abinda Hafsat keyi domin tasan su hajiya kubra sunyi mutukar kokari akanta kuma sun taka muhimmiyar rawa acikin rayuwarta wanda har abada bazata manceba kuma bata da abinda zata iya biyansu da shi,
.
Wata tsadaddiyar mota ta alfarma kirar Lexus new series 2017 aka bude mata tashiga, nan kannen hajiya kubra suka sakata atsakiya yayinda surayya kanwar yusleem tashiga gaban motar,
Direct gidan mami aka wuce da ita inda mamin nacan ita da jama'arta suna zaman jiran zuwansu,
Yanayin farin cikin da mami ke ciki abin bazai misaltu ba domin kana ganinta zaka gane irin dunbin farin cikin da take ciki,
Har tsakiyar bedroom dinta aka shigar da Hafsat wacce ke tukunkune cikin wani babban mayafi dark blue kalar leshin dake jikinta,
Rungumeta mami tayi tana fara'a,
"Barka da zuwa cikin zuri'ata 'yata,ubangiji Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina da duk wani sharri daga gareku, Allah yabaku zuri'a dayyibah, nidama tun can a matsayin 'ya na daukeki kuma yanzun ma kina nan ahaka baki sauya ba, insha Allah zamu rikeki amana"
Jin abinda mami tafada yasa kawayenta dake baibaye da ita sakin guda,basufi minti talatin agidan mami ba aka wuce da Hafsat gidanta wanda ke can wata unguwa da ake kira da babbar inuwa domin gaba daya mazauna unguwar shaharrun mutane ne wadanda sukeda hannu da shuni,
Shi kanshi yusleem fadin girman gidansa da tsarinsa abune mai wahala domin gidan yatsaru iya tsaruwa,
Cikin babban bedroom dinta aka shigar da ita ta zauna akan gefen makeken gadonta samfurin Italy,
Saida yan Kawo amarya suka fita sannan Amina kawarta da surayya suka shiga cikin dakin,
"Amarya kinsha kamshi, nidai bari inje intafi.." Inji Amina,
Dago jajayen idanuwanta Hafsat tayi ta kalleta,
"Haba Amina bazaki bari angwayen suzo ba?"
Dariya surayya tayi tareda bararrajewa akan gadon,
"Waye zai Kawo miki angwaye? Indai yaya yusleem ne Allah shi kadai zai zo gidan nan garama kibarmu muje mu tafi, nidai dama kin san gobe da sassafe zanyi miki asubanci..."
Jin abinda surayya tace yasa Amina tashi tsaye,
.
"To shikenan bari intafi, Hafsat sai nadawo ganin gida lokacin kin dawo cikin nutauwarki domin nasan yanzu bakya tareda ita..."
"To Amina nagode, Allah yabar zumunci, nagode"
Tashi surayya tayi tabi bayan Amina suka fita tare,
Tsuru Hafsat tayi tana bin dakin da kallo wanda yasha furniture's na alfarma kalarsu dark purple, duk tsoro yabi ya cikata saboda babu motsin komai agidan, ta wuri daya hankalinta ya kwanta shine tasan akwai masu gadi acikin gidan wanda yanzu haka suna can gate suna aikinsu,nan tazauna taci gaba da zuba idon ta Inda zataga shigowar angonta.
K'arfe 10:30 yusleem yashiga gidan mami kasancewar yan biki suna nan basu tattafi ba yasa gidan inbanda hayaniya babu abinda kakeji kamar dare baiyi ba,
Fitowa mami tayi wurinshi ta tsaya tana kallonsa, gaba daya ta fahimci bashida wata walwala,
"Yusleem..." Ta kira sunanshi tana kallonsa,
"Na'am.."
"Kasan abinda nakeso dakai? Na hadaka da girman Allah yusleem ka rike Hafsat amana, dan Allah karka cutar da ita, sannan ka taimaka ka rufa min asiri karka sakar musu 'ya, yusleem idan ka aikata daya daga cikin wadannan wallahi bazan yafe makaba sannan ka nemi wata uwar amma baniba, Allah yayi maka albarka ya baka zuri'a tagari"
Hannayenshi duka suna cikin wandon farar shaddar dake jikinsa yana tsaye yana jin mami har ta kammala,
Gyada kai yayi batare da yace komai ba ya sunkuyar da kai,
"To kaje katafi mana"
"Ehh yanzu zan tafi, inasu Abdul suke? Ko shi ko khalifa wani yazo muje yayi dropping dina saboda dama shu'aibu yaron office dinane yakawo ni kuma yawuce"
"To bari nakira maka daya daga cikinsu, ina zuwa"
Juyawa mami tayi ta nufi sashen samarin,da khalifa tafara yin arba dan haka shi takirawo ta nuna masa yusleem a inda yake tsaye ya cire hularshi yana lanlankwasa ta,
Batare data koma wurinshi ba tawuce zuwa ciki shikuma khalifa ya nufi wurinsa daga nan wurin da aka tanada domin adana motoci sukaje khalifa yadauko guda daya yusleem yabude yashiga suka fita daga cikin gidan,
"Yaya ka siyi yan abubuwanne?"
Kallon khalifa yusleem yayi,
"Mefa?"
"Wai da yaya ina nufin dan nama haka da sauransu.."
"Kaima yanzu bakada kunya kamar Abdul ko?" Yafada yana kallon titi,
"A'a yaya bahaka bane,nayi tunanin ko kamanta ne shine natuna maka"
Bai sake cemasa uffan ba har sukaje gidan nan yabude kofa yafita ya nufi ciki yana takawa ahankali.....
*
***Ahankali yaci gaba da takawa yana tafiya tamkar wani marar lafiya ko kuma wanda yake jin tausayin kasar,
Hularshi yatura baya zuwa keyarshi ya zuba hannuwanshi acikin aljihun wandonshi domin wani dan dari dari yakeji,
Babban falon dake girke atsakiyar part din guda biyu yabude yashiga, hanyar da zata sadashi da bedrooms din Hafsat yabi har ya isa ga dakin da take ciki,tana kishingide ta dan fara gyangyadi amma ba bacci takeyi ba,
Ahankali yatura kofar dakin yashiga, daga bakin kofa ya tsaya bayan yasake zuba hannuwanshi acikin aljihun wandonshi,
Dan gyaran murya yayi kadan wanda hakan yayi sanadiyyar bude idon Hafsa ta tashi zaune da hanzari,
.
"Zo...." Shine kawai abinda yace da ita cikin sanyayyiyar muryarshi yajuya yafara tafiya, tashi tayi tasauka daga kan gadon tabi bayanshi,
Saboda irin yadda yake daga kafa dakyar yana tafiya ahankali yasa harta cimmashi awani dan madaidaicin corridor, cikin falonta suka shiga,
Kan dining ya nuna mata,
"Ga abinci can idan kina jin yunwa.."
Daga haka bai sake cewa komai ba yajuya yafita ya nufi part dinshi,
Cikeda mamaki Hafsat take binshi da kallo, lallai wannan yusleem din ba kanwar lasa bane yanzu dama akan kawai zai nuna mata abinci ne yasa yatasota?
Kan dining table din takarasa, bakaken ledodi ne cikeda fruits daya ledar kuma kaji ne gasassu guda uku sai juice da fresh milk,
.
Dan yunwa kam tabbas tana jinta domin rabonta da cin abinci tun lokacin da aka fara hidimar bikin nan bata iya zama taci abinci ta koshi ba,
Zama tayi ta bude ledar tafara yagar kazar tana ci saida taji ta koshi sannan ta mayar ta rufe ta tashi,
Bedroom dinta takoma tashiga bathroom ta wanke hannunta da bakinta tadawo ta kwanta, Sam bata kara jin duriyar yusleem ba har asuba tayi gari ya waye,
Wanka tayi ta shirya tayi kwalliya tasaka wani jan Swiss material,
Fita tayi zuwa falo tana bin ko ina da kallo domin dukiyar da aka zuba afalon da shi kansa tsarin falon ba kadan bane,
Haka taci gaba da zama shiru har surayya tazo, shigowa tayi tana dauketa kulolin abinci,
"Amarya bakya laifi.." Surayya tafada cikeda tsokana,
"Ni dan Allah zubo min abincin nan inci yunwa nakeji"
"Ai dole kiji yunwa amaryar mu, yanzu kuwa zan Kawo miki.."
Kitchen ta shiga ta dauko filet tazubo mata wainar shinkafa da miyar agushi wacce taji kaji domin inbanda kamshi babu abinda takeyi,
.
"Ga abinci, ina yayan? Ko bai tashiba?"
Shiru Hafsat tayi saboda ita bata sanma me zatace ba domin rabonta da ganinshi tun jiya da daddare,
"Duk yunwar ce ne ta hanaki magana?"
Murmushi Hafsat tayi ta gutsuri wainar tafara aikawa cikinta, kan dining table surayya takoma taje ta kinkimo ledar kajin da yusleem yakawowa Hafsat jiya,
"Ai wannan baku ci bama, kun tsaya jin kunyar juna ko? To ni bari inci"
Hafsat najinta bata tankaba domin ita yusleem yayi bala'in daure mata kai saboda ko atarihi bata taba jin angon da yayiwa amaryarshi hakaba, ace kazar ma bata da darajar da zai dauka yakai mata har sai ya kirata tazo ta dauka da kanta,
.
Abincinta taci ta koshi ita kuma surayya tana faman yagar kazar da ta rage jiya, bayan sun gama ne surayya tajata,
"Zo muje kiga sauran bedrooms din"
Fita sukayi daga falonta suka shiga corridor din da zai sadaka da dakunan baccinta wadanda suke guda biyu ajere sai can gaba dasu daga karshe wata kofa ce itama daban, bayan sun gama dudduba dakunan ne suka shiga wannan kofar, wani lafiyayyen falo Hafsat tagani mai mutukar kyau wanda yasha kaya masu tsada sannan akwai wata babbar kofa wacce tafita tawaje har zuwa kan wata katuwar balcony,
Coffee & milk colour ne gaba dayanshi sai wani kamshi yake na musamman,
Zama surayya tayi acikin daya daga cikin kujerun falon,
"Wash kafata, kinga bedroom din can leka kigani saboda wallahi nikam nagaji.."
.
Batare da tunanin komai ba Hafsat ta nufi bedroom din ta murda kofar ta shiga, dakine babba wanda girmansa zaiyi girman falo, wani babban royal bed ne agirke aciki sai kamfacecen mudubi da sauran kayayyaki, kamar ance ta kalli gefenta tana kallon wurin taga wata babbar kujera mai kamada dan karamin gado, yusleem ne kwance akai ya rungume pillow akirjinsa idanuwansa arufe abisa dukkan alamu bacci yake yi,
Tafi minti biyu tana kallonshi kafin tajuya zata fita harta bude kofar taji maganarshi cikin muryarshi mai mutukar sanyi da zaki,
"Zo nan..."
Cikin tsoro ta waiwaya ta kalleshi, bude idanuwanshi yayi yana kallon sama bai kalleta ba,
Mayar da kofar tayi ta rufe takarasa inda yake,
"Gani.."
"Menene ya kawoki?"
"Babu komai.."
Shiru taji yayi baiyi magana ba sannan har lokacin bai daga ido ya kalleta ba maimakon hakama sai yajuyar da kanshi da yayi yana kallon wani wuri,
"Ina kwana..?" Tace dashi saboda tunawar da tayi bata gaidashi ba,
.
"Lafiya.." Taji ya amsa,
Tana nan tsaye shiru bai sake yimata magana ba dan haka tajuya tafita,
Gani tayi surayya bata inda tatafi tabarta, wucewa tayi takoma part dinta acan ta iske surayya ta kunna makekiyar tv din dake manne abangon falon ta kamo tashar zee world,
Ganinta yasa surayya fara yin dariya kasa kasa,
"Amarya da alama dai jiya yaya bai gayyaceki dakin nashi ba shiyasa har nakaiki baki san can bane"
Zama Hafsat tayi tana yamutsa fuska,
"Dama kin san dakinsa ne shine kika ce inshiga ko?"
Dariya surayya tayi,
"To ba gashi kinyi gaisuwar safe ba.."
.
Kyaleta Hafsat tayi batace komai ba amma yanzu ta fahimci miskilin mutum Allah ya hadata zama dashi,
Haka suka cigaba da zama itada surayya har yan uwan hajiya kubra suka zo suka tafi suna tafiya yan uwan mami da kawayenta suma suka zo, duk wanda yazo gidan sai yasa albarka kuma sai yaji yayi sha'awarsa domin yayi sosai, amma wasu daga cikin kawayen mami da sukazo suka ga gida sannan suka ga Hafsat saida tausayinta yakamasu domin sun san itama kwana nawane yusleem zai tarkatata yakorata da saki dai dai dai dai har uku.
Har dare surayya tana gidan sai bayan sallar isha dasu khalifa suka zo tace zata bisu tatafi,
Hafsat kallon samarin tayi wato Abdul da khalifa duk da bata taba ganinsuba amma tasan dai kannen yusleem ne domin ga kama nan sai dai duk cikinsu shine fari domin har surayya batafi Hafsat din fariba shikuwa yusleem farine sol,
"Kinga kannen yaya, yakika gansu? Sunfishi kyau ko?"
Murmushi Hafsat tayi, "ke kika sani"
Gaisawa sukayi daga nan sukai mata sallama suka tafi,
Tunda suka tafi kuma tazauna shiru ita kadai daga karshema taji tsoro yafara shigarta dan haka ta tattara takoma bedroom dinta tayi shirin bacci ta kwanta.
.
Tun daga wannan ranar bata sake saka yusleem acikin idonta ba,kullum tareda surayya suke wuni har dare, da haka har tayi sati daya agidan,
Rabonta da ganin yusleem kuwa tun ranar da surayya tazo last wanda yashigo falon yace mata gobe kukun da yasamo mata zai fara zuwa tace a'a zata rinka girkinta da kanta, juyawa yayi gurin surayya tatashi ya maida ta gida, tun daga ranar Hafsa bata kara ganinshi ba gashi yanzu surayya bata nan sati biyu kenan da tafiyarta Kaduna gidan kanwar mami,
Haka take wuni ita kadai babu abokin hira, bata san fitar yusleem ba bare tasan dawowarsa.
Ranar alhamis da safe misalin karfe 11 saiga mami tazo gidan,
Da murna Hafsat ta karbeta, bayan sun gaisa mamin ke tambayarta yusleem din tashi tayi tafita tace bari ta kirashi,
Faduwa gabanta yafara yi lokacin data doshi dakin nasa, ahankali ta tura ta shiga, tayi sa'a kuwa yana nan,
Yana kan gado akwance yana bacci,
"Yaya... Yaya.." Tafara kiranshi, bude idonshi yayi, kallo daya yayi mata ya maida idanuwanshi ya rufe,cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadi yace,
"Menene?,idan ina bacci ba a tashina"
"Mami ce tazo shine tace inkira ka,amma kayi hakuri"
Ganin bashida niyyar amsa mata yasata juyawa zata fita, har takai bakin kofa taji muryarsa,
"Zo.." Komawa tayi wurinshi,
"Bude drewar dinnan ki miko min t shirt dina"
.
Budewa drewar din tayi ta dauko masa t shirt guda daya ja ta mika masa,
"Ajiye anan"
Ajiyewa tayi ta juya zata fita,
"Kinga..."
Dawowa tasake yi,
"Kin iya dafa tea?"
"Ehh na iya"
"Ki dafa min, kicewa mami ina zuwa"
Da "to" ta amsa tajuya tafita tana mamakinshi acikin ranta domin sam bashida alkibla tarasa gane inda yasaka gaba......
*
***Tagumi Hafsat tayi tai shiru tama rasa abin cewa domin bata san ta inda zata faraba,
"Baiwar Allah karki tashi hankalinki, nidai kawai abinda nakeso kisani shine yaya yusleem fa ba dutse bane mutum ne dan haka duk taurin kansa wata rana dole ya bukaci mace, dan haka daurewa zakiyi ki zage kiyita shisshige masa har yazo hannu kin gane ai?
'Yar rangwadar nan, kwalliyar nan, tsabtar nan..." Surayya tafada tana dariya,
Kallonta Hafsat tayi idanuwanta har sunyi ja,
"Surayya kenan da alama baki gama fahimtar yayan naki ba, yaushe ma ya zauna agidan bare har insamu damar yi masa wadannan abubuwan? Kedai kawai Allah yabani mafita"
"Amin, zaima baki cikin ikonsa"
Haka suka cigaba da tattauna maganar har tsawon wani lokaci,yauma kamar koda yaushe saida da daddare sannan surayya taja motarta ta tafi,
.
Tafiyarta yasa Hafsat jin gidan yayi mata tsittt, part din yusleem ta shiga baya cikin falon dan haka ta nufi bedroom dinshi nan dinma baya ciki, har zata fita tajiyo motsin ruwa acikin toilet alamun wanka yake nan tajuya tafita,
Bata kara sashi a idonta ba tun daga ranar,dan haka kullum wunin kadaici takeyi wannan dalilin ne yasa tayiwa Ummi waya tace a Kawo mata keken sakarta domin ko babu komai zai rinka dan debe mata kewa idan babu abinda takeyi sai tarinka hawa tanayi,
Washe gari hajiya kubra taje gidan takai mata keken da sauran kayan da zatayi amfani dasu wurin sakar, wannan shine karo nafarko da ummin taje gidan nata shiyasa murnarta takasa boyuwa,
Ita ason ranta ma ummin ta zauna ta wuni amma fur taki ko minti talatin batayi ba tatashi zata tafi,
Bin bayanta Hafsat tayi ta rakata anan hajiya kubran ke fada mata cewar ai yusleem sau biyu yana zuwa gida gaishesu bayan bikin, mamaki ne ya kama hafsa saboda bata zaci zai iya zuwaba duk da tafi zaton cewar mami ce zata tilasta shi yaje, sallama sukayi da ummin tatafi ita kuma takoma cikin gida.
.
Samun keken sakar nan akusa da ita shine dalilinta yanzu na rage zaman tunani duk da wani lokacin tana ganin anya kuwa rayuwarsu ita da yusleem zata yiyu ahaka? A matsayinsu na mata da miji ace sai suyi kwana 3 basu ga junaba, sannan bai damu da yaci abincinta ba balle har magana ta shiga tsakaninsu,
Gama wannan tunanin keda wuya ta mike ta nufi falonshi, baya ciki dan haka takarasa dakin baccinsa can dinma baya nan amma ga laptop dinshi nan a ajiye akan gado, karasawa tayi ta dauke laptop din ta gyara gadon daga nan ta zarce da gyara dakin gaba daya,
Bathroom tashiga nan taga ya jika kananan kayanshi acikin bocket da dukkan alamu so yake su jiku yasa acikin washing machine yawanke domin tasan bazai taba yin wanki da kansa ba tunda itama da ba kowan kowaba an ajiye mata injin wankin sai dai ita bata ma fiya amfani dashiba tafi ganewa tayi abinta da kanta,
Tsayawa tayi ta wanke masa kayan tass tadauka tafita ta shanya, tana cikin shanyawa yadawo yana sanye da kananan kaya jeans da t shirt,
Binshi cikin falon tayi bayan ta kammala shanyar kayan,
"Sannu da zuwa..."
"Yawwa..." Ya amsa mata aciki ciki daga nan bai kara koda kallon bangaren da takeba bare tasa ran zaiyi mata sannu na aikin da tayi masa,dan haka tawuce takoma part dinta,
Wadannan abubuwan dake faruwa sune suka hanata bacci adaren yau har misalin karfe daya idonta biyu, tanata juyi tajiyo kamar alamun tafiya atsakar gida a tsorace ta tashi taje gaban window ta daga labule tafara lekawa ahankali, kasancewar tsakar gidan akwai haske tal kamar rana shiyasa tasamu damar hango yusleem din wanda ke kokarin bude kofar motarshi,
"Ina yaya yusleem zaije acikin daren nan?" Ta tambayi kanta,
.
Kafin ta iya bawa kanta amsa tuni har yashiga motar mai gadi ya bude masa yafice, ita tsoro ne ma ya kamata domin duk atunaninta agidan mami ne wani abu yafaru nan takoma ta zauna jugum tanata nazari amma motsi kadan sai tatashi ta leka ko yadawo amma shiru,
Haka takasa bacci sai sake sake da haka har asubah tayi a lokacin ne taji dawowarshi da kamar taje wurinshi taji abinda yafaru sai dai tafasa,alwala taje ta dauro tazo ta tada salla.
Misalin karfe 8 tashiga falonshi bayan taci kwalliya cikin wata dark purple din shadda,
Kwance ta sameshi yana bacci akan doguwar kujera yana sanye da farar t shirt da bakin boxer, karasawa dakinshi tayi ta gyara masa tafito, lokacin da ta fito kuma yana zaune yana danna wayarshi, gaisheshi tayi ya amsa daga nan yaci gaba da abinda yake yi, jin baice mata komai ba yasata fita takoma falonta taci gaba da harkokinta,
Tana kan kekenta tana karasa hada rigar data fara jiya taji sallamar Amina kawarta, da murna ta tari aminan wacce ke daga kafa dakyar domin cikinta yadan fara tsufa,
Ba karamin dadin ganin aminan tajiba nan suka baje a falonta suka hau hirar yaushe gamo, wuni cur Amina tayi mata sai yamma ta tafi,
Haka taci gaba da zaman kadaici agidan domin surayya ma takoma makaranta kuma bazata sake dawowa ba har saita kammala, yau watanta biyu da wani abu agidan kuma tunda tazo bata taba fitaba shiyasa yau ta kuduri niyyar tambayarshi zuwa ganin gida,
.
Yana kokarin fita tayi gaggawar tsayar dashi, tsayawa yayi batare da yajiyo ba,
"Yaya dama yau ina son zuwa gidanmu ne"
"Allah kiyaye hanya, idan kin shirya akwai driver"
Daga haka yayi gaba abinshi, shiryawa taje tayi tafito tana dauke da rigunan jariran da ta saka wanda zata tafi dasu takaiwa Ummi domin asayar mata,
Kamar yadda yusleem yace haka ta tarar da driver yana zaman jiranta nan ya dauketa yakaita gida, murna wurin hajiya kubra abin ba acewa komai nan tashiga yin nan nan da ita, Hafsat ba ita tabaro gidanba sai dare domin saida tajira alhaji sa'id yadawo suka gaisa,
Daren yauma kamar rannan kasa bacci tayi can taji fitar yusleem daga gidan agogo ta kalla karfe 2 saura na dare,
"To wai shi wannan ina yake zuwa cikin talatainin dare haka?"
.
Sake saken zuci tayita yi har saida asuba takawo kai, awannan lokacin ne taji dawowarsa azamar sauka daga kan gadonta tayi tanufi part dinshi da sauri domin tana son taga awanne yanayi yake,
Acikin falonshi ta buya a bayan labule, ahankali taji ya bude kofa yashigo, lekashi tayi nan taganshi acikin nutsuwarshi yake ita tayi zaton zata ganshi cikin maye ko makamancin haka, zama yayi ya bude wani dan karamin akwati nan taga kudi fall kuma duk daloli ne ba naira ba,
Mayarwa yayi ya rufe ya tashi yashiga bedroom dinshi, sadadadawa tayi tafita takoma dakinta tana tambayar kanta to daga ina yaya yusleem yake?
Wasa wasa kullum cikin dare sai taji fitarsa kuma bashi zai dawoba sai aubah ashe dama can haka yakeyi sanine batayi ba saboda lokacin da zai fita tayi bacci shiyasa har yaje yadawo bata saniba, kasa gane inda yake zuwa tayi domin fitar tasa kusan kullum ne tamkar ibada kuma baya tashi fita sai tsakiyar dare,
Yau kam ta daura aniyar binshi taga inda yake zuwa domin tunaninta yanzu yafara bata cewar ko yaya yusleem dan fashi ne?
.
Hana idonta bacci tayi har karfe dayan dare tana jira taji motsin fitowarsa amma shiru, karfe biyu shiru har da rabi duk shiru, hakura tayi ta kwanta nan bacci ya dauketa can cikin baccinta taji dirin motarshi agigice ta tashi ta leka abin haushi wai sai ganinshi tayi yafito daga cikin mota alamun yadawo daga wurinda yaje,
Da haushin wannan abun ta wuni da yamma sai gashi ya shigo cikin part dinta yana sanye cikin farar shadda mai mutukar kyau da tsada dinkin tazarce sai jar hula da yasaka,hannunsa daure da agogon fata fari kafarshi kuma yasa farin takalmi half cover tsaf dashi fadin irin kyan da yayi abun ba acewa komai,ita bama tafiya ganinshi da dogayen kayaba sai dai idan ranar juma'a ce tayi wannan kam yanasa manyan kaya amma idan bahaka ba kullum cikin kananan kaya yake,
"Zanyi tafiya zanje America daga can zan wuce India saboda akwai likitan da zan gani acan,idan akwai abinda kike bukata ki duba cikin bedroom dina akwai kudi..." Yace da ita cikin muryarsa mai sanyi,
"Allah ya kiyaye hanya yadawo dakai lafiya"
Bai amsaba yajuya yafita,bayan tafiyarshi part dinshi taje ta shiga bedroom dinshi tahau binciki wai ko zataga wata alama wacce zata tabbatar mata da gaskiyar abinda take zargi amma babu abinda tagani haka ta hakura ta mayar da dakin ta gyara ta fita,
.
Washe garin tafiyarshi mami ta turo driver ya dauketa can ta zauna har tsawon sati 2 sai ana gobe zai dawo sannan takoma gidanta kuma sosai taji dadin zama tareda mami domin tana mutukar kaunarta tareda kulawa da ita,
Tunda yadawo take bibiyarsa tana fakonsa saboda so take sai tagane inda yake zuwa cikin dare da abinda yake yi, kullum bata bacci har tsawon kwana biyar da dawowarsa saida ta sakankance ranar da tayi bacci aranar ya fita daf da asuba kuma sai gashi yadawo,
Wani haushine ya cika mata ciki gashi kuma tun daga ranar bai kuma fitaba, duk da haka bata hakura ba haka taci gaba da saka masa ido,
A wata ranar lahdi har zata kwanta sai tajiyo motsinsa, tashi tayi ta sadada tafita har yabude motar zai shiga ko me ya tuna oho sai yafasa yanufi ciki amma dai yabar motar a bude, ganin haka yasata lallabawa tabude bayan motar tashiga ta makure ta buya,
Tafi mintuna talatin aciki bai dawoba, tana shirin fita sai taji alamun tahowarsa nan takoma tasake makalewa ta yadda bazai ganta ba,
Shiga cikin motar yayi yatadata ahankali ya murza ya doshi gate din fita.......
_Sakon fatan alkhairi ga yan group din Duniyar littattafan Hausa, tabbas kunfi kowa son alwashi..._
*
***Sake lafewa Hafsat tayi a lungun kunjerun baya wato wurinda ake ajiye kafa, tana jinsa yana driving din yana dan jan karamin tsaki, titin emirs palace yahau,
Gaba daya garin tsitt yake babu motsin kowa sai haushin karnuka wadanda idan sun ji motsi suke kaurewa da yi,
Wayarshi ce tadanyi kara nan taga ya dauka yakara a kunnensa, cikin sansanyar muryarshi taji yace,
"Am on my way...." Wani dan tsakin yaja bayan ya kammala wayar ya ajiye,
.
Haka yaci gaba da yin driving ahankali shi kadai atsakiyar titi domin hatta jami'an tsaro masu yin patrol sun gama aikinsu sun tafi,ita mamakinshi ma takeyi ganin ko tsoro bayaji shi kadai a titi kamar aljani,
Wata hadaddiyar atishawa ce ta tahowa Hafsat batare data shirya ba nan tayi hanzarin toshe bakinta da hancinta amma duk da haka saida yar kararta ta fita,
"Atshhh..."
Jin sautin yasa yusleem wanda ke yin driving dan juyowa nan tayi saurin sake kwantawa abayan kujerar, maida kallonsa titi yayi yaci gaba da tukinshi,
Jin alamun yatsaya yasata dan dago kanta domin ganin ko inane, bata san ko ina bane amma tana dan iya jiyo maganganun mutane, dukar da kanta tayi har saida taji fitarsa sannan ta dago tafara kallon wurin,
Wani babban hotel ne mai tsananin kyau wanda yakeda fiyeda hawa 20,harabar wurin kadai ta isheka nishadi da kallo domin itama kawace take da abubuwan saka nishadi, wurin haske ne tarwal kamar rana sannan ga mutane nan sunata hada hadarsu mata da maza,
.
Hango yusleem tayi ya nufi cikin hotel din nan tayi yunkurin binshi amma abin haushi ya kulle motar kuma babu yadda zatayi ta iya budeta domin motar tashi ba kamar sauran motoci bane, motarshi motace mai tsada wacce ta amsa sunanta domin ko a zagayen garin bata tunanin akwai wanda yake da irinta,
Dukan kujera tayi cikeda haushi, damuwa gamida bacin rai domin taso ace tabishi abaya taga karshen gudun ruwansa,
Tana nan zaune tana kallon yanda mata da maza ke zuwa suna shiga cikin hotel din kamar bazasu kareba domin maimakon ma su ragu sai sake karuwa suke,
Tagumi Hafsat tayi aranta tana tunanin ko mahukunta suna ina hakan take faruwa?,
Tana nan zaune tana jiran taga ta inda yusleem zai bullo amma shiru sai misalin karfe 5 saura sannan ta hangoshi yana fitowa daga cikin hotel din, saurin komawa maboyarta tayi ta lafe, saida yadan jima awaje bata san me yatsaya yiba sannan yabude motar yashiga ya tadata,
Tana jinsu suka hau titi suka nufi unguwarsu, karar bude gate taji alamun sun iso gida lokacin anfara shiga masallaci sallar asubah,
Kasancewar gidane yasa yusleem bai kulle motar ba fita kawai yayi yatura kofar yanufi ciki, saida yajima da fita sannan hafsat ta lallaba ta fita,
.
Ganin kamar giftawar mutum yusleem yayi lokacin da yake tsaye agaban window dinshi bayan yadauro alwala, da sauri yafita yabi ta kofar da zata sadashi da part din hafsat,
Bai taba shiga bedrooms dinta ba sai yau, wannan shine karo nafarko da yataba takawa zuwa dakunan barcinta,
Bedroom din farko yafara shiga nan babu kowa aciki har cikin toilet yaduba amma babu kowa, rufe dakin yayi yakarasa dayan yana shiga tana fitowa daga bathroom da alama alwala tayi,
Ganinta yasashi juyawa yafita, dan lekashi Hafsat tayi,
"Ohh Allah, Allah kasa dai ba ganewa yayiba.." Tafada acikin zuciyarta,
Tana idar da salla ta kwanta ramuwar baccin da bata samu tayiba tunda ta kwanta kuma ba ita ta tashiba sai misalin karfe 10 nasafe, wanka tayi tashirya tasaka wata doguwar riga ta leshi pink colour da stones ajiki, kitchen tashiga ta dora breakfast sannan ta dafawa yusleem tea tanayi tana addu'ar Allah yasa karya gwasaleta,
Saida ta kammala yin breakfast dinta taci sannan ta dauki nashi ta nufi part dinshi,
Yana kwance akan tsakiyar fankamemen gadonshi yana ta bacci, abisa dukkan alamu har yanzu bai tashiba,
Dan karamin stoll tajawo ta dora masa akai ta tsaya tana kallonsa,
"Menene kika tsaya min aka kina kallona??" Taji yafada batare da ya bude idonsa ba, ita tsorata ma tayi saboda ganin tun lokacin data shigo dakin idanuwanshi a rufe suke,
"Ahhh babu komai..., dama breakfast nakawo maka.."
.
Murmushi taga yayi akaro nafarko tsakaninta dashi domin tun ranar data fara ganinsa bata taba ganin murmushinsa ba sai yau,
"Shiga toilet ki hada min ruwan wanka.."
Taji yasake fada ahankali,
"Toh" bude bathroom dinshi tayi tashiga, saida tafara dauraye toilet din sannan ta hada mishi ruwa acikin bathtub tasaka salt nawanka da turaren wanka domin duk gasu nan tanade asaman wata yar madaidaiciyar kanta wacce ke daure ajikin bangon toilet din,
Lokacin da tafito atsakar dakin ta sameshi yana tsaye yana yin mika nan tabashi hanya yawuce yashiga ita kuma tasoma gyaran dakin tana yi tana yan kalle kalle ko Allah zaisa idanuwanta su gane mata wani abu, har kasan gado ta leka amma babu abinda tagani,
Tana kammala gyara dakin shi kuma yana fitowa fita tayi tabashi wuri domin yashirya, a falonshi ta zauna tana nan zaune har yafito,zama yayi ya dauki remote ya kunna tv,
Ita dai Hafsat tana zaune tana binsa da kallo duk inda ya motsa, har azahar tayi bata bar falonba saida taga yafita salla sannan taje takwashe kayan da ta kawo masa breakfast aciki takoma part dinta amma data kammala lunch ma can tasake komawa sukaci gaba da zaman kurame.
.
Abin mamaki tamkar yasan shirin da Hafsat keyi akansa ko kuma yanada masaniyar abinda take shirin yi sai ya canja taku, acikin kwanakin gaba daya baiyi fitar dareba sai dai amma idan yafita kafin sallar magrib baya dawowa sai 1 ko 12:30,kuma ranakun suna dan sassabawa domin wata ranama da rana yake fita to bazai dawoba sai 1 wata rana kuma tun safe idan yafita office baya dawowa sai 12 wata rana kuma sai yayi zamansa agida ko nan da kofar gida bazai fitaba sai dai idan time din salla yayi yafita yaje masallaci yadawo, gaba daya yasa Hafsat acikin wani yanayi domin takasa fahimtar ta inda zata gano abinda yake aikatawa aboye wanda abisa dukkan alamu babu Wanda yasani,
Yafi sati biyu yana wannan shifting din daga rana zuwa dare ko kuma daga yamma zuwa dare,
Ganin kamar idan aka cigaba da haka Hafsat bazata samu abinda takeso ba yasata yimasa dabara,
Tea ta dafa masa takai mishi ta zauna acan nesa dashi, saida yadawo daga sallar azahar sannan yasha, nan yaji duk kasala ta rufeshi, wannan dalilin ne ya hanashi fita gaba daya ranar domin har salla agida duk yayi,
Karfe 2 nadare daidai yayi shirin fita nan yaje wurin da yake ajiye keys din motocinshi yasoma dubawa, yayi neman duniya amma baiga na BMW dinshiba shikuma yafi son yaje da ita domin sabuwar motace dan haka ba kowa bane yasanshi da itaba sabanin sauran motocinshi,
Wani key din yadauka yafita, Hafsat da tun jimawa take cikin bayan motar a boye tasake gyara buyan da tayi ganin ya nufo parking space din amma abin haushi koda yazo sai taji ba motar da take ciki yashiga ba wata daban yabude yashiga yayi reverse zai fita haushi ne ya cika mata ciki domin fa saboda haka ta dauke key din BMW dinshi ta boye saboda kar taje yasake kulleta kamar yadda yayi mata rannan tanaji tana gani yafice daga gidan batare data bishiba,
.
Ciki takoma tana cizon yatsa wato duk shirin data dade tanayi Yatashi abanza kenan,tsabar takaici bata ma san lokacin da yadawo ba.
Ganin tarasa mafita yasata tambayarshi cewar zataje gidansu bai hanataba kamar yadda tayi tsammani dama, koda taje gidan acan tawuni amma yamma tanayi tacewa Ummi tafiya zatayi, nan ummin tayi tayi da ita akan tajira salisu driver yadawo yakaita amma taki,
A perfect guys & ladies hotel ta sauka ta biya mai adaidaita sahu kudinsa tatafi can cikin wasu shuke shuken flowers ta tsaya, har akayi magrib bataga alamun daya daga cikin motocin yusleem ba tana nan tsaye har akayi isha alokacin ne ta saddakar da bazai zoba,
Fitowa tayi takama hanya zata fita tana zuwa gate din hotel din tahango motarshi tana dosowa kamar a mafarki babu shiri tajuya tabi ta bayan wasu bishiyoyi ta nemi mafaka duk da tasan ba lallai ne yaganeta ba saboda bazai taba tsammanin ganinta awurinba,
Tana ganinshi yafito bayan ya rufe motarshi ya nufi ciki yana yin waya yana sanye cikin kananan kaya, lababawa tayi tasoma binsa abaya abaya har zuwa ciki, akofar wani daki taga yatsaya mintuna kadan aka bude masa yashiga,batayi kasa agwiwa ba tabishi har kofar wannan dakin,
.
Tsayawa tayi tana tunanin ta ina ya kamata tafara, tafi minti goma atsaye daga karshe kawai ta nufi kofar ta murda abin mamaki abude tajita nan tashiga ahankali, wani dan madaidaicin falone wanda yacika da sanyin air condition, leken cikin bedroom din tafara yi amma kuma bata iya hango komai nan tadan tura kofar ahankali ta zira kanta ta leka, abinda tagani shine yayi sanadiyar sulalewarta awurin ta suma bayan ta kwalla kara mai mutukar firgitarwa.....
_Tofa ko me Hafsat tagani? Nidai Ummi Shatu banida wannan amsar..._
*
***Ahankali tafara bude idanuwanta wadanda suka yi mata nauyi ga wani irin ciwo da kanta ke faman yimata kamar zai tsage,
Dishi dishi take gani kafin daga bisani ta dan fara ganin dishi dishin yana washewa har ya b'ace gaba daya,
Mami ta hango zaune saman wata kujerar roba ganin ta bude idonta yasa mamin matsawa gareta,
"Sannu Hafsat..., sannu kinji, Allah yabaki lafiya..."
Runtse idanuwanta tayi take wasu zafafan hawaye suka gangaro daga cikin idanuwanta, ko kadan bata burin ta sake ganin yusleem ayanda taganshi dazu kuma ko tunawa bata son ta kara yi domin wannan shine mafi munin gani da idanuwanta suka taba yi tunda tazo duniya,
"Sannu Hafsat, kukan me kikeyi kuma?" Mami ta tambayeta tana dafata,
.
"Kukan ciwo mami, kukan ciwo nakeyi mami ba kukan komai ba domin kaina wani nauyi naji yayi min banda azabar ciwon dake addabata..."
"Sannu, sannu Allah yabaki lafiya, ina zuwa bari inkirawo likita saboda yace idan kin bude idanuwanki inkirashi.."
Fita mami tayi daga cikin dakin nan Hafsat tasake mayar da idanuwanta ta rufe tana hawaye, a hakikanin gaskiya abinda tagani ne yasata wannan kukan bawai ciwon kan da take tareda shi yanzu bane,
Tana nan kwance tana hawaye taji shigowar mami da dr,
Gaban gadonta likitan yakarasa yakai hannunsa kan goshinta ya taba,
"Sannu, yanzu me kikeji yafi damunki?"
"Dr ciwon kai ne kadai ke damuna.."
"To insha Allah shima zai daina nan da dan wani lokaci.."
.
Dukufa likitan yayi yafara rubutu ajikin wani dan madaidaicin file saida ya kammala sannan yadago ya mikawa mami takardar,
"Ga magungunan da za asamo mata tasha bayan taci abinci, Allah yakara bata lafiya.."
Karbar takardar mami tayi shikuma likitan yasaka kai yafice daga cikin dakin,
Wayar yusleem mami tasoma nema ringing biyu zuwa uku ya dauka,
"Kana inane? Kai nake jirafa.."
Kashe wayar tayi batare da Hafsat tajiyo abinda yusleem din yafada ba,
Ba afi mintuna biyar da gama wayarsu da mami ba sai gashi ya turo kofa yashigo, kawar da kanta hafsat tayi daga gefen da yake ta mayar zuwa wani gefen,
"Wannan shine mijin kaddara..." Tafada acikin zuciyarta,
"Wai kai me yasameta? Inata tambayarka abinda yasameta harta suma haka amma kaki yimin bayani.."
"Yanzu dai mami ai ba lokacin yin wannan maganar bane, abinda kuke bukata nake son ji"
.
"To kaga dai magungunan da dr yace asiyo tasha bayan ta ci abinci amma gaskiya ni ina ganin idan har takara kwana biyar bataji sauki ba gara ka kaita chairo..."
Dan sajenshi ya shafa ya karbi takardar dake hannu mami,
"To shikenan bari nasamo drugs din indawo.."
Yana fita hajiya kubra na shigowa hannayenta dauke da babban basket din abinci,
"Hajiya siyama ya mai jikin? Nifa kalau muka rabu da ita saida ma nayi nayi da ita tajira salisu yadawo yakaita amma furr taki ashe tsautsayi ke janta.."
"Ehh haka Allah yake ikonsa ai, nima wallahi sai waya kawai yusleem yamin wai yakaita asibiti..."
Ajiye kayan hannunta hajiya kubra tayi ta matsa wurin Hafsat tana yimata sannu,
"Wai ya akayi haka tafaru? Hafsat garin yaya..?"
"Ummi kaddara da tsautsayi, nima ban san abinda ya sameni ba kawai jina nayi nafadi,shi lokacin da abin yafaru ma yana office inajin sai wayata aka dauka aka kirashi..." Ta karashe maganar hawaye na bin kuncinta,
"To Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba.."
"Amin summa amin, Allah yatashi kafadunta yabata lafiya..." Inji mami,
.
"Tashi kici abincin to, tuwon shinkafa ne miyar zogale.."
Dakyar Hafsat ta iya tashi ta zauna saboda irin yanda kanta ke tsananin sarawa, tafara cin abincin kenan yusleem ya shigo dauke da magungunan da likita ya rubuta mata,
"Mami gashi..."
"Yawwa ansamo, to bari tagama cin abincin sai tasha, ashe kaima baka gida lokacin da abun yafaru? Tace kana office sai awaya aka kiraka.."
Kallonshi Hafsat tayi domin taga irin yanda zai karbi maganar,
Shiru yayi baiyi magana ba saima bude kofa da yayi yafita,
Tunda yafita bata sake jin motsinshi ba,ita kanta tasan daren ranar bazata iya bacciba ba don Allah ya taimaka anhada mata da magungunan bacci ba acikin maganin da aka bata,
Tareda mami suka kwana a asibitin ita kuma ummi tatafi sai da safe ta dawo takawo musu abincin karyawa,
.
Kwananta uku a asibitin dr yace zasu iya tafiya gida, duk da ta dan samu saukin ciwon kan dake addabarta amma ta gagara daina kukan da takeyi wannan kam yazame mata kamar ibada wani lokacin sai suna zaune kalau sai kawai aga tana hawaye gashi daga mamin har Ummi sunyi tambayar duniya amma taki fada musu damuwarta wacce ke sata kukan,
Yanzun ma da zasu bar asibitin hawaye ne ke faman bin kuncinta ganin haka sai mami tace kawai hajiya kubra tatafi da ita gida ta dan sake warwarewa,
Tunda suka koma ummi ta tisata agaba tana yimata tambayoyi,
"Hafsat kin dai san yanzu aduniyar nan bakida wanda yafini daga ni sai Alhaji, ki sanar dani abinda yake damunki, idan baki fada minba wa kike dashi wanda zaki fadawa?"
Murmushin karfin hali Hafsat tayi,
"Ummi wallahi bafa kukan wani abu nakeyiba, kawai wani abin mamaki da ban tausayi nagani ranar da nabar gidan nan..."
"Me kika gani?"
"Ummi wata matace suke tafiya da yarta, tana rike da hannun yar fa yarinyar ta kwace ta ruga da gudu zata dauko wani abin wasa da ta hango ashe tsautsayi ne saiga mota tabi takanta gaba daya ta tanitseta, wannan abun shinefa ya hadda samin wannan suman da nayi..."
Dafata hajiya kubra tayi,
"Allah sarki Hafsat to ai dama idan ajali yayi kira ba makawa sai antafi, Allah yajikanta mukuma yasa mucika da kalmar shahada.."
"Amin Ummi"
.
Tashi hajiya kubra tayi tafita, tana fita Hafsat ta kifa kanta ajikin pillow tasoma kuka mai sauti domin da duk kukan zuci take yi wanda yafi nafili ciwo,
Kwananta biyu agida amma kullum sai mami tazo dubata yusleem ne kadai bai taba zuwa ba, aranar da tayi kwana uku mami tace tashirya su tafi inyaso idan takarasa warwarewa awurinta sai takoma gidanta, shiryawa tayi suka tafi gidan mamin nan mami tasoma bata dukkan kulawa domin dakin surayya tabata ta zauna aciki wanda yake dauke da dukkan abubuwan jin dadi irin wadanda ba agidan kowa ake samuba sai gidan wadanda suka amsa sunansu masu naira,
Dukkan abinda take so shi ake Kawo mata domin ga ma'aikata nan agidan kashi kashi ita kanta mamin babu abinda takeyi sai dai idan tana bukatar abu tayi waya kawai akawo mata shiyasa koda yaushe cikin ado zaka sameta tasha kwalliyarta ta zubawa jikinta gwala gwalai,
.
Dawowarta gidan mamin ma bai hanata daina kukan da ya zame mata jiki ba domin kullum cikin yinsa take,
Kwananta biyar agidan mamin amma bataga yusleem ba nan tafara tunanin to kodai tafiya yayi ne?
Tana cikin wannan tunanin tajiyo maganar mami a falo kuma da alamu yusleem dinne yazo, runtse idonta tayi tafara zubar da hawaye wanda har mami tashigo bata san tashigo ba,
"Hafsat, wai me yake damunki ne, kukan nan naki yayi yawa kuma nasoma zargin cewar akwai abinda ke saki kukan, ki fada min gaskiya karki boye min.."
"Mami babu komai, wallahi babu abinda ke damuna, wannan kukan ni kaina ban san meyasa nake yinsa amma nasan bazai rasa nasaba ba da accident din da naga anyi rannan ba"
.
"To hafsat ai sai hakuri, haka rayuwar take sai dai Allah yasa mucika da imani, ki shirya anjima mijinki zai zo ya daukeki ku tafi.."
"To mami.."
Ai mami nafita hafsat ta rushe da kuka saboda yanzu ita bata son ganin yusleem kwata kwata kuma da alama shima yagane haka domin tun rannan bai sake rab'ar inda takeba.
Misalin karfe 8 nadare yazo daukarta, kuka mami ta sameta tanayi nan hankalinta yatashi ta fara tambayarta,
"Hafsat ko wani abun yusleem din yake yi miki?"
Jijjiga kai tayi, "a'a mami babu abinda yake min"
"To ko bakya son komawa gidan nashi ne yabarki anan?"
"A'a mami zan koma"
Zama mami tayi agefenta,
.
"Hafsat kar muyi haka dake, ki fada min gaskiya idan har akwai abinda yusleem yake yimiki karki boye min"
"Wallahi mami babu komai, ni babu abinda ya taba yimin muna zaune lafiya dashi,kukan rabuwa dake kawai nakeyi mami da kuma irin soyayyar da kike nuna min nasan duk duniya nafi kowa yin sa'ar surika tagari mai sona"
Rungumeta mami tayi tasoma shafa kanta,
"To hafsat ai kema surakace tagari shiyasa dole in kaunaceki kuma wallahi ina sonki irin soyayyar da nake yiwa 'yayan da na haifa,yanzu dai shikenan tashi kizo muje dan yazo yana jiranki share hawayenki daina kukan"
Akwatin kayanta tadauka tareda yin karfin halin tsayar da hawayen dake zuba a idonta tafito suka fita da mami domin shi har yajima acikin motarsa,kasancewar ranar juma'a ne shiyasa yake sanye da dogayen kaya na ash colour din shadda mai tsadar gaske,
Gaban motar tashiga batare da ta kalleshiba amma kamshin turarensa na beautiful oud sai cika hancinta yake sallama sukayi da mami tanaji mamin nace masa yakula da ita sosai sannan banda matsanta mata,kuma indai taji yayi mata wani abu to sai ransa yabaci, kasancewar yan miskilancin suna kusa ko amsawa baiyi ba,
.
Jan motar yayi suka fita suka nufi gidanshi babu wanda ya kalli wani bare har yayi magana nan tafara tunanin to ko shima fushin yake?
Lokacin da suka karasa gidan, trolley dinta taja ta nufi ciki batare data dubi side din dayake ba,gidan tsaf tsaf taganshi kamar tana nan, a bedroom dinta tazauna kan bed side drewar tayi tagumi sai kuma tafara kuka,
Handbag dinta wacce tafita da ita ranar data bishi hotel ta suma ya dauko yabita dakinta, cilla mata jakar yayi saman kan bed dinta yajuya zai fita,
"Yaya yusleem..."
Takira sunanshi, cak yatsaya batare da yajiyo ba,
"Meyasa ka zabi wannan mummunar sana'ar acikin rayuwarka? Duk sana'o'in duniya karasa wacce zakayi sai wannan? Kasan kuwa irin mummunan tanadin da Allah yayiwa masu irin wannan sana'ar? Meyasa ka zabi duniyarka akan lahirarka?"
.
Ahankali yajuya yafara takawa ya nufi inda take tana zaune hawaye nafaman bulbula daga idonta kamar anbude fanfo.....
0 comments:
Post a Comment