ALWASHI Page 21-25
.
***Saida ta rintse idanuwanta sannan ta goga mishi sabulun ajikin kasunbar tashi bayan ta shafa ruwa,
Ahankali tasa shaving stick din tafara shaving kasumbar tashi wacce take bala'in burgeta domin itace takara kawata fuskar tashi,
"Nanah tunanin me kikeyi ne kike nema ki hada da fatata..."
Taji muryarshi bayan yarike hannunta, sai lokacin tadawo daga duniyar tunanin data tafi, dan murmushi tayi,
"Babu komai..."
"Ban yarda ba"
"Saboda me?"
"Saboda nasan ba gaskiya kika fada ba"
Cigaba da yimasa shaving din tayi tana murmushi,
"Ohh yaya yusleem.."
"Ohh nanah..."
Dariya tayi, "angama"
"Inji wa?" Ya tambayeta yana shafa habarshi,
"Allah angama ko sai nakawo maka mirror kagani?"
"A'a tunda kince angama shikenan"
Candle din tabar mishi tafita, tana zuwa tsakiyar dakin taga ankawo wuta, ita sai yanzu ma ta tuna da wata wutar nepa domin tunda suka dawo wannan gidan ba ataba kawowa ba sai yau,
Wurin da zasu kwanta ta gyara musu ta shirya ta kwanta,
.
Maganar yusleem ce tasata dan juyawa ta kalleshi,
"Nanah shine baki fada min ankawo wuta ba?"
"Au dama baka saniba? Ai nazaci kwan ban dakin akunne yake.."
"Inajin dai wutar cikin ban dakin batayi gaskiya.."
Kaya yasaka ya dauki laptop dinshi yajona charge, da Hafsat har ta kwanta amma ganin wuta yasata tashi taje zata dan rage sakar dake gabanta,
"Wai ke bakya gajiya da sakar nanne?"
"Ina gajiya mana, amma yanzun dai ban gajiba..."
"To asauko lafiya.."
"Amin yaya yusleem.."
Kunna laptop dinshi yayi yafara game ita kuma tana kan keke tana sakarta amma dan jefi jefi suna yar hira,
Wata wak'a taji ya kunna yanabi ahankali,
_"Ehh shin yanzu idan kika barni ina zan kwana....,so naki yake tab'a raina, nagane da cewa yanzun so ne asalina,ki aminta dani alkawari mu rikewa juna,inhar nabarki inane zansa kaina,kimin uzuri kome nai sone sanadina,duk mai kaunarki sahibine ni awurina...."_
Shiru tayi tana sauraren yanda yake bin wakar yanayi ahankali cikin muryarsa mai sanyi, da zarar wakar takare sai taji yasake dawo da ita farko yanabi kamar mai yin hadda, murmushi tayi,
"Yaya yusleem dama ka iya waka?"
Rage volume din wakar yayi,
"Ban iyaba amma nakoya saboda wata yarinya guda daya..."
"Lallai...."
"Ina son wakar nan Allah nanah, duk lokacin da nake jinta jinake kamar danni mawakin yayita..."
Murmushi Hafsat tayi,
"To akunna min nima inji mana"
"Gata kiji, na sadaukar miki da ita"
Volume din wakar yakara yanda zata jiyo sosai nan yaci gaba da bin baitikan wakar har takare yasake kunnawa,
Har Hafsat tagama hada rigar da take yiwa amir tataso bai daina jin wakar ba yana kwance laptop din nakusa dashi,
"Yaya yusleem akashe wakar nan haka zanyi bacci.."
"Inkunna mana american film dai mu kalla.."
"To shikenan kunna kafin bacci yayi gaba dani.."
.
Kwanciya tayi ata bayanshi tadora kanta akan pillow tana kallonshi yana kokarin lalubo film din da zai kunna musu,sai taga yakara kyau saboda gyaran fuskar da tayi mishi, fuskarshi tafito fes sai kyalli take,
Black men shine film din da yasaka musu, juyawa yayi ya kelleta,
"Wannan ai nakare miki bakya gani.."
Janta jikinshi yayi yadauki kanta yadora akirjinshi suka cigaba da kallon wanda yakaisu har karfe 1 nadare sai lokacin bacci yasace Hafsat baima san tayi baccin ba saida yayi magana yaji shiru,
Kashe kallon yayi ya kashe laptop din yasake gyara mata kwanciyarta ajikinshi.
Rayuwarsu haka ta kasance, Hafsat ta hanashi yafita ya nemi aiki idan yayi magana sai tace to me suka rasa ai basu rasa komai ba, shi kansa yasan babu abinda suka rasa din amma wani lokacin yakan zauna yayi tunani tunda bazasu dawwama ahaka ba gashi lokuta da dama kewar maminshi data yan uwanshi tana damunshi domin yana mutukar sonsu sannan ya shaku dasu sosai,
Hafsat koda yaushe cikin kwantar mishi da hankali take tana nuna masa cewar wannan halin da suke ciki shine kadai marufar asirinsu da zarar sun koma wurinsu Mami to asirinsu zai tonu asan abinda yafaru, hakura yayi ya zauna bai fita ya nemi aiki ba koda yaushe suna daki shida ita tana aikin sakarta shikuma yayi musu girki ya kunna wakar da yazamar da jinta kamar ibada , yana bi yana abinda yake yi, hatta sauran matan dake haya agidan sun saka musu ido koda yaushe suka zauna gulmarsu sukeyi wai su jarababbu ne kullum suna daki basa rabuwa kuma baya barin Hafsat tana fitowa,
Da dan kudaden sakar da Hafsat takeyi suke samun na cefane kuma duk da haka suna zaune cikin rufin asiri basu da wata damuwa saita rashin danginsu atare dasu.
Yau tunda safe yusleem da rashin lafiya yatashi domin yajima baije yaga likitansa ba kuma akwai magungunan da yakesha wanda yajima baisha ba shiyasa lalurar ta tashi mishi tun daren jiya amma yayi kokarin boyewa kada Hafsat tagane, haka ya lallaba suke Yar hira sama sama har abin yafara fin karfinsa domin wani zazzafan zazzabine ke yimasa sallama....
*
***Daurewa yusleem yaci gaba dayi bai bari ta fahimci komai ba har tagama shiryawa ta fita kitso wurin maman amir,
Kafin tadawo tuni har zazzabin ya rufeshi, akwance tadawo ta tarar dashi yayi ruf da ciki,
.
"Yaya yusleem kayi salla kuwa...?"
Shiru taji nan tayi tunanin kodai barci yake yi dan haka ta nufeshi da niyyar tashinshi,
Agaban katifar ta zuba gwiwowinta ta dan kai hannu da niyyar taba jikinshi amma sai tajishi zafi zau,
Cikin rawar jiki ta daddafa shi,
"Yaya yusleem menene? Baka da lafiya? Meya sameka?"
Juyo da kanshi yayi ya bude idanuwanshi wadanda sukayi jajur ya kalleta,
"Nanah cikina ke ciwo gashi zazzabi ya kamani.."
Zama tayi agefenshi fuskarta kamar zata fashe da kuka,
"Sannu yaya yusleem, to yanzu wanne magani zan samo maka? Ko paracetamol zaka sha?"
.
"Uhmm Kawo min insha to"
Har tatashi sai tadawo ta zauna,
"To ai bakaci abinci ba"
Girgiza mata kai yayi,
"Bazan iyaci ba bana sha'awar kowanne irin abinci, zan dai sha ruwan zafi"
"Yaya yusleem amma da ka daure kaci abincin komai kankantarshi..."
Daga mata kai yayi alamun to saboda ganin yanda tadamu ta daga hankalinta lokaci daya,
Shinkafa da wake da mai da yaji ta zubo mishi dama ita ta dafa tunda safe,
.
Zaune ya tashi ta gauraya masa shinkafar tasoma bashi, cokali uku kacal yayi ya mike yashiga toilet da sauri nan yafara kwara amai baji bare gani, da sauri tabishi cikin toilet din inda yake aman ta rikeshi, bayan yagama amayar da abincin da yaci dinma bai daina aman ba,
Ruwa ta zuba masa ya wanke bakinshi bayan ya gama, rikoshi tayi suka koma cikin daki hawaye suna zuba daga cikin idanuwanta,
Kwanciya yayi yadan bude idonshi ya kalleta ganin tana hawaye yasashi rikota zuwa jikinsa ya kwantar da ita tareda dora kanta bisa kirjinshi,
"Menene na kuka?"
Shiru tayi bata amsa ba, amma kuma hawayen basu bar fita daga idanuwanta ba,
.
Kokarin kwantar mata da hankali yayi ta hanyar zame dan kwalin dake kanta,
"Baki nuna min kitson da akayi miki ba..."
Goge hawayen fuskarta tayi tana jinshi yana kirga adadin yawan kitson duk da cewar acikin karfin hali yake yi amma ita tadan ji sauki acikin zuciyarta saboda ganin ya dan ware,
"Kayi salla ne?"
"Banyi ba, dafa min ruwan zafi insha sai nayi alwala saboda naji ruwan kamar da sanyi"
Tashi tayi ta dafa masa ruwan zafin ta zubo masa a cup tasa Lipton da sugar tabashi yasha sannan takai masa wani ban daki ta rakashi yaje yayi alwala yafito,
Kwanciya yayi ruf da ciki bayan ya idar da sallar yaja bargo ya lulluba, tagumi Hafsat tayi tana kallonsa idonta fal fal da hawaye,
.
Haka suka wuni acikin wannan hali har dare yayi tunda dare yayi kuma bacci yagagari idonsu domin wani irin shassheka yusleem yakeyi kamar wanda yayi gamo, kuka Hafsat tasashi agaba tanayi ga kakarin amai da yaketa yi amma kuma yakasa banda zazzafan zazzabin da yake jikinsa gashi dama throughout yau baici komai ba cokali ukun da yayi ma a shinkafa da waken data dafa saida ya amayar da ita tass ruwan zafi kadai ya iya sha,
Rirrikeshi hafsat tayi tana kuka domin ita bata ma san yanda zatayi ba ganin dare yayi sosai bare tace su tafi asibiti,
Addu'a take ta tofa mishi afuskarshi zuwa can bacci ya daukeshi, lullubarshi tayi tazuba masa ido tana kallonsa, har asubah tayi bata runtsa ba,
Tashi tayi tai salla zuwa can taji kakarin amai alamun yatashi, tashi tayi da sauri taje ta rikeshi,
"Sannu yaya yusleem, sannu..."
Kai yake daga mata har yasamu yadaina kakarin aman,
Ruwan zafin data dora mishi ta je ta sauke ta zuba mishi yayi alwala yayi salla tabashi tea yasha, kwanciya yayi yadora kanshi akan cinyarta jikinsa zau dan zafi,
Bacci taji yasake komawa nan ta zame tatashi taje ta harhado kaf kan kudadenta dake cikin dakin wanda ta lissafasu Dubu goma sha daya ne da dari biyar,
.
Tagama yanke hukuncin zasuje asibiti idan gari ya waye saboda wannan rashin lafiyar ta yaya yusleem da karfinta tazo idan ba atareta da wuriba gaba sai azo asha wuya,wurinshi takoma ta zauna ta taba jikinshi har lokacin akwai zafi da alama zazzabin bai sauka ba.
K'arfe 9 suka gama shiryawa domin tafiya asibitin,
"Wanne asibitin zamuje?" Yusleem ya tambayeta,
"Private mana yaya yusleem"
"Private akwai tsada nana, muje general"
Girgiza masa kai tayi,
"Yaya yusleem general hospital babu confidential saboda asibiti ne na kowa da kowa yanzu idan mukaje can wallahi sai kowa yasan abinda ake ciki nikuma bana son sirrinmu ya fita amma kaga idan private ne babu ruwan kowa da mu balle har musa ran wani zaiji maganar"
"Shikenan tunda kince haka"
.
Tashi tayi ta rikeshi yatashi yasa takalmi suka fita, maman amir ta biyosu tana yimusu Allah ya kiyaye hanya,
Sai da sukaje bakin titi sannan suka samu keke napep nan ta tare musu suka shiga suka nufi wani private hospital,
A reception yusleem ya zauna taje ta bude mishi polder dubu biyu sannan za abiya kudin ganin Dr dubu biyar,sannan sai anfara yimishi general test na komai da komai domin ayi saurin fahimtar matsalarshi daga nan sai aturashi wurin likitan da yadace yaganshi dan haka sai ta biya kudin test dubu biyu, duk haka ta biya takoma wurinshi suka nufi laboratory,
.
Babu bata lokaci akayi masa duk gwaje gwajen da za ayi aka basu result sannan aka nuna musu wurinda zasuje suga likita,
Zama sukayi suna jiran na ciki yafito bayan yafito ta rikeshi suka shiga cikin office din wanda ajiki anrubuta sunan likitan wato Dr Sufyan,
Dan siriri ne likitan baki kyakkyawa yana sanye da bakaken suit da farin glass a idonshi,
Bude sakamakon da suka Kawo masa yayi yaduba kafin yadago yana kallonsu bayan ya cire farin glass din dake idonshi,
"What..." Yafada ahankali yana kallon paper din,
Maida kallonshi garesu yayi, yajanyo wani dan karamin card yafara rubutu,
"Me yasameshi? Tun yaushe ne bashida lafiya? Yana iya cin abinci?,ya kakejin ciwon cikin? Menene yafi yimaka ciwo ajikinka?"
.
Duk wadannan tambayoyin yusleem ne ya amsasu da kanshi, card din Dr yamika musu bayan yagama rubutun da zaiyi,
"Ok ga wannan kuje pharmacy Ku siyi magani, zai rinka shan guda daya kwal akullum.."
Karba sukayi suka fita, a reception tabar yusleem tatafi pharmacy domin siyo maganin, takardar ta mika domin abata maganin,
"Hajiya kwali daya ko biyu?"
"Abani kwali biyu"
"Ok kudinki yakama dubu dari da sittin"
Idanuwa Hafsat tazaro,
"Dubu dari da sittin?"
.
"Ehh ai duk guda daya dubu tamanin ne"
"Ok tom ina zuwa bani takardar"
Karbar takardar tayi tafita tanufi office din Dr sufyan, knocking tayi sannan tashiga,
"Madam ya akayi?"
"Dr maganin naje zan siya naji ance wai dubu tamanin ne guda daya"
Gyara farin glass dinshi yayi yanuna mata kujera ta zauna,
"Kin san mijinki gay ne?"
"Ehh nasani likita.."
"To wannan maganin shine kadai maganin da zai rinka sha domin samun lafiyarshi saboda idan bakuyi kokari yasamu maganin nan yana sha ba komai zai iya faruwa dashi,dan haka am advising you kiyi kokari ku mallaki wannan maganin duk tsadarshi.."
"To shikenan likita za asiya insha Allah"
"Ok Allah yabashi lafiya"
"Amin, nagode"
Tashi tayi tafita tanufi wurin yusleem zuciyarta cikeda tunanin inda zataje ta samo kudin domin ita yanzu dubu biyu ne da dari biyu da hamsin kacal awurinta.....
*
***Kafin ta k'arasa wurin yusleem tayi karfin halin tsaida hawayen dake yi mata ambaliya akan kuncinta,
Murmushin karfin hali ta kakaro tayi lokacin da ta isa wurin yusleem,
.
"Yaya yusleem tashi muje..., anjima zan dawo na sai maka maganin saboda yanzu kudin hannuna bai kai ba"
Kallonta yayi yana jingine ajikin kujerar dake jere acikin reception din,
"Nawa ne?"
"Ka tashi muje kawai yaya yusleem..."
Bai sake yin magana ba yatashi, hannunshi ta rike suka fita, suna fita suka samu keke napep suka shiga,
Lokacin da suka koma gida ruwan zafi kadai ta dafa mishi domin baya iya cin abinci komai yaci sai yayi amansa, tana kokarin fita maman amir ta aiko mata da dan wake,
Kasa zaunawa taci tayi saboda idan har ba kudin nan taje ta nemo ta siyowa yusleem magani ba hankalinta bazai taba kwanciya ba,
.
Wurin kafintocin da suka siyi kujerunta takoma tasake kai musu tallar dayan kujerun nata na babban falo babu bata lokaci suka tafi gidan taje ta bude musu,
Duk haduwar kujerun nan da kyawunsu amma sai kafintocin sukayi mata tayin wulakanci wai dubu 60 zasu siya, kin siyarwa tayi nan suka kara dubu goma yazama dubu saba'in,ganin kudin basu cikaba yasata fito musu da wani show glass dinta wanda aka zuba mata humra da turaren wuta aciki, dubu goma sha biyar suka siya,
Saida suka fitar da kayan sannan ta rufe gidan tatafi, kai tsaye asibitin da sukaje da yusleem ta koma taje pharmacy ta siyo mishi maganin sachet daya,
.
Lokacin data koma gidan samunshi tayi yana bacci dan haka ta ajiye mishi maganin ta shiga wanka tafito, harta shirya bai tashi ba sai da ta idar da salla sannan taji motsinshi, juyawa tayi ta kalleshi,
"Sannu yaya yusleem"
"Yawwa, kin dawo?"
"Nadawo lokacin kana bacci.."
Mikewa tayi taje kusa dashi ta zauna,
"Yaya yusleem ga maganin nasiyo maka"
Kallonta yayi bayan ya gyara zamansa,
.
"A ina kika samo kudin da kika siyo?"
"Yaya yusleem kujerun nan naje nasiyar, lafiyarka yanzu ni tafi min komai.."
Hannunshi ya dora akan nata,
"Amma meyasa kika zabi sayar da kayanki? Ba ga nawa kayan ba wayoyina da laptop dina"
Girgiza masa kai tayi,
"Nawa kayanma naka ne, sannan nasan yanzu aduniya baka mallaki komai ba sai wayarka da laptop wannan dalilinne yasa bazan bada goyon bayan mu siyar dasu ba.."
.
"Nanah agaskiya ban san da wanne baki zan yimiki.."
Saurin rufe masa baki tayi bata barshi yakarasa ba,
"Inbaka maganin kasha yanzu ko zaka dan ci abincin da Maman amir ta Kawo min?"
"Bazan ci komai ba, bani maganin kawai nasha"
.
Tashi tayi ta dauko mishi ta hado da ruwa, abin mamaki kwata kwata kwayoyin maganin kwallo 6 ne aciki bamasu wani yawa bane sai dan karen tsada abinda yayi mutukar tayar da hankalin Hafsat,
Saida taga yasha maganin sannan ta dauko dan waken da maman amir takawo mata taci,
.
Hannu ya mika mata bayan tagama cin abincin ya kwantar da ita akusa dashi, kasa kasa yake yi mata magana suna yin yar hira.
Tunda Hafsat taga yakusa shanye maganin hankalinta yatashi nan tasake komawa wurin kafintoci ta sayar musu da gadajenta gaba daya taje ta siyo mishi magunguna saboda sam bata son ta doshi umminta ko abbanta da lalurar yusleem domin tasan asirinsu yana iya fallasa,
Haka taci gaba da daga kayanta tana sayarwa tana siya masa magani wanda yanzu haka bata da komai domin hatta su fridge dinta da sauran kayan kallonta duk ta siyar ta hada kan kudin ta ajiye wani kuma ta saiwa yusleem magani, yanzu abu dayane ke damunta shine kullum yusleem yana shan magani amma sauki baya samuwa kuma har yanzu baya iya cin abinci sai ruwan zafi gashi kusan 3weeks da zuwansu asibitin,
.
Sake shiryawa sukayi suka koma asibiti ganin dr sufyan, bayan yagama dudduba yusleem sun kama hanyar fita har sun kai kusa da gate Hafsat ta dakatar da yusleem,
"Yaya yusleem tsaya zo mukoma wurin dr akwai abinda nake son fada mishi"
"To Nana shiga kifito mana, bari injiraki anan"
Komawa office din dr sufyan Hafsat tayi, zaune tasameshi yana rikeda cup yana kurbar tea,
"Madam ya akayi?"
"A'a babu komai likita dama cewa nayi ko zaka sauya mana wani maganin saboda wannan din yayi tsada da yawa kuma har yanzu bai warkeba gashi baya iya cin abinci..."
.
Tunda tafara jawabi ya kura mata ido baya ko kiftawa har saida ta gama, ajiye cup din dake hannunshi yayi ya dora hannuwanshi akan table,
"Wato madam abinda zaki fahimta shine mijinki dan homo sexual ne wanda kusan lalurar ma taci karfinsa so dole sai magani mai karfi zai rinka sha, wannan maganin ba ako ina ake samunsa ba saboda tsadarshi dan inajin ma gaba daya garin nan baifi chemists guda uku zaki samu ba wadanda suke kawoshi, amma ni zan taimaka miki zan rinka baki maganin free mutukar zaki amince da abinda zan fada miki.."
"Likita ni sassauci nake son kayi mana ka sauya mana wani maganin wanda bai kai wannan tsada ba.."
"To ai madam condition din da mijinki yake ciki yanzu dole irin wannan maganin zai rinka sha,amma ni zan taimaka miki.."
"To nagode dr, nagode madalla.."
"A'a ai ba wani abu bane, zan baki card wanda yake dauke da address din gidana dake cikin G. R. A. Governor road.." Yakarashe maganar yana lasar lips dinshi,
Sai lokacin Hafsat ta fahimci inda maganar tashi ta nufa,
"Dr aini ba yar iska bace sannan banyi kamada matan banza ba wadanda zasu iya cin amanar mazajensu ba..."
Hannu ya daga mata,
"Amma shi mijin naki meyasa yaci taki amanar yaje maza suka bata masa rayuwa? Shifa da maza yan uwanshi ma yarinka alaka,Bari infada miki gaskiya kidaina wahalar da kanki akan mijunki domin situation din da yake ciki yanzu bazai taba kallonki a matsayin mace ba bare har ya iya kusantarki saboda lalurar dake tare dashi, gaba daya bayanshi yakusa lalacewa domin sperm din dake shiga ciki babu wurinda zai fice shine sai yarinka taruwa yana taruwa har idan yakai wani stage sai wurin ya lalace har tsutsotsi su rinka fita ta wurin dan haka kidaina wahalar da kanki abanza, ni zan rinka bashi magani kyauta duk da tsadarshi mutukar kin amince da bukatata domin nan asibiti nane wadannan magungunan kuma tun daga India nake iyo ordersu ake kawo min.....!"
Sassauta muryarshi yayi cikeda yaudara da son janyo hankalinta,
"Kinga maimakon ki zauna kina yimasa wahala bayan bazai iya amfana miki komai ba gara kisamu wanda zai rinka debe miki kewa duk lokacin da kika so...!.
*
***Cikeda tsana da takaici hadeda bacin rai wanda ya bayyana fushi mai tsanani akan fuskarta Hafsat take kallon Dr sufyan wanda yake zaune bisa kujerarshi yana dan juyawa ahankali abisa dukkan alamu ko auren farima dakyar idan yayi duba da yanayinsa haka kuma ahaife yusleem bazai girme mishiba,
.
"Madam bakice komai ba, abinda nake son ki fahimta shine wallahi idan kika cigaba da zama da wannan mijin naki dan homosexual to zaki nak'asa rayuwarki ne domin babu abinda zai amfana miki saboda yanzu shi yamafi bukatar dan uwanshi namiji sama dake domin masu aikata irin wannan mummunar dabi'ar akwai wani stage wanda idan har suka kai wannan level din to wallahi zai zamana bama sa kaunar mace kwata kwata bare har suyi sha'awarta, mijinki ayanzu dai haka presently bazanyi saurin yanke hukunci ba but yana daf da karasawa wannan stage din muddin baku dage da bashi wadannan magungunan yana sha ba.."
"Likita ni dama sassauci nazo nema wurinka bawai maganar banza ce takawo ni ba kuma har tunda sassaucin bazai samuba to babu matsala amma kaji tsoron Allah..."
Takarasa maganar cikeda fushi ta mike saurin dakatar da ita dr sufyan yayi,
.
"Haba yar kyakkyawa kyakkyawa, wallahi kinada kyau dan Allah..."
"Allah ya shiryeka tunda bakada aiki sai fasikanci da matar aure..."
Bata sake jiran abinda zai fada ba tafice daga cikin office din gabanta yana tsananta faduwa domin babu Wanda yataba tunkurarta da maganar banza irin wannan sai Dr sufyan, ko yusleem da yake mijinta bai taba yimata magana makamanciyar wannan ba,
Jan kafarta tayi zuciyarta tana yimata wani irin kunci da radadi, kamar amafarki ta jiyo muryar dr sufyan abayanta yana yimata magana da alama sake biyota yayi bai hakura ba da mugun nufinshi,
"Hajiya tsaya kiji, dan Allah kibani 5 minutes kacal infada miki wata magana.."
Afusace tajuya ta kalleshi,
"Dr nahadaka da girman Allah karabu dani, kadaina bina, yanzu idan mijina yaga kana bina me zai yi zargi?"
Jin yanda ta bude murya tana neman tara masa mutane yasashi tsayawa, ahankali yafurta,
"Zan barki amma bawai dan nahakura ba.."
Juyawa yayi yakoma ita kuma tabishi da kallon mamaki zuciyarta tana harbawa da karfi,
Wurin yusleem ta tasamma komawa kwakwalwarta abirkice saboda abinda taji dr sufyan yafada gashi kuma nanda 2 weeks dole su sake dawowa asibitin domin za asake checking din yusleem agani,
Awurinda tatafi tabarshi anan tasake samunshi yana tsaye ya dafa gate din asibitin yana jiranta,
Hannunshi takama tarike acikin nata,
"Yaya yusleem mutafi ko.."
.
Kallonta yayi yana dan murmushi,
"Au kin dawo?"
"Nadawo muje gida kawai abinda naje nema bai samuba dama nufina wai asauya maka maganin nan zuwa wani tunda naga har yanzu babu wani improvement.."
"To me likitan yace miki?"
Cewa yayi wai wannan din dai shine zaka cigaba dasha.."
Shiru yusleem yayi har suka samu adaidaita sahu suka shiga baice komai ba, daidai lokacin da zasu tare keke napep din khadija tsohuwar matar yusleem wacce yasaka last kafin ya auri Hafsat tana cikin motarta tadawo daga makaranta tacikin glass ta hangi wani kamar yusleem parking tayi da niyyar komawa wurinsu amma kafin ta juyo har sun shige keke napep din sun tafi,
Bata hakura ba tabi bayansu acikin motarta, ahankali take binsu ta yanda babu wanda zai gane cewar su takebi har suka shiga layin unguwar da suke,
.
Tsananin mamaki ne yakama khadija domin har wata zuciyar tana cemata wannan ba yusleem bane yayinda wata zuciyar kuma take gasgatata cewar shine,
Adaidai kofar gidan da suke suka sauka bayan hafsat tabaiwa mai keke napep din kudinshi, hannunshi rikeda na Hafsat suka fito zasu shiga ciki, saurin fitowa daga cikin motarta khadija tayi tabisu da sauri,
Dakin da suka shiga ta tasamma shiga domin yau ta rantse kuma ta dauri aniyar sai taga kwakwaf,
.
Suna shiga cikin dakin akan katifa suka yada zango, tunani Hafsat takeyi shin tafadawa yusleem yanda sukayi da dr sufyan ko tayi shiru saboda bata san abinda zaije yazo ba sannan bata son kuma tayi shiru wani abun yasake bullowa tarasa mafita,
Kanta taji yusleem yana shafawa ahankali yana yimata magana,
"Wai meke damunki ne?"
Kakaro murmushin dole tayi ta kalleshi,
"Babu komai yaya yusleem kawai dai nagaji ne"
Kafin wani acikinsu yakara magana tuni muryar khadija ta karade cikin kunnuwansu wacce ke tsaye akofar dakin tana doka musu sallama, Hafsat ce ta amsa sallamar sannan tatashi daga jikin yusleem inda take kwance ta tafi duba ko wacece ke sallamar domin ita duk atunaninta ma daya daga cikin yan hayar gidanne ke sallamar......
****
Kallon mamaki Hafsat ke yiwa khadija lokacin da ta fita kofar dakin domin ganin ko wacece ke sallama ganin khadijan yasata shiga cikin mamaki domin bata taba ganinta ba,
Dan gyara tsayuwarta kadan khadija tayi bayan ta zubawa Hafsat idanuwanta tana yimata kallon kurulla domin tun daga kafarta tafara kallonta har zuwa samanta,
"Baiwar Allah wakike nema?" Hafsat ta katse shirun nasu ta hanyar tambayar khadija,
"Ammm yusleem nagani shine nabiyoshi saboda ina son yin magana dashi.."
Shiru Hafsat tayi kafin tasake yin magana,
"Ok to amma daga ina kike kuma wa zance mishi?"
"Anan garin nake, kice mishi khadija mu'az ce.."
.
"To ina zuwa.." Hafsat tace tareda juyawa takoma cikin dakin,
Bin dukkan lungu da sako na gidan khadija keyi da kallo tana mamakin yanda akayi har yusleem yake iya yin rayuwa acikin wannan gidan na haya wanda babu komai na alatun more rayuwa aciki,
Acan cikin daki kuwa koda Hafsat takoma wurin yusleem zama tayi agefenshi gabanta yana faduwa,
"Yaya yusleem watace tazo nemanka wai sunanta khadija.."
Dan damm taga yayi kafin ya yunkura yatashi zaune,
"Yanaji kayi shiru ko akwai matsala ne? Ni tsoro nakeji kar asirinmu ya tonu,kar taje tafadawa mami.."
"Babu abinda zai faru insha Allah, ki shigo da ita"
Tashi Hafsat tayi ta sake lekawa inda khadija ke tsaye tana faman touching din phone dinta,
"Yawwa bismillah shigo.."
.
Tare suka shiga cikin dakin, ganin yanda dakin yake awani takure yasa khadija sake shiga cikin tsananin mamaki,
"Yusleem... Dagaske kaine anan? Me yafaru? Lafiya kuwa? Me yakawoka rayuwa a irin wannan gidan?"
Duk wadannan tambayoyin khadija ta jero sune cikeda mamaki lokacin da take yunkurin zama akasan carpet din dake dan shimfide agaban katifarsu,
"Yusleem wai dagaske kai dinne kodai idanuwana ne kemin gizo.."
"Khadija nine nan.." Yusleem yabata amsa yana kallonta,
Jijjiga kai tayi tagyara zamanta,
"To meya faru dakai har kazo nan? Saboda ni ban san wani abu yafaru dakaiba domin ko jiya agida da yamma muna tareda mami agidanmu.."
"Khadija wata matsala aka samu babba wadda ta tilasta min dawowa nan.."
"Amma dai mami bata saniba ko?"
"Ehh to gaskiya ban bari tasani ba har yanzun nan danake yimiki bayani saboda wani dalili.."
"To amma yusleem meyasa zakazo nan wurin kazauna? Irin wannan rayuwar sam bata dace dakai ba, dubi yanda duk kabi kasauya ka dawo wani kala..."
Murmushi yusleem yayi,
"Khadija kenan kin san dai ai komai yana faruwa ne da dalili, kawai dai ki kalli wannan a matsayin wata kaddara wacce take tawa kuma dole saita sameni.."
Jijjiga kai tayi,
"Hakane, to Allah ya rufa asiri.. Sannan insha Allah nayi alkawari zan baka gudun mawa dari bisa dari acikin rayuwarka.."
"Nagode khadija amma ni babu wata gudun mawa da nake nema daga gareki.."
Jin abinda yace yasa Hafsat saurin kallonshi, tashi khadija tayi tai musu sallama tafita, har kofar daki hafsat ta rakata bayan taga fitarta ne takoma wurin yusleem,
.
"Yaya yusleem gaskiya banji dadin abinda kafada ba, ai ni sai nake ganin ko babu komai wanda ya nuna yanayi dakai yafi..."
Bai barta takarasa ba yajata jikinshi ya rufe mata baki da hannunshi yana kallonta,
"Nanah akwai dalilin dayasa kikaji nafadi haka, wallahi ba dan Allah khadija zata taimaka mana ba, akwai wata manufa atare da ita.."
"Taya kasani?"
"Saboda khadija matatace ada, saida muka rabuda ita sannan na aureki.."
"To ai ba lallai bane abinda kake zargi yazama gaskiya ba, nidai dan Allah idan tasake dawowa next time karka yi mata irin wannan.."
Kura mata ido yayi saboda jin abinda tafada, lallabashi takoma yi har ya amince,
Washe gari da safe misalin karfe 11 saiga khadija tasake dawowa gidan lokacin hafsat na gyarawa yusleem farcenshi, da fara'a Hafsat ta karbeta suka gaisa, fuskar yusleem kuwa babu yabo babu fallasa,
Cigaba da yimishi gyaran farcen Hafsat tayi yayinda ita kuma khadija ta zauna tana kallonsu aranta tana tunanin yanda akayi har Hafsat tasamu irin wannan damar awurin yusleem domin abisa dukkan alamu tasamu fada mai girman gaske awurinshi sabanin su da ko kallo basu isheshi ba lokacin da yana tareda su,
.
Ajiyar zuciya ta dan sauke sannan ta kalli yusleem wanda idonshi ke kan hannayensu shida Hafsat wanda ta rike nashi cikin nata acikin zuciyar shi kuwa dan murmushi yakeyi saboda ganin yanda kalolin fatarsu guda biyu ta hadu tashi fari tata kuma bak'a,
"Uhmm yusleem dama cewa nayi bari nabiyo na dubaku saboda naga kamar baka da lafiya ko? Domin duk ka sauya"
Kafin yayi magana Hafsat ta amsa,
"Ehh wallahi zazzabi yake fama dashi amma hakanma da dan sauki.."
"Ayya Allah yakara bashi lafiya.."
"Amin.."
Kallo na tsanaki khadija ta rinka bin dakin dashi aranta tana mamakin tayadda akayi wai yusleem yadawo haka duk da cewar jiya yayi mata bayani amma gaskiya har yanzu bata gamsu da bayanin dayayi mata ba duba da irin tarin dukiyarshi da matsayinshi ada,
Mikewa tayi tsaye tana murmushi,
"Yawwa bari naje na tafi sai wani lokacin idan nadawo.."
Cikeda fara'a Hafsat ta kalleta,
"Zaki tafi? To mun gode madalla Allah yasaka da alkhairi.."
"Nagode khadija, sai anjima" yusleem ya fada yana damke hannun hafsat acikin nashi, fita khadija tayi tana fita yusleem yaja hafsat jikinshi yana murmushi, lakuce mata hanci yayi,
"Yau fa banga kinci abinci ba?"
"Kaima ai bakaci ba, gara ma ni amma kai yaushe rabonka da abinci"
Murmushi yayi ya matse kanta akan kirjinshi tayanda har tana iya jiyo bugun zuciyarshi,
.
"Hafsat wani tunani nafara gameda ke da rayuwarki..., ni ina ganin kodai in sawwake miki ne kitafi gidanku kije kici gaba da rayuwarki cikin kwanciyar hankali saboda nasan na takura rayuwarki da yawa ba kadanba..."
Jin abinda yafada yasa gabanta mummunan faduwa bayan zuciyarta ta harba da karfi, dagowa tayi ta kalleshi idanuwanshi sun danyi ja kadan, ganin ta kura mishi ido abinda bata taba yiba yasashi sake mayar da kanta ya kwantar bisa kirjinshi,
Daga shi har ita shiru sukayi babu wanda ya iya cewa uffan domin kowa da abinda yake sakawa acikin ransa.
Abangaren khadija kuwa bayan tafita daga wurinsu yusleem tafi minti goma sha biyar tana tsaye ajikin motarta takasa shiga, tunani take anya kuwa yadace tabar yusleem acikin wannan halin?
Girgiza kai tayi,
"Am sorry yusleem dan gaskiya yazama dole nasan abinyi..."
Shiga motarta tayi tai mata key tafita daga unguwar, fitarta keda wuya bata zame ako inaba sai gidan mami mahaifiyar yusleem, cikin sa'a kuma mamin na gida bata fita ko inaba,
Lokacin da khadija ta shiga kawataccen falon na mami mamin na cikin bedroom dinta tana shiryawa kamar me shirin zuwa unguwa, jin sallamar khadija yasata fitowa falo,
Kallo khadija ta dan bita dashi, tana sanye cikin wani swiss les dan gaske golden colour sannan tasaka sarka da earrings da warwaro duk golden gashi tasha jan lalle kai idan kaganta bazaka taba cewa ta ajiye samarin yara ba,zama mamin tayi tana murmushi saboda ganin khadija......
***
Gaisar da mami khadija tayi bayan sun gaisa ne khadijan tafara tunanin ta inda ya kamata ta bullowa da mami maganar yusleem, zuwa can dai ta dan nisa tace,
"Mami nikuwa yusleem yana kasar nan..?"
Murmushi mami tayi,
"Yusleem baya nan khadija, nikaina rabon da inyi magana dashi kota wayane anjima, daga yin tafiya shikenan shine har yau..."
Jijjiga kai khadija tayi,
"Ai kuwa Mami naga yusleem, yana nan agarin nan babu inda yaje domin naganshi da idona kuma har magana munyi dashi jiya da yau, yanzu ma daga wurinshi nataho nan.."
.
Mamakine ya bayyana akan fuskar mami,
"A ina kika ganshi khadija? Yaushe yadawo..?"
"Ai dama mami babu inda yusleem yaje yana cikin garin nan kawai dai wurin zama ya sauya, agaskiya mami na tausayawa halin da naga yusleem aciki.."
"Meya sameshi khadija? Dan Allah fada min idan wani abune ya sameshi" mami tayi maganar cikin rudewa,
"Ba wani abun tada hankali bane mami, kawai dai muje inkaiki gidan da yake ki ganshi da idonki.."
Da hanzari mami ta tashi tashiga bedroom dinta ta dauko mayafi ta fito jikinta har wani yar tsuma yake saboda taraddadin halin da zataje taga yusleem aciki,
Acikin motar khadija suka fita, ganin irin yanayin unguwar da khadija ke kokarin shigar dasu yasanya mami fara kokwanton anya kuwa khadija yusleem dinta tagani kuwa? Kasa hakuri mamin tayi har saida tayi magana,
"Khadija anya kuwa idanuwanki sun gane miki gaskiya?, me yusleem zaizo yayi anan? Sannan tayaya za ace waima yadawo kasar nan amma ni a matsayina ta mahaifiyarshi inkasa sani..."
.
"Mami ai magana kam takare tunda gamu munzo kofar gidan da yusleem ke ciki, zaki ganewa idonki komai"
Shiru kawai mami tayi amma bawai dan ta yarda da khadija bane a'a sai dan dai kawai ba abokiyar yin mahawararta bace shiyasa bazata yita jayayya da itaba,
Bude kofa kowaccensu tayi ta fito daga cikin motar, nan suka tasamma cikin gidan gadan gadan bayan khadija tarufe motarta,
Wani mamakin ne yasake lullube mami lokacin da suka shiga cikin gidan saboda yanda taga tsarin gidan yake dakuna ratata banda kaca kacan da gidan yayi sannan ga mata nan atsakar gidan kowacce tana harkar gabanta, watama ko riga babu saiko daurin kirji,
Kofar dakin da su yusleem suke khadija ta karasa dasu suka tsaya khadija tafara doka sallama,
Cikin barcin da ya daukesu sama sama kunnuwansu suka fara amsar sallamar da khadija keyi,
Hafsat ce ta dan bude idonta gamida sake kankame yusleem wanda take kwance ajikinshi,
Jin ansake kwada sallamar da karfi yasanyata tashi tana jan dan karamin tsaki, shi kanshi yusleem din shima baiji dadin wannan katse mishi baccin da akayi ba, juyi yayi yasake gyara kwanciyarshi ita kuma Hafsat ta dauki dan kwalinta tafita,
Tana yaye labulen tayi arba da mami da khadija wadanda ke tsaye akofar dakin, tamkar acikin mafarki haka Hafsat tagani, take kuma gabanta yashiga faduwa,
Tunda mami taga Hafsat tasan abinda khadija tabata labari gaskiyane dan haka yanzu bata da sauran kokwanto kuma,
Cikin rawar baki Hafsat tace,
"Mami..."
"Na'am Hafsat, ashe dagaske kuna nan kuna rayuwa batare da sanina ba..?" Mami tayi maganar cikin sanyin jiki,
"Mami shigo daga ciki"
.
Shiga cikin dakin mami tayi bayan tacire takalminta, cikeda mamaki take bin kowacce kusurwa ta cikin dakin da kallo wanda take ganinshi kamar dakin girki irin na kauye,
Har lokacin da suka shigo yusleem baisan cewar mami bace domin baccinshi yakeyi hankali kwance amma jin maganarta yasashi juyowa da sauri bayan yatashi,kallon mamin yakeyi fuskarsa dauke da mamaki gamida al'ajabi,
"Mamie..." Yakira sunanta yana mutsutstsuke ido,
"Yusleem wacce zuciyarce tabaka wannan mummunar shawarar har kazo nan kake rayuwa batare da sanina ba? Meyasa zakayi min karya?"
Wadannan sune tambayoyin da mami ta jefo masa batare da ta amsa kiran da yayi mata ba, fuskarta kunshe da fushi da bacin rai take kallonshi.......
***
Rasa abinda zaice yusleem yayi illa kallon mamin da yakeyi wadda itama shi take kallo kafin daga bisani ta mayar da kallonta kan Hafsat wacce ta sunkuyar da kanta kasa,
Dakin nasu mami takoma tafara kallo kusurwa bayan kusurwa,
"Mami dan Allah kiyi hakuri wallahi akwai kwakkwaran dalilin da yasa kikaga hakan tafaru, zamuyi miki bayanin komai...." Hafsat tayi karfin halin yin magana,
Mami bata bawa Hafsat amsar maganarta ba illa sake balbale yusleem da fada da tayi,
.
"Ka dauko yarinyar mutane kazo ka ajiyeta anan kana wahalar da ita, dubi yanda takoma, kalli kaima yanda ka zama duk kabi ka rame kayi baki daga gani kana cikin mawuyacin hali, to da ace khadija bata ganku taje ta fada minba da sai yaushe zaku nemeni? Da sai ka kashe musu 'ya sannan zakaje min da mummunan labari? Yayi kyau"
Mikewa mami tayi ta kalli khadija wacce ke zaune ta sunkuyar da kai tana sauraren duk abubuwan dake faruwa,
"Tashi mu tafi khadija"
Kallon yusleem mami tayi,
"Kai kuma na baka nanda mintuna 20 ku tattaro duk kayanku kuzo gida ku sameni, idan kuka wuce haka to ina mai tabbatar maka ranka sai ya baci.."
.
Fita mami tayi daga cikin dakin khadija ta rufa mata baya,
Kallon yusleem Hafsat tayi bayan mami tafita,
"Yaya yusleem katashi mu bita, idan munje gidan sai muyi mata bayani atsanake kaga kamar fa tayi fushi..."
Dafe kanshi yayi wanda ke yimasa wani irin ciwo,
"Kibari kawai muci gaba da zama anan idan ta huce sai muje mu bata hakuri"
Girgiza kai tayi bayan ta rike hannunshi cikin nata,
"A'a yaya yusleem, mubi umarninta mu tattara kayanmu muje, bai kamata muyi watsi da maganarta ba.."
Tashi tayi batare da tajira abinda zaiceba ta shiga tattara kaya dama kuma kayan ba wadansu masu yawa bane, cikin toilet ta shiga ta kwaso inner wears dinsu dake shanye tazo ta zuba acikin trolley, har lokacin yusleem na zaune baiko motsa ba,
Kayan da tasan bazai yiyu su tafi dasu yanzuba ta tattara wuri daya ta adana sannan tafita daga dakin taje dakin maman amir tayi mata sallama, kasancewar sunyi sabo maman amir harda kuka, ita kanta Hafsat din da hawaye tadawo cikin dakin,
.
Tashi yayi ya rungumota jikinshi yana murmushi,
"Menene na kukan kamar ance bazaku sake haduwa ba..., sorry.."
Har lokacin hawayen basu bar zuba a idonta ba,
"Ya isa haka, kiyi shiru dan Allah"
Dakyar ta iya tsayar da hawayen yusleem ya dauki trolley dinsu suka fita acikin ranshi yana mamakin mata su babu wuya yanzun nan zasuyi maka kuka,
Har waje mutanen gidan suka rakasu duk da ba wai wani zumunci mai zurfi sukeyi ba,
Adaidaita sahu suka shiga yakaisu har gidan mami,
.
Gidan yana nan kamar da babu abinda ya sauya sannan ga ma'aikata nan kowa yana aikinsa kamar yanda suka saba, ganin su yusleem yasa masu gadin gidan saurin amsar kayan dake hannunsu suka shigar musu dashi ciki,kowa sai sannu da zuwa yake yiwa yusleem domin duk atunaninsu daga doguwar tafiya yadawo,
Acikin falo suka iske mami tana zaune tana shan ruwan lipton sannan ga soyayyen chips with kidney sos tana dan tsakura kadan kadan tana ci da dukkan alamu sai yanzu take yin breakfast,
.
Jin sallamarsu yasanyata dagowa ta kallesu bayan ta amsa, akasa Hafsat ta zauna yayinda yusleem yazauna akujerar dake kusa da ta mami,
"Hafsa ga abinci can maza tashi kije kici kinji..."
"Wallahi mami munci abinci sai dai idan anjima.."
Shiru mamin tayi batace komai ba taci gaba da kurbar ruwan tea dinta, suna nan zaune shiru babu wanda yasake magana har mami ta kammala cin abincin,
Sunkuyar da kai Hafsat tayi tasoma bawa mami hakuri,
.
"Mami dan Allah kiyi hakuri da abinda yafaru, wallahi ba laifinsa bane laifina ne domin nice nabashi wannan shawarar kuma nima nayi hakanne dan gudun kada mu tayar miki da hankali, amma dan Allah kiyi hakuri.."
Ajiyar zuciya mami tayi ta kalli yusleem sannan ta kalli Hafsat,
"To shikenan Hafsat nahakura, amma meyake faruwa? Nasan dai duk yanda akayi akwai abinda ke faruwa daku"
"Ehh mami da akwai, bashin banki yaya yusleem yaci sukuma kin san dokarsu idan baka biyasu ba sai sun sayar da komai naka, to shima yaya yusleem din hakance tafaru kuma lokacin nasan idan kikaji hankalinki tashi zaiyi shiyasa nace mubari tukunna sai zuwa wani lokaci sai mu fada miki..."
.
Tafa hannuwa mami tashiga yi tana salati,
"To garin yaya?"
Kallon yusleem tayi,
"Kai agarin yaya kaciyo bashin banki batare da sanina ba?"
"Mami tsautsayi da kaddara, saboda dama tun asali da wannan bashin nasu nayi arziki, komai da kika sani nasune, nikuma nayi hakanne dan incika burinki inzama mai wadata kamar yadda kike muradi..."
Katse shi mami tayi cikin fada tace,
"Ungo nan.." Dakuwa tayi masa sannan ta dora da cewa,
"Shikenan kuma dan ina son kayi arziki sai kaje ka aikata ba daidai ba? Ai ni bance kayi kudi kota halin kaka ba, haba yusleem meyasa zakabi shawarar zuciya? Ko dan gaba karka sake aikata makamancin wannan, yanzu da ace sun kamaka sunje sun daureka me gari yawaya?"
.
Dan zamewa yayi ya jingina bayanshi da jikin kujerar ya lumshe idanuwansa,
Kallon Hafsat mami tayi,
"Bashida lafiya ko?"
"Ehh mami amma da sauki, matsalar dai baya iya cin abinci"
Shiru mami tayi ta danyi tagumi,
.
"Hakika wannan wata jarrabawa ce daga Allah, domin ni dinma duk kudaden dake cikin account dina na turawa yan makaranta domin sun kusa dawowa, gashi na sissiyo kayan abinci wadanda zasuyi mana 1 month,ma'aikatan gidan nan ma wallahi wannan watan ko albashi ban biyasu ba nace suyi hakuri sai yusleem yadawo.."
"To ai babu komai mami duk wannan ba wani abu bane Allah zai bamu mafita" inji Hafsat,
"To hafsa rashin lafiyar tashifa? Ni duk ita tafi daga min hankali"
"Mami babu komai insha Allah zai samu lafiya, gobe zamu sake komawa asibitin ma ayi masa test..."
.
"To wai menene ke damunsa?" Mamin ta tambaya cikin damuwa,
"Mami harda ulcer dai saboda baya cin abinci wallahi"
"To Allah yabashi lafiya, goben sai muje asibitin mugani"
Shi dai yusleem yana jinsu baiyi magana ba da zaman kujerar ya isheshi ma dakin surayya yashiga wanda yake makotaka da na mami yaje ya kwanta akan gadonta,
Ita kuma mami afalo duk tabi ta damu sai jajanta rashin lafiyar yusleem takeyi, Hafsat dince ma mai karfin halin kwantarwa da mamin hankali tana cewa babu komai,
Saida lokacin salla yayi sannan Hafsat ta dauki kayanta ta nufi bedroom din surayya, akwance ta samu yusleem amma ba bacci yakeyi ba,
"Yaya yusleem tashi kayi salla..."
.
Tashi yayi yana kallonta,
"Hafsat meyasa baki fadawa mami gaskiyar abinda yafaru ba? Saboda ko dan nan gaba ya kamata ace tasani"
Zama tayi kusa dashi,
"A'a yaya yusleem fadar bata da alfanu hakan dai da akayi shine daidai"
"Shikenan.." Abinda yace kenan yatashi zai fita, bin bayanshi tayi zuwa falo ta dauki trolley din kayanshi tabishi, part dinsu Abdul ya bude yashiga, bedrooms biyu ne aciki sai falo domin suma samarin kowa da dakinshi, dakin khalifa yashiga tana biye dashi, juyawa yayi ya kalleta,
"Wai kina nufin ke adakin surayya zaki zauna?"
"Ehh mana"
Murmushi yayi ya karbi trolley din hannunta,
.
"Ashe dama karya kike da kikace bazaki iya kwana babu niba.."
Murmushi ne ya kwace mata tajuya zata fice yayi hanzarin rikota,
"Debo kayanki kidawo nan"
"Tohm" ta amsa amma bawai aikatawar zatayi ba domin tana jin nauyin mami ba kadanba,
Sakinta yayi tafita shikuma ya nufi cikin toilet.
Koda takoma part din mami salla tayi tafito falo nan ta hango kuku yana shirya lunch akan table, fitowar mami ne ya katse mata tunaninta,
Kan table suka hau, fried spaghetti da salad kukun yadafa sai kunun shinkafa, suna ci suna hira har suka gama, kunun Hafsat ta dauka tatafi kaiwa yusleem ko zai iya sha,
Akan carpet din salla ta sameshi yana tura sako ta email dinshi ackin laptop,
"Yaya yusleem ga kunu.."
.
Dagowa yayi ya karba ya dan kurba, zama tayi agefen gado, babu laifi yadan sha kunun ganin haka yasa taji dadi sosai, maganinshi ta dauko mishi ya karba ya hadiya daga nan tatashi tafita.
Wayarta ta Kunna bayan ta koma, ko minti biyu ba ayiba Ummi takirata, cikeda zumudi ta dauka suka gaisa nan take fadawa ummin cewar yau suka dawo amma suna gidan mami,
Suna gama waya da ummin kiran Amina yashigo, ita dinma korafin bata samunta awaya tayita yimata gashi ta jima da haihuwa mijinta yanata zuwa gidan domin yafada mata amma baya samunsu, Allah yaraya Hafsat tayi mata tace sunyi tafiya ne amma tunda sun dawo tana nan zuwa,
Komawa wurin mami tayi bayan sunyi sallama da Amina, nan take fadawa mami yusleem yadan sha kunun da takai masa tunda hakane zata rinka dama masa kullum.
Misalin karfe 8:30 nadare suna zaune afalo suna kallon tashar zee world itada mami sai gashi yashigo da cup din kunun data kaimasa, zama yayi yasoma kurbar kunun, Hafsat da mamine ke dan yin hira lokaci zuwa lokaci yana zaune yana jinsu,
Yana kallo hafsat ta shige daki bayan tayi musu saida safe, itama mami ba ajima ba tashiga nata dakin suka barshi afalo shi kadai, sai wurin 11 yakashe tv da sauran kayan wutar dake cikin falon, dakin surayya wadda Hafsat ke ciki ya shiga ya maida kofa ya rufe, gani yayi harta jima da yin bacci, bargon yabude yashiga yayi kwanciyarshi tareda mannuwa ajikinta.
Said a asubah sannan Hafsat tasan yana cikin dakin, tashi tayi tashiga bathroom tayi alwala tafito, ahankali tafara tashinsa saboda bata son mami ta jiyo,
.
Tashi yayi yana lullumshe ido alamun baccin bai isheshi ba,
"Yaya yusleem katafi saida safe..."
Hammar da yafara ya karasa sannan ya kalleta,
"Ina zan tafi?"
"Masaukinka..."
Baice komai ba yasauka daga kan gadon yanufi toilet, lokacin da yafito har ta idar da raka'atanul fijr tana kokarin tada ikamar sallar asubah,
Tashi yayi yakoma kan gadon ya kwanta bayan ya idar da sallar, yana kokarin lulluba da bargo Hafsat ta bazamo tazo tana masa magana kasa kasa,
"Dan Allah yaya yusleem katafi.."
"Ina?"
.
"Dakinka mana, bana son mami tazo taganka"
Kafin yabata amsa suka fara jiyo knocking abakin kofa da sauri Hafsat ta diro, maganar mami tajiyo tana cewa,
"Hafsat, Hafsat kitashi asubah tayi.."
"Na'am mami"
"Au ko kin tashi ma?"
"Ehh mami"
"To shikenan.."
Daga nan tajiyo alamun tafiyar mami,hannu ya mika mata yana daga kwance,kafada ta makale ta kwabe fuska, shi dinma hakan yayi kamar yadda tayi,
"Zo dan Allah"
Kan gadon ta hau ta mika masa nata hannun, kama hannun nata yayi yajata ya kwantar da ita yaja musu bargo.
_Fatan alkhairi ga Hajjaju, Chuchu, Maman sultan, pheey, Maman humy, Anty sis, Dshanty, Reane_Gh,meela adeel,meernah parrot,khadija sadeeq,Billy s fari, Billy s jega, ummu abrar, anty Baraka, Maman mujahid da duk wadanda ban ambata ba, wannan shafin nakune kyauta domin jin dadinku._
*
***Misalin karfe 9 Hafsat tafarka daga bacci, juyawa tayi ta kalli yusleem wanda ke rike da hannunta yana kanannade da ita, dakyar ta iya tureshi daga jikinta ta tashi,
Wanka tashiga tayi tafito ta shirya agurguje, falo ta leka tagani ko mami tafito domin sam bata so mamin ta fahimci cewar yusleem awurinta ya kwana, ganin mami bata fito ba sai masu aiki dake faman mopping din falon yasata sakin ajiyar zuciya,
Juyawa tayi tasake komawa cikin dakin, tashinsa tasoma yi tana dan bubbuga gefen pillow din da kanshi ke kai,
"Yaya yusleem...,yaya yusleem katashi"
Ido guda daya ya bude ya kalleta,
"Me zan yi miki?"
"Safiya fa tajima dayi dan Allah katashi"
.
Mayar da idonshi yayi ya rufe yajuya mata baya yasake jan bargo ya lulluba, tashi tayi tafita, kuku ta hango yana jera musu breakfast akan dining,
Zama tayi acikin falon tama rasa me zatayi, ajiyar zuciya tayi aranta tana fadin dama matsalar gidan masu kudi kenan ko katashi da wuri karasa abinda zakayi,
Tana nan zaune tana kallon shirin gari yawaye a tashar arewa 24 har mami tafito, kamar kullum mamin tasha kwalliya kamar me shirin zuwa gidan biki,
Sauka kasa tayi tagaida mami, cikin fara'a da sakin fuska mami ta amsa domin tana jin son Hafsat tamkar na yar da ta haifa,
Kan dining suka dunguma suka fara karyawa,suna daf da gamawa mami ta kalleta tace,
"Shi wannan sarkin baccin bai tashi bane? Ai da yatashi saboda maganar zuwa asibitin ko"
"Ehh gaskiya kam, bari nagama sai inje in tasoshi.."
Kafin Hafsat ta rufe baki sai gashi ya bude kofa yafito yana yamutsa fuska, sunkuyar da kai Hafsat tayi kamar ruwa ya cinyeta, mami kuwa dubanshi tayi ta kawar da kai,
"Ka manta da maganar zuwa asibitinne kaki tashi da wuri?"
.
"Wallahi ina sane mami, ban manta ba" yakarasa maganar yana kallon Hafsat ta gefen ido wadda yasan ba haka tasoba,
"To ai sai kaje kashirya.."
Wucewa yayi yafita zuwa part din su khalifa, wanka yayi yafito ya zauna domin shafa mai, yana zama Hafsat tashigo hannunta rikeda jug dan madaidaici,
"Ga kunun..."
"Babu gaisuwa?"
.
Yafada lokacin da yake shafa man a hannayenshi,
"Ina kwana?"
"Ni bazan amsa ba, zo nan.."
Dan sake matsawa tayi tana kallonsa,
"Gani.."
"Kinsa Mamie tana yimin fada ko, bayan kuma kece kikayi sanadiyyar makarata saboda dumin jikinki da naji"
Juyawa tayi zata fita daga dakin fuskarta dauke da murmushi,
"Zo nan, Allah karki fita"
Dawowa tayi ta tsaya, tana nan tsaye har yagama shiryawa ya dauki kayanshi yasa,
.
Kunun da ta Kawo mishi yasha sannan suka fita domin Tafiya asibiti,
Afalo suka iske mami cikin shiri nan suka dunguma domin tafiya amma kuma suna fitowa compound din gidan sai ga motar khadija ta kunno kai kuma tareda mahaifiyarta suke wannan dalilinne yasa mami fasa zuwa asibitin tace da yusleem da Hafsat kawai suje driver yakaisu ita kuma takoma ciki itada hajiya fa'iza da khadija,
Ganin irin gaisuwar da yusleem sukayi shida khadija yasa Hafsat yimasa magana domin daurewa khadija fuska taga yakeyi bayan kuma ita bataga laifinta ba, ganin baya son maganar yasata yin shiru ta kyaleshi.
Lokacin da sukaje asibitin Hafsat kin shiga office din dr sufyan tayi tai zamanta awaje sai yusleem ne yashiga shi kadai, ya dan jima aciki kafin yafito,
"Yaya yusleem ya kukayi?"
"Yace nanda 4 days nakara dawowa lokacin result din taste din da yayi min yafito.."
"To Allah dai ya jiyar damu alkhairi"
.
"Amin, muje mu tafi gida tunda babu abinda yayi saura, Dr din yana tambayarki wai yau banzo da matata ba nace tare ai muke kina waje wai ai dama yasan bazaki barni nazo ni daya ba..."
Dan murmushin yake tayi batace komai ba amma acikin ranta fadi take "Dan iskan Dr",
Lokacin da suka koma gida sai mami ita kadai domin su khadija sun tafi, ganin sun dawo da wuri mami tace Hafsat ta shirya taje driver yakaita gidansu tagaisa da iyayenta,
Garin dakakkiyar busasshiyar kubewa da kuka da daddawa wanda Maman khadija ta Kawo wa mami su mamin tabawa Hafsat tace takaiwa umminta tsaraba,
.
Yusleem yana kwance akan kujera mami na kujerar kusa dashi Hafsat din tafito zata tafi,
"Mami idan nadawo zan biya ta gidan amina kawata, haihuwa tayi shine zanje inga babyn.."
"To sai kin dawo, Allah ya raya.. Ki gaida hajiya kubran"
"To mami zataji"
Fita tayi nan yusleem yatashi yabita, tana daf da fita daga cikin kitchen yayi saurin rikota,
"Mami zaki tambaya unguwa saboda itace take aurenki ko? To gidanku kadai na amince kije daga nan karkije ko ina"
Juyawa yayi zai koma falo tayi saurin rikoshi,
"Dan Allah kayi hakuri yaya yusleem.. Kaji"
Shiru yayi mata ita kuma taci gaba da yimasa magiya, dakyar ya amince yace taje.
Acikin kitchen ta iske Ummi lokacin dataje gidan, ba karamin dadin ganinta hajiya kubra tajiba nan suka baje suka fara hira irinta uwa da 'ya da haka har Alhaji sa'id yazo ya samesu yadawo daga buga bugarsa domin shima ya haduda jarrabawa irinta rayuwa sai dai ita Hafsat bata saniba har saida ummi tayi mata bayanin abubuwan da suka faru na iftila'in da ya afkawa alhaji sa'id din bayan ya sayar da kadarorinsa ya tura asiyo masa kayayyaki amma har yau kayan basu fitoba gashi saboda rashin kudi kwangilar ma ba samuwa takeyi ba dan dai kawai yanada amini ne mai fada aji,
.
Kuka Hafsat tayi ba kadanba dalilin jin wannan labarin da hajiya kubra ta bata amma kuma tasan jarrabawa ce daga Allah shiyasa ma bata daga hankalinta ba,
Dayake sun dade basu hadu da umminba yasa Hafsat takasa tafiya da wuri har saida aka kira sallar magrib, bayan tayi sallane tatafi lokacin driver yazo daukarta, ko gidan aminan ma bataje ba gida ta wuce direct,
Mami kadai ta tarar afalo tana waya da surayya nan ta zauna har mami ta kammala wayar itama tabata suka gaisa domin rabonsu da juna tun lokacin da surayyan takoma school,
"Hafsa kin dawo? Ya kika baro mutanen gidan?" Mami ta tambaya tana kokarin ajiye wayarta,
"Lafiya lau mami, suna nan lafiya, Ummi tana gaidaki tace ayi miki godiya..."
"Babu komai wallahi, kayan ma nawa suke.."
.
Zama sukayi dan shiru suna kallon tv zuwa can Hafsat ta mike ta nufi bedroom, tana shiga ta iske yusleem akwance,
"Lafiya kuwa yaya yusleem?" Ta tambaya,
"Wallahi zazzabi ke damuna hafsa"
Ahanzarce takarasa kusa dashi jin jikinsa zafi zauuu tayi gashi yana dafe da cikinsa wanda ke ta faman murda masa,sannu ta shiga yimasa yana amsawa dakyar, zuwa can taji ya kamo hannunta ya dora akan cikin nasa,
Jikinta rawa yafara saboda ganin yanda yusleem yake yin murkususu gashi bata son taje tafadawa mami hankalinta yatashi,
.
Ruwan sanyi ta dauko tasoma shafa masa acikin nashi nan yaji ciwon yafara lafa masa ahaka har bacci ya daukeshi, ganin yasamu bacci yasa ta fita wurin mami wadda take zaune akan abin salla ta idar da sallar isha tana jan carbi,
"Hafsa ga tuwo can, wallahi yau shi naji ina sha'awa shine nace kuku yayi.."
Murmushin yake Hafsat tayi ta girgiza kai,
"Kafin nataho ma agidan Ummi saida naci abinci,wallahi na koshi.."
Wuri tasamu ta zauna amma lokaci zuwa lokaci tana dan shiga bedroom din taduba yusleem sai dai har 10 tayi bai tashiba, har sukayi sallama da mami tashiga dakinta itama ta shiga daki yusleem bacci yake,
Akusa dashi ta kwanta tana kallonshi yana rike da cikinshi, sai wurin 11 sannan yatashi yayi sallar magrib da isha wadanda ke kanshi domin bai samu damar yiba,
.
Kalau yayi sallar ya idar tana zaune tana kallonshi yana idarwa kuma yace sai ta dama masa kunu yasha yunwa yakeji, tare suka fita zuwa kitchen din ta tafasa ruwa ta dama masa kunun suka koma daki, saida yagama sha sannan suka kwanta, tana ji yafara tsokanarta kamar bashi bane dazu yake murkususu kamar zai mutuba,
.
Bata San lokacin da yagama tsokanar tataba domin bacci tayi tabarshi, can tsakiyar dare kuma kamar acikin mafarki take jin kakarin amai nan tatashi taganshi kwance yana juyi yana rikeda cikinsa, ruwan sanyi ta debo tafara shafa masa amma yanzu ji yake kamar ruwan zafi tafasasshe take Shafa masa, kunun da yasha kuwa saida yayi amansa gaba daya,rikeshi tayi nan ya kuwa kankameta kamar zai koma cikin cikinta daga shi har ita babu wanda yasake runtsawa har asuba tayi ita dai agaba tasashi tana hawaye,
.
Ganin abin yayi yawa gashi yana yin wani irin amai kore kore yellow yellow yasa hafsa zuwa ta sanarwa da mami lokacin karfe 5:30,
Driver mami tayiwa waya kasancewar a B/Q yake zaune, nan da nan yafito suka kama yusleem suka nufi asibitin Dr sufyan dashi,
Kallo daya zaka yiwa mami da Hafsat kagane acikin tashin hankali suke domin kowannensu fuskarshi kunshe take da tashin hankalin,
Emergency aka kai yusleem bayan kamar mintuna 30 Dr mufid yafito dauke da file din yusleem domin lokacin Dr sufyan bai fitoba,binsa mami da Hafsat sukayi abaya domin jin abinda zaice,
"Hajiya in my opinion ni ina ganin cewar is better for u idan kuka fitar da patient dinku kasar Cairo ko kuma India saboda sincerely speaking yana cikin bad condition domin cutar dake tattare dashi itace take cousing din wannan ciwon cikin da yake fama dashi, and kuma akwai wani aiki da zasuyi masa wanda mu bazamu iyaba, so idan zai yuyu in the next 3 days ku samar masa visa sai ku fita dashi domin magana tagaskiya bama karbar patients wadanda lalurarsu tazama chronic kuma worst saboda kinga nan is private hospital dole sai mun zama muna him takatsantsan..."
Yana ida wannan bayanin yagyara farin glass dinshi yayi gaba, sororo mami da Hafsat sukayi kowannensu yana tunanin hanyar da za abi har akai ga fitar da yusleem kasar waje....
0 comments:
Post a Comment