ALWASHI Page 26-30
***
Daga mami har Hafsat ji sukayi kamar ruwa ya cinyesu dalilin jin bayanin da dr yayi musu nan hankalin kowanne acikinsu yakai kololuwar tashi,
Mami ce tafara magana fuskarta cikeda murmushin yake,
"Hafsat babu komai kinji, karki daga hankalinki insha Allah zamu samu yanda zamuyi..."
Wasu hawaye ne suka zubowa Hafsat tasa gefen hijabinta ta share batare da tayi magana ba,
Kama hannunta taji mami tayi suka bar wurin suka koma reception,
"Yanzu Hafsat ina zuwa bari naje gida nadawo kinji..."
"To mami sai kin dawo, Allah kiyaye hanya.."
Tashi mami tayi tafita, yayinda ita kuma Hafsat taci gaba da zama awurin zuciyarta kunshe fal da tarin tunani.
Tana nan zaune tarasa abinda yake mata dadi tahango dr sufyan yana kokarin shigowa cikin reception din hannunsa dauke da wata yar madaidaiciyar bag, ko kallonsa batayi ba ta dauke kanta takaishi can gefe, shikuwa kura mata ido yayi har ya bace ya nufi office dinshi,
.
Kimanin mintuna 30 da tafiyar mami sai gata ta dawo, tun kallon farko da Hafsat tayi mata ta fahimci cewar akwai damuwa a tattare da ita amma dai sai batayi magana ba domin daga ita har mami din kowa ba son yin maganar yake ba,
Emergency suka shiga wurin da yusleem ke kwance yana bacci, gaban gadon sukaje suna kallonsa,
"Ni wannan abu ya daure min kai, wai menene takamaimai abinda yake damunsa ne? Ni duk ban fahimci bayanin da Dr yayiba hafsat..." Mami tayi maganar idanuwanta na kan yusleem wanda yake kwance yana fitar da numfashi,
"To nima dai mami maganar dr ta daure min kai amma a iya sanina dai wannan ciwon cikin shine ke damun yaya yusleem"
"To ko komawa zanyi wurin Dr din insake tuntubarsa inji?"
"A'a mami da dai mun hakura kawai munyi yanda yace din.."
"To yanzu hafsat ina zamu samu kudaden da zamuyi hakan? Hafsat yanzu ba babu abinda muka mallaka inbanda wannan motar kwaya daya da nake hawa sai ko gidan da muke ciki..."
"Babu komai mami ki kwantar da hankalinki insha Allah komai zai zama daidai saboda Allah baya taba dorawa bawansa abinda bazai iyaba"
Ajiyar zuciya mami ta yi suka fita daga cikin emergency room din suka koma waje suka zauna,
Wuni guda cur yusleem yana bacci sai yamma yafarka, hafsat ce ta karasa wurinsa domin ita mami tatafi gida ta dawo wanda tafiyar tata bazata rasa nasaba ba dayin wanka sannan da shiryo abinci,
"Sannu yaya yusleem.."
Kai ya daga mata ya lumshe idanuwansa,
"Yaya yusleem zaka sha kunun?"
Girgiza mata kai yayi bayan ya bude idonsa, kicin kicin yaga tayi tabata fuska kamar zata saka kuka, ganin haka yasashi daga mata kai alamun zaisha,ita kanta tana lura dashi sam yanzu baya son yaga bacin ranta,
.
Dan murmushi tayi ta tsiyayo masa kunun acikin cup ta zauna agefen gadon, yunkurawa yayi yafara kokarin tashi ta taimaka masa, duk da cewar dakin basu kadai bane akwai mutane da yawa aciki amma haka ta rinka bashi abaki yana kurba idan kuma ya disa sai ta lashe, kallonta kawai yake yi da idanuwanshi wadanda suka dan firfito har tagama bashi duk da dai bai shanyeba amma yadan sha dayawa,
Taimaka masa tayi ya kwanta ta gyara masa kwanciyar, ta zauna tana kallonshi, hannunta taji ya riko acikin nashi tareda lumshe idanuwanshi ahaka har wani baccin ya sake daukarshi.
Zuba mishi ido tayi takai hannunta bisa kuncinshi tasoma shafawa ahankali tana jin wani irin tunani yana ratsa zuciyarta, ahaka Mami ta dawo ta isketa jikinta sukuku wanda daga gani ranta abace yake gaba daya,
Jugum sukayi babu wanda yake yin magana acikinsu har tsawon wani lokaci domin kowa shi yasan tunanin da yakeyi,sai can Mami tayi karfin halin yiwa hafsat magana,
"Hafsa kitafi gida kije kiyi wanka sai kidawo.."
Duk da bata son tafiyar amma bata musawa Mami ba haka tayi mata sallama tatafi bayan ta leka yusleem ta window nan taganshi har lokacin bacci yakeyi ga drip nan ahannunshi wanda ba ajima da daura masa ba domin duk jikinshi yayi yaushi,
Mami saida ta tabbatar da cewa hafsat tatafi sannan tatashi ta nufi office din Dr sufyan,
Kimanin mintuna samada arba'in mamin ta shafe acikin office din na dr sufyan sannan daga bisani tafito, tana zama hafsat nadawowa,
.
Zama suka cigaba dayi har zuwa dare, lokacin ne aka fito da yusleem daga emergency aka kaishi wani daki wanda gado ne guda daya aciki irin na marassa lafiya sai fridge dan karami sannan ga yar karamar tv nan daure ajikin bango sai dan madaidaicin bathroom aciki,
"Hajiya wannan dakin kwana uku kadai zamu bashi muna treating dinshi domin dama narigada nafada miki cewar fitar dashi outside shine kadai solution agareku, therefore nan da 3 days zamu baku sallama so sai kuje gida kuci gaba da kula dashi idan kuma before time din kun sami kudin fitar dashi outside sai ku fitar dashi.." Dr mufid yafada yana sunkuye yana rubutu ajikin file din yusleem,
Kallonshi Mami da hafsat sukayi har ya kammala jawabin sannan yafita,
"Hafsat wuce kije kitafi gida ki kwanta inyaso idan Allah ya nuna mana gobe sai musan abinyi.."
Girgiza kai hafsat tayi ta kalli mami,
"A'a Mami kibarni anan din ke kitafi gida, ni zan kwana tare dashi.."
"Hafsat kije ki huta kinji, babu komai"
"Dan Allah mami kibarni kitafi, wallahi ko naje gidan ba iya barci zanyi ba"
"To shikenan tunda kinki, bari ni naje natafi, Allah yabashi lafiya"
"Amin mami"
Saida mamin tasake duba yusleem din sannan tayiwa hafsa sallama tatafi,tana fita harabar asibitin tahango dr sufyan tsaye ajikin motarshi kirar Benz new series 2017 yana sanye cikin kananan kaya, wurinshi mami takarasa dama abisa dukkan alamu ita yake zaman jira, bude mata kofar motar yayi tashiga tazauna sannan yazagaya side dinshi bayan yarufe yaja motar suka bar harabar asibitin.
.
Cikin dakin hafsat tashiga ta zauna akan wata kujera tana kallon yusleem wanda keta faman barci, lokaci daya ta tashi zunbur ta isa gefen gadon ta zauna, bude idonshi taga yayi,
"Sannu yaya yusleem"
Kai ya daga mata sannan yadanyi murmushi,
"Yaya yusleem ko kana bukatar wani abu ne..?"
Kanshi ya girgiza har lokacin fuskarshi tana dauke da murmushi, shiru tayi ta dan jingina da jikin bango, gyangyadi ta dan soma yi amma da zarar baccin yafara daukarta zatayi firgigit ta bude idonta,
Matsawa yusleem ya danyi yakamo hannunta, idonta Wanda yake cike da barci ya bude domin daren jiya bata samu tayi ba,
"Kizo ki kwanta..."
"Bari inshinfida hijabina akasa kawai sai in kwanta saboda kar intakura maka"
"Gashi na matsa miki"
Girgiza kai tayi zata sauka daga kan gadon, tashi shima yayi da niyyar sauka tayi saurin rikeshi,
"Haba yaya yusleem kaida bakada lafiya,dan Allah kakoma ka kwanta"
Dakyar ya kwanta din hannunshi rikeda ita dole ta hakura ta kwanta akusa dashi,
.
Sassafe saiga mami tazo, office din dr sufyan tafara zuwa amma lokacin bai fitoba, wurinsu hafsa taje, hafsat din tana zaune akan kujera shikuma yusleem yana kan gado akwance,
Tare da mamin suka cigaba da zama har karfe 9 tayi lokacinne driver yakawo musu abinci amma ita mami bata samu damar cin abincin ba domin hankalinta yana can office din Dr sufyan, hajiya kubra da alhaji sa'id ne suka zo duba yusleem din bayan an dan gaggaisa mami ta zare jikinta ta fita, office din Dr sufyan tashiga wanda yake abude alamun yana ciki,
Lokacin da hafsat tafito domin raka su hajiya kubra sukayi kicibus da mami, godiya mami tayiwa su hajiya kubra sukayi sallama suka wuce ita kuma tanufi dakin da yusleem yake,
Hafsat kam saida ta rakasu har wurinda motarsu take sannan tajuya ta takoma, tana shiga cikin dakin ta iske mami tana shirya kudi rafa rafa sabbi kal yan dubu dubu acikin jakarta wadanda zasu doshi samada naira dubu dari tara, cikeda mamaki hafsat ta karasa gaban mami wacce ke zaune akan kujera.....
_Fans kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu, kun san jiki da jini amma alhamdulillah naji sauki sosai, hakika bani da bakin da zan gode muku,duk wadanda suka kirani suka gaisheni da wadanda suka min text nagode Allah yabar zumunci._
*
Gaban Mami hafsat takarasa ta tsugunna fuskarta cikeda mamaki,
"Mami wannan kudin fa?"
Fadada murmushi mami tayi batare da ta dago ta kalli hafsat ba domin hankalinta yanaga kan kudin da take lissafawa,
.
"Hafsat wani al'amari ne ya gudana wanda yayi sanadiyyar samuwar wannan kudin, kinga dr kwana uku kacal yabamu yace daga nan sallamace zata biyo baya to shiyasa naga gara fa intashi atsaye innemo kudi duk inda yake domin mu fitar da yusleem kasar Cairo.."
"Hakane mami, amma yanzu kin san kudi yana wuyar samuwa shiyasa nace garin yaya aka samo wadannan kudaden masu yawa.."
Rufe handbag din mami tayi ta maida hankalinta gurin hafsat da niyyar yimata bayani amma kafin takai ga farawa sukaji anturo kofar dakin da suke ciki anshigo, dukkaninsu maida idanuwansu wurin sukayi domin ganin wanda zai shigo,
Khadija ce ta shigo hannunta rikeda basket din abinci, tana sanye cikin bakar doguwar riga ta yane kanta da mayafin rigar inbanda kamshi babu abinda take zubawa,
"A'a khadija ce? Sannu da zuwa" mami tayi maganar tana fadada fara'arta,
"Yawwa sannu mami" khadija tafada tareda ajiye basket din hannunta ta durkusa kasa tagaida mami,
"Mami ina kwana? Ya mai jikin? Allah yabashi lafiya"
Cikin raha mami ta amsa gaisuwar, kallon khadija hafsat tayi tayi mata sannu da zuwa sannan suka gaisa,
.
Gaban gadon yusleem khadija takarasa amma har lokacin bai tashi daga bacci ba dan haka tadawo wurinsu mami ta zauna suka cigaba da zaman tare,
Zuwa can bayan yan wasu mintuna nurse tashigo ta dan dubashi tayi rubutun da zatayi tafita, fitarta babu wuya yusleem din yatashi, idanuwansa fess yasaukesu akan hafsat wacce ke zaune kusa da khadija, ita kuma khadijan sai danne dannenta takeyi awayarta,
Tashi hafsat tayi taje wurinda yake itada mami,
"Hafsat taimaka min inje bathroom.."
Ba iya hafsat dince kadai ta rikeshi ba harda mami suka taimaka mishi yasauko daga kan gadon suka rirrikeshi,
Tasowa khadija tayi tana cewa mami,
"Ayya mami barshi, kawo intayata.."
"Lahh babu komai khadija da kinyi zamanki kin huta" inji mami,
"A'a mami dan Allah barshi kije ki zauna"
Hade fuska yusleem yayi bai bari khadijan takai ga rikeshi ba yafada cikin toilet, dukkansu sororo sukayi banda khadija da ke yin dan murmushin yake,
Dukkansu komawa sukayi suka zauna hafsat ce kadai ta tsaya tana jiran yafito, bai jima sosai ba yabude kofa yafito yana faman bin bango, rikeshi hafsat tayi har zuwa gefen gadon,
"Salla fa nake son yi" yace da hafsat,
"To bari in shimfida maka dan kwalina sai kayi.."
.
"A'a inada carpet acikin mota bari inkawo.." Khadija tace sannan ta mike tafita, dan satar kallonshi hafsat tayi har lokacin fuskarshi kicin kicin take babu walwala,
Karbar dardumar hafsa tayi bayan khadija ta Kawo ta shimfida masa,yahau yatada salla,
Tashi yayi yakoma kan gadon bayan ya idar da salla, gaishe da mami yayi tai masa sannu sannan suka gaisa da khadija,
Tea Hafsa tatashi ta hada masa takai masa,
"Yaya yusleem wannan bata fuskar duk na menene? Ka saki ranka mana"
Hannunta yariko tareda cup din ruwan zafin yana dan murmushi,
"Ai kece kika sani yin fushin..?"
"Saboda me?" Tafada tana dan zame hannunta daga nashi,sake rike hannun yayi yaki saki,
"To ai gani nayi kunyi min rufdugu alhalin ke daya ma zaki iya rikeni..."
.
Murmushi tayi ta dan kalli wurin dasu mami ke zaune nan taga hankalinsu ma kwata kwata ba akansu yakeba domin hirarsu sukeyi itada khadija,
"Yaya yusleem kenan..."
Cup din da hannunta yahada yarinka kaiwa tea din bakinsa yana kurba har yakusa kammalawa, muryar mami ce ta katsesu,
"Hafsat ina zuwa bari mu fita tareda khadija tayi dropping dina saboda ayau zuwa gobe nake so agama komai na tafiyar yusleem ban son abun yadauki lokaci.."
"To shikenan mami sai kin dawo, Allah yasa adace"
Sallama sukayi da khadija suka fita tareda mami, kwanciya yusleem yayi ya tallafe kumatunsa da hannunsa guda daya yana kallonta,
"Kici abincin ki tayani wanka"
.
Sunkuyar da kanta tayi taci gaba da tsiyayo tea acikin cup,
"Uhmm, ko bakiji ba?"
"Naji yaya yusleem"
Ido ya tsura mata lokacin da tafara kurbar ruwan tea din, ganin ya kafeta da ido yasata tashi ta bar wurin ta matsa can nesa dashi, murmushi yayi ya lumshe idanuwansa.
Tunda mami tatafi bata samu dawowa ba har yamma abincima sai khadija ce takawo musu kuma yanzun ma kamar da safe bataga sakin fuska awurin yusleem ba amma hafsat ita kam ta karbeta hannu bibbiyu domin bataga aibunta ba,
Alla Alla hafsat tarinka yi mami tadawo domin ta kosa taji hanyar da mamin tabi tasamo makudan kudade haka masu wuyar samuwa.
Mami bata samu dawowa ba sai bayan sallar isha, lokacin Dr yazo ya rubuta musu sallama bayan mami ta bibbiya kudaden da yakamata su biya asibitin,
.
Driver ne ya daukesu suka nufi gida kuma dama jikin yusleem din yadanyi sauki ba kamar ranar da sukazo ba domin yanzu ko aman yadaina,
Afalo suka zauna dukkaninsu hafsat tagama matsuwa da son jin abinda mami zatace amma taji mamin tayi shiru sai lissafe lissafen kudi taketa faman yi,
"Yusleem nasamu munyi nasara komai ya kammala insha Allah nanda kwana biyu zaka tafi kasar Cairo domin ance visa din kasar tafi saurin samuwa fiyeda ta kasar India.."
"To mami Allah yasaka da alkhairi Allah yakaimu lokacin"
"Amin, Allah yasa asamo abinda akaje nema Allah yabaka lafiya"
"Amin mami, bari inyi wanka" yace da mami bayan ya mike yana yiwa hafsat kallon zo ki rakani, taganshi sarai amma saita dauke kanta tayi kamar bata ganiba dolenshi yajuya ya fice shi kadai,
Bayan fitarshi hafsat ta kalli mami,
"Mami kodai gwala gwalanki kika siyar?"
Dakatawa mami tayi daga yin abinda take ta kalli hafsat,
"Hafsa ai ni yanzu banida gwalagwalai, jiya darana bakiga nakoma asibiti raina abace hankalina atashe ba?
.
Wallahi infada miki dawowa nayi na iske safe dina wurin da nake ajiyar gold din abude an kwashe babu komai aciki, koda nakira mai gadi na tambayeshi sai yace min wai bakuwa nayi kuma yace mata babu kowa agidan amma tace ehh zata shigo ta jirani, ban san wacece ba amma duk yadda akayi itace ta sace min wadannan gold din kuma dama iya saiti daya gareni sauran duk nasayar bana gasken bane.."
Zaro ido hafsat tayi saboda jin satar da akazo har gida aka yiwa mami,
"Mami Allah ya kiyaye gaba, Allah yamayar miki da alkhairi, yanzu kuma ya akayi?"
"Shine naje nasamu shi shugaban asibitin wannan yaron sufyan nace masa zan sayar da kodata (kidney)guda daya sannan suma su khalifa shida Abdul idan sun dawo za aciri tasu guda dai dai tunda dama guda dayace ke amfani ajikin dan adam.."
Zabura hafsat tayi ta zazzaro ido, cikin rawar baki tace,
"Haba mami, ya za ayi kisayar da kododinku? Ai bai kamata dan za agyara wani kuma abata wani ba.." Takarashe maganar hawaye nabin kuncinta,
.
"Ai magana takare hafsat tunda shima sufyan din yabani shawara ta hanyar cewar idan inada wata kadara kamar gida ko fili gara insiyar akan insaida kodata data yarana, to kinga yanzu bamuda wasu kadarori inbanda wannan gidan kwaya daya shine yace to mahaifinsa zai sai gidan kuma insha Allah zaiyi mana taimako ta hanyar bamu aron gidan muci gaba da zama har zuwa ranar da zamu mallaki namu,adaren jiya mukazo muka ga gidan bayan ya debo dillalai kuma sunyiwa gida kudi, ansiya miliyan daya.." Mami takammala maganar tana dan murmushin yake domin zuciyarta wani zafi takeyi mata.
Hafsat ji tayi tasamu yar nutsuwa saboda jin bayanin mami,
"Allah ya rufa asiri mami, Allah yasa adace kuma"
"Amin hafsat, kinga yanda rayuwa ta juya mana ko? Mun kawoki kinata faman shan wahala"
"Dan Allah mami kidaina fadin haka, ai yanda Allah ya tsara min kenan.."
"Allah yayi miki albarka, insha Allah gobe zamu yi signing atakardar gidan daga nan sai inbasu copy.."
.
Shiru hafsat tayi tana jin tausayin mami yana kwaranya acikin ranta domin tasan karfin hali kawai mamin keyi amma ita kadai tasan yanayin da take ciki,
Ganin mami ta tashi tashiga cikin bedroom dinta yasa itama hafsat tatashi tashiga dakin surayya,
Kayan jikinta ta cire tashiga wanka, lokacin da tafito ta hangi yusleem kwance saman gado yayi d'ai d'ai, hijabinta ta janyo ta saka tana kallonshi, shi dinma juyawa yayi yana kallonta daga kasa har sama......
*
D'auke kanta tayi daga kallon yusleem taje gaban mirror tafara shiryawa, shikuwa sai faman binta da idanuwa yake domin duk wani motsi da zatayi akan idonshi ne,
Tashi tayi da niyyar ta dauki kaya tasa amma ganin ya kafeta da ido yasata shiga bathroom tasa kayan sannan tafito,
"Yaya yusleem dan Allah katashi katafi,ni wallahi bacci nakeji, kaga dai 2 days banyi bacci ba..." Tafada cikin shagwaba bayan ta zauna agefen gadon, hannunta ya kamo yarike cikin nashi,
"To ai yanzu ba hanaki baccin nayi ba, zo ki kwanta"
"Ni gaskiya katafi, bana son mami ta..."
Saurin katseta yayi ta hanyar jawota jikinshi,
"Karyar kunya kikeyi nanah, saboda Kinga mami fa tajima da sanin cewar tare muke kwana tunda ko lokacin da tararmu agidan haya muna zaune adaki daya ta tarar damu ba dakuna biyu ba.."
Jin ya ambaci gidan haya yasa taji Maman amir ta fado ranta,
.
"Kaga kuwa dazu da rana Maman amir ta kirani tana gaisheka tace inyi maka sannu..."
"Ina amsawa kawar Maman amir..."
Murmushi tayi tafara kokarin zamewa daga jikinsa amma ya riketa gam,
"Ba kince bacci zakiyi ba, to kiyi mana"
Shiru tayi domin dama bawai baccin takeji ba ita dai kawai tana kunyar mami tasan anan yake kwana,
"Ya kukayi da mami? Ta fada miki a inda tasamo kudaden nan kuwa? Saboda wallahi sam hankalina yaki kwanciya" yayi maganar cikin raunin zuciya yana shafa kanta,
"Ehh ta fada min yaya yusleem, wannan gidan ta saida kasan lafiyarka tafi komai muhimmanci agaremu yanzu..."
.
"Hakane to amma..."
Katseshi hafsat tayi ta hanyar kai hannu ta rufe masa baki, shiru yayi yana jin yanda take shafar kasumbarshi dake baibaye a fuskarshi,
"Ai yaya yusleem babu abinda yakai uwa dadi, kowacce uwa tana son danta acikin kowanne irin yanayi koda kuwa duk duniya zata ki shi to ita zataso kayanta, kasan meyasa nafadi haka?"
Girgiza kai yayi alamun a'a,
"To da mami kidney dinta tayi niyyar sayarwa da tasu Abdul..."
Gani tayi idanuwanshi sun firfito waje ya yunkura yana kokarin tashi, mayar dashi tayi ya kwanta takoma jikinshi ta dora kanta akirjinsa,
"Ka kwantar da hankalinka ai bata sayar ba, gidan nan ta siyar shine aka samu kudaden da zaka tafi Cairo..."
Ajiyar zuciya yayi yakai hannu ya rungumeta,
"Dole hankalina yatashi hafsat, idan mami da yan uwana suka sayar da kidney dinsu menene ribar? Babu riba at all saboda nan gaba za azo ana facing problems a lot,tunda kinga akwai kidney disease ko wani abu mai kamada haka"
.
"Hakane amma tunda Allah ya takaita abin ai shikenan karka daga hankalinka, Allah yabaka lafiya, ni yanzu babban burina shine inga kasamu cikakkiyar lafiya kamar kowa"
Murmushi yayi ya kamo hannuwanta,
"Kin kosa insamu lafiya ayi wacce za ayi ko?"
Dariya tayi ta boye fuskarta akirjinsa,
"Kai yaya yusleem ni wallahi ba abinda nake nufi ba kenan"
"To me kike nufi?"
"Ni kawai inganka lafiya kadaina wannan zazzabin da amai da ciwon ciki shine kadai burina"
Kanta yafara shafawa yana murmushi,
"Nikuwa kin ga babban burina shine idan nasamu lafiya inbawa matata dukkan hakkoki wanda addini ya rataya min awuyana, sannan inmaidata mace sosai..."
Boye fuskarta tayi tana dariya,
"Kai yaya yusleem.."
"Kai nanah hafsat, da kin zaci zamu zauna ahaka ne? Uhm"
Shiru tayi masa tana dariya har lokacin bata bari yaga fuskarta ba,
"Uhmm?" Yasake tambayarta, shirun tasake yimasa, hannunta yakama yakai bakinsa yayi kissing dinshi, ji tayi ya rungumeta tsam tsam,
.
Kunyace ta lullubeta domin abin na yusleem yau yagirmama duk da dai dama yasaba rike hannunta ko ya dafa kafadarta ko yaja mata yan yatsun kafarta ko kuma yadafa kafadarta amma bai taba yunkurin kissing dinta ba sai yau,
Wasu wasanni masu nauyi yau yake yimata wanda bai taba yimata ba, sun jima cikin wannan yanayin kafin ya rungumeta yana fitar da numfashi ahankali, kwanciya tayi luf ajikinsa da haka har bacci ya dauketa domin dare yayi sosai.
Tunda tafara baccin ba ita ta tashi ba sai karfe 7,ita kanta tayi mamakin makarar da tayi, dudduba gefenta tayi nan taga babu yusleem babu alamunsa,
Wanka tashiga tayi agurguje tafito tayi salla taci gaba da zama shiru, tana zaune akan abin sallar taji shigowar mami,
"Hafsat yau makara kikayi ne? Naji shiru baki fitoba"
Tashi Hafsa tayi tana ninke dardumar da tayi salla,
"Ehh wallahi mami, ina kwana?"
"Lafiya lau, idan kin shirya kifito ga breakfast nan yana jiranki"
"To mami bari inzo.."
Fita mami tayi ita kuma ta tsaya tana nazarin ta yadda zata fita falo domin bata son su hadu da yusleem, ta dade tsaye akofar dakin tana ta tunani kafin daga bisani tayi kuru tafita,
.
Akan kujera ta hango yusleem kwance yana kallon tv ita kuma mami tana zaune tana hada ruwan zafi,
Kin kallon yusleem tayi taje kusa da mami ta zauna itama tasoma hada ruwan zafin,
"Kai yusleem bazaka yi breakfast din bane?"
"Mami sai zuwa anjima yanzu ruwan zafi kadai zan Sha"
"To bari akawo maka"
Hada masa tea din hafsat tayi ta dauka takai mishi, zaune yatashi yana kallon fuskarta amma saita kawar da tata fuskar,
"Yaya wankan safe...?" Yafadi lokacin da zai karbi cup din, shiru tayi masa tayi hanzarin barin wurin aranta tana tunanin yanda akayi yazama marar kunya tsakanin daren jiya zuwa yau,
.
Misalin karfe 10 nasafe suna zazzaune acikin falon sai ga khadija tashigo, tana sanye da orange colour din atamfa da mayafi kalar atamfar da yar karamar hand bag,
Duba yusleem tayi tatafi bayan sun gaggaisa, bayan tafiyar khadija mai gadi yashigo yace anyi baki wai masu siyan gidane suka zo, mamice tafita bayan ta dauki wasu takardu,
Wasu mutane guda biyu tasamu tsaye a compound din gidan suna jiranta amma yau babu dr sufyan,
"Sannu alhaji, wadannan sune takardun gidan gashi.."
Karbar takardun wani dan dattijon mutum yayi yafara dubawa, yajima yana nazarin takardun kafin ya dago yana kallon mami,
"Hajiya wannan wanda sunansa yake jiki shine mai gidan?"
Jijjiga kai mami tayi,
"Ehh shine yarona ne"
"Yana ina yanzu?"
.
"Yana ciki"
"Zan iya ganinsa?"
"Me zai hana, bisimillah zo mu karasa"
Yusleem yana zaune a falo ya tisa Hafsa agaba yana tsokanarta sai gasu mami sun shigo tashi yayi daga kusa da Hafsa yakoma wata kujerar ya zauna,
"Yusleem ga bakinka" inji mami, cikeda mamaki ya kalli mutanen nan yaga babu wanda yasani acikinsu, zama wannan dattijon yayi ya kalli yusleem,
"Yusleem baka ganeni ba ko?"
Daga kai yusleem yayi alamun eh,
"Zaka iya tunawa shekaru shida da suka wuce kaje neman aiki a wata ma'aikata ta yada labarai? A lokacin anyi maka interview daga baya kadawo akace maka baka samu aikinba"
Murmushi yusleem yayi alamun ya tuna,
"Ok sai yanzu natuna ai dayake shekarun an dan kwana biyu"
.
"To yusleem tun lokacin da kayi interview kasamu wannan aikin kuma abangarena wato department dina, nine nan nahanaka aikinka nace baka samuba amma gwamnati ta daukeka sannan duk watan duniya tana biyanka albashi na naira dubu hamsin da biyar banda allowances d sauran alkhairan da baza arasaba, nine na rinka rike kudin ina harkokin gabana dasu har lokacin da zaka samu promotion daga grade level 9 zuwa grade level 12,haka na rinka ninke kudinka ina kasafin gabana har saida naji wani malami yayi wa'azi akan mutane masu aikata laifi irin nawa, to tun daga nan nasoma binciken hanyar da zanbi insadu dakai inbaka hakkinka da aikinka amma kuma duk lokacin da nakira wayarka bata shiga, daga karshe danaga narasa yanda zanyi inganka sai narinka tara maka albashinka ina ajiye maka kuma ina juya maka acikin kudadena na kasuwanci wanda yanzu haka duk dukiyata tamuce nida kai, kayi hakuri yusleem ka yafe min domin na danne maka hakkinka kuma na cutar dakai..."
Jin maganar yusleem yayi kamar acikin mafarki, bashi kadaiba hatta su mami abin yabasu mamaki mutuka amma kuma duba da irin zamanin da muke ciki yanzu sai mamakin nasu baiyi yawa ba domin yanzu zalunci awurin mutane ba abune mai wahala ba,
"To ai alhaji ni banma san me zance ba domin gaba daya kaina yagama daurewa.." Yusleem yayi maganar yana kallon mami wadda ita dinma shi take kallo zuciyarta kamar kankara dan farin ciki domin arzikin danta da alama yakusa dawowa,
.
"yanzu tashi zakayi kazo muje inkaika kamfanoninmu da gidajenmu da kuma shagunanmu wadanda ake sayar mana da kayayyakin da kamfanin mu yake sarrafawa, yusleem wallahi kullum da kai nake kwana acikin raina inata addu'ar Allah yasa sai mun hadu nabaka hakkinka kafin na amsa kiran ubangijina, gashi yau burina yacika, zan sauke babban nauyi, zan baka albashinka na shekaru shida sannan kuma zan raba dukiyata gida biyu inbaka taka, haka kuma zamuje can ministry of information domin abaka office dinka wanda yake can yana jiranka.., yanzu tashi mu hanzarta mu tafi"
Farin cikine ya lullube Hafsa nan tasoma yiwa ubangiji godiya acikin zuciyarta, ji take kamar ta zuba ruwa akasa tasha dan farin ciki,
Alhaji musa mori bai bar yusleem yasake wata magana ba yasashi agaba suka fita yace zaije ya sauke nauyi,
Har tsakar gida mami da hafsat suka rakasu saida suka ga fitarsu sannan suka koma ciki cikeda farin ciki da murna, dan murna ko abincin rana kasa ci sukayi suna jiran suga dawowar yusleem amma har dare bai dawoba gashi kuma washe gari da safe zai tafi kasar Cairo,
.
Yusleem kuwa tunda suka fita basu samu zamaba suna can sunata yawo ana nunnuna masa filayensa da gidaje da shaguna da kamfanoni, basu suka samu Kansu ba sai karfe 9 nadare nan alhaji musa yagayyaceshi suje gidanshi suci abinci amma yusleem yaki yace gida zaije domin gobe da safe zai tafi kasar Cairo nan suka rabu da alhaji musa akan sai bayan yadawo sannan zasu karasa duk wasu abubuwa wadanda suka dace, suka kawoshi gida suka ajiyeshi.
Afalo yasamu su mami zaune suna sauraron zuwanshi kowannensu da gani babu tambaya yana cikin walwala da farin ciki, zama yayi agajiye kusa da hafsat yana murmushi,
"Wallahi yau nasha wahala mami, munyi tafiya sosai har wasu yan kauyuka mukaje.."
.
"Ikon Allah, Allah mai yadda yaso, Allah yasanya alkhairi dai" inji mami,
"Amin" ya amsa mata tareda kwashewa yadda akayi yasanar da ita, murna dukkansu suka rinka yi sai lokacin suka iya cin abinci, faten wake da kifi yaji albasa da manja, acikin faranti babba hafsat ta zuba musu suka hadu gaba dayansu sukaci harda mami,
Mamince tafara tashi tawuce bedroom dinta tabarsu awurin, kallon hafsat din yakeyi yanda taketa wani sussunne kai ita adole kunyarshi takeji, bai kulata ba yatashi yafita, wanka yaje yayi ya duba kayanshi yasa domin har hafsat ta hada masa yan kayan da zai tafi dasu,
.
Saida yashirya tsaf sannan yanufi part din mami, dakin da hafsat take ciki yatura yashiga, tana tsaye gaban mirror tana shafe jikinta da turare mai dan karen kamshi da dadi,
Abayanta yatsaya yana kallonta yana shakar kamshinta wanda yatasamma rikita masa kwakwalwa,
"Ashe nidinma dan gatane tunda gashi nan ana shirin yimin tarba ta musamman" yafada cikin tsokana,
.
Shiru tayi bata tanka ba, ji tayi yadauketa yayi saman gado da ita, rungumeta yayi yana bata labarin abinda yafaru tun daga fitarsa har Kawo dawowarsa,
"Yaya yusleem ai Allah yaga sadaukarwar da kayi kuma yaga irin tuban da kayi shiyasa bazai taba barinka katabe ba.."
"To ai da taimakonki hakan yafaru madam, Allah yayi miki albarka.."
Kasa amsawa tayi domin tuni taji yasoma yunkurin irin wasannin da yayi mata adaren jiya,
Duk da yanata maganar yagaji yagaji yau amma hakan bai sashi yayi barci ba, yanda sukaga rana haka sukaga dare har asuba tayi, saida sukayi salla sannan suka kwanta bacci.
Itace tafara tashi lokacin karfe 9 nasafe tayi wanka tafita wurin mami, bayan sun gama breakfast tana shirin taje ta tasoshi sai gashi yafito, kamar ta nitse dan kunya duk da tasan yanzu mami tagama gane adakin yake kwana, tagefen ido ta kalleshi lokacin da yana gaida mami,
"Yusleem karfe 11 fa zaku tashi, kayi sauri kashirya muje mu rakaka" mami tayi maganar tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, tea kawai yasha yatafi shiryawa,
10:30 daidai yafito tsaf cikin shirinsa natafiya, yasha kananan kaya, iya hafsat ce kadai acikin falon tana jiran mami tafito tana tsaye gaban wani console tana ganin fuskarta, abayanta ya tsaya, yariko kugunta nan tayi saurin juyowa,
Murmushi yayi yakai mata kiss saman bakinta tayi saurin gocewa, hannunta yariko,
"Jiya baki ki ba yau kuma tsabar gulma ce tasaki kin yarda?"
Hannu tasa tarufe fuskarta, jin mami na kokarin fitowa yasashi sakinta nan suka dunguma suka tafi, motar mami suka shiga driver yaja suka fita daidai lokacin motar khadija ta Kawo kai nan tayi reverse tabi bayansu.....
_Gaisuwar fatan alkhairi ga Anty A'isha (mama 4),Anty Aisha (maman minal),Maman sultan, & Hawy yanmata_
*
.
Ta cikin mirror din saitinshi yake hango fuskar hafsat wacce ke kunshe da abubuwa guda biyu wato farin ciki da kuma sabanin haka,
Mami kuwa tamkar tafi kowa farin cikin wannan tafiyar ta yusleem domin zaka gane hakan idan har ka kalli fuskarta,
Tafiyar mintuna 15 zuwa 20 ne yakaisu airport din suna yin packing saiga khadija itama tayi packing din tata motar akusa dasu dan haka kusan atare suka firfito,
Cikeda fara'a ta karaso wurinsu tasoma gaisar da mami, cikin fara'a mami ta amsa domin acikin farin ciki take, dan kallon yusleem tayi taga hankalinsa ai bama anan yakeba domin yana tsaye shida hafsat suna yin magana,
Tsayawa dukkaninsu sukayi ajikin mota suna jiran su,
Hawayene suke kokarin zuba a idon hafsat yusleem yayi saurin kama hannunta suka bar wajen, can dan nesa dasu mami sukaje yafara rarrashinta,
Hannuwanta duka biyu yarike yana kallon fuskarta,
"Haba nanah karki zama raguwa, kiyi hakuri kinga da ace tun farko kudin nan sun fito dawuri to da tare dake zan tafi..."
Hawayen da taketa kokarin hana zubowarsu ne suka zubo sharr nan yakai hannunshi ya goge mata,
"Daina kuka, me kike so inkawo miki idan zan dawo..?"
Shiru tayi idanuwanta na kallon kasa,
"Abin dadi?, ko kayan kwalliya?", taji yasake tambayarta, girgiza masa kai tayi alamun a'a,
"To me kikeso?"
Nunashi tayi da dan yatsa,
"Ni kaina...?" Yayi maganar murya kasa kasa,
Kai ta daga masa,
Hannuwanta taji ya matse tareda janta zuwa kirjinsa bata fargaba tajita rungume ajikinshi,
"Yaya yusleem su mami..." Tafada tana kokarin zamewa, sassauta rikon da yayi mata yayi yana murmushi,
.
"Ki kwantar da hankalinki idan nadawo zaki sameni har sai ma kin gaji dani"
Murmushi tayi ta zame jikinta tana kallonshi, shi dinma kallon fuskarta yake yana murmushi, wurinsu mami suka koma yayi musu sallama ya dauki yar jakar kayanshi yawuce,
Saida sukaga tashinsu sannan suka bar airport din suka dunguma suka koma gida har khadija.
Bayan komawarsu gida harkokinsu sukai tayi amma da zarar hafsat tashiga daki sai taga kamar zataga yusleem, haka taitajin kewarsa har dare yayi, duk irin baccin da yacika mata ido amma lokacin da tazo ta kwanta sai taji ta kasa baccin kwata kwata, sai uban juyi data rinka yi tana tuno mijinta, dakyar tasamu bacci ya dauketa bayan dare ya raba.
Washe gari da safe bata samu damar fitowa da wuri ba sai wurin misalin karfe 11 lokacin da ta fito mami na shiri fita dama ita take jira,
"Hafsa ga breakfast can ni fita zanyi, ina son zanje gidan hajiya Sarah amma ba dadewa zanyi ba"
"To mami Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo"
Fita mami tayi tatafi ita kuma ta nufi dining area, zama tayi ta karya duk da abincin bawani mai yawa taciba, falo tadawo tazauna ta kamo tashar b4u tana kalla domin zaman shiru babu dadi,
Har bacci yadan fara daukarta sama sama taji sallamar khadija wacce abisa dukkan alamu yanzu ta mayar da zuwa gidan kullum tamkar ibada,
.
Tashi zaune hafsat tayi tana murmushi,
"Sannu da zuwa.."
"Yawwa hafsa, ko mamin bata nan" inji khadija wacce ke sanye cikin wata doguwar riga ta atamfa,
"Ehh mami ta dan fita wallahi" hafsa tabata amsa bayan tatashi zaune,
Zama khadija tayi, bayan sun gaisa suka dan fara hira kadan kadan,
"Hafsa kowa yayi mamakin yadda akayi kika samu kan yusleem har kuka kai wannan lokacin tare, saboda yusleem baya iya zama da mace.."
Murmushi hafsa tayi,
"Baya zama da mace kamar ya? Aini ban san wannan labarinba ko a mafarki"
"To kuwa a lissafi kece mace ta fiyeda goma da ya aura, kuma saida ya sakeni sannan ya aureki, ni kinga bamufi wata biyarba tare"
Jijjiga kai hafsa tayi alamun tausayawa,
"Allah sarki, Allah yarufa asiri kin san ai dama lamarin aure sai hakuri domin shima rai gareshi..."
"Hakane amma nida ina zargin ko aljanu gareshi ko kuma da saninsa tsabar cin mutunci ne, shiyasa ma ni yanzu wallahi auren yagama fitar min daga raina domin kin san naji dadi shine gari bawai nasaba ba.."
"To ai ba duk aka taru aka zama dayaba khadija, sai kiga nan gaba kin samu inda zakiji dadin hankalinki ya kwanta..."
"Kayya hafsa, kin san ai duk wanda miciji ya sareshi to idan yaga tsumma gudu yake, hafsa arayuwar aurena tafarko ban tsinci komai ba face bakin ciki da bacin rai da takaici, shiyasa ko zan kara wani auren gaskiya ba yanzu ba sai zuciyata ta nutsu tukunna"
"Ubangiji Allah yazabi abinda yafi alkhairi, babu komai ai jarrabawa ce daga Allah"
"Amin.."
.
Haka sukaci gaba da yin hirarsu har azahar tayi sai lokacin khadija tatafi, tun daga wannan rana kuma kullum zatazo susha hirarsu da hafsat wani lokacin ma harda mami, ita hafsa tausayin khadija takeji domin irin labaran da take bata na kuncin rayuwa da rashin samun farin ciki wanda ta rinka fuskanta agidan aurenta nafarko, shiyasa take tausayinta domin tasan irin wannan rayuwar tunda itama tashiga makamanciyarta abaya, koda yaushe yanzu khadija tana gidan haka kuma idan bataje da safe ba to zataje da rana ko da yamma wani lokacin harda daddare ma zuwa take tamaida gidan mami kamar gidansu haka ta dauki hafsat a matsayin yar uwa kuma abokiyar shawara domin ko sabon bazawari tayi saita fada mata,
Yauma kamar kullum hafsa tana zaune tana tsifar kai ita kuma mami tana gyaran farcenta saiga khadijan tashigo da alama daga sch take domin karfe 2 saura narana,
Da mami kawai suka gaisa tahaye dining ta zubo tuwon shinkafa miyar zogale tadawo wurin hafsat ta zauna,
"To inbanda abinku kuma ga tsifar gashi ga abinci?" Mami tafada tana murmushi,
Dan kwali hafsat ta dauka ta rufe kanta, "bari inbarshi anjima na karasa idan tagama"
Tashi mami tayi ta shiga kitchen domin tajiyo buruntun kuku aciki,
Mami natashi khadija ta dubi hafsa dama da labari tazo mata,
"Hafsa inata son inbaki labarin wani guy Al'amin, saurayi ne fa amma yadage sai ya aureni duk da nace masa nataba aure"
Murmushi hafsat tayi, "to kibashi dama mana kigani, wallahi khadija kiyarda indai kinga baida problem"
Murmushi khadija tayi ta yanko laumar tuwo tasa abakinta,
.
"Shikenan zan gwada ingani, bari inyi sauri ma domin munyi dashi zaizo da yamma"
"To Allah ya tabbatar da alkhairi"
Saida khadija taji tayi nak sannan ta hada nata yanata tatafi, kullum hakace take faruwa domin acewarta dama gidan mami gidansu ne domin dama aminiyar mahaifiyarta ce.
Tunda yusleem yatafi basuji duriyarsa ba saida yayi sati biyu sannan yakira su murna ranar awurin mami da hafsa ba acewa komai, sun jima suna hira dashi yana yimusu bayanin abubuwan dake faruwa sannan sukayi sallama,
Haka da daddare ma saida ya kuma kira suka kwashe awanni shida hafsat suna hira, yanzu har tasan lokacin kiranshi domin kullum sai yakirasu da safe da daddare,
Satinshi 7 acan yafara shirye shiryen dawowa amma idan yadawo bayan wani lokaci zai sake komawa,
Hafsat tunda taji zai dawo tarasa inda zata cusa kanta dan murna wanda hatta mami saida ta fahimta, saloon mami takaita aka wanke mata gashinta aka gyarashi, bayan sun dawo gida mai kunshin dake yiwa mami tazo ta zane mata kafafunta da hannaye da bakin lallai mai adon ja,
Tarba ta musamman mami da hafsat suka shiryawa yusleem,karfe 3:30 jirginsu yasauka nan mami da driver suka tafi daukoshi banda hafsa wacce tazauna domin karasa girke girken da aka dora sabodayau tace itace zatayi girkin da yusleem zaici.....
***
Lokacin dasu mami suka dawo gidan hafsat tana cikin daki tana shiryawa, saida ta kammala sannan tayi sallar la'asar domin lokaci yayi,
.
Tana tsaye gaban mirror tana gyara fuskarta bayan ta idar da sallar ta hango wulgawar mutum ta cikin mirror atsorace ta juya amma abun mamaki bataga kowa ba, tsorata tayi takama hanya zata fita daga dakin taje falo wurinsu mami,
Ji tayi anyi mata wata irin damka, tuni numfashinta yafara neman daukewa, ajikin mutum tajita anrugumeta tabaya tayadda bazata iya ganin fuskar mutumin ba, kara taso fasawa amma ina bata samu zarafin yin hakanba domin ji tayi anrufe mata baki da abinda bata san ko menene ba sai daga baya sannan ta fahimci cewar da bakinshi ne,
Wani sanyayyen kamshi ne mai dadi yake ratsa kofofin hancinta gaba daya,
Sassauta rikon da yayi mata yayi ya dago da fuskarta yana kallonta,
"Nanah hafsat..."
Firgigit tayi tabude idanuwanta akan fuskarsa ganinshi yasata daka tsalle ta rungumeshi na tsawon wasu mintuna,
Riketa yayi yana dan juyi da ita ahankali, dago da fuskarta tayi ta kalleshi, tabbas yaya yusleem dintane amma kuma tamkar wanda aka canjashi domin farar fatarshi tasake haskawa farin yakaru, gashi fatar tashi tasake laushi lubus kamar ta jarirai, kyakkyawar fuskarshi kuma tasake cika da kyau, annuri, da farin ciki,
Ji tayi gaba daya tagama raina kanta saboda yusleem yafita tako ina ita sai take ganinma ayanzu haka ai bata da wani abu atare da ita wanda take ganin zata iya jan ra'ayinshi domin yafita kyau yafita komai na rayuwa,
Hancinta taji yaja domin har lokacin tana dale ajikinshi hannayenta sakale awuyanshi,
.
Bude idanuwanta tayi daga dogon tunanin data lula ta kalleshi, ji tayi ya rike fuskarta yana kokarin sake saita bakinshi akan nata, shi kansa bakin nashi da lips din dake jiki da fararen hakoran dake jere aciki tasan abin kallone, lumshe idonta tayi tana jiran taji saukar lips dinshi akan nata amma sai taji sabanin haka maimakon yayi kissing din bakinta sai tajishi asaman kirjinta, saurin tureshi tayi tasoma kokarin kwacewa tana dariya,
Riketa yayi shidinma yana yin dariyar kasa kasa,
"Bakiyi min ko sannu da zuwa ba.."
Tana shirin yin magana suka jiyo maganar mami tana nufo kofar dakin,
"Hafsa har yanzu baki idar da sallar bane? Idan kin idar kifito ki hada salad din saboda nace kuku yahada yace kece kika ce karya taba sai kin fito..."
Bude baki tayi zata amsawa mami amma takasa saboda shakewar da muryarta tayi, rufe mata baki da hannunshi yayi yabawa mami amsa da,
"Mami har yanzu fa bata idar da sallar ba.."
"To idan ta idar kafada mata, sannan ku fito muci abincin..."
"To mami..."
Saida ta tabbatar da cewar mami tatafi sannan ta kalleshi,
"Kuma da tashigo taganmu fa gashi kace mata wai salla nake yi.."
Murmushi yayi ya lakuce mata hanci,
"Ai bazata ma shigo ba saboda tasan nidake yau tamkar tif da taya zamu kasance...."
"To kazo muje kar taga mun dade tayi zargin ko wani abu muke yi.."
Murmushi yayi ya dauketa nan tasoma mutsu mutsu, ajiyeta yayi ta fice shikuma yashiga toilet yayi alwala yafito yayi salla,
.
A falo ya samesu ita da mami sun baje girke girken da aka wuni anayi saboda shi, akusa da mami ya zauna yana kallon hafsa wacce ke tsugunne tana hada salad wanda zasu ci abincin dashi,sai lokacin wai ya lura da kunshin dake hannunta duk hidimar dazu idonshi bai kai kan kunshin ba,
Tashi mami tayi zuwa kan dining domin debo wasu kwanuka,
Hannunshi yakai kan na hafsa,
"Ya akayi dazu banga kunshin nan ba sai yanzu? Koda yake ai ni yau dinne gaba daya amaryar tawa tagama rudani, ta dauke hankalina"
Murmushi hafsat tayi saboda jin abinda yace, janye hannunta tayi daga jikin nashi saboda taga mami na kokarin fitowa ganin haka shikuma ya wayance da lakuto salad din yakai bakinsa,
Kamar koda yaushe a cikin babban faranti yauma suka zuba abincin suka hadu suna ci, idan yusleem yafaki idon mami sai ya kwace abincin hafsa ya kai bakinsa,
Tun daga yanayin cin abincinsa mami da hafsa suka gane cewar lafiya ta samu domin yau yaci abinci sosai wanda rabon da yaci irinshi har anmanta,
Komai da suka girka saida yaci, kallonshi kurum hafsa keyi saboda ganin yanda ya bude ciki ya narki abinci,
.
Kan kujera yaje ya mike, mami na zaune kusa dashi suna dan yar hira dangane da tafiyarsa da dawowar tashi yana sanar da ita abubuwan da suka wakana,
Hafsa kam wurin da suka gama cin abinci tashiga gyarawa tana kwashe na kwashewa tana kaiwa kitchen ba zuwa tayi tasasu agaba ba domin tasan tsakanin d'a da mahaifi dole akwai abubuwan da zasu tattauna atsakaninsu,
Saida ta kalkale wurin tass sannan ta kunna turaren wuta lokacin har 6 tayi, tashar zee world ta kunna tazauna tana kallo bayan ta dora dan karamin pillow din kujera akan cinyarta,
Tana ta kallonta sam hankalinta baya kansu mami, pillown taji anzare an kwanto akan cinyarta,
Saurin kallon wurin dasu mami ke zaune tayi nan taga mamin bata nan, kallonshi tayi lokacin da yake kara gyara kwanciyar kanshi akan cinyarta,
"Wai yaya yusleem yau da me kazo ne? So kake sai mami tafito ta ganmu?"
"Mami bazata fito yanzu ba ai, tashiga bedroom dinta kuma kin san idan tashiga bata fitowa sai bayan tayi salla"
Shiru tayi, hannunta ya kamo ya hada da nashi yana gani,
"Kinyi kyau..."
.
Shiru tasake yi domin sai tana ganin kamar gatse yake yi mata, shikuma tsakaninshi da Allah har cikin zuciyarshi yake fada,
"Yanaji kinyi shiru? Uhm"
"Babu komai"
"Ban yarda ba" yafada yana murza babban dan yatsanta,
"Lokacin salla yayi fa.."
Tashi zaune yayi yana kallonta,
"Tashi muje to muyi"
Tashi tayi tabi bayanshi zuwa cikin bedroom din,
"Kishiga ki fara yin alwalar"
"Nifa inada alwalata"
Murmushi yayi ya matsa kusa da ita,
"Allah karya kike, infada miki gaskiya? Wallahi ko tsarki bakida shi garama kije ki sake kiyi alwala.."
Tamkar kasa ta tsage ta shige haka taji dan kunya, ganin yana kokarin sake yimata wata tabargazar yasata juyawa da sauri ta fada cikin bathroom din ta turo kofa, murmushi yayi ya cusa hannuwanshi cikin aljihun wandon jeans din dake jikinsa......
_Fans aci gaba da yimin uzuri domin har yanzu ban gama warwarewa ba, fatan alkhairi agareku all..._
***
Yana tsaye ya bawa kofar bathroom din baya hafsat ta fito hannunta rikeda dan kwalinta tana kokarin daurawa,
Juyowa yayi yana kallonta, ganin gashin kanta wanda yasha gyara da yayi yasashi karasawa gabanta ya rike dan kwalin,
"Yanmata harda su gyaran gashi shine ba anuna min tuntuni ba?"
Hancinshi yakai kan gashin wanda har hafsat na iya jin dumin numfashinsa wanda ke sauka akan gashin nata,
Hannunshi tarike tana mai bata fuska,
"Yaya yusleem dan Allah kabari, Allah lokacin salla zai wuce.."
.
"Da yaushe ma aka kira sallar? Da sauran lokaci ai baby.."
Ribom din dake daure da gashin nata ya warware yasoma baza mata shi akan kafadarta,tamkar mai yimata tafiyar tsutsa haka taji,
Rike hannunshi tasake yi,
"Nikam gaskiya yaya yusleem alwalata..."
Murmushi yafara wanda yakarashe shi da dariya,
"Ta karye?"
Girgiza masa kai tayi alamun a'a,
"A'a dai baby hafsa fada min gaskiya, ta karye?"
Runtse idonta tayi tana rikeda hannunshi,
"Dan Allah kabari kar time din salla yakure mana.."
"To bari naje masallaci..."
Har yasaketa yasake rikota,
.
"Bari kawai nakarasa karyata inyaso sai kisake sabuwa"
Kafin takai ga yin magana har ya kama lips dinta,
Mintsininshi tayi a hannunshi nan yasaketa yana dariya, fita yayi daga cikin dakin zuwa bathroom din dake cikin falo anan yayi alwala yatafi masallaci.
Koda hafsa ta idar da sallar magrib kin fitowa tayi anan inda tayi salla ta kwanta har saida lokacin sallar isha yayi sannan tatashi ta gabatar da sallar isha da shafa'i da wutri,
Batare da ta cire hijab din da tayi sallar ba tafita falo wurin mami,
Mamin nazaune da carbi a hannunta tana ja sannan kuma tana kallon labarai a tashar BBCW,
Tana zama yusleem yana shigowa, kin kallonshi tayi tamaida idonta kan tv, a kusa da mami ya zauna wato kujerar dake kallon ta hafsa,
"Hafsa akawo abinci ko?" Mami tayi maganar tana kallonta,
"To mami bari nakawo muku nidai nakoshi.."
"Nima gaskiya na koshi amma zansha kunu" yusleem yayi maganar yana zaro wayarshi daga aljihun jeans dinshi,
.
"To shikenan adama mana kunun gaba daya sai musha" inji mami,
Tashi hafsa tayi zuwa kitchen, mintuna kalilan ta damo kunun ta dawo falo dauke dashi,
A cup ta zuzzuba musu ta dauko sugar da madara tasa musu,da kafarshi ya tabota kasancewar tana zaune akasa kusa da kujerarshi, dagowa tayi ta kalleshi,
"Wannan na waye kike zubawa?"
"Nakane.." Tabashi amsa,
"Yayi yawa ai, rage"
Sauka kasan shima yayi kusa da ita,
"Bar sugar dinnan haka, amma ki kara milk da yawa"
"Duk wannan wadda nasa batayi ba?"
"Nifa ke nake yiwa gata yarinya, ko bakya so indaina?" Yayi maganar cikin rada rada tayadda mami bazata jiyo ba domin tana dan nesa dasu,
Shiru tayi masa saboda tagane abinda yake nufi, ita yau mamaki yake bata domin kamar zuwansa Cairo dinnan rashin kunya yaje ya koyo domin tunda yashigo cikin gidan yau yaketa yimata abubuwa masu nauyi,
Tura masa gwangwanin madarar tayi gaba daya da kunun nashi tadauki na mami takai mata tadawo ta zauna tasoma shan nata kunun,
Tana jinshi yanata dungurinta tarabu dashi daga karshe ma tashi tayi tawuce cikin daki tayi kwanciyarta, wayarta ta jawo nan taga miss called din umminta, kiranta tayi suka gaisa suka dan taba hira daga nan sukayi sallama.
.
Tana kwance lullube cikin bargo taji shigowarshi, rufe idonta tayi kamar mai yin bacci, akusa da kafarta ya zauna yakama yan yatsun kafar yasoma jansu daya bayan daya suna yin kara, duk da tanajin zafi shiru tayi masa ita adole bacci take yi,
Jin tayi shiru yasashi haurawa saman gadon, abayanta ya kwanta bayan ya dan ture bargon da take ciki,
Kamshin turarenshi da taji shine ya haifar mata da kasala, luf tayi tana jinshi yana baza mata gashin kanta,
Juyo da ita yayi tana fuskantarshi, jikinta ne yabata cewar kallonta yake domin tsawon mintuna biyar zuwa shida tajishi shiru baiyi koda motsi ba kuma tasan ba bacci yake yiba, ahankali ta bude idonta guda daya kadan ta kalleshi ai kuwa kamar yanda ta zarga ganinshi tayi ya zubawa halittar kirjinta manyan idanuwanshi ko kiftawa bayayi, ganin yana kokarin kai hannu yasata saurin juya masa baya kamar mai bacci, juyo da ita yasake yi,
Rike masa hannu tayi tabude idonta,
"Keda kike yin barci ya akayi kikasan abinda ke faruwa?"
.
"Dan Allah nidai ka kashe hasken nan"
Murmushi yayi ya kalleta,
"Bakya son inganki ahaske? Nikuma da nafi son inkare miki kallo sosai"
Jan bargo tayi ta rufe har kanta, sauka yayi daga kan gadon yaje yakashe hasken yadawo amma abin mamaki koda yahau kan gadon ji yayi babu ita babu alamunta nan yafara shashime amma bai jitaba,
"Hafsa, hafsa, dama wayo zakimin kenan.."
Jin bata amsaba yasashi sauka daga kan gadon yafara bin bangon dakin yana lalubenta domin bai zo da wayarshiba,
Shiru bai jitaba sai can yajiyo kamar motsinta awurin gaban mirror, ahankali yataka yaje wurin, hannayenshi ya mika da niyyar damkota amma sai aka samu akasi suka sauka akan abunda yaketa zumudin samu yanzu,
"Wai wai yaya yusleem..." Tace dashi tana rike hannunshi,
Rikota yayi ya dagata yadorata akan kafadarshi ya lulubi gado ya hau har lokacin tana kan kafadarshi,
"Allah ne yaga zuciyata shiyasa yabani cikin sauki.." Yace da ita yana kokarin kawar da sleeping gown dinta,
.
"Dan Allah kayi bacci kaga daga tafiya kadawo..."
Murmushi yayi mai sauti wanda har sai da ita kanta taji,
Bata kara jin muryarshi ba har tsawon wani lokaci,
Duk da cewar bacci yacika mata ido amma haka tahakura,
A tsakiyar kirjinta ya kwantar da kanshi ahaka bacci ya daukesu,
Dakyar ta iya tashi da asuba saboda tsabar bacci, komawa tayi ta kwanta bayan ta idar da salla,tana kwanciya yazo ya matseta ya kwanta abayanta.
K'arfe 10 tatashi, wanka tayi ta shirya tasa atamfa blue ta fita, iya mami ce kadai a falon tana duba jaridar daily trust, durkusawa tayi tagaida mami sannan tahau kan dining tahada tea tasha,
"Yafada miki yafita ko?" Mami ta tambayeta,
"A'a mami ai sai yanzu natashi"
"Hakane kuma, can yatafi gidan alh musa mori zasu karasa wannan yawon ganin kadarorin nasu wanda suka fara rannan"
"To Allah yadawo dashi lafiya"
"Amin amin".
Koda yusleem yafarka daga barci bathroom yashiga yayi wanka yafito, ganin hafsat bata tashiba yasashi fita zuwa part dinsu Abdul, acan yashirya cikin farar shadda kal da ita yasa agogon azurfa yafito bayan yashafe jikinsa da turare, sauri sauri yashiga part din mami yasha tea domin alh musa nacan yana jiranshi, wurin hafsa yakoma har lokacin bacci take gagarumi bata da ranar tashi, yan yatsun kafarta yaja, ganin ko motsi batayi ba yasashi yiwa dan madaidaicin bakinta kiss da wuyanta,shi baisan dalilin da yasa baya iya dauke idonshi daga jikinta ba musamman ma kirjinta idan yazuba mata ido shagala yake, saida yakai hannunshi wurin sannan ya iya kwantar da kwalamarshi yafita,
Yana fitowa daga dakin itama mami nafitowa daga nata,
.
Keyarshi yadan fara sosawa sannan ya durkusa yagaida mami, sallama yayi mata yakarbi key din motarta yafita,
Lokacin da yaje gidan alh musa dake unguwar millionaires estate aharabar gidan ya ajiye motarshi wadda tafito a matsayin bare acikin sauran motocin dake farfajiyar gidan domin duk sunfi tashi aji da matsayi,
Wata zukekiyar budurwace tafito sanye da wata hadaddiyar bakar gown, hannunta rikeda hand bag da key din mota tasha takalmi mai mutukar tsini tasa bakin face afuskarta, ashekaru zata kai 30 sai kamshinta ne ke kai kawo acikin iskar dake kadawa a compound din gidan, hango yusleem tayi yana fitowa lokacin da take kokarin bude motarta sabuwa dal,
Fasa shiga cikin motar tayi ta tsaya tana karewa yusleem kallo domin ko acikin finafinan India tasan ba kasafai aka fiya samun handsome, classic guy kamarshi ba.....
***
Tsayawa yusleem yayi ajikin motarshi bayan yafito, wayarshi ya zaro daga cikin aljihun wandon shaddarshi yasoma kiran hafsat saboda yasan yanzu may be tatashi daga baccin da yataho yabarta tanayi,
Har tayi ringing takatse bata dauka ba da alama bata kusa, sake kira yayi domin yasan bazai samu nutsuwa ba har sai yaji muryarta,
Kiranta yaci gaba dayi amma shiru bata dauka ba domin bata cikin bedroom din tana falo tareda mami, saida yayi mata 5 miss called, ana 6 dinne tashiga cikin bedroom din, wayar na daf da tsinkewa ta daga tareda zama agefen gado,
"Yaya yusleem lafiya...?" Tace dashi bayan ta kara wayar a kunnenta,
"A'a..." Yabata amsa yana murmushi,
"To meyake faruwa?"
"Ji nayi ina tsananin son jin muryar matata saboda nabarota tana bacci, ko har yanzu baki tashiba?"
Murmushi tayi najin dadi,
"Natashi, gashi har naci abinci naje wurin mami muna hira"
Murmushin shima yayi,
.
"To nima idan nadawo za ayi hirar dani"
"Allah yadawo dakai lafiya, Allah ya tsare ka ya kare mana kai"
"Amin, sai nadawo"
Katse wayar yayi yana murmushi, wayar tashi yamaida cikin aljihu ya nufi kofar da zata sadashi da falon bakin alh musa mori,
Duk wadannan abubuwan da yusleem keyi akan idon wannan matashiyar budurwar ne domin tamkar tv haka ta tsaya tazuba masa ido tana kallonshi, ganin ya shige tadaina hangoshi yasata fasa fitar da zatayi ta juya takoma cikin gida domin har ga Allah tanada bukatar sanin ko waye wannan kyakkyawan saurayin, gentle mai aji,
Ta kofar dake cikin part dinsu ta bi tashiga falon mahaifin nata,
Shi kam yusleem baima san da itaba domin lokacin da yagama wayarshi kansa tsaye yanufi wurin alh musa,
A falo ya iskeshi yana karyawa, durkusawa yusleem yayi yagaida shi sannan yatashi yazauna akan kujera,
"Yusleem ga abinci kazo kazuba kaci, ina so kadauki nan gidan a matsayin gidanku domin bakada shamaki atare dashi"
Murmushi yusleem yayi,
"To alh nagode, Allah yasaka da alkhairi"
.
Duk da bashida sha'awar cin abincin amma yadan hada ruwan zafi rabin cup yana kurba,
Wani kamshine mai mutukar ratsa zuciya ya dokeshi kafin zazzakar muryarta ta cika kunnuwansu,
Cikin nutsuwa tashigo cikin falon mahaifin nata ta durkusa agabanshi tana gaidashi kanta akasa,
"Hafsat baki fita ba yau?" Alh musa yayi maganar cikeda kulawa, jin an ambaci hafsat yasa yusleem kallonta, kyakkyawa ce iya kyau saida yaji gabansa yafadi,
"Ehh abba dama saboda naji umma tace katashi baka jin dadi shiyasa ma ban fitaba"
"To ai babu komai kin san jikin tsufa dama hakane.."
Gaida yusleem tayi cikin nutsuwa da ladabi, ya amsa mata fuska asake,
Dauke idonshi daga garesu yusleem yayi yana sauraren tattaunawar tasu har suka gama,
Mikewa tayi tafita yayinda alh musa yajuya ga yusleem,
.
"Yusleem wannan itace babbar yata hafsa, itace babba tanada kanne guda hudu daya mace uku maza"
"Allah sarki.." Yusleem yafada yana murmushi,sake kallon alh musan yayi yace,
"To alh ni ina ganin tunda baka da lafiya ma kawai mubari gobe idan Allah yakaimu sai nazo muje, dama dan ban san bakada lafiya bane da bazan zo ba sai gobe"
"To shikenan Allah yakaimu, nagode yusleem"
Sallama sukayi yusleem yafita, gaba daya kamshin turaren nan dayaji yatada masa da kwalamar hafsanshi,
Shiyasa yake sauri yasamu yaje gareta ko zaiji sauki, bude motar tashi yayi cikin sauri yashiga yayi mata key yafita daga gidan,
Tun daga fitowarshi har fitarshi duk akan idon hafsat hakan yafaru saida taga fitarshi sannan takoma ciki.
Lokacin da yusleem yakoma gida, afalo ya iske hafsat da khadija suna hira da alama mami bata nan, gaidashi khadija tayi ya amsa batare da yatsaya ba yawuce dakin hafsa,
Kallon hafsa khadija tayi,
"Bari nakarasa tunda maigidanki yadawo sai wani lokacin zan sake dawowa.."
.
"To shikenan Allah yadawo dake khadija, nagode"
Rakata kofar falo hafsa tayi tajuya ta nufi wurin yusleem, a kwance tasameshi yayi rigingine yana kallon sama, hannu ya mika yarikota zuwa jikinsa ya kwantar da ita,
"Harka dawo? Amma kamar fa kadawo dawuri..."
Shiru yayi mata yana laluben zip din rigarta,shirun itama tayi aranta tana tunanin to ko dama abinda yadawo dashi kenan?
D'an dukan kirjinshi tayi, "yaya yusleem kayi magana mana"
Sake rungumeta yayi yana shakar kamshin dake tashi daga jikinta,
"Matata naji ina bukata shiyasa nadawo gareta..."
Murmushi tayi aranta tana mai jin farin ciki yana ratsata sai dai kuma har yau takasa banbance shin halaccin da tayi masa ne yake sashi kyautata mata ko kuma zuciyarshi ce tafara kaunarta?
Kasa lalubo amsa tayi dan haka tayi gaggawar kawar da tunanin acikin ranta, mirginata kasa taji yayi shikuma yana samanta,
.
Soyayya mai mutukar sanyi yashiga nuna mata cikin nutsuwa domin komai nashi dama a nutse yake aiwatar dashi babu baragada, kissing dinta yajima yanayi har zuwa wani lokaci,wasu wasanni masu sanyaya zuciya yashiga yimata wanda saida yaji yasamu nutsuwa sannan ya sarara mata,
Rungumeta tsam tsam yayi yana jin wata irin nutsuwa tana saukar masa, fatar kunnenta yakama da hakorinshi yana ciza ahankali yana hura mata iska awurin,
"Wai yaya yusleem dama abinda yadawo dakai kenan?"
"Hafsa sau nawa zan amsa miki ne? Nace miki eh, eh, ehhhh..."
Murmushi tayi tarike hannunshi duk kunya tagama baibayeta kawai daurewa takeyi,
"Ina mami tatafi?"
Sai lokacin hafsat ta tuna da cewar mami na iya dawowa ako wanne lokaci dan haka tafara kokarin zame jikinta, riketa tsam yayi,
"Mami fa ba nisa tayiba dan Allah kabari karta dawo ta samemu..."
"Kin kusa ai kibar mamin dan wallahi daukeki zanyi inkaiki inda zamu rayu mu biyu babu mai katse min hanzarina.."
Murmushi tayi tasamu ta zare jikinta dakyar tatashi tana yimasa dariya kasa kasa saboda ganin yanda duk shaddar jikinsa tayi wani arnen squeezing,
Rikota yayi lokacin da take kokarin sauka daga kan gadon, hannuwanta duka biyu tasa ta kare fuskarta tana yin wata dariyar ahankali.....
_Gaisuwar fatan alkhairi ga maman fati, ina mutukar kaunarki mamana..._
***
Ahankali ya tashi zaune har lokacin yana rikeda ita,
"Menene kike yimin dariya?"
"Babu komai.."
"Ban yarda ba"
Wata dariyarce tasake subuce mata,
"Nasan abinda kike yiwa dariya shikenan, anjima ki shirya zaki rakani unguwa"
Dadine taji ya kamata shiyasa fuskarta tasake fadada da farin ciki,
"Tom Allah yakaimu, amma ina zan rakaka?"
"Zance..." Yabata amsa tareda kokarin sauka daga kan gadon, saurin rikoshi tayi saboda jin abinda yace,
"Zance?" Ta maimaita abinda yace cikin sigar tambaya,
"Ehh ko bakya son inyi miki kishiya?"
.
Shiru tayi masa tasakeshi, dan kwalinta da rigarta da sauran kayanta wanda yayi mata fatali dasu tabi ta tattara ta nufi wurin drewar kaya ta tsaya,
Dan kallonta yayi yasaki murmushi domin bai taba ganin fushinta ba sai yau,
Tashi yayi yaje gabanta tana tsaye tana kokarin saka riga, kunnuwanshi duka guda biyu ya rike,
"Am sorry nanah hafsat..."
Bata kulashi ba taci gaba da abinda takeyi, hannuwanta yarike,
"Nace kiyi hakuri wallahi dawasa nake yi miki.."
"Ni kadaina bani hakuri saboda ba fushi nayiba"
Rungumeta yayi gaba daya ajikinshi yana murmushi,acikin kunnenta yafara yimata rada,
"Gidan su Ummi fa nake son ki rakani daga nan sai muje gidansu kawarki Maman amir"
.
Duk da taji dadin zata je gidansu da gidan su maman amir hakan baisa ta saki fuskarta ba,sassauta rikon da yayi mata yayi,
"Baby ashe haka kike da kishi shine ban saniba?"
Sake bata fuska tayi ta zame daga rikon da yayi mata, fita tayi gaba daya daga cikin dakin tanufi falo tana tafiya tana kokarin zuge zip din rigarta, tana zama mami na shigowa,
Sannu da zuwa tayi mata ta karbi kayan dake hannunta, kinkimar kayan da mamin tazo dashi hafsat tayi takai cikin dakin mami tafito lokacin har yusleem yafito yana zaune kusa da mamin,
Ko kallonshi batayi ba tawuce tazauna, dan kallonta yayi ya rausayar dakai alamun ban hakuri, dauke kanta tayi taki kallonshi,
"Mami dan Allah kibawa yarinyar nan hakuri naga sai fushi take dani daga yimata wasa....." Tajiyo yusleem yana fadawa mami,
"Ahh fushi kuma?" Mami ta tambaya, juyawa tayi ga hafsa,
"Hafsa meya faru??"
Murmushi hafsa tayi cikeda jin kunya tace, "Allah mami ni babu komai ba fushi nakeba"
"Wallahi mami karya take yi fada mukayi saboda wai kawai nayi mata wasa nace zata rakani zance wurin budurwata..."
Jin abinda yace yasa mami yin murmushi tatashi ta wuce kitchen wurin kuku tabarsu afalon saboda ta fahimci maganarsu ce ba tataba,
Ganin mami tafita yasa yusleem kallonta yana gyarawa hularshi karinta,
"Wallahi Allah hafsa wasa nake yimiki, wallahi ni banida wata budurwa kin san dai bazan rantse miki akan karya ba.."
Jin abinda yace yasata sakin ranta kadan amma bawai dan ta huceba sai dai ko babu komai zuciyarta ta danyi sanyi domin ta tabbatar da gaskiyar abinda yafada tunda har ya rantse mata,
Tashi yayi yafita saboda jin batayi masa magana ba, tunda yatafi bata kara jin motsinshi ba har karfe 2 narana, suna zaune suna cin abinci taji yakira mami awaya,
"To shikenan bari mugama sai tazo, ehh tana nan zuwa" mami tafada sannan takatse wayar tajuya tana kallon hafsa,
.
"Yusleem ne wai idan kin gama kije ki karbo mana kayan tsarabarmu, kiji wani kinibibi tun dasafe bai bamu ba sai yanzu..."
Murmushi hafsa tayi saboda tagano wayonshi kawai son ganinta yake shine ya bullo tanan,
Saida mami tasake tuna mata bayan sun gama cin abincin sannan ta tashi tatafi, baya cikin falo dan haka tawuce ciki, akan gado ta hangoshi zaune yana daddanna wayarshi,
"Mami tace kana kirana, gani.."
"Zo..."
Karasawa tayi gaban gadon ta tsaya batare data kalleshiba tun bayan kallon farko da tayi masa saboda daga shi sai gajeren wando da farar vest iya shaddar da yasaka kawai yacire,
Hannunshi ya mika ya kamo nata ya fisgota da karfi, babu zato tajita tafada kanshi, matseta yayi yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi, sam baya gajiya da lalubarta dan haka nan take yafara,
.
Duk da tana dan fushi dashi amma hakan baisata juya masa baya ba,soyayya ya nuna mata sosai ita har mamakinshi ma tayi,
"Baby wallahi bana gajiya dake,kefa kina gajiya dani...?"
Shiru tayi masa ta dauke kanta cikeda kunya,
Hancinshi yagoga ajikin nata,
"Uhm...?"
Shirun tasake yimasa, hancinta yaja tareda lakuce mata shi yana murmushi,
"Bacci nake son ki dan tayani baby zuwa anjima sai kitafi wurin mamin ko?"
Bai jira amsarta ba ya rungumeta tsam tsam ajikinshi yana shafa sumar kanta wacce tasha gyaran saloon......
0 comments:
Post a Comment