IZINA CE Page 16-20
.
Da safe k'arfe goma zainab ta kira shkr da yake yau lahadi ba makaranta cikin tsamin jiki ta tashi ta shiga Baba da maama da hafiz ne zaune tana shiga ciki mama ta harareta ta zauna rakub'e baba yace "yanzu ki gayax mana dawa kike yawo kusan shekara ke tun yaushe ma kuke tare? kallon hafiz tayi ya doka mata harara tsawa baba ya daka mata ba magana nake miki ba!" bakinta ya hau rawa "Baba karatu muke" mari taji an bata bBaba yace "mu zaki raina baki zauna kina karatu a makaranta ba sai wani gardi ne zai koya miki?" Mama tace "ai sun dad'e domin dasu take waya ai nagaya maka ta canja hali"
.
Baba yace "lefin kine ai dabaki k'wace ba" mik'a mata hannu yayi "bani nan wayarki" jikinta na rawa ta bashi "to daga yau ni na sakaki a makaranta ko? to na cireki k'afarki karna k'ara gani awaje kuma mustaph zan gayawa ya turo shashashar banza da wofi wlh kin bani mamaki shukr amma kanki ki kaiwa tashi ki bamu waje" kuka wiwi take ta fad'a kan gadonta "wayyo an rabani da haris wallahi shi nake so" haka tayita kuka har ta koshi ba wanda ya kula da ita cikin kwana 2 duk taa fige ta fita hayya cinta ga ba fita wa nan kenan .
Yau satin ta biyu kenan ta rasa madafa ga ba School so take kawai ta saamu damar yiwa haris waya cikin saa saiga mardiya nan wajen 3 taji dadin zuwanta Maridya tace "yanaga kin rame?" shkr tace ke Ina cikin wani hali yanzu an rabani da haris an hanani Makaranta an k'wacen waya"
.
Mardiya tace "duk me yasa?nan tace kawai don anganni amotar sa" Maridya tace "kinga abinda Nake fad'amiki ko? hmm wallah da ace son gaskiy Yake miki da tuni yazo gidan nan kan Maganarki tunda yaga shiru baya jinkI"
Shkr tace Bani aron wayarki pls nan Mardiya ta bata dama ta hardace number din haris ta buga kirr sai ring take wajen three times saai ana hud'u ya d'auka jin muryarsa yasa ta fashe da kuka "haris" nan yace "shkrta meya faru ne? wayarki akashe naje sch naku ance bakya zuwa" nan ta gaya mai dalili yaace "oh no an kwafsa mana" shkr tace "yanzu dai kawai ka turo manya haris" yace "kai inada tafiya wata hud'u kinga kuma sai nayi fafutukar amincewar su Dady don ba lalle a Amincen Aure yanzu ba amma zan san abinyi" nan taace "duk abindaa kaa yanke kabugo number nan" yace to nan ya kashe dama handsfree tasa mardiyya tace "kinga ko wallahi ba Aurenki zai ba jikin shkr yayi sanyi shikam haris sam be d'auki maganar da muhimmci ba haka ya basar domin ba aure agabansa yanzu dan so yana santa amma ba aure agabansa yanzu haka y manta da maganar, sati daya da maganar su ya d'aga egyt bai sake bugo wayarba itakam shkr ganin hakan yasavtasha jinin jikinta duk tayi sanyi ta rasa mafuta.
Ana hakkan iyayen mustaaph suka kawo kud'in zance dana saka rana inda aka sanya wata buyi domin baba yace baisan asaka da yawa. kuka sosai shkr takeyi kullum idan suka buga wayar haris akashe ga lokacin biki yana k'aratowa mama kuwa shirye -shirye kawai suke ba wanda kebi takan skr tun tana jiran haris har ta ta hkr.
.
Yau da take zaune adaki tana jin Rai dangin goro da ake aradio ana gamawa aka sako programm na malama Tasalla nabilsi tana magana akan tab'arb'areaw zamani da rud'ar daya kewa yaran zamani inda take jan hankali kan matan dake biyewa maza suna soyayyar shan minti haka taita kawo ayoyi da tsoratarwa akan masuyi ak'arshe tace da yawa yawan wanda suke hakan sammarin basa Aurensu idan ma,anci sa' a sun aure sun,to zaman zargi zasuyi da rashin girmama juna.
kashe radio d'in tayi sabili da jikinta da yayi sanyi ta hau kuka tsoron ALLAH ya shige ta da nadamar biyewa haris da tayi tunani ta hauyi yanzu ya zatayi nan ta d'au d'amarar neman yafiya ga ALLAH da istigfari tun daga lokacin take ta istigfari kullum dare bata bacci sai sallar dare tare da neman yafiya yanzu ko yaushe karatun kur'ani take haka taje tanemi yafiyar mama da Baba suka yafe mata nan taji dad'i yanzu tana saurarar mustaph su mama sunji dadin ganin sauyawarta.
Haka lokaci yayi taja har lokacin bikin ya k'arato ansha shagalin biki sun shirya da meena kawayenta sun yawaita haka akasha shagali aka mika ta gidanta amarya ta tare
Tunda taje gidan mustaph ke Mata wata zafafaffiyar soyayya da kulawa nan danan ya mantar da ita komai ya dasa k'aunarsa aranta ayayinda takeji ba ishi lalle shedan yaso rudarta da tuni ya rabata da jarumin namji a yanzu ne ta gane haris bema iya soyayya ba kan musty nan ta goge haris aranta hakan suke fa rayuwa cike da so da k'auna har bata so ta tuno da abinda sukai tare da haris setaji ranta yaa b'aci har tukwicin mota musty yayi mata saboda aman lafiya.
Shekarar ta d'aya yanzu da aure wata rana da yamma tafara ganin kiran haris inda yace ta yaudareshi bata bari ya dawo sunyi Aure ba, bayan tasan yana sonta ita kuma tace yayi hkr tayi aure ALLAH baiyi ita matar sa bace shi kuma yaci alwashun bazai rabu sa ita ba domin tasa ce.
kullum sayya kirata ta canja layi wajen uku amma bata sanin inda yake samu t ta shiga tashin hankali duk ta rame domin barazanar da yake kan,sai ta yarda sun cigaba da shanawar su ganin taki hakura yasa ya kawo mata hoton hakan ya dimautata ganin ita dashi a hoton manne da juna suna ta kiss ga hannunsa kan kirjinta bata tab'a zaton ya d'aukesu hoto ahakan ba.
AN DAWO LABARI
www.itzays.tk
ANDAWO LABARI
.
juyi tayi tare da muskutawa saboda jin kanta da taji yayi nauyi tashi tayi ta zauna ta rafka tagumi wayarta ta fara laluba amma bata jitaba sai hotunan data jiyo nan ta d'auko ta kallah ta fashe da kukaa a ssalub'e tag tashi ta bud'e wardrobe nata ta cusa a ciki ta mayar falo ta fita ta samu gurri ta zauna ta kalli agogo hud'u saura tunani tafara kode ta gayawa musty ne wata zuciyar ta kwab'eta kan zata taso da balli wayarta ta auka ta latsa numbobi ta kamo sunan mardiya ta rangad'a mata kira ring 2 ta auka shkr tace "aminya kina gida?" Mardiya tace kizo ina buk'atar taimakonki plsss" mardiya tace "meya faru?" "kede sekinzo"
" ok ki jirani zuwa gobe da safe" tace "ALLAH ykaimu" ayanzu mardiyy ce kadai kawar shkr domin itace ke mata kawance na amana tuni ta rabu da hassana domin ba kawar kirki bace nan ta tashi tayi sallah ta shiga kitchn:
.
Bangaren haris kuwa zaune a d'akinsa tsumayi yake yaji kiran shkr kan amincewarta yaji shiru gashi sai buga wayar ta yake akashe nan yaja tsaki "lallema yarinyar nan" kallon kudu da arewa yayi ya mik'e zai fita saiga bala abokinsa nan suka cafke bala yace "yadai mutumina nazo ka bani 4k ne wlh nashiga kwata" haris ya tabe baki yace "kaci sa a dama ina nemanka kasan na sakawa shkr tarko da wuya in bata fad'a ba" tafawa sukai Allah mutumina jerawa sukai suka fita sharholiyarsu.
.
Washegari da safe shukra tun wuri ta tashi tayi breakfast musty Ya shirya ya tafi office karfe goman safee kiran haris ya shigo tak'i d'auka haka yayi ta Kira karshe y turo msg da sauri ta bude inaso ki sani yauda k'rafe hud'u inason ganinki kizo nan city park idan ba hakaba su nan aurenki matacce kuka ta saka na shigaa uku haka ta cire d'ankwali ta hau kuka wiwi har mardiyya ta shigo bata sani ba "lafiya mezangani shkr ko wani abunne ne y hadaku da musty" shkr ta share hawaye "da ace shine ma da sauk'i zamu shirya kanmu mariyya se yanzu nake dana sanin sanin haris domin ya zamemun jaraba yanzu ya hanani zama lafiya agidana" mardiyya ta zauna "wai meke faruwa ne? Kinsani a duhu" nan shkr ta kwashe komai ta gaya mata amma ta rufe hotunan daya kawo mata bata fad'a ba "tabbs shkr haris yacika shed'ani ya rasa me zai kokawa da ita sai sunanar ma aiki" shkr tace "yanzzu hakan nan yayi mani text wai mu had'u anjima inba hakaba , zai mutu" mardiyya tace "tab! wlh karkije haka kawai zzanbaki shawarar karki fad'awa, musty" shkr tace "sis zan gayamai saaboda kardaaga baya yaji kuma abin yafi haka"
Eh daa wan nan ma shkr kede karki soma zuwa" shawarwaari ta bata ta sukai sallama kan zasuyi waya tunda ta tafin ta shiga tunani kiran sane y shigo nan ta shiga rud'ani haka ta dauka azafafe tace "malm kadena kirana"x dariya yasa "shkr kenan har kinmanta shanawar da mukayi ai bakida wata fangima awajena"
jinjina kaitayi cike da takaici me dauke,da tarin nadama "ya isa haka da da yanzu ba daya ba koda na biyemaka kai ka rud'eni yanzu ni kam ALLAH ya shiryeni yanzu kaima ina fatan zaka shiryu"
.
Haris yace "Daga baya kenan yanzu hakan nan gani zaune da waya a hanuuna gefe ga systerm kinji na rantsae inhar yau baki zoba wlh saina watsa hotuna nan duk wata kafar yad'a sakon ni irinau insrgrm, tweeter ,watsup fecebook da suransu kuma sunanki zan saka ke hatta email na mijinki na sani ta nan zan tura mai bazan iya rabuwa dake sabida na dandani zumarki ke macen gaban goshi ce don haka duk abinda zanyi sai nayi dana tura kinga kuwa fitowama saiya gagareki"
Jikinta ne ya hau rawa ta wullar da wayar dayake handsfree ne tasa tanajin dariyar sa da k'arfi ta fad'a "haris dan grman ALLAH kayi hkr ka rabu dani"
"shkr ai sekin dawo gareni zan kyaleki wlh kinji na rantsae in bakizo city park ba karfe hudu saina watsa" jikinta na rawa "zanzo" yawwa "ko kefa banda african time kit,ya kashe" zubewa tayi akan kujera ta dora hannu aka wayyo na shiga uku kaicona dana biyewa san zuciya gashi ta kaini ashe haka rayuwa take tabbas naga izinah ya ALLAH kakawon dauki kwanciya tayi jin kanta na bugawa take,baci yq dauketa.
www.itzays.tk
.
Ba ita ta farka ba sai 3 tun safe ko abinci bata ci ba shayi kawai ta had'a don bata sha awar cin komi msg ne ya shigo ta bud'a "karfa ki manta hudu ta kusa" rafka Tagumi tayi haka ta zari hijab ta dau waya Ta turawa musty cewar ta tafi gidan kanwar babarta motar ta ta shiga tana tafiya tana kuka wajen 4:30 ta k'arasav shigar ta keda wuya ta gano shi gabansa ga drinks yana zuka had'e rai tayi ta doshi wajen atsaye ta tsaya "malam gani" murmushi yayi "kin karya doka amma saboda sonda nake miki na hakura gaskiy nayi rashi" harara take zuba mai ya tako yazo gabanta "dama abinda nakeso kisani shine doka ce duk randa nake bukatarki to zamu hadu a otal tunda kink'i kaso aurenki ki aureni gobe kizo idan ba hakaba kiga aiki da cikawa" mari yaji ta bashi idonta yayi ja "haris bana tsoron ta mutu balle tayi rai duk abinda zakai mu zuba dan halak ka fasa aga wanda zaici kasani duk wanda Allah ya shirya ya shiryu kenan ALLAH shi zai rufan asiri bazai sa na tozarta sunnarsa ba koda zaka kasheni wlh bazan biye makaba wlh nayi dana sanin had'uwa dakai mayaudari"
.
Nan ta juya tana kuka ta tafi cikin fushi ya mike yayi bal da teburrin "saina nunawa shkr bakin rijiy ba wuriin wasan makaho bane wlh saina kashe auren kuma na aureta" afussace ya shige motar sa ya fita.
Tunda ta koma gida take kuka ko girki ta kasa Nan da nan zazzabi ya rufeta ta rasa madafa bata son aurenta ya mutu nan ta kudiri aniyar gayawa musty komai ta fanjama fanjam karfe 6 ya shigo gidan ganin halin data ke ciki yasa ya sunkuceta ya fita da sauri ganin bata motsi asibitin dake gavansu yaje nan suka karb'eta emergency doctor ya dubaata yace damuwa da eashin cin abinci ne sukai mata yawa nan yayi treatment nata 7 ta farfad'o likita ya rubuta magani suka koma gida haka musty yaje ya dafa indomie ya kawo dakyar taci.
Bayan Ta gamaa yazo ya zuna ya kalleta dear meya sameki? rungumeshi tayi tana kuka "banason na rabu dakai yazama dole na gayama matsalata tsohon saurayina don ban aureshi ba shine yakemin barazana nanta gaya mai komai amma ta boye zancen hoto idan musty yay ja yace "lalle wan nan zai sanr yazzo gona ta" karbar numbee,din haris yayi a wayarsa ya tashi ya fita.
da kyar ta tashi taje taaa yo alwala tazo ta hau sallah haka ta zauna taita adduaa kan ALLAH ya rufa mata asiri musty kuwa yana fita yaa kira haris ya dauka musty cikin fuahi yace "wlh idan baka rabu da matata ba saina nuna maka baka da wayo"
Haris yace au ta sanar maka " to muzuba ai ba wata fangima sa zakai mun don haka koni ko kai akan shkr"
Musty cikin takaici ya kashe wayar kamar yayi kuka wani zazzafan kishi ya cikashi dan yanda yakeji da ace zaiga Haris ba makawa inda bindiga saiyya harbe shi. tsaki yayi ya koma gidan ya zauna inda shkr ke zaune tana kuka musty ya rungumota yana shafa bayanta nan bacci ya d'auketa k'arfe goma ya tasheta suka tafii daki.
.
k'arfe goma sha biyu na safiyar lahadi Haris na zaune sai buga k'afa yake sai zuk'ar taba yake yana zaune cikin mota ya zuro k'aafar sa bala ne ya bud'e gaban motar ya shiga Haris yace "big boy yade ko garin ne? haris yace "na rasa yadda zanyii na yakice shkr ina sonta yarinyar ta hadu don nasan shegen mijinta da wuya ya sakota shida ita sun batan rai wallahi sati bazaiyi ba saina raba su na aureta wai harni mijinta zai gayawa magana dole na bashi alamar dazai shiga rud'ani"
.
Bala yace kaima kaika zauna Kana batawa kanka lokaci kawai ayita ta kare tunda taki baka had'in kaai ka bata shawarar k'arshe in batai ba kawai seka d'au mataki" yawwa ka kawo shawara nan ya jasu suka tafi bayan kwana biyu shkr hankaalinta ya dawo jikinta tama manta da wani Haris yanzuma da take zaune tana karanta littafin meemi murmushi take don jin yanda jaruman littafin ke zuba soyayya kamar ba gobe. dede lokacin taji k'arar waya bata duba ba ta d'auka "shkr kizo city park anjima da misalin karfe hudu ina son ganinki if not wlh zaki sha mamaki sainaje na tayarwa da iyayenki hankali sai nayi abunda zasu tsine miki" gabanta ne ya fadi haari ashe tsohuwar soyayya na komawa gaba da zalinci don ALLAH kabarni na zauna agidana lafy don ALLAH ka kyakeni"
.
"Zancen kikeso shkr wlh in baki zoba ki tanadi abinda zaki shaidawa iyayenki" kit ya kashe zama taayi tana tunani k'arshe ta yanke shawarar zuwa tayi don tayi mai kashedin karshe.haris kuwa sai washe baki yake domin yasan target d'in da yayi dole komai ya cab'e murmushi yayi ya d'au waya "bala kaje ka kai fa ka tabbatar komai ya yiwu bana son asamu matsala ,san nan nan da rabin awa zan bugo maka sai kayi aiki na biyu" nan ya kashe.
.
karfe hudu daide ta faka motar taa gaban wajen ta bude ta shiga ciki yana tsaye yana ganinta ya tawo "welcm beauty" fuskart a tamke kamar an aiko mata da mutuwa yace "ga guri zauna musha drinka" nan tace "ba zama zanba ka gayan mene ne?"
.
" pls ki dawo gareni ko kizo mu cigaba da inda muka tsayaa" kallon banza ta watsa mai Allah ya tsare ni wlh da in koma irin rayuwar nan gwanda na rasa raina"
dariya yayi yadau wayarsa yaa kira bala yana dauka yace "lokaci yayi" nan ya kashe yayi murmushi "babya meye?" baya tayi ya bita taji wajen arufe juyowa tayi "malam meka ke nufi ne?
.
AAcan kuwa b'angaren musty lokacin karfe biyar yana kokarin fita daga office don komawa gida yaji kira ya shigo wayarsa sallama yayi daga can akace yanzu hakan nan matarka na tare da tsohon saurayinta suna soyewa kaje city park don idonka ya gane maka" kan yayi magana kit aka kashe take fuskar musty ta canja ya shiga rud'ani da firgita kokwanto yaashiga yayi mezai kai shkr wajen wani juyawa yayi afusace ya doshi motarsa har ya bud'e yaji ana kiransa ganin masinja yazo "yallabai gashi daazu wani yace a baka" mika mai yayi yace "ok"
.
Nan ya shiga gaban motar kanya tashi motar ya bude Haka yaci karo da picture wanda suka d'aga mai hankali yaji duniyar na juya mai afusace ya tuka ya juya baya yaayi hanyar da akai mai kwatance.
.
Shkr kuwa tsugunnawa tayi tana kuka ta dago "ALLAH zaimin sakayya bazan taba yafemaka ba" ahankali ya tako yazo ya bud"e mata da sauri ta suri jakarta tafita tsayuwa tayi a kusada get don ta dauko muk'ullin mota sai jin hannu tayi ajikinta tana juyowa ta kwashe Haris da mari zatai magana ya kamo hanunnta dede lokacin musty ya danno motarsa tun kan ya budw motar hawaye suka fara ziraro mai afusace ya fito kan Haris yayi Bai aune ba ya janyo shi ya kaimai naushi abaki nan ya dafe gun ita kam shkr na gefe tana kuka musty ya kuma kai masa naushi haris ya tare shima yayi kokarin ramawa musty ya tare ganin hakan yasa shkr ta shiga tsakani ganin mutane sunfara taruwa awajen afusace ya janyo shkr ya wullata mota ya figa.
Haris kuwa duk dukan dayaci seda ya Murmusa ganin samun nasara hakan shima ya shiga mota ya tafi.
.
Kuka kawai take tirka inda musty ke a tsaye ya dago ya kafa mata jajayen idauwansa da sula rine saboda takaici "Ashe cin amanata kike shkr? ashe maganar da kikai mun k'arya ce kin cucueni kinci amanata, kina da aurena kina bin wani"
" wlh musty tunda na aureka bantaba kula wani ba na gayama tsohon saurayina ne wlh sharri yaso had'an zuwa yayi ya kamota ya matse ta "me kika daukeni? yanzu a ina naganki ?ko zaki cemin bake kika kai kanki ba?" wulla mataa hotuna yayi "wan nan kuma yaushe kuka yi?"
Dena gani tayi nadan lokaci san nan ta dawo jiki na rawa ta dauka "wlh bansan anyi ba" dauka tayi ganinta ta dashi sun kafa kai suna selfie kowanne na dariya daya kuma ya kwanto a kafadarta dan sanyi taji daba wancenn hotunan baane da tasan se muatu yakusa makureta
Shkr kije gida shkr na sakeki saki daya "innalillahi wa inna ilaihi rajuun" kuka ta fasa "haris ka cucen" shikam musty fita yayi kama wani mahaukaci sai kishi dake cin sa.
0 comments:
Post a Comment