IZINA CE Part 1-5
.
Hawayen dake kwance A saman fuskar ta ta share ta mik'e cike da kasala tana maijin Jiri na neman kwasarta.
kiran wayarta ne ya karad'e d'aukacin ilahirin d'akin da take ciki, da sauri cike da Razana akan fuskarta ta juya da alamar tsoro akan fuskarta. Jayuwa tayi kusa da wayar takurawa screen din wayar ido. Jikinta na rawa ganin me kiran wayarta ta, tafi minti biyar atsaye har kiran ya katse bata d'auka ba. Adaide lokacin ya kuma shigowa cike da fargaba ta d'auka had'e da cewa "hello" daga can akai magana yayin da ta saka Speaker domin taji da kyau.
Dariya me maganar ya kwashe da ita.... "Uwargidan Musty"
dafe k'irji tayi donjin muryar wanda take tsammani,take ranta yayi matukar b'aci da kakkausar murya ta maida mai magana.
"Haris na gaya maka ka rabu dani! meya sa kake san sani amatsala ne ehe?? Akanka na canja layi taya akai ka sami wan nan?? ka takurawa Rayuwa ta kaji tsoron Allah!"
Dariya ya kwashe da ita "lalle Shukura harkin manta waye ni? ai to kisani duk inda kike nasani duk wani takun ki kisani akwai wani target danake akanki kuma hak'a na yakusa cimma ruwa,ina baki shawara daki samawa kanki Lafiya ki sallama na rasa inda kika koyo taurin kai yanda nasanki simple baby ceke"
.
"Enugh! Haris" ta fada cike da fusha "baka da tunani ne? nifa matar Aurece! don haka ka fita harkata domin na maka nisa kasani ina d'auke da igiyoyi uku akaina sunnar ma'aiki nake yi don haka ka rabu dani haba sekace baka san kima da darajar sa ba! to this is the first nd last da zaka kara kirana if not zan baka Mamaki".
K'it ta kashe wayar ta zauna ta dafe kai dake sara mata, wasu Hawaye ne ke kwaranyo wa akan beauty face nata idanuwan ta sunyi luhu-luhu alamar ta dad'e tana kukan.
**********
Ya Dad'e tsaye akanta yana kallota Wanda ita ta Lula Duniyar tunani D'an gyaran murya yayi ta d'ago firgigit cike da tsoro kar Allah yasa beji wayar da tayi ba. Dan murmushi ta saki ta mik'e "Mustyna welcome" cike da D'an tsoro.
D'an kallonta yayi yace "Shukra na yade? na ganki duk kin birkice" kafad'arsa ta dafa "Mustyna yaushe ka shigo?" kamota yayi suka zauna gefen gado yace "yanzu na shigo na ganki kin Lula duniyar tunani kode tunani na kike ne??"
.
Murmushi tayi tace "eh mana tun d'azu nake missn d'inka."
Dariya yayi ba wani nan kede na rasa kwana 2 me kika sa aranki, duk kin fad'a haba babyna kome ke da munki ai seki gayamin ni zan share miki Hawaye."
Gabanta Ne ya fad'i nan ta tuno da kahon zukar da Haris ya kafa mata tun sati uku da suka wuce kullum sayya kirata yana Mata barazana.
Hure Mata ido yayi firgigit ta dawo daga k'aramin tunanin data lula "yace inaga senaje anmin checking naki" dariyar yak'e tayi tace I know my dear nasan ka damu dani, Murmushi yayi ya lakuce Mata hanci "Ashe kinsan zan iya Amma kike sakaci." Dariya tayi med'an sauti ta mik'e tsaye "Oya muje kayi wanka ka canja kaya kaci abinci."
"Yawwa babyna" nan suka mike atare suka fita daga d'akin.
*********
Can kuwa b'angaren Haris bayan ta katse wayar ya k'urawa wayar ido cike da zogin Zuciya ya cillar da phone d'in kan gadonsa yana cije leb'e tare da shafa sumar sa, murmushi yayi "ni shukra zataiwa haka! lalle dole na nuna mata kuren ta domin ta lalatan tsari na hannunsa ya d'unkule ya D'an daki gefen gadon ya mik'e yana kai-kawo a d'akin azuciye ya fita harabar gidan su ya d'auki motar sa ya fice.
Drect gidan abokinsa uzaifa ya tafi yana k'ok'arin shiga Shi yana fita ya gano Shi "Aa frnd daga ina?" yace "kai raina abace yake" uzaifa yace "meyafaru?"
jingina yayi jikin motarsa yace "wai shukra ni tayiwa haka?" uzaifa yace "to wai mesa bazaka k'yaleta ba komi taima ai yanzu tayi Aure."
Da k"arfi ya daki motar sa "No uzaifa babu yarinyar da zatai min haka na k'yaleta" uzaifa yayi tsaki "sekai tayi to dama an gayama don kunyi rayuwa baya dole sai ta Aureka tab! ja jiki" haushi ne ya ishi Haris yabar wajen tare da kokarin kiran wata new budurwa da yayi suka hau hira wan nan kenan.
.
Zaune take a falonta tana karanta wani littafi taji Ana knocking door D'an tsaki tayi ta tashi ta bud'e razana tayi da gudu tayi baya can kuma ta tsaya tana mai zare ido cike da in ina tace "Haris wai Mena tsare maka ne? ka rabu dani da da yanzu aiba d'aya bane Me yakawo ka gidana ehe?"
.
Murmushi yayi yana k'ok'arin shigowa nan ta danna k'ofar da k'arfi yayi baya taga-taga zai fad'i nan ta tsaya tana huci "wlh ka fita konaima ihun kwarto."
Shuky yanzu har kin mantani ni haris kin manta rayuwar da mukai abaya karki hukuntani da rashinki mana kece life d'ina"
Wani kuka ta saka kaicona ni shukra nayi dana saninka arayuwa gashi yanzu ka hanani sakewa agidana nan ta d'aga murya "na gayamaka ka rabu dani nayi aure yanzu don haka ka k'yale ni wlh zanma ihun kwarto."
"Ke shukra dakata Haris ya ambata wane dare ne jemage be gani ba .....? to kisani ni Haris na biyo miki ta laluma kinkasa fahimta wlh zan biyo miki ta bayan gida komi ta fanjama- fanjam."
.
Numfashi taja na kuka "ta Allah ba taka ba Allah bazai baka damar keta haddin sunnah ba insha Allahu."
Murmushi yayi ya juya ya fita daga ainihin gate d'in azuciye ta d'au Hijab ta fita gun Maigadi tace "yanzu Lawan mesa zakabar wan nan ya shigon gida Hajiya kiyi hkr wlh bansan baki sanshi ba cemin yayi Shi Dan uwan me gidanne."
"To Amma kasan ance Sai ka bugo waya ka tambaya ko?"
"Ayi hkr hajiya mantuwa nayi"
"To daga yau karka Kara barin wani namiji ya shigo koda tace Shi Dan uwane Sai ka bugo an tabbatar."
yace "insha Allahu"
Nan tajuya ta shige gidan direct d'akinta ta shige ta fad'a gado ta rushe da kuka wayyo na shiga uku ni shukra meke shirin faruwa da ni? na cucu kaina nayi danasanin sanin haris gashi yana neman dagulamin lissafi agidan aurena sai maganganu take hade da kuka ta. kusa rabin awa ganin karfe 2 dede har tayi yasa ta mik'e tayi toilet tayo alwala tayi sallah san nan tashiga kitchen Dan d'orawa musty sanwa.
**********
Dukan bencin dake gabansa yayi ya zuki taba ya furzar ya kalli sani yace "wlh k'aryar Shuky ta sani kwandon shara ta manta irin Rayuwar da mukai ba irin son dabata nunan ba Amma kaga tashi d'aya tayi aure wai harni zanje gidan ta tace zataimin ihun gardi."
Sani ya mik'e "to kai har ma ta ina kasan gidan ta" haris ya harareshi "kai kasan idan inason Abu dole na samu ko? to sannu ahankali na gano gidan ta" Sani ya bashi hannu suka tafa "shegen kaya nasanka ba kada dama."
.
"Kuji tsoron Allah domin duk abinda kuke wlh yana kallonku" atare Haris da sani suka Juya ganin uzaifa yasa haris yayi tsaki "wai uzaifa na gaya ma in baza kaban shawarar yanda zanyi na kwato shukra ba to ka k'yaleni Uzaifa yayi Dariya kadai juri zuwa Rafi .......... ku rasa inda zakuyi tambad'ar ku sai gun matar aure Haris yace malam ba ruwanka."
Shiru uzaifa yayi bai K'ara cewa komi ba ya zauna jim kad'an awajen san nan ya mik'e yayi tafiyar sa.
******
Zuwa tayi ta sunkuya tana d'aura mai zaren takalimin sa shikam inbanda kallonta ba abinda yake "iluv u my wifey" ya furta d'agowa tayi ta kalleshi "me too darling" d'auko turare tayi ta farfesa masa suna murmushi hannunta ya rik'e yace "my wife agaskiy nayi dacen macen kirki datasan salon kulawa da miji akullum na kalleki sainaji shauk'in sonki."
.
k'uramata idon da yayi ne yasa taji kunya tad'an hure mai Ido murmushi yayi "the most beautiful woman" dariya tayi me sauti "hmm mustyna kana kod'ani fa da yawa"
Nan takalli agogo "Oya muje kayi breakfast bansan ka makara gurun aiki."
"Okey madam" yayi mata wani cool smiling nan da nan taji zujiyarta ta narke haka sukai breakfast ta rakashi har mota ta bashi peck a kumatu tajuyo sunawa juna bye.
wani dad'i Mara musaltuwa takeji agaskiy ita shukra tayi sa ar miji domin tunda sukai aure yake gwada Mata san yayyar soyayya suna kaunar junan su murmushi take ta bugawa har ta shiga falon ta k'irrr wayarta tayi k'ara take k'irjinta ya buga daramm!
Domin harga Allah ta manta da wani bacin rai Amma kiran nan ya tuno mata da barazanar haris akanta. Jikinta na b'ari ta wullar da wayar kan kushin dede lokacin wayar ta katsae can kiran ya kuma shigowa duba wayar tayi taga sunan mamanta b'aro-b'aro akai nan ta dafe k'irjinta cike da jin dad'i domin har ga Allah ta d'auka haris ne.
Da sauri ta d'auka "hello mama dagacan maman tace ya ina ta kira bakya kusane??"
"Eh mama ina kitchen" "ok dama ina son gaya miki ne Zahida ta haihu an samu namji yakamata ki daure kije" "kai Amma nayi murna mama Allah dai ya raya gobe ko jibi zan shigo sai zainab ta rakani tunda bansan gidan ba" mama tace "Okey Allah y kaimu sai kima duba abbanku don bai jin dadi"
Dan muskutuwa tayi daga zaman "to mama ki gaidashi sai nazo" nan ta katse.
.
Goslow ake yi na fitar hankali sai tsaki take tare da dana sanin bin hanyar ita aganinta hanyar tafi mata sauk'i da gidan nasu.Ganin ko motsi motoci basi yasa ta kashe motar ta D'an sunkuya.
.
Can kamar 10 mint motoci suka fara ja ahakan ta samu damar wucewa feeeeee motar ke gudu can ta D'an duba mirrow taga Ana binta ta baya duk kwanar da tayi sai taga motar na binta k'irr wayarta tayi k'ara ganin zainab ke kiranta yasa ta dauka tasa speaker "Hello Zee kin ganni shiru ko?"
Zee tace "eh wlh"
"Hold off ne ya tsareni" zee tace "nidai inajira don har na sare" dariya tayi "sorry sis."
Gani tayi ansha gaban motar ta gabanta ne ya fadi ganin Haris Shan kunu tayi yasa Dariya "duk guje- gujenki wollahi sai kin bi abinda nakeso" zaro Ambulance yayi ya wulla gaban motar ta yace idan kin gani ki yankewa kanki shawara domin su sun isheni na mik'asu ga Mijinki kinga kuma taki ta k'are zab'i ya rage naki" wani Munafikin Smiling yayi ya tafi ya shiga motar sa yaja .
Jikinta na rawa ta d'auka ambulance din ta bud'e wani wawan razana tayi sakamakon cin karo datayi da abinda ya d'aga mata hankali .take ruwan hawaye suka wanke Mata fuska kifa kai tayi kan sitiyari tana kuka na fitar rai tunanin tane ya tafi can cike da tarin Dana sani hausawa sukace ashe keya ce tabbas wan nan shine babban kuskuren Dana tafka d.agowa tayi Allah kashiga lamarina ka yafemin kura-kuraina Dana aikata nan ta d'auki hotunan ta cusa a jaka ta ja motar tayi gaba.
Minti ashirin ya kaita gidan su taje ta gaida Babansu tamai ya jiki tafito.
Sai kwala kiran mama mama take "gani nan wannan kiran fa? kamar zaki tashi sama."
.
"Mama wlh nasan zee na jira na mama tace aikuwa ta dad'e da shiri kuma mama kinga banganta ba bata d'akinta fita tayi da sauri ta ganta gaban mota tace "lalle ke har kin likimo aciki" tace "eh ai Naga ke d'ince sai aslow kin fiya nawa" haka ta jasu suka tafi.
Safa da marwa kawai take ad'akin yayinda fuskarta ke d'aukeda matuk'ar damuwa d'age kai tayi "mesa zakana takuramin Haris kak'yaleni nai zaman aurena mana haba! ita kad'ai take magana kamar wacce ta zare tabbas duk Wanda bai gina rayuwa mai kyau ba a samartakar sa lalle ya tafka babban kuskure bantab'a sanin abinda nai zai dawo ba sai yanzu ya Allah ka rufan asiri cikinta taji ya bada kuuuu alamar yunwa ya tsine fuska tayi tare da shafo cikinta Sam bata sha 'awar cin abinci ma domin tarasa madafa.
Muskutawa tayi ta matsar da hotunan daga gabanta don kallonsu na sawa zuciyarta na tsalle. sanin yau sai shida musty zai dawo shiisa batai k'ok'arin girki ba haka ta zauna ta lula duniyar tunani tiryan- tiryan rayuwar ta tabaya ta fara dawo Mata tamkar ashirin fim.
TUNA BAYA
Ku biyo Meemi donjin abinda ya wa kana arayuwar Shukra nasan kuna da tarin tambayoyi kan meye alakar haris da shukra da kuma dalilin da yasa ya takura Mata idan kuna biye tiryan tiryan da sannu 'yar mutan kano zata gamsar daku.
********
TUNA BAYA
.
Gidan Alhaji ibrhim matsakaicin gidane mai d'auke da Matar Aure guda d'aya da yara biyar Nazir shine babba sai Shukra san nan Zainab sai halima da Auta Muhd yana zaune agarin kano a Unguwar tudun wada.
.
Allah ya rufawa Alhaji ibrhim asiri inda daide gwargwado yake da rufin
Asiri ma'aikaci ne a makarantar Secondry inda da yake shugaba wato principal yana da tsantseni da zafi kan yaransa sun taso cikin tarbiya me kyau da girmama na gaba. Matar sa Hajiya Maryam ta kasance me sauk'in kai da sanin yakamata tana kulawa da yaranta musammm shukra da Allah y bawa kyau data kula kuma tana da rawar kai.
.
Suna zaune dukkansu afalon gidan kowa na cin abinci Ana hira in ka dauke Naxir da baya nan yanzu hakan yana can ABU zaria yana karatu. dama Al adar gidan kenan Babansu ne yayi sallahma suka amsa sukai mai sannu da zuwa ya zauna ya basu tsarabar su d'agowa yayi ya kalli maaman nasu yace "ina shukra ne?"
.
D'an tab'e baki tayi tace "kasanta da saka abu arai wai don ta fad'i jamb shiisa take ta kuka tun bayan da taje ta dubo" kallon halima yayi "jeki kiramun yayarku" da gudu ta tashi taje d'akin su tana kwance tana kukan.
.
Halima ta tsaya kanta tace "Dady yace kizo" ahankali ta mik'e ta fita k'ura Mata ido yayi harta zauna yace "yanzu uwata Har yanzu baki daina kukan ba? yara nawa ne suka fad'i Jamb kiyi hkr next yr sai ki zana wata kinji ko" ta d'ago "to Baba" haka ta koma salo -salo.
.
Shukra yarinyace mai shekara 18 alokacin ta gama secobdry Allah yabata k'ok'ari a sch sai akaci rashin sa'a bataci ba, Allah ya zubawa Shukra farincjinin Samari ko yaushe ta fita sai anbiyo ta ance anaso. hakan k'awayenta basa san jerawa da ita saboda tana kashe musu Market ita kuma shukra irin 'yan matan nan ne masu so ace Ana son su duk namijin da yace yana sonta to zata ji dad'i kuma zata bashi number dinta.
.
Yauma kamar kullum sun taso daga islamiya suna tafiya itada k'awarta Mardiyya sun shawo kwana kenan wani Saurayi dake kan mashin ya tsaya agaban su D'an basarwa sukayi saurayin ya sauka yana kallon shukra yace "sannu 'yan mata" Mardiyya tace "kayi hkr sauri muke" shukra ta Dan mintsineta ta maida kallonta kansa ya yi murmushi 'yan mata kozan samu number naki Dan farr tayi da ido "ba matsala" nan ta bashi suka wuce Maridyya tace "nikam shukra kina ban.mamki ke kowa yace yana sonki sai kin kula shi haba sekace bakida class Ai farinjini ba hauka bane duk sanda muka fita inde aka tsaida Ke sekin bada number ke ko tsoro ma bakyaji yanda duniyar nan ta lalace" shukra tace ni mardiyya kinga bansan fa irin haka bakyau wulakanci ne shiisa ki kaga haka"
Mardiyya ta tab'e baki "adai juri zuwa rafi" kwanar gidansu tazo yasa suka rabu.
.
Tunda ta shiga gida take murmushi Tare da jin alfahri akanta nafa Ita tana da farinjini wajen karfe 7 yaro yayi sallama mama dake bakin famfo tana d'auraye kwano tace "wa'alaikumussslm"
.
"wai Ana sallama da shukra" dai -de lokacin ta fito mama tace "Jekace tana zuwa" ya fita ta kalli shukra "sai kije Har tafara tafiya maman tace "zo nan!" Shukra tad'an juyo abinda Zan gaya miki ki kula Naga koyaushe sai anzo sallama dake Haba kinsan dai babanki bai san kina fita hira bako?" sunne kai tayi "tom mama" haka tafita.
.
Arba tayi da saurayinta salihu nan suka tsaya inda suka Saba tsayuwa wajen kamar 20 mint sai ga mota ta faka k'irrr wayarta tayi k'ara ta d'aga na daga cikin motar ne yake magana tace "ok" ganewa da yayi yasa salihu ya yi Mata sallama ya tafi haka ta juya gurin na motar ta tsaya shima ya fito nan suka hau hira kowanne da kalar abinda zai ce mata ganin 8:30 tayi yasa sukai sallama ta koma gida.
.
Nan ta tarar maama nata kallon 'kofa tana ganin ta tayi hamdala yauwwa gwanda ki dawo don nasan yanzu babanku na hanya "ina dai dad'a Jadda da miki ki kula ni fa bansan tara Samari wan nan shegiyar wayar ma bata da amfani don naga sekiyi ta waya sai kace mai bussiness" shukra ta tura baki mama "Wlh niba komi bane kawai de bana san nai masu wulaknci ne" mama tace "tode ki kula ki tsaida guda d'aya" tace "to mama."
.
Haka ta shiga d'aki ta zauna tana tunani ita Sam duk cikin samarin nata guda biyar da suke zuwa babu Wanda yayi mata kawai de tana Kula su ne saboda zama wuri daya tsutsayi inji sarki..lalle
0 comments:
Post a Comment