IZINA CE Part 11-15
.
sakale -sak'ale haka take binsu abaya harsukaje fucultyn suka nuna mata k'anwar tasu.
"Meena ga k'awa munyi miki itama sabuwa ce" nan Meena ta ce "welcm suna na Ameena abdussalam kefa?" tace "shukra ibrahim" sun dan tab'a hira sukaga anata shiga hall nan suma suka mik'e suka shiga.
A kwana atashi yau watan shukra d'aya tana daukan lucture ido ya bud'e sungane kan komi itama Meenar 'yar rawar kai ce duk class nasu ansansu da shegen iyayi da rawar kai gason nuna iyawa.
.
Bayan wata uku Haris ne zaune cikin mota yana kad'a kai sakamakon dad'in kid'an daya keji can ya hangota ta tawo nan ya murmusa tana zuwa tabud'e gaban mota ta shige "My luv harka iso?" yace "waya gaya miiki ina wasa akanki tab!" nan ta murmusa "yawwa kinga sak'on dana turo miki ta whatsup?" tace aa daling wayar ba caji ne" yace "ok" nan ya figi motar sukaja suka bar farfajiyar school d'in tun sati biyu baya kenan ya fara zuwa school d'in yana d'aukanta amatsayin zaina kaita gida sai ya biya da ita wani gun daya san ba mutane ya zauna suyi ta hira, yanzu ma da suke wani waje mekamar gardn a zaune tace "nawan wlh so nake kawai lokacin Auren mu yayai ina sonka sosai"
Shafa sumar sa yayi tare da sakin wani murmushi naki wasasa ne domin ni ji nake kamar na had'iye ki nan ya kamo hannunta "baby tab'a hat nawa kiji dariya tayi ta nok'e"
"Ainasan kana sona" nan ya shafo fuskarta "kina da kyau baby pls ki bani dama na nuna miki son danake miki tace kadena tab'ani bakyau ai soyayyr da muke wlh bame irinta basai katabani ba" nan ya harareta "baby da sauranki ai yanzu soyayya itace ku nunawa juna afili d'an kiss d'in nan da hug duk da ni banayi amma nasan masuyi don bakiga yanda suke burgeni ba" shukra tayi tsai "nikam na tsani soyayyr shan minti gwanda in anyi aure ayi" d'an matsowa yayi kusa da ita baby idan mukai Aure xan baki asalin k'auna jitai jikinta ya canja batai auneba taji bakinsa anata da saurri taja baya ya matse ta kici- kici suka hauyi dak'yar ta k'wace "Haris na gaya ma banason wan nan abun kabari mi Aure mana!" nan ta juya ta d'au Jakarta tayi waje shikam jiyayi jikinsa ya mutu murmushi yayi "baby i luv u" ya mik'e ya bita har takai bakin titi sai zuba sauri take ganin K'arfe hud'u tayi nann hankalinta ya tashi kuma k'a ida duk ran talata k'arfe biyu tana gida Hon taji abaynta babyna "yi hkr tawo muje bazan k'araba wlh sonki da kyanki ke d'imautani wani murmushi yayi nan danan taji wani sonsa taji ta huce ta bud'e gaba ta shiga yaja har unguwarsu ya kaita ya ajeta abayan layinsu.
.
k'arfe goma na dare shukra suna kallo wayarta tayi kara ganin layin musty yasa tayi tsaki a yatsine ta d'auka "ina jinka" beyi mamakin yanda yaji voice nata ba domin yasan za a rina sam shukra bata damu dashi ba aganinta be iya soyayya ba, "kina lafiya?"
Tace "lau" yace "madalla to meye labari? tsaki tayi ciki- ciki babu nan yace ok dama na bugo mugaisa duk ina kewarki" tab'e baki tayi "bacci nakeji" yace "ok saidaaaaaaaa safe"
Kit ta kashe Kanma ya kashe mama na kula da ita "ke kuma zumburar me kike? na kula duk sanda yaron nan zai bugo waya sai kina jin haushi ina lefin wanda ya damu dakai dande ba shasha shun samarinki bane shisha"
"Mama fa bashi bane" tashi tai ta shige daki
.
k'arar kirarn harins ne ya shigo nan taji wasai a zuciyatta.
"Tawan" naam "nawan wlh my dear wlh kaine araina"
"Nima hakan tawan hau whtsup ki gani" da saurita kimtsa ta kwanta ta hau online Olready yana online gani nawan yace "wlh kamar na had'iyeki nakeji. uhum "haris kenan kanka ka sani wlh babu wanda nake k'auna face kai wlh akanka xan iya komi"
wani dad'ine ya ishe shi jin kalamanta yace "beauty bari kiga wasu pictures amma fa sekin daure don kawai na nuna miki ne wata banzar yarinyace ta turon wai fa ala dole sona take amma sam batada kamun kai." shukr ta hade rai "dama kana da budurwa bayan ni?" ta tura mai sad face.
"Tawan kema kinsan keta dabance banda kowacce budurwa bayan ke wan nan itake kid'anta domin bata gaba na nan ya kalallamet harta hak'ura tace ya turo mata ta gani take ya watso mata wasu bad pictures da sauri ta rufe ido tana sallallmi "amma wann ba tada kamun kai" yace inafa nan tai shiru tana kalla yace "yade?" ta maida mai "wlh wani iri nakeji" nan ya samu dama "ko nazo ne? tace "ina? yace gunki ta watsup nan ta sa dariya ,ganin ya samu dama yace bara na na kiraki
haka ya kirata yana ta kod'a surorin jikinta ita kam tanajjn dadi tun tana jin kunya tazo tana sonji jin yanda muryarta ta canja yasa ya hau yi mata maganganun da basu dace ba haka ya tayar mata da hankali yayi mata bye ya kashe.
Zaune ya tashI "yes hak'ana yakusa cimma ruwa angaya mata ni nawasa ne nan ya nemi layin wata Budurwar tasa ya kira .ita kuwa saida taje tayi wanka lokacin kowa yayi bacci ta dawo ta kwanta ta samu kanta da son dad'a ganin bad pictures din nan wan nan kenan.
.
Tuni Haris yakoya wa skhr chatin na batsa haka xaita turo mata vedio tana bud'ewa idan sun gama chat ya bugo mata waya su cigaba yana mata xancen batsa tun tana kaucewa har ta saba in basi bama bata jin dadi nan shukr duk t futsare.
A SCHOOL inta je batasan zaman lucture fita take ga samari kowa a class nasu yace yanaso ta saurareshi ganin canjawar datayi Meena ke mata faad'a amma bataji ,ita Meena barta da raawarkai da iyayi amma tana da kamum kai. dakwa antashi haka haris xaizo y d'auketa su je wani gun hakan y samu damar yimata su kiss da sauran abubuwa da yake dama ya gama koya mata a chat nan abun ya shigeta ba ranar banza ba da bazai yi romance da itaba .
Mama na kula da canjn shukra Intai mata magana tace karatu take tsayawa`a shcl ahakan suka fara exams na second semister nan yad'an d'aga mata k'afa har suka gama akai hutu alokacn hafix y gama ABU zaria yadawo kuwa gida ita kuwa shukr tun dawowar hafiz ta dad'a shiga matsi ga ba damar fita saboda schl ana hutu nan duk ta takura saide tai k'aryar zuwa gidansu hassana .
. yauma da Haris yazo suna zaune a inda ya saba zama gidan su hassana da yake wajen akwai d'an duhu sabili da rumfar dake gun suna hira hannunsa na hijab dinta sai lumshe mai ido take kamar daga sama sukaga wan hassana tsaye sai hararan shukra yake wani kallo ya bugawa haris da borin kunya ya janye hannun itakam shukra kunya ce taji ta kamata.
.
"Malam daga yau karka k'ara zuwa nan gidan da sunan xance wato mune banzaye ko ka maida nan gurin lalubarta ko? Dama kune masu b'ata yaran mutane Allah y shiryaka"
Haris ya mik'e "baby sai munyi waya" ya fita Be kalli wan hassna ba nan kabir ya juyo "kin ban mamaki amma Albasa batai halin ruwa ba kin b'ata wayonki wlh ashe ke ke koyawa hassana futsara ko? to daga yau karna k'ara ganinki "
Sumi sumi ta mike tayi waje yayi tsaki ya shege gida duk gidan SU HASSANAR shi kad'ai ke taka musu burki kuma suke tsoro.
Shigar shukra gida Mama dake tankad'e tace "shukra zonan" taje ta zauna ta kalleta tajin jina kai "wato ke yanzu k'afarki bata san zama ko? to ki kiyayeni dln kinga babanku bayanan ko? to aiga yayanku yana nan duk wani abu da kike karki fasa" tura baki tayi gaba tana k'unk'uni zata shige d'aki taji an doke bakin da k'arfi tasa k'ara da kuka "menayi maka?"
Hafix yace "Mama aiba sa'arki bace tana magana kina tura baki gaba dan kin koyo fitsara ni na rasa meke damunki" harara ta Daka mai ta shige daki cike da haushi biyu.
www.itzays.tk
Haka rayuwa tayi ta tafiya har hutunsu ya k'are suka koma ba wanda yaji dad'in komawar nan kamar shukra da Haris domin zasu dad'a gamewa soyayyarsu suke hankali kwance.
SHUKRA ce tsugunne gefen baba tana matsar k'walla da k'arfi Baba ya daka mata tsawa "Shukra me kike ne? wasa kike ne a makarantar? ace ki rasa me zaki fito result dashi sai pass ina k'ok'arin ki yake? first semister ai kinyi k'ok'ari ace 1.0 haba"
.
Mama dake jan carbita sallame ta d'ago tace "kaima de ka fad'a domin tasa wasa aranta kuma kullum se yamma take dawo wa idan nai magana tace karatu takeyi " kukaa take kanta akasa "Baba kayi hkr wlh nayi yanda ya dace mugwayene Malaman su suke ragewa"
"Yimun shiru ke kad'aice a Makarantar ne ?ko ni ba malami bane angaya miki bansan kan Makaranta ba? to wlh karki bari musa k'afar wando d'aya dake inde baki dage ba domin sena sab'a miki kinsan yanda nake fafutukar karatunku kuwa? to ki gyara de tashi ki bani guri."Mik'ewa tayi takoma d'aki.
.
Salon da haris ya canja shine hafiz na ajeta a schl shi kuma zai d'aukeeta su tafi wurin hutawa sam yaanzu karatun baya kanta sam bataji fadan baba ba yanzuma daya kaita wani d'an k'aramin restourent don suci abinci d'agowa yayi ya kalleta sam yanzu shukra kunya tabarta ko tsoro bataai kar wani idon sanin yazo ya gantaa ALLAHN daya sota ma ba mutane da yawa.
Bayan sun gama suka fita yana driving ya kalleta "dear bari na kaiki gidan yayata ku gaisa tana yawan son ganinki" murmushi tayi "kai amma naji dad'in jiin hakan amma schl zan koma" wani shu'umin murmushi yayi "habade kina ban dariya idan muna tare kina maganar schl karki damu dis semister zaki samu score me tsoka ni zan miki shige da fice, anan ne fa muke samun damar had'uwa."
.
kallonsa tayi ta kashe mai ido d'aya "da d'ina dakai akwai iya tsara kalamai" wani kallo yabita dashi nan suka karya kwanar unguwar suka doshi gidan me gadi ya bud'e gaban tane ya fad'i yayin da ta fito gaba yayi ta bishi abaya suka shiga falon. Wata mata tagani tsaye alamar unguwa zata "Aa wanake gani kamar haris" murmushi yayi "gaade surukarki na kawo" zuwa tai ta rik'e hannu shukra "kai masha Allah ka iya zab'e kaga gidan bakowa maa nima fita zanyi bansan zaku zoba" k'walawa me aiki kira tayi "kawo musu lemo" nan taa kawo Anty ta zauna suka dan tab'a hira "haris yace ki tafi kawai ba damuwa naga anata kiranki" tashi tayi ta ajewa shKr ledar data d'auko "ki gaida gida surukata" ta fita da sauri haris hakn ya bashi damar da wowa kusa daa shukr "babyna yadai" tace "mutafi kawai" murmushi yayi "haba de ki zauna mu huta man Pls dan dauko mun wani cup mana a kitchn naga 'yar aikin tafita wanki" ok tashi tayi yabi bayanta da kallo yaja wani gwauron numfashi da sauri ya zaro wani magani ya jefa a lemon dake gabanta ko mint ba ai ba yaa narke tana dawowa ta zauna nan ya tsiyayi lemon "baby karashe lemon naki mu tafi" ahankali ta d'aauka ta kurb'a gabanta na fad'uwa tas ta shanye kamar magic taji jikinta ya mutu kamar mejin bacci mik'ewa tayi taaji kamar zata fadi takoma ta zauna ganin hakan ya taso yaazo kusa da ita a zuciyarsa yana lalle yau zan cika burinaa 'haka ya hau yi mata su kiss nan da nan ta fita hayyacinta shimaa hakan ganin yana neman wuce gona da iri nan tafara k'ok'arin hanashi amma ba karfi domin ta kasa tab'uka komi acikin wan nan haalain 'yar aiki tazo zata shigo falon ta gansu da gudu ta koma da baya nan hankalinsa ya dawo jikinsa ita kam shukr k'arfin hali tayi ta mik'e tana layi tad'au jakarta tafita zuciyarya ba dad'i ganin hakan shima ya tashi ya fita.
Shukr har azuciyarta haushinsa takeji sa'arta dayaa be keta mata haddi ba amma duk wani romance ba wanda be da itaba kuka tasaka jikinta na rawa tana tafiya ahankali domin duk abunda suke bata tab'a tunanin zece zai je nan ba tari adedeta sahu tayi tahau haris dake gefe acikin mota sai hon yake ammmaa taki waiwaye gidan su hassana direct tace dan adedeta ya a jeta ta bashi kudi atsorace ta shiga don bata so kabir ya gantaa ya koreta dan d'akin hassna tayi tana zaune sai wulla loma shukr ta shiga kamar yar maye kwanciya tayi akan gadon hassana tace "ke shukr yana ganki kamar mara lfiy" d'agowa tayi hassna bacci nakeji bari inna tashi zan gaya miki" kamar mushe ta hau bacci.
www.itzays.ml
Bayaan awa uku lokacin k'arfe hudu dede shukr ta tashi tad'aan ji dama-dama abinda takeji ya saketaa nan ta tashi tayi wanka tad'auro alwala ta d'akawa hassna dake bacci duka da sauri ta tashi meye tace "sallah haka itama taa mike tayo sukai sallah bayan sun idar hassna ta zauna bakin gado "wai ni k'awas d'azu meya faaru ne naganki a hargitse? ga wayarki sai ring take"
Shukra ta tab'e baki "kinsan haris yau ya kusa yimun fyad'e" zaro ido hassna tayi "ke danna ALLAH!" shukr tace "kawai ALLAH ne ya kiyaye nikam daga yau nadena biyewa haris Yana tab'a jikina d'inma na dena yarda" hassana tace "tab aini kin ganni nan duk wani tab'e -tab'e ba wanda bamai da saurayina kawai de banyarda da awuce wani gun ba' kinsan mazan nan da wayo sunfimu kawai ki basar ki mai kaashedi ku cigaba da inda aka tsaya kodan kudin da yake cikaki dasu ai kya hakura" shukr data rik'e baki "au! kema dama kinayi?"
Hassna ta fasa dariya "ke yanzu fa da wuya kiga saurayi da budurwa ba ayi" nan shukra taji duk d'an haushi ya fara tafiya (Mata a kiyaye a kula da irin Samarin sa za ana kulawa karkiga wai kinada farin jini ace kowane namji ya kulaki ki tsaya to ahakanne tun ana had'uwa dana kirki har zakizo ki had'u dana banza wanda dama surarki ke rud'arrshi duk yanda zai sai yayi don ya samu biyan bukatar sa seyayi san nan akula da k'awayen banza domin suke hure wa su kunneALLAH ka shirya dukkan matasan dake wan nan d'abia)
Sun gama hirar shukr ta tashi ta tafi gida.
www.itzays.tk
Sati d'aya kenan da faruwan hakan amma haryanzu shurkr fushi take da haris yauma data ke zaune bakin bishiya a sch haris yazo da yake suna zama agun yazo ya zauna" babyna ta juyo nan yace "pls forgive me nashiga wani hali"
" Haris inde kasan ketan haddi zakayi wlh bazan sake kula kaba inama lefin tattab'enin ma da kake ( mu kula ALLAH subhanahu wata ala ya hane mumunai da kusantar zina karkiga wai kuna tab'a jikin juna kuna su kisss da romace kice wai ba komi bane ba wani abu bane tunda ba ai me gaba d'aya ba to wallahi kinyi kuskure domin kin halartar da abinda ALLAH ya haramta Allah ya shirya 'ya'yan musulmi)
"Haba shukra na wlh bana bacci da cin abinci pls ki yafemun na dena nan ya taro k'walla sai gasu nan shar shar suna sakkowa ganin hakan yasa jikinta yayi sanyi tace "na hak'ura" azuciyarta tana lalle ba k'aramin so haris kemun ba tunda yake kuka Akaina. Ganin hakan yasa ya kalallameta da hira har suka sake wan nan kenan.
"Kinga Mardiyya idan kinSaan abinda zaki gayan ne To kiyi shiru" mardiya dake zaune kan stool a d'akin shukra shigowarta kenan tana mata fad'a kan abinda take "kinga shukra wallahi watace take min zan cenki itama a schl naku take tace bakya karatu kullum akwai wanda ke zuwa ya d'aukeki haba ina wayonki yake? ki ji tausayin su baba mana duk fafutukar ganin kinyi karatu amma kina yaudararn su haba ki gane mana ayanzu muna wani bahagon zamani wallahi inbakai taka tsantsan ba sai yabi dakai ki rabu da haris sam ba mutumin kirki bane"
.
Shukr ta d'aga mata hannu "wacece wadda ma ta gaya miki ina tasan ke k'awatace? mardiya tace "k'awataace zuwa tayi Gidanmu tana ganin album d'ina taga hotonki shine fa take gayan wlh shukra ki rabu da shi haba! kefa ammiki mijima amma kin sashi kwandon shara wai sunan be iya soyayyaba wlh ba anan take ba, domin irinsu sae an aure suke nunawa ki kula! wlh duk abinda mutum yake Alllah mahaliccinsa nagani Kuma ana rubutawa akwai ranar da gab'ob'inka su zasuyi maka sheda wanda bakinka bazai yiba idan kayi aikin assha dasu su fad'a haaka na alkairi kiji taoron ALLLAH wlh kuma abin kunya ne ace wataran iyayenki suji ba baki naakee miki ba kuma na fita hakk'in kawancen mu"
Shukr jikinta yayi sanyi tace "naji zan dena nan suka canja wata hirar .,
Akwana atashi har Mustaph ya dawo daga tafiya ya gama course inyazo gun shukr saide yayi ta magana amma bata cemai uffan sede tayi ta chat da haris duk da inta dago yana mata kwarjini sam abinda,take mai yana bashi haushi yana damunsa inyayi magana ta tab'e mai baki hakan badon an riga manya sun shigaba da tunanin hak'ura yake da ita sede yabawa zuciyarsa hkr haka zai gaji ya tafi kullum kuma da abinda zai kawo mata ta amshe ba kunya wan nan kenan.
Yau Monday hafiz ne ya d'auki shukr ya kaita Makaranta akan babur dinsa yaje ya fakata ta sauka ya juya ko minti batai ba saiga haris yazo yay mata waya tazo motar sa ta shige ya figa dama sunyi dashi zasu munjibir park
Hafiz ya dawo sai waige -waige yake domin shkr taa manta handout nata yana tsaye sai mata waya yake akashe ganin meena yasa ya tafi wajenta gaidashi tayi yace "ina k'awarki ne? yanzu na kawota ga handout ta manta nata wai inama take?" dama meena nasan samun damar fadar abinda shkr keyi nan ta gyara mayafi "ai yayanmu wlh sede adage da addua domin tun second semistr saurayi ke fita da ita yanzu nima mun ja baya da kawancen namu don ta canja k'awaye duk adalilin ina gaya mata gaskiy bataji yanzu hakan ya d'auke ta sun fita kullum kuma hakane kana ajeta yake d'aukanta"
Idan sane sukayi jajawur jikinsa har rawa yake ya d'ago "meena nagode Allah ya saka insha ALLAH za a d'au mataki"
"Meena tace to yayanmu sai anjima "ta tafi shima ya hau babur ya tuka afusace.
.
Afusace ya tuk'a babur d'in zuciyar sa na tafar-fasa nan ya fafara babur dinsa don yaje gida ya fesa, dede yaje Round about ya tsaya don abasu hannu kamar ance ya juya ya nan ya gano shukr gaban mota sai kurb'ar lemo take suna dariya kan ya motsa nan bada hannu nan ya bisu abaya tiryan- tiryan haka yake binsu har suka b'ace mai da gani cikin takaici daya cikashi ya juya yayi hanyar gida mama na kitchn tana had'awa baba abinci don be fita ba yau zainab ma duk sun tafi schl hafiz ya shigo idanu wansaa jajur ya tsaya gefen kitchn kamar yayi kuka,mama ta dago ta kalleshi "hafiz yaa naganka a haka?
kallonta yayi "mama ba anyiwa shkr miji ba?"
"Eh k'warai meya faru?" numfashi yaja mama shkr ta canja wai ashe kuulm na kaita schl ina sauketa saurayi ke zuwa ya d'auketa su fita daga makaranta su tafi wani gun kawarta ta shaida mun kuma bayan na fito wallahi mama da idona naganta gaban mota na bisu abayaa aammaa suka bacen."
.
Mama kuwaa suman tsaye tayi zama tayi kan kujera yar tsugunne ta dafe kai na shiga uku yanzu duk tarbiyar da naiwa shkr kuka ta saka "yanzu hafiz bakasan inda ya tafi kaita ba na shiga uku" hafiz yace mama ki hkr kawai muga dawo warta" dede lokacin baba ya fito yana tambayarta inna gama ganin tana kuka ga hafiz atsaaye yasa yace "meya faru ne?"
malam,yanzu shkr dama dab'iar data koya kenan" taa fashe da kuka "wai meye ne? Baba ya ambata hafiz ya gaya mai "innalillahi wa inna,ilaihi rajuun ya ambata" koma wa daki yayi yana kai-kawo yakasa tsugun nan ya kuma fitowa ya d'auko waya ya dannaa kiran shukr dede lokacin suna zaune itada haris ya manna ta ajikinsa tamkar matar sa sai kashe musu selfie yake wani ai dariya wanii ai murmushi wayarta keta ring amma bata ji sabosa shed'an yana k'awata mata halin da suke ciki wanda dad'i suke ji Apple haris ya d'auko ya bata abaki ta gutsira suna aikawa juna murmushi.
Acan gida kuwa Baba wajen 20mis call bata d'auka ba hakan ya fusatashi ya aje ya juya ya cewa mama "lalle na yarda zamani ya baci ban tab'a zatan shukr zata biyewa rud'in sa ba duba da tarbiyar da muka bata ko zainab ba zatayi haka ba amma makarantar nan bata karbi shukr ba"
Mama tace "d'ane ka haifeShi baka haifi halinsa ba", haka baba yak'i fita mama ma hankaalint atashe domin gaabanta har fad'uwa yake.
Acan kuwa shkr da haris guje guje suke na ma,abota shauk'in soyayya da k'yar ya kamota suka zube agun haka suka gama shanawar su tamakar mata da miji sun manta da hakan haramci ne babba. "Nawan wai yaushe zami aure? kallonta yayi "sekin gama schl" tace "to Allah y kaimu" jakarta ta d'auko ta zaro wayarta ganin kira rututu yasa ta k'walalo ido kiran hafiz dana Baba kamar aci babu, nan gabanta ya fad'i "Allah yasa de ba wani abun ya faru ba" haris dake kallonta "yade babyta?" tace "kiran baba na gani da yawa"
" kema dea meyasa baki kashe wayarba?
nan ta mik'e "Nawan mutafi kaga k'aarfe 5 dede fa" mik'ewa yayi suka tattare abubuwansu suka sa amota "muje to amma bangajj dake ba" fari tayimai da ido "gobe ma rana ce ai nayi maaka tana dinta" dad'i ne ya kamashi "komai naki swt ne babynaa iluv u so much" nan suka shiga motar ya tuk'a suka d'au hanya .
,
Mama dake kai kawo sai hawaye take zainab dake gefe "Mama kiyi hkr insha ALLAH yanzu zaki ganta baba ne ya leko "wai har yanzu bata shigo ba?" K'wala kiran hafiz yayi ya fito "jeka dad'a duba hanya" hafiz ya tashi ya fita kicib'us sukayi a soro shukr na shigowa wani banzan kallo ya watsa mata ya duba agogonsa k'arfe shida da rabi besan sanda yaa d'auketa da mari ba kwala ihu tayi "menayi maka?" nuna mata hanya taayi suka shige ciki Mama da Baba ne atsaitsaye fuskar su duk a had'e tsayawa tayi "mama meya faru?" Baba ya daka mata tsawa "kinci gidanku" daga ina kike da wane d'an iskan saurayi ake ganinki dashi?" gabanta ne ya fadi na shiga uku Mama kuwa harara ta bita dashi ta shige d'aki duka taji ko ta inax Mama ta rufeta dashi da caribi wullar da kajarta tayi ta fada d'aki Mama ma ta bita hafiz kam yana kallo Mama tai mata duka baba ma ya shigo da bulala ya mik'awa hafiz "zane min yar iskar yarinyar nan" dama haushinta yakeji nan ya hau jibga tana ihu zainab Dasu auta kuwa sai kuka suke saboda ta basu tausayi seda ta jibgu san nan ya kyaleta inbanda ihu ba abinda take kowa,ya barta a wajenn haka taci kukanta ko abinci batayi ba nan domin zazzabi ya rufeta.
0 comments:
Post a Comment