IZINA CE Part 6-10
.
Kullum haka k'ofar gidan su sai kaga wani yazo gunta tamkar gidan maza don har jira wasu keyi hatta 'yan unguwa sun gane ta domin duk yan matan layin ba wacce ke tara samari kamar shukra kodan Allah yayi mata k'ira me kyau ne wacce ke d'aukan hankalin samari duk wan nan budurin da ake Alhji ibrhm bai sani ba domin sai 8 yake dawo wa lokacin ta gama sallamar su abun yanawa mama ciwo yauma kamar kullum suna zaune suna cin tuwo atsakar gida sabili da yau da D'an zafi yasa suka shimfida tabarma don susha iska idar da sallar mama keda wiya takalli zainab dake kai lomar tuwo "ina ita shukrar naga kinaci ke kad'ai?"
"Mama Wlh gatacan tana waya ni kuma yunwa nakeji" ran mama ya b'aci ta shiga falon ta ganta tayi d'ai -d'ai ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya sai dariya take da alama da saurayi take cikin fushi mama ta k'wace wayar "wai mesa shukra kika canja d'abia ne? Haba! kullum bakida aiki sai waya to wai da suwa ma kike ne? bansan shiririta kode k'awaye ke zugaki ne? turo baki tayi "mama Wlh bakowa da frnds nake waya wanda mukai candy tare" mama tace "bawani nan kide kula na gaya miki atoh! kuma ki tashi ki je kuci abinci inaga ko sallah ma baki ba ko?"
"Mama nayi fa!" nan ta fita ta zauna Sam jitai abincin ya fita aranta.
.
Gama cin tuwon su keda wiya yaro ya shigo wai Ana sallama da shukra da sauri mama ta fito "kaje kace bata nan" haka yaro ya fita shukra kuwa in banda turo baki ba abinda take kira mama ta k'wala Mata ta shiga shukra kina jina ko?" Tace "eh daga yau na haramta dodon da ake mana akofar gida haba yarinyr ki dake kin maida gida kullum dare kamar dandalin samari kodan to Wlh karnaji kar na gani don bakiga fad'an da Babanku yayi mani jiya ba kan wani makocin saa ya sameshi amsallaci yayi mai magana wai an sakeki sakaka kina tara samari abin yayi mai ciwo dak'yr na bashi hkr don ransa ab'ace yake" tsoro ne ya shigi shukra don tasan fad'an Baban in aka tab'oshi cike da in ina tace "Mama ki bashi hkr nadena!"
"Atoh kima cigaba keda kike sanyin karatu kyasa Babanku ya Aurar dake bakiyi karatun ba" jikin shukra yayi sanyi
.
Sallamar Baba ce ta katse musu maganar nan ta runtuma d'aki aguje mama ta tashi taje tsakar gidan domin harya zauna su halima sun kewayeshi Mama tayi mai sannu da zuwa ta kawo mai try na abincin sa. Har ya fara ci ya d'ago ina uwata take ne?? Wai mesa kullum ita tana d'aki ne?" k'wala kiran ta yayi hantar cikinta ce ta kad'a ta aje wayar ta fita tamkar munafuka don tsoro. Kar yayi mata fad'a nuna Mata jakarsa yayi "bud'e ki d'auko file ahankali ta bud'e ta zaro yace scratch card na jamb na sayo miki domin an dad'e Ana Rigistration don ma naga d'alibaina zasuyi shiisa na sayo miki" mama tace "ikon Allah yanzu har shekara ta zagayo?" baba yace "Wlh Ai kamar yaune game yawan rai" itakam Shukra in banda murna ba abinda take cike da d'oki Baba yace "to abinda Zan gaya miki ki dage ki karatu bana ki shiga makaranta don bansan zaman haka gobe sai kije ki Rigister jiki na rawa ta d'auka "Baba ngd ta shige d'aki
Haka dai lokaci yayi ta tafiya har suka zana jamb cikin ikon taci sai zaman jiran admition yau tana kwance sai sharar bacci take hankali kwance Hassana k'awarta tazo sai jitai an d'aka Mata duka ta tashi Hassana tasa dariya "sarkin tsoro yaushe kikazo? tace "ke yanzu dama d'inki nazo ki rakani kuma na gayawa Mama kawai d'auko Hijab naki" tashi tayi "ni kawai kin katsen Sweat dreams d'ina"
"Kyaji dashi nide yi sauri" sauri- sauri ta shirya suka fita ahankali suke tafiya har sukaje gun me d'inkin da yake ba nisa bayan layin su ne suna zaune Hassana na kwatancen d'inkin da takeso wata dalleliyar motace ta tsaya a wajen. Saurayi da budurwa ne suka fito suka shigo tinda suka shiga idanunwan sa na kan shukra duk da ba wani kwalliya tayi ba amma ta tafi da ruhinsa zama yayi agefen ta "'yan mata" juyowa tayi ta kalleshi ta juya nan Yace "pls In bazaki damu ba ina son number naki" tab'e baki tayi D'an karkatar da kai yayi "Gaskiy kina da kyau Wlh" murmushi tayi ta jin an yabeta jin ya samo lagonta yasa yace to bani number din mana me kyau" nan ta karanto mishi fuskarsa ya shafo "well zaki iya kirana da Haris I wll call u later" Nan k'anwar tasa ta fita suka tafi. Murmushi shukra tayi Hassana ta tab'ata ke taso mu tafi ko da yake naga kinyi Market dama ke duk fita sekin Market dama nice keda farin jinin ki Wlh danayi sha'ani" shukra tace "kinsan Mama ta hanani fita hira sede fa mi waya shima wan nan bansan me zance masa ba" duk randa kukai zaizo kice masa zaki gidanmu kawai seki mai kwatancen gidan namu sai kuna had'uwa a can ammafa inkin wankeshi sai kina yafo min." tafawa sukayi "kin kawo shawara"
*********
Cikin D'an k'an-k'anin lokaci Soyayya ta k'unsu tsakanin Shukra da Haris kullum suna kan waya tun safe inya fara bugowa har dare mintuna kad'an -kad'an aikin gida ma shukra ta rage taya mama sai de taita aiki ita tana d'kai tana waya. cikin sati biyu Haris ya siyo zuciyarta don Haris akwai iya kalamai da Lafazi na Jan hankali yau da yace zaizo tun da rana ta cewa mama zata gidan su Hassana zasu taya Mamansu aiki, daya ke yanzu duk randa wani wanda zaizo zance gunta Gidan su Hassanar take kaisu da yake gidansu Hassanar irin gidan nan ne da kowa sai abinda yayi niyar yi wato Uwa ba kwab'a Baban su kuma irin mai zuwa fataucin nan ne sai yayi wata uku bai dawo ba wan nan dalilin yasa suke sake saka ka ,itade mama na Mamakin zuwan shukra Gidan su Hassanar duk da tasan Mardiyya Itace best frnd d'in shukran amma bata zuwa gidan su kamar yanda ta tsira zuwa gidan su Hassanar yanzu saide data tambayeta cemata take karatu ake k'ara masu.
Wata uwar kwalliya Shukra taci tayi balain kyau kamar ka sura ka arce Mama ta d'ago "yanzu shukra keda zaku tayata aiki shine harda fesa uwar kwalliya haka?"
"Mama Wlh kawai sha awaryi nake innaje Ai ba baci zan ba"
"Kide kula shukr na gaya miki" wayarta ce tayi k'ara d sauri ta fita haris ne keta kira minti ashirin ya kaita gidan su Hassana da yake bayan Layinsu gidan yake.
Tun daga naisa ya hango ta nan ya zuba Mata eyes har wani lashe lips yake k'araso war ta yasa yace "ashe kallan tsoro nai miki ran nan" Murmushi tayi "mu shiga ciki nan zuka shiga suka je inda aka tanadi kujera don zamansu.
.
Dab da ita ya zauna har yana Gogar jikinta nan tad'an matsa wani kallo yayi Mata "sorry ko! ke d'ince akwai rikita mutum" hira suke sai kod'a ta yake yana yanko mata lafazai na k'auna ba abinda yake inbanda kallon lips nata da yasha red jambaki. kamo hannunta yayi ya rike nan ta fisge ta had'e rai "gaskiya kadaina tab'ani mana haris"
"Sorry beb bana iya controlling kaina ne kwalliyarki ta tafi dani"
"To nidai ka daina! komi zakai de mi hira Banda tab'a jiki"
Okay baby afuwan" tare da wani Smilling wana shi kad'ai yasan ma' anarsa yace "babyna ya kamata fa kiyi new phone cuz inaso kema kina Hawa social media D'inan! jifa wayarki Ai kinfi k'arfinta ki bani chance na kawo miki new one" nan tayi murmushi ta kad'a mai idanuwa take yaji jikinshi yarrr! Murmushi yayi ya kalleta "me kikace?" tace "Babana yace bazan rik'e Big phone ba yace sai zanyi Aure wan nan ma saboda frnds nawa ne shiisa ya bani,Samarina da dama sai da sukace zasu bani waya Nace masu Aa"
"Kai! kai! kai!" Ya fad'a da sauri ta d'ago tace "meye Darling" yace "Dankari yanzu dama kina da wasu samarin?" sunkwi dakai tayi "Ai mun dad'e dasu to nikam inde kina sona sai de ki dai na kulasu" dariya tayi san nan tace "ok dea zanyi yanda kace"
" Dat my baby shiisa nake sonki Wlh sonki har b'argo na nakeji tamkar na Maidaki cikina iluv u so much" Murmushi tayi "luv u too Wlh haris duk cikin Samarina nafi sonka Murmushin samun nasara yayi ganin duhu ya k'arato y mik'e dea ba na wuce nan ya zato bandir 'yan d'ari biyr ya mik'a mata nok'ewa tayi "No darling kabarshi" yanda tayi sai ya Birgeshi "wow babyna iluv u" Murmushi tayi mai kashe rai ta juya dai de lokacin Hassna ta shigo gidan "Aa yau haris ne? yace "eh mana kinga babyna taki karb'ar abin hannuna" hassna da yake Mayyyar Money ce take hannunta ya fara rawa "kasan k'awartawa kwai kawaici" nan ya mik'awa Hassna ta karb'a "gashi ki bata" y zaro yan 100 ya bawa hassana "wan nan kuma naki ne" godia ta hauyi tamakr tsohuwa nan ya fita yana wulla key d'auke da Murmushi kan face nasa.
,
Shukra dake zaune a falon su Hassna sai Murmushi take Sam ta rasa inda zata tsoma ranta domin haris duk ya kashe Mata zuciya. Hassana ta shiga 'shegiyar kwaba kinga kyan da kikai!"
"Ya san ranki" nan ta wulla Mata kud'in "to ke wa yake gudun masu gidan rana to bud'e kunne kiji ki saki jiki ki wanki gayu fitar da kike Ai ba'a banza ba kinga Kya dinga kashe abubuwan dake gabanki ba tareda kin takurawa su maman ba" shukra tace "hmm nida mama ta hanani karb'ar kud'in samari"
Zauna nan yarinya lokacin kine kici arziki a mazaunin sa ki barsa da nice da kyanki da farin jininki da kinga sanabe idan ma kina tsoro to kina kawo ina aje miki bakya ganin yanda 'yan mata ke kashe ado to Ai duk yawaicin kud'in samari suke ci" nan ta zauna ta tsara shukar da yake hassna akwai baki da wayo nan da nan ra ayin hakan ya shigi shukra "hassna ke kam samarinkii sazu sha wan ka kinsan Shi kansa Haris wai duk saina dena kula samarina"
Hassna tace tab! Ai kowane da mazaunin da zaki ajeshi" dede lokacin Muhd ya bugo wayar shukra da bazata d'auka ba sai kuma t dauka da sauri Hassna ta karb'e waayar ta kashe tace "bari na gaya miki salon yanda zakiyi kan ya kuma bugowa kinga inya bugo sai kice ki wankeshi nan take" nan tai Mata rad'a akunne suka saka dariya "kinga ma cajin wayr ya kare kan y bugo" hassna tace "badamuwa Ai" nan ta mik'e "keni na tafi kar mama Taga na dad'e" nan ta fito ta rakata ,tana zuwa gida bata jima ba Baba ya dawo sukai mai sannu da zuwa nan ya kirawo shukra ad'akinsa taje yace "akwai wani da yake yawan damuna kan maganarki duk da Baban sa ne ke zuwa guna nuna sha'awar hakan sabili da d'ansa ya ganki yana so shiisa na bashi dama yazo Ku sasanta" dam! gabanta ya fad'i "Baba karatunfa? dariya saka "Ai uwata na fiki san kiyi karatu Ai karatu zakiyi shi kawai zuwa zai in kina sonsa to shikenan in kuma akasin hakan se abashi hkr" Dad'i ya kashe Shukra ta tashi ta koma d'aki ........
WAYE HARIS.......
Kubiyoni dadin book din na gaba
*******
WAYE HARIS
Haris d'ane ga Alhaji Mamman maidala shahararren D'an kasuwa ne dake zaune abirnin kano tsohon D'an kasuwa ne wanda ya dad'e yana taro yana da yara biyar Sawwam shine babba sai Haris Mai bi masa sai Rabia dake Aure a kaduna San nan Khalid da Rufaida.
.
Hajiya sa'adatu Itace Mahaifiyar Haris ita kad'aice Mata agun Alhji Mamman tana da Addini hakan yasa "ya'yanta suka taso cikin d'abia me kyau inka dauke Haris daya fita izakka domin Dan gatan Alhaji Mamman ne duk yafi sansa duk cikin yaransa hakan ya saka ya tashi a sangarce tun yana yaro hajiyaa sadat tayi iya bakin k'ok'arin ta amma abin yaci tura.
Shekarar Haris 25 yana da girman gab'b'ai domin inka ganshi sai ka d'auka yayi 30 Allah yayishi da son Mata inde ya had'u dake to sayya siye zuciyarki harki aminta dashi.
Tun dawowar sa daga Turkey inda yayo dgree nasa yanzu hakan yana zaune agida sai de ya shiga wancen motar yafita waccen yace bazai aiki ba balle kasuwanci don yaga Babansa ya sakar mai nera tun Babarsa na fad'a har ta gaji
Dabiar da ya koyo acan inda yayi karatun wato Shan taba ga balain son mata inde ya hadu dake to saiya yanda yayi kuka dinke yan mata ne dashi tuli kuma yana sakar musu bakin aljihu shiisa,suke rubibinsa duk da nawani kyau gareshi Ba saide gayu kawai tabar da yake sha kam Wanda kullum sai sawwm yayi mai fada Amma baiji.uzaifa abokinsa ne da suka taso tun suna yara komai tare suke sede dabiar su tasha bam-bam tun bayan dawowarsa daga turkey ya hadu da sani ya zamanto irin halinsu daya wannan yasa suka zama abokai.
************
Kanta asunkuye yake domin data kalleshi gabanta ke fad'uwa yana dukan Tara -tara ga wani tsoro dake shigar ta tabbas gayen ya had'u wane Haris sai de kwalisa da haris zai nuna mai ,amma ko ta ina yafi Haris Had'uwa dagowa tayi zata kara tantacewa caraf suka had'a ido tayi saurin yin k'asa dakai.
"Uhum me kikace? na dad'e ina sonki se yanzu baban Ku yaban dama inason jin ta bakinki."
Bakinta ne taji yayi nauyi takasa furta ko kalma d'aya take Haris ya fad'o Mata arai ta runtse ido tabbas tana son Haris amma wan nan ma duk wani qualities da take so game da namji ya had'a Murmushi tayi Mustapha dake kallonta yace "dama ance dariyar Mace Amintar ta" nan ya mike ni zan wuce nan ya aje Mata wata leda ya fita.
.
Tafi minti goma a tsugune "meke nan nayi? Hmm wa kaina tab! banfa amsa ba! Amma har yayi Riga malam lallema wan nan Amma ba damuwa nan ta d'au shegiyar ledar da k'yar ta iya d'aukan ledar ta shige gida.
Lokaci yana ta tafiya hakade musty da shukra ke tasu soyayy kullum Shi zai kira koyaushe ya kira busy Sam bata damu dashi ba ta samarinta take.
Watan musty d'aya tare da shukra ya kuma zuwa nan yake sanar Mata zashi America kan wani course dazaiyi na 1yr kanta asunkuye tace "Allah ya kiyaye" musty yace "shukra nikam bana son tafiyar nan duk da nasan Baba ya bani ke amma samarin zamanin nan ba dama suga me kyau sai suyi ta binta well ki rik'en amana wlh I really luv u...
Ya danyi shiru tare da kallonta "kinsan da su dad nawa ma cewa sukai akawo kud'in angani anaso sai momyna tace abari na dawo wai saurin me ake nikam nasan ina tsoro plss shukr duk ki sallami wani Saurayi dake zuwa nasan bazaki rasa ba domin ke tawa ce ko ba haka ba"
Sunkuya wa yayi yai mata Murmushi sunne kai tayi na gulma Wani. kwali ya fito dashi ga wan nan waya ce don inason muna gaisawa nayi ma baba magana ya amince na baki" jiki na rawa ta amsa ya zaro wata leda ya bata ya mik'e sai minyi waya gobe jirginmu zai tashi" "Allah ya kiyaye ta fad'a kallonta yayi da murmushi saman face nasa "plss shukrana ki rik'en amana" nan ya fita ta bishi da kallo tabbs Musty ya had'u Amma tasan tafison Haris da gudu ta shig gida "Mama zo kiga wayata."
Mama dake kitchen ta fito nikam Sam da yabi ta tawa dabe baki waya ba duk da de yanzu ammiki katangar k'arfe ma da Samarin an Riga anba dake aishi kenan bake ba kula Samari" shukra azuciyar ta kam yanzu ma ta fara kulasu ta turo baki gaba haka kawai don an badani sai ace bawanda zan kula tab! Maama tace "tunanin me kike?"
"Aa bakomi mama" ta shige d'aki
***********
"Kai Amma shukra ki godewa Allah Amma wayar nan tayi kyau yau kece ke rik'e da galaxy S6. Amma musty y birgemu nayi murna."
Shukra tace "Mardiyya kinsan me? bafa wani sonsa nake ba, kawaide ya had'u ne" Mardiyya tace "aini tunda kika ban labari nasan duk ya kere samarinki har wan nan Haris d'in nide sam bemun ba" shukra ta d'aga Mata hannu "Haba agabana kina wani kusheshi" Mardiya ta rik'e Hab'a "kai sis! to meye? Naga yanzu an miki miji to meye kuma naki da Haris" shukra tace "kuma don anmun miji sai nak'i soyayya da wasu tab! ai yanzu na fara ni ai allurar cikin ruwa ce"
Mardiyya tace Wlh nasan Hassana ke zugaki saboda sam itama irin ra'ayinta kenan! ki kula da samarin zamanin nan kinga yanzu duniya ta b'aci tunfa kina had'uwa da na arxiki Wlh sai kinzo duk na tsiya zakina had'uwa kizo kuma ki had'u da wanda zai Zameki jalala dama wasu su ba wani abu ke kaisu gun 'yan mata ba sai iya shege da rage zafi na tabbata kad'an ne acikin samarin naki ke miki zancen zasu aureki don Allah na tambayeki? haris ya tab'ai miki zancen ze aureki??" Shukra ta kalleta ta harareta "bai tab'a ba sai me! yace sai yanemi aiki zaimin maganar turowa" Dariya Mardiyya ta saka "lalle shukr sai kace baki shiga class ba Haba! Wlh duk wanda zai zo ma da zancen aure shine na kulawa ba tatarikuciri ba" Shukra tace "ke ni kin damen wai angaya miki ba aure zamu ba tab!" Maridyy tace Allah ya sawwke nikam da musty nakeyi kuma agidama su mama Shi suka sani bawani Haris ba, akashe waya lafiya sai anjima a islmiyya.
.
Cikin k'ank'anin lokaci shukra ta gane wayar nan domin zuwan da Haris yayi ya ganta da waya ya karb'a duk ya d'ora ta a network yanzu ta rage waya da Samarin sun koma kullum tana chatin sabin shiga seta kai k'arfe 2 na dare tana online tana hira da samari musamman Haris baiyin chat sosai amma saboda shukr saiya dad'e akai.
Da in musty y kira tana d'auka suyi hira amma yanzu Sam bata damu ba koya kirama basarwa take taci gaba da abinda take.
Domin acewarta bai iya soyayya ba.
.
Adaide wan nan lokacin ne kuma Addmition ya fito ta samu kuma murna gunta ba bakin fad'a inda ta samu Northwest university ranar litinin sukaje sukai Rigitration sati biyu tai tana harkar Makarantar har tana gama.
.
@7:00
suna tsaye da safe Baba zai fita Mama na tsaye ya kira shukra ta tsugunna "gani baba."
Yawwa "Ranar monday zaku fara Lucture saiki Kula banda shirmen k'awaye da shashanci kiyi abinda ya kaiki wan nan shine buri na"
.
Mama tace ni Wlh da zama abi ta tawa dama Aure kaiwa yarinyarr nan se taje can tayi kaga rawarkai gareta Wlh Sam da aurenta zaifi" baba yace "ki Mata addua kawai Aure ai lokaci ne kuma kinga Mustaph baya nan" Mama tace hakane kuma" baaba yace "ni na tafi" sukai mai adawo lafiya.
.
Mama ta kalleta "Wlh shukra muddin baki maida hankali ba saina sab'ar miki kodan yanda mahaifinki ya jajirce kan karatunki to kema ki dage , kuma banda kule kulen samari da kawayen banza don na sanki shukra" turo baki tayi "kai mama ni Meye ruwana dasu abinda ya kaini shi zanyi"
"Atoh kima daiyi."
.
Ranar Litinin da safe k'arfe 8 shukra ta fece kamar zata gidan biki nan ma mama saida kumai Mata kashedi ta kula kamar ta tabud'e Ido ta ganta acan haka ta keji .shigarta school taga 'yan mata da samari kowa na harkar gabansa wasu na zaune suna hira wasu kuma lokacin suke zuwa dayawa wasu basu San fuculty nasu ba wanda itama shukran na d'aya daga ciki haka taita yawo tsayuwa tayi dai de kusa da wani book Shop wasu 'yan Mata sukazo wucewa tace don Allah intambayeku? d'aya ta waigo "Allah yasa munsani" shukra tace fuculty of mass communication nake nema" d'ayar tace "oh da alama ke sabuwa ce ko?" tace "eh."
Murmushi tayi "ai duk new comer sai sun samu hakan, biyomu akwai sis namu course naku daya itama sabuwa ce" Dad'i shukr taji "ngd sosai" nan suka fito shukr tabisu abaya......
0 comments:
Post a Comment