DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI✍🏼
SHIMFID'A
NIAMEY
Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne
birni mafi girma a kasar, dake da girman murabba'in kilo mita (239.30) Tun a
karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba'a dauke shi da
wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a
shekarun (1890). A shekarar (1926) ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu
a hankali yawan jama'ar yankin ya yi ta karuwa daga (3,000) a shekarar (1930)
zuwa kimanin (30,000) a shekarar (1960). Yawan jama'ar Niamey ya kai (250,000)
a (1980), a shekara ta (2000) kuma (800,000). Babban musabbabin karuwar jama'a
a Niamey shi ne na yawan kaurar jama'a a lokutan fari.
A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai
wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma
cibiyoyin nuna al'adun gargajiya na Amurka da Faransa da Nijar. Hakanan kuma
akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin. Kashi (90)cikin dari na jama'ar Niamey
Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika.
SA'AYRASA
MASARAUTAR SA'AYRASA yana bangaren kudu maso gabashin Nijar,
kuma yana da girman murabba'in kilo mita (156,906). Masarautar Sa'ayrasa na
iyaka da Masarautar Fabarusa, ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta
kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi. Masarautar Sa'ayrasa ta kasance d'aya daga
cikin masarautar da ba su da yawan jama'a, wanda kidayar shekara ta (2001), ta
nuna yawan mutanen masarautar ya kusa dubu dari hudu. Jama'ar Masarautar
Sa'ayrasa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa. Tattalin
arzikin masarautar ya ta'allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina.
Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da
kayan lambu irin timatir da barkono. Sai dai kuma duk da noman da ake yi a
masarautar, masarautar ta kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda
fari.
FABARUSA
MASARAUTAR FABARUSA shi ne ya fi kowanne yanki girma a
masarautar Nijar, wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita (634,209), watau
kwatankwacin kashi hamsin da biyu cikin dari na girman Nijar baki daya.
Masarautar Fabarusa ta had'a da Hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai
cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar Masarautar buzaye ne; akwai kuma Tubawa
da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana'ar jamaar masarautar ta asali itace
cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun (1990), harkar bude ido ta zama
wata babbar sana'ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na
samawa Nijar kashi (20)cikin dari na kudin shigar da take samu.
NIAMEY 1/01/2000
Tafe su ke cikin mota,tin da suka baro masarautar su wato
Sa'ayara ta tsunduma cikin kogin tunani, ba ta gushe ba har su ka shigo Niamey,
in da makarantar su wato SOVEREING GIRLS SECONDRY SCHOOL ta ke. Wato ‘ya’yan manya da sarakuna na sassa,masarauta
da yankunan jamhuriyyar Nijar waannan makarantar su ke. Ajiyar zuci ta saki
ganin sun doshi kofar makarantar, yayin da motoci biyu da ke gaban ta su su
faka, ta su wacce ta ke ta uku ita ma ta faka. Waigawa ta yi dan ganin ko
d'ayar da ke tafe bayan ta su ta sami isowa,ile kuwa sai gasu sun karaso a
hankali su ka faka bayan ta su. Hankalin ta ta mayar kan kofar makarantar ta
su. Motoci huɗu ne jere reres su ka taho kawo Gimbya Binta yar sarkin Sa'ayrasa
makaranta. Ta fari ɗauke da dogarawa guda biyu da direba, ta biyu bayi ne mata
su huɗu, sai kuma wacce Gimbiyar 'yar sarki mai dole ke zaune gidan baya, ta yi
ɗai-ɗai ta na shan kamshi, tare da ita baiwar ta ce Bintu zaune gaban mota da
kuma direba,sai cikon na hud’un dogarawa ne su huɗu zaune, biyu gaba biyu baya.
Tsawar da ta ji an
daka mata ya sa ta yi firgit ta dawo cikin hayyacin ta, jin an furta,
‘’idan kin gama
rubuta wasikar jakin da ki ka saba sai ki fita’’.
Faɗin _(driver)_
matu'kin mota ya na mai muzurai. Hakan ya sa ta saurin fitowa daga motar dan
kuwa har sun shigo farfajiyar makarantar ba ta sani ba. Tini sauran bayi yan
uwanta sun yi sahu suna jiran fitowar Gimbiya Binta. Cikin su Bintu ta shige ta
tsaya kan na ta sahun, yayin da dogarai su ka karaso cikin azama, su ka yi na su
sahun ta ɗayan ɓangaran. Daga bayin har dogarawa kalar yadin da ke sanye jikin
su ɗaya, ruwan toka ne da shuɗi. Rigar ruwan toka sai zanin shuɗi.
Kan su sunkuye babu mai motsi kai kace gumaka aka aje,
matu'kin ya buɗewa Gimbiya Binta kofa. K’afafun ta fara fiddowa waje, sanye
cikin takalmi fata mai dankaran tsada, sai bayan wasu yan dik’ik’a sannan ta
k’arasa fitowa. Tuni suka fara ma ta kirari da faɗin,
‘’taka a hankali
Gimbiya yar sarki mai dole, takawan ki lafiya sarauniyar mata’’.
Sanye ta ke cikin kayan makaranta, riga da _skert_ buje sai
kuma hijabi wanda ke tsayawa iyaka kafaɗa. Alkyabba ce ta alfarma ɗaure bisa
kayan makarantar. Cikin sarauta da tak’ama ta ke takawa ɗaya bayan ɗaya ta
wuce, su ka rufa mata baya. Haka su ka wuce ciki zuciyar Bintu cike da tunanin
halin da akwatin karfen ta zai shiga matukar ba ta dawo da wuri ba dan Ado
matu'ki ba mutunci gare shi ba, dan ya
koma da kayan Kuka Sheka ba k’aramin aikin sa ba ne. Hantar cikin ta tuni ta kaɗa
Motoci sai shiga da
fice su ke kasancewar yau rana ce ta dawowar ɗalibai daga hutun zango na uku.
Kai tsaye sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka nufa, wanda a k’a'ida kowanne ɗaki
dan d’alibai biyu aka yi. A dai-dai katangar da ta raba harabar makaranta da
sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka tsaya, dan kuwa babu damar dogarai su shiga ɗakin
kwanan kasacencewar dokar makaranta ta hana maza shiga. Nan su ke jiran
dogarawa masu ɗauke da akwatina su k’araso su
karb’i akwatunan dan karasawa da su ciki. Ita kuwa Gimbiya Binta kai
tsaye ta shige,biyu daga cikin bayim biye da ita, ya rage daga Bintu sai bayi
guda biyu. Dan sauri jikin ta har ɓari yake, Allah-Allah ta ke su samu su
shigar da kayan Gimbiya Binta dan ta samu damar kwaso na ta. Sai da su ka ɗauki
kusan minti goma kafin su k’araso ɗauke da kaya niki-niki, wanda kuwa faɗar
adadadin su aiki ne ja, wai kuma a hakan ma akwai saura cikin mota. Haka suka
shiga jidar kayan su na hawa da su sama,bhar bene na uku tukanna ka isa ɗakin
Gimbiya. Ta nan kishingiɗe kan gado, ɗakin yayi fes-fes dama tin ana sauran
kwana uku a dawo makaranta a ke gyarawa.
Su na hawa su na sauka har sai da su ka yi sahu uku. Bintu
na Murna da sun sake komawa za su kwashe sauran kayan. Budan bakin Gimbiya
Binta sai cewa ta yi,
'’akwati nawa ne su ka rage?’’.
’Daya daga cikin
bayin ta amsa mata da,
"huɗu ne su ka yi saura ranki shi daɗe'’.
Gimbiya ta ce,
"to! Za ku iya tafiya kubarwa ɗiyar bayi sauran ta
k’arasa hawa da kayan’’.
Tuni idanun Bintu ya
raina fata, ba wai wuyar hawa da kayan ba ne damuwan ta ba, a'a ita ta dan akwaitin k’arfe ta ta ke. Cikin
girmamawa su ka durkusa su na mai faɗin,
"an gama ran ki shi daɗe'’,
hannu kawai ta ɗan ɗaga musu alamar sa iya tafiya. Cikin
hanzari su ka daɗa rusunawa kafin su tashi su ka fice. Ai fa Bintu ba ta san
san da ta arta a na kare ba, ta na ji sauran bayin suna dariya suna cewa:-
‘’Ba ke mai yiwa
Gimbiya hidima a boko ba, Allah shi k’ara’’,
ɗaya ta k’ara da "ai tin da aka zab’e ta wani girman
kai ya game jikin ta, ɗiyar bayi a makarantar girma’’.
Yi ta yi kamar ba ta ji su ba, ta k’arasa ta ɗauro akwati ɗaya a ka d’aya kuma ta jawo shi a hannu. Ba ta
kai ga hawa bene ba ta yi kaciɓus da su, haka su ka wuce ta suna mata dariyar
kyeta. Cikin himma ta haye abun ta sama, sai da ta kai ga kofar ɗakin ta tsaya
dan ta ɗan sami nutsuwa dan kuwa idan Gimbiya ta gano ta lalle kashin ta ya
bushe. A hankali ta tura kofar tare da sallama. Gimbiya ko ta nuna ta san ta
shigo bare ma ta amsa sallamar. Cike da nutsuwa ta aje akwatinan sannan ta
fito, nan ta sake zurawa a guje, ta kwaso sauran akwatinan kamar dai yanda ta
yiwa biyun farko. Aje akwatinan ke da wuya ta juya da niyyar sake fita, Gimbiya
ta daka mata tsawa,
"ina zaki? Nufin
ki ni zan jera mi ki kayan yau kuma ɗiyar bayi?’’.
Jiki na rawa Bintu ta
zube k’asa ta na mai faɗin,
"tuba na ke
ranki ya daɗe ni ce zan jera dama sauri na ke dan kwaso nawa kayan kar Ado ya
manta ya juya da su’’.
Shiru idan Gimbiya
Binta ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka. Da shirun yayi yawa Bintu ta ɗaga
kai ta kai kallon ta gare ta, sai gani ma ta yi ta runtse ido kamar mai bacci.
Dole jiki ba laka Bintu ta tashi ta shiga jera akwatunan, sai da ta gama
tsaf sannan ta durk’usa ta ce,
‘’ran Gimbiya ya daɗe na idda’’.
Sai da wasu dak’ikai su ka shuɗe, har Bintu ta na tunanin ko
dai bacci ta ke sannan ta ji ta ce,
‘’kya iya kwaso tsummokaran na ki’’.
A wulakance ta yi furucin cike da 'kas'kanci. Russunawa ta yi cike da girmamawa ta ce,
‘’godiya na ke ran ki shi daɗe", ta tashi ta fice. Nan
fa duk nutsuwar ta ya gushe, ta ranta a na kare, ba ta ji ba ta ba ta gani.
Dalibai ma su shiga da fice cikin farfajiyar wajan faɗi su ke,
"ta fara, in dai wannan ce dama duk dawowa hutu haka ta
ke".
A guje ta fito daga harabar ɗakin kwana ta shigo sashen
ajijjuwa. Ba ta ga tahowar shi ba sai ji ta yi karo da shi. Ta yi saurin yin
baya saura k’iris ta faɗi ya yi saurin sa hannu biyu ya rik’o ta. Sakin baki ta
yi ta na kallan sa,ta ma manta da gudun da ta ke.
Sanye ya ke cikin bakar _suite_, wankan tarwaɗa be mai dan
faffaɗar kafaɗa. Ya na da dogon hanci, yayin da gashin bakin sa da ya zagaye
bakin na sa ya k’ara masa kyau da k’warjini. Idanun sa rufe cikin bakin gilashi
hakan ya sa ba ta sami damar ganin kwayen idanun na sa ba. Kamar daga sama
muryar sa ya dakin dodon kunnan ta,jin ya ce
‘’hankali mana gudun
me ki ke haka ke kuwa?’’.
Ta yi saurin ja da baya,hakan ya sa shi sakin ta.
’’Yi hakuri dan Allah Ado direba zai tafi da kaya na’’.
Bintu ta furta idanun ta na shirin kawo ruwa. Sai a sannan
ya dubi kayan jikin ta ya na mai faɗin,
‘’Tabbas wannan
shigar ta ki ta bayin Masarautar Sa'ayrasa ne, ina shigowa na ga motocin na su
na fita, sun manta da ke ne...?’’,
ba ta bari ya karasa maganar ba bare ta bashi amsa ta sa
gudu ta na mai faɗin,
"shikenan ni Bintu sun tafi da akwati na,shikenan na
banu na shiga uku na lalace’’
Cikin rashin fahimta ya bita da kallo har sai da ta kure
masa sannan ya d’aga kafad’a ya sauke sannan ya yi ciki abun sa.Isar ta wajan
yawan motoci masu kai kawo ya k’aru,sai dai babu motocin Sa'ayrasa babu alamar
su. Kwallar da ke idanun ta tuni su ka fara gangarowa bisa kuncin ta.
Bintu na shirin juyawa ta hangi akwatin ta jefe tsakiyar
filin, da gudun ta ta k’arasa ta rungumo abin ta ta na maida numfashi. Wani mai
mota ne ya ba a mata k’ura sa’annan ya
lek’o ya na fa in
"shashasha sai kin jawo wani ya taka ki’’
ko aga kai bata yi ba bare ma ta san ya na yi. Ita dai burin
ta ya cika ta sami akwatin ta.
Offishin shugaban makarantar katan ofishine wande aka kawata
shi kai ka ce ofishin shugaban wani yankin ne. Ganin wanda ke zaune gaban sa da
kuma abun da ke tafe da shi ya sa shi zufa na ba gaira ba dalili rufe shugaban
makarantar. Kana ya nisa tare da fa in
"(your excenllency) Ya mai girma....’’
"Aisar,ko ka kira ni Aisar Gaddafi Nur,(his excenllely)
ya na gida yallabai’’
ya katse shi hankali kwance. Zufa shugaban makarantar wanda
dalibai ke kira Malam Hamisu ya goge,ya na mai gyara murya ya ce
"toh Yallbai,yanzu dai nufin za ka yi bad da kama kamar
malami cikin wannan makaranta ta mu har tsawan zango aya.....’’
Yana mai murmushi ya ce
‘’ba bad da kama ba Yallabai,gyaran lafazin shi ne ina neman
alfarmar koyarwa a makaranta na tsawan zango aya’’
cikin nazari Mallam Hamisu ya ke duban sa "me zai sa
dan Shugaban kasa so ya koyar a makarantar nan?na zango aya? Ko shakka babu ya
na daga cikin motanen oye wanda ke yiwa kasa bincike da aiki cikin surru, dama
ba tun yau ya ke jin maganar ba,kaddai wani sharrin aka kullawa makarantar
sa.....’’
Zancen zucin da ya ke yi cikin ran sa kenan dan kuwa ruwa ba
ya tsami banza. Can dai ya gyara murya sannan ya ce
‘’Yallabai....’’
‘’Aisar’’
Saurayin ne ya k’ara
katse shi ya k’ara da
"tunda zan zauna k’ark’ashin ka ya kamata ka saba da
kira na da sunana.’’
Cikin jinjina kai Malam Hamisu ya amsa da
"Haka ne Aisar,muna maraba da kai,kuma ina mai tabbatar
ma ka mu yan kasa ne masu kishin kasan mu,na gari ma su san ci gaban kasar
mu.’’
Ya na mai murmushin nuna gamsuwa Aisar ya tashi tsaye gami
da mik’a ma Malam Hamisu hannu ya ce
"madallah da kai,kuma na gode kwarai,gobe InshaAllahu
zan fara koyarwa sai a bani aji a kuma zaga da ni makarantar sauran Malamai su
sanni ko koyar da ni sharad’an makaranta idan akwai, duk abun da ka ke buk’ata
in koyar shi zan koyar’’
Mallam Hamisu shi ma in tashi yayi,ya na murmushin yake ya
amshi hannun Aisar,fa i ya ke
"Madallah Allah ya nuna mana’’
amma a zahirin gaskiya a tsorace ya ke da Aisar.
Sai da ya raka shi har kofa ya tabbatar ya tafi sannan ya
dawo ofishin sa da sauri dan ha a taron zaman Malamai na gaggawa dan kuwa shi
gani ya ke akwai matsala shi ya sa aka mu su shunan Aisar. Shi kuwa Aisar ya na
fita shugaban su ya kira ya na mai sheda ma sa
yanda su ka yi da Malam Hamisu,Shugaban na su yayi murna kwarai dan kuwa
kamfanin da su ke bincike akai kusa da makarantar ne. Ko da ya aje wayar sai ya
tsinci kan sa ya na mai waige waige ko zai sake ganin wannan baiwar,amma yawan
daliban da ke kai kawo,da wanda su ka sa masa ido ya sa shi kasa gane wacece
wace
"ba mamaki ma ta sami motar garin na su"
abun da ya fa a kenan kafin ya shige motar shi da ya saba
basaja da ita ya bar harabar makarantar.
Wacece Bintu
Bintu Bala Mahuta sunan ta,amma Bintu iyar bayi ake kiranta
a masarautar su kasancewa suna aya ta ci da da Gimbiya Binta, wato sunan
maihaifiyar ta wacce Allah yayiwa rasuwa wajan haihuwar Gimbiya Binta.
Mahaifiyar Bintu wacce ta ke babbar baiwar matar sarki wacce ake kira da uwar
bayi,ta haifi Bintu yau,washegari aka haifi Gimbiya Binta kuma mahaifiyar Binta
ta ce ga garin ku. Kun ga kenan sunan su aya,banbancin ranar haihuwar su kwana
aya,dan haka shekarun su ma aya.
Shekarar Bintu goma sha biyar da haihu,mahaifin ta babban
bawan wazirin Sa’ayrasa ne,kasancewar haka tare da alfarmar mahaifiyar ta da
take babbar baiwar matar sarki mai rasuwa ya sa da za a kai Gimbiya Binta
makarantar kwana aka zab’e ta cikin bayi domin kula da ita,dan ko a cikin
‘ya’yan bayi babu wanda ya san fada da al’adun ciki kamar Bintu. Ta wannan
hanya aka rab’uka ta cikin makarantar su Gimbiya Binta musammam dan hidimar ta.
Amma fa a wahalce ta ke samin ilimi,kai ba ma ilimi ba komai na Bintu cike ya
ke da wahala. Wanka ne kawai ba ta yiwa Gimbiya Binta,amma komai na ta ita ce.
Wanki da guga da a k’aidar makarantar akwai mai yi musu amma ita Gimbiya Binta
sam ba ta yarda sai dai Bintu ta mata,hatta jakar makarantar ta ma Bintu ke
gyarawa ta aukar mata. Idan jinga aka ba su sai dai ta yi na ta ta kuma yi na
Gimbiya Binta, sai dai idan malamin da ya san rubutun su ne shi ne sai ta jira
idan Bintu ta gama ta kwafa. Rubutu kuwa idan an mu su a allo sai dai ta kwafi
na Gimbiya Binta,idan sun dawo aki ta kwafi na ta.
Batun wajan kwana kuwa aki aya su ke,duk da gadaje biyu ne a
akin ba ta isa ta kwanta a gado Gimbiya Binta na gado ba, ah ah sai dai ta sami
yar tabarma ta rab’ike daga can gefe a k’asa. Tun masu kula da akin kwanan
na magana har sun hakura sun yi shiru
dan sun ga tsakanin baiwa da uwar gijiyar ta sai Allah. Bintu ba ta isa ta riga
ta bacci ba,kuma dole ta riga ta tashi ta ha a mata ruwan wanka. Wajan cin abunci
ba ta isa ta zauna cikin yan uwan ta alibai ta ci abunci ba,sai dai ta jira
Gimbiya ta gama,ta raka ta aki ko aji sannan ta dawo ta ci na ta. Kuma a duk in da su ke sai ta tabbatar kowa
ya san Bintu iyar bayi ce, shi ya sa ma ta hana ta sa kaya in dai ba shigar
bayin Sa’ayyarasa ba idan ranar sa kayan su na gida yayi.
Allah ya yiwa Bintu wani abu wai shi tsayi da diri,dan kuwa
jikin ta ya girmi shekarun ta. A shekarun ta tana da zubin cikakkiyar budurwa
idan ba fuskar ta aka kalla ba ba wanda ba ya b'oye shekarun na ta.
Bintu baka ce,irn bakin nan na wayayyun matan nan da ba sa
shafa man da zai sake mu su kala. Doguwar fuska gare ta,amma ba mai tsayi sosai
ba,ta na da manyan idanu ga hanci har baka,sai wushirya da ke mata kyau duk
sanda ta dara ko ta bu e hakora. Ta na da suma matuka,ko ta aure kan ta da
kallabi yawan sumar be b’oyuwa.
Daga ita har Gimbiya Binta aji uku suke. Ba ta da buri da ya
wuce su kai aji shi da su gama makarantar ko ta huta da jarabar Gimbiya,dan
kuwa ko k’awaye Bintu ba da shi a makarantar.
Aisar Gaddafi Nur
Aisar saurayi ne mai kimanin shekara talatin a duniya. Aisar
ya da e cikin aikin sa da ya ke matuk’ar so tun kan mahaifin sa ya zama
shugaban kasan jamhuriyyar Nijar. Aiki ne wanda ake mu su lakani da mutan
b’oye,wato masu bincike da kula da kasa amma ta k’ark’ashin k’asa. Tin hawan
mahaifin sa kujerar shugaban k’asa ya na ji ya na gani dole aka dakatar shi
saboda yanayin aikin na su na sirri ne hatta sunan da ya ke amfani da shi cikin
aikin da ban ya ke da sunan sa na yanka,ba zai yiyu a ha a da siyasa ba dan ba
mamaki ma wata rana aiki ya bi ta kan gidan na su. Amma shi ba haka ya so ba.
Hakan ya sa sam Aisar ba ya san shiga sabgar gidan gwamnati ko abun da ya shafi
harkar siyasar baban shi. Ko zama gidan shugaban k’asan ma be cika yi ba,in ka
gan shi ciki toh wajan iyayen sa ya je gaidawa ya tafi,in da Allah ya taimaka
ba shi ka ai ba ne ya na da yayye ba laifi, dan ba kowa ba ne ma ya san shi a
matsayin an shugaban kasa. Hakan be sa kungiyar Aisar janye dakatar da shi da
su ka yi ba,har ma ya fidda rai ya hakura har sai baban shi ya sauka kwatsam ya
ji kiran aiki na wani bincike da ya bi ta kan wani kamfani da ke kusa da
makarantar su Bintu. Yayi murna kwarai duk da kuwa aikin ba nasa ba ne,shi
kawai taimako zai yi shi ya sa sai dai ya rab’uke daga gefe har sai lokacin
taimakon yayi. Kungiyar ta su ce ta ba shi izinin neman koyarwa a nan
makarantar ta sovereign girls secondry school,su ka kuma ce ya je da sunan sa
na ainihi tun da hawan baban sa mulki an fara ya awa cewa ya na
kungiyar,kasancewar shi cikin makarantar shi zai ba su damar yin basaja,yanda
wancan kamfanin ba za su yi zargin su ake bi ba har su gama binciken su.
2/01/2000
Zaune su ke cikin aji. Kamar yanda ta saba kujerar ta na
bayan na Gimbiya Binta. Ta doka uban tagumi in ban da k'ugin yunwa babu abun da
cikin ta ya ke dan kuwa raban ta da abunci tin na dare da ke yau sun makara,
hakan be sa Gimbiya ta aga mata k’afa ba ta bari ta ci abunci lokacin da ta ke
cin abunci,kafin ta gama kuma aka shiga aji. Ta na ji ta na gani sai hakura ta
yi.
Duka duka ba su kai talatin ba cikin ajin amma gaba aya sun
ciki ajin da surutu. Hirar abubuwa masu tsada da k’asashen da su ka tab’a zuwa
kowa ya ke. Ita kuwa Bintu da hirar ta su ko hankali ba ya bata sai hamma ta
ke,ta kalli agogon bangon ajin,awa aya ya rage a fita gajeran hutu dan cin
abunci. Malamin da ya kamata ya shigo kuma ya ki shigowa, sai kawai ta kifa kan
ta bisa teburi.
Shirun da ta ji anyi ya tabbatar mata da Malam ya shigo aji.
Ta yi sauri ta ago kan ta sai gashi kowa ya tashi tsaye ita ka ai ce zaune,baki
bu e ganin wanda ya ke tsaye gaban ajin. Kamar yanda ta gan shi jiya yau ma
bak’ak’en kaya ne sanye jikin sa,idanun sa rufe da bakin glass. Da kyar ta sa
mu ta ja jikin ta ta tashi.
Gaishe su yayi cikin harshen turanci nan da nan su ma su gaishe
shi. Ya umarce su da su zauna. Da zaman su da jin wani abu ya sauko mata lokaci
guda ne,ta yi kasake ta na tunanin wannan wani irin saban lamari ne? Can dai ta
yi tunanin dan wannan abun da ya saba zubo mata lokaci lokaci ne.
Malam ya gabatar da kan sa a matsayin saban malamin su na
fannin zaman lafiya da sulhu [peace and conflict resolution" ta re da fa a
ma su sunan sa wato Aisar Gaddafi Nur. Ko da jin sunan aji aka fara kus kus,
daga fa in
"Gaddafi Nur shugaban kasa?’’
sai mai fa in
"haba da ma ni na ga yayi min kama da wanda na
sani,ashe dan shugaban kasa ne’’
wata kuma
"toh me zai yi da koyarwa kuma?ba mamaki su nan ne ya
zo aya dan kuwa an shugaban kasa ya fi karfin koyarwa’’
Ita dai Bintu ta saki baki ta na kallan sa,shi ko lura da
ita be yi ba. Gashi ta na fama da wani saban lamari da ke zubo mata har ta na
ji ta an fara jikewa. Tun ta na gane abun da ya ke fa a har ta zo ta dena dan
kuwa ta fita hayyacin ta. Har fitar sa be lura da ita ba,ita kuwa gaba aya
hankalin ta a tashe ya ke ganin abun da ya b’ata ba kayan makarantar ta ba
hatta in da ta ke zaune.
Aisar na fita jiniya ta yi k’ara,lokacin fita hutun karamin
lokaci yayi,dalibai su ka fara fita domin cin abunci da sauran su. Amma tashi
ya gagari Bintu. Jaka Gimbiya Binta ta cilla mata yanda ta saba,wato ta auka ta
biyo bayan ta. Murya na rawa Bintu ta furta
"dan darajar Allah Gimbiya ki yi min rai ki gafarce
ni,na tuba’’
cike da mamaki ta juyo ta na duba ta,yan aji tuni kowa ya
watse daga ita sai kawayen ta biyu masu masifar girman kai,Ruqayya da Zahira.
Zahirar ce ta ce
"kun ga shashashar banza,me ki ka yi da za ki hau
magiya kamar iyar marok’a?’’
Ruqayya ta amsa da
"to menene banbamcin iyar bayi da ta marok’a?’’
Cike da nuna b’acin rai Gimbiya Binta ta ce ‘’jakar tawa ce
ba za ki sami damar auka ba ko kuwa tashin ne ya gagare ki?’’
Bintu na kuka ta ce
"Allah shi taimake ki,wani abu ne kamar jini ya zubo
min.......’’
‘’JINI!’’
Ruqayya da Zahira su ka ha a baki yayin da su ka ja gefe
cikin nuna kyamkya mi. A wulakance Gimbiya ta ce
"duk sanda jinin ya dena zubo mi ki kya tashi,dan Allah
ku zo mu tafi ko na dai na ganin wannan k’azantar’’
Zahira ce ta auki jakar na ta su ka tafi su ka barni. Tini
duk wata yunwa ta dena jin ta,ta aura kan ta bisa taburi ta na hawaye,ta rasa
in da za ta sa kan ta.
Ba ta jima a haka ba ta ji wani sanyayyen kamshi ya bakonci
hancin ta,a hankali ta ago. Hannun sa ruk'e da bakin gilashin sa,fuskar sa auke
da alamar tambaya, ya ce
‘’wannan fuskar ina na san ta ne?’’
Bintu ta yi saurin kau da kai gefe ta na mai adduar Allah
kar ya tuna. Ai kuwa dai adduar ta ba ta karb’u ba jin ya ce
"Sa’ayyarsa,tabbas. Dama ke daliba ce a makarantar
nan?me ya same ki ki ke kuka?ko dama ke kullum cikin tashin hankali ki ke? na
wucewa na hango ki kai kife kan tebur bayan yan uwan ki dalibai suna can suna
cin abunci’’
maimakon ta bashi amsa sai ta yi ka sake ta na kallan sa
yayinda hawaye ke zuba daga idanun ta. Ya ce
"ba da ke magana ba?ba kya ji ne?’’ rasa abun da za ta
ce masa ta yi sai hawaye kawai. Nan fa ya k’ule be sanda ya daka mata tsawa ba
ya na mai fa in
"tashi tsaye na ce!’’
Ba ta san sanda ta tashi tsaye a gigice ba,nan idanun sa ya
sauka bisa kujerar da ta ke zaune,sannan ya dawo da kallan sa ga kayan
makarantar ta da ya b’aci.
Tausayin ta ne ya lullu6e shi,dan daga ganin yanayin ta ka
san fararriya ce.
‘’zauna ina ki jira ina zuwa’’
Ya fad'a a sanyaye,kafin ya juya ya fita ba tare da ya jira
ta amsa masa ba,dama ko ya jira in ma ba amsawa za ta yi ba. Cike da da kunya
da takaicin yanayin da ya gan ta, ta koma ta zauna, gaba d’aya ji ta yi ta
tsani kan ta,kan ta ta kifa bisa teburi. Jim ka d’an ta ji muryar d’aya daga
cikin masu kula da d’akin kwanan dalibai,wacce su ke kira iya Dije,ta na fad’in
‘’wacece ne? d’ago kan ki na gan ki’’
Bintu ta d’ago kan ta a hankali ta dube ta. Ganin fuskar
Bintu ga idanun nan na ta ya yi jajur dan kuka Iya Dije ta ce
‘’aw Bintu da ke ce?yo menene na kukan har haka? Ai girma ne
ya zo,maza ungo wannan zanin ki d'aura mu je ki gyara kan ki’’
Ta mik’a mata zani,hannun Bintu na rawa ta kar6a da saurin
ta. Ta tashi a hankali ta d’aura zanin ta na mai bin kujerer da ta 6’ata da
kallo.
‘’kar ki wani damu da wannan, Shatu na nan tafe za ta
gyara,ke dai mu je ki fara gyarawa tukun’’
Fad’in Iya Mairo yayinda ta d’auki jakar Bintu ta wuce
gaba,Bintu na biye da ita. D’akin kwanan d’alibai su ka wuce, d’akin su Bintu
ta zauna ta yi jiran ta bayan ta koya mata yanda za ta yi ta gyara kan ta. Sai
da ta yi wanka ta shirya sannan ta wanke kayana da zanin da Iya Dije ta bata.
Bayan ta gama ne ta je ta sami Iye Dije zaune ta na jiran
ta. Kamar wacce ta yi laifi ta d’an ra6e daga gefe,kan ta sunkuye ta ce
‘’Iya Dije na gode da kulawar ki,wallahi ba da sani na ba
ne,ban ta6’a ganin irin haka ba’’
Murmushi Iya dije ta yi jin maganar Bintu,kana ta dafa
kafad’ar ta tana mai fa’d’in
‘’Yaro dai Yaro ne,dama kowa akwai ranar da ya ke
farawa,kuma kowace cikakkiyar budurwa ta na yi,auta ta ma ba ta dad’e da farawa
ba’’
Da sauri Bintu ta d’ago kan ta ta ce "Allah? ita ma ta
yi kuka?’’
‘’ah ah’’
Iya Dije ta amsa mata,sannan ta k'ara da
‘’da ke ta tashi cikin mata kuma ta na zuwa islamiya toh ta
san komai,kawai dai ta shiga damuwa na rashin sabo,da fatan ki na dai zuwa
islamiya a masarautar ku’’
Bintu na mai girgiza kai ta ce
‘’ah ah makarantar allo na ke zuwa,shi ma kuma sai idan babu
aiki sosai a fada,da aka sani wannan makarantar ma sai na dena zuwa gaba
d’aya’’
Iya Dije ta ce
"assha ai makarantar islama na da muhimmanci ga rayuwar
d’iya mace, kin ga da kina zuwa da yanzu kin san duka hukunce hukunce da ya hau kan ki, lalle
idan an yi huta ki ce da gyatumar ki ta sanya ki cikin islamiya, ba a tsufa da
neman ilimi bare ke da kuruciyar ki kin ji ko?’’
Bintu ta gyad’a kai. Kana Iya Dije ta kara da
‘’yanzu hukunci babba ya hau kan ki tunda kin balaga, yanda
za a rubuta wa mahaifiyar ki ko ni kai
na hukunci haka ke ma za a rubuta mi ki dan kuwa yanzu mu da ke duk d’aya ne
har ga Allah, kin tashi daga yarinya. Dan haka ki kula ki kyau ta ta rayuwar ki
ta duniya da lahira, ki ruk’e mutunci ki da na iyayen ki. Ba ruwan ki da maza
muddin ba da kwakkwaran dalili ba,kin dai san mai wasa da maza karya ce ko?’’
Kai sunkuye Bintu ta jinjina kai alamar ‘’eh’’ Iya Dije ba
ta gushe ba ta k’ara da
‘’yauwa, wannan sabon Malamin da ya zo yayi kira akan ki,
menene dangantakar ku?’’
Nan fa Bintu ta fara kame kame, ta ce
"iye? na’am? Wai wannan d’in nan? wallahi ni ma ban san
shi ba Iya Dije,yau ya fara koyar da mu fa"
Cikin nazari Iya Dije ta kura mata ido kafin daga bisani ta
nisa ta ce
‘’kar ki saki jiki da kowane d’a namiji muddin ba muharramin
ki ba ne, wato wadda babu auratayya tsakanin ku, kar ki sakarwa kowa fuska ko
hannu kar ki yarda wani ya ta6’a ruk'e mi ki idan ba haka ba mutuwa za ki
yi,kin ji ko?’’
A tsorace dan ta ji batun mutuwa ta amsa da
‘’Toh, wallahi dama ni ba ruwa na da maza, ko a masarautar
mu ma ba na sakar mu su fuska, yaya Ubaliya ma sheda ta ne’’
Kai Iya Dije ta jinjina alamar gamsuwa. Nan ta cigaba da
bawa Bintu shawarwari. Ko da ta zo tafiya har ta kai ga k’ofa ta ce
‘’Bintu ya batun turare ina fatan dai ki na da shi, dan
yanayin da ki ke ciki sai fa da turaren’’
Bintu na d’an soshe soshe ta ce "Iye?dama dai Inna ta
ta bani garin alimun ta ce ina had’awa da leman tsamin sai na ke gogawa a
hammata ta’’
‘’eh toh wannan ma ba laifi,amma ki na bukatar turare,dama
wannan Malamin ya ce na fad’a masa idan ki na da bukatar wani abu,na fad’a
masa. Kuma kar ki manta ki na canza wannan audugar da na baki a kankari, ban da
k’azanta dan Allah idan ba haka ba kuwa za ki ji ki kina wari na gaske’’
Cike da jin kunya su ka yi sallama, Bintu ta mata godiya
sosai. Bayan fitar ta ne ta ji yunwar da take ji ya dawo ma ta, saboda haka sai
ta bu6e akwatin k’arfen ta,ta fito da ajiyar garin kwakin ta da kuli ta sha ta
k’oshi. Ta na gamawa da saurin ta ta gyara wajan dan kar Gimbiya Binta ta gani
ta zubar mata da ragowar. Ko da ta ga ta sami nutsuwa,ta shifid’a tabarmar ta,
ta yi kwanciyar ta kafin lokaci ya cika ta koma aji. Gaba d’aya kunyar Malamin
nan ne ke damun ta musammam yanzu da Iya Dije ta fed’e mata daga bindi har
wutsiya na game da sabon rayuwar da ta shiga,ga shi shi dai kullum ba ya sa’ar
ganin ta cikin hayyacin ta. Da wannan tunanin bacci mai dad’in gaske yayi gaba
da ita.
Saukar marin da ta ji ya sa ta yi firgit ta tashi zaune
hannun ta bisa kuncin ta ta na mai murzawa. Ba ta bari ta gama wastsakewa ba ta
rufe ta da zagi, fad’i ta ke
‘’dan uban ki wannan bawan har ki zo ki kwanta ki na barcin
asara kin manta bauta ya kawo ki makarantar nan? k’azama wawuya!’’
Da sauri Bintu ta d’urk’usa jika na b'ari ta ce
‘’Allah ya huci zuciyar gimbiya, tuba na ke, ban san sa’in
da baccin ya sace ni ba, ki min aikin gafara’’
A wulak'ance Gimbiya Binta ke duban Bintu,kafin ta furta
‘’ga wanki can na su diras d’ina,bayan kin gama ki min guga.
Kuma ki sani yau bazan iya kwana d’aki d’aya da ke ba cikin wannan k’azantar da
ki ke. ki d’au k’azamar tabarmar ki ki aje daga can lungun,kuma ki san abun da
za ki ce da su Iya Dije su ka gan ki a nan kwance dan idan ki ka kuskura ki ka
kira sunana wallahi sai na lahira ya fi ki jin dad’i’’
Cike da ladabi Bintu ta duk’a ta na mai fad’in
‘’Godiya na ke ran ki shi dad’e’’
Gimbiya Binta ta k’ara da
"wallahi na tsane ki,duka cikin bayain fada babu wanda
na tsana kamar ke,wai amma a rasa wacce za a had’u ni da ita sai ke!’’
Ta shure Bintu ta wuce ciki,kan gado ta nufa ta zauna
d’ai-d’ai abun ta. Kai sun kuye Bintu ta tashi, ta nad’e tabarmar ta sannan ta
kwashe wankin Gimbiya. Gaba d’aya a takure ta ke yin komai musammam yanda
tafiya ma mai kyau da kyar ta ke gudun kar ta sake b’aci.
Sai da la’asar sakaliya ta gama wankin,bayan ta yi shanya ta
na shirin fara guga su Zahira su ka shigo d’akin. Nan fa su ka zauna in ban da
maganar Aisar babu abun da su ke.
‘’Aisar Gaddafi Nur ai ba k’aramin had’uwa yayi ba’’ fad’in
Gimbiya,ta k’ara da
‘’ni abun da ke ban mamaki ganin shi a matsayin malami’’
"ko ni ma na yi mamaki gaskiya’’
Zahira ta taya ta.Ajiyar zuciya Gimbiya Binta ta saki kana
ta ce
"ni fa k’awaye na wallahi na kamu, gaba d’aya ya shiga
rai na’’
Maryam da Zahira su ka sa shewa, Maryam ce ta amsa mata da
"ai dama ni tuni na d’ago jirgin ki,kar ki damu ai
jinin sarauta ba sa nema su rasa’’
‘’ko ba dan jinina ba ai na isa a soni,ba ku lura da yanda
ya ke kallo na ba ne?’’
Fad’in Gimbiya cike da tak’ama, wanda hakan ya sanya
k’awayenta yi mata kirari su na dad’a wasa ma ta kai. Bintu da ke jiyo su daga
can gefe ta murmusa cikin ranta fad’i ta ke "Malam Aisar ya cika jarumi
tinda har ya shiga ran Gimbiya’’ ajiyar zuciya ta saki ta na mai fatan Allah ya
tabbatar da alkhairi.
*******
Kamar yanda Gimbiya Binta ta ce,ranar a d’an wani lungu
cikin d’akin Bintu ta samu ta ra6’e. Da kyar ta iya samun bacci saboda sauro.
Da asubar fari Gimbiya Binta ta tada ita,kuma ba ta bari ta yi amfani da
band’akin su ba,sai k’asa ta sauka.
Bayan sun shiga aji sun fito hutun cin abunci da azahar,
Gimbiya ta hana ta zama cikin d’akin cin abunci,wai ta na sa ta tashin zuciya.
Tsaye ta ke bakin d’akin cin abunci, sai had’iyar yawu ta ke dan yunwar yau
tafi ta kullum. Rana ko ta take sosai dan kuwa su na sa ran samuwar ruwan sama
kwana kusa. Gashi in da ta ke tsaye sam babu inuwa, bini bini sai ta sa tafin
hannun ta ta goge zufar da ke faman ketowa bisa kuncin goshin ta. Da ta ga abun
ba na k’arau ba ne,ta sanya hannun ta cikin aljihu ta d’auko k'ulin ta da ta
d’an k’unso a yar leda. Wata bishiya ta hango,kai tsaye ta nufe shi ta na
k’ok’arin kwance ledar k'ulin. Ta gaban d’akin cin abuncin malamai wuce.
Ta taga ya hango ta,lokacin guda ya bar cin abuncin da ya
ke hannun sa ruk'e da cokali ya bi ta da
kallo. Tin da ya ke be tab’a ganin wacce ta iya tafiya tafiya irin na Bintu ba.
Tafiya ce a nutse ko wacce k’afa in aka aje sai an tsagaita kafin ta biyu ta
biyo ta. Gashi dai babu alamar tak’ama a tattare da tafiyar amma sai ta zama
tak’amar ce ma gaba d’aya. Kuma tsayin ta ya sa haka. Be dene kallan ta ba har
ta isa ga bishiyar ta zauna. Ganin ta bud’e wata yar leda ta na fitar da wani
abu ta na afawa a bakin ta sannan ya tuna fa yanzu lokacin cin abuncin d’alibai
ne,me ta ke yi a waje,ya aje cikoli ya tashi kai tsaye ya fito ya nufo in ta ke
zaune.
Bintu ta ba ta hango shi ba,ba ta kuma ga tahowar shi ba,ta
ciko hannun ta da kuli kenan ta afa a bakin ta , sai kawai ganin shi ta yi
tsaye kan ta,bakin ta cike da k'uli ta d'ago kai su ka had’a ido nan da nan
gaban ta ya fad’i,cikin zuciyar ta kuwa ihu ta kurma
‘’wayyo ni Bintu aradu wagga Malami ya takura ni!’’
0 comments:
Post a Comment