Cikin sauri ta tashi tsaye ta gaishe shi da harshen (French)
faransanci wanda da dama da shi su ka fi amfani a makaranta. Gaba d’aya ta
manta da wani kunyar sa da ta ke ji yanzun da ta gan shi tsaye gaban ta dan
kwarjinin da ya mata. Kan ta sunkuye
tana wasa da ledar k’wilin ta ya amsa mata a takaice fuskar babu walwala ya ce
‘’me ki ke yi waje lokacin cin abunci?’’
‘’Gimbiya Binta na ke
jira ta gama cin na ta sai ni ma na ci nawa’’
ta amsa zuciyar ta d’aya ba tare da ta d’aga kai ta kalle shi ba.
Cike da mamakin amsar ta ta ya ke duban ta, ita sam bata
lura da kallan na ta da ya ke ba. Kana ya ce "wacece Gimbiya Binta?’’ jin
tambayar na sa Bintu ta bud’e baki,cike da mamaki ta ce "laa ba ka san
Gimbiya Binta ba? Yar sarkin Sa'ayrasa fa, wata fara tas kamar d’iyar larabawa,
ta na da kwarjini matuk’a’’.
Badaban ran sa a 6ace
ya ke ba, yanda ta ke kod’a Gimbiyar ta ta sai da ta kusa ba shi dariya. Amma
sai dad’a tsuke fuska ya yi kafin ya k’ara da ‘’ban san wakike magana akai ba,
amma abunda na ke so na sani shi ne shin dokar makarantar ce sai wata Gimbiya
ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’
Tuni Bintu ta fara shan jinin jikin ta dan kuwa tabbas idan
hukumar makarantar ta ji wannan maganar matsala zai zame mata. Kana ta ce
"iye! Na’am? Dama wai,dama ai..........’’.
"dama me?” ya katse ta ya na mai duban ta. Nan fa Bintu
ta shiga cikwikwiya ledar hannun ta, ta rasa amsar da za ta ba shi.
"dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin
abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’ ya dad’a maimai ta mata tambayar
cikin k’aguwa. Ganin ba ta da niyar amsawa rai 6ace ya furta "menene
dangantakar ki da wannan da ki ke kira gimbiya ?ya sunan ki?’’
Cike da tsoro Bintu ta amsa ma sa "sunana Bintu, Bintu
Bala Mahuta, ni d’iyar bayi ce, ni ce baiwar da ke kula da Gimbiya Binta ta
masarautar Sa’ayrasa.....’’
‘’wannan ne ya bata damar hana ki abunci? Haka ake gudanar
da lamarin wannan makarantar? Saboda zalinci? Toh daga yau ya k’are ni Aisar ba
na san zalinci kuma ba zan juri ganin zalinci ba’’ ya na gama magana ya juya a
fusace ya fara tafiya, ganin haka Bintu da tun da ya fara magana ta gama
firgita, ba ta san sanda ta saki ledar k'wilin ta ba, ta bi shi da sauri tare
da shan gaban sa, sai ga ta ta zube gwiwowi biyu a kasa. Da sauri ya ja ya
tsaya ya na mai duban ta cike da mamaki ganin duk zafin ranar be hana ta saka
tafukan hannayen ta biyu k’asa ba ta mai duk’ar da kai kamar wacce ta ke shirin
shigewa k’ark’ashin k’asa.
Hankali tashe ta shiga jero masa magiya ta na mai fad’in
"tuba na ke, ka gafarce ni, na tuba, ka yiwa Allah da manzon sa kar ka
had’a ni da Gimbiya, aradu idan ta ji wannan maganar na kad’e har ganye na,ka
min rai, na tuba....’’ ta k’arasa maganar na ta cikin kuka. Aisar kuwa kasa
magana yayi ya na mai duban ta cike da tausayawa kana daga bisani ya ce
‘’tashi....."
maimakon ta tashi sai ta dad’a kask’antar da kai ta yi kasa
ta na kuka, jin kukan na ta ya ke har ran sa. Idanun sa runtse ya ce ‘’ya salam
wannan wata irin yarinya ce mai shegen taurin kai! ki-ta-shi-na-ce’’ a hankali
yayi maganar kamar mai koyan magana. Sai a sannan ta tashi, amma har lokacin
hawayen ta ke.
Kallan ta yayi na wasu dan dak’ikai, kafin ya mata nuni da
inuwar da ya tadda ta zaune ya ce koma
can ki zauna ina zuwa. Baki ta bud’e da niyar yi masa musu, amma ko da su ka
had’a ido sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’toh’’ ta yi sauri ta koma
k’ark’ashin bishiyar in da ta jingina jikin ta, ta na mai mayar da ajiyar
zuciya ganin Aisar shi ma ya juya ya tafi.
Ta na mai addu’ar Allah ya sa ya hakura kar ya dawo har ta
samu ta shiga d’akin cin abunci. Sai a sannan ta lura da ledar k’ulin ta a
k’asa ta yi sauri ta d’auko ta ka6e
dattin da ya mak'ale jikin ledar kafin ta tura cikin aljihun ta dan kuwa shi ma
ya fita ran ta. Jim kad’an Aisar ya dawo d’auke da wata yar bakar leda, ya
mik’a mata ledar tare da fad’in "gashi maza ki je ki sami waje ki ci’’
ledar ta bi da kallo, wani irin kamshi ke ziyarta hancin ta daga cikin ledar,
tuni ta mayar da mugun yawu, ta na mai girgiza kai ta ce "ah ah na gode ai
ba na jin yunwa dama’’ "ba kya jin yunwa?’’ ya maimaita cikin sigar
tambaya. Kai ta gyad’a masa alamar eh. Amma mai za su ji? ‘’kulululu’’ sautin
da ya fito daga cikin ta kenan wanda ya ke gasgata zargin Aisar na Batun Bintu
ba ta jin yunwa yasasshen zance ne.
Cike da jin kunya ta sunkuyar da kai k’asa, duk 6acin ran sa
sai da ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa. ‘’kar6a ki ci maza kafin a koma
aji’’ sai da ta d’an yi jim, kafin daga bisani ta sa hannu biyu ta karb’a ta na
mai godiya, fad’i ta ke ‘’Godiya na ke, madallah, Allah ya saka ma da alkairi’’
ba ta jira jin amsar shi ba tayi gaba, hannu na rawa ta ke k’ok’arin bud’e
ledar dan ganin abun da ya ke, ganin lafiyayya abuncin da ke cikin ledar tuni
ta fara k’ok’arin fara kaiwa baki dan ta ma manta da Malam Aysar da ya bi ta da
kallo cike da tausayawa har ta k’ure masa. Kai ya jinjina ya na mai shan
alwashin maganin wannan zalincin da Gimbiya ta ke yiwa Bintu na hana ta cin
abunci cikin d’alibai yan uwan ta. Shin dama har yanzu ana irin wannan zalinci?
wannnan wani irin sakaci ne daga hukumar makarantar, da ga alama dai ba banza
ta kawo shi makarantar ba, babu mamaki watan rufe makarantar ce ta tashi muddin
ana irin wannan zalincin da sanin hukumar makarantar. Da wannan tunanin ya nufi
ofishin Malam Hamisu. Yayi rashin sa’a ba ya nan dan haka dole ya hakura ya
koma ofishin zaman malamai da k’udirin cikin ran sa.
Yanda Bintu ke cin abunci kamar wacce ta shekara ba ta ci ba
ya sa ta saurin gamawa kafin su koma aji. Suna komawa kuwa lokacin koyarwar
Aisar ne. Da shigowar sa ba tare da 6ata lokaci ba ya fara abunda ya kawo shi,
wato koyarwa. Darasin na sa yau akan "Gaba" ne. Aisar ya fara da
tambayar misalan yankuna ko masarauta masu tarihin gaba tsakanin su, ba
jamhuriyar Nijar kad’ai ba har mok’otan su. D'aya daga cikin d’aliban ce ta
d’aga hannu, in da Aysar ya bata damar amsa tambayar, ta ce "kamar gabar
da ke tsakanin masarautar Sa’ayrasa da masarautar Fabarusa’’ Aisar na mai
jinjina kai ya ce "haka ne ku tafa mata’’ aji aka d’auki tafi "raf
raf raf"
Bayan haka ya k’ara tambayar "su waye ‘yan masarautar
Faburasa cikin ajin nan?’’ wajan mutum uku ne su ka d’aga hannu, bayan wani
d'an sakanni ya ce su sauke, masarautar Sa’ayrasa ma su d’aga hannu. D’alibai
shida ne su ka d’aga hannu, ciki har da Gimbiya. Bintu kuwa ta na can ta na
tunanin duniya, gaba d’aya hankalin ta ba ya ajin. Hannun su d'age be ba su
izinin saukewa ba dan shi hankalin sa kan Bintu ya ke, suma kuma ‘yan ajin sun
lura da hakan dan su ma d’in Bintu da ta doka uban tagumi su ke kallo.
Kamar daga sama ta ji ya ce ‘’Bintu hankalin ki ba ya aji na!’’
ta yi firgit ta dawo cikin hankalin ta ta na mai cire hannun ta daga tagumin da
ta yi. Ganin idanun kowa kan ta, ga hannun wasu daga cikin yan ajin har da
Gimbiya d’age ya sa Bintu kai duban ta ga Aisar, in da shi kuma ya maimaita
mata umarnin da ya ba su. Da saurin ta ta d’aga na ta hannun sama sannan ya ce
su aje hannun na su. Wata har da fad’in "wash hanuna" a hankali yanda
Aisar ba zai jiyo ta ba.
Bintu ba ta tsorata ba sai da ta ga Gimbiya ta juyo ta watsa
mata harara. Wani mugun yawu ta had’iya tuni hantar cikin ta ta kad’a. Malam
Aisar kuwa be gushe ba ya cigaba da "shin wa zai fad’a min lokacin da
gabar ta samo asali?’’ d’aya daga cikin su ta amsa da "gabar ta samo asali
ne tun kaka da kakanni amma anfi dangan ta shi da lokacin mulkin sarki Abdulrahaman
III na masarautar Faburusa’’ Malam Aisar ya ce a tafa mata sannan ya sake
tambayar hanyoyin da ya dace a bi domin kawo karshen gaba tsakanin k’asa da
k’asa ko masarauta da masarauta. Dalibai da yawa su ka d’aga hannu, amma ga
mamakin kowa sai ji su ka yi ya ambaci sunan "Bintu’’
‘’Wayyo shi dai sai ya fad’awa kowa ya san sunana ko menene
haka?’’ ihun da Bintu ta kurma cikin ran ta kenan. Gaba d’aya ajin idanu su ka
zubo mata yayinda ta tashi a hankali murya kamar ba nata ta ba, ta furta abun
da ya fara zuwa bakin ta "auratayya tsakanin masarautar’’ nan fa aji aka
kwashe da dariya, Zahira ta ce "auratayya tsakanin bayi, d’iyar bayi ta
auri dan bayi.....’’ aka dad’a sa dariya.
Kunya ta rufe Bintu kamar ta shige k’ark’ashin kujera ta
6uya. "shiru!’’ Aisar ya daka musu tsawa. Aji yayi shiru kamar wanda ruwa
ya shanye, ran malam ya 6aci. ‘’wata mara tarbiya ce ta yi wannan maganar?’’ ya
tambaya a fusace. Aka rasa mai bashi amsa, har sai da ya sake maimaitawa sannan
Zahira ta tashi tsaye gwiwa a sanyaye. Bintu ya duba ya umarce ta da ta zauna
kafin ya koma ga Zahira. Ya ce da yan aji kowa ya dube ta, shin ita yar wata
yanki ce. Ta na zumb’ure zumb’ure ta amsa da ‘’Niamey’’ kai ya girgiza kan ya
ce ‘’Niamey na alawadar da masu hali da kalimi irin na ki, kalamai ne irin na
marasa tarbiya wanda su ka tashi a watse, lalle idan har Jamhuriyar Nijar na da
yan k’asa irin gaba tsakanin yankuna ba zai tab’a yankewa ba, fitar min daga
aji kuma kar ki sake shigowa in har ni ne cikin ajin’’ Zahira ta wuce fuuuu za
ta fita ya ce ‘’dube ta k’azama kawai’’ kunya ya rufe ta ta fice da sauri.
Jikin kowa yayi sanyi, tin ba ma Bintu ba. Aisar kuwa be
sake cikakken minti goma ba ya fice da ga ajin,dan kuwa tabbas d’aliban
makarantar na fama da rashin tarbiya na gaske. Surutai kuwa ta sha wajan yan
aji, daga mai fad’in "kun ji yanda ya ke kiran sunan ta kuwa?’’ sai mai
fad’in ‘’ta yaya ya san sunan ta bayan be ta6a tambayar sunayen mu ba?’’ ita
kuwa Bintu kai ta kifa bisa teburi dan Allah kad’ai ya san masifun da ke gudana
cikin zuciyar Gimbiya, ta san yau kam sai yanda aka yi da ita wai d'an daudu a
kabari.
Bayan an tashi daga makaranta, ko kallan ta Gimbiya Binta ba
ta yi ba ta ta wuce gaba ita da Ruqayya, Bintu na rawar jiki rik’e da jakar
Gimbiya ta bi bayan su. Ba su zame koina ba sai d’akin su in da su ka tadda
Zahira na jiran su dan gasawa Bintu gurasa danya a hannu.
Zagaye Bintu su ka yi tsakiyar d’aki, sai ta fad’a musu yanda aka yi Aisar ya san
ta yasan sunanta da har ya ci mutuncin Zahira saboda ita. Bintu na raba idanu
ta ce ‘’Dan Allah Gimbiya ki min afuwa, aradu shi da kan sa ya tambayi
sunana........’’
Ji ka kake tas! Gimbiya ta kwashe ta da marin da sai da
Bintu ta ga wuta a idonta, a gigice ta sa hannu bisa kuncin ta na mai fashewa
da kuka. Gimbiya ba ta gushe ba ta ce " Yar iska! A shekarun ki har kin
iya karuwanci?!!!’’ Ta sa k'afa ta shure Bintu. "Yo dama ana raba bayi da
karuwanci ne Gimbiya?’’ Rukayya ce ta ara ta yafa. Zahira ta k’ara da, "Wallahi tunda ki ka sa mutum kamar
Aisar ya ci mutuncina sai kin yabawa aya zak’inta."
Ita dai Bintu ta kasa magana, kanta durk’ushe, sautin kuka
kad’ai ke iya fita daga bakinta. Gimbiya ta ce ko dai ta fad’a mu su yanda aka
yi ya san ta har ya tambayi sunan ta ko ta kira waya fada a zo a mayar da ita
Sa’ayrasa. Jin haka haka nan da nan Bintu ta shaida musu komai. Duka da mari
babu wanda ba ta sha ba. A fad’ar Gimbiya don tasan tana da k’udirin auren
Aisar ya sa ta ke masa shisshigi dan ta 6ata ta wajan shi, toh wallahi ta yi
kad’an, duk randa ta yarda wani abu ya k’ara shiga tsakanin su ta tabbatar
ranar zaman ta a wannan makarantar ya k’are. "Godiya nake Gimbiya’’ a
Abinda ke fita daga bakin Bintu kenan har su ka k’araci
masifar su, su ka tafi d’akin Zahira.
Bintu na zaune inda suka bar ta, ta had’e kai da gwiwa in
ban da ajiyar zuciya babu abun da ta ke, sai ga Iya Dije ta shigo da sallamar
ta. Ganinta Bintu ta yi saurin gyara zama ta na mai k’ok’arin goge hawayen da
ke fuskar ta gudan kar Iye Dije ta gani. Cike da mamaki Iye Dije ta ce
"Bintu lafiya? Me ya sa ki kuka haka? Ya na ga idonki d’aya ya
kumbura?’’ "Ba na jin dad’i ne Iya
Dije, ciwon kai da ido na ke’’ Bintu ta yiwa Iya Dije k’arya gudun abun da zai
je ya dawo. Cikin nuna tausayawa Iya Dije ta ce " Ayya Allah ya sauwake,
na ce dai kin je kilinik (clinique, karamin asibitin makarantar) an duba ki
ko?’’ Kai Bintu ta girgiza alamar ah ah, sannan ta k’ara da ‘’Ba sai na je ba,
ina da magani, idan na sha shikenan."
Kallan ta Iya Dije ta ke kamar mai nazarin wani abu, kafin
daga bisani ta ce ‘’Toh Allah ya sauke.’’ Ta ja wata yar kujera ta zauna sai a
sannan Bintu ta lura da ledar hannunta, a gaban Bintu ta aje ledar kan ta
tambaya "Shin al’adar ta ki ta d’auke ne?’’ Cikin nuna jin kunya Bintu ta
girgiza kai alamar ah ah. Iya Dije ta ce "Ai bakomai, dama daga kwana
d’aya har zuwa kwanaki goma sha biyar yakan iya kai wa. Dama batun turaren ne,
Malam Aisar ya ba ni kud’i, sanin ba a bari dalibai su fita daga makaranta yasa
na yi karambani na siyo miki’’ Ta sa hannu cikin ledar sai gashi ta fito da
kwalaban turare har guda uku, ta aje gaban Bintu ta na fad’in ‘’Kinga wannan
Danduwala ne, ga kuma Kafin-kafin, ga Binta Sudan duka na ki ne." Ta
k’arasa maganar tana mai washe hak'ora don tasan ba k'aramin gwanin ta ta yiwa
Bintu ba, duk da dai rabin kud’in da Aisar ya bata a aljihun ta ya k'are.
Bud’ar bakin Bintu sai cewa ta yi "Iye Dije na gode
amma dan Allah ki mayar masa, aradu ba zan iya karb'a ba, ba na so’’ ‘’La'ilaha
illallahu!" Fad’in Iye Dije ta na mai tafa hannu "Ku ga yarinya za ta
watsan k'asa a ido! Ba kya so a na wani dalili? Iyye?!!!’’ Ta yi tambayar ta na
mai fidda idanu ganin Bintu na shirin kwance mata zani a kasuwa, don kuwa karya
da gaskiya ta had’a ta fad’awa Aisar kan buk’atun Bintu, haka ya bata kud’i CFA
na gugan CFA har (10000 CFA), fiye da rabin kud’in ta kashe. Bintu ta rasa
amsar da za ta bata, ta tsinci kanta tana mai fad’in ‘’Na ga ba na buk’ata ne
Iya Dije.’’
Ba ta ankara ba sai ganin Iya Dije ta yi ta d’aga hannunta
tana mai k’ok’arin cusa hancin ta k’ark’ashin hammatar Bintu. Da sauri Bintu ta
ja da baya ta na k’ok’arin kwatar kanta, fad’i ta ke ‘’Iye Dije ya haka?” Iya
Dije kuwa duk da babu abinda ta shak’a na wari daga jikin Bintu don kuwa Bintu
irin mutanen nan ne wanda sam ba su da warin jiki, sai ga ta ta yi baya da
sauri ta na mai toshe hanci ‘’Kin ji yanda ki ke bugawa ki na hamami kuwa? Har
ki ce ba kya buk’ata? Shi kan shi Malam Aisar d’in wannan hamamin na ki ya ji
shi ya sa ya ce na tambaya ko ki na da buk’atar turaren.’’
Jin haka kunya ta rufe Bintu, kamar k’asa ta bud’e ta shige.
Ta na mai yin k’asa da ido ta ce ‘’Ai idan Gimbiya ta gani ko ta ji ina kamshin
turare ma su k’amshi haka Iya Dije kashi na ya bushe’’ Sai a sannan hankalin
Iya Dije ya fara kwanciya, ta ce ‘’Yo ba sai ki 6oye yanda ba za ta gani ba,
sai ki na sawa kad’an haka, ni dai ba zan mayar da wanga turare ba’’ Ajiyar
zuci Bintu ta saki ganin babu yanda za ta yi dole ta hakura ta kar6a ta na mai
godiya. Ita kuwa Iya Dije ko da ta samu ta cusawa Bintu turare sai ta sami
kwanciyar hankali, dan da ba ta san yanda za ta yi ta biya da kud’in Aisar da
ta ci ba.
Aisar kuwa sai da ya tabbatar ya kaiwa Malam Hamisu
k’orafinsa kan rashin tarbiyar d’alibai da kuma zaman wata d’aliba a waje
lokacin cin abinci ba tare da ya ambaci sunan Bintu ba. Malam Hamisu ya nuna
rashin saninshi kan maganar yanayin cin abincin d’aliban, kuma ya yi masa
alk’awarin d’aukar mataki. Saidai batun rashin tarbiyar d’aliban ya ce su ma
hakuri su ke da su kasancewar kowani tsuntsu kukan gidansu ya ke, amma In sha
Allahu za su k’ara tsauri kan lamarin.
Washagari da safe wajan taron d’alibai (Assembly), Mallam
Hamisu ya ja kunnan d’alibai akan bin duka, musammam wanda ba sa halartar wajan
cin abinci idan lokacin yayi, ya kuma tsawatar da hukunci mai tsanani muddin
aka ga d’aya daga cikin d’aliban na aikata hakan. Da wannan Bintu ta sami
saukin samin cin abinci tare da yan uwan ta d’alibai duk da kuwa sai da ta sha
tuhuma gun Gimbiya akan zargin ko ita ta kai k’arar ta.
Kwanci tashi haka rayuwa ta kasancewa Bintu cikin makaranta.
Gaba d’aya gudun Aisar ta ke, tun shi ma bai gane ba har ya zo ya gane ya daina
nemanta. Ita kuwa Zahira hakuri ta je ta bashi tare da sa bakin Malam Hamisu ya
hak’ura ya bari ta koma ajin na shi. Gimbiya Binta babu irin cusa kai da ba ta
yiwa Aisar, amma sam ba ta gabansa bare ya san ta na yi, manyanta ma yan aji
biyar da shida fama su ke bare ita karan kad’a miya acikin jerin ‘yan mata.
Da yammacin ranar lahadi, ana saura sati biyu su Bintu su
fara jarabawa. Yanda garin yayi wasai, gajimare yayi lub-lub, ciyawa da bishin
da ke cikin lambun sun yi kore shar, ga wani ni’imatacciyar iskar da ked’awa
wanda sanya rassa da ganyayyakin bishiyun da ke cikin lambun rausayawa suna mai
fuzar da feshin ruwa sanadiyar ruwan sama da ya sauka ya kuma tsaya mintina
talatin da su ka wuce ne ya sanya Aisar
da ke kwance kan kujerar hutun da ke k'ark’ashin d’aya daga cikin rumfunan
lambun, in banda kukan tsuntsaye da kuma k’arar saukar sauran ruwan sama da
yayi ragowa bisa kwanan rumfar lambun babu abun da ke tashi.
Sanye ya ke cikin bakar riga mai k’aramin hannu, da wando
wanda ya ke shi ba gajere ba bai kuma kai masa har k’asa ba. Idanunsa lumshe
tamkar mai bacci, ko da yake da zai sami bacci da hakan zai fi so dan kuwa
tunanin da ya dad’e ya na damun sa yanzun ma shi ya sa shi gaba. Ba kuma
tunanin kowa bane, face na Bintu, musammam yanzu da aikin binciken su ya k’are,
Bintun ce ta zaunar da shi a makarantar da tuni ma ya dakatar da koyarwa, dan
kuwa dai hakin su ya riga ya cimma ruwa a game da aikin su. Abin takaicin shi
ne tsakanin sa da Bintu sai dai a aji, duk yanda zai yi ya ganta bayan aji ya
gwada amma abu ya faskara, don kuwa dai Bintu gudun sa ta ke k’iri k’iri. Shi
kan shi bai san meyasa ya kasa cire yarinyar daga ransa ba, amma dai yau idan
har bai sa ta a idanunsa ba zai iya shiga damuwa. Gashi kuma yau lahadi ko makarantar bai shiga ba bare ya ganta a
aji. Nan fa wata dabara ta fad’o masa, ya tsinci kansa ya na mai murmusawa.
Ajiyar zuci ya saki yayin da ya bud’e idanu a hankali jin
d’igar ruwa bisa fuskarsa sanadiyar iska da ta kad’o wani reshe zuwa cikin
rumfar. Tashi ya yi zaune ya na mai duba lokaci, k’arfe biyar daidai, ya aje
hannu inda ya tashi cikin azama ya na mai k’ok’arin zura takalmi cikin
k’afafunsa. Kai tsaye ya fice daga cikin
lambun, ya bi ta farfajiyar gidan ya shige falonsa wanda zai sada sa da d’akin
baccinsa. Cikin k’ank’anin lokaci ya sauya kaya izuwa farar jamfa da hula tare
da farin takalmi. Ya gama fesa turaren sa mai kamshin gaske ya wuce cikin
motarsa. Hankali kwance ya fito daga gidansa, sai gashi kan titin francophonie,
kai tsaye ya nufi makarantar Soverign.
Minti goma kacal ya kai shi makarantar, Allah ya taimake shi
ya had’u da Iya Dije a bakin gate ta na shirin fita kenan. Tsaida Ita ya yi,
ya nemi alfarmar ganin Bintu. Iya Dije
da tun da ta ga Aisar da yamma haka, gashi ranar lahadi ta san banza ba ta kawo
zomo kasuwa, ta yi kud’irin samun wani abu daga aljihun sa. Jin buk’atar ta sa
sai ta yi hamdala cikin ran ta, ta na mai
gyara tsayuwa ta ce ‘’ai kasan yanayin dokar makarantar ne Malam, an
hana d’alibai kebewa da Malamai musammam irin wannan lokacin da ba na d’aukar
darasi ba’’
Duk da maganar ta Iya Dije
ta yiwa Aisar wani iri, jin ta yi amfani da kalmar ‘’ke6ewa’’ amma sai
ya basar, ya na mai murmusawa ya ce ‘’ba ki fahimce ni ba Iya Dije, ba wai
tsayar da ita zan yi ba, kawai dai sak'o zan bata, na ga fita ma za ki yi ko?’’
nan fa Iya Dije ta samu mafaka, ta amsa da ‘’eh wlh kasuwa zani, zan saro kaya
duk da dai ba wani jarin arziki gare ni ba’’ ganin Aisar ya sanya hannu cikin
aljihu jikin ta har rawa ya ke. Ilai kuwa sai gashi ya fito da kud’i CFA na
gugan CFA, ba tare da ya k'irga ba ya mik’awa Iya dije ya na mai fad’in ‘’gashi
ki k’ara kan jarin na ki’’
nan Iya Dije ta cafe kud’i saura kiris ta had’a da hannun
Aisar, fad’i ta ke ‘’kai dai ba ka gajiya, madallah, yo ai in da yarda ai na
yarda da kai, bara na kira maka Bintu Bala Mahuta, amma dan Allah kar ta dad’e
ka ga dai ni fita zan yi’’
Aisar na murmushin nuna jin dad’i ya amsa da ‘’toh, ina nan
kusa da ofishin malamai ina jira.’’ da azar6a6in jiki Iya Dije ta koma ciki ta
na k'irga kud’in da aka ba ta.
Bintu na zaune cikin d’aki, kasancewar Gimbiya Binta ba ta
nan ta je karatu, itama ta sami damar yin na ta karatun. Sanye ta ke
cikin shigar su na bayin Sa’ayrasa dan ba ta isa ta sa kayan gida ba duk da dai
yau d’in kowa ado ya ke yi. Sai ga Iya Dije ta shigo, kallo d’aya za ka mata ka
tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Ta na mai washe baki ta ce
‘’Bintu tashi maza ki
biyo ni, Malamin ku ne ya ke neman ki, eh! Malam Aisar’’
jin sunan Aisar Bintu ta fidda Ido tare da fad’in ‘’Iye?’’
Iya Dije ba ta damu
da yanayin tsoron da ya bayya na fuskar Bintu ba, ita dai burin ta shi ne ta kai ta ga Aisar ta samu ita ma ta
fita,
ta ce; ‘’ke tashi mana, ni kasuwa zani kin ga dai yamma ta
yi sosai, shida na yi ba lalle na samu shiga ba, kuma kayan abincin ku na sati
zan kar6o’’
‘’Iya Dije dan Allah ki ce ba ki ganni ba’’ ta fad’a ta na
yin rau-rau da idanu kamar mai shirin yin kuka.
Baki bud’e Iya Dije ta ce ‘’kun ji ni da yarinya, yo me zai
mi ki da za ki sa ni yin k’arya da tsufa ta, na k’i na ce ban gan ki ba d’in’’
Bintu ta ce ‘’Iya Dije aradun Allah Gimbiya ta ce idan ta
ganni da shi sai na lahira ya fi ni jin dad’i, ki min afuwa ki taimake ni’’
‘’wannan kuma ke ki ka sani, idan dai ba ke ki fad’a ma ta
ba ina za ta san ma kin gan shi? Ko ta na nan ne?’’ Bintu ta girgiza kai alamar
aha ah. ‘’toh maza yafa mayafin ki mu je’’ Bintu ta ce ai ba ta da mayafi. ‘’ai
kuwa dai ba na tafi da ke ti6i ti6i da ke haka ba, budurwa kamar ki ki ce ba ki
da mayafi? A garin na ku haka ki ke yawo?’’ Iya Dije ta tambaya ta na mai duban
ta.
Kana Bintu ta amsa
mata da ‘’ina da su, su na gida ne Gimbiya ta hana ni zuwa da kayan gida’’
Cike da nuna Allah wadai da halin Gimbiya Binta, Iya Dudu ta
ce "wannan shi ne zancen 6ir in ji
tusa, menene amfanin hana ki ado ko rufe
jikin ki ? Ke tashi mu je ko aran zani ne na baki ki yafa ko ma d'auko wannan
d’an hijabin nan da ku ke sawa ki yafa, ai yafi babu kaka ta wajan uba’’ .
Hakan ko Bintu ta yi,
ta na magiya amma Iya Dije ba ta fasa jan ta ba su ka fito daga 6angaran d’akin
kwanan d’alibai, tun suna wuce d’alibai wanda ke zaune farfajiyar wajan har ya
zama tsilla tsilla kad’ai ake gani, musammam da ka baro sashin kwanan d'alibai
su ka shigo farfajiyar makarantar. Ganin sun nufi ofishin malamai gaban Bintu
ya fara fad’uwa.
***
Wata baranda gaban ofshin malamai su ka hangi Aisar zaune
kan kujera, ganin Bintu tuni wani farin ciki ya lullu6e shi har cikin ran sa.
Da kyar ya iya jira su ka k’araso in da Iya Dije ta bar shi ta na mai yiwa
Aisar kashedin kar fa Bintu ta dad'e. Ba tare da wata damuwa ba tun da ita dai
ta cika jakarta da kud’i ta yi gaba ta bar Bintu da Aisar. Ganin yanda Bintu ta
bi bayan Iya Dudu da ido, Aisar ya ce Bintu ko bin ta za ki yi ne?”
Da sauri ta mayar da hankalin ta gare shi, ta gaishe shi
cike da girmamawa. Ya amsa a takaice tare da mata nuni da wata kujera da ke
gaban ta sa ya ce ta zauna dan kar ta b’ata k’afar ta cikin ca6in ruwan sama.
Ba musu ta ja kujerar can nesa da tashi sannan ta zauna, kan ta sunkuye ta na
wasa da yan yatsun hannun ta, ita dai Allah Allah ta ke Aisar ya sallame ta ko
ba dan Gimbiya da sauran d’alibai ba, ko dan sanyin iskar damina da ke kad’awa.
Jin shiru be tanka ba
ya sa ta yanke hukuncin tambayar dalilin kiran na ta, amma ko da ta d’aga kai,
sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ashe duk zaman nan kallo yake k’are
mata. Da sauri ta k’ara yin k’asa da ido, ganin haka ya murmusa ya ce
"Bintu gudu na ki ke ko?’’
Shiru ba ta amsa masa ba, ya k’ara da ‘’ya karatu? Ki na dai
yi sosai ko? Ko da ya ke na ga kin ci gwajin da na mu ku sosai’’ kamar ya na
magana da dutse Bintu ta k’i amsa masa. Be gushe ba ya ce ‘’daga wannan zangon
zan dena koyarwa a makarantar ku, ban san me ya sa na ke fad’a mi ki ba, amma
ina jin ya dace ki sani ne’’
Jin haka Bintu ta tsinci kan ta da fad’uwar gaba, ba ta san
sanda ta ce "saboda me? Ba dai laifi mu ka maka ba ko?’’
kai ya girgiza mata sannan ya ce "yanayin aiki ya sa,
amma inshaAllahu zan sa a maido da k'anwata makarantar nan kin ga sai ki sami
k’awa ko?’’ murmushi Bintu ta yi wanda ke k’ara bayyana kyan ta, hakan ya sa
Aisar fad’in
"dama haka ki ka iya murmushi?’’
sai kuma Bintu ta tsuke fuska, ta na shirin tambayar dalilin
kiran na ta, wayar shi da ta hau k’ararrawa ta tsaida ita. Da ke wayar tafi da
gidan ka(handset) be gama cika gari ba, hannun wane da wane kad’ai ake gani,
waya ce kirar (Nokia 3310), dan haka baki bud’e ta tsaya ta na kallan wayar har
ya d’aga ya kara bisa kunan sa, ji take da zai bata ta d’an kara kunan ta da ba
haka ba.
Bintu ba ta dad’a shagala ba sai da ta ji ya ambaci sunan
Barde, nan da nan ta manta da wani nauyin Aisar da ta ke ji, ta fara Allah
Allah ya gama wayar.
Ta gani ya kashe ta ce "Malam dama kasan Yaremi Barde
na Fabarusa?’’
‘’ Na san Barde, amma yanzu ba da shi na yi magana ba’’ sai
da ya ba ta amsa sannan kuma mamakin yanda aka yi ta san Barde ya kama shi, be
san sanda ya ce ‘’Yerima Barde ke? Ina ki ka san Barde ke kuma ki na yar
masarautar Sa’ayrasa?’’ ya tambaya cike da mamaki.
Nan fa Bintu ta fara jero bayani cike da nuna gwanintar yan
ajin su ma ba a barsu baya ba ta ce "ai rannan a aji aka yi hirar shi,
ance shi ne mai kyawun duniya kuma k'asar nan kaf babu wanda zai gwada masa
k'asaita, rabin yan ajin sun ta6a ganin shi, ni ma ina so na gan shi ko da sau
d’aya ne a rayuwa ta’’
Jin kalaman Bintu tuni Aisar ya had’e rai, yayi k’icin
k’icin ya fara fad’a "wato a shekarun ku har kun san ku zauna ku yi hirar
samari ko? Ba ku san komai ba sai kula samari da karanta littafin soyayya ko?’’
"wallahi malam ba na kula samari ni ba yar iska ba ce’’
furucin Bintu kenan yayinda idanun Bintu su ka fara kawo ruwa, sai a sannan ta
ankare da 6aran6aramar da ta yi na tambayar Barde, duk da dai ita ba da wata
manufa ta yi. Ganin Bintu na shirin masa kuka har da batun ita ba yar iska bace
ya sa hankalin sa kwanciya, wato kenan ba ta kula samarin tun da har ta masa
wata fassara na da ban, hakan ya masa daidai har ya na mai murmusawa. Ita ko
Bintu ta shi ta yi da sauri ganin wasu d’alibai sun fito daga d’akin karatu, ta
ce malam dama karatu na ke Iya Dije ta ce za ka bani sak’o’’
Sai a sannan ya tuna fa ashe ba ranar makaran ta ba ne,
gashi shi babu wani sak’o da ya kawo mata dama ganin ta kawai ya ke san yi.
Amma gudun kar ta d’auke shi sakarai fakewa yayi da dama ya zo wucewa ne ta
makarantar ya ce bara ya tsaya ya ji ta na karatu kuwa, maza ta koma ta cigaba da karatun. Da wannan
ta masa sallama, har ta na fad’awa cikin ca6i dan saurin kar wannan d’aliban da
ta hango su gan ta tare da Aisar. Shi kuwa gogan na ta ko ganin su be yi da ke
su ma d’in lab’ewa su ka yi domin su tabbatar da abun da su ke gani.
***
Sai da Bintu ta k'urewa ganin sa sannan ya tashi ya nufi
motar sa, ya gifta ta gaban wannan d’alibai da ke leb’e bayan wata yar katanga
sam be lura da su ba har ya kai ga motar shi ya shige ya fice daga makarantar.
"kut yau kuwa za yi bantan uwa a makarantar’’ fad’in
d’aya daga cikin d’aliban kenan wacce su ke Marry yayinda su ke fitowa daga
wajan 6uyan su ganin Aisar ya fice. Su uku ne, kuma dukan su yan aji shida ne
ma su mik’amin. Marry ita ce mai ruk’e da muk’amin horo, sai shedigyal da kuma
mai kula da tsafta da lafiyar d’alibai, wacce su ke kira da Sikanti.
Marry ba ta gushe ba jiki na rawa tsabagen masifa ta k’ara
da "wai ido na ne ke zagi ko kuwa Malam Aisar na gani da wata kwaila a
makarantar nan?’’ Cikin Jimami Shedigyal ta ce ‘’ni ma dai abun nan ya ban
mamaki, ki ga yanda mu ke bin sa ya na mana wulakanci amma ya rasa wacce zai bi
sai Bintu d’iyar bayi’’ sikanta dan mamaki ta ma kasa magana. Marry ta d’aga
k’afa ta doka k’asa cikin ca6ali, nan da nan zanin ta ya 6aci amma ko aji kin
ta, idanun ta ya rufe, kana ta ce ‘’ba d’iyar bayi, ko d’iyar saraki ce yau sai
ta ci Uban ta, za ta min bayanin dalilin da ya sa ta kyebewa d Malami, kut
Malamin ma wanda na ke so dan uban ta? Yau sai ta lashi kashin b’and’akin k’asa
dan uban ta Bintu ta ke kowa? Ta yanki tsiya!" ta wuce fuu, dama ga ta
jibgegiya tabarakallah. Su shedigyal su ka rufa mata baya, kai tsaye sashin
kwanan d’alibai su ka nufa.
***
Bintu kuwa komawar ta d’aki ta tadda Gimbiya ta dawo tare da
k'awayen ta, ko da ta tambaye ta daga in da ta ke sai ta mata k’aryar Iya Dije
ce ta aike ta. Ta ci sa’a yan masifar Gimbiya ba sa kusa, hankalin ta na kan
labarin da Zahira ta ke ba su. Can gefe Bintu ta zauna ta na mai mamakin
dalilin da Aisar ya fad’a mata na zuwa ganin ta. Zaman ta ke da wuya ta ji ana
kwala mata kira "Bintu Bala Mahuta dan uban ki sauko!’’
Ba Bintu ba hatta su Gimbiya sai da su ka kasa kunne su na
jiran tsammani. ita kuwa Bintu jikin ta ne ya hau b’ari jin muryar Marry da
gaba d’aya ya 6angaran d'akin kwanan d'alibai. Gimbiya ce ta kai kallan ta ga
Bintu ta na mai tambayar ‘’yar nema me kuma ki ka yiwa wannan mai fasalin
mazan?’’ Bintu ta kasa magana tsabar tsoro, nan fa su ka k’ara jiyo har gowar
Marry ta na mai fad’an ‘’dan uban ki na ce ki sauko kimin bayanin wani malami
ki ka kyebe a bayan aji!’’
Nan fa Bunti ta kware saboda firgici da tsoran maganar da
Marry ta furta, inda Gimbiya, Zahira da Ruqayya su ka tashi tsaye a a tare,
Gimbiya na fad’in ‘’ki tabbatar wannan malamin da ake magana akai ba Malam Aisar
ba ne!’’
Can waje kuwa tuni d’alibai kowa ya fito jin shela da tonan
siririn Marry, wasu ma babu cikakken sitiran arziki jikin su haka su ka fito
bawa idanun su abinci dan kuwa sun san koma wacece wannan ta shiga hannun Marry
ta kad’e har ganyen ta, musammam jin ance "ta kyebe da Malami."
"BINTU BALA MAHUTA! Ko ki sauko ko na zo na sauko da ke
ta!’’ fad’in Marry ta na mai kumfar baki.
Tnx but plz is book 2 page 18 of bintu diyae bayi CE?
ReplyDeleteGood abu kam yayi naji dadin littafinnan
ReplyDeleteFrom Hausa Ebooks