*WAIWAYE ADON
TAFIYA*
Wanene Sarki Sule Inuwa Magaji?
Shi ne Sarki na
ishirin bisa gadan mulkin Sa’ayrasa. Ya hau kujerar mulki a shekara ta (1984),
bayan Sarki Inuwa Magaji mai rasuwa, lokacin ya na da shekara arba’in a duniya.
Allah ya azurta shi da ‘ya’ya goma sha takwas, ya birne takwas saura goma a
raye, maza takwas, mata biyu.
Mata hud’u ya aura, uwargidansa marigayiya Hajja Fatima
Abdu, wacce ta rasu bayan shekara d’aya da hawar sa mulki, wajan haihuwar
Gimbiya Binta. Haka kuma ita ta haifawa sarki yara takwas, kasancewar auren
saurayi da budurwa su ka yi da Mai martaba, ‘ya’yan ta su an manya duk da dai
yawanci ba su yi tsahon rai ba dan sai da ta birne hud’u kafin ta samu masu
zama guda hud’u. Yerima Inuwa mai shekara talatin, yayi aure har da yara uku,
Yerima Nuhu shekara ishirin da biyar, Gimbiya K'amariyya mai shekara ishirin da
haihuwa sai kuma Gimbiya Binta .
Sai kuma matar shi ta biyu Hajja Salame wacce ake kira Hajja
Kilishi, ita Allah be nufe ta da haihuwa ba. Sai ta uku Hajja Maimunatu ana
kiran ta Uwar fada, yaran ta biyu, Hassan da Hussain wanda su ke sa'annin
Gimbiya K’amariyya sa kuma amaryar wacce ta ke kanwa ce gun Hajja Fatima Abdu,
aka d’aura masa bayan rasuwar sa mai suna Masarriya, ana kiran ta da Inna
Salti(wacce za ta haihu da yawa), yaran ta hud’u, duka maza. Sun had'a da
Yerima Hamza wanda shi ne babba mai shekara goma sha uku, sai mai bin sa Yerima
Abdallah dan shekara goma, na ukun Yerima Ahmadu, shekara takwas sai autan ta
Yerima Nadir mai shekara biyar a duniya.
Kasancewar ‘ya’yan sa mata biyu kacal a duniya da kuma
soyayyar da ya ke yiwa uwar su, ya d’auki san duniya ya d’aura ma su, musammam
K’amariyya wacce kamar ta d’aya da mahaifiyar ta kamar kabo da kabo. Hakan shi
ya zame babban rauni ga Sarki Sule.
***** ******
Sai da su ka shige tsaunika da duwatsu, suna mai ketare
yankuna da dama ta sahara, kafin su hau mik'ak'k'iyar hanyar da za ta sada su
da Sa’ayrsa. Ta babbar kofar wanda ake yiwa lak’ani da kofar Magaji Babba su ka
shiga yanki. Rana ne sosai kwallewa a yankin daga gani ka san ruwa be sauka
baw, kamar ma ruwan sama be sauka a yankin ba bana. Jama’ar gari kowa sabgar
gaban sa ya ke, daga masu zuwa ko dawowa daga kasuwa, sai masu zuwa gona, mata
wasu da goyo wasu da yara a hannu su na ta hidimar su, ya yara su ma ba a bar
su a baya ba, su ma da na su sabgar irin ta yara.
Babban abun da Bintu ta lura da shi, shine rashin annushuwa
da kuzari na jama’ar yankin, ba kamar yanda ta saba ganin jama’ar yankin cikin
farin ciki da annashuwa ba.
‘’Shin ko dai akwai wani abu da ke faruwa wanda ba mu da
masaniya akai?’’ Tambayar da ta ke yiwa
kan ta kenan, amma gudun magana ya sa ta kasa kada baki ta tambayi sauran bayi
‘yan uwan ta, har su ka kai ga kofar fada.
Ta k’ofar gabas su ka shiga fada, wanda dama in dai iyalan
sarki ne ta nan su ke shiga.
Nan da nan jama’ar fada su ka fito tarban Gimbiya, ciki har
da k’annan Gimbiyar wato Yerima Hassan da Yerima Husaini, Yerima Abdallah da
kuma Yerima Hamza. Murna da farin ciki gun su kuwa ba a cewa komai.
Ana cikin wannan yanayin ne Bintu ta fito ta, bayan ta d’au
d’an akwatin k'arfen ta, ta ja gefe babu wanda ya lura da ita bare a damu da
halin damuwa da ta ke ciki. Ganin Gimbiya ta fito, da sauri ta k’arasa cikin
bayi yan uwan ta, in da su ka zube domin kai gaisuwa ga su Yerima, sannan bayi
su ka taka mu su baya su ka shege izuwa fada.
Bintu na durk’ushe ba ta tashi ba ta ji an tab’a kafad’ar
ta, a hankali ta d’aga ido, tuni murmushi ya maye fuskar ta yayin da ta tashi
tsaye ta na mai rungume yayan ta Habibu. Cikin farin ciki ya ce ‘’Kauna(kanwa)
mu na ta ke kewan ki, tin ba ma Inna ba, yo kawo akwaitin na ki mu tahi ko?’’
Saboda murna Bintu kasa magana ta yi, sai kawai mik’a masa
akwaitin ta yi. Akwaitin ya d’auka, ya na ruke da hannun ta su ka wuce sashin
su na bayi. A hanya ya ke tambayar ya yaga idanun ta sun yi jajur haka? Ta ce da
shi idanun na ta ke ciwo shi ya sa. Ya ce da ita ta dai sha magani dai ko? Ya kara da Allah ya
sauwake.
'Bangaran su na bayi b’angare ne mai d’auke da sashi-sashi
na gidajen bayi. Gidan su Bintu wanda ya ke na uku cikin jerin gidajen bayi,
gida ne ginin k’asa, mai d’auke da d’akuna uku da falo, sai kuma d’akin dafa
abinci da kuma 6and'aki guda d’aya.
"Dakunan biyu a cikin falo su ke, na ukun kuma tsakar
gida ya ke kusa da dak’in girki, in da 6and'aki ke daga can gefe daf da soro.
Ba wani girma ne da tsakar gidan ba haka zalika d'akunan, idan ana zafi da kyar
su ke iya bacci, musammam yanayi irin wanda su ke ciki a yanzu, ruwa be sauka a
yankin ba. Falon na su kuma babu komai ciki daga daga ciminti sai tabarma.
A tsakar gida su ka tadda Inna ta na tankad’en hatsi,
kasancewar ta bababbariya baka ce wulik, doguwa ta na da dogon hanci, fuskar ta
d'auke da zane da fashin goshi irin na al’adar barebari. Duk da Bintu ba ta
kama da ita, akan ce tsayi da garin jikin Bintu na Inna ne, haka ma gashin kan
ta wanda idan ta ware ya na saukar mata har gadon baya.
Da gudun ta Bintu ta je ta rungume ta, Habibu na mai fad’in
‘’Gide ga autar ta ki na kawo mi ki Inna’’
Cike da farin ciki ita ma ta rungume d'iyar ta ta, fad’i ta
ke "Usoo am morantiye, wushe k3shero, is3maa?? Nda zawol?"(sannu yan
boko, sannu da zuwa, an dawo? Ya hanya?)
‘’Lahiya limi Alhamdulillah, mun same ku k’alau?’’ Cewar
Bintu. Inna na mai duban ta cikin nazari ta amsa da ‘’lahiya limi, Gide ya na
gan ki da idanu haka jajur?’’
Bintu na fara'a dan gudun kar Inna ta gane halin da ta ke
ciki, ta ce idanun ta ke ciwo. Ita ma sai a sannan ta lura da yanda Inna ta
rema ta lalace, d’aga idan da za ta yi ta kalli Habibu sai ta ga ashe gwara
Inna ma akan shi. Cike da alamar tambaya ta dawo da kallan ta ga Inna, kana ta
ce "lafiya kuwa Inna? Ya na gan ku a rame haka? Ina Baba?’’
"Ya na fada.’’ Amsar da Inna ta bata kenan a takaice.
Kana Bintu ta ce ‘’Yo to lafiya na ganku haka?’’
Inna ce ta amsa mata da "Yanzu dai ba lokacin tambaya
ba ne, Habibu maza k’arasa mata da kayan d’aka, sai ke kuma ki watsa ruwa ki ci
abinci ma yi maganar ko?’’
Cike da fargaba Bintu ta gyad’a mata kai kafin ta shige
d’akin ta wanda ya ke d’aya daga cikin na falon, Habibu biye da ita.
Shigar su ta bi d’akin na ta da kallo, d'an karamin d’aki ne
mai d’auke da gado na k’arfe mai (spring)na daidai kwanciyar mutum d’aya, sai
kuma wani k’atan buhu gefe in da Bintu ke aje kayan sawa. Ko tabarma babu a
d'akin, sai siminti da ya bi ya faffashe rugu rugu. Gefe guda Habibu ya aje
akwatin sannan ya fice ya bar Bintu ta na mai zubewa bisa gadan ta a gajiye.
Lalle kuwa kowa fa ya bar gida gida ya bar shi.
Daga waje ta jiyo Inna na fad’in ‘’Ki hito ki watsa ruwa fa ‘yar nan’’
Bintu ta amsa ‘’Gani nan hitowa(fitowa) Inna’’
Bayan Bintu ta ci abinci, ta watsa ruwa, Inna ta shiga ta
same ta kwance ta na hutawa. Ganin Inna ya sa ta tashi zaune, Inna na murmushi
ta ce "Gide na aza kwana ki ke(na zaci bacci ki ke)’’
Kai Bintu ta girgiza mata, cike da farin cikin yau ga ta da
Innarta, ta ce ‘’A falke na ke Inna (ido na biyu Inna)’’ Nan ta zauna kusa da
ita in da ta fara mata tambayoyi game da makaranta kamar dai yanda ta saba. Jin
Bintu ta ce komai lahiya lau, bai hana Inna fad’in ‘’Ki dai k’ara hakuri da
takwarar ta ki, na ce dai lafiya lau ku ke zaune ko?’’
Da har Bintu za ta fad’a mata halin da ake ciki, sai ta fasa
don kuwa ta san halin Inna da sa abu a rai, sai cewa ta yi ‘’Lahiya lumi.”
"Ngla zauro, Ala barraaz3( da kyau Allah ya yi
albarka)" Fadin Inna ta na mai dafa kan Bintu. Bintu ba ta gushe ba ta
yiwa Inna tambayar da ya tsaya cikin ranta, ta ce
‘’Inna me ke faruwa ne?’’ Kai Inna ta girgiza sannan ta ce
‘’Wannan annobar ta duk shekara ita ta sake bayyana Bintu.’’
Gaban Bintu ya fad’i ta na mai dafe k'irji ta ce
‘’Fari?’’(Annobar yunwa, sanadiyar k'arancin ruwan sama)
‘’Aradu ma kuwa, wanga ma ai tafi ta kowacce shekara,
talakawa mu na cikin wani hali, dussa ma da za a bawwa awaki gagaran mu yake,
hatsin da ki ka ga ina tankad’ewa na gidan sarki ne, Allah ya sa ya shigo ta
hannuna, na sami dussar ko ba komai ma sami na karin kumallo, na dare kuma ma
ci ragowar babban gida.’’ Cewar Inna.
‘’Innalillahi wainna ilaihi rajiun’’ Fad'in Bintu kenan
yayinda zufa ya shiga keto mata. Inna na mai girgiza kai ta ce ‘’Abunda mu ke
ta fad’a kenan ‘yar nan’’
kana Bintu ta ce ‘’Yo to Inna me zai hana mu nemi taimako
wajan sauran masarautar? Ai na ga ba laifi k’asar mu dai akwai abinci ga
taimakon juna’’
Inna ta ce ‘’Uhum ina ne ba a nema ba? Su ma ai sun gaji,
yau da gobe ya wuce gaban wasa ai, ridda karya kuka tatsa’’ Zuciyar Bintu d’aya
ta furta ‘’Fabarusa fa.....’’
Da sauri Inna ta doke bakinta, hannun Bintu bisa bakinta,
Inna na mai zare ido ta ce ‘’Kul ashirni zanne(rufa min asiri), shiga uku
takabar sarakuwa!(sirika) Kar ki sake ambatan yankin ga dan Allah, kin manta
bakar gabar da ke tsakanin mu, ahir ba da ni ba saka lallen kaza!’’
Ajiyar zuci Bintu ta saki tare da fad'in "Yo to Inna ai
dalili ne ke sa a kama kaluluwar sarakuwa...(Dalili ke sa a kama kaluluwar
sirika)"
Inna na girgiza kai ta ce "Na ce ki bar maganar ga
Bintu, ba na kwawarniya shiga rumbum k'ore."
Ta na mai jinjina kai ta bar maganar, fatanta Allah ya kawo
musu d'auki, Inna ta amsa mata da amin. Ranar har Bintu ta kwanta ba ta ga
dawowar mahaifinta ba, dama dai idan ana cikin fari har kwana ya kan yi can
fada.
***** ******
Washegari da sassafe, Bintu na bacci wata baiwa daga babban
gida ta yiwa Inna sallama. Inna da ta yi
zatan kiran na ta ne ta ce ‘’Allah sarki, hallau kun ji ni shiru ko?’’
Jin haka baiwa ta ce ‘’Gide kiran ga ba na ki ba Uwar bayi,
wannan kira na Bintu ne daga Gimbiya Binta’’
Kafin Inna ta bata amsa, mahaifin Bintu ya fito a fusace, in
da ya hau Inna da fad’a ‘’Yanzu ki na nuhin(nufin) wanga d’iya ta na nan ta na kwana(bacci) har
k’arfe bakwai na safe ba ki tashe ta ba tsabagen lalacewa! Yagana anya kuwa?’’
Cikin sanyin murya Inna ta furta ‘’Ayi hakuri na ga jiya ta
dawo shi ya sa...’’
‘’Yo to da hakurin ya mutu nawa ki ka biya kud’in sadaka?’’
Jin haka Inna ta ja bakinta ta yi shiru, ba ta ankara ba sai ganin Baba ta yi
ya shige d’akin, haka kuma be fasa fad’an da ya ke ba, har ya iske Bintu ta yi
d’ai-d’ai ta na baccin ta cikin kwanciyar hankali. Be yi la’akari da rabon da
ya sa ta a ido watanni uku kenan ba, ya rufe ta da fad’a da zagi. Ita kuwa
Bintu kamar a mafarki ta ke jin muryarsa, a hankali ta bud’e ido, ko da su ka
had’a ido cikin magagin bacci ta furta ‘’Baba?’’
A fusace ya yi mata dak’uwa ‘’Baban ubanki! Hegiya kin saki
la66a da su k'a66a ki na ta kwanan asara! Tashi maza ki wanke ido ki tahi
babban gida!"
Nan da nan Bintu ta wartsake, ta na mai raribar hijabinta,
ta ce ‘’Yi hakuri Baba, jiya na dawo ban ganka ba.....’
‘’Yo to ai gashi kin ganni, yar tselan uwa mai kama da
kuliya’’
Ko a jikin Bintu haka ta fito Baba na biye da ita, dan kuwa
idan da sabo ta saba, dan ba dan Baba shi ya haifeta ba da sai ta ce ya ma
tsane ta ne gaba d’aya. Har yanzu mita Baba ya ke, ita dai Inna d’auke kan ta
ta yi, ta shiga wasu sabgogin gaban ta. Baba ne ya ce da baiwa mai jiran Bintu
ta je ta ce ga Bintun nan ta tafe. Ta na fad’in ‘’Madallah’’ ta kama hanyar ta
tafi.
Buta Bintu ta d’auka ta kewaya bayi, da ta fito ta sa
dakakken gawayi da gishiri ta wanke hakoran ta, sannan ta wanke fuska. Baba da
ke tsaye gefe ya na jira ya ce ‘’Maza kama hanya ki yi gaba’’
‘’Malam na ce a bari ta yi karin kumallo ko?’’ Fad’in Inna
cike da nuna damuwa’
‘’Kayya! Wani kari kuma Gimbiya ta yi kira? Ke rabu da ita,
idan kin dawo kya yi karin, wuce ki tafi’’ Cyewar Baba.
Silifa ruwan d’orawa ta sanya a k’afar ta, har za ta fita
Inna ta ce ta tsaya su tafi tare. Amma Baba ya ce babu wannan maganar, karshen
ta ma ya yanke hukuncin raka Bintu da kan sa. Haka ya sa ta ta gaba, ya na biye
da ita, duk wanda su ka gani a hanya sai ta tsaya sun gaisa da Baba, a haka har
ya kai ta ga filin sukuwa, sanna ya juya
ya koma gida.
Tafiyar Baba ke da wuya Bintu ta hangi Yerima Nuhu tare da
tawagar sa bisa doki, ganin su ya sa Bintu d'aga k’afa ta na mai adduar Allah
Ya sa kar su cimma ta, amma ina Allah bai amsa addu'arta ba, domin kuwa ganinta
ya sa Yerima dukan bayan dokinsa da dorinar hannun sa a hankali, hakan ya sa
dokin k’ara sauri haka tawagar ta shi wanda ya kunshi abokan sa guda hud’u, nan
da nan sai ga su gaban Bintu su na mai tada k’ura yayinda su ke jan linzamin
dawakan dan su sami su tsaya.
Ganinsu gabanta nan da nan ta zube k’asa ta na mai fad’in
"Rangwame salamun, masu duniya ku na shagalinku, babban bijimi babban
Yerima, hadari malafar duniya, barka da siddi!’’
Yerima Nuhu wanda ya ke kyakkyawan saurayi, musammam idan ya
sha rawani da shiga irin ta saraki, ya tsinci kan shi ya na mai murmusawa,
yayin da abokansa su ka amsawa Bintu da ‘’An gaishe ki yarinya’’ Shi kuwa
kallonta ya ke cike da shauki, ya ce ‘’Mu na lahiya Bintu arziki?’’ Dama da
sunan da ya ke kiranta kenan.
Cike da nuna ladabi ta ce ‘’Lahiya lumi ran Yerima Nuhu ya
d’ade." Kai ya gyad’a kafin ya zunguri dokin shi yayi gaba, haka sauran
abokan na sa su ka rufa masa baya. Sai da ta tabbatar sun yi nisa sannan ta
tashi ta na mai ajiyar zuciya, ita dai har ga Allah ba ta san irin kallan da
Yerima ya ke mata ba tun yau ba, shiyasa ma duk inda ya ke ta ke gudun shi, ko
da yake k’awarta wacce su ke kira Cangwai ta ce ina ma ita yake yi wa haka da
sauran bayi ‘yan uwanta sun shiga uku da tak’ama. Da wannan tunanin Cangwai ta
fad’o mata, ta na mai tunanin ko me ya hana ta zo tun jiya ta ganta yanda ta
saba oho, bayan kiran Gimbiya za ta je ta duba ko lafiya, idan kuma sun had’u a
babban gida shikenan.
Cikin wannan tunanin ta k’arasa soran da zai sada ta da
cikin gidan sarki, wanda su ke kira babban gida. Ginin k’asa ne wanda aka gina
tin tale-tele mai cike da kayan ado na al'ada. Sauro shida ne reras, wanda
kowanne d’auke ya ke da shimfid’u da ado, biyu daga cikin su da d'akuna, wasu
kuma tsuntsaye ne fal ciki musammam jemagu su ka mamaye saman ginin. Haka Bintu
tai ta shiga ta na fita, wani ta tadda dogarai, wasu kuma bayi haka ta na
gaishe su har ta fito sarari, sai ga ta farfajiyar gidan sarki. Duk da shi
ginin bulo ne, amma komai na gidan tsarin al’ada da kuma tambarin sarauta ke
gare shi. Wato tsayawa fasalta irin kyawun gidan sai na cika shafi be k’are,
dan kuwa tsari dai na al’ada da sarauta gida ya tsaru.
Inna Salti Bintu ta fara cin karo da kasancewar 6angaran ta
ne na farko cikin jerin matan gidan. Ta fito daga 6angaran na ta kenan sanye cikin shiga ta alfarma, abin ku da
bafulatanar mace Allah ya bata kyau, gashi sam ba ta tsufa. hannun ta rik'e da
na Yerima Nadir, sai baiwar ta wacce ta ke biye da ita. Ganinta nan ma Bintu ta
zube domin d’ibar gaisuwa ta na mai fad’in ‘’Barka da safiya uwa ma ba da mama,
farar aniya alkhairin duniya, jikinki fari, tufar ki fara, zuciyarki fara wane
balbela.....’’
Murmushi ta saki ta na mai mamakin yanda karamar yarinya ta
iya zaro magana har haka, ko da yake zama da mad’aukin kanwa shi ke kawo farin
kai. Shi kuwa Yerima ganin Bintu tuni ya saki hannun Inna Salti ya na mai
fad’in ‘’Inna Salti Bintu ce!’’ Har da tsallansa sai gashi jikin Bintu ya na
mai rungumota. Ita ma Bintu dariya ta ke saboda farin cikin ganin Yerima Nadir.
Inna Salti kuwa kallansu ta ke, ta na mai mamakin wannan soyayya da ke tsakanin
Bintu da autan nata, dan kuwa duk cikin bayi babu wacce ya ke sakarwa fuska,
amma idan ka ganshi da Bintu ko ciki d’aya su ka fito sai haka. Cikin fara’a
Inna Salti ta ce ‘’Brkan ki dai Bintu, an dawo lahiya?”
‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e’’ Cewar Bintu.
‘’Toh ja66ama.’’
Yerima Nadir ya dubi Inna Sallati ya ce ‘’Inna Salti zan yi
wasa da Bintu’’
Inna Salti na mai murmushi ta ja hannun Yerima Nadir ’’Tunda
ka ga ta yi sammako haka, ko shakka babu aiki ke gare ta, ko Bintu?’’
Jin haka Bintu ta san me Inna Salti ta ke nufi, kana ta ce
‘’Dama Gimbiya Binta ce ta yi kira na."
‘’Ka ji ko Nadir? Didi ta yi kiranta’’ Cewar Inna Salti. Ba
dai haka ya so ba, amma be fasa tambayar ko anjima Bintu za ta yi wasa da shi
ba, in da ta amsa masa da eh, da haka su ka yi sallama, sai da ta tabbatar sun
wuce sannan ta tashi daga sunkuyen da ta yi, kai tsaye 6angaran su Gimbiya ta
nufa ta na mai fad’uwar gaba.
K’atan falo ne mai d’auke da ado irin na gidan sarauta, haka
kuma ya na d'auke da d’akuna biyu, kowanne da b’and’aki ciki, wanda na fari shi
ne na Gimbiya K’amariyya, sai kuma na Gimbiya Binta daga can 6angaran.
Bayi ne guda hud’u ke ta kai kawo. Kai tsaye d’akin Gimbiya
Binta ta nufa, ganin babu kowa bakin k’ofar d'akin ya sa Bintu kwankwasawa a
hankali. Sai da ta kai wajan minti goma tsaye bakin k’ofa sannan ta ji muryar
Gimbiya Binta ta na fad’in ‘’Gide wata maratarbiyar na samu a nan?’
Cikin rawar murya Bintu ta ce ‘’Ran gimbiya ya dad'e Bintu
ce....’’ Shiru sai bayan wasu d’an dakik’ai
ta sake furta ‘’D’iyar bayi ki ke kowa? Kya iya shigowa’’
A hankali ta murd’a hannun k’ofar, tuni wani ni’imantaccen
kamshi ya daki hancin Bintu, sa k’afarta, ta ji ya lume cikin lallausar
kafet(carpet), ga wani rab'a mai ratsa jiki da ya kama d'akin. Babu shakka
d’akin Gimbiya Binta yana da fasalin d’akin d’iyar turawa. Komai na d’akin fari
ne fat.
Lullu6e cikin bargo, idanu lumshe ta ce ‘’sai yanzu ki ga
damar zuwa?’’ kofar ta mayar ta rufe sannan ta zube k’asa ta na fad’in ‘’Tuba
na ke Gimbiya, barka da asuba.’’
Ba tare da ta bud’e idanunta ba ta yi nuni da d’an yatsa
zuwa akwatinan da aka jibge gefe guda, sannan ta ja bargo ta rufe fuskar ta. Ko
da ba ta yi magana ba, Bintu ta gane umarnin da aka ba ta. Dan haka tashi ta yi
ta na mai bin akwatinan da kallo, su goma sha biyu ne cif. Himma ta d'aura, ta
bi akwatinan d’aya bayan d'aya ta na fito da kayan ta na jera su cikin durowar
Gimbiya.
Wasa wasa aikin nan sai gashi ya d'auke ta awa d’aya. Ta na
kan akwati na k’arshe ne Gimbiya K'amariya ta shigo cikin shiga na alfarma.
Kallo d’aya za ka mata ka tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Gimbiya
K'amariyya fara ce kamar Gimbiya Binta, doguwa ce siririya, dan kuwa sam ba ta
garin jiki, ba ba'a ba, irin wannan matan ne da ake yiwa lak'ani da
"Muciya da zani" Tsabar rashin jiki. Ta na da kyawun fuska daidai
gwargwado dan har ta fi Gimbiya Binta.
Da sauri Bintu ta zube ta na mai fad’in ‘’barka da safiya
Gimbiya’’
Da fara’ar ta ta masa da ‘’Barka dai, kya iya cigaba da
aikinki’’
Bintu ta koma ga aikinta, inda Gimbiya K’amariyya ta zauna
gefan gadon Gimbiya Binta. A hankali Gimbiya Binta ta yaye bargon daga fuskarta
tana mai murmushi ga yar uwarta, ashe duk lokacin nan idanun ta biyu.
‘’A kwana a hantse sai d’iyar sarakai.’’ Cewar Gimbiya
K’amariyya tana mai dafa kafad’ar Gimbiya Binta. Tashi ta yi zaune kana ta ce
‘’Gidai ban fa gane wanga farin ciki na ki ba, hallo ana fama da fari gidai ki
na fama da farin ciki? me an surrin?(kin gan ki ban gane wannan farin ciki da
ki ke ciki ba, muna fama da fari ke ki na ta farin ciki? Menene sirrin?’)’
Kwanciya Gimbiya K’amariyya ta yi gami da runtse idanu,
sannan ta furta ‘’Barde ne’’
Cikin nuna rashin fahimta Gimbiya Binta ta maimata ‘’Barde
ne?’’
Idanunta ta bud’e ta na mai duban Gimbiya Binta ta ce
‘’Soyayya na ke da Yerima Barde na Fabarusa!’’
Wato ba Gimbiya Binta ba, hatta Bintu da ke can gefe sai da
ta tsaya cak ta na fidda idanu jin batun na Gimbiya K’amariyya cikin ran ta
tana mai maimaita ‘’Yerima Barde mai kyawun duniya? Kai ba k’aramin baiwa Allah
yayiwa Gimbiya K'amariyya ba’’
Cikin k’aguwa Gimbiya Binta ta ce "Didi ina ku ka
had’u? Takawa(sarki) ya sani? Da gaske kyawunshi ya wuce na kowa a duniya?’’
‘’Wanga tambayoyi haka kauna(kanwa) ta? Kimin d’aya bayan
d’aya’’
Kana Gimbiya Binta ta ce ‘’Toh, ina kuka had’u?’’
‘’A k’asa mai tsarki mu ka had’u, kin san mun je ki na
makaranta’’
‘’Ya san ke wacece kuwa?’’
Gimbiya K’amariyya na mai d’aga mata hannu ta ce ‘’Tsaya dai
ki ji komai, bayan had’uwar mu, jinin mu ya had’u, hallo mu ka kulla soyayya
mai k’arfi, kullum cikin waya mu ke ta sabuwar wayar tafi da gidanka da ya
shigo k’asar ga, mun yi alk’awarin amre(aure) da kuma kawo k’arshen gaba da ke
tsakanin masarautar nan ta mu guda biyu, hallo hakan ne ma ya sa Allah ya had’a
mu’’
Gaba d’aya Bintu ta manta da aikin da aka saka ta, ta saki
baki da hanci ta na jin lamarin ubangiji, ‘’Ashe dai da rabon za ta ga Yerima
Barde a rayuwarta’’ Farin cikin da ya mamaye ranta kenan. Kamar daga sama ta ji
an daka mata tsawa
‘’Yallah can (dalla can) makira fita ki ba mu wuri! Ki ga
yanda ta saki baki da hanci ta na jin mutane, wato ki sami wanda za ki d’auka
ki watsa rariya(waje) ko?’’
A firgice Bintu ta dawo cikin hayyacin ta ta na mai raba
idanu kamar 6era cikin tarko yayin da ta zube k’asa.
Gimbiya Binta bata gushe ba ta k’ara da ‘’Idan na ji wanga
magana ta hita rariya(idan na ji wannan maganar ta fita waje) sai dai uwar ki
ta haifi wata! Aradu ma kuwa!’’
‘’Lalle ma kuwa, yo to ai na manta tana nanniya’’ Cewar
K’amariyya ta na duban Bintu. Jikin Bintu na rawa ta ce ‘’Tuba na ke! Aradun
Allah na tuba, in na kara kada rabbi ya gafirce ni!’’
‘’Hita yallah(fita dallah) jaka kawai!’’ Gimbiya Binta ta
daka mata tsawa. Tuni Bintu ta tashi jiki na rawa ta fita.
Bayan fitarta Gimbiya Binta ta ce "Wai har wanga d’iyar
bayin ni za ta yiwa alherin maye ramuwa da mugunta? Har ta isa had’a
samrayi(saurayi) da ni?’’
Baki bud’e Gimbiya K'amariyya ta ce ‘’Kwarainiya mota a randa! Shi ko
wanene wanga samrayi?’’
Gimbya Binta na mai murmushi ta ce ‘’Aisar Gaddafi
Nur."
Cike da mamaki Gimbiya K'amariyya ta ce ‘’Kai haba dan
Allah, Aisar dan shugaban k'asa gide?"
Gimbiya Binta ta gyad'a mata kai.
"Yo to in ban da abun ki ina tusa zata hure wuta? Ina
d’iyar bayi ina dan mulki? Ai komai tsiyar 6arawo ya bar wuta a murhu’’ Cewar
Gimbiya K'amariyya.
Please help me with cigaban bintu diyar bayi ce
ReplyDelete