Alia ce zaune a falo tana cin abinci , sadiq yayi sallama ya shigo ta amsa sallamarsa tare da mai sannu da zuwa sannan ta cigaba da cin abincinta,zama yayi a gefenta sannan yace "Abba fa? batareda ta dago ta kallesa ba tace yana ciki tana rufe bakinta Abba ya fito yana ganin Sadiq yace "hr ka shirya? Eh ya amsa mai, yace toh ai sai mu wuce,tashi Sadiq yayi suka fice.
Suna fita Alia itama ta tashi ta shige ciki ta sako hijabinta ta dauki key ta fice. Ba ita ta dawo gidan ba sai wajajen magrib ta tarar da su Abba a falo sunyi jugum,suna ganinta suka taso Abba yace " daga ina kike? Cikin i'i'na tace TH naje nayi submitting internship application Abba tunda mukazo nake ganinsa a daki n i hv bn wondering y bnyi submitting ba,ajiyar zucia iyayen nata sukayi sannan suka koma suka zauna,waya Abba ya cire ya kira Sadiq yana dagawa yace ka dawo gida gata ta dawo,bai jima da aje wayan ba Sadiq ya shigo kallo daya ya mata ya kauda kai ya miko wa Abba key yace Abba bari inje inyi sallah Abba yace bari mu fita tare sannan suka fice. Ummanta ta dubeta tace Sam Alia baki kyauta ba kuma bnga laifinki ba dauke miki kafa da muke shi ya jawo hakan amma Abbanki zai shigo zan mai magana zamanku gidan nan ya isa haka ai ynxu kin warware tunda hr munfi wata da dawowa ku koma can gidanku dan na gaji da halinki,jibi yanda yaron nan ke dawainiya da ke da mu duka amma sam baki tausayinsa baki ma basa darajarsa a matsayinsa na mijinki hr zaki sa kafa ki fice bada izininsa ba toh ki sani ynxu ba krkashinmu kike ba ko da na baki izinin fita shi bai yarda ba toh umarninsa zaki bi dan yafi mu hakki a kanki in kuma rayuwar da kika zabawa knki kenan sai kije kiyita yi kiyita jawa kanki fushin Allah,haka kawai dan kinga yaro bai magana kiyita cutarsa,tana gama fadin haka ta juya tayi shigewarta dakinta,Alia kuwa cikin sanyin jiki ta shige dakinta,da yake tana fashin sallah ta haye gado tana nazarin maganganun umma,toh mai ma wannan bawan Allah ya mata da bazata iya sawa zuciyarta yarda da shi hr ta so shi ba tunda iyayenta sun yadda da shi ko don farin cikin iyayenta zata sawa zuciyanta sonsa kuma ta zauna da shi ko dan dawainiya da yayi da ita. Tana jin shigowar Abba hr ya hau sama sannan ta fito sanye da mayafi ta wuce dakin Sadiq,ta jima a tsaye tana sallama jin shiru ya sa ta murda kofan ta shiga ta ga dakin ba kowa hr ta juya zata fice ta hango wayarta da ya bata a asibiti ta dawo ta dauka ta bude,hoton da sukayi tym da sukaje gun su Hamida ne jikin screen in ta jima tana kallo sunyi bala'in kyau amma ta kasa tuna yaushe aka dauka,haka tayita bi tana kallon hotunan wanda yawanci a garden na gidan sukayi,fita tayi ta shiga watsapp ta bude kan chat nasu ta fara karantawa,jin an bude kofan yasa ta saurin boye wayan a bayanta,yayi mamakin ganinta a dakinsa ya karaso ya zauna batareda ya ce mata komai ba itama ta nemi waje ta zauna,shiru sukayi duka sannan tayi gyaran murya tace "dama naxo in baka hakurine a bisa fita da nayi batareda neman iziniba insha Allah hakan bazai sake faruwa murmushi ya mata yace bakomai anytime kikeson fita kuma bana nan zaki iya tafia muddun zaki tsaremun knki which i trust u can,itama murmushin ta mai sannan tace nagode tareda mikewa sai da ta isa kofa ta juyo tace mai sai da safe ta fice hannunta rike da Wayan.
Tana fita ya fada toilet yayi wanka yayi shirin kwanciya sannan ya haye gado,hannu ya mika dan daukan wayarta a ma'ajiyarsa ya ga wayam wayarsa ya dauka ya fara dialing layinta ita kuwa lokacin tayi nisa wajen karanta chat nasu taga kol nasa ya shigo,kaman bazata daga ba kawai ta daga tareda karawa a kunne amma batayi magana ba,shima a bangarensa shiru yayi,sai da suka jima a haka sannan ya mata sallama,can kasa ta amsa mai,yace dama na kira dn bnga wayan bane tunda yana wajenki sai da safe sannan suka aje wayan,kunna data yayi ya ganta online amma bai mata magana ba ita kuwa tayi nisa wajen karanta chat nasu wasu su kashe mata jiki wasu su sata daria,a haka hr bacci ya dauketa. Sadiq kuwa hr ya sauka yaga tana online yayi tunanin ko bacci tayi shima ya kashe wayarsa ya kwanta.
Karfe bakwai na safe ta fito cikin shiri ta tarar da su akan dining itama ta karasa ta zauna tareda gaishesu sannan ta ja plate ta zuba abincinta ta fara ci a hnkali hr suka gama suka koma falo suka brta ita kadai,ta gama itama ta dawo falon,gefen Abbanta ta zauna daga ganinta yasan da magana yace "ya akayi Darling Daughter? Tace dama Abba zncen internship ina inne inaso yau in fara zuwa, shiru yayi sannan yace " DD ni banda say a wannan al'amarin illa na kira asibitin na shaida musu changes da aka samu amma zncen zuwa ba a gidan nan ba in kun koma can gidanku sai ki ma mijinki magana in ya yadda toh sai ki fara zuwa dama munyi da ummarku gobe zaku koma amma ynxu na cnza ra'ayi anjima da daddare sai mijinki ya daukeki ku je abunku ba wanda ma zai raka ku tunda shi sadiq in yasan gidan,komai da zaku bukata akwai a can sai dai kayanki ki shiga ynxu ummanki ta tayaki ki fara hadawa zuwa anjima, tashi tayi ta shige dakinta ta fara shirya kayanta dan ta kagu ta fara zuwa aikinta,bata jimaba ta gama hadawa.
Wajen taran dare Sadiq ya jasu zuwa sabon gidansu bayan Abba da umma sun musu nasiha sosai. Hanyan polo suka nufa,daidai wani milk flat ya tsaya yayi horn mai gadi ya bude suka shige, parking lot ya karasa yayi prkn sannan suka sauko ya tayata daukan akwatinta. Hr dakinta ya kaimata sannan ya sa kai zai fice,tayi gyaran murya tace gobe inaso in fara fita aiki in ka amince,Allah ya kaimu ya bata ansa sannan ya ida fita,toilet ta fada tayi wanka sannan ta fito tayi shirin kwanciya tabi lafiyar gado. Ba ita ta farka ba sai wajajen shida tayi sauri tayi wanka ta shirya cikin eng wear riga da skirt ta yi rolling da karamin gyale sannan ta dauki wani babba ta yafa a kafadarta ta fito falo rikeda jakarta da labcoat a hannunta ta wuce kitchen dan shan tea,kunya ne ya lullubeta ganinsa a kitchen yana soya doya ita sam ta mnta da wani breakfast ma,cikin jin kunya ta gaishesa ya amsa mata tareda da tambayanta darenta,cup ta dauka ta fara hada tea ta koma falo ta zauna tana shan abunta, gani tayi ya fito ya aje mata plate a gabanta shima ya ja kujera ya zauna kasa dagowa tayi dan wani kunyansa da take ji, ji tayi yace ki ci mana, ba tare da ta dago batace am k, yace ashe kuwa baki shirya tafia ba dan sai kin cinye kap zamu fita dan ni zan na kaiki in daukoki,idonta ne ya kawo kwalla dan hr ga Allah bazata iya cinye abincin da ya sa mata ba,shi kuwa ya wuce dakin dan shiryawa yana dariyan mugunta dan ya santa da rashin cin abinci ,har ya fito bata wani ci abin kirki ba ya dubeta ta tsurawa plate in ido tayi kalan tausayi,murmushi yayi ya karaso ya sa hannu ya dauki plate in ya kai kitchen,tashi tayi itama ta bi bayansa ta dauraye cup in da ta sha tea aciki sannan suka fice. Bakwai da rabi daidai suka shiga TH ya nemi waje yayi parking sannan ta bude ta sa kafanta zata sauka,a hnkali ta juyo tace pls kr kayi abinci znyi kokari in tashi da wuri in dawo inyi,murmushi kawai ya mata sannan yace kol me in kin tashi sannan ta shige.
Sauri sauri take ta je tayi reporting dan ta dan makara,wayantane ya fara kara ta fara kici kicin cirewa a jaka yayinda take tafia,ji tayi tayi karo da mutum file na hannunta duk ya tarwatse ta sunkuya ta fara tattarawa yayinda ta ke bawa mutumin hakuri,shima sunkuyawa yayi yana tayata sannan suka dago tace am very sorry wlhy saurine nake first day as an intern n i dnt wanna gv a wrong impression sai sannan Dr Grema yaga fuskanta wanda ya sa numfashinsa ya kusa daukewa itama tunani ta fara tana son tuno inda taga fuskarsa amma ta kasa,shi kuwa mamakinta yake hr ta mai sallama ya sake tsayar da ita yace ur nem pls Alia ta bashi amsa batareda ta tsaya ba,ya bi bayanta da ido yana mamakin changawarta,ji yayi an dafasa Ya juyo yaga abokinsa Dr Aliyune yace "Memory loss, Dr Grema ya yi saurin gane me yake nufi,Dr Aliyu ya cigaba da cewa jiya bayan ka tafi Dad nata yaxo yayi reportn n guess what, ward da matarka take can aka turata lets hope she dnt remember her too,ya dan bugi kafadarsa sannan ya wuce jimawa yayi a tsaye sannan ya wuce ya shiga office nashi.
Alia kuwa tana isa aka nuna mata office nata ta shiga ta sa labcoat nata sannan ta fito ta jona rounds, kan wani yaro suka zo dan kimanin shekara daya Dr Usman da suke bi ya juyo ya ce ina Dr Alia? " am here sir ta bashi amsa, karanta mata case na yaron yayi sannan yace any idea wt his diagnosis myt b shiru tayi na yan wasu dakikai sannan tace,Cystic Fibrosis ta bashi ansa, Excellent, inji Dr Usman sannan ya fara musu lectures akan yaron da inka gnsa kasan yana jin jiki,Dr usman yace wr is mrs Grema nasha gaya mata ta daina barin yaron nan shi kadai bai gama rufe bakinsa ba Hamida tazo hannunta dauke da buta tana ganin Alia butan hannun nata ya fadi daga hannunta tayi sa'a ba ruwa a ciki gaisheta duk suka yi sannan Dr usman ya nuno Alia yace nasan itace baki santa ba shs our new Dr one of our finest during her skul hia kuma ita zan sa a kan case na yaronki cos an bn labari shs gud wn it cums to paediatrics da itama zamu yi wa danki aiki b4 dn komai naku ynxu ita zakina consulting, kai kawai ta gyada mai sannan Suka wuce kn wani patient. Alia bata samu zama ba sai wajen sha biyu ta zauna a nurses station tana rubuta report, Dr Grema ne ya shigo ward in ya xo ya tsaya a gefenta yace Sannu da aiki Dr Alia dagowa tayi ta mai murmushi sannan tace yauwa Dr.........Grema ya bata amsa,ya ce hws ur first day as an intern? Grt ta bashi ansa tareda tashiwa tace kaima a nan kake,nop ya bata ansa i hv a pt hia sannan suka shige ciki duka kan gadon su Hamida ta tsaya wanda tunda ta hngosu suna zuwa zuciyanta ya hau bugawa, sannu shine abunda Alia tace mata sannan ta ja bedhd tickt nasu ta sa wani paper a ciki,gani tayi Dr Grema ya zauna yana wasa da yaron tace patient inka knan kai ya gyada mata, tace "Dr Usman has assigned me to him n am super excited dan yace i wil b prt of his surgery murmushi ya mata sannan suka fara discussion, Hamida kuwa ta cika tayi fam,wani tsaki ta ja wnda ya sasu juyowa taga sai harara take watso mata,sallama ta mai ta wuce office nata,karasowa tayi tace Dr Grema dnt try me wlhy kr kasa in tara ma jama'a a asibitin nan da har zaku zo kuna cin fuskana ita kuwa hrda nunawa kamar bata sanni ba,shiru ya mata sannan ya tashi ya ce ai ba yau kika fara ba kuma na saba da wannan halin naki kuma ko da wasa kika tunkari Alia sai na mugun bata miki,kuma inma ta nuna halin ko in kula a gareki bnga laifinta ba n FYI ta samu memory loss due to wat u n i did she neither remembers u nor me so dealt wt dt n lt her b but muddin kika ce zaki tada mata hankali wlhy a bakin aurenki dan tafiki matsayi a guna,hrynxu itace gabana itace a raina in kuma kinaso ki gwada kuma toh ya sa kai ya brta tsaye wajen cike da mamaki.
Alia kuwa na zuwa bakin office nata ta ci karo da flower a aje a kofanta da wani card ta dauka tareda shiga office in,ajewa tayi akan table nata tareda zama sannan ta bude card in,hapi first day at work shi ta gani,murmushi tayi sannan ta rufe ta ja wayanta dan duk a tunaninta shi ya aje mata ta kuwa ga message nasa yana tambayata ya aiki,kiransa tayi ta gode mai sannan tace mai ta zai iya zuwa ya dauketa sannan suka aje wayan.
Galleryn wayanta ta shiga dan tana gani kaman ta ga Dr Grema da matarsa a ciki sai kuma ta nemi pic in ta rasa,hakan ya sa ta aje wayan ta fara shiri
Yana isa ya ciro wayarsa ya kirata bai jimaba ta fito tana kulle office nata,tana juyowa taga Dr Grema tsaye yana kallonta,ta dan raxana amma ta dake,ya tako zuwa gabanta yace "unless i forgt tym na tashi is four,murmushi tayi tace " na krbi excuse for today dan akwai abunda znyi a gida yace "muje toh in rakaki, a'a lt me nt tk u away frm ur work ta amsa mai, yace " dama brk zani so u aint tkn me away frm wrk, suka jero suna tafia hr suka fito waje tana hango Sadiq ta dubesa ta ce "bari in karasa dts ma husband ova dia,ya kai kallonsa inda ta nuna yayi saurin ganesa take yanayinsa ya canza,miko mata file nata yayi yace "see u tmrw na danyi mantuwa zan koma ciki bai ma jira amsarta ba ya koma, ta tako a hankali zuwa inda Sadiq yake tsaye yana jiranta yayi kyau cikin kananan kaya,wasu yan mata da ke wucewa sai kallonsa suke,murmushi tayi dan ta san mijin nata mai kyau ne dole mata suyita kallonsa kai kace wani balarabe ne, sallama ta mai da ta karaso ya juyo ya amsa tareda mata murmushi sannan ya bude mata mota ta shiga shima ya zagaya ya shige suka br asibitin.
Suna isa ta cire kayanta ta sa na shan iska ta wuce kitchen ta hau aiki,cuscus tayi da sauce in kayan ciki ta dan hada musu coconut drink ta jera a plate ta juyo dan kaiwa parlor ta gansa tsaye bakin kitchen yana kallonta da alama ya jima tsaye a wajen,kunyan kayan da ke jikinta ya kamata,ya karaso ya krbi plate in dake hannunta yace" lt me hlp u ya fice tana biye da shi,kan carpet ya aje musu ya tashi ya kunna TV, ya dawo ya zauna,ta ja plate biyu zata zuba abincin ya dubeta yace "ai plate daya ya ishemu ko kinfi so ki ci ke daya,batareda ta amsa ba ta mayarda daya plate in, bayan sun gama cin abincin tare sukayi wanke wanke Sannan suka dawo falo suka cigaba da kallo, Canza station in yayi zuwa MBC2 inda suke wani horror spectral,Alia sarauniyan tsoro sai gata rabe jikinsa intaga kaman wani abun zai faru sai ta shige jikinsa kafun a gama film in kusan ta gama haye wa jikinsa wanda hakan ya sauke masa wani kasala,ana gama film ta sauke ajiyar zuci sai sannan ta lura da ynda ta wani kanainayesa ta dan gyara zamanta tareda jnye jikinta krshe ma tashi tayi ta shige dakinta yayinda shikuwa ya kwanta tareda rufe idonsa yana tunanin sensation da yaji lokacinda fatarta mai laushi ya gogi nasa. Ba ita ta fito ba sai bayan la'asar ganin baya falon ya sata shigewa kitchen ta musu dinner ta juye a flask sannan ta koma ciki dan yin wani aiki, Tana duba abu a laptop nata ta ji shigowarsa falon ta rufe itama ta fito ta samesa zaune yana kallo ta wuce kitchen ta dauko musu abinci ta zo tayi serving suna gama ci ta mai sai da safe ta shige dakinta dan gama abunda ta fara ba ita ta rufe laptop in ba sai wajen sha daya ta ja bargo ta kwanta tareda kashe swtch na wuta da ke gefenta, tana rufe idonta horror film da ta kalla ya fado mata rai ta tashi da sauri tareda bude idonta a hnkali sai taga kaman tana ganinsu kunna wutan dakin tayi sannan ta sake kwanciya amma dukda haka tsoro bai brta ba, kaman ance kalli sama taga wani spider na saukowa ta gefen gadonta ta saki wani ihu tayi bakin kofanta, spider kuwa da iyayi ya tsaya daidai kan gadon yaki tafia gashi ba iya kasheshi zatayi ba dan in akwai abunda Alia ke tsoro toh spider ne,bude kofarta tayi ko mayafi bata dauka ba dan ji take in ta koma zai hau jikinta,dakin Sadiq ta wuce ta samu hr yayi bacci itama ta haye gadon dan gefe da shi ta kwanta,tana kwanciya aka dauke wuta ta mirgino ta kankamesa ta wani shiga jikinsa dan tsoro,shi kuwa bai ma san tanayi ba dan yayi nisa,a haka bacci ya dauketa. Kiran sallahne ya tasheta ta bude idonta a hankali tareda yin addu'an tashi ta gnta a jikinsa,dagowa tayi taga idonsa abude yana kallonta tayi saurin rufe idonta dan wani kunya taji,a hankali ta fara sauka daga kan gadon ta juya mai baya sannan ta ce sorry na takuraka ko i cldnt slip in ma room dts y, murmushi yayi ya sauko shima yace "shine ni kika zo kika hanani bacci while ke kinyi kayanki pisfully nxt tym bake ba kallon horror dan i dnt slip wt ppl who snore,dagowa tayi suka hada ido sannan ta sunkuyar da kanta tace" i dnt snore fa, yace" ai ni bntaba jin mai munshari irin naki ba tunda kika shigo ko runtsawa banyi ba, cikin yanayi na nuna damuwa tace "dagaske i snore kuma na hanaka bacci, gani tayi yana guntse dariyarsa ta dan bata rai tace dts nt funny Ya sadiq, kaga ynda ka tada mun hankali kuwa,toilet ya shige yana daria itama dariyan tayi dan ta gane tsokanarta kawai yake ya fito yace ni natafi masallaci tace dan Allah ya Sadiq muje ka daukan hijabina tautau a dakina,saninta da tsoron abun ya sa yace zauna in dauko miki,tace " da kayana da labcoat ina pls, yace "wani iri zan dauko miki? Kowanne ta bashi ansa sannan ya fice dan dauko mata kafun ya dawo hrtayi alwala itama ya mika mata kayan ya wuce masallaci,tana idar da sallah ta wuce kitchen ta hada sandwich ta dawo tayi wanka. Tana sa kayanta ya shigo tayi saurin rufe kirjinta,fita yayi dan ta gama shiryawa ya koma falo yayi zamansa,ta fito cikin shiri batareda ta kallesa ba tace brkfst is ready dan duk ynxu kunyarsa take,tare sukayi breakfast sannan ya kaita wajen aikinta. Tana isa bakin office nata yau ma taga flower da card,a zuciyanta tace yau kuwa wa ya kawo mun it cnt b Sadiq dan in shine yaushe hr ya fito ya aje mata dan he was home tru out kuma bazata ce da safe yazo ya aje ba cos tare suka zo,tabe baki tayi ta bude office nata ta aje flower da card in ta wuce ward dan gaida patients, wajensu hamida taje last dan su a vip suke, ta gaidata ta amsa ba yabo babu fallasa tana mamakin mesa wannan mata ke mata haka,hannu ta sa ta dauki yaron tana mai wasa tana dan duddubashi shi kuwa sai wasa da stethoscope in wuyanta yake ta zo ajesa ya wani kankameta wai sam bazai sauka ba daria tayi tace yi hakuri mukarram in nagama aiki zan dawo sai muje yawo yaro kam yaki fir Hamida kuwa ta cika kaman zata fashe jin Muryan Dr Grema sukayi a bayansu yana ganinta ya sakar mata murmushi wanda ya sa idon Hamida ya dan ciko da hawaye,yaron ya fara mika mai hannu ya sa hannu ya karbesa yana yaron daddy ykk,sai san Alia ta gane mijintane no wonder taga taketa kumbure kumbure murmushi tayi a zuciyanta tace mata dama kin kwantar da hnkalinki dan miji gareni, juyawa tayi zata tafi mukarram ya pasa ihu yana miko mata hannu juyowa tayi dan tasan dan ita yake wannan ihun ta tako ta sa hannu zata karbesa Dr Grema yace Dr Alia yau kinyi yaro murmushi tayi dan itama yaron ya kwanta mata a rai, Hamida ce ta zo ta krbe yaron cikin zafin nama tace zn basa nono kuma wanka zaiyi sannan ta juya ta zauna ko kallonsu bata sake yi ba,abun ya ma Alia ciwo sosai a zuciyanta tace dole ta tunkareta suyi magana dan bazata yadda da hakan ba imna tana ganin kwace mata miji zatayi zata fito ta gaya mata itama matan aurece ta dubi Dr Grema tace bari in wuce ni yace ok lt me c u to ur office dn we dscuss abt ma son, Hamida tace "Baban Mukarram inada magana, yace " i guess it can wait, no it cant ta bashi ansa,sanin in ya biye mata bazasu kare da kyau ba ya sa ya ce da Alia zai sameta inya gama ta juya a zuciyanta tana dariyar halin Hamida, zata so taga mijinta dan ta nuna mata ba abunda zai sa taso mijinta ita da ke da kyakkyawan miji son kowa kin wanda ya rasa meh zatayi da mijinta da wannan tunani ta shige office nata. Wajen karfe sha biyu ta kira mijin nata ta shaida mai tayi stew tun jiya da dare yana freezer akwai kuma rice a cooler sai yayi warming godia ya mata sannan yace dnt forgt to kol me in kin tashi.
Yau ma dakinsa ta kwana dan tace sai ya kashe spider zata koma krshe ma sashi tayi ya kwaso mata kayanta ta dawo dakinsa gaba daya shikuwa dukda ya kashe yace bai gani ba dan baiso ta koma dakinta dan ko ba komai tana rage mai zafi.
A yan kwanakinnan sunyi wani mugun shakuwa in ka gansu gwanin sha'awa kai kace tunda can masoyane.
Yau da taje office tayi mamaki bata ga flowern da aka saba aje mata ba, ba ta sa abun a rai ba ta wuce ciki dan duba pt nata ta gama ta dawo office nata ta ga flowern dagawa tayi ta duba ko zata ga wanda ya aje amma bataga kowaba fita tayi ta tambayi security tace pls wa ya fita daga nan ynxun nan,yace mai kawoki kullum innan shine ya fita ynxu murmushi tayi ta koma ciki flowern manne a hancinta tana shakar kamshinsa, Dr Grema da ke labe kuwa wani murna yaji ganin taji dadin flowern da ke aje mata baisan ita ta dauka mijinta ne ke ajewa ba, tana shiga ta dau waya ta kirasa tace "ance ka shigo ynxu,yace " eh but naga bakya office kuma bnso in katse miki aiki dama nazo wucewa ne nace bari in dan dubaki, tace nagode sosai for everything sannan suka aje wayan, card in ta bude wanda ya kunshi kalamai na soyayya,lumshe idonta tayi yayinda take jin wani sabon yanayi gameda mijinta na ratsata,ynxu ta yadda tanason mijin nata kila dama can suna soyyayarsu kafun ta mnta komai ganin komai da takeso ya sani kuma yana kokarin yi dan ya faranta mata, ranan cikin farin ciki ta yini. Yau da ta tashi ta kira wayansa a kashe kawai ta fito dan taran napep,Dr Grema ne yayi parking yace ta shiga su tafi ta so kin shiga amma ganin ya nace ya sa ta shiga,suna isa kofar gidansu lokacin kuwa Sadiq ya fito zashi daukanta, tace ga mijina ka sauko ku gaisa krfin hali yayi ya sauko suka gaisa Sadiq kuwa ya amsa mai cikin sakin fuska sannan suka shige ciki. Bayan ta canza kaya ta ci abinci ta zauna a falo shima ya shigo ya zauna a gefenta ta mai sannu da shigowa ya amsa cn ciki ya maida hnkalinsa kan TV, can ya dubeta yace waye ya kawoki dazu, tace "Dr Grema sunansa kuma ni Dr yaronsane na kira wayanka a kashe shine ya rage mun hanya, " toh daga yau ban yadda ki sake shiga motarsa ko na wani ba in baki sameni ba ki hau mota kawai ki dawo, toh ta bashi ansa sannan ya tashi ya shige ciki ransa na tafasa dan yanda ya gnta da Dr Grema hr wani daria take ko mai ya gaya mata oho, tun daga ranan ya daina sake mata sosai ko abinci ma sun daina ci tare gashi a kan gado ma ya kaurace mata gashi ita ta saba da kwanciya a jikinsa, tun abun baya damunta ya fara damunta sai dai taki masa magana. Tana kwance a kan gado ya shigo bai bi ta knta ba ya hau can nesa da ita ya kwanta, a hankali ya fara jin sheshekar kukanta ya juyo zuwa inda take ya rungumeta shi kansa ya san bai kyauta ba amma zafin kishi ya rufe mai ido dago fuskarta yayi ya hada bakinsa da nata ita kuwa bata yi yunkurin hanasa ba ganin haka ya sashi zarcewa dama hakurinsa ya gaza a daren ranan ya maida Alia Mace. Da safe da ta tashi duk kunyarsa ya gama lullubeta,shi ya taimaka mata tayi wanka ya tayata shiryawa duk yanda yaso hanata fita taki ta zauna tace zata duba mukarram inta sai ta krbi excuse ta dawo,tare suka fita ya jira ta gama suka komo gida tare. Ranan shi da kansa ya shiga kitchen yana shirya musu abinci, ummace tayi sallama ta shigo ta tashi ta ma mnta bata jin dadi ta haye kan umman nata, "tace ni cikani yarinya sam baki girma,dariya tayi tace" umma dazu ya Sadiq ke cewa gobe zamuje dubaku sai gashi kinzo, tace "nima na zo gaisuwane shine nace bara inzo in dubaku, ina sadiqun? cikin jin kunya tace yana kicin, harara ummanta ta watso mata tace shine kuma kike zaune a nan, kan ta kara bude baki ya shigo hannunsa daukeda ruwa dan duk yana jinsu yace "sannu da zuwa umma, sannu Sadiq ta amsa mai sannan tace " mai kuma ya hadaka da kitchen dan nan mesa ita bazata shiga ba, yana dan murmushi yana sosa keya yace bata jin dadi umma, tabe baki tayi tace " kai dai daure wa krya gindi mutumin da ya kusa kryani ka wani ce batada lafia,kwa dai ji da shi, bata jimaba ta musu sallama ta tafi.
Yau da wuri ta isa asibiti dan ance mata jikin mukarram ya tashi ko breakfast ta kasa zama tayi,tana shawo kwanan office taga Dr Grema na aje flower da card,mamaki ne ya cikata dama shine ke aje mata su,sai da ta ga ya bar wajen ta karaso ta dauki flowern tareda bude office nata ta zauna tana nazari,ol ds while ta dau mijinta ke aje mata ashe shine toh mesa zai yi hakan ba yan yasan tanada miji kuma hw did he knw irin flowers da take so,ganin bata da ansan tambayoyin nan ya sata tashi dan zuwa duba dansa, bata gaishe da Hamida ba dan ko tayi bata ansawa ta hau duba makarram da duk ya fita hayyacinsa ganin abun zaifi krfinta yasa ta kira Dr Usman suka hadu duka suka basa kula na gaggawa hr ya samu yayi stable, kuka hamida ke yi hr suka gama sannan ta dubi Dr Usman ta mai godia, Alia kuwa ko a jikinta ta br wajen, minti minti take zuwa ta dubashi zuwanta na hudu ta tarar da Dr Grema zaune da iyalan nasa Sannu kawai ta musu sannan ta dan shafi kan mukarram ta sake duba vitals nashi ta dubi Grema tace "ina son ganinka pls, Hamida ce ta taso tace "Dr Alia inaga zuba miki ido nake yi ina shiru shi yake baki daman shiga gonata, koh me zaki fada ki fada a gabana ina jinki amma ki daina bibiyanmu miji, is it so hard to find anoda man da bazaki hakura da shi ki nemi wani ba, daga yau bana son ganinki kusa da mijina ko dana we'll ask Dr Usman to assign sum1 to his case amma bn son family breaker kusa dani dan naga gaba daya ba uban kadai kike hari ba hr da dan nawa kuma bari in shaida miki i cn go evry length to protect n kip wts rytfully mine so dnt push me Alia for if u do i wl mk sure u dnt eva regain ur memory, idonta ne ya cicciko da hawaye ta juya ta ga mutane sun taru a kofan dakin,she hs nva bn humiliated lyk ds before ta fice tana hawaye yayinda Dr Grema ya bi bayanta, a corridor ta durkushe tana kuka a hankali Dr Grema ya sunkuya yana bata hakuri, mamakinta dayane ta ya Hamida ta san tanada memory loss,ina ta santa, dafata yayi tayi saurin jnye jikinta tace " duk abunda ya faru kai ka jawo mun, i knw ov d flower,i saw u kip it today,kuma am sure kasan ni matar aurece,i dnt blame ur wife for wat she did dan duk kai ka jawo so pls stay away frm me, I cnt Alia ya bata amsa, u r my lyf Alia bazan iya rayuwa babu ke ba cikin mamaki take kallonsa ya cigaba da cewa "Alia dnt lt ma one mstk ya rabamu nine masoyinki na asali i knw u dnt remember n its crazy but am ur true love Alia pls kar ki hanamun kanki in kika kini zan shiga wani hali, juyawa tayi dan ta bar wajen dan gaba daya ya rikita mata kwakwalwa tana juyowa suka hada ido da Sadiq, yanayin da ta gansa ya tabbatarmata yaji komai ya juya ya bar wajen ta bi bayansa da wuri hr ya kusa kofa ta kamo hannunsa ta ce pls ka tsaya its not wat u tink, cikin bacin rai yace "i told u to stay away from him ashe baki jini ba, ol ds while i ws tinkn kin fara sona ashe ni kadai ke haukana, hw can u still love him after wat he did to u, cikin kuka tace i dnt knw wat u r tlkn abt kuma ni wlhy ba sonsa nake ba kai zuciyata ke so, murmushi yayi mai dauke da ciwo yace Alia u dnt love me ur hrt is always wt him dts y u choose to hide wat he did for u dan ki cigaba da sonshi, cikin daga murya tace u r confusing me! Yace " u r d one confusing tins Alia, u r d one hiding from the truth bcs u r afraid of it, afraid u wil luz d ppl u luv ppl who dnt gv a damn abt u n its not dt u dnt remember u chuz not to remember it bcs u stil luv dem despite wat dey did to you bt u hv to remember so st us both free tunda ya fara magana taji kanta na juyawa gani yayi zata fadi yayi sauri ya tarota ta fadi a jikinsa Sumammiya
0 comments:
Post a Comment