_a sanadinki yau har asibiti nazo gwaji_
_wannan wane irin
iskanci ne zaki zauna a falo a haka?_
_ka manta ni yar
iskar ce in ya taya ai sena bada kai bori ya hau ko_
_yana nan tafe_
Kwalliya taci sossai ta sha ado tayi kyau ta zauna zamam
jiran sa.sanda ya dawo ya sameta a falo tana kallo yaji dadin ganin ta a haka
daga jiya zuwa yau yayi kewarta da babyn shi ya dauke kai ita kuma tayi
murmushi ta mike tsaye seta dan gurda kafarta wayyo Allah na wayyo.Allah kafata
wayyo...ai da sauri ya karasa gun ta habibaty na lafiya?
Ta zumburo baki da dan shagwaba tace masa uhm ba lafiya ba
ba kaine ba kake fushi dani ka ki min magana kayi banza dani da baby?
To.ai ke kika jawo
muga kafan naki?
Ta dora masa a kan cinya kin yi nauyi da yawa
Ai babyn ne me girma
Ke ba wani dama can katuwa ce ke ni babyna ba ruwan sa
To tin yana ciki.za
a min son kai
Eh to ya zaki yi
Lallai to ban yadda ba se a cire babyn dan baza a raba
kasona da babyn ba
Kin ma isa?wallahi
kar ki soma
Kin san nayi kewar ki
da yawa ya za ayi ne yau?
Ya kuwa ta fada
Ya mata rada a kunne ta ce ohh sede babyn ya vaka
Kin ji ki ko zo muje
tawan my icecream my chocolate my sweer love
Uhm dadin baki yana
jan ta tana komawa da baya ya dauke ta cak a karshe ta dinga dariya tana
tsungulin sa wallahi kin zama muguwa wasa wasa.
Ta cije shi a kunne kara yayi yana mata wani kallo.
*****
Bayan wata daya da sati uku
Amira ta sauka lafiya
ta samu baby boy inda aka sa masa muhammad kabeer (kabeer)
An yi suna an ci an
sha an yi rabo yaro yayi goshi.
A katsina aka yi sunsn a gidan ta dan yusuf yace ba bidi'a
shi kam a zo masa gida ba za a hada dada da aiki ba ko a nesanta shi da babyn
shi ba dan yana da son yara.
****
Komai normal yake tafiya a rayuwar familyn dada kowa sai son
barka a cikin wannan shekarar aka yi bikin nas da ni'imatullahi da kamal ko
wannen su ya samo mata kuma da gidajrn su ga ayyuka dama suna yi matar sa amina
suna kano ne suma tana da fara'a da son mutane shi yasa suka saba da yan gidan
su nas haka ma matar ni'ima salma ita kuma matar kamal hauwa'u ita ma akwai
sakin fuska.
Ai dole a saba da
dangin dada dan basu da daga kai.
*kumo*
Fadima da rabi'a ma
basa wani kadaici dan mazajen su ksn su a hade yake ga kula da suke basu ga
kuma kulawar surukai
Duk yamma suna
babban falo suna hira kamar duk gidan su daya ba hayaniya dake mubarak me
barkwanci ne sede faruk da yake dan miskilsnci amma gaban matar sa kamar aku
parrot dan magana abun har mamaki yake bawa mubarak fadima tace ina ruwan ka
suma suna dauke da juna biyu wata uku uku se jiran ranar da ske jira.
*****
Watan haihuwar
humsira ya kama ba yadda dada bata yi ba ya dawo da ita gida amma yakiya shi
baxai iya ba suyi hakuri to hamma ka bsri mana naje gun dada na haihu a can
Naqi humaira a ina
amira ta haihu?
Gidan ta
To kema gidn ki zski sauka ayi komai ansn bazan iya barin ki
zuwa wata dikko ba a wannsn yanayin daga baya kya je
Ai shi kennsn
Uhm naji shi kennsn din yarinya da son yawon tsiya ba kya
tunsnin halin kadaicin da zan shiga ciki in kin tafi kin bar ni ke ksn ki kawai
kk sani in zauna ina kula dake kawai na wani kai ki dikko ko saboda ga bahon
miji
Oh ni me na ce ina
kace ba za a ba?eh to ba shi kennsn ba Allah ya raba lafiya da nsn da can duk
daya ne ai.
Da safiyar yau Allah
ya sauke ta lafiya a gida ma haihwar ta zo mata gadan gadan ba karamin kokari
tayi ba wajan haihuwa d kanta gashi baya nan a asibiti ya kwana ta rasa yadda
zata yi seta kira shi a waya da sauri ya kira abokiyar aikin sa munibah taje ta
gyara su da babyn da maman babyn tas suka fito abin su yaron jawur ga hanci
kyakkya wa da shi son kowa kuwa.
Ta sa masa kaya masu
nauyi ta sa masa safa ta hannu da ta kafa da hula ta ajiye shi kan gado haka ta
taimaka mata ta gyara kan ta suka kwanta gyara bandakin tayi ta fesa masa turar
ta wanke da kyau
Tana fitowa masdook
na shigowa yana hamdallah yadda ya ga abar kaunar sa lallai iko na Allah da
yawa yake ba a ja dashi muhiba nagode fa aa ba komai ina tukuici na kaga baby
kuwa kato jawur dashi
Haba bani shi na gani
ita dai humaira kallon sa kawai take yi tana murmusawq lallai humaira kin iya
nukufurci
Ba matsalq ko muhiba
Eh alhamdulilahi ta sauka lafiya se godiyar Allah amma naji
dadi.
Ya masa kiran sallah ya bashi zam zam yasha ya tauna dabino
ya sa masa a baki ya yi masa hudubar sunan da zai sa masa
Hamma meka sa masa?
*Ahmad*
Ta kalle shi duk sunsn su abbi a tsallake a sa sunan abba?
Ban son haka ai sunan
sa ne
Uhm kawai tace masa
lallai ya mata karamci a rayuwa gashi ma kamr ki daya da shi dan wayo bayan
nafi son shi a kan ki
Dariya kawai tayi
tana daga kwance ungo shi bara na kira gida na sanar musu da kyautar da Allah
ya bamu
Uhm gaskiya kam
Ba a wani jima ba
maganar ta karkade dangi autar dada ta sauka lafiya ta santalo ktakyawan
saurayi tsoho ahmad aka dinga murna.
Washe gari sega dada da yamma kuma hajiya da maryama suka
karaso dasu fadima gida ya cika makil da dangi dan dadi anata barka abban ta ya
aiko da akwati biyu na kyan baby da
kaysn me jego an masa takwara.
Mubarak ma seda yaxo
dashi za a yi suna sis din shi ba wani namji an masa aboki aka gysra masa daki
ana masa dariya kaji shakiyin uba komai na suna dashi ake da masdook ko kunya.
In ana ma jaririn
wanka masdook ya kafa ido kar a sa masa sabulo ko kunys baya ji.
Aiba kunya a tarairayar d'a aje a sa masa sabulu.kawai a ido
ko hanci yayi ta kuka .
Haka aka yi suna aka
watse su hajiya da dada sune yan zaman
wankan.jego ba karamin takura masa suka yi ba sukam gaba daya ya kagu su wuce
Kullum da safe da daddare se an mata wankan.jego ita da baby
ga tuwon dawa da suke bata wai yana kara karfin jiki ga kunu da take sha.
Yaron ko ya yi kubul bul da shi ga shi ja sak aisha humaira.
Kwansn su dada arba'in da biyu suka fara shirin komawa gida
masdook kam tsabar dadi ya kasa boyuwa dada ta masa rankwashi wato murna ma
kake ko zamu wuce saboda mun shigar ma hanci da kudundune ko ?
Kaci kaniyar ka
kuwa dan tare zamu tafi
Ina?
Yawon arba'in
Tab lallai tsofafin nan so kuke ku kashe masdook duk yadda na yi kewar su
Ta masa unbola tana
dariya sun gama shiryawa daga nsn zasu bini dikko suyi sati su zazzaga dangi
bayan sati kuma zata wuce gombe suma ta musu sati sai ta dwo se ka cinye ta
Kawai kallon ta yake
dada har kin tsara?
Sa wasa ko kana da ja ne?
A'a ni mezan ce miki
ai kin gama dani kawai kai ka san wannan kuma ai
Yaushe zaku tafi?
Gobe da safe insha Allahu nasiru zai zo tare zamu yi dashi
dan in anje da kai bazaka bari ayi abunda ake so ba.
Dada da fin karfi
kike wallahi ya fada a ransa.
Ai shi kennsn Allah
kaimu gobsn amin.
Amma kin shiga
lokacina
Uhm kwa warware in
kun dawo
Yana sosa keya ya
shige daki yana dariya
Daga wanka ta fito
Ahmad na kwance ya
sha kaysn masu kyau a jikin sa ysna tsotson hannu
Tana goge jikin ta
tace masa hamma ahmad fa kai ya gada ?
A me ?
Tsotson hannu mana
Kee wallahi zan make ki abunda ya wuce zaki dawo dashi sanda
nsyi wayo na ma ina aka haife ki shekara goma sha biyu fa na baki cif cif yar
banza
Ta kama baki tana
dariya
Wai ma waya fada
miki ?
Wa kuwa
Hmm dada ko?
Kaima ka sani ai
Ya mike ya dau ahmad din yana masa wasa ta canja kayan ta
tana fesa turare
Kina ji ko gobe
zaku wuce
Dada ta fada min
da ksi zamu ko?
Hararta yayi munafuka a zuciyar ki har tsalle take dan dadi
ina nan dada tace ban da ni
Dada rigima haka
zami dau hanya gobe
Eh
Yaushe zaka zo to zamu yi kewar ka fa
Tab sede kuyi dan
tace se kun dawo ma hade a nsn
To lallai ma
Kawai ka biyo ni gombe
Baki da kunya
wallahi gidan surukan nawa zan biyo ki
Zan hakura har ku
dawo ya zanyi nayi kwana da kwanaki ba
bare kuma karin sati Allah dai ya kiyaye kawai za a ce
Amin.
Se tausayin sa ya kamata
Yaron ya fara kuka
Amsa bashi ya shs ya gaji
To
Yana zaune ysna kallon su yana jin wani dadi a ransa yadda
ya ga iyalinsa cikin koshin lafiya seya godewa Allah ya kuma gode masa.
Yana tsotso yayi bacci ta kwantar dashi ta kuma lallaba ta
kama mijin ta dan tasan me yake buksta tunda bazata bashi du ba ai ta bashi
rabi ma'ana suyi romancing junan su .ba karamin dadi yaji ba ya dinga shi mata
albarka yana mata godiya.
Ranar kwana suka yi suna hira a tsakanin su washe gari suka
shirya suka gama komai suka dau hanyar dikko ta katsina
****
Kamar yadda suka tsara hakan ce ta kasance sun zaga dangi ko
ina sannsn suka koma gombe nsn ma sun zazzaga seda tayi sati daya da kwana uku
dan taga kawaye mubarak kuma ya hanata tafiya wai be gaji da ganin ta ba .
Har seda hamma
masdook ya dameta da mita tukuna ta fara daukar haramar komawa kano ta dabo.
Ranar da ta dawo ranar be barta ta huta ba ya dirje ta iya
son ransa har seda aka kira assalatu tukuna sannan ya sarara mata ya tafi
massalaci.
Rayuwa me dorarwa ce ta kassnce cikin familyn mubarak dikko
Allah ya azurta su da yaya da jikoki masu hadin kai da biyaya a tsakanin su ba
babba ba yaro ga ilimi daidai gwargwado ka kyauta da kirki.
Matan su mubark ma sun sauka lafiys sun santalo mace da
namiji
Da me sunsn dada da
kuma mubarak 2 sun musu takwara a gida daya.
Duk karshen shekara
se an hadu a gidan dada an yi sati sna raha ana capter
Arxiki ya hsbaka ya
yalwantu a tattare dasu madook yusuf har shago ya bude na kayan alatu a kano
Yaran sa biyu yanzu
da kuma mace me suna hajara.
Aisha na da wani
cikin a jikin ta dan ahmd ya shekara biyu da rabi
Ni kiyi ta haifa
min yara ko dari ne ni ina so dan sune gatana.
Wannsn taron ma an hallara
Dada ta kalli sama ta godewa Allsh ta kuma godewa Allah da
ya bata ikon ganin yayan jikokin ta taga yayan ta taga jikokin ta ga kuma yayan
jikokin ta ta gani meya fi mata wannsn dadi ina ma malam na nan ya ga baiwar da
Allah ya basu
Allah abin godiya A
kullum nakan ji dadi in har na waiwaya naga zuri'a ta ba karamin dadi nake ji
ba a tattare da ni
Ku rike junan ku da
amana kunji yaran nan ku cigaba da hada kn ku ku cigaba da *zumunci*dan kuwa
shi ne jarin ku ko bayan raina nasan zaku riki junan ku gaba daya Allah
ubangiji ya sada ni da ku a gidan Alljana
Amin.
Ta fashe da kuka suka
yi kanta gaba daya jikokin nata suka rungume ta.
*****
Bayan sun dawo.gida ne take tsonan shi wai hamma in tambaye
ka?
Uhm ina jinki
Ina budurwar ka
zainab?
Hararta yayi
Ban sani ba
Hhhhhh wai Allah kai
hamma kaso baiwar Allahn nan da yawa
Ke din ce kin yi min
katutu kin hana ni sakat a zuciyata
Zainab tayi naci
tayi tayi amma ta kasa samun kofa har gidan si naji na mata warning na ci mata
mutunci dan na gano bibiysta take kuma so take ta wahalar min dake ta shiga
tsakanin mu dan ta samu galava Allsh ya fita shi ne fa baban ta yace ta fito da
miji cikin sati biyu in ba haka ba ze bata me gardin gidan sa ai seta fashe da
kuka tana bani hakuri ta hakura zancen da nake miki ma yanzu ta yi aure kuma
yayan ta biyu dan yan biyu ta haifa duk maza kyawawa baki gan su ba kuwa
Kaje kennsn eh ina
zuwa dan abokina take aure
Kai hamma kwakwa kai
ka hada su kennan?
Uhm kinga ko na samu lada
Gaskiya kam kq samu
dama ina wata zee ina kai ai da matsala
Ban san kuri yarinya
kin san dai ita ce first love.
Ai ta hau ruwan
cikin sa tana masa duka ta ko ina ahmad ma ya cangalo yan kafafun sa ya hau
gadon ya taya ta suna dkan sa da hannun sa yana dariya yaga abun wasa
Masdook kam dariya
yake tayi yi hakuri wasa nake miki only na kinji bari ahmad harda kai kake
dukan dada?
Ashe group dinku daya
wadda za a haifa nasan ni za ta biyo muma mu rama
ALLAH ka daina
kira.min sunsn wata nice first and last luv din ka ya hada da ita da dan sa da
cikin ya rungume ysna mata wasa an gama swirry an gama.
Nima nsn nacs muku
bisallam
Nan na kawo karshen
littafin *aisha humaira*
Kuskuren da muka yi Allah ya yafe mana.
Ina fata na
nishadantar daku masoyan aisha humaira.
_so ba yin sa ake
ba so yana faruwa ne kawai lokacin da ya so kuma ga wanda yaso a sanda ya so ko
wanne so da tsarabar sa dan kina son mutum ba lallsi ki same shi ba Allah me
yin yadda ya so ne me juya ala'amuran sa_
*Allah ubangiji ya
hada kowa da gwanin sa kuma miji na gsri me kula da dukksn bukatun ka mata kuma
ba auren ba rashin yin biyayyar msta su daure suna biyayya ga mazajen su suna
musu abunda zai sa suji dadi har su sa musu albarka banda kace na ce da miji
dan yana kawo bakin jini se kuma a fara smun sabani koda kece me gaskiya bashi
hakuri wata ran zaki ci ribar zamam taren dan mace aljannar ta na karkashin
kafar mijin ta to yar'uwa ya zaki yi wasa da wannan aljannar? Shi zaman soyayya
ai zama ne na amana tunda sna son juna se a daure a ci maganin zama tare dama
me auren hakuri*
Daga marubuciyar:-
*Cin fuska*
*Waye nawa?*
*Zumunci*
*Rayuwa ta*
*yar waye?*
*hatsaniyar so*
*yanayi*
*baka yi min adalci ba*
*rukkaya*
*kausar*
*firdausi*
*na amince*
*karshen rigima*
*hilal da ilham*
*so*
*ban yarda ba*
*son maso wani*
*kuskure*
*meye laifina ?*
*abotar mu*