Ma dai daichin gida ne wanda ya tsaru iya tsaruwa, masu
hidimar gidan sai kaiwa da komowa suke.
Gabaki dayansu suna zaune a dinning table suna breakfast ba
wanda ke cewa komai har suka kammala
Ammii ce ta kwashe
kwanukan takai kitchen tahau wanke wa.
30mints later
Daddy ne ya fito cikin shirin sa na zuwa daurin auren dan
kaninsa wanda xa ayi a garin Karaye
"To Ammii zan wuce to daddy Allah ya kiyaye hanya
"
" Ameen ameen sai na dawo.
Tafe yake akan hanyar sa ta zuwa Karaye gudu yake ta tsulawa
kamar dan shi akayi titin kasan cewar
titin ba cunkoson abin hawa.
Sai da yaxo dai
dai inda ze shiga garin gwarzo ya taka kusa aiko tayar sa ta fashe.
INNA LILLAHI WA INNA
ILAIHIRRAJU UN shine abinda daddy yake maimai tawa, waye zai tai makeshi da
sanyin safiyar nn gashi bashida spare
tier balle ya canja.
Daddy yana tsaye
jikin motarsa yana neman mafita tunani yake kodai ya bar motar ne yatafi gurin
daurin auren? To in ya tafi wa zai bar
wa motar sa, yasan komai zai iya faruwa idan ya tafi.
"To ynx ya
zanyi yace afili.
Sauri yake tayi kasan cewar yau daurin auren amininsa ya
zama dole ya halarchi wnn daurin auren.
Tundaga nesa ya hango
shi kuma tabbas yaga alamar yana cikin yanayi na neman taimako kasa ya farayi
da motarsa yayi parking dan gaba da daddy sannan ya fito.
Sannu Alhaji
Yawwa sannu yaro
"wani abu yasami motar ne?
" Ehhh taya ce ta fashe gashi banida spare.
"subahanallahi" Aikuwa inada spare a bayan motata nn ya xagaya ya dauko masa tayar.
Bari naje nn gaba
kadan akwai masu gyara sai suzo su saka maka
To madallah inji
daddy yana mai fadada fara 'arsa. Daga nn safeer yy gaba shikuma daddy ya
tsaya.
Befi 20mints sai
gashi da Mutum biyu sun dawo nn suka shiga daura taya suka gama.
Nagode sosai yaro
"Bakomai wlh ae yiwa kaine "
Ina kanufa daddy ya tambaya.
Karaye zani daurin
auren abokina, Ae nima nn na nufa
Daga nn kowannen su
ya shiga motarsa suka kama hanya wanda cikin lokaci kadan suka isa kuma aka
daura auren dasu.
Sai bayan da aka
daura auren ne Alh. Al 'ameen sarakee Ya samu kebewa da safeer inda ya bashi
complementary card dinsa
"Ga wnn card
dina ne don Allah gobe ka sameni a office"
To nagode kuma insha
Allah xaka ganni....
ASSALAMU ALAIKUM wa
alaikumussalam sannu da zuwa Alhaji
"yawwa Ammii ya gidan?
"
" lafiya kalau Ammii tace tana binka bayan Alhaji zuwa
daki.
3 hours later
Shukra kixo inji daddyn ki yana son magana dake
To Ammii shukra
tace tana mikewa daga kwancen da take
Da sallama ta shigo
cikin dakin cike da biyayya ta gaida mahaifinta
ya answer da fara 'arsa.
Zuwa chan daddy yayi
gyaran murya ya fara magana kamar hk
"shukra inaso
ki bude kunnenki ki saurare da kyau kuma ki dauka cewa maganar da xan fada miki
umarnine ba shawara ba.
Gaban shukra ne
yashiga bugawa da sauri sauri to me daddy xe gaya mata ne wae
" Kina jina ya
katse mata tunanin da take "
" Ehhh Kawai ta
iya cewa tana sauraronshi
Nayi miki miji kuma nn ba da dade waba sai zo ku fahimci
juna
" miji kuma
shukra tace tana xaro idonta
Alhaji miji fa kace
"Ehhh miji mana
menene "?
Ae naji ka fadi
abinda baxe yiwu bane
Ae kuwa dae sai ya
yiwu kuma ki zuwa ido ki gani yana gama fadar hk yafice daga gidan ma gaba
daya.
KO WANENE MIJIN DA ALH SARAKEE YA XABA WA YARSA?
SHIN XASU AMINCE DA
AUREN KO KUWA A A?
Knocking yake a kofar office din Alh sarakee
" yes come in
inji sarakee,
Kai tsaye safeer ya
shiga cikin office din har kasa ya durkusa yana gaida Alh sarakee
Abun ba karamin dadi yama sarakee ya answer fuskarsa a sake
" Have a sit
"Thank you sir
Safeer nasan xakayi mamakin abinda yasa na nemeka kuma ni
anawa ganin ba abun mamaki bane, Alfarma
nake so kayimin dan Allah
" Alh wace Alfarma kakeso nayi maka
Inaso dan Allah duk abinda nace kayi min kayi
"indai be
sabawa addiniba me zai hana nayi maka
" be saba bama cewar Alh sarakee cikin sauri
" gyara xama
yayi yafara dacewa
A gaskiya na yaba da hnklin ka shine nakeso na hada ka da
yata dan Allah ka aure ta
Maganar ta xowa
safeer a BAZATA baxe iya cewa a a ba amma shi har ga Allah bashida burin Aure a
wnn lokacin
" Dan Allah
karka ce a a inaso kasani yata batada wani aibu ba kuma dan tarasa mijin aure
ne na bakaba a a kawai dai dan na yaba
da hankalin kane nakuma ji dadi da ka temaka min a lokacin da nake tsananin
bukatar temako
" To Alhj
madallah nagode
" nine da
godiya safeer ynx sai ka bani number
wayar ka kuma in kuma in ka samu lokaci sai kazo ku sasanta kanku ko
To insha Allah
xanxo.
Yawwa baka gayamin suwaye iyayenka ba da kuma karatunka da
inda kake aiki
"sunana safeer muhammad mai lafiya babana shahararren dan kasuwane, nayi
makarantar primary da secondry a garin Abj kasancewar kasuwanchi yakai
mahaifina can garin Abj bayan na kammala secondry ne muka dawo garin kano inda
na samu Admission a B U K na karanci "Architectural technology" ynx hk ina aikin gwamnati sannan kuma ina
aiki on my own nakanje gari gari indai ai nemeni ina zuwa nayi Aiki.
To masha Allah, Allah
ya taimaka
" Ameen ameen
Alhj nagode
" Nine da godiya sai najika
Daga hk sukayi
sallama.
WASHE GARI
shukra wai me yake
damunki ne ace tunda aka miki maganar auren nn shikenan bakida wani aiki sai
kuka
"Ammii ya xanyi
da raina wae ni xa ayi wa auren dole
To shukra ya xakiyi
ae sai hkr kawai
" yanzu Ammii ba abinda xakiyi akai?
To me xanyi shukra
ae a gabanki yace na zuba ido ko? sbd
haka rungumar kaddara ne kawae ya dace dake a halin ynx
"Bazan iya ba
wlh Ammii banason koma wane ne kawai a kyaleni
To ae sai ki bari
inya dawo kije ki gaya masa (zuwa
wannan lokacin Ran Ammii ya soma baci da kalaman shukra) tana kaiwa nn tafice mata a dakin.
Wayar shukra ce ta
fara ringing kamar BAZATA dauka Ba sai kuma da dauka "Aneesa ce class mate
dinta tun a secondry har zuwa ynx da suke karantar" Optometry " a B U K.
" Hello Aneesa Y
kk
"lfy shukra are you coming today?
"i don't think so
Buh why?
Am not feeling better
"wishing u quick recovery shukra luv
Thanks
Aneesa dan Allah
inkin gama lectures ki biyo gida kafin ki tafi
"to insha
Allah zaki ganni
Da sallama Aneesa
tashigo cikin gidan Ammii ta samu a falo suka gaisa ann ne ta tambayeka
shukra..
Tana ciki tana
aikin kuka.
" kuka kuma Ammii bari nashiga ciki na sameta
to.....
Shukra wae me yake damunki ne Ammiii tace min kina kuka
Hmmmm Aneesa ba
dole inyi kuka ba wae ni xa ayi wa auren dole..
What...come again shukra i didn't get u aure fa kika ce
"Ehhh aure
wae daddy xemin da wani banza wnd ban sanshi ba
To ynx shukra zuba
ido xakiyi ayi auren bawani mataki da zaki dauka.
Hmmmm banida wani
zabi Aneesa abinda dae na sani
shine" Wallahi tallahi daga ranar da aka daura auren nn daga ranar
koma wane mijin yayi sallama da kwanciyar hankali da xaman lafiya.... Tunda dae
ya zabi aure na tokwa ya xabar wa kansa masifa ne wae ni shukra zai Aura....
Hmmmm!!!
Hmmmm to nidai ba
abinda xance sai dai
Ince Allah ya kyauta
"Ameen inji
shukra"
Nidai Kinga tafiya ta cewar Aneesa tana mikewa
"ki gaida
mamah"
Zataji insha Allah tafada tana ficewa daga dakin.
@Safeer's house
Dukansu na gani zaune a palourn mamah suka kallo
Safeer ne ya ke ta
satar kallon Abba, Abban ne ya lurada shi
"Safeer ya
akayi ne
" Abba wata magana nake so nayi daku sai dai ban san
yanda zaku dauki maganar ba,
Juyowa Dukansu
sukayi suna fuskantar shi suna jiran suji me zai ce
"muna jinka
Safeer fadi me kake so kace kaji
Nan Safeer ya gyara
zama ya fara basu labarin tun haduwar sa da Alhj sarakee har zuwa bashi yar shi
da yayi
"
Alhamdulillahi "shine abinda daddy yace yana me kara fadada murmushin kan
fuskar sa
" ynx yaushe
ne bikin to inji Mamah ta fada da murnar ta.
Yace baxe dau lokaci
ba
To Allah ya nuna
mana
Ameen Dukansu suka
hada baki gurin fada
Yeyyyyyy!! Miemie
ce tasa ihu ynx xan fara kiran kawaye in fada musu bikin yaya na yazo
Kae ranar akwai
buduri wlh xamusha rawa da one leg yeeeeyyyyy ta cigaba da ihu....
Dukansu dariya suke banda Safeer daya hade ransa dama shi ba
shiga harkarsu yake ba shi baya son rainin hnkl
"zan koya miki hnkl wlh meye hk
mtwsssssss ya fada yana ficewa daga palourn.
Allah ya shirye ki
miemie inji Aysher (yayar miemie ita take bin Safeer).
Alh sarakee ya yanke auren Safeer da shukra nn da sati biyu
xa a daura aure inyaso ta tare koma yaushe ne.
Yau ta kama ranar da Safeer xexo Ammiii ce ke shirye shiryen
ta banda shukra dake kwance a daki kamar kullum tana aikin kuka..............
Safeer ne ke saukowa
daga upstairs cikin shirin sa na zuwa gidan su shukra sanye yake da shadda light
brown gezna hannunsa sanye da agogo kirar rolex kansa da hula
Kai tsaye falon
Mamah ya nufa ya shiga ya durkusa kusa da Abba ya shiga gaida iyayensa cike da
ladabi
Da fara arsu suke
answer wa
"za a tafi neman auren ne miemie ta fada tana buya a
bayan mama
Ai kuwa a xuciye ya
taso kamar wanda xe doke ta "yi hkr inji mamah kaifa babba ne
" Mamah yarinyar nn ta raina ni wlh inaji fa dana
gaisheku sai da answer
Dariya daddy yayi
yace ayi hkr kaji "tashi ka tafi kar ka makara
To kawae yace ya
fice ransa a bace.....
"kai tsaye safeer gidansu shukra ya nufa wanda cikin
lokaci kadan ya karasa, parking yayi a inda aka tanada domin parking motochi
sannan ya fito
"kai tsaye cikin gidan yanufa xuciyarsa tana harbawa da
sauri da sauri ai kuwa sai yaci karo da kaninta
"yana ganinsa
ya taso da fara arsa
" Good afternoon uncle
"Afternoon! How are you
"Not bad
" good "
Shukra fa? Ya tambaya
" tana ciki tana kuka
"toooooo to ynx xaka iya karamin ita
"Ehhh ammii
tace in kazo ka shigo daga hk yayi gaba shikuma yabishi har guest room ya zauna
shi kuma ya fita
Ammii! Ammii! Ammii
" Na am meye ne kake ta kirana ta fada tana fitowa daga
kitchen
"Ammii mijin
Aunty shukra ne yazo
" ohhh har yazo
ince dai ka kaishi guest room ko
"Ehhh Ammii
yana chan yace in kirata
" to jeka abinka zan turo ta
"To kawae yace ya koma gurin safeer inda suka cigaba da
hirar su kamar dama chan sunsan junansu ne.
"sanda Afeer
ya fita Ammii kai tsaye dakin shukra ta shiga 'shukra tashi ki shirya ga safeer
chan yaxo yana jiranki' tana gama fadar hk tafice ba tare da ta jira
me Zata ceba"
Koda Ammii ta fita shukra xamanta tayi batada niyyar tashi
har sai da takai 40mints a zaune
"Ammii ce ta
leko 'ynx shukra har ynx kina nn a zaune kinbar yaro yanata jiranki shima fa
yana da abinyi amma ya vari yatawo gurinki amma kika barshi a zaune ko?
" A a Ammii ynx xan tafi fa.
"karma ki
tafin mana ynx in kira Daddy in fada masa
" Dan Allah
kiyi hkr Ammii wlh ynx xani ta fada tana mikewa
Ammii ce ta fara
fita sannan itama ta fita
"kai tsaye guest room ta shiga Amma koda ta shiga sai
tayi tsaye abinta ta kuma sunkuyar da kanta dan ko kallo ma be isheta ba"
"Tsahon lokacin
suka dauka ba wanda yace da dan uwansa komai
" safeer ne ya
katse shirun ta hanyar mikewa yana cewa toni xan wuce
"sai na dawo ko
" komai bata ce ba illa matsa masa da tayi ya huce
Yana fita ita ma
ta fice kai kai tsaye dakinta ta shige ta rufe.
"koda safeer
ya koma gida be nuna wa iyayensa hk ne ya faru ba kuma koda Alhj sarakee ya
kirashi cemasa yayi to karbe shi hannu biyu - biyu.
" To biki fa ya gaba to kamar yadda Alhj sarakee yace
xa a daura aure inyaso ta tare daga baya hk kuwa akayi
" Yau ta kama
saturday wanda yaune za a daura AUREN
iyayen sai farin ciki suke banda yayan da suke a cikin tsananin bakin
ciki musamman shukra da ba son auren take ba
'Har gwara na
safeer wanda shi daman tunda yaga shukra yaji sonta ya shige shi sai dai yayi
wa kansa ALKAWARIN baze taba nuna mataba har sai ya koya mata sonshi
( uhmm su safeer manya)
"To abokan
safeer duk sun hallara a gurin daurin auren don taya shi murna".
Sanye yake da farar shadda tasha aiki wanda aka yimusu shida
Abbansa iri daya, bakin takalmi da bakar hula yasa sai kuma farin agogo da yasa
sai kyalli yake yana ta fara a wadda shi kansa besan na menene ba kawae dai ya
tsinchi kansa cikin farinciki ne a yau din
( Niko nace luv ne).
To Daurin auren ya
samu halartar manya manyan mutane daga ko ina a fadin Nigeria wanda yawanchinsu
abokan Abba da daddy ne
"An daura
AUREN akan sadaki naira dubu dari.
Haka dai daurin
aure ya watse kowa na farin ciki ana kuma ta sa albarka.
To kamar yadda
daddy yace shukra BAZATA tare ba hk kuwa akayi bata tare dinba tunda ynx ma
final exam dinta xata fara ta kammala university.
To shukra fa sun
fara exams gadan gadan wanda ynx ma sun kusa gamawa shikuma safeer ya cigaba da
zuwa Aikin sa kamar da.
Shukra ta
kammala exams dinta kuma ansa ranar tare war ta nanda sati uku.
"Duka banga
rorin biyu shirye shiryen su suke tunda xa ayi mothers night kafin akai amarya
dakinta.
" yau ta kama
saturday wanda yaune xa ayi mothers night shukra taci kwalliya kamar ba gobe
"Fancy Makeover" itace ta mata kwalliya kuma tayi shirinta cikin wani
material me tsadar gaske kalar peach tasa head orange (hmmmm abin dai ba a cewa komai readers
zanso kuga shukra yau din nn ba karya) takalmi da jaka duka orange tasaka.....
"Daga nn dai
aka dunguma zuwa" Shukra event centre "inda ann ne za ayi mothers night
din.
To anchi ansha
Alhamdulillahi guri ya kayatu daga nn ne aka kwashi shoki sannan aka rufe taro
da addu a aka dauki amarya aka wuce da
ita gidan ta dake nn Nassarawa G R A.................................
ASALIN SU
Alhj AL 'ameen sarakee haifaffen garin adamawa yola ne yayi
karatun primary & secondry dinsa a garin Adamawa wanda daga nn yayi exam
jinsa wato Jamb ya kuma samu point me kyau
Ya nemi admission
a usman danfodio university sokoto wanda cikin yardar Allah ya samu ya fara
karanta 'Geology'.
To bayan ya
kammala karatun sa ne be dade ba yasamu Aiki a wani company a garin kano inda
ya tattaro gaba daya ya dawo kano da xama
"Alhj sarakee
ya hadu da matar sa fateema ne (Mahaifiyar shukra) a saudiyya inda yaje aikin
hajji
" itama
fateema gabaki daya yan gidan su suka je Aikin hajjin kasancewar mahaifinta me
Arzikin gaske shine senator na kano central a wnn lokacin
"To kasan
cewar A lokacin Aikin hajji suka hadu yasa basu wani fahimci junansu ba sundai
yi exchanging numbers na niyyar in sun dawo gida sarakee zaije ya sameta.
" to bayanda
suka dawo gida ne Alhj sarakee yaje gidansu fateema kuma ta hada shi da
iyayenta..
Baban fateema ya
yaba da hnklin sarakee kwarai shiyasa ma bayan dayayi bincike a kanshi sosai ya
nemeshi ya kuma shaida masa ya turo iyayensa.
" Iyayen Alhj
sarakee sun zo sun kuma yi duk abinda ya kamata akasa ranar biki wanda ba a
wani dau lokaci ba aka daura auren aka kuma kai fateema gidanta dake unguwar
'Farm center'.
To zaman fateema
da sarakee xama ne abin sha awa domin akwai girmamawa da mutunta juna.
'Haka zaman su ya
cigaba har na tsawon shekara biyar wanda a wnn shekara biyar din fateema ko
bari bata taba yiba balle haihuwa abinda yayi matukar daga mata hnkl kenan
"A bangaren
sarakee kuwa sam abin be dameshi ba shine ma kullum yake kwantar mata da
hankali yana cewa haihuwa ta Allah ce Kuma lokaci ne beyiba in yayi xa ta haihu
" To da wannan
kalami na sarakee fateema tayi amfani wajen kwantar da hankalin ta.
Ana cikin haka ne
fateema ta sami ciki, zo kaga murna wajen sarakee da fateema kai har ma da
iyayansu wanda daman suma rashin haihuwar ya damesu shiru dai kawae sukayi.
"Ciki dai yana
samun kulawa yadda ya kamata
Haka suka cigaba da
kulawa da cikunsu har watan haihuwa yayi wanda Alhj sarakee takanas ya tafi
'Egypt' danyin siyayyar kayan baby
" To ana gobe
fateema xata haihu sarakee ya dawo wanda washe gari da asuba fateema ta tashi
da ciwon mara da ciwon baya wanda sarakee be bata lokaci ba ya dauki fateema
sai asibiti.
" Cikin
lokacin da be wuce awa daya ba fateema ta haifo kyakykyawar yarta me kama da
Alhj sarakee sak daga nn akayi discharging dinsu kasan cewar fateema da babyn
lafiya kalau suke.
" Ranar suna
yarinya tachi suna 'ZAINAB' wato mahaifiyar Alhj sarakee hakan nema yasa suke
kiranta da suna 'SHUKRA'
" Sai da
shukra ta kai shekara 7 sannan fateema ta kara samun wani cikin. To wnn cikin
ma anyi farin ciki da samun shi kasancewar sun cire rai ma da kara samun wani
cikin.
," Haka dai
take ta rainoncikin har lokacin haihuwar yaxo inda ta haifi yaron ta namiji.
"shikuma sunan
mahaifin fateema yaci wato Mukhtar suke kiransa da 'AREEF.
" Tundaga kuma
wannan lokacin har zuwa ynx fateema bata kara haihuwa ba.
"Haka yaran
suka taso cikin soyayya da kuma kulawar iyaye sosai yaran suke da tarbiyya ga
girma ma manya ga kuma kunya da tsoron Allah.
CIGABAN LABARI
" TO koda safeer
ya taso daga office gidan mahaifin shi ya wuce kai tsaye inda iyayen nashi suka
hadu suna mai nasiha kan ya kula da matar sa domin amana ce a gurin.
" Godiya safeer
yayi musu sannan kuma ya kama hanyar gidansa xuciyar sa cike da sake sake
tunani kawae yake wace irin tarba shukra xatayi masa?
" zata karbi
kaddara ne ta zauna dashi a hk ko kuma BAZATA karba ba?
"To da wnn
tunanin ne safeer ya karasa gurin wani suya spot ya siyi kaji da kuma fresh
milk xe kaiwa amaryar sa...........
" Bayan
yagama da suya spot kai tsaye gidansa dake nassarawa G R A ya nufa koda ya isa
yayi worn a gate, gate man ne Y taso da fara arsa ya bude mishi yana gaida shi
da fara arsa.
" To safeer
dinma da fara arsa yake answer wa kafin ya wuce gurin da aka tanada don parking
yayi parking motarsa sannan ya nufi cikin gidan kai
tsaye..........................
Ko da SAFEER ya
shiga cikin gidan kai tsaye dinning area ya huce ya ajiye kayanda ya shigo dasu
sannan ya shige dakinsa.
"kayan jikin
sa ya rage ya fada bathroom don yin wanka.
" A bangaren
shukra kuwa yan kawo amarya na fita ta mike ta rufe kofar ta sannan ta koma
tayi wanka tasa sleeping dress nata ta kwanta.
"Bayan kamar
30 mints da shigar SAFEER toilet ya fito daure da towel a waist nasa da kuma
wani a hannun sa yana goge kansa dashi.
" kai tsaye
gaban dressing mirror sa ya wuce ya shafe jikinsa da lotion sannan yasa turare
ya wuce kan gabon sa dan sa kaya wanda already dama ya fito dasu.
Bayan da ya gama
shirya ne ya fito ya nufi dinning area ya dauko ledar da yashigo da ita sannan
ya wuce dakin shukra.
"Yana
karasawa ya murda handle din kofar amma ga mamakinsa sai yaji kofar a rufe gam.
Cikin bacci shukra
taji ana taba handle tsaki kawae taja tana hararar kofar kamar yana kallonta.
" A zuciyar ta
take cewa munafiki da ajinka xan bar kofar a bude ne" mtwsssssss ta dada
jan tsaki sannan ta juya baya ta cigaba da baccin ta.
"Shiko SAFEER
juyawa yayi ya nufi dakinsa jin kofar shukra a rufe.
" Washe gari
misalin karfe 12:00 na Rana ko wannen su na dakin sa.
"knocking din da
ake a kofar falo ne yasa SAFEER fitowa ya karasa ya bude kofar.
"kokarin
tureshi take yi xata shiga ciki da basket a hannunta
" ke bakida
hankali ne wae kike ture mutane ya fada a tsawace yana binta da mugun
kallo...... Wallahi ki kiyaye miemie inba hk ba hmmmm ya fada yana wuce wa
cikin falo.
"Dan nazo
gidan ka shine kake min hk ta fada tana tura baki gaba kamar xatayi kuka.
" Ammiki din
ya fada yana hararar ta (shi sam be so wannan yarinyar tazo ba don surutun ta
yafi aikinta yawa).
"Wae ke me
kika zo mn gida da sassafe.
" Baki ta saka
tana kallon shi da mamaki 'ynx ne safiya ya SAFEER?...
"To ynx ma ba wannan ba ina Aunty na.
Tana ciki ya fada a
takaice.
"Au ita bata
rashi ba ikon Allah koda yake
ae da gajiya gwara ta huta.
" Gajiyar me ya
fada yana mikewa wane zai daketa.
"Tana ganin
haka ta mike gajiyar biki fa nake nufi.
God save you ya fada yana koma kan kujera.
" To ynx yaya
haka xan tafi ban ganta ba.
"Ehhh yace
yana nuna mata kofa 'fita Dalla kinzo kin Sani a gaba da surutu
Fita tayi tana
waigensa tana zuwa bakin kofa ta labe shikuma ganin ta fita yasashi komawa daki
tunda bashi da abinda xeyi.
" Aiko miemie
na ganin ya shige daki tashigo cikin gidan da saurinta tana waige- waige.
Kai tsaye dakin
shukra ta huce aiko sai ta ganta tsaye jikin dressing mirror tana makeup.
" Aunty shukra
ta fada tana yi mata murmushi.
"Murmushi
itama shukra take mata haka kawai taji tana son yarinyar.
" ya sunanki
ta fada tana kamo hannunta.
Sunana miemie.
"Miemie ya gida
ya mamah?
" lafiya kalau
muke.
Aunty wae me yasa yaya ya hanani inzo gurinki ta tambaye ta
tana karewa dakin kallo.
"Bakomai
miemie inaji saboda sanda ya fita ina bacci shiyasa yayi tunanin ban tashiba
(Tayi mata karya).
Ok na dauka sbd
yaga kin gajine bayaso in tashe ki.
" Gajiyar me
miemie? Ni ban gaji ba ae.
Uhmm kawae tace
tana hayewa gadon.
" Dariya
shukra tayi ta koma ta cigaba da makeup dinta.
"A takaice
dai miemie a gidan ta yini sunata hira da shukra kamar dama sun saba da juna.
" Sanda
miemie xata tafi sai da shukra ta cika katuwar leda da kayan makeup ta bata.
Godiya sosai
tayi mata sannan SAFEER ya dauketa suka tafi.
" Yau ma da
safeer ya dawo dakin shukra ya wuce amma yasame shi a rufe juyawa kawai yayi ya
koma dakinsa kasan cewar a gajiye ya dawo (shi dama ba wani abu xe mata ba
kawai dai zai duba lafiyar tane kamar yadda mahaifinsa yace amana ce a gurin
sa).
" Yau sati
biyu da bikin safeer & shukra amma cikin sati biyun nn safeer be taba sa
shukra a idonsa ba.
Dawowar sa
daga masallaci knn amma ga mamakinsa sai yaga kofar shukra a bude ae kuwa sai Y
xarce dakin.
" Shigarsa yy
dai dai da fitowar shukra daga toilet daure da towel dinda be karasa rufe mata
cinya ba..
Kallon kallo suka
shiga yi kafin shukra ta bude baki ta fara zaggaga mishi masifa.
Wnn wani irin hauka ne xaka shigo dakin Mutum ba excuse ta
fada tana hararar sa..
Hauka ya nanata
kalmar a zuciyar sa
"Allah ya baki
hakuri ya fada yana juyawa zai fita.
" Yana zuwa
bakin kofar ya rufe da key sannan ya xare key din ya sa a aljihun wandonsa.
"Takowa
yayi gabanta fuskar sa a daure ba alamar dariya.
" Iya tsorata
shukra ta tsorata nn ta shiga yin baya - baya shi kuma yana binta.
"Hannu yasa
ya jawota yana kokarin kunce towel din jikin ta" Bari ba miki cikin
mahaukachi yanda ko waje kika fita kika ga mahaukachi vazakiyi masa goriba
tunda kina dashi.
"Kuka tashiga
yi tana turashi yayinda take rike towel dinta da dayan hannun, Amma dake karfin
ba daya ba sai da ya kunce towel din sannan ya turata zuwa gadon shima ya hau.
" Ganin
batada wata mafita yasata fara rokonsa 'Dan Allah ya safeer ka bari wlh tsoro
nakeji, na tuba bazan sake ba.
" Gani kawai
shukra tayi safeer ya mike ya nufi kofar fita sannan yasa key ya bude ya fece.
(shi dama beyi niyar mata komai ba kawae dae barazana ya mata).
" Tun daga
wannan rana shukra take masifar tsoron safeer bakuma ta sakachin kin rufe kofar
ta.
" Yau ta kama
monday kuma yau safeer zai koma aiki sbd hk ya tashi da wuri ya gama shirin sa
na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. Ko dinning be kalla ba
tunda yasan shukra ba zatayi masa girki ba.
" Yasa kai xe
fice kawae tasha gabansa hade rai yayi yana kallon ta shi sam be ma kula da ita
a palour'n ba,
," ya safeer
dan Allah xan bika ka kaini gida
To jeki dauko
hijabi mu tafi..
Ihu murna tasa ta
shige daki da gudu
"koda shukra tashiga cikin dakin bata wani dade ba
kasan cewar dama a shirye take mayafi kawae ta dauko ta fito ta samu safeer
zaune cikin motarsa yana jiranta.
"Bude motar tayi ta shiga bata cemasa ba shima bece
mata ba haka suka kama hanyar gidan su shukra kowa na sake sakensa cikin ranka.
"cikin
lokacin da be wuce 40 mints ba suka karasa gidan su shukra, kasancewar safeer
nada aiki sosai a office yasa ko da shukra ta fita be bita cikin gidan ba.
" Ango kasha
kamshi abokinsa yace masa yana dariya irinta tsokana.
"Koma bece ba
yakaro yana mika masa hannu suka gaisa sama - sama kasan cewar sun kusan
makara.
" sanda shukra tashigo cikin gidan bata samu kowa a
palour ba hakan nema yasa ta shigewa dakin Ammii kai tsaye.
"zaune ta
samesu ita da Areef suna kallon wani serious.
" Da mamaki suke kallon ta kafin Ammii tayi
karfin halin mata magana
"ke kuma
lafiya kika xomana gida da sassafe, ina safeer din yake ta fada taba kallon
kofa kamar me neman shi.
" Ya wuce
office in ya tashi zai shigo ae ta fada tana wucewa kan gadon Ammii.
"Aunty shukra
yaushe ya safeer xe dawo inji Areef.
" Ban Saniba ta
fada tana juya masa baya.
"To Aunty ki
kirasa ki tambaye sa mn.
" Karka dameni
Dalla malam.
" Bekara cewa
komai ba illa ma fitan da yayi daga dakin.
" Duk abinda
suke Ammii na jinsu sai da Areef ya fita ne ta juyo tana kallon shukra
"shukra anya
ko kuna zaman lafiya da yaron nn
" Ammii wace
irin magana kikeyi ne wae, waya gaya miki bama zaman lafiya.
"Halinka
nasani ae shukra.
" To Ammii ki kirasa mn ki tambayesa.
"Bazan
kirasa ba sai dai in bari shawara kan kiji tsoron Allah kada ki tauye wa yaron
nn hakkin sa karki ganshi shiru - shiru ki zaluncesa, idan mu bama ganinki
Allah na ganin ki.
" Kai Ammii
dan Allah wae waya fada miki bama zaman lafiya me ma ya kawo maganar xalunta da
wani tauye hakki.
" kedai kika
Sani inji Ammii tana ficewa daga dakin.
"shiru shukra
tayi tana tunanin mgnr da Ammii ta gaya mata, tanason daukar maganar Ammii amma
shedan yana mata huduba.
4:00 pm
" Daddy ne ya shigo cikin gidan daga office shukra
yasamu a palour, da mamaki yake binta da kallo.
"Daddy sannu
da zuwa ta fada kafin Ta durkusa har kasa ta gaida shi.
" Ba yabo ba
fallasa ya answer sannan ya shige dakinsa, Ammii ma ta fito daga kitchen tabi
bayan daddy.
4:40 daddy ya
fito palour yace Ammii ta kira masa shukra.
"Bayan Ammii sun fito tare da shukra dukansu suka zauna
a kasa suna jiran me xance.
"shukra
lafiya na ganki a gida kuma.
Ita abinma
mamaki ya bata exactly tambayan da Ammii tamata irinta daddy ya mata.
" Lafiya kalau
daddy kasan yau ya koma office shine yace bari ya kawoni gida inya dawo xexo mu
tafi.
"Ajiyar
zuciya daddy ya sauke yace to madallah Allah ya dawo dashi lafiya.
Ameen sukace dukkansu kafin kuma shiru ya
ratsa palour ' n.
" Shukra
ce ta katse shirun ta hanyar cewa daddy daman inason magana da kai.
"Dawo da
kallon sa yayi kanta sannan yace ina jinki.
" Daddy so
nake asamomin Aiki in dinga zuwa da xaman gida, kaga duk kawayena damuka gama
service aiki suka samu.
"sbd
kawayenki na aiki shine kema xakiyi Ammii ta tamabeyata.
" A a Ammii
gani nayi da zaman gidan ai gwara na dinga zuwa aiki ko.
"To shukra
ae alhakin aikinki ba a hannu na yake ba mijin ki keda ikon samo miki aiki
baniba.
" To daddy
kamishi magana dan Allah ta fada kamar zatayi kuka.
"In banda
abinki shukra ae kin fini kusa da safeer ke yakamata ki tamvayeshi, kuma bama
wannan ba yana iya yiwuwa in tamabyeshi kuma bayaso amma ya amince sbd ni na
tamvaya baxe iya cewa a a ba kuma Kinga ae na shiga hakkin sa ko, Amma idan ke
kika tamabyeshi tunda ba tsoronki yake ba xe gaya miki gaskiya in yana so ko
baya so.
"To tace
tana goge kwallar data cika mata idonta.
Shiko daddy
yana gama maganar sa ya tashi ya shige dakinsa.
Ammii ce ma ta
tsaya tana bata baki kantayi hkr ta tambayi mijinta inya bari to, in be bari bq
kuma sai ta hkr.
6:00 pm safeer
ya tashi daga aiki yana cikin tattara files din dake gabansa abokinsa ya shigo.
"Gaisawa suka shiga yi kafin Abokinsa ya zauna,
" safeer wae
ya naganka haka ne so silent inji haiydar.
"Bakomai
safeer yace yana dauke kansa daga kallon haiydar.
" Da komai safeer sai dai in baxaka
fadamin ba, amma a gani na be kamata ka boye min komai a yadda muke da kai Amma
bakomai in bakason fadamin bazan matsa mk ba.
"ka gane
haiydar wallahi kwata kwata banida kwanciyar hankali tunda akayi auren nn, na
dauka bayan auren komai xe dai - daita ashe tashin hnkl ma yana gaba.
" Haba
safeer ynx akan wnn ka tayar da hankalin, maxa fa gwagwarmaya aka sansu dashi,
ae kai da kanka xaka jata a jikin ka ka mantar da ita cewa AUREN BAZATA aka
yimata ka koya mata sonka bawae ka tsaya zuba ido ba.
" Ta yaya
haiydar? Taya zan koya mata sona, bayan tunda akayi bikin yau sati biyu knn ban
taba sata a ido na ba sai yau, beside ma she is arrogant as a dethroned chief,
she is feeling herself because she comes from a very influensive family. Thats
why she's doing what she want to me, Amma bakomai idan munada rabon farinta ran
juna watarana sai mu faranta idan kuma bamuda shi sai Allah ya kawo mana
mafita.
To Allah ya
kyauta haiydar ya fada yana mikewa.
Mikewa shima
yayi yana cewa Ameen suka a tare inda safeer ya nufi gidansu shukra kai tsaye
bayan ya tsaya a well care ya musu shopping.....
7:30 pm safeer ya isa gidan shukra bayan yayi parking motar
sa ya fito ya nufi cikin gidan rike da shopping din daya yi musu.
"Dukkansu a palour ya samesu, durkusawa yy har kasa
suka gaisa da daddy sannan Ammii.
"Bayan kamar
10mints suka fito gabaki daya don musu rakiya, har gaban motar su suka rakasu
Ammii na dada yiwa shukra nasiha kan tabi mijinta.
" uncle zan
biku "
" A a Areef gobe akwai skul ka bari ran friday zanzo
sai mu tafi"
To kadai yace ya
koma cikin gidan ransa a bace don ba hk yaso ba.
Minti talatin
ne yakai su shukra gida bayan safeer yayi parking ne duka suka fito kowa ya
nufi dakinsa.
"To washe
gari safeer gidansu yakai shukra daze tafi office.
" Da murnar
Mamah ta tare ta, bayan ta gabatar mata da abun motsa baki ta kira mata Aysher
ta fice ta basu guri
"Hira sosai
sukeyi da Aysher anan ta gane Aysher nada kirki aranta tace dukansu suna da
kirki da son mutane sosai.
" Aysher wae
ina miemie ne "
" miemie taje skul amma ynx xaki ganta ta dawo
sbd suna exams ne"
"To Allah ya
dawo da Ita lafiya"
"Ameen
Aysher tace" sannan suka cigaba da hirar su.
"Ko da
lokacin girki yayi ma tare sukayi da shukra kasancewar shukra ta iya girki
sosai.
"
12:14miemie ta shigo cikin gidan da gudun ta kamar an jefo ta aiko tana ganin
shukra tayi gurin da gudu ta fada kanta tana murnar ganin ta.
"Itama da
murnar ta take tamvayar ta" ya exams "
" Exams Alhamdulillahi
Aunty, ina ya safeer?
"Yaje office
miemie"
"to kawae tace sannan tashiga cikin don yin wanka.
08:40 safeer
yazo ya dauki shukra inda Mamah ta cika shukra da tsaraba suka rakasu har gurin
mota.
"Aunty shukra
xan biki miemie ta fada a hnkl yadda bazasuji ba
" To jeki debo
kayanki mu tafi "
" Aunty Mamah
bazata bari ba sbd skul "
" To kiyi hkr
ran friday zansa ya safeer yazo ya tafi dake kimin week end a chan ko.
"Ihu murna
tasa ta shige cikin gida da gudu.
" Yau ta
kama friday kamar yadda safeer yayi Areef alkawari yaje ya dauko shi bayan sun
sha Fama da Ammii wae baza shiba ze takura musu.
Ko da suka
shiga cikin gidan shukra da miemie da Aysher suka samu a palour suna hira
abinsu.
Dakinsa ya xarce
bayan sun gaisa dasu Aysher don watsa ruwa.
" mamaki ne
ya cika Aysher ganin shukra ko kallon Safeer batayi ba ballan tana ma ta gaida
shi.
" Wai dama har
ynx basa zaman lafiya ne? Ta tambaya kanta.
"Ataikace dai
su miemie yini sukayi agidan da daddare safeer ya maida su gida.
11:00pm shukra,
safeer, Areef na zaune a palour suna kallo, safeer ne ya mike yayi wa Areef sai
da safe sannan ya wuce da kinsa.
" Uncle ni a
gurinka zan kwana inji Areef ya fada yana bin bayan safeer
" To Areef je Aunty tama wanka kazo mu kwanta.
"To ya ce
sannan ya wuce dakin shukra.
" karfe uku
dai - dai shukra ta farka sbd wNi axababben ciwan mara, dama tayi yi ko wani
month, kuka take tayi tana juyi tun tanayi ita kadai a daki har ta saki ihu
wanda ya sa safeer farkawa a gigi ce.
" Da sauri
ya karaso dakin shukra inda ya sameta tanata juyi a kasa.
" jikin sa
har wani rawa yake yana kokari dakata sai jero mata sannu yakeyi.
Haka dai ya daga
ta ya kaita motar sa sannan ya dawo dakinsa daukan key.
"Duk wannan
abun da akeyi Areef be saniba baccin sa kawai yake hakan ne ma yasa safeer be
taba shiba ya dauki key dinsa ya fice da sauri.
Kai tsaye
asibitin Aminu kano ya wuce da ita inda cikin sa a a ka karbeta akayi emergency
da ita.
"kaiwa da
komowa kawae yake a bakin emergency gumi duk ya jika shi, sai tunani yake
azuciyar sa 'wnn wani irin ciwo ne yarinya sai suma takeyi (Don sau uku tana
suma a hanya kafin suxo).
" yana
cikin wannan tunanin ne wata nurse ta fito take gayamasa an bawa shukra gado
takuma bashi list na maganin da ake bukata.
" sai asuba
bayan safeer ya dawo daga mosque ne yasamu ganin shukra.
"koda
yashiga cikin dakin idonta biyu tana ganishi ta dauke kai tare D rufe ido kamar
me bacci.
" ya jikin
ki ya tambaya yana xaman abakin gadon.
"Kamar baza
tayi magana ba sai kuma chan tace 'Da sauki'.
" ALLAH ya kara sauki to"
"shiru ne
ya ratsa dakin kafin safeer ya dauko wa yarsa yayi dialing number'n Aysher.
" Bayan sun
gaisa ne yake fadama ta shukra ba lafiya ynx hk ma suna Asibiti.
"Dakin
Mamah ta shiga ta gaya mata sannan ta wuce kitchen don hada musu breakfast.
" Kallon sa
take tanason masa mgn amma takasa.
"shine ya
fahimci hkn a nn ya tamvayeta.
" wani abu
kike so "
" Ammii nakeso ka kira min"
"komai bece B
yashiga dialing number'n Ammii inda yana shiga yamika mata tare da ficewa a
dakin.
" kusan tare
Ammii D mamah suka iso.
"Bayan sun
gaisa ne Mamah ta yiwa shukra ya jiki.
" Da ladabi
ta answer sannan ta gaidasu duka.
"shukra wae
meke damunki ne inji Ammii.
" kamar baxata answer ba chan tace 'ciwon mara'
Baki sake Ammii
take kallon ta da mamaki wae ciwon mara.
"ita dai
tasan in mace na ciwon mara da zaran tayi aure take denawa, likitochi da kansu
suke bada shawarar auradda mace mai ciwon mara.
" to meyasa
har yanzu shukra take ciwon mara, kardai har ynx ba abinda ya shiga tsakanin
yaran nan?
Inko hk ne shukra
zata gane kurenta.....
SAFEER ne ya shigo cikin dakin hannunsa rike da kaya, a
bakin kofa ya ajiye kayan sannan ya karaso ciki ya durkusa kusa da Mamah suna
gaisawa da Ammii cike da ladabi.
"ya me jiki
Mamah ta tambaya"
"Da sauki
Mamah"
"Allah ya kara sauki "
" Ameen suka
hada baki dukansu wajen fada.
"Ammii ina
Areef"
"Areef yaje skul "
To Allah ya dawo
dashi lafiya.
Ameen.
" Safeer bazaka je office bane Ammii ta tambaya?
"Ehhh Ammii
zan zauna Ann!
" A a baza ayi hk ba tashi xakayi ka tafi
inyaso anjima kazo kaji jikin nata inji Mamah.
AE tama ji sauki
inji Ammii Tafada tana hararar shukra, don ita jira take su kebe da shukra ta
fada mata dalilin dayasa taki bawa safeer kanta"
"Tashi kaje
gida kayi wanka ka tafi office kaji dan Albarka cewar Ammii."
"To Ammii
Allah ya bata sauki ya fada yana ficewa daga dakin"
2:40dai - dai
safeer suka shigo shida haiydar hakan ne ma yasa bayan sun gaisa da su mamah
suka fita suka basu guri"
"Gaisawa
haiydar sukayi da shukra cike da girmama juna, sannan haiydar ya ajiye mata
bandir na 100 ya mata sallama suka fito tare da safeer.
" se bayan
magrib sannan safeer ya tafi kai maamah da Aysher gida, sai a nn ne Ammii ta
samu damar kebewa da shukra.
" shukra
"
" Na'am Ammii ta fada ba tare da ta dago ta kalle taba.
"HAde rai
Ammii tayi sannan tace' dake nake shukra dago idonki ki kalle ni"
"A sanyaye
shukra ta dago tana kallon Ammii zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri wane
zata fito don tsoro da fargabar.
" ki fadamin
dalilin dayasa kika kika hana safeer kanki shukra "
" Tambayar
tazo mata a BAZATA dan bata taba tunanin Ammii zata gane ba (Yaro yarone).
"uhmm uhmm
Ammii.... Ke ki kiyaye, ki kiyaye ni shukra ni ba sa'ar bace wallahi.
" kafura ce
ke shukra da zaki dinga tauyewa miji hakki?
"Ashe dama baki daukemu da daraja ba shukra?
" Mu bamu isa
dakeba ashe shukra?
" Wallahi
shukra ki bani kunya ban taba tunanin xakiyi haka ba da hankalin ki dakomai, Ace
mahaifinki ya isa da safeer Amma be isa dake ba ko" karki manta bafa mu
muka haifi safeer ba Amma yamana biyayya amma ke kikasa yimana biyayya shukra.
"A wnn
lokacin shukra kuka take wane dashi aka aikota"
"To ki Sani
wallahi idan mijinki yabi mata alhakin harda ke xa a raba"
"zakiso ace
mijin ki na neman mata shukra?
" Da sauri
shukra ta girgiza kanta alamar bata so "
To wallahi shukra
kiyiwa kanki gata tun baki kaishi bango ba ya sake ki ko ya karo miki aure a
banzaba.
" AUREN BAZATA
hauka ne shukra?
" A a Ammii
dan Allah ki yafe min wlh bazan sake ba dan Allah karki gayawa daddy, nayi miki
Alkawarin "ZAN GYARA KUSKURE NA".
""
Karma ki gyara kinji shukra "
" Ammii dan
Allah kar kiyi fushi dani wlh na dena hali na, insha Allah bazan kara halina
ba.
"Daga nn
Ammii bata kara cewa komai ba, shukra ko kukanta ta cigaba dayi tana me dana
sanin" KUSKUREN DATA TAFKA A RAYUWAR TA "
" kwanan su
shukra uku akayi discharging dinta kuma alhamdulillahi ta samu sauki hakan nema
yasa Ammii tace a wuce da ita gidanta.
"Ammii da
kanta tace safeer ya dinga kula da shan maganin shukra sbd shukra batason mgn,
kuma yayi mata Alkawarin hakan"
"To kullum
safeer shike bawa shukra maganin sbd tunda ta dawo din nn bata rufe kofa kuma
har gaida shi take yi.
" jiya
shukra ta gama shan maganin ta hakan nema yasa safeer beje dakinta ba kamar
yadda ya saba duk dare.
"shukra ganin
har yanzu safeer bezo ba yasa taji BAZATA iya hkr ba sai taje ta duba shi
saboda yanzu ba lefi ta dan fara sabawa dashi kasancewar har hira yana dan
yimata inyaje bata magani.
" Dakinsa ta
nufa kai tsaye gabanta na faduwa dan bata san ya zai dauki xuwan nata ba.......
0 comments:
Post a Comment