"Sun dade sosai sunayin sallar, sunawa kansu addu 'ar
samun zaman lafiya, Bayan sun idar ne Safeer ya fuskanci Shukra ya fara mata
Tambayoyi akan Addinin ta kuma Alhamdulillahi yaji Abinda yake sonji, kasan
cewar Shukra Ma' abociyar Addini ce "
" Tashi ki kwanta kinji Shukra "
" To tace sannan ta cire Hijab dinta ta hau gadon ta
kwanta "
" Sai da Safeer ya karayin Sallah raka 'a Biyu ya kara
rokon Allah kan ya basu zaman lafiya sannan ya musu Addu' ar samun zuri'a
dayyiba"
"Daf da Shukra ya kwanta har tana iya jin numfashin sa
akan fuskarta, Hakan ne yasa ta Runtse idonta sosai "
" Shafa kan Shukra yake A hankali har zuwa jikinta,
Sannan yasa bakinsa akan nata yana tsotsa a hankali "
" Wani nishadi Shukra taji tanaji bata masan cewar ta
iya kiss ba sai yau Kawai jitayi ta fara mayar masa da martani "
" Ganin da nayi Safeer na kokarin zame rigar jikin Shukra
ne yasa na jawo musu kofar na dawo palour na zauna "
" 4:00Am inata gyangyadi nafara jin kukan Shukra nace
barin leka ko za a nemi taimako na "
" A zaune Safeer yake yayinda Shukra ke rungume a
jikansa yana aikin lallashi "
" Sannan Shukra kinji kwanta bari na hada miki ruwan
wanka "Ya fada yana kwantar da ita"
"Toilet ya nufa ya hadawa Shukra ruwa me zafin Gaske
yasa Dettol a ciki sannan ta fito"
"Cak ya daga Shukra be direta ko inaba sai cikin ruwan
zafin, Ae Shukra najin ta A ruwan zafi ta Kankame Safeer sosai hade da Sakar
masa kuka sosai "
" Hankali tashe shima ya kara Kankame ta yana mata
sannu "
" Kiyi hakuri kinji Shukra in kika shiga ruwan zafin nn
zaki dena jin zafin kinji "
" A hankali ta gyada masa kai hade da runtse idonta
"
" Sai da Safeer ya gama Gasa Shukra sannan ya hada mata
ruwa ta tsarkake kana, ya dauke ya maidata kan gado wanda dama ya changer bed
shirt din tun tana wanka"
"Toilet din ya koma shima yayi wanka sannan ya fito ya
kwanta a kan gado ya jawo Shukra jikinsa yana lallashinta yana kuma gaya mata
How sweeter she is "
" A haka dai bacci ya kwashe su dukansu, Sai Asuba
sannan suka farka "
" Daga ta yayi Cak kamar dazu ya kaita toilet ya zaunar
sannan ya zuba mata ruwa tayi Alwala "
" Jiransa tai yayi Alwalar shima sannan suka fito tare,
Shine ya shimfida musu abin Sallah ya daukowa Shukra Hijab tasaka sannan ya
tada Ikama "
" Sai da su kayi Nafila raka 'a 2 sannan sukayi Sallar
Asuba, kafin suka koma gado suka kwanta rungume da juna "
Shukra ce ta fara yin bacci ta barshi yanata tunanin Daren
jiya, Yayi matukar farin ciki da ya samu shukra virgin, Dama yasan Shukra
kamila ce ya kuma sa ran samun budurcinta"
Sai gurin 11:15Am suka farka Shukra ce ta mike tana takawa a
hankali kamar wata me koyan tafiya tayi hanyar kofa "
" Riko hannunta yayi yana tambayar ta inda zata "
" Zanje kitchen ne ta fada masa kanta a kasa don wani
kunyarsa taji tanaji, Batajinma zata iya hada 👀dashi "
" No kibarshi kawai ki koma ki kwanta zansa Aysher tayi
mana breakfast din ko Miemie sai ta kawo mana"
"A a ba sai ka basu wahala ba zanyi da kaina"
"Sai yaji ta burgeshi sosai ya kuma kara mata matsayi a
zuciyarsa "
" Haba Shukra kinfa gaji taya zakiyi wani girki, Tunda
nace zansa Aysher tayi ki hakura kawai "
" Gani tayi bazata iya cigaba da musu dashi ba saboda
wani zazzabi daya ke neman rufe ta sai kawae ta cire hannunta a nasa ta koma
kan gadon ta kwanta "
" Parlour ya fito ya zauna sannan ya kira Aysher ya
fada mata tayi musu breakfast ta aiko miemie dashi Shukra batajin dadi"
"Bayan kamar minti Arba'in Shukra ta fito daga wanka
kenan sukaji ana knocking a kofar parlour "
" Safeer ne ya mike daga kwancen da yake ya fita ya
bude kofar, Miemie ya gani tsaya a bakin kofa rike da basket "
" Karban Basket din yayi sannan yace 'ki gaida Mamah
yana kokarin rufe kofar "
" Shammatar sa tayi a shige parlour' n tana masa
dariya, Ae da sauri yayi kanta yana cewa'Zo ki fita malama "
" Da gudunta ta kara sa dakin Shukra ta sameta kwance a
kan bed ta lumshe idonta kamar me bacci "
" Aunty wai bakida? Ko dai haihuwa zakiyi ne ta fada
tana shafa cikin Shukra tana neman baby"
"Mikewa Shukra tayi zaune ta cire hannun Miemie dake
kan cikinta "
" Miemie ina Mamah?
"Tana Gida tace na gaisheki "
" Ina Answer wa "
" Miemie Harda kara matsowa kusada Shukra tana
tambayarta
'Aunty wae inji Anty Aysher wae bakida lafiya?
'Aunty ciki ne da k..... "
"Shigowar Safeer ne ya katse wa Miemie surutun ta"
"Har gaban Miemie yazo yaja kunnenta har sai da tayi
kara yace
"Wae me
yasa bakya jin magana ne, Ba ce miki nayi ki tafi gida ba shine harda fakar ido
na ki shigo da gudu kina min dariya ko"
"Yi hakuri yaya dan Allah Sakar min kunne da zafi fa ta
fada tana goge kwallar data zubo mata, Dan sosai take jin zafin rikon da yayi
mata "
" Bazan sake ki ba sai kin fada min me kike cewa kika
ganni kikayi shiru"
"Shukra ce ta janyo miemie tana goge mata hawayen
fuskarta"
"Kai ya Safeer yanzu kan tazo muna hirar mu shine zaka
sa ta kuka fisabilillahi Shukra ta fada kanta a kasa hk kuma murya can ciki don
sosai take jin zazzabi da ciwon kai "
" Ni Gulman tane banaso shiyasa ya fada yana fita daga
dakin"
"Tare sukayi breakfast din harda Miemie dan dama batayi
ba ta tawo "
" Zazzabin daya rufe Safeer ne yasa shi yin bacci, sai
bayan la 'asar sannan ya farka yayi sallah ya koma bacci"
Ganin duk suna bacci ne yasa miemie tayi musu Tuwon semovita
miyan agushi tasha busashshen kifi da ganda😋, A flask tasa tajera a
dinning sannan ta koma dakin Shukra ta samu bata tashi a bacci ba "
" Kayan jikinta ta cire tashiga toilet tayi wanka, Ta
fito ta shirya sannan ta koma parlour ta zauna tana jiran Safeer ya tashi ya
maidata gida"
"Sai bayan magrib dukansu suka farka inda Safeer ya
jasu sallah dan bayajin ze iya zuwa masallaci "
" Sai da sukayi Dinner ne Safeer yace Miemie ta taso ya
maidata gida dan yasan inya barta zata iya cewa zata kwana"
"Dukansu suka fito harabar gidan, Inda Shukra ta shiga
gaba Miemie kuma baya suka kama hanyar gidan Mamah.............
"Cikin lokacin da be wuce minti Arba 'in ba suka karasa
gidan Mamah "
" A tare suka shiga cikin gidan dukansu inda suka
tararda da Aysher kadai a parlour tana karatun wani hand out "
" Mikewa tayi da fara' ar ta ta riko hannun shukra suka
zauna sannan ta shiga gaida ta cike da ladabi "
" Sama taje ta kira Mamah sannan ta dawo suka cigaba da
hirar su, Bayan kamar minti 3 sai ga Mamah Da Abbah sun sauko a tare "
" Shukra ce ta sauko daga kujerar da take suka shiga
gaisawa da surikanta Kanta na akasa, Sannan Safeer ma ya gaisa da iyayen sa
"
" Shukra ya jikin "Mamah ta tambaya
" Jiki Alhamdulillahi ae naji sauki "
" To Allah ya kara lafiya "
" Ameen suka ce dukansu kafin Aysher ta tashi ta kawo
wa Shukra ruwa da lemo "
" Da kinbarshi ma Aysher muda zamu tafi yanzu ta fada
kasa _ kasa kuma a kunyace"
"Lah bakomai Wallahi Aunty "
" Bayan kamar minti goma Safeer ya mike. Yana duba
agogon hannun sa
"Tashi mu tafi Shukra dare nayi fa"
" a a kabarta Anan mana tadan kwana biyu tunda bata jin
dadi "Inji Mamah"
"Jiyayi zuciyarsa tabada wani Dum, Aiko ya hade
rai A a Mamah dan Allah ki bari mu tafi
ae taji Sauki ya fada yana Riko hannun Shukra "
" To marar ta 👀 cewa akayi ra 'a rike tane wae
kake wani cin Magani "
" Ba hk bane Mamah nima fa banida lpy ina bukatar
kulawar ta nima dan Allah kiyi hakuri "
" Miemie! Miemie dauko min key din dadin Safeer kizo ki
bude masa "
" Mamah tace sannan ta juya tana kallonsa "kai ma
sai ka zauna a nn din a kula daku gaba daya tunda bakada lafiya"
"Komawa yayi ya zauna hade da dafe kansa yana magana da
zuciyarsa
"Mamah
BAZATA gane irin son danakewa yarinyarnan bane tayama zan iya barinta ae inma
yazama dole ta zauna nima ko zama zanyi"
"Abbah ne ya kalleshi sannan ya dawo da kallon sa gun
Mamah.
"Mamah ki barsu su tafi mana tunda ta samu sauki ko,
Kuma shima yace bayajin dadi yana bukatar kulawar tafa "
" Aiko ko zasu tafi sai dai suje da Miemie ko shara da
wanke wanke ta dinga tayasu tunda basuda lafiya "Inji Mamah"
"Safeer ne yayi saurin dawowa kusa da Mamah 'Dan Allah
Mamah ki barta baseta jeba, (Shi harga Allah bayason zuwan yarinyarnan gidan
sa)
"Sai fa taje, In ko BAZATA jeba sai dai kabar Shukra
anan, Dan ba ta yarda za a bar me yaron ciki tana wahalar da kanta "
" A zuciyarsa yace kowa yace mata Shukra cikin da ita,
A fili kuma yace To naji Mamah amma dan Allah ki bamu Aysher wannan yarinyar ba
abinda zatayi mana wallahi "
" Bawani nn kaidai kawae baka so najene amma naga yau
ni nayi muku dinner akaci ana santi Miemie tace tana hararansa "
" Pillown kujera ya jefa mata sannan yafara magana yana
huci (wai shi ransa ya baci) "
" Yaushe nafara wasa dake wae miemie, wallahi zan gyara
miki zama, mayyata kawae nace bazaki kin dage sai kinje "
" Kome zakace sai dai kace amma saita je Mamah tace
sanda tamike tayi hanyar room din su Aysher dan hadawa Miemie kayan tafiya
"
" Yi hakuri kaji Safeer addu 'a zakayi mata Allah ya
shirye ta inji Abbah "
" Yanzu saboda Allah Abbah yarinyar nan abinda take ya
dace shekara goma sha biyu ae ba wasa bane, Ita Aysher sanda tana shekarun
Miemie haka tayi wallahi sai na gyara mata zama in tazo gida na "
" Hakuri zakayi Kaji Safeer kidinga yimata fada da
nasiha amma banda duka "
" Fitowar Mamah rike da trolley ne miemie na biye da
ita yasasu yin shiru, Miemie sai dariya takewa Safeer shi kuma yana watsa mata
uwar harara, Aysher da shukra ma dariya suke "
" Mikewa sukayi dukansu suka fito dan yimusu rakiya,
sai da motarsu ta fita daga get din gidan sannan su Mamah suka koma "
8:20pm suka karasa gida Safeer ne yafara shiga gidan sannan
shukra janye da trolley 'n miemie a bayanta kuma miemie ce sai muxurai take
tasan haduwarta da Safeer ba sauki"
"Sai da Shukra takai Miemie dakinta ta sata tayi wanka
ta fito ta shirya ta kwanta ta yi mata add' a, ta kashe mata switch din dakin
sannan tayi dakin Safeer "
" Sanda ta shiga ta tarar har yayi wanka yayi bacci,
Wankan itama tashiga inda bata wani dau lokaci ba ta fito tayi joining Safeer a
bed "
" Karfe 3:00dai dai zazzabi ya damu Safeer ya tashi
yana ruwan sanyi, Bayan son ya tashi Shukra shiyasa ma ya sauka akan bed din
"
" Kamar ance Shukra bude idonki ta farka ga mamakinta
bataga safeer akan bed ba sai tayi tunanin ko toilet ya shiga "
" Bayan kamar minti biyar ta mike da niyar zuwa toilet
din ta duba shi, can ta hangoshi kwance akan center carpet "
" Da sauri ta karasa gurin shi ta da goshi ae batasan
sanda ta sake shi ba saboda wani xafi da taji jikinsa yayi (tsaf za a gasa
masara tsabar zafin da jikinsa yayi lols) "
" Sai sannun take jera masa duk tabi ta ruda kanta
"
" Shukra ki kwantar da hankalin ki zazzabi nefa kawai
"
" Ya Safeer zazzabi ne kawae fa kace "Ta fada tana
mikewa ta shige toilet"
"Hannunta rike da wani dan karamin farin towel da kuma
wani bowl cikeda ruwa ta fito takaraso wajensa"
"Dago kansa tayi ta dora akan cinyarta sannan ta cire
singlet din jikansa ta sa towel din a ruwan ta matse sannan ta fara goge mai
jikinsa "
" Haka ta dinga yi masa har sai da taji jikinsa yayi
sanyi sannan ta maida bowl da towel din toilet "
" Ko kafin ta fito har Safeer yayi bacci a gurin, Ganin
bazata iya maida shi kan bed din ba ne yasata kwanciya a kusa dashi da daura
kansa a Hannunta (Yadda akewa yaro in xeyi bacci) Ai bata wani dade ba baccin
ya dauketa itama "
" Da asuba safeer ne yafara tashi shi kwanciyar tasu ma
dariya ta basa kamar wani danta"
"Sai da yayo alwala sannan ya dawo gurin Shukra, Daga
ta yayi a hankali yadda bazata firgitaba "
" A hnkl take bude idonta akan Safeer, Murmushi yake
mata itama haka, Addu 'ar tashi daga bacci yashiga karanto mata, Binsa tashiga
yi har suka gama sannan ya rakata har bakin toilet din ya dawo yana jiran
Fitowar ta "
" Sai da je tashi Miemie tasata yin Alwala sannan suka
dawo dakin safeer yasasu Sallar "
" Duk su ukun a gurin suka kwanta sai gurin 9:15 shukra
ta tashiga tashiga toilet don yin breakfast "
" Ruwan zafi ta dafa tasa cikin tea flask ta debo kayan
tea ta jera su a dinning sannan ta dawo kitchen tafara musu Gireba, wadda zasu
hada da tea"
"Bayan ta gama ne taje ta tashi miemie ta hada mata
ruwan zafi tasata wanka, Sannan itama tashiga wanka a dakin Safeer "
" Bata fito ba sai da shima ta hada masa ruwan wankan
sannan ta fito ta tarar ya tashi a bacci ma "
" Ya safeer ka tashi lafiya "
" lafiya kalau "
" Ya karfin jiki kuma "
" Alhamdulillahi "
" Masha Allah, ka shiga na hada maka ruwan wanka "
" To nagode Shukra Allah yayi miki Albarka "Ya
fada yana shiga toilet"
"Wata Ash colour jallabiyya tasa ta daura bakin
dankwali tashafa powder da maroon lipstick ta fito parlour tasamu Miemie suka
fara hira abinsu "
" Dukansu nagani a kan dinning suna breakfast Miemie
nayiwa Shukra labarin Haiydar sunata dariya abinsu "
" wayar Shukra ce ta fara ringing, Duk suka juyo suna
kallon wayar sai da Shukra ta fasa ihu sannan ta dauki wayar "
" Hello Neesa luv "
" Bawani Neesa luv
munafika kinyi Aure kin manta mutane ko"
"Haba dae Aneesa ni na isa na manta ki ne, kiyi hakuri
dan Allah tafada kamar zatayi kuka"
"Ke kika Sani, Dama fada miki zanyi anjima zamuzo sai
kimin sending address naki"
"Yanzu ma kuwa shukra tafada cikeda murna, Baki fadamin
kedawa zaki zo ba"
"Ni da DR. Sumayya wannan wadda ta tafi sudan din
"
" Na ganewa, Dawa kuma?
"Da soofy galadanchi, Da Aysher bichi, da Aunty Ameena
kaura, Da Eeshatullah da fancy da Ma sultan da Aunty sis da meela adeel "
" Ihu ta saki ashe yau inada manyan baki a gidan, ME
kuke so na girka muku "
" Bamuda zabi mudai inji Neesa "
" Yawwa Neesa naji kamar kince da meela adeel za a zo
"
" Eh meye"
"Dan Allah ki rufa min asiri kar tazo tamin snatching
Irin yadda taso tayi wa Ruky mama "
" Hhhh ni ban iya rashin mutunci ba bazan iya cewa
bazamu zo da ita ba, Kema da kinsan irin rokon da ta dinga min azo da ita da
baki ce hk ba "
" jiki a sanya ye SHUKRA tace to Neesa luv sai kunxo,
Ta kashe wayar tana bawa Safeer labarin yau sunada Manyan baki a gidan "
" Tare suka shiga Kitchen ita da Miemie, steamed cous -
cous da Egg sauce suka farayi sannan sukayi fried rice sukayi Banana, coconut
and pineapple Drink suka sa a fridge sannan Shukra tashiga wanka don sun mata
waya sun tawo, Tabar Miemie tanayin liver sauce...........
"Bayan kamar minti goma Miemie ta gama liver sauce din
ta shige toilet don yin wanka ita ma "
" Shukra da Miemie ne kadai a parlourn suna kallo kuma
suna jiran zuwan Manyan bakin su "
" Knocking din dasuka ji a kofa ne yasasu mikewa
dukansu suna rige rigen bude kofar, Shukra ce tayi nasarar bude kofar ae ko sa
Aunty sis ta fara cin karo, Rungumeta tayi tana murnar ganinta don she really
missed her "
" Basu guri tayi suka shigo parlourn suka zauna, Meela
se karewa palour kallo ake, Miemie ce ta durkusa har kasa tana gaida su daya
bayan daya "
" Shukra ce ta shiga kawo musu drinks da bottle water,
Bayan sun gaisa da shukra kuma sai suka tsinke da hirar yaushe gamo"
"Shukra a ina kk aiki ne "Soofy ta tambaya"
"Ke ni bana wani Aiki, Aikin gidan miji na nake "
" Shukra knn meyasa bazaki sa ya nema miki aiki ba ko a
nn Maryam clinic ne da kuke kusa "
" Ke nifa Aikin ya fita a raina, Amma dae zan gwada
"
" Sai bayan zuhr prayer sannan Miemie ta Fara kawo musu
Abinci, Neesa ce tayi service nasu suka fara ci suna santi (Kunsan ni na koya
ma Shukra girki dole suji dadin sa) "
" Shigowa Safeer yayi da Sallama a Bakinsa ya durkusa
har kasa yana Gaida Aunty sis, Bayan sun gama gaisawa ne kuma su soofy
Galadanchi, Neesa luv, DR. Sumayya suka fara gaida shi cike da ladabi, Sosai ya
yaba da Hankalin kawayen Shukra "
" Meela dai batasan sanda glass cup din hannunta ya
fadi kasa ba gurin kallon Safeer (Snatcher anga HANDSOME guy 🤣) "
" Juyowa sukayi dukansu suna kallon meela da mamaki,
Shukra ko hade rai tayi tana kallon Meela kafin ta juya taja Hannun Safeer ta
shige Bedroom dinsa dashi "
" Meela wae har ynx kina nn da halinka saboda Allah, ki
sa Mutum a gaba da kallo har da fasa cup inji Aneesa Rai a bace "
" Nan dai suka sa Meela a gaba suna ta mata fada, Aunty
sis tace suyi shiru duk sukayi kuwa "
" Nasiha tashiga yiwa Meela me ratsa jiki,(Uwar Arziki)
Har kuka sai da Meela tayi tana bawa Aunty sis Hakuri tana kuma tabbatar nata
ta dena Halinta "
" Hade rai tayi tana watsa wa Safeer harara 'Ya safeer
ba seda nace karka dawo gidan ba sai sun tafi, Amma shine ka dawo ko?
"Haba Shukra me yayi zafi wae haka nifa zuwa nai mu
gaisa da Aunty sis "
" Bata kara cewa komai ba ta juya ta fice tana
huci"
" Shukra ce ta fito tana huci taja Hannun Meela ta
turata waje sannan ta nuna ta da dan yatsa 👉🏻kada ki kuskura
koda wasa ki kara zuwa gidan Daga hk ta rufe kofar ta ta dawo suka cigaba da
hirar su da kawayenta "
" Sai da sukayi sallar La 'asar sannan suka tafi inda
Shukra ta cikasu da tsaraba, Suka tafi suna murna, Suna fita Soofy Galadanchi
ta dawo tana tanbayar Shukra ta koya mata yadda ake Garnished cous - cous
"
" Karki damu Soofy anjima mu hadu online zan koya miki
"
" Godiya tayi mata sannan tafice inda ta samu suna
jiranta, daga nn suka wuce gida "
" Tunda Shukra ta shiga daki bata fito ba sallar Magrib
ma a daki tayi ta har ynx bata gama hucewa ba kan abinda Safeer yayi mata, Tace
kar ya dawo saboda tana kishinsa bataso wata mace ta kalleshi, Office ma da
dahali da ta hanasa zuwa, Amma sai da ya dawo "
" Da sallamar sa ya shiga dakin Shukra ya hango ta can
karshen gado ta kifa kanta jikin pillow da alama kuka take "
" Da sauri ya karasa kan bed din ya dagota ya Rungume
tsam a jikinsa yana bubbuga bayanta "
" Batayi wani yunkurin kwa cewa ba sai ma kara kankame
shi da tayi don dama hakan take bukata a halin yanzu, So kawai take ya
lallasheta ya bata hakuri ko taji sanyi a ranta "
" Yi hakuri kinji Shukra cute, Kidena zubar da
hawayenki a banza bayan nace miki Mazaunin mace HUDU kike a gurina, Ba wadda ta
isa na kalleta bayan inada ke, Cry no more swthrt kinji "
" Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki batasan sanda
murmushi ya kubuce mata ba, Ta wani kara narke masa "
" Nagode Ya safeer "
" Murmushi shima ya sakar mata ya shafa fuskar ta yace
'Ashe kina sona har haka Shukra, irin wannan kishi Haka "
" Harara ta watsa masa irin ta wasan nn sannan tace'
waye yace maka ina sonka "
" Kishin da kika nuna da kuma kukan da kike kan wata ta
kalleni yasa nagane kina sona "
" Hannayenta Biyu tasa ta rufe idonta cike da kunyar
sa, tana dariya kasa kasa "
" Dagata yayi suka sauko daga bed din suka fito parlour
hannunsa rike dana Shukra "
" Sai zuwa 10:00pm suka tashi Miemie tayi dakin Shukra
sukuma sukayi dakin Safeer don yin Bacci "
" Washe gari Wajen 12:00am bayan sun gama breakfast
Shukra tace zata Gidan Ibteesam, Tare suka tafi da Miemie suka bar Safeer kadai
a gida yana cigaba da Aikin Construction na company da yasamu "
" Wayarsa dake kan center table ne tashiga ringing,
Karasawa yayi ya dauka da Sauri ganin Haiydar ne me kiran "
" Assalamu alaika Haiydar ya kk ya Hajiya "
" Lafiya kalau muke Safeer me kirki cikin kwanta goman
da kayi kana hutu baka taba kirana a waya ba koda wasa, Amarya ta mantar da kai
mutane ko"
"Eh ta mantar din in kayi zuciya kaima kayi AUREN
"
" Karka damu nanda Shekara uku zanyi Aure Miemie nayin
Graduation (Candy), "
" Ka wahala wallahi Haiydar lokacin ina nn da dan yaro
ma "
" Kai ka Sani nidai AUREN SOYAYYA zanyi ba AUREN
BAZATA Haiydar ya fada yana dariya
"
" To sai me ae AUREN BAZATA Alheri ne, duk wanda beyi
Auren bazata ba ae be ji dadin Aure ba wallahi "
" Hhhhhhhhh a hakan "
" Nidai yanzu ba wnn ba jiya mutumin daya baka Aikin
Company a san Francisco yaxo munata kiranka bakayi picking ba, So yace next
week yakeso a fara Aikin so saika zama cikin shiri ko"
"Eyya kuyi hakuri kunsan in ana tare da Amarya ba a iya
komai amma insha Allah zan kirasa muyi magana "
" Kai ka Sani jibi dai zaka dawo Aikin ae inji Haiydar
wanda yana gama fadar hk ya kashe Wayarsa "
" A nn Safeer ya kira mutumin suka gama mgn kan Next
week ze tawo san Francisco "
" Sanda su Shukra suka dawo Safeer ya basu labarin
komai, Zo kuga tsalle gurin Miemie za aje inda ba 'a taba zuwaba ko a mafarki
"
" Ke kuma Ihun me kike hk, To ba inda zani dake Anan
kinzo kin shiga rayuwar mu shine kike so ki bimu can a cigaba da samana eyes ko
"inji Safeer yana hararan Miemie"
" Fasa masa ihu Miemie tayi ni wallahi sai kunje dani
"Shukra dai batace komai ba sai kallonsu take
" Baki sake Safeer yake kallonta, Wani sabon salon
iskanci ne wnn kuma Miemie? To wlh zakiyi kuka me dalili kinji ya fada yana
murde mata bakinta "
" Shukrah ce ta janye ta tana lallashinta "
" Kai ya
Safeer dan Allah kawai kasata kuka ana zaune kalau, In bazaka jeda itaba kace
bazani da keba ba saika sata kuka ba "
" komai beceba sai daukan car key dinsa da yayi ya fice
daga gidan ya tafi gidan Mamah ya fada mata, Sosai suka tayashi murna tare da
yimasa fatan alkhairi "
" Bayan yabar gidan Mamah gidan Ammii ya wuce wanda
cikin sa 'a ya tarar da Daddy, Nan suma yayi musu bayanin tafiyar sa sukayi
masa Addu' a sannan ya dawo gidansa ........
"Yau ta kama Monday kuma yau Safeer ze koma Aiki saboda
hk Shukra tunda tayi sallar Asuba bata koma ba tashiga Kitchen don hada musu
breakfast "
" Sweet potato ta soya tayi egg sauce sannan dafa ruwan
zafi tasa a tea flask ta jera a dinning sannan ta shiga dakinta donyin wanka
"
6:50am Safeer ya turo dakin Shukra cikin shirin sa na fita
office, Ita kuma lokacin ta fito a wanka knn tana shafa cream a jikinta"
"Wae har ka shirya ya Safeer ta fada cike da Mamaki
"
" Eh mn zokiyi serving dina breakfast na wuce sauri
nake yau Ahmad zezo "
" Waye Ahmad kuma "
" Wanda zanyiwa Aikin company a san Francisco mana
"
" ok, To jirani insa kaya sai inxo "
" To, miemie bata tashi bane ita "
" Eh itada ba fita xatayi meye nata na tashi da wuri
haka, "
To kiyi sauri dae kizo ya fada yana fita daga dakin"
"Bayan Safeer ya gama breakfast sai da Shukra ta rakasa
har mota ta jira ya fita a gidan sannan ta dawo ta fara gyaran gidan "
" 12:00pm Ahmad yazo Office din Safeer kuma sun gama
mgn kan cewa ran friday zasu tawo san Francisco, Sosai yaji dadi yadda Safeer
ya karbi Aikinsa ya kuma yi masa alkawarin zuwa akan lokaci "
" Yau saura kwana 2 tafiyar su Safeer saboda haka yace
Shukra ta shirya kayan Miemie su Maidata Gida da daddare "
" Bata rai Miemie tayi wane zatayi kuka, Sai hararar
Safeer take kasa kasa, karaf suka hada ido "
" Zo nan Miemie ya fada rai a hade "
" Kukan shagwaba ta saki taje ta makale a jikin Shukra
kamar karamar yarinya "Aunty Shukra Kinga yaya ze dakeni ko
" ME kika yi masa Shukra ta tambaya tana kallon Safeer
da Fuskar tausayi (Irin kar ya daki Miemie)
"
" Harara na tayi ya bata Answer yana dauke kai "
" Shukra ta dawo da kallonta kan Miemie wadda take ta
zare ido kamar tayiwa sarki karya, Miemie bakya jin Magana ko kina abun kamar
karamar yarinya, Ya Safeer din sa 'ankine da kike hararar sa?
" A a Aunty Shukra yi hakuri bazan kara ba "
" Kima kara, Shukra ta fada tana jan hannun Miemie zuwa
daki "
" Koda suka shiga dakin kayan Miemie suka hau hadawa,
Sosai Shukra ta yiwa Miemie nasiha kan halayenta, Da alama nasihar ta shige ta
don har kuka sai da tayi tana bawa Shukra hakuri "
" Tun 7:00 pm suka tafi gidan Mamah maida Miemie, Mamah
tayi mamakin nitsuwar Miemie don yan kwana kin da tayi a gidan Safeer sosai ya
ke mata fada, Shukra kuma tayi nasiha "
" Sun dade gidan don se wajen 11:00 su Aysher suka
rakasu mota suka tafi gidansu"
"Washe gari Da Safeer zai tafi Office sai da ya sauke
Shukra a gidan Ammii sannan ya wuce "
" 4:30pm Safeer ya shiga Office din Haiydar da sallama
a bakin sa, Ya samu guri ya zauna yana fuskantar Haiydar "
" Malam wae yaushe zaka fito da mata ne kayi Aure, ko
baka gaji da zaman gidan Hajiya ba?
"sai nan da shekara uku meye matsalar ka?
"Kaga Malam in zaka dawo hayyacinka ka dawo Miemie fa
tayi maka kankanta kabarwa Abdallah kawae ka nemi wata "
" Bazan bar masaba yaje shima ya nema mana inji Haiydar
ya fada rai a bace "
" To na fahimce ka bakada Budurwa ne shiyasa, Ko
kanason Aysher na baka ita "
" Banason ta ni Miemie nake so kuma ko kaine babanta
baka isa ka hanani AUREN taba" Haiydar ya fada sanda ya mike yana tattara
kan table dinsa "
" ni na isa na
hanaka auren Miemie? Allah ya baka Hakuri zo muje gidan Ammii zan dauko Shukra
sai ku gaisa ma "
" To kawai yace sannan suka fito a tare kowa ya shiga
motar sa suka kama hanyar gidan Ammiii "
" Sanda suka je gidan Ammii ana kiran sallar Magrib
saboda haka basu shigaba sai da sukayi sallah a wani masallaci kusada gidan
"
" Sai bayan sallar isha sannan suka baro gidan Ammii,
Areef harda kukansa (Kukan rabuwa) "
" Washe gari Safeer beje Aiki ba fita yayi yayo musu
siyar yar duk wani abu dayasan zasu bukata kuma bazasu samuba acan "
" Da yamma wajen karfe biyar Safeer da Shukra kwance
akan gado rungume da junansu suna hirar su ta masoya akayi Knocking a kofar
parlour "
" Safeer ne ya mike yasa rigarsa sannan ya fice don
duba waye "
" Yana bude kofar yaga wata yarinya kamar Shukra take
da yarinya a hannunta, Yarinyar na ganinsa ta fara mika masa hannun alamar ya
dauketa tana kiransa da Daddy"
"Hannu yasa ya karbeta sannan suka gaisa da Mamanta,
Guri ya bata ta shigo parlourn sannan ya wuce bed room din Shukrah don kiranta
"
" Da fara 'a dauke a Fuskar ta ta karaso parlourn
"Sannu da zuwa Ibtee, ya Gida ya Amal?
" Lafiya kalau muke, ae Amal fushi take dake tunda kin
dena zuwa gurinta "
" Eyya Amal tayi hkr tana raina wlh, Naga ta makale wa
ya Safeer kamar ta sanshi "
" Ae da alama mijin kin nn yana son Yara da yawa,
Yaushe za haihu ne Ibtee ta fada tana neman daga rigar Shukra "
" Rike Hannun Ibtee Shukrah tayi tana dariya, Ke ni
banida ciki fa "
" Zama ki fadi gsky ne "
" Daga nn Shukrah ta mike ta kawo wa Ibtee lemo da ruwa
"
" Sai da aka kira sallar magrib sannan Safeer ya kawowa
Ibtee Amal yawuce Mosque, itama gidanta ta tafi"
"Zuwan Ibtee ne ya hana Shukrah hada musu kayan su sbd
hk bayan sun gama cin abinci sunyi sallar isha shukra ta shiga daki don hada
musu kayan "
" A tare suka hada kayan da Safeer sannan sukayi shirin
bacci don jirgin karfe bakwai zasu bi "
"Safeer ne ya musu addu ' a ya tofe musu jikinsu sannan
suka kwanta rungume da juna"
"Yimin labari me dadi Shukrah, Safeer ya fada mata a
kunnenta "
"Ya Safeer ni ban iya lbr ba sai dai kai ka yimin,
Shukra ta fada kasa kasa"
"To zan miki wani iri kike so "
" Kowanne ma "
" Nan Safeer ya fara mata labarin cikin kunnenta "
" Sai dariya Shukrah take kyalkyalawa tana kara shigewa
jikinsa, a takaice dai sai da Suka raya daren ranar, "
" Tun kafin Asuba Suka farka sukayi wanka sukayi nafila
suka jira sallar Asuba, Tea kawae suka sha suka sa kayan su a booth suka tafi
gidan Mamah "
" Aysher da Miemie suka dauko sannan suka wuce Airport
"
" Jiran minti goma sukayi sannan aka kirasu, Suka wuce
suna daga musu hannu, Zo kuga kuka gun Miemie harda birgima a kasa wae kar
Shukrah ta tafi ta barta "
" Aysher ce taja motar ta maidasu gida har amotar
Miemie kuka take, suna zuwa gida ta kwanta a parlour sai bacci.......
"Cikin jirgi Shukra sai bacci takeyi daga Zaunen da
take, Safeer ne ya kwanto da ita jikinsa dan tafi jin dadin baccin"
"Ko da aka kawo musu abinci ma be karba ba don yasan
Shukra bazata ciba, kuma dama shi bayajin yunwa, Cigaba da Aikinsa yayi har
suka isa San Francisco "
" Jirginsu na landing Shukra ta farka tana raba ido,
Mikarda ita safeer yayi suka sauko a tare "
" Wayarsa ya dauko ya shiga dialing number Ahmad, Wanda
tana fara ringing ya dauka don dama sunyi waya da safeer ya fada masa sun kusa
sauka "
" Mota Ahmad ya dauko yazo ya samesu a zaune kan
resting chairs na airport din, safeer na ganinsa ya mike da fara 'arsa sukayi
musabaha kafin suka gaida da Shukra "
" Nan ya kwashi trolley dinsu yasa a mota suma suka
shiga suka kama hanyar gidan sa "
" sun samu tarba ta musamman gurin matarsa Azeeza, Yar
Nigeria ce itama, bayan sun ci abinci ne kuma Safeer da Ahmad suka fita dan
ganin inda za a gina Company 'n sukabar Azeeza da Shukra suna hira kamar dama
can sun san juna "
" Har dare basu dawo ba, Abinda ya daga hankalin shukra
kenan sosai take son ganin mijinta, wayarta ta dauka da niyyar kiransa sai kuma
ta tuna batada number sa, Dan karamin tsaki taja kamar zatayi kuka wae batada
number mijinta (Abin takaici) "
" Azeeza ganin dare yayi sosai kuma dawowar Ahmad ba
yanzu ba yasa ta nunawa SHUKRA dakin da zata kwanta, Ita kuma ta shige nata,
Zaman kusan awa biyu Shukra tayi amma shiru Safeer be dawo ba sbd hk ta shige
daki kawai ta kwanta "
" Shiru tayi bayan ta kwanta zuciyar ta cike da tunanin
Safeer, Batajin zata iya bacci ba a jikin Safeer ba juyi kawai take a kan gadon
sam bacci ya ki zuwa, Ahaka dae bacci barawo ya kwashe ta "
" Cikin bacci taji ana shafa ta tai saurin bude ido don
dama baccin beyi wani nisa ba "
" Cikeda shagwaba take kallon sa idonta taf da hawaye
"Ya Safeer
shine kaje kayi zaman ko, Ka barni inata jiranka" Tafada tana fashewa da
kuka
"Jawota yayi jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali
"Yi hakuri
Shukra cute kinki insha Allah gobe bazan dade ba yau dinma dan farko ne bakiga
guraren da mukajeba, Amma wallahi kina raina sai tunanin ki nake"
"Murmushin jin dadi tayi ta kara shigewa jikinsa 'kaci
abinci ya Safeer?
"Naci dazu Shukra yanzu wanka zanyi "
" A tare suka mike suka shiga toilet din ya tsaya a
gefe ita kuma ta hada masa ruwan wanka "Bitayi jefensa zata wuce yayi
saurin rike hannunta"
"Ina zakije kuma ya tambayeta kasa kasa yana kashe mata
ido daya "
" Zanje in fito ma da kayane fa ta bashi Answer tana
kokarin kwace hannunta "
" Kara damke hannun yayi 'ki bari muyi wankan mana
"
" A a ya Safeer nifa nayi tun dazu "
" Ban yarda ba sai kin sake "
" Kasa cigaba da jayayya dashi tayi dan haka kawae sai
ta rufo musu kofar toilet din ta dawo ciki "
" Safeer ne ya shiga ciremata kaya, ita ko kunya duk ta
hana ta sukuni sai sunkuyar da kanta take, haka dae ya gama cire mata kayanta
tsaf shima ya cire nasa ya hau jikata da ruwa "
" Itama jikashi ta fara yi suna dariya abinsu, A hk dae
suka soma wanke junansu wanda tun Shukra na nokewa har sai da ta saki jiki
"
" Safeer na gani ya fito daga toilet dauke da Shukra a
hannunsa kamar wata baby ya nannade ta da towel, Karasawa yayi ya kwantar da
ita a tsakiyar gadonsu sannan yaje inda trolley 'nsu ya dauko cream ya dawo kan
gadon "
" Kunce towel din jikinta ya shiga yi inda Shukra ta
runtse idonta, Shiko ko a jikinsa sai da ya cire mata towel din gaba daya
sannan ya soma shafa mata cream din cikin wani salo me wuyar fassaruwa yake shafa
mata, Shukra dai jinta tayi kamar ba a duniya wani irin abu ne taji yana yawo a
jikinta, batasan lokacin data janyo hannun Safeer ba ya fada jikinta "
" Nan suka shiga kissing junansu cike da kaina wane
zasu cinye kansu, Romancing kansu sukayi tayi kamar ba gobe, Niko ganin haka
yasa na fito na barsu susha love "
" Washe gari tun 7:00am Safeer da Ahmad suka bar gidan
har dare Shukra nata baza ido ba labarin Safeer, Hawaye ne ya cika idonta
tanason ganin Safeer tana tsananin bukarsa, Gashi ta manta bata karbi number sa
ba "
" Ganin kuka na neman cin karfinta yasata mikewa da
sauri tashige daki, Kwantawa tayi kan gado ta rungume pillow tana kuka mara
sauti "
" Karar wayarta ne ya katse mata kukanta, kamar bazata
dauka dan saida yazama missed call ma sannan ta dago wayar ganin Aneesa ce me
kira yasata saurin dialing "
" Ringing biyu Neesa tayi picking
"Hello Neesa
luv ta fada can ciki"
"Shukra Y kk, Ya jikin kuma?
"Jikin me kuma Neesa nace miki banda lafiya ne?
"Muryanki ya fada min bakeba "
" Keni lafiya na kalau "
" uhmm, Yaushe zaki haihu ne Neesa ta tambaya tana
dariya kasa kasa "
" Wani irin Haihuwa ana zaune kalau ae ni sainaci
amarchi na kamar shekara 2or 3 kafin na fara haihuwa "
" Koba shekara biyu ko uku ba Neesa ta tambaya tana
dariya sosai "
" Dariyar me kuma haka Shukra tace wane zatayi kuka
"
" Jinayi kince shekara uku Shukra wa yasani ma ko yanzu
kinanan da katon cikin ki, Zama da kyar tashi dakyar Aneesa ta bata answer
"
" Dogon tsaki kafin ta kashe wayar ta ta kifa kanta
jikin pillow ta cigaba da tunanin other half nata "
" Tanaji Neesa nata kiranta amma batabi takai ba ta
cigaba da tunaninta tana addu a Allah yasa kar yau ya dade kamar jiya "
" To yau kam Su Safeer sun dawo da wuri dan agida
sukayi sallar isha, Bayan sun idar sukaci abinci sannan kowannensu ya shige
dakinsa "
" Shukra bako kunya ta tashi tabi bayan Safeer inda ta
tarar harya shige toilet, Azeeza ma ganin Shukrah ta mike yasata itama mikewa
tabi bayan Ahmad "
" Sai da Safeer ya kira Haiydar sukayi hira sosai,
Sanda sukayi sallama ne Haiydar ya fara tambayar Safeer Shukra "
" Safeer ya dawo da kallon shi kan Shukrah dake kwance
akasa ta nannade kafafunta da nashi kamar mejin sanyi,Gashin kanta ya rufe mata
fuskarta, Hannu yasa ya ture Gashin gefe ya dago kanta, sai anan ya gane ashe
ma bacci take, Nan dae ya fada ma Haiydar Shukrah tayi bacci sukayi sallama,
sannan yayi wa Shukrah addu a shima yayi "
" Sai da Safeer da Ahmad sukayi kwana 5 basa zaman gida
Shukrah har ta fara ramewa "
" Shukrah ce zaune kan abin sallah bayan ta idar da
sallah azahar tana yiwa Safeer addu 'ar kariya, Jin datayi a turo kofar dakinsu
yasata saurin dagowa "
" Ware ido tayi tana kallon sa da mamaki, Tunda sukazo
san Francisco basu taba haduwa da rana ba "
" Fuskarta dauke da Murmushi ta karaso ta rungumeshi
"
" Ya Safeer sannu da zuwa Shukrah tace tana riko
hannunsa, Ta zaunar da shi a bakin gado ta haye cinyarsa bakinta yaki rufuwa
dan dadi "
" Yawwa Shukra na sameki lafiya?
"Lafiya kalau, Ya Aikin?
"Alhamdulillahi, Aiki ma ankusa kammalawa "
" Masha Allah shiyasa yau kadawo da wuri knn"
"Eh mana, Gobe ma bazan fitaba zan kaiki yawo "
" Ihun murna Shukrah ta sa kafin ta mike taje ta hadawa
Safeer ruwan wanka, Bayan ya shiga toilet ne ta fito masa da farar t-shirt da
three quarter ta fesa musu perfume ta zauna tana jiran fitowarsa "
" Shukrah ce kwance kan jikin Safeer da alama bacci
zasuyi "
" Kinsan irin son da nake miki kuwa Shukrah "
" Saurin sa tafin Hannunta na dama tayi ta toshe
bakinsa 'Yi shiru Ya Safeer kayi bacci kaji "Shukrah ta fada tana harar sa
" Harshen sa yasa yana tsotsar tafin hannun nata, Bata
janyeba haka bata hana saba, sai ma kwantar da kanta datayi a kirjinsa hade da
lumshe ido, A haka dae bacci me dadi ya kwashe su............
"Kamar yadda Safeer yayi wa Shukra Alkawari kan cewa ya
yau baze fita ba haka kuwa akayi be fitan ba,"
"Bayan Sallar Azahar ne Safeer ke Sanar da Ahmad yana
so ya fita da Shukra, Ahmad din kuma ya Amince ze zagaya dasu suga garin kamar
yadda Safeer din ya bukata"
"Dukansu na gani a harabar Gidan cikin Shirin su na
fita, Ahmad ya zauna a driver sit inda Safeer ya zauna a gaba Shukra da Azeeza
kuma Suka zauna a baya "
" Mesium ya fara kaisu, Sannu a hankali yake musu bayan
duk abinda suka gani,Bayan sun gama da Mesium ya daukesu ya kaisu San Francisco
state University sosai suka zagaya a cikin University kafin suka fito suka tafi
wani hadadden Restaurant nan Suka ci abinci suna ta hira abinsu, "
" Bayan sun fito ne Shukra taga wani dan Asibiti karami
a gefe tace tanason shiga, Ae kuwa sai da suka shiga aka zagaya dasu, tayi kuma magana da wata
likitan ido inda Shukra ke fada mata Optometry ta karanta, Sosai Doctor taji
dadin Haduwa Da Shukra har tayi mata tayin Aiki cikin Asibitin, Shukra ta mata
bayani kan cewa ita bakuwa ce a San Fancisco Aiki ne ya kawo mijinta, Sun dan
taba hira kadan Sukayi Exchanging phone number daga nn sukayi Sallama Suka bar
Asibitin "
" Koda Suka bar Asibitin ba gida Suka wuce ba Saida
suka ce Bitch suka yi kalle kallensu sannan suka dawo gida da niyyar gobe
zasuje San Fancisco state zoological garden "
" Koda Suka dawo Gidan Sallar isha kawae sukayi kasan
cewar sunyi Magrib nan cikin Asibiti, Kwanciya Shukra tayi bacci me dadi ya
dauketa, Shi kuma Safeer sai da Suka dade da Ahmad a Parlour suna magana kan
Company kafin sukayi sallama kowa ya shige dakinsu "
" Bayan Safeer yayi shirin bacci ne ya kwanta kusa da
Shukra yana ta binta da kallo kamar me Shirin gano wani abu a tare da ita,
Kawai gani yayi ta kara haske tayi wani kyau, Idan har idonsa be masa karya ba
ze iya cewa Shukra tayi kiba, To ko weather garin ta karbeta ne "
" Matsawa yayi sosai ya Rungumeta a jikinsa yana shafa
ta sai yaji jikinta yayi santsi kamar jikin jariri, Ransa yana basa wani abu
sai kawai ya share, Yana addu 'ar Allah yasa hasashensa ya zama gaskiya A haka
dae bacci ya kwashe shi "
" Washe gari gurin sha daya bayan sun gama breakfast ne
suka shirya sai Zoological Garden, Sosai gurin yayi wa Shukra kyau dan ko kusa
bazaka hadasu da na Kano ba don iya shi ta taba zuwa "
" Riko Hannun Safeer Shukra tayi lokacin da Zuwa zo
Gurin lion, Yana ganin su ya fara ihu yana tsalle kamar yana son fito, Shukra
ta kankame Safeer a jikinta ta fasa masa kuka jikinta har wani rawa yake ta
tsorata iya tsorata har bata iya jin abinda Safeer din ke ce mata "
" Sun dau Tsawon lokaci a haka Safeer sai shafa bayanta
yake yana bata hakuri a Ransa kuma yana tunanin wannan irin tsoro na Shukra
"
" Shukrah ce ta fara dagowa daga jikin Safeer ta kalle
shi tana goge hawayen fuskarta
"Ya Safeer mu tafi gida Zazzabi
nakeji"
"Sannu Shukra bari su Ahmad su Dawo sun dan za gaya can
ne ya fada yana jan hannunta suka zauna "
" Riko shi tayi sosai don har yanzu a tsorace take
Shima ganin hakan yasa shi Kwantar da ita kan kirjinsa yana buga bayanta a
hankali, A haka su Ahmad suka dawo suka samesu inda Safeer yayi musu bayanin
komai, Nan dae suka koma gida"
"Shukrah ce ta fara shiga gidan ta kwanta nan palour ta
rufe idonta, A tare suka shigo dukkansu, Ahmad da Azeeza suka shige dakinsu
Safeer kuma ya dauki Shukra cak ya kai daki ya kwantar "
" Sai wajen 3:20pm Shukra ta farka duk jikinta ba dadi
ga Zazzabi ta rasa inda zatasa kanta taji dadi kawae sai tasaka kuka, Safeer
yana toilet yajiyo kukan Shukra ya fito da Saurin sa ya hawo kan gadon inda
take "
" Shukrah tayi Saurin fadawa jikinsa ya kankameshi
kamar zata shiga cikin sa, Nan yaji jikinta yayi zafi sosai abin ya bashi
tsoro, Yayi Saurin kwantar da ita ya fice daga dakin "
" Azeeza kadai ya samu a Parlour yayi mata bayanin
komai, Nan ta mike da sauri takira Ahmad suka je inda Shukra, Azeeza jin yadda
jikin Shukra yayi zafi yasa ta fashe da kuka, abinda ya daga hankalin Safeer
"
" Da Hanzari Ahmad ya dauko car key dinsa Safeer ya
dauko Shukra bayan Azeeza ta sa mata Hijab Suka wuce Asibiti "
" Suna zuwa Aka karbe ta, Bayan test test da akayi
Doctor tayi musu babban Albishir cewa Shukra nada ciki har na wata Biyu "
" Zo kuga murna gun Safeer kai bama shi kadai ba harda
Azeeza da Ahmad tunda su basu taba haihuwa kuma sun dau Safeer da Shukrah
tamkar yan uwansu wannan ne yasasu jin kamar su za ayi wa haihuwar "
" Sai ba adi salatul Magrib sannan suka baro hospital
kuma Alhamdulillahi jikin Shukra yayi sauki sai dai rashin kwarin jiki kawai
"
" Sosai Shukra ke samu gata gun Ahmad, Safeer da
Azeeza, Don Azeeza ta hana tayin komai cikin gidan har ruwan wanka ita ke hada
mata da kanta "
" Kayan baby kuwa abin ba a cewa komai don kullum Ahmad
ya fita sai ya siyo su hakama Safeer don ya zama dan gari "
" Safeer ne ya kira Aysher ya gaya mata Ankoyi sa a
ranar Ammii da Areef sun zowa Mamah ziyara, Nan Aysher ta fada musu maganar
cikin Shukra, zo kuga murna gun Ammii da Mamah bakin su yaki rufuwa su a dole
murnar samun babban jika suke a take Ammii takira Daddy ta fada masa kusan ma
Daddy duk ya fisu don cewa yayi inyagama abinda yake a Dubai zai wuce san
Fancisco ya gansu "
" Mamah ta kira Shukra tayi mata murna tayi mata addu
'ar samun lafiya, Ita dai Shukrah kunya kamar ta nutse, sai bayan sunyi sallama
da Mamah ta juyo kan safeer tana dukansa da hannu biyu tana mai kukan shagwaba
"
" Shine kaje ka fada wa su Mamah inada ciki ko? Yanzu
da wani ido kake so na kallesu "
" Rike hannayenta yayi ya janyota Jikinsa ya Matse ta
har sai da ta saki yar kara sannan ya sassauta rikon "
" Shukrah Ai ko ban fadawa mutane ba zasu gani ae in
mun koma "
" Ni bazan koma ba sai na haihu, Ta fada cike da
shagwaba "
" Ae baki isa ba nanda 2 weeks zamu tafi don next week
za a gama Aikin company kuma office suna nema na "
" Ni bazan tafi ba sai dae kaje ka barni a nan "
" Bazan barki ba Shukrah "
" Nan dae Shukrah ta cigaba da kukanta na shagwaba wae
ita bazata je aga cikin taba sai dae a ganta da baby "
" Shiko Safeer shiru yayi yana jinta don yasan inya
biye mata rigima zatayi tayi masa don ita cikin nata da tabara, Rigima da
shagwaba yazo mata, Ahaka dae bacci ya dauketa ya sauke ta daga jikinsa ya mata
addu a shima yayi ya Rungumeta sai bacci...........
"Misalin karfe daya da rabi Shukra ce da Azeeza a kitchen da Alama Lunch
suke hadawa, Azeeza na daga gefe tana dafa white spaghetti Shukra kuma tanayin
Beef Goulash "
" Wayan Shukra ne ya shiga ringing ta ajiye spoon din
Hannunta ta nufi wayar, Ibteesam ce me kiran shiyasa Shukra tayi saurin picking
tana mata sallama
"Shukra
Fadamin da bakin ki dan Allah inji Ibteesam da murnar ta"
"ME zan fada miki Shukra ta tambaya "
" Ki fada min SIRRIN BOYE (sabon Novel dina bayan AUREN
BAZATA insha Allah) inji Ibtee tana dariya "
" Dariyar itama Shukra tayi don ta gane me take nufi
"
" Wata nawa ne?
"Wata Biyu ne "
" kice Amal ta kusa samun kanwa inji Ibtee "
" Ta kusa kam "
" Daga nn dae suka cigaba da Hirar su ta kawaye har sai
da Shukra taji Beef Goulash dinta na neman kamawa sannan tayiwa Ibtee sallama
ta koma kan girkin ta "
" kamar yadda Daddy yayi Alkawarin zuwa San Francisco
ganin Shukrah Haka kuwa akayi ranar wata friday ya kira safeer ya fada Masa
gobe ze biyo jirgi yazo ya gansu, Shukrah kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don
Farin ciki "
" Ranar da Daddy zezo Abinci kala kala Shukrah da
Azeeza sukayi, Karfe Uku saura jirgin su Daddy yayi landing a San Francisco,
Inda ya kira Safeer a waya Sukaje Shida Ahmad suka tawo Da Daddy "
" Rungume Daddy Shukrah tayi don Murna kafin taja
Hannunsa ta Zaunar da shi kan One sitter ita kuma ta zauna a gaban sa tana masa
labari sai dariya suke "
" Azeeza ce ta kawo wa Daddy Abinci da Drinks sannan
Suka gaisa Nan Safeer da Ahmad ma Suka zo suka kara Gaisawa da Daddy kafin suka
tafi suka barshi yaci Abinci "
" Koda Ahmad da Safeer suka fita Hotel room suka kamawa
Daddy sannan suka je sukayi masa Siyayya
me yawa suka kai Room din sannan suka dawo gida "
" Sanda Suka tafi Mosque ne suka yiwa Daddy bayanin
Komai kuma yaji Dadi, Da suka idar Suka kai Daddy Hotel din Sannan suka dawo
gida "
" Safeer da Shukra zaune a dakin su Ga abinci a gaban
su
"Shukrah yanzu bazaki ci abinci ba, kin taba ganin inda
akayi haka? Bafa ke kadai bace ba "
" Ni bazan ci wannan abin ba ta fada tana nuna masa
plate din gabansu kamar zatayi kuka "
" To naji me zaki ci "
" Dan wake ta fada tana kwanta wa a jikinsa "
" 😳Dan wake kuma Shukra? Haba da Allah yanzu a
ina zan samu dan wake a nn, Kuma naga da ae bakya cin Dan waken "
" Toni yanzu shi nake so ta fada tana fashe da kuka
kamar an mata wani abun "
" Rungume ta yayi tsam yana lallashi amma taki jinsa
sai kara volume din kukan ma tayi "
" Yi hakuri Shukra dan Allah ki fada min wani abun amma
banda wanda bazan samu a nn ba "
" To naji na canja Dan - Malele zanci "
" Safeer kamar zeyi kuka yake ji, Tabarar Shukrah ta
soma damunshi, "ynx fisabilillahi Shukrah a ina zan samu wani Dan -Malele
a nn"
"Toni shi zanci "
" Shiru yayi mata be kara cewa komai ba ya janyo plate
din ya fara cin abincin sa "
" Shukrah ganin ya kyaleta ya sata fasa masa kuka sosai
har tana bubbuga kirjinsa, Rike hannayenta yayi da nasa guda daya yana cigaba
da cin abincin sa har anan bece mata komai "
" Shiru tayi ta kara lafewa a jikinsa tana sauke ajiyar
zuciya har bacci ya dauketa "
" Sai da ta gama cin abincin sannan ya kwantar da
Shukrah a kan gado sannan ya dauki plate din yakai kitchen ya dawo ya kwanta a
kusa da Shukrah bayan ya musu addu 'a, Da tunanin rigimar Shukra bacci ya dauke
shi "
" Cikin dare yunwa ta damu Shukrah ta mike ta fara
bubbuga Pillow' n safeer, Bude idonsa yayi ya sauke su kan Shukrah da tayi
kalar tausayi tana kallonsa "
" Ya akayi? Ya tambayeta da muryan bacci "
" yunwa nakeji ta fada tana jan hannunsa "
" Mikewa yayi ya fita, kitchen ya je ya hada mata Tea
sannan ya dawo ya samu ta shiga Toilet "
" Tana fitowa ta nufi inda yake da sauri ta karfi cup
din hannunsa bata damu da zafin da tea din yake da ba ta kafa kai ta fara sha,
Bata ajiye ba sai da ta shanye tsat, Ta zauna bakin gado ta rufe idonta tana
maida numfashi, Wani tausayin ta yaji yana shigarsa sosai "
" wani zafi Shukrah taji tana ji sai gumi take, Ganin
da yayi tana gumi ne yasashi shiga toilet ya hada mata ruwan wanka, Ya dawo ya
daga ta ya cire mata rigar jikanta ya dauketa cak sai toilet, Da kansa yayi
mata wanka sannan ya dauko ta ya dawo da Ita ya kwantar kan gado shima ya
kwanta sai bacci "
" Sai da Daddy yayi 1week a San Francisco, sosai yayi
wa baby siyayya shima sannan Y soma shirin komawa Nigeria, Shukrah yar Rigima
wae sai ta bishi,jin safeer be ce mata
komai ba yasata yin shiru da maganar "
" Ranar da Daddy ze koma dukansu ne suka rakashi
Airport sai da su kaga tashin su sannan suka koma gida suma "
" Yau ake taro bude
Company 'n Ahmad, Sosai manyan mutane suka halarci taron kasan cewar
Ahmad shahararre kuma fitacce a San Francisco state, Bayan gaishe gaishe, ciye
ciye Ahmad ya gabatar da Safeer a
matsayin Manager' nsa, sosai abun ya bawa Safeer mamaki don be taba tunani ba
kuma koda wasa Ahmad be fada masa ba, "
" Se bayan da aka kammala taron ne Safeer ya samu
kebewa da Ahmad inda yayi masa godiyar wannan alherin da yayi masa "
"Safeer ya kira Mamah ya fada mata irin Alherin da
Ahmad ya masa, Nan Mamah ta bukaci Safeer ya hada ta da Ahmad din, Ya bashi
wayar kuwa inda Mamah tayi masa godiya sosai sannan tayi masa Addu 'a, Sosai
Ahmad din yaji dadin yadda Mamah tayi masa "
" Yau saura kwana Biyar su Shukrah su koma Nigeria,
Sosai Ahmad da Azeeza suke musu tsaraba
wanda yawanci kayan Babe ne, Azeeza ce ma tayi wa Aysher da Miemie tsaraba,
inda Ahmad yayi wa Mamah da Ammii tsaraba shi kuma "
" Ana gobe zasu koma cikin gidan ba wanda yayi bacci
suna tunanin rabuwa (sabo turken wawa), Jirgin bakwai da rabi zasu bi hakan
yasa koda su safeer suka dawo daga mosque wanka ya shiga bayan ya fito ne itama
Shukrah tayi "
" 6:40am dukansu suka fito suka shiga mota Sai Airport,
Cikin mota Shukra da Azeeza sai kuka suke sun rungume junansu, Suma su Safeer
kawae dauriya suke irinta mazaje amma suna jin ba dadi a ransu wannan ne
dalilin da yasa basu hana su kukan ba ma "
" 7:30 aka fara kiran sunansu, safeer da kyar ya janye
Shukra a jikin Azeeza bayan ya mata alkawari zasu sake dawo wa kafin ta haihu
tunda shine manager 'n company' n Ahmad so akwai bukatar zuwansa San Francisco
akai akai "
" Sai da Su kaga tashin su sannan Ahmad yaja Azeeza
mota wadda har anan kukan take (Sabo da dadi rabuwa ba dadi) "
" A Nigeria Miemie da Aysher ne a kitchen suna ta girki
kala kala, Dama Mamah ta nemi alfarmar Ammii kan tazo gidanta su tari su
Shukrah gaba daya "
" Ammii bata watsa kasa a idon Mamah don tun 9:00am
sukazo ita da Areef "
" To cikin jirgi Shukra sai kukanta take Safeer na
Aikin lallashi, Da kyar ya samu tayi bacci sannan hankalinsa ya kwanta "
" 2:00pm Jirgin su yayi landing a Airport na Malam
Aminu kano, Suna fita Safeer ya kira Haiydar ya fada masa sun karaso sannan suka
koma gefe suna jiran zuwan Haiydar din "
" Bayan kamar minti ashirin sai ga Haiydar ya zo ya
fito ya tayasu zuba kayan su a booth ya jasu sai Farm Centre "
" Miemie najin tsayawar mota ta fito da gudu dai dai
sanda Shukrah ke fito da ga motar Haiydar, Miemie tayi tsalle ta Rungume shukra
cike da murnar Ganinta, ita ma Shukra da murnar ta ta rungume miemie suka shige
gidan gaba daya "
" Shukrah na ganin Ammii ta fada kanta ta rungume hade
da sakar mata kukan shagwaba "
" Baki Ammii ta saki tana kallon Shukrah da mamaki
"Kukan na
meye to Shukrah"
"Na dadi ne Mamah ta bawa Ammii Answer "
" Sai Anan Safeer da Haiydar Suka shigo gidan Nan fa
aka shiga gaishe gaishe kowa fuskar sa dauke da fara 'a, Bayan an gama ne
Aysher ta shiga kawo musu drinks "
" Ruwa kawai Safeer yasha suka tafi Mosque shida
Haiydar, To itama Shukrah Sallah tayi sannan tazo tace Miemie ta bata abinci
taci don ita cikin nn harda wani mugun ci yasa mata "
" Coconut rice da Egg sauce Miemie ta zuba mata sai
mixed fruit ta ajiye mata a gaban ta, "
" Ae Shukrah na kai Spoon din baki taji zuciyar ta ba
tashi ta yarda Spoon din da sauri tana kokarin mikewa, Amma kafin ta mike tuni
ta fara Amai a inda take "
" A tare dukansu suka nufeta Aysher ta rike ta tana
mata sannu jikinta sai rawa yake
"Aysher ki
dauke wannan abincin banason ganinsa Shukra ta fada a wahale"
"Sai da Aysher ta dauke abincin takai kitchen sannan ta
dawo ta fara gyara gurin "
" Mamah ko rike Shukrah tayi suka shiga daki ta taimaka
mata ta dauraye bakinta ta hada mata ruwan wanka ta shiga sannan ta dawo palour
inda Ammii "
" Sanda Safeer ya dawo gidan sai dube dube yake yanason
ganin Shukrah Amma bai ganta, Kiran Miemie yayi da hannu ta dawo kusa dashi ta
zauna "
" Shukrah fa? Ya tambaye ta kasa kasa "
" Nan miemie ta masa bayanin komai, aiko yayi saurin
ture plate din gabansa ya shige dadin Mamah "
" Tana kwance a kasa da alama fitowarta a wanka knn
idonta a rufe kamar me bacci ya kara sa kusa da ita ya zauna, Shafa fuskarta da
yayi ne yasa ta bude idonta da sukayi ja alamar tana jin jiki sosai "
" Mikewa tayi ta shige jikinsa don ba abinda take
bukata a halin yanzu sai shi, Tana so taji dumin jikinsa "
" Kara rungume ta yayi tsam kamar za a kwace masa ita
yana shafa gashi kanta har zuwa bayanta, yana mata rada a kunnenta "
" Kara shigewa jikinsa tayi tana lumshe ido, ita kadai
tasan abinda takeji a jikinta (Nace wannan ko sun manta a gidan Mamah suke)
"
" kokarin kunce towel din jikinta yake aka bude kofa ya
juyo da sauri yana kallon kofa, miemi ya gani a tsaye ya watsa mata harara
"
" ME ya shigo dake cikin dakin nn? Ya tambayeta rai a
bace "
" Ammii ce tace in kira kaci abinci "
" Dalla fita k bani guri ya fada yana nuna mata kofa
"
" Fita tayi da sauri dan tana tsoron bacin ransa "
" Wayarsa ya ciro yana snapping fuskan Shukra, Kafin
kuma ya shiga kiran Aysher "
" Da Sallama tashigo cikin dakin Amma ganin a yanda
suke yasata saurin juyawa "
" Dariya yayi sannan ya ce ta daukowa Shukra kaya tasa
"
" Fita tayi bata wani dade ba ta dawo kanta a kasa ta
mika masa kayan ta fice da sauri"
"Da kansa ya saka wa Shukra kayan kafin ya soma
lallabata kan tazo suci abinci amma tace bata san cin komai, da kyar ta yadda
zata sha Tea "
" 4:15 pm Ammii tace itafa gida zata tafi, Safeer ne ya
maidata gidan sannan ya dawo "
" Sai bayan Magrib Abbah ya dawo suka gaisa da Safeer
ya kara masa murnar zama manager a San Francisco "
" Shukra ma tazo suka gaisa da Abbah inda yayi ta
samata albarka yana addu ar Allah ya sauke ta lafiya ya bada nagari "
" Sai da sukayi Sallar isha sannan suka musu rakiya har
mota suka tafi gidansu, Gidan tsaf yake don
Aysher da Miemie sun zo jiya sun gyara"
"Shukrah ce ta fara wanka tana fitowa ta kwanta sai
baccin gajiya, Safeer ma da ya fito daga wankan kwanciya kawae yayi ya musu
addu a sai bacci............
SAFIYA TA GARI
"Washe gari Safeer beje ko ina ba a gida ya yini, Sai
bayan la 'asar ne Haiydar yazo, Sosai suka yi hira, Shukrah ta fito daga daki
da gani a bacci ta tashi, Tana ganin Haiydar ta saki ranta suka shiga gaisawa
cikeda girma ma juna, Kallon Safeer tayi taga ita yake kallo "
" Ta bata rai tana harararsa' Zani gidan Ibtee tace
tana turo baki "
" Maida kallon sa yayi kan wayarsa yace 'Bazaki ba'
"
" Tafi minti biyu tsaye tana kallonsa kafin tasa kukan
shagwaba harda bubbuga kafa a kasa kamar karamar yarinya "
" Ganin ko kallonta yaki yi yasa ta zuwa gabansa ta
Fisge wayar hannunsa
"Ni wallahi
sai ka kula ni"
"Dariya Dukansu kusa sa ba kamar Safeer da yakeyi
tsakani da Allah harda Sakkowa daga kujera "
" Abin ya kara bata haushi dama yanzu abin haushi ba
wuya yake mata ba, Ta kara fashe wa da kuka tana kallon Haiydar wanda yake
kokarin tsayar da dariyar sa "
" Harda kai
ko? Nagode "
" yi hakuri Shukra, Ki rabu dashi kinji, yi tafiyar ki
gidan Ibtee ki tawo min da Amal in zaki dawo, Safeer ya fada kamar bashi ya
gama mata dariya ba yanzu "
" Bazani ba ta fada tana hullar da wayarsa a kasa
sannan ta wuce dakinta ta rufe kofa harda key ta fada kan gado tana cigaba da
kukanta "
" A parlour Haiydar ya kalli Safeer "wae kae meye
hk ne zaka sa yarinya a gaba kana mata dariya"
"Dariyar ya kuma yi kafin yace ae mu biyu mukayi mata
dariyar naga "inji Safeer
" Amma ae taka tafi bata mata rai, wae meye ma abin
dariya "
" Ni mamaki ta bani Duk fa yau bata kulani ba in nayi
mata magana sai tamin Shiru ko kallo ban isheta ba, shine ta bani dariya yanzu
ae tazo tana wani bata rai wae zata gidan Ibtee "
" Murmushi me kyau Haiydar yayi sannan yace me kayi
mata taki kula ka?
"wallahi ban mata komai ba rigima ce kawai irin tata
"
" To Allah ya kyauta Haiydar ya ce tana kallon wayarsa
da ta shiga vibrating, Sanda Haiydar ya daga wayar shi kuma Safeer mikewa yayi
ya shige Dakin Shukrah "
" Tana zaune tana charting a bakin gado ya karasa kusa
da ita ya zauna sannan ya karbe wayar Hannunta "
" ME zaki ci, Ya tambaye ta yana kallonta "
" Murya can ciki tace bakomai "
" kamo hannayenta yai duka biyun yana kallon cikinta
daya dan turo kadan dan ita shukra dama cikinta a shafe yake, "Haba Mana
Shukrah Cute ya zaki ce ba zaki ci komai ba, ki daure ko tea kisha"
"Ni bazan sha ba ta fada wane zatayi kuka "
" Ni Gidan Ibtee zani tayi min Tuwo "
" To Alhamdulillahi tunda zaki ci tuwon tashi na rakaki
gidan Ibtee, Ya fada yana nikam da ita, Hijab ya dauka a kan gado ya sa mata ya
rike Hannunta suka fito parlour inda tayiwa Haiydar sallama don ba da wuri zata
dawo ba "
" Har bakin gate din su Ibtee yakai Shukra yace ze jira
ta ta kawo masa Amal, Tana shiga parlour taga Amal tana wasa ta dauketa takai
masa sannan ta koma cikin gidan "
" sanda ta shiga gidan taga Ibtee tana leka bayan kujera,
Shukra ta hade rai don batason yin dariya "
" Lafiya Ibtee, Meye a gurin shukra tace tana lekawa
itama "
" Ke banga Amal ba kuma fa wallahi yanzu na shiga daki
na dawo kuma ban ganta ba Ibtee tace hankali tashe "
" Shukrah ta gimtse dariyar ta ba tare da Ibtee ta gane
ba tace to waye ya shigo gidan ya dauketa? dama baki rufe parlour ba? "
" Inafa na rufe, keni zo mu fita Dalla ta fada sanda
tasa Hijab dinta "
" Ai kuwa bamuga ta zama ba Shukrah tace sannan tana
hannun Ibtee suka fito "
" Fitowarsu tayi dai dai da fitowar Haiydar da Safeer,
Amal na hannun safeer ya bata wayarsa tana wasa da ita "
" wata Nannauyar ajiyar zuciya Ibtee ta saki ta kalli
Shukra, Shukrah ta tuntsire da Dariya harda rike ciki "
" Ibtee takai mata duka 'bakida kirki Shukrah dama
kinsan tana gidanki baki fadamin ba kikasa na tashi hankalina"
"Har anan Shukrah dariya take taja hannun Ibtee ni zo
muje kimin Tuwo shi nake so wallahi, "
Kin jawa kanki ae bazan yiba"
"Haba Ibtee Swthrt, matar abu turab, uwar gida sarautar
mata daga ke ba kari, Maman Amal Beauty, dan Allah kimin tuwon kinji Shukrah ta
fada sanda suka shigo parlourn "
" To naji zanyi shknn Ibtee tace tana karasawa kitchen,
ita kuma Shukrah tayi zaman ta a parlour dan in ta shiga kitchen taji kamshin
miyar baxata iya ciba "
" Sai ba adi salamu magrib sannan Shukrah ta koma cikin gidanta inda ta dauko
Amal ta dawo wa da ibtee ita ta koma ta samu Safeer zaune a palour yana Aiki a
system dinsa "
" Ya Safeer zo muci tuwo ta fada tana ajiye flask din hannunta
a kusa dashi, Ta wuce kitchen dauko plate da spoons ta zuba musu, Ta mike ta
bude fridge ta dauko musu lacasera ta ajiye tana kallon Safeer "
" Sai da ya kammala abinda yake sannan ya switching
off system din sannan ya sauko suka soma
cin abincin "
" Washe gari gurin 11:00 Safeer yace Shukra ta shirya
yakai ta gidan Ammii daga nan su biya su gaida Hajiyar Haiydar, Shukra harda
dan tsalle ta shige toilet don yin wanka "
" Safeer ya juya ze fita kenan ya hango wayar Shukra
dan dressing mirror, Da sauri ya karasa ya dauka Kai tsaye contact dinta ya
fara dubawa cikin sa 'a kuwa yaci karo da wata Number anyi saving as MY NUMBER,
Da sauri ya dauko wayarsa ya dau Number yasa yayi dialing, Tana fara ringing
yayi saurin Rejecting yayi mata Saving number sa as "HUSBY"
"Sannan yayi saving tata number as "WIFEY"
"Koda Shukrah ta fito da sauri ta shirya ta samu Ya
Safeer a parlour suka kama hanyar gidan Ammii"
"sanda suka isa Safeer ne ya dauko wa Shukrah tsarabar
su Ammii suka shiga a tare cikin sa a kuwa suka tarar da Daddy na gida "
" Safeer ya dade sosai yana hira da Daddy sannan Y musu
sallama ya tafi "
" Misalin karfe hudu da rabi wayar Shukrah dake hannun
Areef ta soma ringing, mika mata yayi da sauri
"Baki sake take
kallon number ita dai tasan ba ita tayi saving number nn ba, Tana ta mamaki har
kiran ya katse wani ya shigo, Sai anan ta dauka da Sallamar ta"
"Jin muryan
Safeer yana Answer mata sallama yasata sauke ajiyar zuciya"
"ki fito mu
tafi gidansu Haiydar"
"To kawai tace sannan ta shiga dakin Mamah tayi mata
sallama ta fito ta samu Safeer a motar sa suka tafi Gidansu Haiydar "
" Sosai Shukrah ta samu karba ta musamman a gurin
Hajiyar su Haiydar, Don Hajiyar Haiydar mace ce mai kirki da son mutane duk da
kasan ce watar ta mai kudin gaske amma kudinta be sa mata girman kai ba "
" Sai da sukayi sallar isha sannan suka koma gidansu
inda Hajiya ta cika Shukrah da tsaraba, sosai Shukrah ta shiga ran Hajiyar don
har tana tambayar ta sanda zata sake zuwar Mata.........
Three Months later
"Shukra zaune a dakinta ta sa akwatuna a gaba tana duba
wa zallar kayan Babe ne aciki, a zuciyarta tana mamakin irin wannan soyayya da
iyayen ta, iyayen Safeer kai harma da Hajiyar Haiydar suke nuna wa babynta,
takai one hour tana aikin kayan kafin ta ture kayan ta jingina a jikin gado
tana shafa cikin ta dan wata shida wanda ya yayi girma sosai sai kace dan wata
tara, Mamaki da tsoron girman cikin ya hana mata nutsuwa a yan kwanakin nan ga
nauyi kamar me "
" Tana cikin haka Safeer ya shigo cikin dakin yana Waya
da alama da friend dinsa suke wayar, Sai da ya gama ya juyo yana karawa Shukrah
kallo wadda gaba daya ma hankakinta baya wajensa, janyota yayi jikinsa yana
shafa kanta "
" Shukrah meye matsalar??
"Tsoro nakeji ya Safeer ta bashi Answer kamar zatayi
kuka "
" Dago kanta yayi yana mata kallon mamaki kafin yace
tsoron me?
"Wannan cikin mana yayi girma da yawa kamar wadda zata
haifi guda goma "
" To Shukrah ae lafiya ce, kuma ma ko guda goma kika
haifa ai ba matsala bane indai Allah ya baki lafiya ko "
" Kuka kawae tasaka masa wae ita BAZATA haifi guda goma
ba "
" Safeer dae yana mamakin Shukrah yanzu ba dama ayi
magana sai tasa kuka, ayi mata wasa ta dauka da zafi, lallashinta yashiga yi
yana cewa insha Allah daya zata haifa mai kama dashi tunda batason goma "
" o o ni me kama dani zan haifa tace tana turo baki
"
" To naji Allah ya sauke ki lafiya shike nan "
" A a "
" Sai me kuma "
" Sai da ta dauke kai kafin tace ni gidan Ammii zaka
kaini "
" Kema dae kya ji kunya Shukrah jiya fa har 10:00pm
kina gidan Ammii kuma yau ma wae sa rai kike na kaiki "
" Kukan ta ta cigaba wannan karon har tana hadawa da
kaimai duka "
" Ganin Abin Shukrah ba me kare bane yasa Safeer saurin
ture ta a jikinsa ya mike ya fice, ita ko Kukan ta take tsakani da Allah a haka
dae bacci ya kwashe ta a gurin "
" Sai bayan sallah magrib sannan Safeer ya dawo gidan
Shukra na zaune a parlour tana cin gireba, suna hada ido ta daure rai ta maida
kallon ta jikin TV"
"Yammata na, yanzu kina kallona na shigo cikin gidanki
amma ba sannu da zuwa ba komai "
" Ban iya ba tace ba tare da ta kalleshi ba "
" Baki iya gaisuwa ba Shukrah ya fada sanda ya karaso
kusa da ita yana binta da kallon mamaki "
" To kaima baka iya dubiya ba ta fada tana murguda masa
baki "
" iye Shukrah ya Safeer din kike yiwa haka? Yayi
maganar irin abin ya bashi mamakin nan "
" komai ba tace ba sai ma juya masa baya datayi tana
cin gireba hankali kwance "
" Ya dade a tsaye yana mata kallon mamaki kafin ya
girgiza kansa ya wuce dakinsa a ransa yana cewa
"Shukrah
dae ta zama a lallaba"
"Shukrah na nan zaune har 9:00tayi, wayarta ce tayi
ringing tayi saurin dauka kamar me jira DR WAHEEDA ta gani jikin screen din sai
da tayi murmushi kafin tayi picking, tayi mata Sallama ta answer "
" Bayan yan gaishe gaishe ne, waheeda tace Shukrah
bakida kirki wallahi ace kin samu cikin har 6 Months amma baki fada min ba
"
" Shukrah wadda kunya ta rufe tayi murmushi batada
abinda za tace shiyasa tayi shiru "
" Kinyi Shiru Shukrah ko bakya jina ne? Waheeda ta
tambaya "
" Da kyar Shukrah ta ce mata kiyi hakuri ae nayi
tunanin ya fada miki "
" Inafa ya fada min, Ae zan gamu dashi ne kedai Allah
ya sauke ki lafiya, Badai wata matsalar ko?
"Ba matsala wlh "
" Daga haka dae Shukrah yi sallama Shukrah dae har anan
bata dena jin kunya ba, Don sosai take jin nauyin DR Waheeda hakan nema ya
hanata sanar mata tun farko "
" To kamar yadda Safeer Yayi wa Shukrah alkawarin zasu
sake zuwa San Francisco haka kuwa akayi don yau Safeer Bayan ya tashi daga
office Golden season travelling agency ya nufa kai tsaye yayi musu visa shida
Shukrah da Miemie "
" Sanda ya shigo gida tarar wa yayi Shukrah tayi baki
wasu yan uwansu sune na katsina suka zo, Tsayawa yayi suka gaisa sannan ya
wuce, Shukrah kamar bazata tashi ba tayi zamanta ta cigaba da hirar ta sai da
wata Auntyn ta Aunty Nabeehart ta harare ta
" Kin tashi
kin bi mijin ki ko sai na kwada miki mari tukun na"
"Turo baki Shukrah tayi ta tashi tana cewa Aunty fa
banida lpy sannan ta shige dakin Safeer "
" Sanda ta shiga ta samu har ya shige wanka saboda haka
sai kawae ta fito mai da kaya tayi kwanciyar ta kana game a wayar sa "
" Sanda ya fito gaban dressing mirror ya nufa ya dauko
cream ya dawo kusada Shukrah ya zauna, Tana ganin haka tayi saurin minimizing
game din ta ajiye wayar ta mike, sai da ta karbi cream din hannunsa sannan ta
kalleshi ta fara magana kasa kasa
"Ya Safeer ka
dawo lafiya ya office?
" Alhamdulillahi, Yau na zo miki da albishir "
" Cikeda zumudi tace ya Safeer menene dan Allah "?
" Inna fada miki me zaki bani as a gift "
" Duk me kake so zan baka wallahi "
" Are you sure! Yace in between laughter dan shi kadae
yasan tanadin da yayi mata "
" Absolutely sure inji Shukra don bata me yayi ba,
"To shknn zan fada miki koma menene amma ba ynx ba sai
dare "
" me yasa sai dare Shukrah ta tambaya cikeda rashin
fahimta
"banason tambaya tayi yawa tunda nace sai dare ae saiki
hakura ko"
"Shukra bata
sake cewa komai ba har dae ta gama shafa masa cream din ta koma wajen bak'in ta
"
" Da daddare bayan Safeer ya fito daga masallaci be
wuce ko inava sai gidan Mamah inda yayi mata bayanin tafiyar tasu, ya kuma fada
mata tare da Miemie zasu tafi "
" Miemie da tunda ya shigo cikin gidan ta rufe idonta
kamar me bacci wae don karta gaishesa ta fasa ihu hade da duro wa daga kan
kujera "
" Ya Safeer dan Allah dani zaka tafi San Francisco
wayyo dadi, Wayaga Miemie a cikin turawa wai! A gaskiya ka gama min komai
wallahi God bless your unborn Babe ta karasa harda yar rawar ta "
" Baki sake Safeer ke kallon ta haka kuma rai a hade,
azuciyarsa yana daya sanin yi mata visa, Wai dama ba bacci take ba tsabar
iskanci ne ya hanata gaida shi ""
"Wata uwar tsawa ya mata wadda ba Miemie ba har Mamah
da Aysher da Abbah dake kokarin shigowa parlourn sai da suka tsorata
"Bakida
hankali ko, to wallahi ki kama kanki kinsan me yake miki ciwo, in kuma kinki
wallahi zan baki mamaki useless kawai"
"Abbah ne ya karaso cikin parlourn ya dafa kan Safeer
sannan yace''kayi hakuri babban yaya sai hakuri addu a zaka tayata da ita kaji
"
" To kawai yace sannan ya mike yana kallon Mamah
yace''ta shirya wednesday zanzo na tafi da ita tunda friday zamu tafi, yana
kaiwa nan ya fice daga gidan "
" Tafiyar 40mints ne ya kaishi gidansa, a parlour ya
tarar da Shukrah a kwance kamar me bacci, ya kara so kusada ita ya dauke ta cak
sai a kan bed bayan ya sauketa ya shige toilet sai anan Shukrah ta bude idonta
don kwanciyar bata mata dadi ba "
" Minti goma ya yayi yana shiryawa bayan ya fito a
wanka, kan bed yahau ya zauna kusa da Shukrah ya riko hannunta ya akayi ne
Shukrah cute?
"Abinda zaka fada min dazu kace na bari sai dare zaka
fadamin "
" Me kike ci na baka na zuba ae ynx zan fada miki,
kedai ba kince duk me nakeso zaki baniba "
" Saurin daga masa kai tayi don ta matsu taji me zai ce
"
" Good gal dama fada miki zanyi Friday zamu tafi San
Francisco "
" Ae Shukrah batasan sanda ta fada jikin Safeer ta
kankame shiba "
" Shima kankame ta yayi hade da zame rigar jikinta ya
zura harshen sa cikin bakinta yana tsotsa as if ya samu sweet ne..............
0 comments:
Post a Comment