"Yau tuesday Safeer na zaune a office dinsa da yamma
misalin karfe 3:20pm Haiydar ya shigo da sallama a bakinsa, Sai da Safeer ya
answer masa kafin ya kariso ya zauna yana facing Dinsa "
" Ajiye Files din hannun sa yayi sannan ya ce
"Haiydar ya
Aikin?
" Alhamdulillahi "
" Dan Allah ka tayani yiwa Hajiya Godiya tana ta hidima
wallahi Allah dae ya kara girma "
" Sai da Haiydar yayi murmushi kafin yace ae bakomai
Safeer yiwa kaine "
" Duk da haka dae kae mata godiyar "
" To insha Allah zan mata, Daga nan dae suka cigaba da
Hirar su wanda mafi akasarin hirar dae akan Miemie ake yinta, Har sai da ran su
ya baci dukansu sannan Haiydar ya mike yana bin Safeer da Mugun kallo "
" Ae dama na
dade da sanin baka sona da kanwar ka shiyasa kake ta wani kakkaucewa to wallahi
duk a binka sai na Auri miemie insha Allah, kuma gobe xanje na samu Abban na
masa magana da kaina Haiydar ya fada yana nuna safeer 👉🏻"
"Murmushi Safeer yayi yana mikewa da niyyar fita sannan
yace Haiydar kanada Matsala wallahi kullum anyi ta maimata magana daya ne wae,
Haba da Allah be a man mana me xakayi da wata miemie yarinya ko gama mallakar
hankali batayi ba "
" Naji koma me zakace sai dae kace amma dae sai naje na
samu Abbah inyaso kafin naje ka rigani zuwa ka zuga kaji ko "
" Ni na isa na zuga shi Haiydar Allah ya bada sa a kaje
wallahi, Kuma Allah ya huci zuciyarka "
Daga nn dukansu suka fito kowa ya shige motar sa ba tare da
sunyi sallama ba"
"Sanda Safeer ya isa Gida Shukrah na kitchen tana
toasting bread, ta fito da sauri tazo ta kama hannun sa tana masa sannu da zuwa
"
" ME ake mana ne Shukrah cute naji gidan kamshi Safeer
yace yana rungumo Shukrah jikin sa "
" Bread nake toasting wallahi yau shi nake Sha 'awa
shukra tace sanda suka karasa dakin, Shigewa toilet tayi don hada masa ruwan
wanka shikuma ya cire kayan jikinsa ya daura towel ya bi bayanta "
" A bakin kofa suka hadu, ta raba zata wuce ta gefensa
yay saurin janyota, "Ina zaki kuma?
" Kitchen zan koma ta bashi answer tana kokarin janye
jikin ta a nasa "
" Ya kwantar da murya kamar me shirin yin kuka 'Da
wanka zaki min Wallahi na gaji yau tunda na zauna ban tashi ba "
" Dariya tayi sannan ta kwace jikinta ta fita da sauri
tana masa gwalo, shima dariyar yayi sannan ya fara wankan sa "
" sanda ya fito ya samu shukra a parlour tana cin
toasted bread nata nan yayi joining dinta suna ci suna hirar su abin sha, awa,
sanda suka kammala Shukrah ta kai bowl din kitchen ta dawo ta sameshi suka
cigaba da hirar su har zuwa lokacin sallar magrib sannan Safeer ya fita mosque
ita kuma tashiga daki don yin sallah "
" Washe gari Safeer beje office ba a gida ya zauna ya
taya Shukrah hada musu trolley sai bayan sallah la 'asar sannan ya tafi gidan
Mamah dauko Miemie kamar yadda ya mata alkawari , Sanda ya shiga gidan Miemie
ce kadai a parlourn Aysher na kitchen, Mamah kuma na sama, Miemie tasa trolley
a gaba ta buga tagumi harda dan hawayenta don ta gama fitar da ran zuwan
Safeer, Ae tana ganin ta fasa ihun murna ta nufo shi da gudun ta, Saurin
dakatar da ita yayi ta hanyar mata wata gigitcciyar tsawa
"Kina kara
sowa nan sai na kwada miki mari wallahi, shashasha kawai"
"Kuka ta fasa tana kwalawa Mamah kira kamar Safeer
yamata wani abun , A tare Mamah da Aysher suka iso parlour'n suna tambayar ta
lafiya "
" Ba yaya
Safeer din nan bane bezo da wuri ba kuma yanzu yazo wae ze mare ni, Miemie ta
fada cikeda da shawgwaba tana kara fashe wa da kuka "
" Ba Safeer hatta Mamah da Aysher da Abbah da ya shigo
yanzu sakin baki sukayi suna mamakin Karfin hali irin na Miemie "
" Kinsa Allah in baki rufe min bakin ki a gurin ba zan
fasa shi inyaso kiyi me dalili Safeer
yace rai a bace "
" Ganin da gaske yake yasa Miemie sa hannunta ta rufe
bakinta tana sauke ajiyar zuciya, zuwa can ta dawo kusa dashi ta durkusa har
kasa sannan tace
"Ya Safeer
Dan Allah kayi hakuri kaje dani wallahi na dena rashin ji"
"Komai beceba sai juyawa da yayi gurin Abbah suka gaisa
sannan yayi wa Aysher da Mamah Sallama, ya juyo yana hararar Miemie wadda har
ynx take a durku she a gaban sa
"Kin dau
trolley mun tafi ko sai na bigeki tukun, Da sauri Miemie ta dau Trolley tayi
gaba abinta ko sallama bata yiwa su Mamah"
"Cikin Mota Ko kallo Miemie bata ishi Safeer ba, ita
kuwa sai satar kallon sa take, kula da hakan da yayi ne yasa shi kallon ta tayi
Saurin sunkuyar da kai kasa, sai yaji ta basa tausayi, Har ga Allah yana son
Miemie fiye da Aysher ma amma halinta ne ke hada su fada, "
" Meye kike kallona ya fada yana maida kallon sa ga
titi "
" Bakomai tace tana kallon gefe, shiru ne kuma ya biyo
baya har suka karisa gidansa "
" Shukrah najin horn tayi Saurin leko wa, ae MIEMIE na
ganinta ta saki trolley hannunta taje da gudu zata rungumeta, Ae Safeer ma sai
ya sa gudu ya riga miemie zuwa ya shiga tsakanin su yana wa Miemie wani mugun
kallo,
"Nawa ake
biyana a gidanku da zaki barmin trolley a wajen nufinki na dauko. Miki ko, kuma
da kika tawo da gudu da me zakiyi"
"jiki a sanya ye Miemie ta koma ta dauko trolley ta zo
tashiga gidan "
" Yau ta kama friday kuma yau zasu tafi San Francisco,
kasancewar jirgin 8:00am zasu bi yasa suka gama shirin su tun 7:00 suka fito
suka tafi daukan Aysher a gidan Mamah don ita zata dawo da motar gida, 7:40 a
Airport ta musu, Nan aka zauna hira har sai da aka kira su, sukayi sallama da
Aysher suka Shige jirgi"
"Cikin jirgi Shukrah da Miemie duk bacci sukayi tayi
har sai da jirgin su yayi landing a San Francisco sannan suka farka, Shukrah ce
ta fara fita sannan Safeer, miemie na ziro kai ta shaki iska me sanyi, ae bata
san sanda ta saki ihu ba ta ware hannayenta duka biyun ta rufe idonta
tace""Wayyo Allah wayaga Miemie a sabuwar duniya, Ni anya ma kuwa zan
koma gida "
" Ae Safeer besan sanda ya finciko ta ya matse bakinta
cikeda da Bacin rai ba don iya kunyata wa ta kunyata sa.............
"Ahmad Safeer ya kira ya shaida masa sun iso sannan
suka koma gefe suka zauna miemie tacika tayi fam kamar zatayi kuka don taji
zafin matse mata bakin da safeer yayi, Sai hararan sa takeyi kasa kasa shiko
bema san tanayi ba don duk hankalinsa nakan Shukrah da take masa hira sai
dariya suke abinsu "
" Zaman kamar minti talatin sukayi wayar Safeer ta fara
ringing, yai Saurin cirota a pocket dinsa sunan Ahmad da ya gani ne yasa shi
Saurin picking don ya gaji da zaman gurin "
" Mun iso fa kuna wajen ina "Ahmad ne ke masa
wannan tambayar?
" Mikewa yayi sai ya hango Ahmad da Azeeza, Gani ina
hango kuma bari mu karaso Safeer yace yana yiwa Shukrah da Miemie alamar su
taso, Kafin sukayi sallama da Ahmad "
" Sanda suka karasa inda suke Shukrah tayi tsalle ta
rungume Azeeza ta ma manta da cikin dake jikin ta
"Kibi A
hankali Shukrah karkije ki bige mana Babyn mu inji Ahmad, sai a nn Shukrah ta
tuno da cikin tai Saurin dafe wa sakamakon wani juyawa da taji yana yi ta
runtse idonta sosai, Sannu kawae suke mata bama kamar Safeer daya bi ya rude,
Azeeza ko ji tayi dama a jikin ta ciwon yake don tana jin Shukrah a ranta ta
dauke ta kamar lil sis din ta Zafeera "
" A haka dae suka shiga motar Ahmad yaja su, ko cikin
motar Shukrah na dafe da cikinta ta kwanto a jikin Safeer sai Sannu yake mata,
Tafiyar kusan minti goma sukayi sannan suka isa gidan Azeeza ta fara fita ta
bude kofar parlour sannan Miemie da Ahmad suka fito, Safeer ne karshen shiga
gidan rike da Shukrah tanata kukan shagwaba wae ciwo, Niko nace wannan yarinyar
ta fiye dangwa lolo 🤣"
"Azeeza taja hannun Miemie ta kaita wani karamin Room
tace tayi wanka sannan taje ta dauko mata trolley dinta, Sanda ta dawo har
miemie ta shige toilet hakan ne yasa ta fita ta wuce kitchen tana kwaso flask
tana kae wa dinning sai da ta gama shirya dinning din sannan ta wuce dakin ta
"
" 30 minutes later "
" Dukansu na zaune a dinning suna cin abinci, Miemie na
kusa da Azeeza suna hira, Miemie tace Aunty can you do me a favour pls "
" why not! What do you want?
"I want you to take me out just to see your state
"
" ok i promise to take you difference places like
Zoological garden, Cinema and shopping mall "
" Cike da murna Miemie tace When?
"Next tomorrow insha Allah inji Azeeza "
" Ae MIEMIE bata san sanda ta mike ta fara rawa ba 💃🏻💃🏻,
Ahmad da Azeeza sai dariya suke mata don ta shiga ransu sosai a dan zuwan nn
nata, Takaichi ya cika Safeer gashi ba kusa dashi take ba balle ya kwada mata
mari ko ya huce takaichi, Yayi ta jifanta da harara amma ta share as if to say
ba da ita yake ba, "
" Azeeza tace Miemie you are very good in dancing when
are you going to teach me?
"Till you take me out, Then i will teach you different
types of dance "
" Am so grateful that you are here you are such a
durlin Miemie inji Azeeza tana fara a jitake dama za a bar mata miemie don ba
karamin son yarinyar take ba, cus she's very clever "
" Safeer dae da haushi ya ishe sa sai kawae ya mike ya
shige dakinsu suko basu kawo komai a ransu ba suka cigaba da cin abincin su
suna hirar su "
" Da daddare bayan kowa ya shige dakinsa Safeer ya
shigo dakin Miemie lokacin tana tsaye tana shirin kwanciya ya hade rai yana
kallon ta
"Bakida
hankali ko Miemie, Ke bazaki nitsu ba a rayuwar ki ko kin fi son kiyita hauka
ana miki dariya ko, kin dauka birgewa ce wannan? Shekara goma sha uku amma
bakida nitsuwa ko kadan, You have to maintain your dignity or else you will
regret your life coming to this world, stupid gal kawae yana gama fadar haka ya
fice rai bace "
" Miemie dae ta dade a tsaye tana tunanin rayuwar ta
Tanaji a ranta ya kamata ta kama kanta ta dena abinda take ko zasu shirya da
Brother 'n ta, haka dae ta kwanta ranta ba dadi har bacci ya kwashe ta "
" Washe gari tare Safeer suka fita da Ahmad, Safeer ya
tarar da aiyuka birjik a office saboda haka ne ma koda lokacin tashin Ahmad
yayi safeer cewa yayi baze bishi ba sai ya gama aikinsa ya tawo daga baya,
hakan kuwa akayi Ahmad yaje yahau commercial car ya bawa Safeer car key dinsa
yace ya tawo a ciki "
" Sanda Shukrah ta jiyo Sallamar Ahmad ta yunkura ta
mike dakyar don cikinta ba karamin girma yayi ba ta fito parlour taga Azeeza na
welcoming Ahmad, sai tayi turus ganin Ahmad kamar shi kadae ya dawo, to shi
Safeer din a ina ya tsaya? Kamar Ahmad yasan me Shukrah take tunani yace safeer
ko? Na baro shi a office yace in kin ganshi a gidan nn yau to ki tabbatar ya
gama ayyukan sa ne "Shukrah dae kamar zatayi kuka ta ce to Allah ya dawo
da shi lafiya sannan taja kafarta da kyar ta koma daki tayi kwanciyar ta kan
centre carpet bata wani dade ba kuma bacci me nauyi ya kwashe ta"
"Sai ba adi salatul Magrib Safeer ya shigo gidan a
gajiye, Azeeza da Miemie ya samu a parlour don Ahmad be dawo mosque ba, Miemie
tayi masa sannu da zuwa sannan ta karbi brief case din hannunsa ta kai masa
daki, sai da ya gaisa da Azeeza sannan ya wuce dakinsu nan yaga Shukrah a kwance
tanata bacci abinta sai yaji ta bashi tausayi tuno war da yayi jiya be barta ta
samu baccin kirki ba, nan dae ya cire kayan jikinsa ya daura towel sannan ya
shige toilet don yin wanka, "
" Sanda ya fito Strait gurin Shukrah ya wuce ya zauna a
gefenta ya dago ta ya rungumeta tsam a jikinsa sannan ya sa hannunsa cikin
lallausan gashin kanta yana shafawa a hankali sai a nn Shukrah ta bude idonta
ae suna hada ido ta fashe da kuka tana kokarin sauka a jikinsa, kara rike ta
yayi sosai sannan cikeda lallashi yace Me kuma nayi ake min kuka, yi hakuri
kinji Shukrah cute "
" Lafewa tayi a jikinsa tana sauke ajiyan zuciya sannan
tace 'Bakai bane ka tafi kayi zaman ka a office ba "
" Eyya yi hakuri kinji bazan kara ba "
" To kawae tace tana murmushi daga nn kuma suka cigaba
da hirar su, Tuni Shukrah ta manta da fushin da take ta ware sai zuba hira suke
suna dariya abinsu "
" Washe gari Kamar yadda Azeeza tayi promising Miemie
zasu fita hk kuwa akayi 3:20 suka fita su biyu dan Shukrah cewa tayi baxata
bisu ba, Azeeza ce tayi driving basu zame ko inaba sai zoological garden, Sosai
gurin ya burge Miemie, sundan dade a gurin kafin kuma suka wuce Cinema suka yi
kallo daga nn kuma suka wuce wani shopping mall Azeeza tace Miemie tadau duk me
take so, Miemie dae bata dau komai ba sai wani Makeup kit data dauka (Dama
Miemie mayyar makeup ce) "Daga nn dae suka dawo a gajiye, wanka kawae
sukayi suka ci abinci suka kwanta sai bacci.........
"Yau ta kama wednesday kuma yau ce ranar da Miemie
bazata taba mantawa ba a rayuwar ta, 12:23pm Miemie na kwance a dakinta taji
cikin ta ta juya ta mike ta shiga toilet, Tsugunar da zatayi taga jini ya zuba
me zatayi in ba ihu, Don ta tsorata iya tsorata though an fada musu a islamiyya
amma abun yazo mata unexpectedly, Mikewa tayi a tsorace taba kuka kamar dan shi
aka aikota tana bubbude kafa kamar me koyon tafiya a hk ta fito palour, Bataga
kowa a parlour ba saboda hk sai ta wuce dakinsu Shukrah "
" Sanda ta shiga dakin Shukrah na toilet Safeer ne
kwance yana duba wayar sa, Motsin da yaji ne yasa shi Saurin dago wa, Miemie ya
gani ta wani ware kafar ta tana kuka sosai "
" Ke zonan, Me ya sami kafar safeer yace sanda ya ajiye
wayar sa akan bed side drawer "
" Karasa wa tayi still tana kuka, Tana kokarin daga
skirt dinta, Safeer ya rike hannunta, meya same kine wae?
"Ba jinayi inajin fitsari ba nashiga toilet ina tsuguna
wa naga jini yana fita a nn ba, Ta karashe maganar tana fashe wa da kuka, haka
kuma tana nuna masa gurin "
" Dan murmushi Safeer yayi don ya gane gaskiyar abinda
ya daga hankalin Miemie, "
" To naji na fahimta Ae ba wani abu Bane dena kukan
kizo nan, safeer yace a kokarin sa na kwantar wa da Miemie hankali,
"Karasowa tayi ta tsaya a gefen sa, tana goge hawayenta
"
" Ae a islamiyya an fada muku cewa duk jinin daya fito
a jikin mace yar shekara tara zuwa sama, jinin haila ne ko? Inji Safeer, Daga
masa kai kawae miemie tayi alamar Eh, Good, Shekaranki nawa?
13,"ta Bashi answer "
To Kinga wannan jinin na Haila ne bana ciwo ba so ki kwantar
da hankalin ki, An koya muku wankan tsarki?
" Eh an koya mana miemie ta basa answer kasa kasa don
wata kunyar sa ne taji ta rufe ta "
" Yawwa to yimin bayanin yadda aka koya miki inji,
Fitowar Shukrah a toilet yasa duk suka mayar da hankalin su kanta, ta rike
hannun Miemie tajata zuwa Toilet, "
" Cikin kayanki akwai sabon pant Shukrah ta tambayi
Miemie?
"Ehhh akwai, Miemie ta bata answer, To ina zuwa yanzu
ki cire kayanki kiyi wanka kinji inji Shukrah inda tana gama maganar ta ta fito
hade da rufe wa Miemie kofar toilet din"
"Kai tsaye Shukrah dakin Miemie ta wuce ta bude trolley
dinta ta dakko sabon pant ta dawo dakin su ta Shirya dan dama a wanka ta fito,
Sanda Shukrah ta gama shiryawa toilet taje tana bugawa don ta fuskanci Miemie
ta gama wankan kunya ta hanata fito wa"
"Bude min kofa kinji Miemie "
" Kamar bazata bude ba sai kuma ta bude, idonta a kasa
don wani nauyin su takeji dukan su, Shukrah tace Miemie dago kiga, Miemie ta
dago a hankali, nan Shukrah ta shiga nunawa Miemie yadda ake sa Pad a jikin
pant sannan ta mika mata ta fice "
" Bayan kamar minti goma Miemie ta fito don taga
tsaiwar bazata kaimata ba, Kanta a kasa tayi hanyar kofa, Safeer yace zonan
Miemie, jiki a sanyaye Ta dawo ta zauna a kasa kusa da Shukrah, safeer yace
baki min bayanin yadda ake wankan ba "
" Kunya ta kama Miemie tayi kasa da kai tana wasa da danyatsanta,
ehen ina jinki Miemie, shi Safeer ma mamaki Miemie take basa yadda take wani
kasa dakai"
"Shukrah tace Miemie ko ya Safeer ya fita ni kimin
bayani?
Daga mata kai Miemie tayi, hakan yasa Safeer kara mikewa
akan gado, ke nake sauraro Miemie karki bata min lokaci don bacci zanyi, Miemie
ganin ba sarki sai Allah yasa ta bude baki da kyar ta fara masa bayani kamar hk
:
"Da farko zan samu ruwa mai kyau wanda dandanon sa ko
kamshin sa ko colourn sa bai changer ba, Idan a budadden abu yake kamar bucket
sai na karkata nazuba ruwan na wanke hannuna sau uku, in kuma a rufaffen a bune
kamar kettle basai na wanke hannunba tunda ba taba ruwan zanyi ba, tana kaiwa
nn ta dago ta kallo shi idonsa a kanta, ya daga mata kai alamar ta cigaba, tayi
murmushi ta dora :
"sai nayi alwala dai dai, wasu sunce bazan wanke kafa
ba sai an zo karshan wankan wasu malaman kuma sunce za a wanke, Sai na hade
hannayena duka biyun na cika su da ruwa na zuba a kaina na tabbatar ko ina ya
samu zanyi hakan sau uku, daga nn kuma sai na raba jikina biyu a tsaye na fara
wanke side din dama na sannan na hagu........
"Masha Allah Allah ya albarkachi rayuwar ki kinji inji
Safeer, Shukrah ta kalli miemie tace kinyi kokari sosai, Maganar Safeer tasasu
juyowa dukansu suna kallo sa, To Miemie sai ki nutsu yanzu kisan me ya dace
dake banda wasa da Maza, su rike hannun namiji ko hawa cinyarsa, in ba hk ba
wallahi zaki samu ciki, kuma kinsan ba kyau ae ko "
" Miemie fa cikinta ya duri ruwa ta gama tsorata sai
raba ido take kamar tayi wa sarki karya, haka dae Safeer da Shukrah sukayi tayi
wa Miemie nasiha, Miemie harda kukanta bayan sun gama Miemie ta mike jiki ba
kwari ta shige dakinta ta kwanta sai bacci...
"Haka rayuwa ta cigaba bayan kwana uku Miemie ta
tsarkake kanta ta cigaba da rayuwar ta, "
" Yau watan su daya a San Francisco kuma next week
Miemie zata koma school hakan yasa da daddare Mamah, aysher da Abbah suna zaune
a parlour suna hira har suka gangaro maganar Safeer, Mamah tace Au bari ma
nakira shi ya kawo min yarinyata tunda shi zaman can be ishe shiba, Mamah ta
janyo wayarta takira Safeer Ringing biyu yayi picking da sallamar sa, Suka
gaisa da Mamah "
" Tunda zaman San Francisco bae ishe kuba kana iya kawo
min yarinya ta next week zata koma school "
" Insha Allah Mamah jibi zaki ganta gobe da safe zan
mata visa, Amma ni bazan samu zuwa ba wallahi aiki yamin yawa anan "
" Kai dae kasani nidai kawae naga yarinyata ehe inji
Mamah "
" Yar dariya Safeer yayi yace insha Allah zaki ganta,
my regards to Aysher daga hk sukayi sallama "
" washe gari sanda Safeer zashi office ya tsaya yaywa
Miemie visa sannan ya wuce "
" sanda ya tashi a office ma beje gidan ba sai da ya
tsaya a market yayi wa Miemie siyayya sosai sannan ya wuce gidan "
" Washe gari Miemie jirgin 12:00 zatabi, 11:30 dukansu
suka shiga mota Ahmad yaja su sai Airport, Azeeza ta siyawa miemie wani Makeup
kit, Miemie sai godiya take mata suna haka har 12:00 tayi aka kira Miemie sanda
zata wuce Ahmad ya bata wata lada, taja trolley ta wuce tana masa godiya "
" Da daddare Safeer ya kira Mamah ya tabbatar Miemie ta
sauka lafiya suka taba hira da Aysher kafin sukayi sallama, Nan ya kira Abbah
suka gaisa sannan ya kira Daddy 'n Shukrah suka gaisa.........
*Nigeria*
"Aysher kwance a kan gado tana duba wani handout yayin
da Miemie take gefen ta zaune tana duba kayan da ta dawo dasu Daga San
Francisco, poly thene din da Ahmad ya bata ta dago da sauri dan taji kamar kwali ne a ciki,
budewa tayi me zata gani inba waya ba
IPhone 6s+ ta bude idon ta sosai
tanaso ta gasgata abin da idon nata ke fada mata, iPhone din dae ta gani, ta
fasa ihun murna, Aysher ta juyo da Sauri tana binta da harara don ita har ga
Allah tayi tunanin wani abu ya same ta Amma ta ganta a zaune kuma har a lokacin
ihun take "
" Meye hk Dalla malama ina bacci zaki dinga min ihu,
inji Aysher ta fadi ranta a bace "
" Aunty Aysher ki tashi Uncle Ahmad abokin ya Safeer ne
ya sai mun IPhone 6s+, Miemie tace tana janyo Hannun Aysher zata tayar da ita
"
" Da sauri Aysher ta tashi tana zare ido ganin da gaske
IPhone din ce a gaban ta, kin nuna wa Mamah ne,? Aysher ta tambayi miemie
"
" Nima fa ban saniba kawae dae ya bani polythene ne
Dazan tawo so ban bude ba sai ynx nake gani Miemie ta bata Answer sanda take
saukowa akan bed ta fice ta shiga dakin Mamah, Abbah zaune a gefen bed yana
duba wasu papers yayinda Mamah take kwance akan bed din da Alama ta fara
bacci"
"Ihun Miemie ne ya sa suka dago dukansu da sauri suna
kallon ta, ta karaso cikin dakin da gudun ta tana mikawa Abbah Wayar hannunta
"
" Abbah kagani Uncle Ahmad ne ya bani ita "
" Murmushi Abban yayi sanda ya karbi wayar yana
kallonta kafin ya dago yace
"Miemie ae
wannan wayar ta miki girma kinsan ma fa ni banason rike waya da wuri saboda
batawa yaro brain yake, haka kuma yana bata tarbiyya"
"Wallahi kam, ae kawae karike mata wannan sai tayi
graduation (Candy) sai ka bata, in wayar take so sai ka siya mata baby nokia ta
dinga communicating da friends nata, Mamah dake kwance har a lokacin ta fada ba
tare da ta dago kanta ta kalli Miemie ba "
" Miemie ta bata rai kamar zatayi kuka tana kallon
Abbah daya maida kansa jikin papers dinsa yana cigaba da dubawa, Abbah Please
karka ji Mamah ka bani wayana kaji "
" Ae kinji me na fada miki bazan bayar ba, zan siya
miki karama wannan sai kin gama skul zan baki Abbah yace sanda ya mike ya shige
toilet "
" Kuka kawae Miemie tasa ta juya ta shiga dakinsu inda
ta tarar Har Aysher tayi bacci, nan ta kwanta tana kuka a hk har bacci ya dauke
ta "
" To Rayuwa ta cigaba da tafiya, ynx Aysher ta kai
level three (3)a B. U. K inda take karantar nursing, so ynx haka madai anyi
posting su Aysher hospitals daban daban don yin practicals inda Aka kai aysher
Malam Aminu kano teaching hospital, so Aysher bata wani shan wahala kasancewar
ta mai kokarin gaske, sosai Doctors din keji da ita kasan dae itace over
roller, "
" Aysher da kawayenta Maryam da Nuriyya tsaye a var
render 'n S. O P. D da wani handout a hannunsu suna duba wa, gabaki daya
hankalin su nakan abinda suke, Sallamar da sukaji anyi musu ne yasasu Saurin
juyo wa suna kallonsa "
" Black jeans ne ajikinsa da white t~shirt yayinda ya
dora white lab ~coat akai yayi un buttoning lab coat din, kafarsa sanye da wani
black shoe hannunsa daure da white watch, Answer sallamar sukayi cikeda ladabi
don shine doctor'n da aka hada su da yanada sakin fuska sosai shiyasa suka saba
dashi sosai "
" Cikeda fara a ya answer gaisuwan su sannan ya kalli
Aysher wadda gaba daya hankalin ta nakan handout, Aysher in kin gama ki sameni
a office yace kafin ya juya ya koma office dinsa "
" Mikawa Nuriyya handout din tayi sannan tabi bayansa,
Be dade da zuwa office dinba ta shiga itama, kara gaisawa sukayi kafin kuma
sukayi shiru tsawon minti goma, zuwa can yace
"Aysher wata
magana zamuyi dake to amma kuma naga kamar Karatu kike so kibani number ki
inyaso sai muyi magana a waya ko zuwa anjima ne"
"Badan Aysher taso ba sai dan kawae ganin girman sa da
take ne yasa ta karbi wayansa da yake miko mata ta sa masa number ta ta mika
masa, Hannu ya miko mata alamar ta basa wayarta aiko ba musu ta miko masa nan
dae yayi mata saving number sa as Mahmoud sannan ya bata, ta masa sallama ta
fice "
" Bayan kamar kwana 2 da faruwar Hakan Mahmoud ya kira
Aysher suka gaisa, Aysher batayi wani mamakin jin cewa Mahmoud yana sonta ba
don dama ta dade da ganin alama, Mahmoud dae be kyale Aysher ba har sai da ya
tabbatar ya samu shiga "
*San Francisco*
" Shukrah da Azeeza zaune a parlour suna hirar haihuwar
Shukrah don yanzu cikin nata nada wata takwas kenan, inda Azeeza ke cewa ita
tafi son a haifi Namiji ita kuma Shukrah wae tafi son Mace suna cikin wannan
musun ne Ahmad da Safeer suka shigo da kaya masu uban yawa daga gani dae daga
kasuwa suke, Azeeza ta mike ta karbi kayan ta shige dasu wani dan karamin daki
inda anan ne suka ware don tara kayan Baby, Shukrah dae daga zaunen da take ta
musu welcome don baxata iya tashiba saboda swelling da legs nata sukayi, Safeer
ne ya karaso inda take ya durkusa gaban ta ya fara massaging mata legs din har
sai da ya tabbatar swelling din ya ragu sosai sannan ya taimaka mata ta mike
suka shige dakinsu, a tare sukayi wanka bayan sun shirya suka dawo parlour inda
Safeer da Ahmad suka fice Azeeza kuma ta shige kitchen "
" White spaghetti ta musu bayan ta gama ta daura soup
kan gas, bata wani dau lokaci ba ta gama ta dauko flask set din ta jera a
dining sannan ta dawo parlour tayi joining Shukrah suka cigaba da hirar su har
lokacin magrib yayi suka tashi sukayi "
" Ba *Ahmad* da
*Safeer* suka dawo ba sai ba'adi salatul
Isha, abinci sukaci a tare suka danyi kallo sannan sukayi wa junansu sallama
Suka shige dakinsu, *Shukrah* ce kawae
ta sake wanka don cikin nn yana sa mata jin zafi sosai,Sanda ta fito har Safeer
yayi bacci saboda haka itama ta kwanta gefen shi sai bacci "
" To rayuwa tanata tafiya don ynx cikin *Shukrah* ya shiga watan haihuwa saboda haka
*safeer* da *Ahmad* sukayi handling company 'n su gurin wani
yaron Ahmad *Ammar* don Ammar yanada Amana da hankali sosai, zaman gida kawae
su *Safeer* suke, Da zarar
*Shukrah* tayi wani motsi na nuna alamar
jin ciwo zasuyo kanta suna jero mata sannu "
" To ana cikin haka har E D D' n Shukrah ya cika, tun
safe Azeeza ta shirya musu trolley, Shukrah dae ta dage bazata hospital ba wae
ita batajin ciwo saboda hk a gida zata haihu "
" Haka suka yini lafiya cikin gidan, sai zuwa yamma
sannan Mara da bayan Shukrah suka fara mata ciwo nan fa hankalin kowa ya tashi
ba kamar Safeer da hankalin ya gama tashi, wani karfi yaji yazo mishi bemasan
sanda ya daga Shukrah ba sai mota, nan Ahmad ya biyo shi, nan Azeeza ma ta fito
da trolley sai hospital.........
"Sun isa asibitin cikin sa a aka karbi *Shukrah* aka wuce labour room da ita, Shukrah tafi
karfin awa daya acikin labour room amma ta kasa haihuwa hakan ne ya bawa
likitocin damar bata inducing drug tasha amma ta kasa haihuwar, Anan kuma suka
fara tunanin yimata C. S ".
" *Safeer* ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kewaye yake
ya rasa inda zaisa kansa, duk da Air condition din dake gurin amma gumi sai
zuba yake a jikinsa kafafunsa sai rawa suke jiyake kamar ya cire ciwon ya dawo
kansa, *Azeeza* da *Ahmad*
sai kokarin bashi baki suke amma sam yaki jinsu, ya zauna ma yaki zama
*Shukrah* kam sai ihun ta take tana
kiran *Ammii, Mamah, Aysher, Miemie kai har meela ma sai da Shukrah ta kira,
yana cikin wannan halin daya daga cikin Doctors din da suka karbi
*Shukrah* ya fito Sukayi Saurin mikewa
suka nufeshi, *Safeer* bakinsa sai rawa yake ya kasa ma yimasa magana, doctor
ne ya dafa kafadar *Safeer* yana bashi
baki kafin ya miki masa wani paper wa yayi signing ayiwa *Shukrah* C. S "
" Duk jarumta irin ta *Safeer* besan sanda ya fashe da
kuka ba, da kyar ya karbi pen a hannun Doctor din ya dora kan paper, maganar da
Wata Nurse ta fito tana yiwa doctor be kan yazo *Shukrah* ta haihu ta samu baby
Boy ne yasa *Safeer* wulli da pen &
paper hannunsa ya bi bayan Doctor cikin dakin, nan *Azeeza* da *Ahmad*
ma suka rufa musu baya sai dakin, Sanda suka shiga dakin har Nurse ta
dauki Babyn ta fice dashi"
" *safeer* ya
kara da gudu da niyyar rungume *Shukrah*
Amma sai yayi Saurin dakatar da kansa don ganin tayi wani mugun nushin
sai ga baby Girl ta fito, Zaro ido sukayi cike da mamaki da kuma farin ciki,
*Safeer* ya rungume *Shukrah* tsam a
jikinsa yasa kukan farinciki, besan da bakin da zeyiwa *Shukrah* godiya ba don ta bashi farin cikin sa Twins,
*Shukrah* tayi karfin hali tasa hannunta tana goge wa *safeer* hawayen idonsa,
Don tafi kowa sanin irin son da *safeer*
yakewa yara, Doctor ne yayi gyaran murya *Safeer* yayi Saurin daga
*Shukrah* yana goge hawayen daya gangaro masa "
" Nan dae Nurses su 2 suka shigo da babies *Safeer*
yayi Saurin karasawa ya karbi Baby girl din shikuma *Ahmad* ya karbi boy din, anan kuma Nurse ta shiga da
*Shukrah* toilet don ta gyara jikinta
"
" Nan safeer ya shiga snapping babies yayi marking duk
contact nasa na WhatsApp yayi musu sending, nan fa aka fara kiransa ana masa
murna, Aysher ma ta kirasa sanda yace takai wa *Mamah* wayar kin karba tayi, tadai ce Allah ya raya
*Twins* "
" washe gari akayi discharging nasu, Abokan aikin su
*Ahmad* sai zuwa suke, kayan Babies kuwa
kamar zasuyi magana don yawa, sai zuwa dare sannan *safeer* ya samu damar kebewa da *Shukrah* ya zuba mata ido tana rike da Baby girl
dinta, tsawon minti Arba 'in suna hk, Har sai da *Shukrah* ta gaji da da kallon
nasa tayi magana"
"Your look is so intense, it makes me nervous, what do
you want? *Shukrah* ta tambayi *Safeer* sanda ta dauke kanta "
" *safeer* ma
dauke kansa yayi sannan yace ALL what i want is your love, can you do me a
favour and give me that much? I promise to live with you for ever, Indeed you
are a blessing, kinbani farin ciki a rayuwa ta, i have never expected dis,
being a Daddy of twins at this very tym"
"Why not? I will give you my luv for the joy you
brought into my life, for understanding my needs, for allowing me to be part of
you at the same time for turning back to the face of all my mistakes *Shukrah* tace harda dan hawayenta "
" Rungume *Shukrah* ,
*safeer* yayi itada Babies dinsu
ya musu selfie.......
" *SAFEER* ya
kurawa twins dinsa ido fuskarsa dauke da murmushi, yanaji a ransa yanzu bashida
wata matsala tunda Allah ya masa babbar kyauta wadda ba kowa yake waba, a fili
yace 'Alhamdulillahi'
" *SHUKRAH* ta juyo ta kalleshi ya mata murmushi yace
'Baki tambayeni
wani suna nayi wa yara khudubah (Huduba)
dashi ba'
" tayi murmushi sannan tace abinda nake taso in tambaya
kenan wallahi, wani suna aka sa musu?
"Murmushi Ya fadada sannan ya dauki Baby boy dinsa ya
rungume yace
'Saboda karamci, da
mutunci, da Alfarma da kuma babbar kyauta da *ALHAJI* *SARAKEE*
Yamin yasa nayiwa dana huduba da suna *AMEENULLAH* Alkunyar sa kuma shine *LABEEB* Inaso a ringa kiransa haka don suna ne me
kyau sosai, Ya ajiye shi gefe sannan ya dauki Baby girl din, itadai *SHUKRAH* sakin baki tayi bawae batayi
sammanin haka ba, a a kawae dae abin yazo mata a *BAZATA* ne, Ta zame daga kan
bed din ta durkusa akan kafafunta zatayi magana *SAFEER* Shima ya zame yayi Saurin sa hannunsa daya ya
rufe mata baki sannan yace, ita kuma nasa mata sunan Mamana wato Khadeeja za a
dinga kiranta da suna *LABEEBA* "
" Hawayen farin ciki ne yazubo mata tayi Saurin goge wa
tana murmushi tana kara jin son *SAFEER*
Na ratsa jinin jikinta don ya mata komai a rayuwa yayi wa *DADDY* '
*NTA*Takwara, tasa hannu ta zame nasa hannun sannan tace
' Hakika banida bakin
yimaka godiya don kayiwa mahaifi na abinda ba a taba yimasa, yayi Saurin
dakatar da ita ta hanyar cewa
'Nima Yamin abinda ba
a taba min ba a rayuwa ta inajinsa kamar *ABBANA* , banajin a kawae abinda zan
masa nabiya sa abinda yamin saboda hk karki ce zaki min godiya kinji "
" Wayarsa ce ta fara ringing yayi Saurin mikewa ya
dauko akan bed *MAMAH* Yagani ajikin
screen din yayi Saurin dagawa yamata sallama "
" Idan kai bazaka dawo ba to ka kawo min *SHUKRAH* kaji ko bakaji ba tace rai a bace "
" Dakyar ya iya bude baki yace *MAMAH* naji kuma insha Allah cikin satin nan zamu
dawo "
" Gobe nake so ku dawo na fada maka... Tana gama fadar
haka ta kashe wayarta "
" *SAFEER* YA
juyo ya kalleta yace *MAMAH* Tace gobe
take so mukoma so ynx zan fita nayi mana Booking flight, Da sauri *SHUKRAH*
tace to don itama zaman garin ya isheta musamman ma ynx data haihu tana bukatar
ganinta kusada *AMMI*' *NTA*
, tare suka fito *AZEEZA* Kadai ce a a parlour don
*AHMAD* Bayanan, *SHUKRAH* ta mika mata babyn hannunta sannan
ta karbi na hannun *SAFEER* , "
" shiko yana fita ya nemi commercial car yace driver ya
kaishi ' *AL* *HARAMAIN* *TRAVEL* *AND*
*TOURS* *LIMITED* , be dauki wani lokaciba ya gama komai, sai da ya shiga wani
shopping complex yayi shopping sosai sannan ya wuce gidan, Sanda ya isa ana
kiraye~kirayen sallar magrib nan yayi alwalla suka fice mosque tare da *AHMAD*, sai da su kayi sallah isha sannan suka kamo
hanyar gida, a hanyar dawowar sune *SAFEER*
Yakewa *AHMAD* Bayanin tafiyar su gobe, sosai *AHMAD* Yanuna rashin jin
dadin tafiyar su koba komai sun saba, kuma yana jin tausayin *Azeeza* sosai don
tasa *LABEEB*& *LABEEBA* Sosai azuciyarta, besan yadda zasuyi goben ba,
Saurin goge Hawayen dasuka taru a idon sa yayi dai dai sanda suke shigowa
parlourn gidan, a tare *Ahmad*
& *Safeer* sukaci abinci don
tuni su *SHUKRAH* sukaci nasu "
" Sanda suka gama cin abincin sukayi sallama, lokacin
da *Safeer* yashiga dakin tararwa yayi *SHUKRAH* na hada musu trolley yakarasa
kan bed ya dauko *LABEEBA* Yamata kiss a kanta yace Babyna ki tashi ga *PAPA*
YA dawo, Baby kice you are welcome *Papa*"
" *SHUKRAH*tasa dariya tace kai *ya* *safeer* karfa son baby yamaka illa, yarinyar da
kwanan ta 3 kawae a duniya kake expecting tayi welcoming naka "
" Hade rai *safeer* yayi yana hararar ta toke ina ruwan
ki, Ni banason irin hk ehe, Dariyar ta cigaba da yi har sai da ta k'ularda
Safeer yaja tsaki sannan ya kwantarda *Labeeba* ya musu addu a sannan ya
kwanta"
"Sanda *SHUKRAH* ta gama hada trolley toilet ta shige
tayi wanka, koda ta fito kitchen ta wuce tahada tea tasha sannan ta dawo dakin
tasaka wata doguwar sleeping dress ta kwanta a bayan *Safeer* "
" Ya Safeer kayi hakuri dani naga kamar kayi fushi,
Shiru yayi mata alhalin yana jinta, nan ta cigaba da masa magiya amma yaki
kulawa, zuwa can dabara ta fado mata tasa harshen ta a fuskarsa tafara yawo
dashi, nan *safeer* ya juyo ya rungume ta....
*washe* *gari*
"Dukansu a airport, *Azeeza* rungume da *labeeba* tanata kuka kamar shi aka aikota, ita
tunaninta daya yadda zatayi rayuwa bau tare da Shukrah ba gakuma twins da tasa
su a zuciyarta,j *Ahmad* ganin kukan *Azeeza* bame karewabane yasashi mata alkawarin kaita Nigeria before or after
naming ceremony, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida
~~~~~~~~~~~~~~~
*HAIYDAR* zaune gaban Hajiyarsa da alama fada take masa
"Haiydar wai
kai yaushe zaka nutsu kayi Aure ne, akan idonka Safeer yayi Aure gashi har
matar ta haihu amma kai kaki kafitarda matar ko"
"Ba hk bane Hajiya yarinyar da nakeso yanzu tayi junior
waec dinta, so jira nake tayi grads sai a fara maganar auren "
" Kana hauka ne Haiydar, nace hauka kake Haiydar,
ajinka zan cigaba da zama da kai har nanda shekara 3 to inma bacci kake ka
farka, Nabaka two weeks kakawo min mata ko in zabo maka da kaina hajiya ta fada
rai bace daga hk tafice ta barshi yana tunanin wae shi za a samowa mata yarasa
me zai kira wannan auren da Hajiya take shirin yimasa (Niko nace *AUREN*
*BAZATA* Xatayi maka), Ringing din dawayarsa yake ne yasa shi daukan car key
dinsa ya fice daga gidan, tafiyar minti talatin ce ta kai shi Airport, nan ya
kwashe su sai gidan Mamah, A hanya ne yake fadawa Safeer Hajiya zatamai AUREN
BAZATA, me Safeer zeyi inba dariya ba. . . Dakyar ya tsayar da dariyar sa yace
karka damu Haiydar *AUREN* *BAZATA*
*ALHERI* *NE*. . .
"Sanda suka karasa gidan Mamah cike suka shame shi da
mutane as if to say ranar sunan ne, *MIEMIE*
Tazo da gudu ta rungume *SHUKRAH*
tana murna da ganinta nan dae aka fara gaishe gaishe, daga nan
*Safeer* ya fadawa *Mamah* ze tafi gidan su *Haiydar*don nan akwai
hayaniya sosai, To kawae yace sannan suka fice "
" Saida *SHUKRAH*tayi wanka taci abinci Sannan ta kira
*Amminta*, *Ammii* naganin kiran amma
taki picking don ita dama me alkunya ce, Text *SHUKRAH* ta mata tace sun sauka lafiya, Bayan kusan
awa daya ta mata reply tace sannun ku to"
*MIEMIE* sai nan nan
takeda twins taki yarda kowa ya dauke su, wae 'ya' yanta ne
Washe gari *Ibteesam* tazo ta kawo wa babies kaya masu yawa,
Hajiyar Haiydar ma tazo nan take yiwa Mamah bayani cewa tabawa Haiydar two
weeks ya kawo mata kuma taga kamar be dau maganar T serious ba amma dae ta
shirya bashi mamaki, don dama akwai wata yar yayarta *Zafeera* zatayi wa yayar tata magana sai a hadasu don
zafeera yarinya ce mai hankali da nutsuwa sosai, dama tun farko tayi wa Haiydar
sha awarta amma da taga kamar zafeera bata gabansa yasa takyale amma tunda dae
yanzu yaki kawo matar toko zata hadasu, sosai Mamah ta goyawa Hajiya baya
acewarta ae Haiydar ya girma, kuma ma ae shirme me zai sashi cewa wae sai ya
jira Miemie, nan dae suka gama magana Hajiya tayiwa Mamah alkawarin duk me ake
ciki zata fada mata, Sanda zata tafi ta ajiye wa twins Rapper na 100 sannan ta
fice, Mamah ta bita tana mata godiya "
" Duk wannan shirin da hajiya takeyi Haiydar be Sani ba
don shi tunda tamishi magana bata kuma yimasa ba, saboda hk yace ko dama wasa
take masa shiyasa ma yasake ya cigaba da harkokinsa"
"Gobe ne suna amma har yau *Ammii* taki zuwa taga su
*labeeb* ,, *Mamah* ta kirata yafi a Kirga amma kullum cewa take gata nan da
taga abin bame karewa bane yasa takashe wayarta, Gidan *Ammii* ya cika da yan uwa da abokan arziki amma ba
*SHUKRAH* koda sukayi wa *Ammii* maganar sunason akawo ta gidan ayi sunan anan
cewa tayi ita ba ruwanta haka sukayi ta surutansu suka gaji"
"Da yamma Alh Sarakee ya duro Nigeria don dama ya dade
a Senegal bayanan ma akayi haihuwar amma *SHUKRAH* ta mishi albishir din
*Safeer* ya mishi takwara, Sanda ya iso
ana kiran sallar la asar saboda haka saida ya tsaya yayi sallah sannan ya
karaso gida, *Ammii* ta mishi girki kala
kala amma saboda zumudin ganin *Labeeb*& *labeeba* Yasa koda yayi wanka be tsaya cin abinci ba
ya dauki babbar trolley daya shigo da ita ya fice, Sanda yake tada mota *Ammii*
ta same shi
"Yanzu Daddy
fisabilillah gidan mutane xakaje ba kara
ba alkunya, koni fa har yau banje ba"
"Daddy dariya yayi sannan yace to Ammii ni na hanaki
zuwa ne? Akwai bukatar naga grand child's dina shiyasa kikaga ma nadawo don
bayau zan dawo ba ka ida sai next week zan dawo amma na tattara komai na ajiye
nazo sannan kice zaki hanamin zuwa ganin su, yana kaiwa nan yayi reversed ya
fice daga gidan, jiki ba kwari Ammii ta koma cikin gidan azuciyarta tana
mamakin Daddy don gaba daya yariga ya saba da turawa komai nasa irin nasu yake
"
" Cikin Sa a Daddy ya samu Safeer da abbah a guest room
da alama suna tattatuna abu me mahimmanci ne, Da fara 'a Abbah ya tare shi yayi
da Safeer ya durkusa har kasa ya gaida shi cikeda ladabi "
" Ashe kuma an samu karuwa? *DADDY* Yace yana maida
kallon sa gun *ABBAH*
"wallahi kam an samu Alh. *sarakee* D Hajiya
*Khadija* Abban yace fuskarsa dauke da
murna, Allah dae ya raya mana su bisa tafarkin addinin musulunci "
" Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen
"gyaran murya Daddy yayi sannan yace Madallah Nagode da Girmamawa ko kuma
ince da bani wani matsayi da kayi safeer, hakika kai abin alfahari ne kuma ka
can can chi yabo Allah ya maka albarka,
Sakamon alkhairin dakamin ka sama yaronka sunana nayi alkawarin daukan nauyin
duk wani abu da za'a ci ko sha na kuma dau nauyin gurin da za'a zauna kai hatta
ragunan sunanma na hutar da kai insha Allah daga nan zuwa dare za a kawo "
" Abbah yayi Saurin kallon shi yace haba Alhaji ae baza
' ayi haka ba, hidimar tayi yawa ae yau fa ka dawo kasar ma gaba daya, ka
barshi wallahi zamuyi komai insha Allah "
" Murrmushin manya Daddy yayi yace bafa ku kuka Sani ba
haka kuma badan bazaku iyaba yasa zanyi
A a kawae dae tukwucin Alheri ne, so karku damu kudai kawai kuyi fatan
ayi taro lafiya a tashi lafiya "
Godiya dukansu suka
mai kafin safeer yace bari yaje yasa akawo Twins, to Daddy yace sannan suka
cigaba da hirar su da Abbah"
"Sanda safeer ya shiga cikin gidan A parlour ya tararda
*AYSHER*, *SHUKRAH* & *MIEMIE*,
Shukrah na Rike da Labeeba yayinda miemie ta rike labeeb, hararar miemie yayi
sannan yace waye ya baki ixinin daukar min yaro salon kiyar dashi ko, ke daman
ba nutsuwa gareki ba, Hade rai Miemie tayi ta ajiye labeeb da karfi kan kujera
har sai da yaron ya fasa kuka, Safeer ya zo da gudu zai rike ta tayi dakin
Mamah da gudu ya bita, Aysher ce tayi Saurin daga labeeb tana jijjiga shi
"
" Jikin Hajiyar Haiydar ta fada, Hajiya Kinga ya Safeer
yanamin gori akan 'ya' yansa ko, kuma don na ajiye masa shine zai dakeni, tana
kaiwa nan ta fashe da kuka kamar wadda ya daka, Shi safeer ma mamaki ne ya hana
masa cewa komai shi a duniya be taba ganin yarinya irin miemie ba, Mamah tace
ae sai ka fita tunda burinka ya cika kasata kuka kaji dadi, Miemie ta fakin
idon Mamah tamasa gwalo tace cikeda shagwaba Mamah yaushe zaki haifar mana
twins muma adena min gori "
" dariya sukayi dukansu sannan safeer ya fice yasa
Aysher Da Shukrah su kaiwa Daddy twins"
WASHE GARI
Tun asuba mutane suka fara cika gidan duk da cewa a tourist
camp za ayi taron sunan amma kafin7:00 gida ba matsaka tsinke, ba ayi girki a
gida ba kasancewar an riga anyi order a can tourist camp din snacks kuma anyi
order a me. Biggs, Drink ko Wata Aminiyar Mamah ce Hajiya Maryam Anas ce tadau
nauyi "
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
12:00pm na isa tourist camp gurin ya cika sosai da yan uwa
da abokan arziki, Bayan bude taro da Addu ' a da wata babbar Malama *safiyya*
*yakasai* da tayi ne kuma aka vukaci D. J Yasa sauti nan fa yan *SHUKRAH NOVELS
suka zage sai rawa suke ba kamar Safiyya* *Galadanchi* da *Zee* *zee*, sai da
komai ya lafa sannan aka fara rabon Mutane sai karba suke, can nagano wasu
mutane sun koma gefe sunata dura abinci da lemo a jaka kara matsawa nayi don
ganin ko suwaye, wazan gani inba, *MEELA*
*SOFTIE* *EESHATULLAH* *MAMAH*
*SKY* *FEUXER* *MARYAM*& *NURIYYA* ba, suna ganina suka fara raba ido, Haka
dae taro ya watse mutane sae sawa twins albarka suke "
" Sai wajen 11:00pm safeer ya samu kubewa da Shukrah,
fitowarta a wanka knn tana shiryawa yakarasa ya rungume ta taba ya a tare suka
sauke ajiyar zuciya, yace mata a cikin kunnen ta
"Bazan taba gajiya da yimiki godiya ba Shukrah kinmin
komai a rayuwa ta, Allah ya miki Albarka kinji, yanzu ki fadamin duk me kike so
insha Allah zan miki "
" Shukrah tai Saurin juyowa tana kallon shi sannan tace
da gaske ya Safeer "
" Yace Da gaske "
Tace Aiki nake so na fara, yace wannan shine yafi komai
sauki, akwai wata kawar Mamah tare sukayi
" *SHUKRAH* tace karka cemin *AUNTY MARYAM ANAS*,
*Safeer* ya kalleta cikeda mamaki sannan yace karki ce kinsan ta?
" *SHUKRAH* ta mishi hararar wasa sannan tace lallai
yaza ayi ace bansan taba tare fa sukayi secondry skul da *Ammii* fa kuma tana
zuwa gida sosai, *Safeer* yayi murmushi
mai kyau sannan yace Masha Allah ynx inna fita zanyi wa *Mamah* magana insha
Allah komai zaizo da sauki don *Mamah* tana bani labarin saukin kan *Mummy
Maryam Anas* tun suna uni maid haka take duk da kasancewar ta over roller amma
bata da girma kai, *SHUKRAH* ma murmushi
tayi sannan tace Allah sarki Allah dae ya shige mata gaba, kuma nagode sosai da
Amincewar dakayi *PAPA'N TWINS*, matsowa *Safeer*yayi ya rungume ta sosai
sannan yace kinfi karfin komai a gurina wallahi *SHUKRAH* Allah dae yayi miki Albarka ya kuma kara miki
lafiya ya kare ki daga sharrin masu sharri, sosai *SHUKRAH*taji dadin addu 'ar
tasa saboda haka ta manna bakinta akan nashi ta soma kissing dinsa sundau
lokaci sosai a hk kafin *LABEEB*ya fasa kuka sukayi Saurin janye wa haka kuma
suka nufeshi da sauri,, *SHUKRAH* C tayi nasarar daukan sa Tasan yunwa yakeji
don duk basu zo hannunta ba, shiyasa tayi Saurin yaye rigarta tasoma feeding
nashi"
"sanda *Safeer* ya fita a dakin gurin *Mamah* yaje
yamata bayani yadda sukayi da *SHUKRAH* kuma hakan ya mata dadi at last dae
zata taimaki mutane da yawa kuma ta mishi alkawarin zatayi, *Mummy Maryam Anas*
maganar a yau ba sai gobe ba, nan
*Safeer* yashiga godiya sannan sukayi sallama da *Mamah* da kanshi ya kai Hajiyar *Haiydar* gida
sannan sukaje ya samu *Haiydar a gida saboda hk suka zauna sunata hira Safeer*
sai
Tsokanar *Haiydar* yake wae za ayi masa *AUREN BAZATA* Sai
da *Haiydar* ya bata ransa sannan *Safeer* ya kyaleshi sanda ya masa sallama ma
ko answer wa ma beyi ba haka *Safeer* ya tafi ya nayiwa *Haiydar* dariyar
mugunta"
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Hajiyar Haiydar* T samu yayar ta *Hajiya Safiya* kan tana son hada *Haiydar*
& *Zafeera* Aure kuma Alhamdulillahi
maganar ta tasamu karbuwa a wajen *Hajiya safiya Da Alhaji mai kano* mahaifin
*Zafeera* kenan Don Alhajin cewa yayi nanda wata biyu za ayi bikin acewarsa ae
su suka haifi yaran kuma sunada hakki akan su haka kuma suna da ikon zaba musu
abinda yayi dai~dai da rayuwar su, saboda hk ba bukatar tambayar *Zafeera* ko
bata sonsa"
" *ZAFEERA* Itace 'ya mace guda daya tilo a gurin
*Hajiya Safiya* shiyasa ta dauki son duniya ta dora mata"
"hajiya kawae dauriya take don sam bata son abinda zai
taba *gudaliyar ta*,kuma tana tunanin yadda zasu kwashe da *Zafeera* DUK da dae
tanada saukin kai kuma tasan bazata ce A a ba, Amma tana ganin dae kamar an
shiga hakkin ta, da kyar ta iya bude baki tace Allah dae ya sa komai yazo da
sauki "
" Ameen Hajiyar Haiydar tace "
" Shiko *Alhaji Mai kano* cewa su kashe kansu in anyi
AUREN, daga nan dae ya mike ya fice, To itama Hajiyar Haiydar sallama tayi wa
Hajiyar Zafeera ta fice "
" Da daddare har Zafeera ta kwanta Hajiya ta shigo ta
kwashe duk yadda sukayi da Hajiyar Haiydar ta fada mata sannan tace
"kuma
Baffanki yasa bikin Nan da wata biyu,"
"Zuciyar Zafeera ta bada wani *Dum Dum Dum* tanason
Hajiyar ta, kuma bata jin zata iya watsa kasa a idanun soyayyar da Hajiyar take
mata uwa uba kuma tarbiyyar da Hajiyar tamata, Saboda hk tace *TO* Asanyaye
"
" Sosai Hajiya taji tausayin 'yar tata amma saboda
batason maganar tayi nisa har tasa *Zafeera* kuka yasata mikewa tace kiyi Addu'
a *Angel* sai da safe "
" nanma *To*kawai tace mata sannan ta kwanta"
"Duk wannan Abun da ake Haiydar be Sani ba don Hajiyar
bata kuma yimasa maganar ba, cikin sati biyu magana ta kankama don har ta isa
katsina dangin su Haiydar din kenan, Hajiyar Haiydar da Hajiyar zafeera sun
shirya staf zasuje Dubai don hado lefen *Zafeera*, koda *Haiydar* ya tamvayeta
inda zata cewa tayi ina ruwansa "
" Sati daya kawae su Hajiya sukayi suka hado kaya masu
yawan gaske uwa uba kuma ga kyau da tsada, Sai bayan da suka dawo ne Hajiyar
tace wae yazo yaga lefen shi, ko kallon kayan beyiba yayi fice war sa don wani
mugun takaichi ne ya durar mishi"
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
"yau kwanan su *LABEEB DA LABEEBA* 40 A duniya amma
*Ammii* bata taba sasu a idanun ta ba sai dae ko a picture shidin ma sau biyu
ne, Ranar da *AREEF* Yaje ganin su yayi snapping dinsu ya nuna mata sanda ya
dawo sai kuma sanda *SHUKRAH* tayi mata sending a WhatsApp "
" Wannan dalilin ne yasa *Mamah Shukrah Aysher da
Miemie* suka shirya mata ziyarar *BAZATA*.. . .
" *AMMII* Na daga cikin daki ta jiyo sallamar su, ta
fito da sauri ta tare shu da fara 'arta
"Sannunku da
zuwa, wannan irin zuwa na bazata haka, da kun Sani kun kira ni kun cemin zakuzo
ae"
" *Mamah* ta dan harare ta sannan tace to in an kira
picking kike, ae ina sane na shirya wannan zuwan bazatan sai da na kira *AREEF*
Ma na tambaye shi ko kina nn ya tabbatar min kina nn din sannan muka tawo
"
" Murmushi kawae *AMMII* Tayi ta wuce fridge ta kawo
musu drinks, *Aysher* ta durkusa kusa da *Mamah* tana gaida *AMMII*, da fara a
ta Answer sannan *MIEMIE* MA ta durkusa ta gaida ta, *SHUKRAH*ma ta gaida ta, ta Answer ba tare da
ta kalle taba "
*MAMAH* Ta dawo da kallon ta gun *AMMII* Sannan tace, ae
kawo muki twins mukayi tunda kinki zuwa ki gansu, Murmushi *AMMII*Tayi sannan
tace ba haka bane ba, abubuwa ne sukayi min yawa, *Mamah* tace to aini gashi
nan nazo da kai na"
" *SHUKRAH* ta dan kallo *AMMII* Aiko suka hada ido,
Ammii tayi saurin dauke idonta, Shukrah tayi Murmushi sannan ta mike ta do rawa
Mata *LABEEB* Kan cinyarta, *AMMII* Tayi
saurin sa hannu ta ture shi saura kadan ya fadi Shukrah ta tare shi tana
Murmushi, Mamah tace yanzu dan Allah wae sai ki ture shi haba *Ammii* gaskiya
ki rage wannan kawaichin naki yayi yawa wlh ynx zamani ya canja fa, Dariya
*Ammii* tayi tace to ae shi kunya, kara da kawaichi a jinin fulani yake, Amma
kamar yadda kika ce na rage zan danyi kokari na rage din, yawwa ae haka akeso
*Mamah* tace tana do rawa *Ammii* *Labeeba* akan cinyarta, cikeda kunya
*Ammii'n* ta daga ta tana Murmushi sannan tace Allah ya raya su yasa masu jin
k'ai ne"
"Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen"
"Yinin ranar duk sunyi shine a gidan *Ammii* amma
*Mamah* ta kula bawata magana data shiga tsakaninsu da *SHUKRAH* a zuciyarta
tana mamakin hali irin na *Ammii* kusan wata biyar fa bataga Shukrah 'n ba tun
tafiyar su San Francisco gashi ynx tazo amma sai share ta take, Tana wannan
tunanin ne taga *Ammii* ta mike ta shige Bed room, *Mamah*ta Dawo da kallon ta
gun *SHUKRAH* tace
*SHUKRAH* tashi kibi *Ammii' nki* kuyi magana kinji
"
Kamar dama jira take
tayi saurin mikewa ta shige dakin da sauri, juyawa Mamah tayi azuciyarta tana
dada mamakin *Ammii*, Sanda *Shukrah* ta shiga dakin lokacin ita kuma Ammi zata
fito, Shukrah tayi saurin rike hannunta tace *AMMA NA* ynx kin dena sona ko? Ta fadi haka ne
sanda hawaye ke fitowa a idanunta "
" *Ammii* cikeda
tausayin 'yar tata tace ban dena sonki ba *SHUKRAH* ya jikin ki?
"jiki Alhamdulillahi, twins suna fushi dake tunda kinki
zuwa ganin su, Dariya kawae *Ammii* tayi sannan tace ae ynx gashi nan kun kawo
su ko?
Eh mun kawo su kam, sun danyi hirar yaushe gamo sannan suka
fito, sai bayan sallah 'r magrib sannan suka tafi bayan *Ammii* ta cika su da
tsaraba "
" washe gari da sassafe *Safeer* ya shigo cikin gidan
*Mamah* ya tarar a parlour tana Karanta *Hisnul muslim* ya durkusa kusa da ita
yana gaida ta, Bayan sun gama gaisawa kuma shiru ne ya biyo baya don *Mamah*
cigaba tayi da karatun ta shi kuma *safeer* zama yayi yana dan Satar kallon ta,
lura da hakan da *Mamah* tayi ne yasa ta ajiye littafin hannunta ta ta dawo da
kallon ta gurinsa "
" Ya akayi ne *Safeer*?
"kara kasa da kansa yayi kafin yace' *Mamah* dama zuwa
nayi mu tafi da *SHUKRAH* & *TWINS*
Tunda sunyi Arba ' in dinko?
"Mamah ta rike ha'ba tana masa kallon mamaki sannan
tace to fitsararre mara kunya ni ae nafika sanin sunyi Arba,in din, to barin
fada maka baxata koma ba sai nan da two weeks don bamu gama gyaran da muke
ba"
*Safeer*ya bata rai kamar zeyi kuka yace wae wannan wane
irin gyara ne dan Allah, nidae kawae a barshi haka wannan ma wanda akayi mata
ya isa "
" Dalla can rufe min baki mara kunya kawae sai kace
bakai ake yiwa gyaran ba, ta nuna masa kofa tashi ka fita ka bani guri, haka
*Safeer*din ya fita yana mita
"Wannan wace
irin rayuwa ce, dan anga Mutum me hakurine sai a dinga masa yadda ake so, an
cemin 40 days zasuyi na hakura amma ynx an canja magana wae sai nn da two
weeks, yaja tsaki sanda ya shige motar sa ya bar gidan"
*SHUKRAH* *SHUKRAH* *SHUKRAH*, Na am *Mamah* Shukrah ta
Answer sanda take fitowa daga daki, wuce kije kitchen ki dauko babbar tukunya a
dora ruwan wanka, to kawae Shukrah tace sannan ta dauko ta ajiye a gaban
Mamah"
"Sassaken bagaruwa Mamah ta zuba sannan ta matse lemon
tsami akai tace Aysher tashi kije ki ta fasa, in yayi saiki jiya ki kira
Shukrah ta shiga ciki"
"Sanda Shukrah ta fito a wanka Mamah tasa Aysher ta
dauko kaskon turaren wuta da bucket na karfe, Mamah tasa Kaskon cikin bucket
din tazuba angurya(wanda ake samu a jikin audiga) tazuba bawon (kwanson) citta
Shukrah ta zauna akai, Bayan an gama wannan Mamah ta kara zuba wani turare da
wata kawar ta ta kawo mata daga Senegal "
" T haka dae rayuwa ta cigaba da tafiya kuma yau
Shukrah tayi sati biyun da Mamah ta kara mata, Mamah tasan halin Safeer sarai
shiyasa ma bata kirasa ta tuna masa ba, Amma ga mamakin ta har bayan magrib Bai
shigoba, abin ya damu Shukrah sosai shiyasa ta faki idon Mamah ta shige dakin
ta fara kiran wayarsa, bugu biyu tayi yayi picking "
" Hello *Papan Twins*
"Yap *Mamin Twins* ya kuke?
"Lafiya kalau muke, kai muketa jira dae"
"Murmushi Safeer yayi wanda har Shukrah na iya jiyo
sautinsa yace ke bakin biyewa Mamah ba kin share ni, nifa da har na fara
tunanin dama akwai wata yarinya teemerh luv tana masifar sona to da har nayi
niyyar zuwa gurin Dad nata in nemi AUREN ta nanda two weeks in za ayi bikin
Haiydar a hada namu kawai "
" Shukrah ta saki kukan shagwaba tana bubbuga kafa Ni
wallahi bazan yarda ba, Ni wallahi kawai kazo mu tafi ko in tawo da kai na
"
" Kukan da Shukrah take ne yasa Mamah ta shigo dakin,
jin abinda Shukran ke cewa yasa Mamah ta fahimci da wanda suke wayar, saboda haka
ta ta koma ta ta samu Miemie aparlour
"Miemie je ki
kiramin Aysher tazo ku kai Shukrah gidanta, to Miemie tace sannan taje ta kira
ta, Mamah da kanta tayi wa Shukrah bayanin Su Aysher zasu rakata, Bayan kamar
minti goma sha biyar Shukrah ta shirya tsaf haka ta shirya twins, Aysher da
Miemie suka tayata sa kaya a booth, Mamah dae tana tsaye sai da taga fitar su
ta koma ciki... . .
"Cikin Mota *SHUKRAH* tayi wa *SAFEER* Text tace masa
tana hanya, zo kuga murna gun sa don beyi tunanin *Mamah* zata yarda ta barta
ta tawo ba, saboda tsabar zumudi zaman cikin gidan gagarar sa yayi saboda haka
ya sa jallabiyya ya fito ya zauna gurin gate man, jefi jefi suke hira, Zaman
kamar minti goma sha biyar yayi yajiyo horn a, ko ba a fada ba yasan su
*SHUKRAH* ne shiyasa ma yayi Saurin mikewa yaje get din da sauri da nufin bude
musu, get man yayi Saurin karaso wa "
" Ranka ya dade, kabari za a bude yace yana kara sawa
jikin get din"
"Yi sauri ka bude dae, ba surutu nace kayi min ba
*Safeer* yace cikeda kaguwa"
"Nan get man ya bude musu, Aysher ta shigo da motar,
yayi Saurin ban bayan motar, Tun kafin Aysher ta gama Parking *SHUKRAH* ta bude
ta ziro kafarta, kadan ya rage
*labeeba* ta fadi a hannunta, Da
sauri *Safeer* ya karaso ya hada ta da
*labeeba* ya rungume su cikeda so da kaina, sam ya manta ma dasu *Miemie*(Baki
abun magana) suna tsaye "
" Aysher tayi Saurin dauke kanta, *Miemie* ta tabo
Aysher, Aunty Kinga ya *safeer* din nn ko kunyar mu ma beji ba, lallai ",
Aysher ta buge mata baki tace kin cika surutu wallahi, bazaki iya dauke idonki
ba"
"Duk wannan maganar a kunnen *SHUKRAH*sukeyinta shiyasa tayi Saurin ture
*Safeer* din tace su *miemie* na kallon muda, dariya kawae yayi sannan ya daga
kafada irin ko a jikin sa din nn,
*SHUKRAH* ta kallo *Aysher*,
*Aysher* tayi Saurin dauke kai, ita Shukrah dariya ma aysher ta bata
tace Bazaku shiga bane kuka tsaya wae, Aysher tayi Saurin kallon ta ta girgiza
kai tace baxamu shiga ba Aunty dare ya fara yi kuma ban iya driving din dare
ba"
"To Kawai *SHUKRAH* Tace sannan *MIEMIE* ta mikawa
*Safeer* *Labeeb* dake hannun ta, *SAFEER* Tsabar mugunta sanda ya karbe shi
sai da ya murde hannun *MIEMIE* yace fitsararriya kawai, Allah ya sa dae kina
karatu don naga har ynx kanki yana rawa "
" Yar kara *Miemie*ta saki sannan ta kallo shi da fuskar
tausayi tace Eyya ya *Safeer* akwai zafi fa, cika mata hannun yayi yace wuce ki
bani guri ni, harda dan gudun ta ta wuce ta shiga mota *Aysher* tayi musu sai
da safe sannan ta shiga motar tayi reversed T fice a gidan"
10:15 *Safeer* ya samu *SHUKRAH* a dakinta tana shirin
kwanciya, ya karaso ya rungume ta ta baya yace mata a kunnen ta kinsan fa yau
ke amarya ce, hope you are ready "
*SHUKRAH*ta danyi murmushi tace twins dae suna jinka ni ba
ruwa na, Dariya shima yayi ya juya ya kallon su, bacci suke hankali kwance, ya
dawo da kallo shi gurinta yace Bawani nn wayo kike son min, ae sun riga sunyi
bacci, Dan ture sa *SHUKRAH* tayi sannan ta ja hannunsa suka kwanta suna
fuskantar junansu "
" *safeer* ya
kara matsowa jikinta yace mata *i luv u Babe beyond your expectation*
"Murmushi *SHUKRAH* tayi tace kayi shiru bacci zamuyi, Matseta *Safeer* ya
kuma yi sannan yace tunda nake da ke ban taba jin kince min i luv u ba, kodai
har ynx bakya sona ne"
" *SHUKRAH* tayi Saurin matse hannunsa dake cikin nata
haka kuma ta runtse idonta don tana masifar jin nauyin kalmar nan, dakyar ta
iya bude baki tace
*My feelings for
you are so strong and deep that i cant convey them in words, because i found no
word strong enough to tell you how much i luv u, You are more than amazing, my
heart is all yours*~i luv u~"
"tana kaiwa nn ta kifa kanta jikin pillow tana dariya
kasa kasa, *Safeer* fa be taba tunanin jin wannan maganar a bakin taba though
he's quit sure tana sonsa, tunda dae alamu sun nuna hkn, Saurin dago kanta yayi
ya zira harshen sa cikin bakinta ya fara tsotsa cikeda so da kauna da kuma
kewarta, kara shigewa jikinsa tayi don tayi missing dinsa sosai 54 days basa
tare fa, haka dae suka raya wannan daren"
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
"yau saura kwana biyar bikin *Haiydar* amma bemasan me
ake ciki ba, don *hajiya* kobi ta kansa batayi ba, duk wani abu da yakamata da
*Safeer*take hatta kayan da zesa suna gidan *safeer* haka ma invitation cards
suna gurin sa "
03:25 pm *safeer* ya shigo office din *Haiydar* da
sallamarsa ya ajiye envelop kan desk sannan ya zauna yana fuskantar sa, ko
kallo *Safeer* be ishi *haiydar*don yana kula da take~takensa, kuma sam zuciyar
sa bata aminta da yawan zuwan da *safeer* din yake gidan su "
" *Haiydar* ga
wannan invitation cards din ka ne ko zaka bawa abokanka na gida, don na office
na gama basu *Safeer*yace yana nuna masa envelop din daya kawo "
" Murmushin takaichi *haiydar*yayi yana bin *Safeer*da
mugun kallo tsawon lokaci sannan ya dauki envelop din ya mika masa yace cikeda
takaichi karbi ka fitar min a office kafin ranka ya baci, kuma wallahi ka cire
hannunka a maganar nan don gudun bacin rai"
"Dariya Safeer yayi sannan ya mike yace ni bazan karba
ba don bana bukatar su, kuma ni bana gudun bacin rai indae akan wannan maganar
ne "
" Fita Dalla malam kafin rai na ya gama baci don
wallahi komai yana iya faruwa " *Haiydar* yace yana nuna masa kofa, Dariya
*Safeer*
Yayi sannan ya fice yana cewa ba lefin ka bane wallahi nanda
wani dan lokaci zaka dawo dai dai ae *Auren Bazata Alheri ne*
" Kwanaki sunja kuma gobe za a daura Auren *haydar*amma
*Miemie* bata samu labari sai yau din da taji Aysher da Mamah suna maganar, ta
zaro ido sannan tazo da sauri ta durkusa kusa da Mamah tace ki kace wae bikin
ya Haiydar za ayi da wata banida ta fashe da kuka tace wallahi ina sonsa ina
kaunar sa Mamah ku rufa min asiri zan mutu wallahi"
"Aysher ta harare ta tace Dalla can rufe mana baki wae,
ina sonsa ina kaunar sa, ke har kinsan wani so "
" Mamah ta janyo miemee jikinta tace yi hakuri kinji
Kinga ynx makaranta kike kuma wadda zai aura yar uwar sa ce, kema inkin gama
school zai aure ki ae"
"Miemie ta turo baki tace ni wallahi bana son kishiya
sai dae ya sake ta ya aure ni, Mamah tace yawwa hk za ayi ke dai ki kwantar da
hnkl 'nki kawae, ynx kitashi kije daki ki dauki ankon ki kan bed ki gwada"
"Mikewa tayi ta nufi dakin tana bubbuga kafa' ni
wallahi bazan je bikin kishiya ba... .
"Friday 26 october 2015 da karfe hudu na rana daukacin
al'ummar musulmai suka shaida daurin auren *ALIYU KABEER DAN KASA* ( *HAYDAR*)
Da amaryar sa *KHADEEJA ABDALLAH MAI KANO*( *ZAFEERA*) Kan sadaki naira dubu
dari da hamsin, daurin auren da ya samu halartar manya manyan mutane daga fadin
Nigeria kai harma da mak'otan Nigeria, "
Da daddare akayi kayatacciyar dinner ta gani ta fada, abokan
haiydar duk sun halarchi dinner din haka ma kawayen zafeera guri ya cika har ba
masaka tsinke kasan cewar harda yan gayyar sodi ma sun je, haka akaci aka sha
aka tashi mutane sai sawa auren albarka suke "
" Washe gari akayi yini da daddare kuma Aka kai amarya
dakinta, misalin karfe goma sha daya na dare haiydar yana mike a dakinsa na
gidan Hajiya bama shida niyyar fita, a bangaren amarya Zafeera kuwa har ta gaji
da jiran ango ta kwanta ta fara bacci kuma generator ya mutu saboda zafi ya dameta,
mikewa tayi ta leko palour amma duhu ya gauraye gurin da kyar ta lallaba ta
leka dakin dake kusa da nata, wanda take kyautata zaton na Haiydar ne amma ga
mamakin sai taga baya ciki, parlour ta dawo ta zauna amma tsoro ya hana mata
sukuni sai take ganin kamar Mutum ne ke giftawa ta gefen ta hakan yasa ta mike
jikinta na rawa ta shige bedroom dinta ta dau wayar ta, number Safeer ta nemo
tayi dialing, Allah ya taimaka mata kuwa ringing biyu tayi yayi picking
"Hello Safeer "Zafeera tace murya na rawa, ba tare
da ta jira yace wani abu ba ta cigaba
" Safeer dan
Allah kazo ka kunna min generator wallahi tsoro nakeji "
" Shi Haiydar din yana ina? Safeer ya tamvayeta cike da
mamaki"
"Nina wallahi ban Sani ba, dan Allah kazo, Zafeera ta
Bashi answer tana fashewa da kuka, dan har ga Allah tsoro takeji tunda a
gidansu bata saba zama cikin duhu ba "
" To shknn gani nan zuwa ki dena kuka, tare ma zamu
tawo da haiydar din kinji safeer yace sanda ya mike ya dau car key dinsa, dakin
Shukrah ya wuce ya mata bayanin komai, ta mishi Allah ya kiyaye hanya sannan ya
fice da sauri "
" Gidan Hajiyar Haiydar ya wuce direct don ya tabbatar
Haiydar yana can, Sanda ya karaso gidan dakin Haiydar ya tura, ae ko ya ganshi
kwance yana ta bacci abinshi, Safeer yaja tsaki sannan ya karasa ya fara buga
mishi pillow 'nda yake kai da karfi, don iya haushi yau haiydar ya bashi "
" Bude ido Haiydar yayi waze gani in ba Safeer, ya hade
rai yace lafiya zaka tashe ni ina bacci "
" Ba lafiya ba Haiydar kai kazo nan hankalinka a kwance
kana bacci kabar yarinyar mutane a cikin duhu ko, to wallahi ko ka taso mu tafi
ko kuma inje in kira hajiya Safeer yace yana hararar Haiydar "
" Haiydar wanda yasan in aka kiramai hajiya tasa ta
kare yayi Saurin mikewa yana hararar safeer sannan yace muje cike da kulewa,
tabe baki Safeer yayi sannan yayi gaba, shima Haiydar din takalmi kawae Yasa ya
bi bayansa, "
" Cikin mota ba wanda yace da dan uwansa ci kanka kowa
sai cika yake yana batsewa, Sanda suka karaso gidan ne Safeer ya kalli Haiydar
yace
"Haiydar
Zafeera amana ce a gurinka duk wani nauyi nata da hakkin ta a wuyanka ya
rataya, kada ka manta zamu mutu zamu koma ga Allah kuma za a tuhume mu kan duk
wani aiki namu, kuma kasan Allah baya yafe hakkin wani akan wani, iya abinda
kai masa ne kawae in ka rokeshi gafara zai gafarta maka, Wallahi indae k
zalunci yarinyar nan sai Allah ya kamaka karka manta yanzu tun a duniya dan
adam yake girbar abinda ya shuka, kuma a hakanma sai Allah yasoka da rahma,
kaje kayi tunani Haiydar, kada ka yarda ranka ya baci hankalinka ya gushe,
nasan anmaka wannan auren ne ba a son ranka ba wannan aurene na baxata, Amma
inaso kayi tunani sosai nanda dan wani lokaci zakaji dadi, yana kaiwa nan ya
fice ya koma motar sa ba tare da ya jira answer ba, don ya nada tavbacin
nasihar sa ta samu shiga tunda yaga jikin Haiydar din yayi sanyi sosai "
" Generator Haiydar ya kunna sannan Y shiga cikin
gidan, Sanda ya shiga ya ganta a takure idon ta harya kumbura don kukan da
tashi, take yaji wani tausayin ta ya shige shi nasihar safeer ta dawo mishi ya
tuna Zafeera fa yar uwarsa ce Kuma yana daya daga cikin wanda zasuji bakin ciki
in wani ne ya aure ta ya wulakanta ta, sannan ya tuna *RAYUWAR SAFEER DA
SHUKRAH* Ta da data yanzu, yasan hakuri da juriya shine jigon farin cikin su yaji
a ransa yana son dan dana rayuwar kwanciyar hankali da zaman lafiya, shiyasa ma
yaji duk tsanarta ta goge a cikin zuciyarsa haka wani sonta da tausayin ta suka
mamaye zuciyarsa, saboda haka ya karasa gaban ta ya durkusa gab D ita ya riko
hannaye ta duka biyun yana mata wani kallo, tsawon wani lokaci kafin ya bude
bakinsa dakyar yace
"Zafeera ki dago ki kalleni, Haiydar ne a gaban ki yake
magana, nasan zakiji zafin wannan auren haka kuma zakiyi bakin cikin auren
wanda bakya so kuma baya sonki, Ni dan uwanki ne bazan ki kiba, matukar dae
zaki cire kowa a ranki ki rungumi kaddara, to insha Allah bazaki samu matsala
daga bangarena ba"
"Daga mishi kai kawae tayi alamar gamsuwa daga nan dae
yaja hannunta suka shiga daki, sunyi alwala a tare suka gabatarda sallar godiya
ga ubangiji haka suka kwanta kowa yana sake saken sa, kai a takaice dae a
wannan Daren Haiydar ya zama cikakken namiji don ya dan dani zumar da bai taba
dan danar taba ya kuma jinjinawa kanwar sa haka kuma ya samata Albarkar rike
mutunci ta da tayi"
"kwanaki sun ja sosai Haiydar ya shiga sabuwar rayuwa
ya yarda zagin iyaye yafi zabinka ya tabbatar wa kansa wannan itace
Kyakykayawar kaddara haka kuma yayi amman na da cewar safeer a kullum wato(
*AUREN BAZATA ALKHAIRI NE*) "
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Yau watan twins shida a duniya sun girma sunyi wayo sosai
haka kuma kyansu ya dada fito kamar ka sace su, kuma yau Shukrah zata fara aiki
a *MARYAM CLINIC* Hakan ne yasata tunda ta tashi tayi sallar a suba bata koma B
tanata kiciniyar hada breakfast ga twins sai rigima suke ta rasa inda zata sa
kanta ta dauki wannan ta goya wannan sukayi shiru abinsu zuwa can ta ajiye su
ae tana juyawa suka kuma fasa kuka, zuciya ta cita ta kwada wa *Labeeba* duka a
bayanta ae ko akan idon safeer wannan abun ya faru ya kara so ransa a hade
kamar be taba dariya ba ita kanta Shukrah ta tsorata, ya daga *labeeba* yana jijjagata saida tayi shiru
sannan ya juya yana kallon Shukrah da fuskarshi datayi ja saboda bacin rai ya
nuna da yatsa yace
"wannan ya zama na farko kuma na karshe dazaki sake
dukarmin yara in bakya sonsu ni ina son su, wannan ma ae mugunta ne zaki kama
yarinya kina duka me ta Sani? Kuma ki hada min kayan su zan kaisu gidan Mamah
kafin in auro wadda zata kularmin dasu, yana kaiwa nn yayi ficewarsa ya barta,
ae Shukrah bata san sanda ta zube ba a gurin tana kuka kamar ranta zai fita,
tayi data sanin dukan labeeba datayi sau ba a dadi, ganin datayi lokaci yana
kure mata yasata mikewa taje tayi wanka a gurguje ta shirya tadau labeeb ta
fice a gidan, Gidan Ammii ta kaisa sannan ta fice, Sanda ta karasa asibiti
office din *DR. MARYAM ANAS* Ta wuce kai tsaye"
"Shukrah bata wani yi mamakin ganin karamci da mutunci
da kuma girmamawar da *Maryam Anas* tayi mata ba don tasan labarinta gurin
Ammii, Mamah da Safeer ta babbatar zatayi abinda yafi haka"
" *DR. MARYAM* Da kanta takai *SHUKRAH* office dinta,
kuma a gaban ta tafara attending patients, sosai ta ya bawa Shukrah kuma bata
boye a cikin ta ba saida ta fito ta fadamata"
"Shukrah nayi mamaki sosai yadda kika iya aiki haka
"
" Dariya Shukrah tayi sannan tace ai ban manta ba
saboda nasa abun a raina kuma ina karanta littattafai sosai dasuka shafi
bangaren ido"
"ae haka ake so Shukrah Allah yayi miki Albarka kinji
DR. MARYAM Tace sannan ta fice"
1:35pm *SHUKRAH* ta gama komai saboda hk sai da ta jira
2:00tayi sannan taje tayi wa Dr Maryam sallama, gidan Ammii ta fara zuwa tayi
sallah taci abinci sannan ta dauki labeeb suka wuce gidan Mamah, basu wani dade
ba tadau labeeba suka wuce gidansu"
"4:35 pm safeer ya shigo gidansa yana wani cin magani
wae shi a dole fushi yake da Shukrah, Shukrah wadda take cikin kitchen da gudun
ta ta rungume shi tana mishi oyoyo, ya tabbatar baze iya yin fushi da Shukrah
ba don ta zame mishi jigo a rayuwar sa, matseta yayi sosai a jikin sa yana
kissing wuyanka, zuwa can yadago yana kallon ta, Shukrah ya office da Aunty
Maryam hope every thing is moving fine "
" Lafiya kalau Shukrah ta bashi answer sannan taja
hannunsa zuwa dakinsa, da kanta ta mishi wanka ta tayashi shirya wa sannan suka
dawo parlour tadau labeeb ya dauki labeeba, sunacin abinci suna basu haka kuma
suna dan taba hirar su, cikin hirar ne Safeer yake fadawa Shukrah iyayen DR. MAHMOUD Sun kawo kudin auren
Aysher kuma ansa ranar biki nanda wata goma "
" To Allah ya sanya alheri ya kuma sa ayi damu Shukrah
tace fuskarta dauke da murmushin jin dadi "
" Ameen ameen likitan ido me bawa mutane glasses, nima
idona namin ciwo har bana iya gani sosai yaushe zaki min glass Safeer Yace yana
dariya sosai"
"Dariya itama Shukrah tayi tace duk sanda ka shirya ka
sameni a office zanmaka daga hk tadau plate din da suka ci abinci tawuce
kitchen don wankewa........
0 comments:
Post a Comment