Inna na mai rafka salati gami da dafe k’irji ta ce
‘’lahaila haillallahu mahammada rasulilahi! Bintu kuma
Malam? Me ya had’a Bintu da masarautar Fabarusa saboda Allah da manzan sa? Yo
to da haka a d’au wuk’a a da6a mana sai mu san kashe mu ake son yi da hujja!’’
Baba na mai nuna Bintu da d’an yatsa wacce ta ke hawaye
d’aya na bin d’aya ya ce
‘’ga ta ga ki nan dai shegen biko’’
Kuka Inna ta sa yayinda ta rungumo Bintu ta na fad’in
‘’bar kuka Bintu, bar kuka d’iyar arziki, addua shi ya
kamata mu yi, innalillahi wainna ilaihiraji’un’’
Ganin haka Baba ya sa kai ya fice ya na mai fad’in
‘’kwa dai k’araci munahuncin ku, bakin alk’alami ya bushe’’
Ranar sam Bintu ba ta sami bacci ba, kwana ta yi ta na kuka.
Shi kan shi yayan ta Habibu ya tausayawa Bintu, zai ji dad’in zama yayan matar
sarki, amma kasancewar auren hatsari ne ya sa shi girgiza da juyayin abun.
Washagari da ciwan mara Bintu ta tashi, kasancewa al’adar ta
ta sake dawowa, ga kuncin zuci da ya addabi rayuwar ta ya sa gaba d’aya ta fita
daga hayyacin ta. Ji ta ke dama motar bayi sun tafi sun bar ta a makaranta, in
ya so Aisar ya tafi da ita ta huta da wannan rayuwa mara ‘yanci. In kuwa ta
tuna shikenan fa ba ita ba komawa makaranta, ita da Aisar sai dai ta hange shi
a akwaitin talabijin idan Allah ya sa an nuna shi sai ta k’ara saka wani kukan
har da shasshek’a. Ko damar shiga babban gida ba ta samu ba, haka kuma daga
Gimbiya K’amariyya har Gimbiya Binta babu wanda ya bi ta kan ta. Musamma
Gimbiya da buri ya cika.
Ranar sarki ya tara iyalen sa a turaka bayan Jakadiya ta
tabbatar ma sa da inganci da ilimin Bintu akan sarauta kasencewar ta tashi
gidan sarauta, wanda su ke da yak’inin lamarin da aka k’ulla zai daidaita ba
tare da an sami akasi ba.
Zaune suke gaban Sarki, Hajja Kilishi ce zaune ta 6arin
dama, kusa da ita Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ne zaune. Sai Uwar fada
da kuma Inna Salti, kusa da ita autan ta Yarima Nadir ne zaune daga 6arin hagu.
Gaban su kuma ‘ya’yan Sarki ne maza, ciki har da babban d’an sa, dokajin
Sa’ayra sa wato Yarima Inuwa, kusa da shi Yarima Nuhu ne. Sai kuma daga can
gefe Yarima Hassan da Yarima Hussaini, Yarima Hamza, Yarima Abdallah da kuma
Yarima Ahmadu su ka yi na su dairar.
Jin batun na Sarki, idan aka d’auke Gimbiya K’amariyya da
Gimbiya Binta da dama ita ta kulla k’ulalliyar babu wanda be girgiza ba. Yarima
Inuwa ne ya duk'ar da kai kana ya ce
‘’Allah shi ja da ran Sarki, shin an zatar da hukunci ne ko
kuwa ana buk'atar shawara daga iyalan Mai Martaba?’’
Sarki na mai duban sa ya ce
‘’mun gama yanke hukunci, amma jin ta bakin ku ba laifi ba
ne’’
Jin haka sai Yarima ya ce
‘’Allah shi kyautata lamarin Babban biji, komai ku ka zartar
daidai ya ke, ina ga zai fi kyau a duba lamarin nan saboda gaba, ran Mai Martaba
ya dad’e’’
‘’Allah ya ja zamanin Takawa, ni ma dai hakan zance, dan
kuwa gaban ya fi baya yawa, muddin ba za mu iya yin yanda su ka tambaya ba, zai
fi kyau a yi watsi da maganar gaba d’aya in ya so sai mu nemi taimako wani
wajan daban ko kuwa a amra masa K’amariyya yanda ya buk’ata’’
Inna Salti ce ta ara ta yafa, dan kuwa kusan ta fi kowa jin
d’acin maganar cikin matan Sarki, hakan ya sa ta kasa yin shiru. Tun da ta fara
maganar Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ke hararar ta ta wutsiyar ido. Shi
kuwa Yarima Nuhu tun da aka fara maganar ya ke son furta abun da ke ran sa, jin
Yarima Inuwa tare da Inna Salti sun share masa fage be yi k’asa a gwuiwa
ba ya ce
‘’Ran ka shi dad’e, ka gafarce ni, amma ni a nawa wautar
wannan lamari ba shi ne mafita ba, shin ya za mu yi a warware wannan sak’ar
idan har aka kulla? Menene makomar wannan baiwa idan Allah ya sa Masarautar
Fabarusa su ka gano wannan lamarin? Menene mazaunin wannan Masarauta ta mu?
Shin gaba ake san kawarwa ko kuwa wata gabar ake san kullawa? Wannan tunani ya
sa na yarda da Inna Salti, mu yi yanda Masarautar Fabarusa ta buk’ata ba tare
da wani sark’akk’iya ba, ko kuwa zai fi kawai mu hakura da batun gaba d’aya in
ya so mu nemi taimako a wata Masarautar ko ma Gwamnatin tarayya duk da dai shugaban
k’asa be da lafiya, da lafiya ya ke na san da ba a kai ga haka ba, kuma ba za a
rasa wanda zai duba wanga lamari ba’’
Ko da Yarima Nuhu ya dasa aya, Gimbiya Binta ji ta yi kamar
ta kurma ihu, ita kuwa Gimbiya K’amariyya har ta fara kwalla ganin Yarima Nuhu
na neman dawo da gaba baya. Shiru ya biyo baya. Har sun fitar da rai da k'ara
jin maganar Sarki, daga bisani ya numfasa ya na mai duban Hajja Kilishi ya ce
‘’wani shawara za mu ji daga gare ki? Shin kin amince mu
aurar da d’iyar mu ga abokan gaba ko kuwa mu sake neman taimako wanda hakan
jinkiri ne wanda ya ke barazana ga
rayukan talakawan mu?’’
Hajja Kilishi na mai nusar da kai cike da kissa ta ce
‘’lafiya toya matsafa, lafiya waliyin Allah, lafiya baya
goya marayu, lafiya adali! Hukuncin ka daida ta Saka Takura, mun ji mun kuma
amince’’
Sarki na mai nuna jin dad’i da batun Hajja Kilishi, haka ya
bi sauran iyalan sa kowa na fad’in na shi albarkacin bakin. Duk da Sarki ya san
Su Inna Salti, Yarima Inuwa da Yarima Nuhu sun fi gaskiya, sai ya bi san ran sa
tare da kafa hujjar an rinjaye su, dan haka maganar ta tsaya. Da wannan su ka
watse kowa da abun da ya ke sak’awa cikin ran sa. Musammam Yarima Nuhu wanda ba
tun yau ya ke da k’udirin mallakar Bintu ba, ko da kuwa a matsayin sad’aka ce,
tin da wata baiwa ta kawo masu tsirkun abun da ta ji Gimbiya Binta da Jakadiya
su na kullawa ya kasa sukuni. Ya had’a goma na arziki ya nemi amintacciyar
baiwar sa, ya ce ta kaiwa Jakadiya, wato na sharan fage kenan kafin ya je mata
da buk'atar sa.
Su Gimbiya kuwa ko da su ka koma na su 6angaran mamakin
yanda Yarima Inuwa, Nuhu da Inna Salti su ka nuna k’iyayyar su k’iri k’iri ta
hanyar k’in amincewa da wannan lamarin, a nasu tun da su ne su ke ciki d’aya su
ya fi dacewa ace sun yi na’am da lamarin, amma ga mamakin su waccan da su ke
kira yan bakin gida su ne su ka fi nuna kauna gare su.
Yarema Nuhu kuwa kai tsaye 6angaran sa ya nufa rai 6ace,
babban takaicin sa shi ne a rasa baiwar da za a sa cikin wannan hatsari sai
Bintun shi ta arziki, Bintu da ya dad’e ya na saka buri akan ta, gaskiya dole
ya san yanda zai yi wannan maganar a rusa ta. Bakin kofa ya ci karo da Baiwar
da ya tura gun Jakadiya, hannun ta nik’i nik’i da kayan da ya bata ta kaiwa
Jakadiya. Da ganin sa ta zube k’asa ta na mai gaishe shi. Cike da mamaki ya ce
‘’ba ki kai mata sak’on ba ne?’’
Kai duk’e Baiwa ta ce
‘’Allah shi taimaki Yarima, Uwar baka ta sake hali, da na
kalle ta sai dak'uwa ta min, kasan Jakadiya gara ce, ga tsiya ga rana, tsiyar
ta ya fi ranar ta yawa’’
Jin haka ya gane me ya faru, ma’ana dai Jakadiya ta yi
tsiyar ta, ta kuma k'i kar6ar tsarabar sa wanda hakan ya na nufin ba zai sami
kowani taimako daga gare ta ba. Cikin zafin rai Yarima ya ce ‘’kya iya tafiya
da kayan’’
Sannan ya tsallake ta ya shige ciki ya na mai bugo k’ofar.
Yayinda baiwa ta had’e kaya ta yi gaba, Allah ya kashe ya bata.
A wuni guda Bintu ta rame ta lalace kamar wacce ta shekara
ta na ciwo. Da Baba ya dawo da daddare ya ke sheda mu su an fa aika Fabarusa,
zance ya tabbata nan da wata d’aya za a amrawa Sark’i Abdulrahman aure da Binta
d’iyar Sarki Sule na Sa’ayrasa. Inna na mai d’aure fuska ta ce
‘’yo to tun da ba da Bintu aka ce ba ai can da su gada, ni
dai d’iya ta ba sunan ta Binta ba, Bintu an sunan ta, haka kuma ba d’iyar sarki
ba ce d’iya ta ce’’
Baba na mai duban ta ya saki murmushin takaici, kana ya ce
‘’ke kuma d’iyar wacece? Ko in ce ke wacece a Masarautar nan
da ga ke har d’iyar ta ki?’’
Inna ta yi shiru, ganin haka Baba ya k'ara
'’shirun da ki ka yi ya tabbatar min da kin tuna ashefa ku
bayi ne, dan haka ba ku da ‘yanci, ki ma godewa Allah da ya sa amrar da ita ya
ce zai yi ba bada ita zai yi sadaka ko sad’aka ba, gide ke dai kin cika butulu.
Toh ki saurare ni da kyau gobenan za a zo a tafi da Bintu ga babban gida, hallo
dangin ki d’aya ba a yarda kin shedawa ba, yo to ina bayi ina wasu dangi ma in
ban da ba'a"
Kuka Inna ta saka ta na fad’in ‘’wannan zalinci da ke shirin
aikata min da wanga yarinya Allah shi isar mana’’
Ciki Baba ya shige kafin ya lek’o da kan sa ta assabari ya
furta ‘’je ki tari Magajin Gabasawa ki sheda masa, yo to ba ni na kar zoman ba,
rataya aka bani’’
Ita kuwa Bintu da ke jiyo su daga d'aki zuciya ne kad'ai ba
ta had'iya ba, tunani ta ke ina ma Aisar ya na kusa ya kawo ma ta d'oki yanda
ya [truncated by WhatsApp]®
Kamar dai yanda Baba ya ce, da sassafe sai ga Jakadiya da
amintaccin bayin Hajja Kilishi sun dokowa Inna sammako. Dan takaici Inna d’auke
kan ta yi dan kuwa ta kasa bud’e baki ta ce da Bintu ta fito ta bisu.
Tun da Bintu ta ji sallamar su ta shige bayan kofa ta yi
zaman ta, duk da ta ji buk’atar Jakadiya amma k’yememe ta k’i fitowa. Ana haka
Baba ya fito ya rufe Inna da fad’a
‘’Magajin Gabasawan za ki yi wa musu ko kuwa Jakadiya? Iye
Yagana? Gide ban san tsaurin idanu fa! Yo to yau ko ke Magajin Gabasawa ya ce
zai aura sauki zan yi bare ma wanga d’iya, aikin banza aikin hofi! Ta na ina
wai? Gide Bintu hito ki bi su in ba haka ba ina make ke! kwankwatsi ma kuwa!’’
Jakadiya na murmushi ta ce
"Mahuta bi su a hankali, ai tsakanin uwa da d’iya sai
Allah bare kuma ace za a raba su rana a tsaka, bi su a sannu Mahuta, in ban da
ke da abin ki Uwar bayi wanga lamari ai alheri ne aka yiwa d’iyar ki, wanga abu
abin san barka?’’
Idan Inna ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka, ganin
haka Baba ya wuce su izuwa d’akin Bintu, ya tadda ita bayan kofa ta had’a zufa
da hawaye. Fad’a ya hauta da shi, ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Amma kyememe Bintu ta k’i motsawa bare ta fito. Aikuwa da Baba ya fusata sai ya
hauta da zagi, jin haka Inna ta shige d’akin da sauri dan ta san daga nan kuma
abun da zai biyu baya.
Ilekuwa shigar ta kenan ta ga Baba ya d’aga hannu ya na
shirin kaiwa Bintu bugu, nan da nan ta shiga tsakani, ta ce
‘’haba Malam! Ai ka ji tsoran Allah abin ga ai sai yayi yawa
maye da hauka!’’
Nan fad’an Baba ya koma kan Inna, ai lalle Inna ke d’aurewa
Bintu, dan haka zai fita ya dawo, in dan ya dawo ya ga Bintu gidan nan sai na
lahira ya fita jin dad’i. Dan masifa da bambami ko sallama be yiwa su Jakadiya
ba ya sa kai ya fice ya na kumfar baki.
Bayan fitar sa Inna ta ja hannun Bintu su ka fito tsakar
gida. Inna na mai duban ta ta ce
‘’Bintu idan har ni na haife ki, toh na baki umarni ki bi su
ku tahi Babban gida’’
Bintu na jin haka ta zube k’asa, hannayen ta biyu ta sa ta
ruk’o k’afar Inna ta na fad’in
‘’Inna na tuba, Inna ki gafarce ni, Inna ki min afuwa, Inna
kar ki ce na bisu, Inna kar ki yarda a raba ni da ke, kwankwatsi na dena 6ata
mi ki rai, idan na k’ara aratta kashe ni’’
Inna na mai janye k’afafun ta daga ruk’on da Bintu ta yi
mata ta ce
‘’na yafe ki duk da ba ki ta6a sa6a min ba, ke d’iya ce ta
gari, dan haka ki sa Allah a ran ki shi ne kad’ai ka iya mi ki, tashi ki bisu,
Allah shi fisshe ki alkairi...’’
Ta na gama fad’ar haka ta shige ciki ta na hawaye. Nan fa
Bintu kuka har da birgima. Su Jakadiya su na nan suna gani sarautar Allah duk
da dai su ma kukan na Bintu ya so ya d’an ta6a su.
Habibu ne ya shigo, ganin abin da ke faruwa ya shiga
rarrashin Bintu, har ya samu ta yi shiru. Ya ce da su Jakadiya su yi gaba gasu
nan biye da su, bara ya had’o kayan Bintu. Jakadiya ta ce ah ah ba a bukata,
ita d’in ta kad’ai ake buk’ata.
Gaba su ka yi, hannun Bintu ruk’e da na Habibu, su na tafe
ya na bata baki da nasiha har su ka isa kofar Babban gida. Nan ma Bintu ta ce
ba ta san zance ba, Habibu be isa ya koma ya bar ta gun su Jakadiya ba.
Jakadiya ta fusata ta hau Bintu da fad’a
‘’yau ina ganin walele gi6in takwaru! Gaskiya ne komai
girman d’an mara kabo be isa aure ba! 'Yar tusa wacce ba ta san arziki ba! Ki
na baiwa d’iyar bayi har kya wa mutane kwawarniya shiga rumbun k’ore, yo to sai
ki ma Babban Bijimi musu da kwarnato in ya so a tsire ki ma ga me asara!’’
Bakin Bintu na rawa, ta saki hannun Habibu, wanda d’acin
maganar Jadiya ya sa shi juyawa da sauri dan gudun kar ya maida mata ya jawowa
Bintu da ma gidan su baki d’aya, ya na jiyo Jakadiya na masife Bintu yayinda ta
ke hankad’a kafad’ar ta zuwa ciki, babu yanda zai yi haka ya tafi ba tare da ya
sake ko waiwaye ba.
'Dakin Jakadiya aka aje Bintu, nan ta sha kukan ta, ta
k’oshi dan kan ta ta yi shiru sai ajiyar zuci kawai.
Jakadiya ta shigo kana ta ce ta saka mayafi ki biyo ta,
Babban bijimi na jiran zuwan su. Kallabin ta ta ware ta yafa bisa kan ta, babu musu
dan kuwa taji tsoran maganar Jakadiya na za a tsire ta, ta bi bayan Jakadiya ba
su zame koina ba sai turakar sarki.
In da Jakadiya ta tsaya daga waje, Bintu ta shiga daga ciki.
Nan ta tadda sauran ilayan Sarki.
Gimbiya Binta ba ta fasa watsawa Bintu kallan wuk’anci ba, ita kuwa Inna Salti
tsabar tausayin Bintu ne cikin ran ta. Yarima Nuhu kuwa Allah kad'ai ya san
tashin hankalin da ya shiga, musammam yanzu da ya ga Bintu gaban Sarki, babu
makawa ya na ji yana gani Bintu za ta si6ice ma sa. Tin shigowar ta ya sa saka
idanu akan ta, k’irik’iri be damu da ba shi kad’ai ne ba, bare ya damu da
fassarar da za a iya masa. Ita kan ta Gimbiya Binta ta lura da irin kallan da
ya kewa Bintu, har zunguran K'amariyya ta yi dan ita ma ta ganewa idon ta, bare
kuma su Hajja Kilishi har da murmushin mugunta, dan kuwa ta k’i jinin Yarima
Nuhu.
Muryar Bintu a shak’e tsabar kukan da ta yi ta kai gaisuwar
ta ga Sarki. Hankali kwance, idan Sarki ya lura da sauyin yanayin da aka samu
game da Bintu tsakanin ranar da ta fara zuwa gareshi da kuma zuwanta a yau, bai
nuna ba don kuwa ko a jikinsa ya amsa, kafin ya k’ara da
‘’Masarautar mu na godiya ga wanga d’iya ta arziki,
kasancewarki baiwa, mun baki ‘yanci, mun ‘yanta ki a yau kin tashi daga baiwa
kin zama d’iya mai ‘yanci...’’
A firgice Gimbiya Binta ta kai kallonta ga Sarki ta na mai
fiddo ido waje dan kuwa ba ta yi zato ba, kar dai danasani za ta yi, abun da ya
fara zuwa zuciyarta kenan yayinda gaban ta ke dukan uku uku. Haka ma kowa na
wajan ke kallan Bintu, wacce ta rasa me za ta yi, murna za ta yi na samin ‘yancin rayuwar ta bayan shekara
goma sha biyar ta na baiwa, ko kuwa kuka za ta yi ta tashi daga baiwa, amma
iyayenta na nan a bayi, tabbas ta tabbata d’iyar bayi. Hawaye ne d’aya bayan
d’aya ke gangarowa daga idanun ta, murya na kakkarwa ta ke fad’in ‘’Godiya na
ke ranka shi dad’e, godiya na ke Allah shi ja da ran Sarki, Alkhairin Allah ya
tabbata a gare Mai Martaba’’
Yarima Nadir da ke jikin Inna Salti ne ya ce " Inna
Salti me ya sa Bintu ta ke kuka?"
Hannun Inna Salti bisa le6enta ta amsa da
"Shhhh"
Wato ya yi shiru, shirun ko yayi.Yarima Nuhu wanda shi kansa
ya rasa shin wai me ya ke ji a lokacin ji yayi kamar ya isa ga Bintu ya sa
hannu ya share mata hawayen idanunta, ji ya ke kamar ya rok’i Sarki a bar ma sa
Bintu, ko da kuwa shi ne abu na k’arshe da zai tambaya gun Sarki ya amsa masa.
Yau ga Bintun arziki an zama ‘yantacciya, wannan fa shi ake kira ga k’oshi fa
ga kuma kwanan yunwa.
Sarki bai gushe ba ya k’ara da ‘’Nan da mako hud'u za mu
amra miki aure ga Masarautar Fabarusa, da an amra za a ba mu bashin da mu ka
buk'ata, hallo tarewar ki can sai nan da mako hud'u kan nan kin sami shiri mai kyau.
Ba mu amince ba sai da mu ka tabbatar de ke baiwa ce mai tarbiya, dattako da kuma sirri,kasancewar
kin iya zama da d’iyar mu lamun lahiya ba tare da ta ta6a kawo mana kukan ki
gare mu ba’’
Gimbiya Binta aka zagayar da kwayan ido ta cikin mayafi, cikin
ranta fad’i ta ke ‘’Yo to ba girin girin ba d'iyar bayi, ta mai......’’
Jin Sarki ya ce ‘’Hajja Kilishi ga wanga d’iya za ta dawo
gare ki ina fatan ke da Jakadiya za ku sa ta hanya, cikin surri ku koyar da ita
dabarun Masarauta duk dai yanda Jakadiya ta sheda mana yarinyar dama mai sani
ce, mu na so duk kan nan ku sani ba mu yarda ko da wasa wani ya k’ara kiran
wannan d’iyar arziki da baiwa ba, haka kuma ban amince a yi mata yanda ake yiwa
bayi ba, ku sani wanga d’iya d’iyar mu ce, dan haka a daraja ta’’
Gimbiya ta cije le6e, ita dai kam wannan lamari ba ya mata
dad’i, ya Takawa ya ke san mata sakiyar da ba ruwa ne, ko da yake ma ita ina
ruwan ta k’arshen ta ajali ne ke kiran Bintu, dan kuwa girman Masarautar
Fabarusa ko jinin saraki sai sun shirya zaman ta bare baiwar da za ta je a
matsayin Gimbiya, tun da dai ta ci nasarar sa min Aisar, ga shi Gimbiya
K’amariyya ta sami Barde ai hutatai. Abunda ta ke jaddadawa zuciyar ta da ta ke
nemen fashewa tsabagen bakin cikin kalaman Sarki kenan, bilhakki danasani ta
fara, dan kuwa ba ta yi zato ba.
‘’Za mu mayar da d’iyarmu Binta kasar Nigeria, in da za ta
je can ta cigaba da karatu kan mu biya bashi ga Masarautar Fabarusa komai ya
warware........’’
Gimbiya Binta ba ta san sanda ta tashi tsaye a zabure ba, ta
na mai girgiza kai. Nan kallo ya koma gare ta har sai da Yarima Inuwa ya daka
mata tsawa ya na mai fad’in
‘’Gide kin manta gaban wa ki ke ne! ko ma ki zauna kar ki
mana sakarci a nan’’
Gimbiya K’amariyya ce ta jawo hannunta, yayinda ta koma ta
zauna a gajiye, tuni idanunta su ka kawo ruwa, ba ta san sanda ta furta.
‘’Tuba na ke Takawa, Allah ya ja da ran Sarki a min rangwame
tuba na ke kar a bari na yi nisa da Mai Martaba’’
‘’Ko kuwa dai ba kya so kiya nisa da Aisar Gaddafi Nur ba’’
Fad’in Gimbiya K’amariyya kenan wacce ke rike da hannun kanwarta ta, cike da
tausayi ta ke dubanta, dan kuwa ita kad’ai ta san zafin da ta ji jin za a raba
ta da masoyinta Barde, yau kuma gashi ‘yar uwarta na shirin rasa na ta
masoyinta sakamakon taimakonta da ta yi. Kana ta kada baki ta ce
"Allah shi ja da ran Sarki, dan Allah a duba lamarin
nan, Binta har yanzu yarinya ce, za ta cutu muddin ta yi nisa da mu.’’
Yarima Nuhu na dubansu, bakinshi kunshe da murmushin mugunta
ya ce
'’Kar ki fad’awa Takawa wanga yashashen zance haka
K’amariyya, idan har wanga d’iya( ya nuna Bintu da yatsa) za ta iya taran aradu
da ka ta shiga Masarauta mai girma a
cikin badda kama, duk da k’aranci shekarunta, ban ga dalilin da zai sa Binta ba
za ta iya zuwa wata k’asar ba domin rufawa masarautar ta asiri ba, yo to menene
nan da makwafta Nigeria, ai Nigeria da Nijar d’aita, ko kuwa ki na nufin za a
aurar da Bintu matsayin Binta ne kuma jama’a na ganin Binta a k’asar nan, dole
sai ta tafi’’
Ya k’arasa magana ya na mai duban Gimbiya Binta da ta ke
kuka bilhakki.
‘’Nuhu ya yi gaskiya, kamar yanda wanga d’iyar arziki ta
mana biyayya, mu na fatan ke ma haka za ki kasance me biyayya a gare mu, saboda
haka sai ki zauna da shirin ki na bulaguro nan da mako hud'u, komai za a yi
jiyo shi cikin surru, kar ku yarda da kowa sai amintaccun bayin ku. Mun yi
magana, Mun sallame ku’’
Cewar Sarki kenan ya na mai kawar da kai daga kallan Gimbiya
Binta gudun kar ta karya masa zuciya, dan kuwa shi dai yaransa su an rauninsa.
Komawarsu d’aki nan Gimbiya K'amariyya ta ga kuka da daru
gun Gimbiya Binta, ba shiri Inna Salti da Hajja Kilishi su ka sallami bayin da
ke cikin 6angaran gudun yad’uwar maganar. Wanda kuma su ka riga su ka ga halin
da Gimbiya Binta ke ciki, Jakadiya ce ta tara su, cikin hikima ta mu su
kashedin ko da wasa kar su yarda a ji halin da Gimbiya Binta ta shiga jin Mai
martaba ya ba da amran ta ga Sarkin Fabarusa, duk wanda aka ji a bakin sa sai
dai uwar sa ta haifi wani. Ai kuwa dai ba su fasa yad’awa ba, ta yanda Allah ya
so ma maganar Jakadiya su ke yad’awa ba asalin zancen gaskiya ba.
Dakyar aka samu Gimbiya Binta ta sarara da kukan da ta ke,
ita sam ta manta da azanci a maimakon ita za a aurar da Bintu, kasancewar haka
ita ma sai an 6oyeta na wani d’an lokaci. Gashi Mai martaba ya ‘yan ta Bintu,
wacce ta ke baiwar ta tin tale tale. Bauhaushe dai yayi gaskiya, in za ka gida
ramin mugunta, ka gina shi gajere.
Da yamma Bintu na zaune d’aki tare da Hajja Kilishi, ilimin
zaman fada ta ke ta koya mata, amma ita sam hankalin ta ma ba ya wajan dan haka
ba wani ganewa ta ke ba. Zuba ido ta ke ko za ta ga Innar ta, amma babu Inna
baba alamar ta. Hajja Kilishi ta ce da Bintu ta lek’a falo ta ce da d'aya daga
cikin bayin ta maza su je 6angaransu Gimbiya K’amariyya su k’ar6o ma Bintu
sak’o.
Ko da Bintu ta fito, ta bayin sai kai kawo su ke cikin
hidimansu, sai ta kasa tsaida d’aya ta aika, duk da dai yanzu ba cikin sahun su
ta ke ba inji Sarki, ita har yanzu ba ta ji wani canji ba, dan haka yanda su ke
haka ta d'auki kanta, sutarar jikinta ma kayan bayin Sa'ayrasa ne wanda dama
shi ne a jikinta tun safe da su Jakadiya su ka zo tafiya da ita. Hakan ya sa ta
yanke hukuncin zuwa da kanta 6angaren. Ta na sa k’afa cikin falon ta yi ido
biyu da Gimbiya Binta, wacce fitowar ta daga d’akin K'amariyya kenan, idanun
nan sun yi jajur.
Ganinta Bintu ji ta yi kamar ta koma a guje, ile kuwa bud’ar
bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi
'’Ke har kin isa ki nuna fuskarki gabana dan ubanki! Ya ki
nan munafuka!’’
Jikin Bintu na rawa ta k’arasa gaban Gimbiya ta na mai
zubewa a k’asa ta ce
‘’Kimin rai, tuba na ke Gimbiya’’
‘’A gidan ubanwa ki ke tuba! Oho wato Takawa ya ce kin zama
daidai da kowa shi ya sa ki ka zo gwada kafad'a da sa’annin ki ko? Shu’uma
daina rawar k’afa, kwalla ba amre ba ne! ki na cikin hatsari muddin Masarautar
Fabarusa su ka san ke fa baiwa ce kuma d’iyar bayi, zamanki a Masarautar na
d’an wani lokaci ne har sai mun cika burinmu, na farko shi ne na gama makaranta
na kuma amri masoyi na Aisar, na biyu Didi ta amri burin ranta, wato Barde, na
uku Mai Martaba ya biya bashi ba tare da an yi amfani da farin cikin iyalinsa
ba, ke kuwa Allah kad’ai ya san ya rayuwar ki za ta kasance, hallo tsire ki
Sarki Abdulraman zai sa a yi idan ya gano mak’aryaciya ya ke amre.....’’
‘’Ku kuwa Masarautar mak’aryata su ka bashi amren ta
ba.....’’
Yarima Nuhu ne ya katse ta, da sauri ta juya ta kai kallonta
gare shi, ashe ya shigo ba ta sani ba. Ya na jingine jikin bango daga bakin
k'ofa, hannunsa sarke bisa k’irjinsa. Sanye ya ke cikin shud’ayan kaya, ya
d’aura farar falmaran akai. Bai gushe ba ya k’ara.
‘’Ina tunanin halin da ki ke ciki ya sa ni tattaki dan zuwa
na ganki, ba shakka garau ki ke tun da gashi kin sa d’iyar arziki gaba ki na
mata yashasshen zance irin na marasa tunani, shin kin manta wanga d’iya ba
baiwa ba ce?’’
Yanda ya ga ta cuna baki ya sa shi fad’in
‘’Dakyau, yanzu ina ga kin tuna, dan haka na miki uziri,
amma daga yanzu ba na fatan sake tuna miki, hallo za ki kula.'’
Ya mayar da kallonsa ga Bintu,
"Bintun arziki tashi ki yi tafiyar ki, gide kar ki sake
tsugunnawa haka gaban kowa, tabbas akwai aiki ja gaban Jakadiya muddin za ki
kasance mata ga Sarkin Fabarusa dole ki wuce raini, ke ba baiwa bace, kar ki
ta6a mantawa da wannan.’’
Da saurin ta ta tashi, ta na mai godiya ga Yarima Nuhu, ta
bi ta gaban Gimbiya Binta, ta zo gaban Yarima Nuhu sannan ta fice ba tare da ta
damu da ta k’arbo sakon na ta gun Gimbiya K’amariyya ba.
Ganin yanda ta ke tafiya ba Yarima Nuhu ba, hatta Gimbiya
Binta sai da ta bita da ido, ba ta san sanda ta je tsaki ba ta ce
‘’Mtsw! Ka ga yanda ta ke tafiya d’iyar bayi sai shegen
tak’ama da isa.'’
Ciki Yarima Nuhu ya shigo sosai, yayinda ya sami kujera ya
zauna ya na mai murmushi ya ke duban k'anwar ta sa sannan ya ce
'’Halittarta ce haka’’
Da sauri Gimbiya ta dawo da kallonta gareshi, cikin rashin
fahimta ta ce ‘’Na’am?’’
‘’Ko ba Bintu ba? Tak’ama da isa ba ta gada ba, amma Allah
ya mata shi a halittar ta, kin ga baiwar Ubangiji ko? Ba ki ga tsayinta da
dirinta ba ne? Su kad’ai sun isa nuna tak’ama, shi yasa na ke mai bakin cikin
rasa ta da zan yi ta sanadiyar san rai irin na k’auna ta.’’
Kamar mai shirin yin kuka Gimbiya Binta ta furta
‘’Yarima......Bintu d’iyar bayi ce!’’
Ya na mai had’e rai ya ce ‘’Hakanan k'auna ce ta na ke kuma
rainon san ta cikin raina tun kafin na mallaki hankalina, ina jin ta har jinin
jiki na duk da kuwa ita d’iyar bayi ce, ni kuma d’an saraki, ki sani na san da
duk wani tukgun da ki ka kulla ke da K’amariyya tare da d’aurin gindin
Jakadiya! Har ki na da bakin kuka dan ance za ki bar k’asa? Da da ki ke gina
ramin muguntar ba ki san za ki iya wad’awa ba?’’
Kuka Gimbiya Binta ta sa, hawaye d'aya na bin d’aya ta ce
‘’Ina soyayya da k’auna ta jini da amintaka? Ni fa ‘yar uwar
ka ce jini d'aya, za ka za6i d’iyar bayi akan yar uwarka? Ka ce da ni wasa ka
ke, ba ka san wanga d'iyar bayi.’’
Tashi tsaye ya yi, ya na mai danna idanunsa cikin nata ya ce
‘’Ni abinda ya ke ban takaici kenan, jini na ta san ta iya
had’a tuggu haka? Kin san abun da ki ke shirin saka babban mutum kamar Takawa
ya aikata kuwa? Kin san girman laifin kuwa? Ina mai gargad’inki, muddin ki na
so mu shirya ki gaggauta kunce wannan sak’ar da ki ka kulla tun kan ya k’ure
miki’’
Ya juya zai fita, har ya kai k’ofa Gimbiya Binta ta k’ara
kiran sunan sa ‘’Yarima....’’
A hankali ya juyo ya na dubanta, idanunsa sun kad’a sun yi
jajur. Gimbiya Binta na mai hawaye ta sake furta ‘’Bintu d’iyar bayi ce......’’
‘’Ita na ke kauna kanwata, idan har ki na so na da farin
ciki kar ki ja min asarar Bintu ta ta arziki’’ Ya na gama magana ya fice, ya
bar Gimbiya Binta ta na mai bin bayansa da kallo.
0 comments:
Post a Comment