Kai tsaye 6angaran Jakadiya da ya zame mata sabon wajan
kwana ta shige, ta tsallake bayi biyu wanda ke ta faman had’e sababbin kayan da
aka d’inko mata, ta shige d’akin Jakadiya ta na mai doka k’ofar gudun kar
Yarima Nuhu ya biyota. K’uryar d’akin ta
shige ta k'udundune ta na mai mayar da numfashi. Ba ta yi minti biyar da shiga
ba bayin su ka biyo ta su na mai tambayar lafiya? Ko ta yi gamo ne?
Baki na rawa Bintu ta ba su amsa da ‘’Don mai sama ku rabu
da ni, ko shakka babu na kusa rasa raina, na shiga uku ni Bintu na lalace,
wayyo Allah Inna ta!’’
Kallon junansu su ka yi, su na mai gyad’a kai cikin jaddada
zatonsu na Bintu ta yi gamo, har an fara jifanta daga Masarautar Fabarusa tun
kan ta shiga Masarautar, su ka juya jiki a sanyaye su ka fito suna mai rufo
mata k’ofa.
Daga waje baiwa ta dubi ‘yar uwarta ta ce
‘’Gide k'ak'a kenan, kinga har an fara yiwa wagga d’iya ture
ko? Babu mamaki wani bakin aljanin aka fara mata ture da shi don ta fita
hayyacinta ta ce ta fasa amran ga, wagga sharri sai kishiyoyi, maza je ki
shedawa Jakadiya tun kafin abu yayi tsamari.’’
Cike da jimamin abun baiwar ta amsa mata da
‘’Wagga batu gaskiya ta, aradu wagga d’iya gamo ta yi, inda
kin lura har launin idanunta ya sauya, bara dai na je ga Jakadiya, mutum hege
ne, mutum ba imani.’’
Tana mai ta6a kafad’arta, ta ce
‘’Maza Ladiyo, ni bara na tsaya daga rariya ko da wani abun
zai faru.'’
Jikin baiwar na rawa ta fara tafiya, tana fad’in
‘’Eh tsaya Kyallu, bara na ruga na dawo, Allah shi fisshemu
daga sharrin mahassada.’’
Ta fice, inda ta bar Ladiyo da tsaron k’ofar Bintu. Ita kuwa
Bintu ita kad’ai tasan abinda ke damunta, yau ta ji ta kuma ga abinda ba ta
ta6a tsammani ba, ko shakka babu tasan rayuwarta ce ta zo k’arshe, ko kuwa dai
Yarima Nuhu ya soma shaye-shaye kamar yanda wasu samari daga cikin bayi su ke
yi. Abinda ke d'agawa Bintu hankali shi ne sake rike hannunta da Yarima Nuhu ya
yi, ita tasan rayuwarta ce ta zo k'arshe.
Jin Bintu ta fara yin gamo tun ba aje ko'ina ba, nan da nan
Jakadiya ita ma ta had’o kayan tsubbuce tsubbucenta, haka ma Hajja Kilishi,
wacce dama ita aka damk’awa Bintu a hannu. Suna mai jan kunnan bayinnan biyu,
Ladiyo da Kyallu, akan kar su sake aji maganar a waje.
A gaba Jakadiya da Hajja Kilishi su ka sa Bintu, tambayar
duniyarnan sun mata akan gamon da aka ce ta yi, amma shiru Bintu ta kasa ce
musu komai don kuwa muddin ta fad’i gaskiya to kashinta ya bushe. Ganin haka su
ka yanke hukuncin fara kare ta tun daga yanzu don babu mamakin sammu da aka
fara mata har da na d’aure baki. Bintu na ji ta na gani aka fara mata lalas da
siracen magunguna, har da na sha da wanka, kan ka ce me tuni ta fita hayyacinta
in banda attishawa babu abinda ta ke yi, ko iya haka aka barta ta san ba
k’aramin masifa ganin Yarima Nuhu ya jaza mata ba.
Bayan siracen da ta sha, sai da Jakadiya ta bi duka ga6o6in
jikin Bintu ta na d’aura mata laya, wai gudun kar a zo mata cikin dare, nan ko
ba su san in ma akwai aljanin ba zai wuce Yarima Nuhu ba, kai Allah shi fisshe
mu aikin jahilci.
Saida su ka tabbatar sun gama kafe Bintu kaf, Hajja Kilishi
na mai duban Bintu da gaba d’aya ta jigata saboda siracen da ta sha, gashi
cikinta har juyawa ya ke tsabagen had’aka na magunguna da Jakadiya ta afka mata
duk da sunan makarin sammu da kafiya, Hajja Kilishi ta ce
‘’Ni ko Jakadiya d’iyarnan na shan maganin da’a kuwa(maganin
mata)?’’
Jakadiya na mai susa k’eya ta amsa da
‘’Yo to wani maganin da’a za a bawa wagga d’iya za a amran
da ita ga tsoho ank’i rami? Ai ni a tunanina tunda dai Sarkin Fabarusa an tsufe
ban ji zai damu da abubuwa irin wagga, ko k’ak’a kin ka gani?’’
Hajja Kilishi na mai murmushi ta ce
‘’Tsoho ba mutum ba Jakadiya, yo to maza ma ai ba sa tsufa,
kar ki so ki ga yanda Takawa ke ji dani duk farin gemun nan nasa, yauwa tun da
magana ta kawo magana, Jakadiya ina mai buk’atar zuwan Takawa gare ni a yau ma,
hallo zannuwa da kallabi har guda goma na nan tafe izuwa ga d’akin Jakadiya nan
ba da dad’ewa ba’’
Dama dai maganar kenan, ta 6ige da Bintu gudun kar Jakadiya
ta ga kamar ta cika naci, don kwana hud’u kenan ita Jakadiya ta ke kai wa
Sarki, kasancewar hatta kwanan matan Sarki sai wacce Jakadiya ta za6a tsabagen
matsayi irin na Jakadai a fada.
Jakadiya kuwa mai idon cin naira, jin zannuwa na tafe tuni
ta kada baki ta ce
‘’Yo to menene, in ma sau goma ki ke san zuwan Babban Bijimi
aradu gun ki ya ka kwana, an gama ranki shi dad’e, sai kin ga zuwan mu.''
Hajja Kilishi na mai jindad’in yanda Jakadiya ke damawa da
ita, duk da dai ta san na d’an k’ank’anin lokaci ne, in dai Jakadiya ce bakin
ganga ta ke, arzikinka shagalinka. Ta mata sallama in da ta barta da Bintu ta
mai mata jawabin yanda za ta yi ta kare kanta a Masarautar Fabarusa. Ita dai
Bintu jinta kawai ta ke, amma ko yaya ta rufe idanunta fuskar Yarima Nuhu ta ke
gani yayinda ya ke furta kalmar so a gareta, haka zalik’a maganganunsa ke mata
yawo cikin kwakwalwarta. Ko shakka babu Bintu ta yi gamo, amma fa da Yarima
Nuhu, mutuwarta kad'ai ta ke jira kamar yanda Iya Dije ta ce muddin namiji ya
ta6a ta.
Zoben Aisar kuwa d’aya daga cikin bayi ne, wanda saurayi ne,
mai kula da lambu ya tsinta yayinda ya ke shara. Ganin zobe mai matuk’ar tsada
yayi saurin 6oyewa cikin aljihunshi, don jira ya ji ko mai shi zai nema, idan
kuma ba a yi cigiya ba ya kai kasuwa ya siyar ya sami kud’i.
********
Kwanaki uku ya rage auren Bintu. Da hantsi Inna Salti ta
kawo ziyararta ga Bintu. Daga ita sai Bintu da ke d'urkushe gabanta ne a
d'akin. A sannu cikin lallami Inna Salti ke mata magana, in da ta ce
‘’Bintu ki sani wannan lamari jarabawa ce daga Allah, saboda
haka ki kasance mai biyayya sai ki ga kin ci jarabawar. Wagga amre za a yi shi
ne cikin surri, duk wanda ki ga ya san wani abu na game da gaskiyar wagga amre
to amintaccen fada ne, hallo sai sun rantse ake ba su amanar ga, dan haka kema
wagga al'amari ya kasance amana a naki 6angaren, idan ki ka kuskura gaskiyar
al’amari ya hito, rayuwarki za ta kasance cikin hatsari Bintu, wanda ba na
fata. Daga sanda aka amra miki amre za ki tashi daga Bintu, za ki fara amsa
Gimbiya Binta.’’
Numfashi ta ja, sa’annan ta cigaba
‘’Kin dai ga yanda sarauta ta ke, a fada aka haife ki ciki
ki tashi har rana ita yau da ake shirin amrar da ke. Hallo sai kin yi
takatsantsan da rayuwar da za ki shiga, zaki shiga rayuwar amre hallo a fada,
akwai wuyar ganewa. A fada ba kowa ne zai 6ud’i hak’ora ya miki dariya ya
kasance masoyi gareki ba, wani sa'in ma mak’iyinki ka iya nunawa kin fi kowa
soyuwa a gareshi, haka zalika ba kowani mai 6ata miki ba ne mak’iyi a gareki,
ta iya yiyuwa kauna ke kawo 6acin ran, don haka ki nutsu ki gane.’’
Bintu na mai share hawaye sai gyad'a kai kawai ta ke. Inna
Salti na mai nisawa ta k’ara da
‘’Ki ji ki k’i ji, ki gani ki k’i gani, ki iya harshenki,
hatta bangon fada kunne gareshi, ki kyautata dangantakarki da kowa, ki sa Allah
a ranki, ki yawaita addu'a da zikiri, ki kasance mai yawan zama da alwala, shin
kin iya azkar?’’
Bintu ta girgiza kai alamar ah ah,
Inna Salti na mai gyad’a kai ta ce
‘’Zan yi k’ok’arin sawa a koya miki kan a kai ki ga
Fabarusa, ki na yi safe da yamma, ni ma da kika ganni anan addu'a ce da
tawassali ga Allah kad’ai ke zaunar da ni a wagga Masarauta bare kuma Masarauta
mai girman gaske kamar Fabarusa.’’
Jakadiya ce ta shigo, yayinda ta zube gaban Inna Salti cike
da girmamawa duk da dai ba yin Inna Salti ta ke ba, ba ta yi mata kyauta da cin
hanci kamar sauran matan Sarki.
‘’Barka da hantsi ranki shi dad’e.’’
‘’Barka dai Jakadiya, na sameki lahiya?’’
‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e.’’
Kana Inna Salti ta maida dubanta ga Bintu ta ce
‘’Inaso na san adadin bayin da za su bi Bintu Masarautar
Fabarusa.’’
Jakadiya na mai gyara zama ta ce
‘’Akwai Ladiyo da Kyallu, wanda Gimbiya Binta ce ta za6esu
da kan ta....’’
Jin haka sai da Bintu ta d’ago ta dubi Jakadiya cike da
fad’uwar gaba, don kuwa ta san hakannan siddin Gimbiya Binta ba za ta ta6a za6a
mata kowani abu ba, muddin ba sharri ba ne. Ita kuwa Jakadiya da ba ta san ma
ta na yi ba, ba ta gushe cikin jawabinta ba
‘’Sai kuma Uwanini, amintacciyar baiwar Yarima Nuhu wanda
shi da kansa ya buk’aci hakan.....’’
Ihu ne kawai Bintu bata kurma ba jin wannan masifar da ake
shirin had’a mata, maganar Inna Salti ne ya d’an kwantar mata da hankali, jin
ta ce
‘’Ita fa Bintu? Shin an tambayeta ko ta na da baiwar da ta
ke son tafiya da ita?’’
Jin haka Jakadiya ta kai kallanta ga Bintu, ta ce
‘’Bintu shin ko kina da wannan buk'atar gide? Wa ki ka za6a”
Bud’ar Bakin Bintu sai cewa ta yi
‘’Innata, dan Allah a tafi da Innata’’
Jakadiya na mai girgiza kai ta ce
‘’Innar ki gobe goben nan za su yi bulaguro zuwa marad’i
bisa ga umarnin Babban Bijimi, har sai an sami lafawar al’amura za su dawo, sai
dai fa ki za6i wata baiwar.’’
Nan da nan Bintu ta fashe da kuka jin Innarta za su bar
gari, Inna Salti ta fara k’ok’arin rarrashinta Jakadiya ta ce
‘’Ai da kin kyaleta ranki shi dad’e, abun ga ne ya zo ga ma
su shi, kukan amre da sallallami '’
Inna Salti ba ta fasa rarrashin Bintu ba, har ta samu ta
d’an yi shiru kafin ta k’ara bata za6i, inda ta za6i aminiyar Inna kuma
mahaifiyar k'awarta Cangwai, wacce aka fi sani da Maman Cangwai.
Da yammaci Inna ta zo mata sallama d’auke da su langar tuwo
da miya, da humra da turaren wuta. Tun zuwanta Bintu ta ke kuka, har yanzu da
Inna ta ke mata jawabi kamar haka
‘’Bintu kar ki damu, wani hani ga Allah baiwa Bintu. Ki yi
addu'a Allah Ya sa hakan da ya zo mana shi an alkahiri, ina so ki sani Allah ne
ya za6a miki wagga rayuwa da za ki shiga, ki sa Allah a ranki shi kad’ai zai
miki gata.’’
Bintu ta gyad’a kai alamar toh.
‘’Duk da amren ga ba a san ranmu za a yi ba, ki na jinin
barebari ba zan bari ki tafi haka ba, wagga(ta nuna kwalaban turarukan da ke
aje gaban Bintu da yatsa) tun kina shekara biyar a duniya na had’a mi ki su na
binne da niyyar sai amrenki ya tashi na hak’o, wannan kuma langar tuwo da miya
da cokali da ludiya wanda na fara miki taro ne, duk da dai na san ba lalle ba
ne a bari ki tahi da su ba, gashinan dai na baki a matsayin uwa, na hita
hakkinki.’’
Bintu na kuka ta ce
‘’Wallahi ba na so! Ba na so Inna! Inna makaranta na ka so,
dan Allah Inna ki taimaka kin ga dai sati uku ya rage mu koma....’’
Rungumeta Inna ta yi cike da tausayawa, Allah kad’ai yasan
iya adadin lokacin da su ka d’auka a haka, kafin Bintu ta zame jikinta daga na
Inna, kayanta ta nufa ta na mai bincikawa, nan ta fito da turarikan da Aisar ya
bata, ta dawo ta durkusa gaban Inna, ta na mai mik’a mata ta ce
‘’Inna ga wagga, dan Allah ki kar6a ko da kuwa ba za ki yi
amfani da su ba, wannan kyauta ne tsakanin uwa da d’iyarta, dan Allah Innata,
wagga shi ne kad’ai abunda na mallaka nawa na kaina’’
Hannun Inna na rawa ta kar6a ta na mai fad’in
‘’Allah Ya sadamu da alkhairinsa d'iyar arziki, Allah ya
sada mu ko da a darussalamu ne, saduwa ta alkahairi......’’
Kuka ne ya su6ucewa Inna, nan su ka yi mai isarsu, har dai
Inna ta ga abin ba na k’arau ba ne, dakyar ta janye jikinta ta fice ta na jiwo
kukan Bintu.
Yarima Nuhu kuwa har da jinya don kuwa babu yanda baiyi ba
na ganin an fasa aurennan amma abu sai dad'a kankama ya ke, haka kuma ya so
k’ara ganin Bintu amma Jakadiya ta k’i. Ta wannan dalili ya sa ko ganin Gimbiya
Binta ba ya san yi, don kuwa ba zai manta da asarar da ta jawo masa da kuma
halin da ta sanyashi ciki ba. Haka kuma bai fasa zayyanawa amintacciyar
baiwarsa yanda ya ke san ta kula da al’amuran Bintu yanda zai kasance ba zai
cutu ba har ya samu ta dawo gare shi.
Ana gobe d’aurin aure da daddare aka yiwa Bintu k’unshi irin
na amare. Yanda ta ga dare haka ta ga rana, haka ma Yarima Nuhu wanda zazza6i
ya rufe har da k’arin ruwa. Aisar kuwa farin cikin zai ga Bintu ne ya hana shi
bacci, don da an bi ta tashi da tun aranar zai d’au hanyar Sa’ayrasa, sa idon
Junaidu da gudun sharrinshi ya sa ya hakura. Haka ma Yarima Barde wanda farin
cikin zai had'u da Gimbiya K'amariyya ya hana shi bacci, da ita kanta Gimbiyar.
******* ******
Washegari tun da sassafe Jakadiya ta sa Bintu wanka da wani
ruwan magani gudun kar bak'in da su ka zo daga Fabarusa d’aurin aure su buk'aci
ganin amarya, ko kuma Sarki Abdulrahman da kansa ya buk’aci hakan bayan an
d’aura masa aure da Bintu ba tare da an shiryawa hakan ba. Leshi fari kyal mai
adon koren duwatsu ta ce ta sanya. Farar alkyabba Jakadiya ta d’aura mata bisa,
da wani takalmi kore. Kai da ka ga Bintu ka ce d’iyar Sarkin ce, ita kanta
Gimbiya Binta da ta shigo ta gan ta sai da ta girgiza, ta kasa zama bare kuma
dama tunda Allah ya wayi gari ta ke fama da fad’uwar gaba na ba gaira ba
dalili.
‘Bangaran d’aurin aure kuwa, misalin sha biyu na rana tuni
babban masallacin fada ya cika mak’il da jama’a, mutan Fabarusa, Mai Martaba
Sarki Abdulrahman ya iso tare da tawagarsa, hakimai da dogarai, har da
‘ya’yansa biyu, Sadauki da na shi abokan, haka ma Barde da abokansa biyu, d’aya
taubashinsa(cousin) wanda ake kira da Yarima Jafar, sai kuma d’ayan mai suna
Khalil wanda ya ke babansa hakimi ne a Masarautar Fabarusa.
Haka ma su Aisar tare da Ministocin da su ka taho wakiltar
mai girma shugaban k’asa, sun sami isowa, inda aka musu mazauni daga cikin
Masallacin. Ba k’aramin kyau Aisar yayi ba, dan kuwa ado ya sha na burgewa
musammam saboda Bintu. Dokakkiyar shadda ce jikinsa, ruwan toka, ya sha d’inki
da aiki irin na manya, ga hularsa da takalminsa kalar zaran da aka masa aiki da
shi, wato ruwan toka mai turuwa, da ka gansa ka ga d’an manya masu ji da mulki.
Allah Allah ya ke ayi d’aurin auren a gama ya nemi Bintu don shi ita kad’ai ta
kawo shi cikin wannan taro, yak’i jinin taro saboda yanayin aikinsa.
Yarima Barde kuwa daga waje yayi zamansa, gudun kar ya shiga
ciki taro da turnak’in jama’a su hana shi ya fito da wuri don zuwa ga sahibibar
ta shi wato Gimbiya K’amariyya. Sanye ya ke cikin farar shadda d’inkin babbar
riga, ga rawani ya sha kai, ka ce za a kira shi Sarki ya amsa. Ango kuwa Sarki
Abdulrahman tare da hakiman sa da kuma su Sadauki suna daga cikin masallaci.
Dake taro ne na manya da Sarakuna, shaddodi kala-kala
tsadaddu ki d'aukar ido da kukama kalar kayan dogarai daga Masarautu iri-iri,
abun dai ba a cewa komai, don kuwa wuri
ya yi wuri, taro ya yi taro sai kamshi da kid’an algaita, kirari da kiran
lafiya na dogarai da marok’a ke tashi. Sarakunan yanki da sassa na cikin
jamhuriyyar Nijar babu wanda be sami halarta wajan ba, Sarkin Agadaz ne, Diffa,
Marad’i, Zindar da dai sauran su.
Daga cikin Masallaci aka fara abinda ya had’a jama’a a
wannan masarauta, wato d’aurin aure, in da aka umarci waliyin Ango da Amarya su
matso kusa. Waziri ne ya fito daga 6angaran Sa’ayrasa, Fabarusa kuma Sarki
Abdulrahaman ne ya nuna kan sa a matsayin waliyi.
Daga waje Khalil ne ke ta yiwa Yarima Barde hira, amma shi ina hankalinsa na
ga Gimbiya K'amariyya, Allah Allah ya ke a shafa fatiha ya tafi garera don jin
soyayyar ta ya ke har ransa, bare kuma yau gabar da ke tsakanin Masarautasu za
ta kau, za su yi soyayyarsu a zahirance ba tare da wani shakku ba. Jin an shafa
fatiha Yarima Barde ya tashi ya na mai fad’in.
‘’Alhamdulillah tunda an amra sai ku tashi mu tafi ko?’’
Har Khalil da Jafar sun tashi, tuni su ka tsaya cak jin
marok’a na fad’in
‘’An d’aura auren *Yarima Abubakar BARDE* tare da *Gimbiya Fatima* akan sadaki (50000
CFA)"
Yarima Barde da sam bai lura da abinda su ka ji ba tsabagen
hankalinsa ba ya wajan, a hasale ya kai kallonsa ga abokannasa ya na mai fad’in
‘’Me ku ke jira ne? Mu tafi, Allah Allah na ke na gana da Gimbiyata.’’
Su kuwa marok’a ba su fasa shela ba. Khalil ne yayi k’arfin
hali ya ce
‘’Da ma kai ne Barde?’’
Cikin rashin fahimta Barde ya ce
‘’Ni ne wa?’’
‘’Angon da aka amrawa amren.’’
Jafar ya bashi amsa a tak’aice. Kai Yarima Barde ya girgiza
cike da murmushin irin ban son rainin hankali fa. Khalil ya ce
‘’Saurara ka ji Barde’’
Nan kuwa muryar wani marok’i da ya zo giftawa ta dafda su ya
doki kunnan Barde, fad’i ya ke
‘’An amra auren Yarima Abubakar Barde da Gimbiya
Fatima....’’
Nan ya ya tsaya cak tamkar wanda aka zarewa rai, su kansu
abokannasa sun girgiza kwaran gaske.
Daga cikin masallaci, ana gama d'aurin auren, inda kowa ya
ke mamakin sauyin al’amura da aka samu, musammam jama’ar Sa'ayrasa, shi kuwa
Aisar tunanin hanyar fita daga cikin jama’a yake, domin zuwa neman Bintu ba
tare da Junaidu ya ankare ba. Bayin Sa'ayrasa ne d’auke da farantin goro da
alawa, su ke bin kusirwa kusirwa in da suke mik’a farin tin jama’a na d'iba san
ran su.
Bawan da ya zo kusurwar da su Aisar su ke, Aisar ya fara
mik’awa, in da ya girgiza masa kai alamar ba ya buk'ata, har bawan zai wuce,
nan idanun Aisar su ka sauka bisa yatsun bawan, me zai gani? Zobensa da ya bawa
Bintu ne cikin yatsun na shi, bai ankara ba sai ji yayi Aisar ya damk’o
hannunshi, a tsorace bawa ya saki farantin hannun sa dan ko shakka babu ya san
tawagar shugaban k’asa ne gabansa.Hakan ya dawo da hankalinsu Junaidu da sauran
‘yan tawagar garesu. Aisar na mai duban idanun bawan ya furta
‘’Ina ka sami wagga zo6en? Menene dangantakarka da mai
zo6en? Ina Bintu d’iyar bayi?’’
Babban gida kuwa 6angaran Jakadiya, Bintu na zaune tare da
su Jakadiya sai ga Gimbiya K’amariyya ta shigo, ta yi kyau kwarai cikin jajayen
kaya, ta d’aura alkyabba ruwan zuma bisa kayan, ga bayi nan biye da ita. Ta zo
kar6ar mabudin wajan aje baki na musammam domin kar6ar Yarima Barde.
Ta na zaune ta na jiran Jakadiya ta shiga ciki dan d’auko
mata mabud'in, su ka ji an shigo 6angaren Jakadiya an gud’a. Tuni hanjin cikin
Bintu ya kad’a don kuwa ta san ta faru ta k’are an yiwa mai dami d’aya sata,
aure dai an aura. Tuni ta fashe da kukan da dama ya tsaya k’asan mak’ogaran ta.
Jakadiya ta fito d’auke da mabud’i, yayinda Ladiyo ta shigo
jiki na rawa, sai tafa hannu ta ke cikin salati da sallallami. Jakadiya ce ta
tambaya ko lafiya, yayin da hankalin kowa ya koma gareta.
Cike da ladabi Ladiyo ta durk’usa gaban Jakadiya ta na mai
fad’in
‘’Yau na ga lafiyar Allah Maigari gauro talaka da mata
hud’u.’’
Cikin k’aguwa Gimbiya K’amariyya ta ce
‘’Me ya faru ne Ladiyo?’’
‘’Wato Allah shi taimaki Gimbiya, ji da gani dai ba ya
k’arewa sai randa kurman bebe ya makance, Sarki Abdulraman na Fabarusa cike ya
ke da abin mamaki, wani lamari sai shi.....’’
‘’Yo to wani abin mamaki? Ya ce ya fasa ne?’’
Jakadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Kana Ladiyo ta ce
‘’Eh to ya fa fasa be kuma fasa ba, da ya tashi yin bazata,
sai ya amrawa d'ansa Barde Bintu.....’’
Hakan yayi daidai da ihun da Gimbiya K’amariyya ta kurma ta
na mai zubewa k’asa sumammiya. Nan da nan aka yi kanta. Bintu kuwa yanda
maganar ya doki kunnenta ta tabbatar ta zama kurma, don kuwa ba ta jin
hayaniyar da ake gabanta
‘’Ya amra ma d’an sa Barde Bintu....’’
Maganar da ke ihu jikin kunnenta kenan.
Tammat Bihamdillah
Nan na kawo k’arshen Bintu d’yar bayi ce kashi na farkon,
sai a dakace ni zuwa bayan sallah da rai da lafiya. Ina mai mu ku fatan yin
azumi cikin k'oshin lafiya. Dan Allah ku saka kawuna marigayi Alhaji Aliyu Abdullahi Sidi (A.A Sidi) cikin
addu’a, Allah ya ji kan sa da rahama.
Dan Allah yaushe ne xa acigaba da wannan littafin bintu diyar bayi
ReplyDelete